MAI TAFIYA CHAPTER 2

MAI TAFIYA CHAPTER 2

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ina mafita? A lokacin da babu mafita!4

Kano, Nigeria

Washegarin rasuwar Muhammadu Hindatu ta tattara na ta ya na ta ta koma gidansu, ‘Yanuwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ma ta gaisuwa.

Ta kudurce a ranta cewar idan fa bata nemi mafita ba to da daya da daya sai ta nemi ‘ya’yanta ta hange su a hannun mutuwa.2

To zaman gidan ma jiya i yau. Makauniyar uwarta na nan yadda take da kannenta gudu uku mata, sai ita cikon ta hudu da ‘ya’yanta biyu cikon biyar da shida wanda suka samu mazauni a dan tsukakken dakin mutum biyu. Maza yanzu ba sa son zawarcin mace mai ‘ya’ya in dai ba dukiya aka bar musu ba, don haka daga mutum ya zo daya, biyu sai ta ji dif.

Wani abu da ya fi daure ma ta kai da kuma ba ta haushi bai wuce gani ganin da kannen nata ke ma ta ba suna ma kallon wacce ta zo ta takura musu. Wani mugun raini ne ya shiga tsakaninsu kamar wacce kan ta aka fara zawarci. ‘Ya’yanta sai suka zama ganguna sai dai ka ji tim! An kai musu duka ba gaira ba dalili.12

Lokacin da tana gidan Habu tana ‘yar sana’arta ba ta taba zuwa gida ba tare da ta ruko musu dan wani abu ba don haka anti sama anti kasa. Amma yanzu da suka gama gano ba ta da wata mamora sai kawai aka guntule antin aka yar a juji ake kiranta Hindatunta sak.8

Ranar wata Alhamis ana kiran sallar La’asar Hindatu na alwala a bakin rijiya, kanwarta mai suna safara na zaune a bakin kofar daki tana cin taliya da manja. Can kamar an koro Abba ya shigo a guje da gare-garensa daga kofar gida. Sai ya tsaya cak a gaban Safara ya kura ma ta ido saboda yunwar da ke addabarsa . Ta kai lomarta ta hudu kenen ta ankara da shi ta ko galla ma sa harara ta ce

” Uhun..ya na ga kana kallona kamar ni na kori ubanka?”1

Hindatu ta dago kai daga alwalar da take tana so ta gane abunda yayi zafi har safara ta jefi Abba da magana irin wannan. Ya kalle ta bayan yayi narai narai da ido ya ce ” Anti Safara yunwa nake ji in zo in ci?” Bai karasa ba ta ce a fusace

” Ca akai maka ta ubanka ce?! Ku ji ni da tsinannen yaro” ta mika hannu ta rankwashe shi.

Hindatu kamar ta share amma sai ta tuna anyi haka ya fi a kirga. Sai ta ce2

” Safara kan abinci ne kike zagi har da rankwashi? Ba dan ki ba ne”

Safara tayi caraf ta ce

” kut, ku ji Hinden nan. Yaro ba tarbiyya ba za a koya ma sa ba? Ko kuwa tambayar da na masa ce laifi? To karya na yi? Na ubansa ne?”2

“Da sauki tunda ubansa ya taba kawowa har kin ci kin goge baki” cewar Hindatu saboda ranta ya fara baci. Cikin rashin kunya Safara ta ce

” Kin ga Hinde, ba ni na kar zomon ba ratayar ma ba a bani ba. Kan Abba ne kike nema ki gayamin magana ko ni na ce ubansa ya gudu ya bar ki ba ci ba sha? Kawai kin zo gida kin cushe mana guri ke da ‘ya’yanki gayyar kwarkwata gayyar kudin cizo!”12

Hindatu ta katse alwalar da take ta iso inda da Safara take ta nuna mata dan yatsa ta ce

“Kar gigin tashen balagarki ya kai ki ki zageni don kin yi kadan kin yi tsararo. Gwara ni na auru ke ki gayamin karen da ya zo ya shinshina takalminki a tsawon zamaninki!”

Toh fa! Wannan magana sai ga harzuka safara har ta dangwarar da kwanon taliyarta ta mike daidai da tsawon Hindatu ta ce

“Na rantse Hinde da aure irin na ki billahillazi gwara na mutu ba mashinshini…auren wahala..auren bakin ciki!”

Ai kafin ka ce me Hindatu ta fizgo ta an fara dambe kamar wasu dadaddun abokanen hamayya. Abba ne ya tafi da gudu ya je ya kira uwar ta fito tana dogara sandarta. Ta daidaici inda take jin rubdugun damben ta kwada sandarta ta na cewa

” Ba ku isa ku saka min hawan jini ba don ba ni kadai na tara ‘ya’ya mata ba a layin nan”. Suka rabu aka mayar da yanda aka yi ,budar bakin uwar sai ta ce

STORY CONTINUES BELOW

“Um..um Hinde na fa fara gajiya da ke. Kafin ki dawo gidan nan salin alin muke zamanmu amma tunda kika zo fadan yau daban na gobe daban. Duk dai kan ‘ya’ya? Ni na ce , wai nan din gidan ubansu ne?”4

Wani abu ya taso ya daki Hindatu a zuciya ta ce

” Hajiya dan Abba ya ce zai ci abinci laifi ne? Yana da inda ya fi nan?”1

” Oho miki!” Ta fada da karfi, ba ya da dangin uba ne ko daga sama ya fado? Maza maza ki tattara su ki maida su dangin tsinannen ubansu don bazan iya ciyar da ke na ci da ‘ya’yanki ba. Don ban da ma kulafuci da rashin zuciya irin ta ki ubansu ya gudu ya bar ki amma kina nane da su. Sakarya kawai!”1

Tana gama fadan ta dogara ta shige dakinta tana mita.

Hawaye ne suka biyo idonta sai tayi sauri ta shige daki. Anan ma ta tarar da maryama kanwarta ta shuro ma ta kayanta ta tura su wani loko, ta ma shinfide katifa a gurin tana sharar baccin rana. Sai kawai tayi zaune kan tantagaryar simunti jin da tayi kan ta ya dau caji na wucin gadi. Ba ta taba tsammanin haka ba daga babarta to amma ko don yau da gobe? Dan yanzu a kalla tayi wata tara a gida ba kas ba as. Yaranta da ake ma ta gori ina za ta kai su? Yaya za tayi? Ina mafita?2

Abba ya zo ya jingina da kafadunta yana share ma ta hawaye ya ce

” Mama ki daina kuka. Anti safara ce ta dake ki ko? Nima idan na girma zan siyi bindiga na harbeta!”

Tayi sauri ta daki bakinsa ta ce1

” Ba a fadan haka ka ji ko?”

Ya gyada kan sa sannan ya ce

“Mama wai ina babanmu? In ji Anti safara wai ya gudu”

Ta tsura ma sa ido sannan ta janyo shi ta dora akan cinyarta a ranta tana juya abunda zata fada ma sa ta ce

” Abba ba ka san babanka ya rasu ba?”

Yayi narai narai da ido ya ce

” To mama yaushe zai dawo?”

Tayi murmushin karfin hali ta shafa kan sa ta ce

” wanda ya mutu ba ya dawowa Abba”

A ranar Hindatu ta sa zuciyarta ta kashe Habu!!5

Kwanaki suka cigaba da ja a haka ba wani canji babu isasshen abinci, ba sutura, yaranta ko makaranta ba sa zuwa. A wata ranar litinin a cikin irin ranakun da tayi Allah wadai da su ta dauki wata atamfarta hitarget da ta fara kodau ta sa. Ta ja hannun diyarta Asiya ta shiga makwabta kitso. Dowowarta gida ta tarar har an yi abinci an raba kanwarta sadiya ita ce da wannan aikin. Ta samu kujera yar tsugunne ta zauna tana yiwa Hajiya uwani sannu da gida.

Hajiyar ta ce

“Kin yi sauri, har an gama kitson?”

Ta ce

“Eh, ai babu layi”

Sannan ta juya kan sadiya da ke gugar kayanta ta ce

” Sadiya miko min abinci na, yunwa kamar za ta karasa ni”

Sadiya ta dago kai ta ce

“Au dama ba ki ci ba ki ka fita?”

Hindatu ta kalle ta a tsanake ta ce

” kamar yaya? Lokacin da na fita kin gama ne?”

