MAHADIN ZUCIYA CHAPTER 23 BY RABI’ATU ADAM SHITU

da zai jagoranci “yarsa ta yi ba daidai ba, abin da nake so dake ki daina ji daga waje…

“Ni ba za ka zo ka tsare ni da dadin baki ba, magana mu ke so mu yi da kai yarinyar da kake magana akan ta tana Zuwa tana gaya mana ba tana yi ba ne domin cutar da kai ko hada kiyayya a tsakanin mu da kai, tana so mu nusar da kai gaskiya. ne, kuma ita ce masoyiyarka ta hakika ta amince tana son ka za ta aure ka” Ya jingina da jikin bangon dakin “Mama…

Baban su ya kira sunan sa gami da kallon sa ido cikin ido “Mu mu kahaife ka, ka sani abin duniya bai tone mana ido ba, ka sa ni cewar baka da mata sai Zulaihat kuma bana so na kara ji ko ga ni ka kula wannan yarinyar na gaya maka”.Yana fadin hakan bai bari Umar din ya yi magana ba ya ta shi ya fice daga in da yake ya fita waje. Mahaifiyarsa ma tashi ta yi ta ce “Ko ka shirya ko baka shirya ba auren ka da Zulaihat mun saka ranarsa sati uku mai zuwa”

Kansa ya sara hankalinsa ya dugunzuma ainun. Mike wa- ya yi ya fita yana hanyar waje ya hadu da Khalil. Khalil din ma fuskarsa babu walwala “Yaya kana ganin irin hukuncin da..

Shi ne wanda ya dace da kai Zulaihat ta cancanci zama mata a wajen ka, tana son ka tana kaunar ka, tana girmama iyayen ka da kowa na cikin gidan”.

“Yaya yakamata ku nutsu ku hada hankalin ku waje daya, mene ne na yi muku da kuke bukatar sai kun sa na bijirewa bukatar ku, kowa yana bukatar rayuwa da wadda ya zabarwa kansa, me yasa kuke so ku cusa min abin ban kaúna.

Yaya ka yi magana da Baba hakan cutarwa ce a gare ni.”

Girgiza kai kawai yake yi yana dan murmushi “Gaskiya ne, gaskiya Umar ka samu kan ka, ka kai har matsayia da ~zabin iyayenka ya zama cutarwa don kawai kana da abin hannu. Kaico Umar, kaico”

Yana fadin hakan ya nufi hanyar cikin gidan Umar din yana Kwala masa kira amma ko juyo wa bai yi ya dube shi ba.

Da kyar ya wuce zuwa gidansa kwata-kwata bai ransa kai tsaye bangaren Zulaihat ya shiga ya kwankwasa mata kofa ta Bude, ta saka kidan turawa da kayan bacci a jikinta,

Ya yi mata kallo tun daga sama har Kasa. Sannan ya shiga cikin falon nata yana jinjina kai “Gidan mu gida ne da kowa yake sha’awa, ba a jin kaina ni da dan uwana, mahaifan mu ba sa tilasta mu yin abin da ba mu so ba, in har ba ibada ba ne, sannan basa dora mana nauyin da ba zamu iya yi ba, kullum cikin raha da dariya muke da mahaifan mu, amma yau na shiga gida dan uwana yana min gani saboda na samu kudi ne yasa nake kin yadda da bukatar su a kaina, mahaifina yana gaya min na bar abin da shine farin cikina, mahaifiyata ta gaya min za ta bani abin da bana so”.

Ya juya in da take tsaye tana binsa da kallo hankalinta a matukar tashe “Me ya kawo wadannan maganganu”

“Ke ce, ke ce Zulaihat, tamkar yar uwa kike a wajena, ban ajiye ki a bangaren da ba zan iya daukar ki ba, me yasa kike so ki hukunta kan ki da zabina a matsayin wadda zaki aura, me yasa me yasa kike so alaka ta dake da Kawun ki ta ruguje, kin yi haka ne da wata manufa, kina so Alhaji ya tsane ni, kina so iyayena su kore ni, kina so dan uwana ya dinga jin na sauya masa saboda na samu duniya, shi ne farin cikin ki”

“Umar baka fabime…

“Zulaihat kin kai ni mukura, sai dai bana jin zan iya daukar hukunci mai tsanani akan ki, to amma zan gaya miki cewar ki gyara tun kafin na dauki hukunci akan ki”

Yana fadin hakan ya fice daga cikin falo. Zube wa kasa tayi akan babbar kujera ta ci kuka ta Koshi, maimakon nadama saita fara cin alwalashin za ta iya kashe Yasmin dan dai tatsira da Umar.

Da sassafe ta tashi tana leken tagar ta tana jiran zuwan Yasmin don ta sanarwa da mutanen gidan su Umar, suzo su ga cewar bai daina kula ta ba, yadda suka yi. da Mama cewar duk ranar da ta Kara zuwa gidan sa ta sanar da su.

Yasmin kamar kullum ta shigo da kayan breakfast. Ta shiga ciki ta same shi babu walwala a tare da shi. Ta dame shi akan ya gaya mata damuwarsa.

“Yasmin wata alfarma nake nema daga wajen ki”

“Ka wuce alfarma ka yi min umarni Umar, shine abin da nake jira daga gare ka, me kake so na yi”.