” Cab! Ai kuwa rabawa nayi ba ke wallahi, ai na zata kin ci” cewar sadiya.3

Wani abu ya zo ma ta wuya ya tokare, wai sadiya kanwar kanwar bayanta ke neman raina ma ta hankali. Babbarsu na zaune amma ba ta ce komai ba, dama ta san ba zata tanka ba.Ta hadiye bacin ranta ta shiga daki ta dauko wata at
amfarta da take boyo tun barka muhammadunta ta kama Asiya suka fita.2

A bayan layinsu akwai gidan wata mata da sukai mutunci a tun zamanin tana budurwa ana kiranta hannatu. Hannatu gogaggiyar ‘yar kasuwa ce da ba ta rabuwa da mutane. Takan siya kaya irinsu atamfofi da lesina kuma takan siyar. Har ma akan yi gulmarta da cewar wai har ma kayan sata takan siya. Tun farko abunda ya dan kawo raunin kawancensu shi ne hannatu na da wayewa ta kin karawa idonta idon kudi ba magana. A lokacin sai Hindatu tayi tunanin ta kai ma ta atamfar nan ta siya ita kuma ta kashe larura da kudin.

STORY CONTINUES BELOW

Shigar Hindatun ke da wuya ta hango ta a zaune a tsakar gida an shimfida katuwar dadduma da kwanukan abinci akai. Sai dai kuma ba ita kadai ba ce kamar yadda ta yi tsammani akwai wata mace zaune a irin kujerar roba nan fara da kwanon abinci a hannunta.

Dukkaninsu auna karkashin bishiyar umbrella da ke tsakar gidan suna shan iska. Hannatu ta kama haba da alamun mamaki ta ce

” Wa na ke gani? Amma dai batan kai kika yi?”

Hindatu tayi murmushi a kunyace ta ce

” ba batan kai ba ne da kafata na zo”

Hannatu ta tabe baki ta ce

” Watanninki nawa a unguwar nan amma ko leke? Gaskiya ba ki da kirki”

Hindatu ta bata hakuri a wasance. Sai hannatu ta ce

” To ga kawata ba ku gaisa ba”

Hindatu ta waiwayo sai ta ji gabanta ya fadi. Zaune akan kujerar wata mace ce hamashakiya daure da wani leshi mai ruwan bula da ratsin fari fari. Daga ganinta ba fara ba amma ta yi wankan mai me tsada! Yan yatsunta tayi ado da zobunan gwal biyu, kan ta ba kallabi sai gashin dokin da aka kara ma ta ya sakko har gadon bayanta. Ba wata kyakkyawa ba ce sai dai daga gani kudi da gayu sun samu mazauni ba shakka. Duka duka ba zata haura shekarun hindatun ba a kallon da tayi ma ta, don haka sai ta jj wani abu ya darsu a ranta, ina ma ita ce ga juyawa talauci baya yanda bakuwar nan ta yi.

Suka gaisa faran faran da ita har hindatu tayi mamaki don ba ta zaci ire irensu da kallon irinta da fuska a sake ba. Matar ta janyo Asiya jikinta ta fara ba ta abincin da take ci wanan abu ya taba ta, dama an ce mai da wawa.

Nan take matar nan ta gama burgeta, ga kudi ga mutunci. Aka yi ma ta tayin abinci, ba ta yi fulako ba ta zauna ta nada anan kuma sai aka bude babin hira. Labari ta shiga ba su tiryan riryan tun daga gudun Habu har yau da aka ma ta rowar abinci. Anan ne bakuwar ta dubi Hindatu ta ce

” kin ga wannan duniyar? Idan ki ka biye ma ta ba ki tashi tsaye ba kina ji kina gani za ki koma abun tausayi.. ai ni tunda na ganewa duniya na sha maganin zama a cikinta.” Sai hindatu ta ji ta birgeta.

Anan ne hannatu ta ce5

” Wannan kawata ce Nusaiba amma Nusy muke ce ma ta. Tare mu kayi makaranta ita ma ta taba aure ta fito. In dai kika bi shawarata wallahi za ki ga haske, ba ke babu jaje”2

Hindatu tayi murmushi ta ce

“Allah sarki”

Bakuwar mai suna Nusy ta dubi Hi datu ta ce

” Ai kin ce kin yi diploma ko?”

Ta caraf ta cafe

” kwarai kwarai, tabbas nayi diploma a school of technology”

Sai ta fito da wayarta hindatu ta bita da kallo sanin waya sai wane da wane, ta lallatsa ta kara a kunne. A cikin wata irin murya da hindatu baga san mace na iya mallakarta ba ta ji Nusy ta na amsa wani da ake kira da yallabai. Mamaki ya cika ta wai dama idan ana waya da namiji har wata kwarkwasa ake? Da taga wai ba ganinsa ake ba.

Ta watsar da wannan tunanin, ita fa ba ‘yar gayu ba ce irinsu Nusy da suka goge da duniya, har me za ta adar? Can ta ji ta ce

” Ina mutuminka kuwa honourable?” Ba ta ji ansar da ya ba ta ba sai ta ji ta ce

” honourable na ka mana kana da wanda ya fi shi ne?” Sai kuma ta kyalkyace da dariya ta ce ” o’o o ‘o wannan karamar kwangila ce ma percentage din ba yawa ,na samo. Ba na ji yana cigiyar mai yiwa yara lesson ba? To ka ce ma sa ina da kawa idan zai taimaka ya sakaya ta” Sai ta ji ta kuma kwashewa da dariya a nishadance ta ce2

” a’a babu sim , ba ta hau network ba”9

Daga baya sai suka yi sallama ba tare da ta ji wata matsaya ba. Ta juyo ta kalli hindatu ta ce

” ki kwantar da hankalinki suna ma tare da wanda nake nema. Lesson ne nake so na samo miki na yaransa ko banza ai kya rage zafi kafin a samu mafita ko?”3

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin ta hada ido da hannatu sakai murmushi ba tare da hindatu ta lura ba. Tayi ta faman zuba godiya. Nusy ta ce ba komai. Har ma ta ce ta kwatanta ma ta gidansu in ya so duk abunda ake ciki za ta gaya ma ta. Hindatu ta kwatanta.

Hindatu tayi ta kirgen kwanaki ko za ta ji da ga Nusy kwatsam ranar sai ga ta. Yau kuma wata tsaleliyar atamfa ce a jikinta wacce aka gutsittsira aka ma ta dinkin fan darinki tsirara. Hindatu ta lalace a kallon gayu irin na ta in ka kalle ta kamar zinariya caa cas gwanin sha’awa a idon Hindatu. Sai dai a ranta tana mamakin shanawar Nusy da tunanin wata irin sana’a take haka mai kawo kudi. Ta share wannan tunanin ganin ba wani abu ba ne da ya shafe ta . Daga nan Nusy ta ce ta zo su je ta nuna mata gidan da za ta yi aikin lesson domin an dace an samu aiki. Murna kamar za ta kashe hindatu!3

Ba ta tsinke da al’amarin Nusy ba sai da ta ga sun doshi wata tsaleliyar mota. To sai fa ta fara jin dari dari a ranta tana jin cewar Nusy din ta fi karfinta. Ta jingina kan ta a hankali tana shakar sanyin ac da kamshin air freshner din da ke manne a motar. Ta dunga rayawa a ranta, ina ma ta ta ce tana murza ta aka titi.. ai da ba karamin morewa rayuwa ta yi ba.

Hindatu ba ta ankara ba ta gan su a gaban wani tangameme gida wanda ya isa a ma sa lakabi da huce haushin duniya. Nusy ta kalleta ta ce

” Nan ne gidan honourable. Nayi magana da shi mun zartar za ki dunga zuwa kina yiwa yaransa na primary lesson na maths da english a wata za dunga biyanki dubu goma. Ya kika gani? Ya miki?”

Cikin tsananin farinciki ta ce ” dubu goma fa kika ce? Anya kin ji da kyau? Ba ga masu NCE ma da ke koyarwa a firamare ba sa daukan hakan a wannan zamanin”

Nusy ta kyalkyace da dariya har da buga sitiyari ta ce

” ke hindatu kin san wanenne honourable kuwa? Kin san mahaukatan kudaden da ya mallaka?Yayi shekara takwas yana dan majalisa banda manya manyan kamfanonin da ya mallaka. Kuma fa ta hanya ta ki ka biyo, aminin yallabai di na ne kut da kut, don haka ko dan ni zai iya miki fin haka. Ke dai ki bi yanda na ce billahillazi halin da ki ke ciki sai dai ya zama labari.1

Hindatu ta jinjina kai hankalinta yayi mugun kwantawa da Nusy. Ba ta gudun talakawa don haka ta yarda mai kaunarta ce. Ta fara yarda shawarwarinta abun bi ne don ga shi har ta fara ganin haske. Nusy ta maida hindatu gida ta ajiye suka yi sallama.2

Bayan rabuwar ta su ne ta daga waya ta kira yallabai suna ta dariyar Hindatu.

Ta ce ” ina sane na bi da ita a haka ai sabuwar hannu ce. Kai yanzu idan na fito baro baro na gaya ma ta ai ba za ta yarda ba. A bar ta ta fara lesson din, daga nan ai shi ya san abun yi”

Ba a wani dade ba Hindatu ta fara aiki a gidan honourable, ba ta san sunan shi ba ba kuma ta damu da ta sani ba. Bai fi sau biyu ta hadu da matar gidan ba huldarta tsankaninta da yaran ne. Da karshen wata ya zo wani mai kula da harkokin gidan ya zo ya ba ta albashinta dubu goma cas! duk da rabin wata ta ci. Murna kamar ta yi me. A satin ta yiwa yaranta rijista a wata makarantar kusa da su. Har ta dan fara murmurewa, wannan muguwar kamar ta tsananin yunwa ta fara barinta. Har abada hindatu ba zata manta da Nusy ba, tana daya daga cikin mutane masu abun hannunsu da ba su kyamaci talaka ba. Daga nan sai kawancensu ya koma na kut da kut.

A yawancin labaran mutanen duniya akwai wata kebantacciyar rana da za su iya ma ta lakabi da ‘azal’ to wannan rana ba ta wuce ranar da ta yi
ido biyu da honourable A B Kankiya ba! Shigowa yayi har inda suke lesson, kallo daya tayi ma sa shekarunsa ba za su wuce hamsin ba amma jin dadin rayuwa ya boye. Jallabiya ya sa fara ya aske kan sa amma hakan bai hana nuna tsilli tsillin furfurar da ke barazanar mamaye kan ba.

Honourable AB Kankiya ya kurawa Hindatu ido yana jinjinawa Nusy da iya aiki da sanin irin kalar macen da ta dacewa sha’awarsa. A karo na barkatai ya ji ya kuma kamuwa da wata irin jaraba da ya kwana biyu bai ji ta ba. A sakwan goma sha biyar ya nakalci halittarta irin nakaltar da ko ita ba ta yiwa kan ta ba!3

STORY CONTINUES BELOW

Baka ce don ko da can Hindatu ba ta yarda da shafe shafen zamani ba. Komai na fuskarta kadaran kadahan ne ba zaka ce da ita kyakkyawa ko mummuna ba. Sai dai wani abu da ita kan ta ba ta sani ba shi ne kyawunta jiki yake don a cikin mata kafin a samu mai kyaun kirarta za a dade. Tsawonta madaidaici ne hakannan da ya kalli idanuwanta sai take tuna ma sa zamanin da yayi wata budurwa ‘yar kasar ethiopia jamaima, idanuwanta kamar mai jin bacci. Karshen magana sai ya hango wata wushirya a hakoranta abinda yake matukar birge shi a mace, nan fa sai kan sa ya dau caji!4

Ya matso kusa da ita yana mai mika hannu a turance ya ce

“Nice to meet you”

Sai ta ji banbarakwai namiji da suna hajara. Ita fa bata saba da irin wannan wayewar ba don haka sai ta noke ta gaishe shi da fatar baki a matsayinsa na wanda ya ceto rayuwarta daga haula. Yayi murmushi, ya riga ya gane ba ‘yar hannu ba ce, da sauranta . Su kayi gaisuwa irinta al’ada ya fice.

Bayan kwana uku da faruwar hakan Hindatu ta taso daga aikinta tana neman tare dan acaba da misalin karfe 5 na yamma. Ba ta wani dade ba sai ga wata mota rantsetsiya baka wuluk gilasanta masu duhu ta tsaya a gabanta. Ta dan ja da baya a tsorace. A hankali aka saukar da gilas na bangaren mai zaman banza sai idonta suka kallo ma ta ubangidanta yana doka ma ta murmushin rashin dalili.

Suka gaisa ya ce

” malama Hindatu ya na ganki a tsaye anan?”

Ta ce

” yallabai ina neman abun hawa ne zan wuce gida”

Ya ce

” Au to in dai haka ne shigo mana na kai ki, nima zan fita ne zan yi wani dan uzuri.”

Sai ta ji gabanta ya fadi har shi ma ya lura da hakan, ta dan ja da baya ta ce

” Aa ba komai zan ma hau achaba na gode”

Honourable ya dan gintse fuska nuna alamun rashin jin dadi ya ce

” Haba, haba ai ko ba kya aiki a gidana ke kawar Nusy ce don na rage miki hanya ba wani abun ba ne.”

Ta dan yi jim, in ta ce bata shakkar honourable tayi karya. To amma kuma fa tana tsoron kar ya ga kamar ta yi ma sa raini a matsayinsa na babban mutum kar a je hakan ya sa ta rasa aikinta. Duk da hakan ta ce

“Wallahi nagode, ba wani nisa gareni ba”

Ko bai ji me ta ce ba ko kuma ya ji ya share ne kawai don bude motar yayi da nuna alamun ta shigo kawai. Cikin dan jinjinawa ta shiga lintsimemeiyar motar, direba ya ja suka bace daga unguwar.

A hankali ta dunga yiwa direban kwatance har bakin lungunsu. Ta dan kaikaici ido ta dubi honourable sai ta lura unguwar yake karewa kallo a tsanake kamar mai kirga adadin bolar da kwatocin da suka zagaye gurin. Ya dan kalle ta da murmushin da ya zame ma sa jiki ya ce

“To ina ne gidan naku?”

Jiki a sanyaye ta daga dan alinta na nuna wani gida a farkon layi mai kofar karfe da tayi tsatsa. Ta fito a hankali daga motar a ranta tana sake sake ya miko ma ta kudi dauri guda ‘yan hamsin hamsin. A cikin wata murya da take nuna hakan ba komai ba ne ya ce

“To malama Hindatu ga wannan kya dan rage wani abun ko?”

Hindatu ba yarinya ba ce. Idan ta ce wadannan halayen da yake nunawa ba su daure ma ta kai ba tayi karya. Don haka tayin farko ta ce

” A’a nagode da ka kawo ni gida ma yayi”

Ya ce

“Shin malama Hindatu ko kina tsoro na ne? Naga kina dari dari kamar zan cinye namanki danye. Wai ko dai Nusy ba ta miki bayanin ya muke ba ne?” Ya karashe yana dariya dariya. Ambatar Nusy sai ta mika wuya. Sai kuma ranta ya fara tariyo mata irin larurin da zata kashe da wannan kudi. Kawai sai ta karba ta soke wani sashe na zuciyarta na gaya mata watakila yau dai ranar juma’arta ce.1

STORY CONTINUES BELOW

Me zai faru? Sai rage ma ta hanya da kyautar bazata ya zame wa honourable wata al’ada kamar cin tuwon dare. Ranar sai ta wuce gidan Nusy ta labarta ma ta abunda ke faruwa. Sai ta nuna mata hakan ai ba komai ba ne in dai ta dubi yanayin arzikinsa. Sai ta nuna mata watakila ma zawarcinta ya ke son yi idan aka dace sai tayi aurenta ta huta.

To dama Hindatu nema take sai kuma masoyiyar zuciyarta ta cigaba da raya ma ta Allah ne maji rokon bawa ya aiko ma ta tsuntsu daga sama gasasshe, shin mai zai hana ta sa hannu biyu ta karbe?5

Da wasa wasa ta gane dai mutumin son ta yake, manufar son wannan ne bata waye da shi ba. Mu’amalarta da shi ba karamin dago tattalin arzikinta yayi ba. Har abun ya zamana cewar wata baya karewa ba tare da ya juye kayan abinci da kudi a gidansu ba. Ba ayi tsawon wata biyu ba ta ji ya tsaya ma ta a rai yayi kane kane. Aka fara soyayya ta ban mamaki!