Ya shaki iska gami da zura mata ido “Yasmin kin san babu wani abu da na fi kauna da ya wuce ganinki a kusa da ni haka ne?”

Ta jinjina kai amma cikin tashin hankali ta kasa dauke ido daga dubansa “Me ya faru na sani Umar kuma ka san na fi kowa sanin hakan”.

“So na ke ki dan ba ni lokaci”.

“Ban fahimta ba Umar, mun daina haduwa

“Yasmin ki fahimce ni”.Na fahimci ka Umar”.

Ta shi ta yi tsaye ta nufi hanyar fita daga dakin hawaye ke zuba daga idanuwanta ta waigo “Baka son gani na ina takura maka shi…

Aka turo kofa Yaya Khalil ne Mama. Mama ta kalli

Khalil shi ma ya kalle ta. Mama ta nufi Yasmin “Ban zaci haka daga gare ki ba, ban zata lalacewar ki ta kai haka ba kin cuci rayuwar ki, kin cuci rayuwarki, kin kashe kan ki da auren ki kina bin maza to ba zaki cutarwa dana rayuwa ba, ta raba shi da Allah da manzon sa, domin duk hannun da ya

taba matar da ba tasa ba, to shakka abincin wuta ne, sannan da ma ‘aiki zai yi shari’a da duk mijin da ya yi zina da matar wani. Ki je ki yi gararabbarki amma ba da da na ba”.

“Mama…

Ya yi min shiru, Mama ta fada a fusace tayi kanta za ta dake ta, Khalil ya rike ta.

“Ki fice ki ba ni guri kuma na rantse da bangiji na Kara. ganin ki a nan sai kin raina kan ki ballagaza Tinkiya”.

Hankalin Yasmin ya tashi Umar kawai take kallo da ya rintse idanuwansa. Ta nufi Umar din

“Kai kuma ka yi asara, duk irin tarbiyar da mu kakoya makake nan, irin tarbiyar da mu kakoya makake nan, ka zabe ta akan mu. To idan har nice na haife ka. Ban yafe maka ba idan har na Kara ganin ka da wannan yarinyar”.

Kalmar tayi masa tsauri bai san lokacin da ya mike a fusace ba “Mama wane irin kalami ne haka, me kike tsammanin don kin ganni da Yasmin, Mama ka da ki manta Kazafi ne muraran a bakin ki, kin jef.

Ta daureye fuskarsa da mari adaidai lokacin Yasmin ta kautar da kanta ji ta yi tamkar ita aka wanke da mari. Ta fice daga cikin gidan kai tsaye eikin tsananin fushi ido biyu suka yi da Zulaihat. Yasmin ta jinjina kai hawaye na ci gaba da zuba daga idanuwanta ta bar gidan ta koma gidan iyayenta ta shiga dakinta ta kwanta Kirjinta ya dauki wani irin, zafi zuciyarta tana bugawa da karfi.

Mahaifiyarta ce ta zo ta same ta a halin da take ciki a lokacin Yasmin ta gama shidewa bata ko numfasawa sai Asibiti. Mahafinta ya sanar da shi halin da Yasmin ke ciki a lokacin da yake dankwafe a office ya kasa tabuka komai. Ya isa Asibiti amma Kiri Kiri sucurity suka hana shi shiga daga Abbas, ya nuna musu hoton sa ya kuma umarce su da kada su bar shi ya shigo, duk rikicin Umar sai dai ya yi

Yana zaune a in da yake Alhaji Sunusi ya zo ya same shi Ya dafa kafadar Umar. Umar ya dago kai ya dube shi da sauri ya mike tsaye “Daddy”. Ya jinjina Kai Alhaji Sunusin ya yi ya ce “Kwantar da hankali, babu wani abu na tada hankali”.

Shi ma Umar din ya zauna jikinsa a sanyaye “Laifina ne

Dady, na kasa yiwa mahaifana magana sun kasa bani damar na sanar da su, Yasmin bata da aure yanzu, gani suke tamkar ina mu’amala ne da matar wani”.

Ka da ka damu, kamar yadda ita ma bata damu da hakan ba, tana maimaita irin dimbin alkairin Mama ne kawai ba wai tunanin abin da ya faru ba”.

Wani irin sanyi ya ji a cikin ransa “Ta tambayi ni”.

“Kai ne wadda ta fara tambaya, ka yi hakuri za ka shiga ka ganta bana so a yi hayaniya anan kamar yadda shi yake so.

-Yanzu ya batun mu, yakamata mu kara saka kaimi”.

“Sun gano gidan, zuwa uku basu same shi ba, amma an tabbatar musu cewar kullum a nan yake kwana”.

Alhaji Sunusi ya girgiza kai “Alhamdulillah, zamu yi mai yiwu wa a yau in sha Allahs”

“Insha Allahu”.

Abbas bai bar Asibitin ba sai da Yasmin,sallame su.

Umar na nan zaune suka fito ta shiga mota da kafafuwanta, Sun hada ido da shi ta yi saurin dauke idanunta. Ya ji dadin ganinta cikin Koshin lafiya duk wani abu da tasa rashin fahimta zata fahimta kuma zata samu farin ciki mai daurewa.

Tun da ya tafi zuwa yayi kawai ya hadu da ma’aikatan sa mutum uku daga cikinsu da ya saka su Aikin akan 

Hmmm