Wani abun mamaki shi ne ba ta taba ji yayi maganar aure ba ko me ya sa? Ga shi ta saki jiki da shi abu kadan sai kamo ta ko ya rungumo ta abinda ba ta saba ba amma kuma ta kasa hana shi. Ba don komai ba sai don tana tsoro kar komai ya tarwatse. Sai karin abun Nusy na kara zugata har takan ma ta nuni da cewar ko fa bai aureta ba to ta lashi banza. Ya kuwa za a yi ta bar banza ta wuce daga baya ta zo tana da na sani? Mafarin tunaninta kenen kuma mafarin tarwatsewar rayuwarta!16

A wata rana ya dauketa a mota ya kai ta wani wajen shakatawa da ake yayi a lokacin mai suna see sweet. A ranar ya dalle ta da sabuwar waya wacce ko baza gari ba tayi ba. Kan hindatu ya fashe yau ga ta da waya wanda sai a hannun wane da wane. Gaskiya yallabai na ji da ita!

Tunaninta ya katse ne a lokacin da ya ce yana bukatar ta ma sa rakiya zuwa Abuja suyi kwana biyu rak a hotel din Nicon Hilton don wani aiki da zai kai shi. Sai ta kwalalo ido a birkice ta ce

” yallabai wai ka zata ni karuwa ce?”3

Ya gintse fuska kamar ba shi ne ma’abocin fara’ar nan ba ya ce

” A tsammanina ina da matsayi a wurinki da kowacce irin bukata za ta samu gurbi to ashe ma ba haka ba ne. Ashe ni haukan banza ma nake ba so na ki ke ba”

Jikinta yayi sanyi ta ce

” kayi hakuri, gaskiya bazan iya ba. Don Allah ka bar maganar nan”

Ya kalle ta da wani irin duba mai wuyar fahimta ye ce

” Au hakane? Ashe da gaske ne da aka ce yawa yawan mata mayaudara ne. So kawai suka sani a baki, amma a zuciyarsu akasin hakan ne. Nagode da kika nunamin haka hindatu”.4

Har ta koma gida kalamansa suna ma ta yawo a rai. Rabuwa suka yi baram baram ta ce ta hakura da shi tunda tsarin rayuwarsu bai zama daya ba. Sai ba ta doshi wajen aikinta ba, to me za ta je tayi?

Abubuwa suka fara ja baya ta ga da gaske dai nema take ta koma rayuwarta ta baya. Tana cikin tsammanin warrabuka sai ta ga bari ta je gidan Nusy don tun bayan rabuwarsu da honourable ta daina daga wayarta. Ta kalle ta shekeke ta ce

” Arziki na bin ki kina gudu. To menene don ya bukaci ki masa kwana biyu? gutsirarki zai yi?1

Ba tun yau ba Hindatu ta gane Nusy cikakkiyar yar tsalle tsalle ce, a gidan kanta take zaune wanda wani maneminta yayi mata kyautarsa sukutum! sai dai taimakon da tayi ma ta ya sa ta kasa rabuwa da ita.

Ba ta ce komai ba har ta bar gidan tana tunani. Ta iso gida rai a bace sai kuma me? Kofar gidan ta gani a cike makil an yi cirko cirko, abinda ya zo ranta kawai babarsu ce rai yayi halinsa.


To amma sai ta dauke wannan tunanin daga ranta bayan ta hange ta a bakin rijiya da sauran mutane ana ta zabga salati. A kidime ta karaso dan ta tantance wannan alamari. A cikin jimla da ba ta wuce biyu ba kanwarta sadiya ke labarta ma ta wai Abba ne safara ta ba shi guga ya debo ruwa sai ya tsunduma rijiya! Amma a halin da ake ciki wani dan unguwar da ya iya ruwa ya shiga ciki ya tsamo shi.!

STORY CONTINUES BELOW

Wani irin zaman ‘yan bori ta yi ta dora hannu aka ta na rusa ihun mutuwa. Wai sai yaushe mutuwa za ta daina yi ma ta wafci daidai? Ta ga hakan ba zai ma ta ba kawai sai ta cakumo safara tana ma ta dukan shan gishiri! Duk yanda aka so a raba wannan mugun fadan bai rabu ba sai da aka tsamo Abba ranga ranga. Wani tsoho ne ya ce

“Yaron nan bai mutu ba, ayi sauri a kai shi asibiti”

A ka dunga dannawa cikinsa ruwa na fita har ya ja wani irin dogon numfashi. Nan take ya sume. Nan aka dauke shi sai asibiti don karaya ma biyu ce a jikinsa.1

A wannan dare barci bai ko ziyarci gurbin idonta ba tana tsaye a harabar asibiti tana jiran sakamako. Sakamakon bai yi mata dadi ba ba kuma wai don Abba ya rasu ba sai don ana bukatar zunzurutun kudi har naira dubu dari da ashirin na gado da aikin da za a masa.

Wani jiri ta ji yana dibarta tana jin kan ta a gajimare. Sai ta daidaici wani dan benci tana kukan mutuwa. Wai me yasa mutuwa bata da alkawari ne? Tana ce a bayanta ta suri muhammadunta shi ne yanzu za ta sure mata Abba? Hankalinta bai kara tashi ba sai da tayi ido biyu da dan na ta yana wani irn kukan ban tausayi ya ce4

” Mama ni ma mutuwa zan yi irin babana? Ba zan dawo ba?”

Daga wannan kalaman na Abba Hindatu ta san dayan biyu. Ko gangar jikinta ko lafiyar Abba!1

Gidan Nusy ta wuce ita kadai gareta ta labarta ma ta yanda ake ciki. Ta ce

” Ya salam Hindatu..ga shi kin zo bani da kudi. Yau da Naira dubu na tashi kacal!” Fuskarta dauke da damuwa.2

Hindatu ga fashe da kuka tana rokonta irin rokon nan na rashin madogara Nusy ta rungume ta ta ce

“Kuka ba zai yi magani ba ina ga kamar muna da mafita”

Hindatu tayi sauri ta ce

” ya kike ganin za a yi?”

Ta ce

” Honourable kadai zai iya fidda ke. Kin ga masoyinki ne ke ce dai kika ki shi”

Tayi shiru

Nusy ta ja tsaki

” Ai kin ga irin matsalarki kenen. Ga yanda za a yi sai a bar yaro ya mutu? Ba ga waya ba mu daga mu kira shi na san zai taimaka.”1

Wata zuciyar ta ce wa Hindatu a kul, dayar na gaya mata faretin da mutuwa take a kusa da Abba. Ta ce ta amince. Aka kira shi Nusy ta masa bayani. Akayi rashin sa’a ba ya gari. Amma ya ce a ba Hindatu wayar. Ya ce

” Hindah wannan fa ba wani abun damuwa ba ne in dai kina tare da ni to baki da matsala. Ki kwantar da hankalinki kin ji baby na. Gobe karfe 11 zan iso kano inshallahi za ayi settling komai, zai samu lafiya kin ji Hindah na?” Ya karashe a wata yaudararriyar murya ta wadanda suka goge da duniya.15

Washegari kuwa bai saba alkawari ba yana dira ya dauketa suka wuce asibiti. Kafin ka ce me har an shiga da Abba dakin tiyata. Wani irin kwanciyar hankali ya mamaye Hindatu sai ta ji kamar Abba ya warke. Tayi ta zubawa honourable godiya. Ya kamo hannunta yana murzawa ahankali ya ce

” Hindah, ai ni ne da godiya” ya daga ma ta gira2

Ta zame hannunta a hankali ta jingina kai a jikin bango, ba ta ce komai ba.

Aka fito da Abba aiki yayi kyau. Sai jiran warkewa kawai. Bayan kamar sati da aikin honourable ya zo Hindatu na zaune a kujerar roba kusa da gadon Abba shi kuma ya samu bacci. Ya kura ma ta idanu kamar tsohon maye ya ce1

” kina ta min yanmatanci ko? Wai..me yasa mata duk girmansu sai sun ja aji? Yau ma ba za a mun rakiyar ba ne?”

Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta ce a kasalance

“Idan kuma yaron ya tashi fa?”

Ya kalleta shi ma a kasalance ya ce

” wannan din shi ma duk yanmatancin ne”?

Murmushi yayi yana karkada yan mukulli ya kara da

” ina jiranki a mota”

Ya wuce abin shi.

STORY CONTINUES BELOW

Wata nurse ta bawa amanar Abba da cewar za ta je ta dawo. Ta fita kamar kwai ya fashe ma ta a ciki.

Da ya dauki Hindatu a mota bai zarce koina ba sai Hamdala guest inn. Ya kama daki mai lamba 9. A cikin kalaman kwantar da hankali da alkawurra da dama ya samu ya cika burinsa a kan ta!6

*****************************

Tana zaune a kujerar gaban mudubi tayi tagumi ba kuka take ba, zuciyarta ta kangare. Mamakin kan ta take, wai yau itace a hotel da wani kato ta kwana da shi?! Shin wai shikenen ta maida kan ta karuwa? Ashe karuwanci ba wuya gareshi ba fadawa cikinsa farat daya ne? Ta ayyana a ranta, tayi ne don ceto ran Abba daga yau ba zata sake ba. Sai dai abinda Hindatu ba ta sani ba shi ne, wannan ne mafarin aukuwar duk wasu al’amura da zasu gabata!

Ya fito daga bandaki daure da tawul a kugunsa. Ya cigaba da share kan sa da dan karamin yana mai kurawa hindatu ido zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama. Ya san Nusy ta san irin kalar matansa amma fa duk da haka ya sha mamaki! Shi ya sa Nusy ta dage da cewar ya nace ba banza ba , ai kuwa kamashonta daban ne. A tsarinsa macen waje duk haduwarta da ya kwana daya da ita to zai aje ta sai wata kuma. Amma alamarin yau yana ba shi mamaki yanda yake jin hindatu a ran sa.

In bai yi karya ba zai iya cewa duk matan da yake mu’amala da su bai taba haduwa da kamar hindatu ba. Da a tsarinsa zai jefar da ita yau kowa ya kama gabansa amma sai ya ji bai iyawa , Hindah din shi daban ce!3

Ya matso har inda take, a zare hannunta daga tagumi ya ce

” Haba Hindah, menene matsalar? Bai kamata kike damun kan ki ba. Ko kina so a canja ma sa asibiti?”

Haka dai yayi ta bi da ita har ta ware. Ya zaro wata brief case ya ciro damin kudi ya zira ma ta a hannu ya hada da na sa ya matse gam.

“Ga wannan” yace da ita “ki dan kula da kan ki don zan yi wata ‘yar tafiya zuwa japan gobe amma sati daya zan yi. Hope ba matsala? ” ta girgiza kai. A ranta tana ayyanawa ita da shi har abada. A rashin saninta shedan din da ke yawo a zuciyarta ya wuce duk yanda take tsammaninsa.

Dawowar da yayi ba su kare a koina ba sai a wani sabon hotel mai suna kings and queens, suka makance a cikin duhun jaraba. Ba ta iya ce ma sa a’a domin shi ma ba ya gajiya da share ma ta hawaye da abun duniya. A gidansu babu wanda ya damu da alamarinta in dai ta samu na kula da yaranta ba ta bar musu dawainiya ba to ba su da damuwa. Hindatu ba ta tsinci rayuwarta a koina ba sai a matsayin farkar honourable AB kankiya!1

Sun fi wata shida suna ta’asarsu son ran su sai ta yanke hukuncin bari ta tuntube shi da batun aure. To da yake dama harkar bariki shirme ce shi a lokacin bama a kan ta hankalisa ya ke ba. Don haka da tayi masa zancen aure sai ya kalle ta galala don shi tunda yake a duniya ma bai taba kawowa ransa aurenta ba. Ba kunya ya gintse fuska ya ce

” Haba Hindah, auren lafiya ana zaune kalau? Da me na rage ki da shi har kike hangen aurena zai sa ki same shi? Ka da ki katse mana jin dadin rayuwarmu mana a daidai lokacin da muke cin ganiyarta”

Ya rungumo ta tamkar wata jinjirar da yake so ya maidata cikinsa yana ajiye wani dalili daya tal a ransa da ya hana yayi mata barin makauniya. Ta zame jikinta a hanakali a sanyaye, in dai ita ba sakarya ba ce ta san yaudarar kan ta kawai ta ke game da A.B kankiya. Ta san holewarsa kawai yake yi da ita amma me? Ita fa mijin aure take nema ashararancin ya isa haka!

Da dai ya ga tana neman botsare ma sa sai ya ji ran sa ya fara baci har ta kai shi ga cewa

” Ku fa ‘ya’yan talakawa ‘yan taka haye ne! Da kun ga mutum da abun hannunsa zai huce lalurarsa da ku sai ku ce sai ya aure k
u. An gaya miki na fito bariki neman aure ne? In je in nemi diyar mutunci mana idan auren zan yi!”7

Ba tayi kuka ba, ta wuce kuka da dadewa. Amma wannan wani irin cin fuska ne? Shin wai ba shi ke nemanta da lallami ba ta amince da shi ? Lallai an ci moriyar ganga za a yada korenta.2

Kamar kullum idan ta shiga damuwa gidan Nusy ta wuce ta labarta mata yadda suka yi. Nusy ta lailayo wani ashar!ta kyalkyace da dariya. Ta dubi Hindatu a sakarce ta ce

” Tun da nake a duniya ban taba ganin marar wayo irinki ba. Kin kasa fitowa daga akurkinki duniya ta san ki. Me aka yi akai Honourable me ki ka samu a duniya har da zaki maida kan ki baiwar wani ta hanyar aure? Me auren Habu ya kare ki da shi da kike marmarin kara wani? Ai hindatu yanzu ganiyar rayuwarki ta sako kai. Ki ajiye honourable kamar yanda za ki ajiye zanin daurawarki ki canja da mafificinsa! A duniyar nema shi ba komai ba ne! Da za ki bini a sannu ki hankalta da alamarin da zan zo miki da shi, to da ke da talauci sai dai kiji a labaran duniya!

Tayi shiru maganarta na samun gurbi a tata zuciyar. Ta dubi yadda rayuwarta ta canja a dan kankanin lokaci da ta samu kulawar naira. Maganar gaskiya ta fita cikin kunci da takura daga ita har yaranta. Ta yarda da maganar Nusy. Sai ta fara jin za ta iya komai saboda kudi!

Nusy ta ce

” Idan har kin amince kuma kina so kiyi fice, to akwai wata kungiya…….”10

Kun ji masomin labarin Hindatu.Yawon duniya mafarki ne, idan an je za a dawo.+

Saudi Arabia

A tsammanin Luba duk wanda aka ce ma ta ya tafi saudiyya to lallai kakar shi ta yanke saka domin arziki ne zai dangwala ya dawo gida yana gwalangwaso. Ga mamakinta sai ta ga ashe ba haka ba ne? Ashe rayuwar saudiyya rayuwace ta mai zaman kanta? Ashe gwagwarmaya ce kowa tashi ta fisshe shi?5

Har a kullum a gudu ka ke kar a kama ka a maida ka inda ka fito. Kullum sai ka nema zaka ci , za ka sha ka kuma tufatar da kan ka. Duk wannan wahala bai sa Luba ta rusuna ba har yanzu zuciyar na nan cike da buri. So take ta bunƙasa ta girma ta buwaya a cikin lamarinta. Rayuwa da babu kwabo rayuwace da ta gwammace mutuwarta da ta wanzu a cikinta. Ita dai kawai ta samu kudi tayi facaka ta more.

Ta cigaba da bin Hajiya ‘yar Sakkwato a sannu ba don ranta na so ba sai dan cewa bata da wanda ta sani sarai kamar hajiyan. To amma a tsarinta dama, za su raba gari da zarar ta samu mafita. Daga baya sai suka koma Madina kacokam inda Luba ta samu sanaar yin tuwon shinkafa, tuwon semo da miyar kuka.

Da ummara ko Hajji ba karamin ciniki suke ba saboda ‘yan Najeriya da basu waye da cimar can ba. A inda suke abinci akwai wata yarinya sa’ar Lubar sunanta samira ita kuma tana suyar dankali da kwai. A tun da can Luba bata son kawa a cewarta wai mata sun cika munafici da gulma. Amma ganin cewar samira tayi zaman shekara hudu a saudiyya ta fi ta wayewa sai tayi tunanin makale ma ta ko ta samu hanyar kubucewa Hajiya.

Samira wayayyiya ce asalinta yar cotonou ce yawonta ya kawo ta saudiyya. Da yake ita kuma luba duk inda mai wayo yake ta kai sai ta fara ma ta ladabin kare. Daga karshe sai suka kulla kawance inda samira ta yi ma ta hanya ta samu aikin wanke wanke a gidan wata balarabiya mai suna Ummu Rumana.

Aikin gidan larabawa wani irin aiki na mai tarin yawa. Ko ina so suke a gan shi fes fes, don Luba har tsani gareta na wanke bango. Ga wani irin wulakanci na nuna banbancin launin fata. Wannan abu ya isheta, ya ita da ta baro gida neman arziki za ta bige da wahala irin haka? Ba wuya kana aiki a gida maigidan ko yaron gidan ya neme ka. Ashe su ma lababawa mutane ne irin mu masu zuciyoyi da halaye irin namu?

A zaton ta idan aka ce balarabe ko wani iri ne to kankat kenen a kyawawan halaye. Ashe abin ba a haka ba ne a zuciya ne? Kes kes nawa ta gani na daga zuwa aiki maigida ko yaron gida ya bige da yiwa yarinya fyade? Wa ya isa ya bi ba’asi? To in dai haka ne mai ya sa suke kallonmu makaskanta? A ce wai har ta kai idan ka hada sawu da wani balaraben a masallaci don ayi sallah sai ya zame ya canja sawu wannan wace irin masifa ce?2

Ta sha canje canjen gidan aiki har ta gaji don kan ta ta dawo gurin Hajiya. Hajiyar ta karkace baki ta dun ga sheka dariya har ta yi ma’ishi kana ta nuna Luba da sabbaba ta ce

” Dan uwarki Lubabatu an ka hwadi miki ni assh shegiya? To bari in gaye miki da uba an ka haihe ni ba ‘yar kwararo ta ba. Yawon duniya ni niz zabe shi a karon kaina don shi ne mahita din haka ban ga dan kazar uban da zai koyan ba!”3

Ta cigaba da kura wa Luba mici micin idanunta ta karasa da

” Uwarki ma Tamadi na hi karhinta wallahi balle yarinya kankanuwa kamar ki!”

Kalmar uwarta da aka ambata ya mata ciwo amma sai ta danne tayi kus, ita fa nema take amma a kasan zuciyarta zagi kwando kwando take juyewa Hajiya. A fili kuwa sai ta ce1

” Hakuri fa za kiyi Hajiya ki daure ki tallafeni yanda ki ka daukoni a gaban uwata ki ka kawo ni uwa duniya, kin ga ai bai kamata ki guje ni ba”2

Hajiyar ta kalli luba tana mai mamakin ladabin harshenta ta ce

” Au ni na gguje ki? Ku ji ni da ‘yal tselan uwa!

Nan dai Luba tayi ta lallaba ta har dai ta amince zata taimake ta. Daga nan sai Hajiyar ta shigar da ita harkar goro shi ne suke zuwa jidda suke sarowa a hannun matafiya. Sana’ar kuwa ta karbe su Luba ta canza ta goge har larabci take ji. Sai dai kuma akwai wata a kasa, mazan da suke cinikayya da su ma fi akasari ‘yan Afrika Hajiya tana hada su da Luba suna nema. Fasikanci dama ba bakon Luba ba ne don haka za ni ce ta tarda mu je mu.1

STORY CONTINUES BELOW

Bayan kamar shekara biyu da zaman Luba a Madina kwatsam rannan sai Hajiya ta shigo ta tarda ta a dakinsu da daddare tana hada kayan siyarwarta. Daga zaune a gefe akwai wata yarinyar Hajiya mai suna Munari. Munari yar Adamawa ce bafulatanar usul ta cikin maye belwa don a hausarta ma zaka gane. Ta fi shekara goma a saudiyya. Ba su cika shiri da Luba ba amma ko cacar baki bata taba hada su ba. Hajiya ta kalli Luba da rawar baki ta janyeta gefe ta ce ba tare da ta damu da Munari da ke zaune ba

” Ji nan niya Lubabatu, ba ki jin ana hwadin za ayi rusau? Daga abunda shiyyi sharu mansur zuwa sharru sittin gabadaya gurin ga gwamnati za ta rusa. Wa ya sani ko abun ya taho ya game da mu a Madina? ga jidda muka komawa tunda dai garin ga ba na uwayenmu ba ne”

Wani takaici ya ka ma ta abu bai kai ya kawo ba ta dunga ambaton uwar mutum. Hajiyar ta ce su dan kebe suka kebe ta ce da ita

” Na yi miki sabon kamu”

Luba da son harkar kudi sai tayi kasake tana saurare.

” Shin kin taba ta’ammali da Larabawa na asalin saudiyya ba ‘yan haure ba? Ta girgiza kai ” kin san Allah tilo shi ke Luba? Sun hi son mata irinki. Matansu Laba Laba na, ba su ga kwarin kirki ga rashin gyara ina hwatan kin gane?”

Luba tayi shiru tana nazari cikin ranta kuwa tunani daya ne muddin ta makalewa larabawan jidda ai kuwa ta gama kudi. Jidda gari ne na kowa da kowa daga musulmai har kiristoci, gari na ‘yanci idan ka kwatantashi da Makkah da Madina. Mutane sun fi ganewa su bar Makkah su je suyi iskancinsu daga baya su dawo, wannan wata al’ada ce da suka fi kwanciyar hankali da ita.

Hajiyar kuwa ta ce

” Ai jidda ita ke ga kwanciyar hankali, ko banza kayi nesa nesa ga Allah (auzubillah) in kin dawo Makkah sai ki tai ki yo dawafi Allah shi wanke maki zunnubanki”6

Ai Luba sai ta ji kamar ta rumgume Hajiyar don dadi lallai lokacin bunkasarta yayi. Idan kuwa har ta bunkasa to ba abunda za ta fara nema sai shaidar zaman kasa. Ai ita ta na ga ta ga wajen zama don ita da Nijeriya in ba sa’a ba sai ziyara. Hajiya ta daka ma ta duka ta ce

” Ke ji nan niya. Tahiyayyiya na sa an ka kawo muni magunguna na asalun mallaka daga sakkwato, jadidan wall
ahil azeem. Ki dibe ni nan sai nibba ki dabaru dubu! Da zaki kama namiji ga nan (ta kama wuyanta) ba ki ga Munari tana daddaga miki hanci ba? Matsayinki take bida. Tana miki bakin ciki yadda ta ga ina jawo ki ga jiki”

Kawai sai Luba ta rungume Hajiya suna kwasar dariya, wasa yayi kyau. Abinda Luba ba ta sani ba shi ne, wannan ne mafarin rushewar wasan na ta a kasar Saudiyya.1

Bayan komawarsu Jidda sai hanya ta kara budewa. Hajiya ta san mutane yadda Luba ba ta zato don haka gama mata da maza mazauna can ya zame ma ta babbar harka.

Dama su larabawa masu mu’amala da bakaken fata su na bukatar sirri musamman idan suna da aure kuma hajiyar ta gwanance wajen tabbatar da hakan. Luba ta makance ta kurumce a son duniya, gani take wannan ya fiye ma ta komai. Larabawan mazan da ke cin amanar matayensu suka samu mafaka a gurinta ita kuma ta samu abunda take so a gurinsu. Ana cikin haka sai wata ta yi mata hanyar aiki a gidan Ummu khalifa.

Abu khalifa mutum ne mai tarin arziki sai kuma Allah ya hada shi fa mace mai mugun son mulki. Kasalalliyar mace mai saka aikin jaraba fiye da duk wani gida da Luba ta taba aiki. Babu inda Luba ba ta shiga a gidan ta gyara daga sashenta har na mijin. Mijin bai cika zama ba don haka a tsawon zamanta ba wai sun taba haduwa ba ne.

Watarana Luba ta dawo daga kasuwar Haraji (sooq kharaj) ta saro gumama ta shigo gidan ummu khalifa ta ga ana ta shirye shirye da girke girke. Sai mamaki ya kamata don sanin ummu khalifa ko tsinke bata dagawa. Daga zuwanta ta hau ta da fada kan cewar ba ta karasa gyaran sashen Abu Khalifa ba ga shi kuma yana kan hanya. Ta na ta maimaita

STORY CONTINUES BELOW

” Allahu yahdee ki, Allah yahdee ki”

(Allah ya shiryeki)

Nuni da ranta ya gama baci kenen.

A cikin ran Luba ta gama zaginta kwando kwando, mata gadon mijinta ma ba za ta iya gyarawa ba, malalaciya kawai. Can wata zuciyar ta ce ma ta ke idan ke ce da matsayinta za kiyi aikin wahala?

” Nan fa daya”

Ta bawa kanta amsa.1

Ta na cikin aikin kwatsam sai ta ga an shigo sai ta dan diririce ashe mai dakin ne, sai ya sakar ma ta murmushi. Ta mayar ma sa don dama niqabinta a dage yake. Ya ce “Afwaan” yana mai ba ta hakuri ganin kamar ta rude. Ta gyada ma sa kai tana mai lura da satar kallonta da yake yi.

Abu khalifa ba zai gaza shekara arbain da biyar ba mutum ne mai mabanbanciyar halayya da matarsa. Yana da matukar kirki da tausayi, ya tara dukiya mai yawa ga shi da kyauta. Matsalarsa guda daya ce bata kai biyu ba, zina.. Mazinaci ne na bugawa a jarida shafin farko kuma ba irin kalar matan da baya kulawa. Ko da ya ga Luba a wannan ranar sai ran sa ya biya amma yayi mamaki don bai taba ganinta ba.6

Ko da Luba ta kyalla ido ta ga kallon da Abu Khalifa ke jeho ma ta sai kudurcewa ranta kaya ya fadi a gindin kaba. Sai take tsirar gyaran sashensa a daidai lokacin da ta san yana nan har ma yayi sabo da ganinta. Rannan dai ya tambayeta

” Hal ta’arafina luggatul arabiyya?”

( shin kina jin harshen larabci?)

“Qalil..min arabiyya”

( ina ji kadan)

“Ma ismuk?”

( ya sunan ki?)

“Ismi Lubabatu”

(Sunana Lubabatu)

“Ah..mashallah..kaifa haluk ya lubabah?”

( ya ki ke ya lubabah?)3

“Ana bi kyar, Alhamdulillah”

(Lafia nake,Alhamdulillah)2

“Ana masrur bi muqabalataki”!

(Na ji dadin haduwa da ke)

Anan suka kulla alaqa wata irin alaqa da ta zamewa Luba sanadin wani babban al’amari!

Luba da Abu Khalifa dama zani ce ta tarda mu je mu kawai sai suka gimtse cif da cif kamar tif da taya. Dama shi halinsa kenen sai ya gamu da luba uwar cin nera kawai sai al’amarin ya musu armashi, bai yi wata wata ba ya fara mallakawa luba kaya na alfarma.1

To dama ita gwanar girman kai ce da dagawa nan da nan sai ta fara izza a cikin yan dakinsu. Ita kan ta Hajiya ‘yar sakkwato sai ganin Lubar ya zame ma ta aiki, ta kwashe kayanta ta koma wani gida. Luba ba ta ga wuta ba ta ga aljanna Abu khalifa ya daure mata gindi sai yanda ta so. Sai dai duk abun nan da yake ma ta cikin sirri ne don yana tsoron matarsa ta sani. Duk wannan tashe da take yi ba ta taba tunanin waiwayar gida ba. Kusan shekaru hudu ba amo ba labarinta kawai sai bankadarta take zubawa. Ta jingine kowani maneminta tana mu’amala da Abu khalifa kadai saboda shi mai tsananin kishi ne.1

Me zai faru? Luba tana cikin cin duniyarta da bakin allura sai ta fara zargin kamar yanayinta na canjawa. Ta dai share da fari saboda duk yawon duniyarta ba ta taba yin ciki ba don kwayar family planning kamar ruwan sha take a gurinta tun zamanin tana harka da su Olu. To sai dai a saudiyya ba wannan kwaya da zata je gaba gadi ta siya sai dai mutanenmu masu zuwa da suke sumogalin din ta suke sayar musu da tsada. Shi kan sa Abu Khalifa ba su taba wata muamala ba tare da yayi amfani da “condom” ba sai kan ta ya daure.4

Ba ta yi sati ba zarginta ya tabbata tana dauke da jiki dan wata biyu cif a mahaifarta hankalinta yayi matukar tashin da bai taba yi ba! Ina za ta kai juna biyu? Wa ta isa ta nuna ta ce shi ne ubansa? Ta ma ina zata fara rainon ciki a garin da baka isa gaba gadi ka je mustashfa ba? Yaron da baka isa ka sa shi a madarasa ba? Duk wannan sai dai kayi kame kame a tsakaninku ku bakin haure.9

STORY CONTINUES BELOW

Shawara dama guda daya ce ta zubar don dai ita ba ta ga wurin ajiye shege ba a duniyar nan. Ga shi ita ba wata kawa ba balle su kashe du rufe kowa sama sama take da shi.

Ita a karan kan ta ta san ciki na Abu Khaleefa ne don haka dole ta boye masa don bayyanawar mugun tashin hankali ne. Idan kuna nema da baki danuwanka don ka haifi shege ba wani abun a zo a gani bane amma balarabe? Idan ta bari ya sani kashinta ya bushe don tsaf zai iya sa. a batar da ita. Abu khaleefa babban mutum ne mai dukiya, iyali ga mu’amala ta arziki da mutane da wani bakin za ta gayawa duniya tana dauke da cikinsa? Daga zaman dadiro? Ba zata iya ba!5

Luba fa ta rasa inda za ta sa kan ta ta ji dadi tayi ‘yan dubarunta amma kamar an shuka dusa, ciki girmansa kawai yake. Ba ta da wata mafita kawai sai ta dangana da Hajiya ‘yar sakkwato.

Ta kalli Luba kallon takaici ganin yadda tayi sabo da raina mata hankali ta ce

” wagga yarinya..wagga yarinya kin ci sunanki kaza ci ki goge baki. Sai yanzun ga kin ka ga damar zuwa dibo ni? Da ta kare miki? To ahir din ki hawainiyarki ta kiyayi rama ta”3

Tayi ma ta tas! Luba ta sauke girman kai ta dunga rokon hajiya da bata hakuri tana ma ta bayani har dai ta huce. Can ta ce

” Yaro yaro ne. Kin san dai bamu iya zuwa asibiti ko? Don saudiyya ba a zubda ciki bari in dan yi miki hadi irin namu. Irin hadin ga nai yyiwa zulai ‘yar damagaran. Shekarun ga da sunka wuce ta dage sai tayi amre..nicce mata duk amre amrenki kar ki sake ki daura da basuddane..me akai akai dan sudan..sai kun tara yara goma ki wayi gari babu shi ya gudu ya barka, ina za ka tasamma nema nai?. Ita ma kahiya gareta kamar ki Luba, ta tai tayi anrenta sai ga ta cikin hwari ya gudu babu labari. Irin hadin ga nai mata ta rabu da kajaga!”6

Ta yiwa Luba hade hadenta ita kuma ta karba jiki na rawa ta kwankwade. A daren ranar da kyar luba ta kai labari saboda yawan jinin da ta zubar ita kan ta Hajiyar ta zaci sai a a lahira.

Hajiya Yar Sokoto ta tsorata iya tsorata har tayi da ta sanin sanin luba a duniya kwata kwata ballantana har ta kawo ta garin jidda.

Tana zaman zamanta za ta je tayi sanadin rai a kama ta a daure ba ta ji ba ba ta gani ba. Sai ta ji ma Lubar ta fice ma ta a kai gwara kawai ta rabu da ita ta huta da kaya tun da dai ta samu na samu. Tun da dai ciki ya fice umma ta gaida assha. Luba kuwa tana warwarewa da ta ga jinin barin nan ya tsaya sai ta ci gaba da sabgoginta.1

Ana murna bako ya tafi ashe bako na labe a bayan ga
ri. Ba a yi cikakken wata uku ba Luba ta fara jin wani motsi motsi a kasan mararta sai abun ya daure ma ta kai ta garzaya wajen Hajiya. Hajiya na taba cikin Luba ta doka salati ta sanar da ubangiji ta ce9

” Lubabatu wallahi cikin ga na nan!”

Luba ji tayi kamar an dauki bulo inci tara an maka ma ta. Kawai sai tayi zaman ‘yan bori. Ta ce cikin karaji1

” Ina ce mun zubar?”

Hajiya ta ce

” Bai zubdu ba Al’quran. Na rantse da Allah Luba cikin ga so shi ke shi tona miki asiri don alamu sun nuna sai ya diro da kahwahunsa. Adashi ne kin ka zuba Luba, sai kin kwashe.”1

Wani kuka ya subuce ma ta. Ta haifi shege sai ka ce a majigin mafarki? Yo ko a Kano ta haifi shege balle a saudiyya? Luba ta zauna anan ta rizgi kukanta Hajiya kuwa ta cigaba da dan hidindimunta ba ta kara bi ta kan ta ba.

Dama tun da Abu khalifa ya fara shagwabata da kudi ta raba muhalli da Hajiyar. Ita a lallai na gaba yayi gaba dama Hajiyar tana kule da hakan. Sai suka yi sallama da Hajiyar akan cewa za ta dawo washegari a san wacce ake ciki.

Washegari da Luba ta dawo sai aka ce ai Hajiya ta kwashe ‘yan kayanta ta bar gidan wani kullutu ya tsaya ma ta a makoshi. Ya Hajiya za tayi ma ta haka? Ta jawo ta ta kawo ta garin da ba uwa ba uba ga cikin shege kwance a mararta shi ne zata gudu ta bar ta? Nan ta fara sake sake amma ba ta ga mafita ba.

Garin saudiyya ya fara fice ma ta a kai gabadaya hankalinta sai yau yayi Najeriya. Ta tuno iya tamadi da bata waiwayeta ba a sama da shekaru hudu cas! Sai ta ja wani takaitaccen tsaki tana tunanin abun yi.

STORY CONTINUES BELOW

Munari yar Adamawa da suka yi zaman daki da Luba ita ta fado ma ta a rai. Ta je ta same ta ta gaya ma ta bukatarta ta kalli luba shekeke a sakarce ta ce

” Au ni ce ma zan nema miki inda za ki haihu a sirri? Gaskiya kina da rainin wayo a lamarinki. Menene kuma gamin kifi da kaska? Ta ina muka hadu da zan taimake ki? To ma wai ni ce na ce kiyi cikin ko kuwa ubana yayi miki?1

Luba tayi murmushi irin na mai nema ta koro bayani

” Munari baki fahimceni ba. Ke kan ki kin san abun kunya ne a ce na haifi shege a bayyanar jama’a wanda suka sanni na san su. Haka kuma kin san uban cikina balarabe ne me iyali. Idan balli ya tashi ta ina zan like? Ni taimakon da nake so ki min shi ne, na san kin san mutane to ki samo min wajen da zan boye in haihu ba tare da wadanda na sani sun gani ba. So nake cikin nan ya zame min sirri.”

Munari tayi caraf ta ce

” Dama haihuwa na da sirri ne? Ai sai dai idan ba ki haife ba! Da can wani shegen ne ya ce kiyi cikin?”

Luba ta katse ta da

” Dakata munari zaki taimaka min ko ba za ki taimaka min ba?”

Munari ta mayar ma ta da

” Wai in taimake ki akan wani dalili? Kanwar uwa ta ce ke ko ta ubana?”

Luba ta ce

“Akan dalilin zan ba ki riyal dubu biyu”

Munari ta mika hannu ta ce

” In ji dumus”

Karantina unguwa ce da aka fi sani da “slum” a turance. Cike take da masu karamin karfi ma fi yawansu wadanda ba ‘yan kasa ba mararsa igama(shaidar zama). Yawa yawan ‘yan Afrika daga kasashe irinsu Niger, Nigeria, Ghana wadanda suka shiga saudiyya sama ta ka kuma zaune a jidda za ka same su a Karantina. Akwai kasuwarsu da take ci duk juma’a anan suke samu su siyarda kayan abinci, kayan shafa da sauransu. A cikin wannan tsukakkiyar unguwar ta Karantina

anan munari ta samowa Luba daki.

Banda Luba akwai wasu mata guda hudu wadanda shekarunsu suka dan tasa suka yi musu karyar cewa mijin luba ya fada hannun yan kame an mayar da shi Nijeriya. Ita Lubar tana kokarin tara kudi ne ta aika ma sa ya samu dawowa. Suka tausaya mata ganin tana dauke da juna biyu suka dan tattaimaka ma ta.

Watannin haihuwarta suka cika cikin gajeriyar nakuda da taimakon ‘yan dakin su da munari ta sallo kyakkyawar diyarta fara kal! Kallo daya zaka yi ma ta ka gane ruwa biyu ce. Luba ta kura mata ido gabanta yana dukan uku uku, yanayin yarinyar ya dauki hankalinta. Wani takaici da bakin ciki ya nanukota data tuna wai yau ita ce ta ajiye shege, sai ta ji gabadaya kamar ta hau kan ta ta murkushe kowa ya huta.1

Yarinya na da kwana bakwai da duhun dare Luba ta sidade ta gudu. Don ma kar a yi cigiyarta sai ta gudu makkah daga nan ta fada madina tana ta canje canjen gurin zama. Kafin kwana bakwai ta hada ‘yan kudadenta ta yanki tikiti sai gida Najeriya!15

*********************************

A lokacin da Luba ta dira a unguwar Birget babu wanda ya gane ta domin kuwa fuskarta rufe take da niqab. Ta iso kofar gidansu ta kare ma sa kallo babu abinda ya kara sai rakwarkwabewa. Ba tayi mamaki ba shekaru sama da hudu ba wasa ba.

Ta saka kai ta shiga ciki sai ta hangi Iya Tamadi a tsakar gida tana daka tunkwal tunkwal, ai ko ta kwararo sallama. Sau daya tak Iya Tamadi ta ji muryar Luba ta dago kai a firgice, ai luba na yaye niqabinta ta wurgar da tabaryar ba ko salati ta kwarma ihu mai hade da kuka ta ce

” Yau na ga ta kai na Luba ke ce ko kuwa fatalwarki?”1

Iya Asabe da ke makewayi ta fito da sassarfa buta a hannu ta na ganin luba ta ajiye buta a kasa ta kama hanci ta rangada guda ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” Yawon duniya mafarki ne, idan an je ma za a dawo!”1

Iya tamadi ta share hawayenta da bayan hannu, Luba ta karaso ta rike ta ta ce

” Haba iyannan wai menene na kuka ba gani ba? Ga shi na dawo”

Iya Tamadi ta ce

” Haba Luba yanzu a ce shekara da shekaru ba amo ba labari. Babu wasika ko ‘yar wayar nan ta zamani da ta fito. Kin sa makiyana suna min dariya ubanki ko a jikinsa wai ai ni na tura ki. Wanna duniya da me tayi kama?”

Ta kare tana share hawayenta.

Luba ta buga wani uban tsaki ta ce

” Yo wai Iyannan ni daga dawowa ta daga wata uwa duniya ko ruwa ban saka a bakin salati na ba..ya salaam an taso ni da korafe korafe.. Allahu yahdeek….Allahu yahdeek Duk mai zagina yayi a banza man kare. Arziki ne na yo shi..Alhamdulillah..na tako shi. Wallahil..azeem Kukan talauci sai dai wata shegiya ta yi ba mu ba!” Ta karashe tana hararar Iya Asabe.1

Iya Asabe ta kwashe da dariyar mugunta tana mai karewa luba kallo ta ce

” Na yaushe kuma? Akwai wanda abun takaici ya baibaye irinki? Kin ki zaman aure sai yawon ta zubar, kano to jiddan ne bamu sani ba? ai muna da labarin komai! Ki je ki jiyo labarinsu hafsy sun yi zamansu dakin mazajensu har da albarkar ‘ya’ya ke kuwa sai yawon kawararo.”

Ta juyo ga iya tamadi da take mata kallon takaici ta ce

” Dama kin daina duba na kin kalli diyarki da kyau, daga gani jego take

Dubi kirjinta tantsan tantsan kwarankwatsa dubu idan aka tatsa za a ga ruwan nono! Eho!…an haifo shege ko an cire shege za a mana rufa rufa. Jama’ar gida ku fito..yau ga abun kunya..ahayye ayyururi!!”1

Ihun da take yi ne ya janyo hankalin mutanen gida ciki har da amaryar baban yara Sabuwa. Ta fito tana yatsina irin na amarci ta ce

” Wai gidan nan gidan aure ne ko na masu zaman kai? Ku kullum kun girma amma ba ku san kun girma ba. Ba za ku bar mutum ya huta ba sai kun cika ma sa kunne da hayaniya..yo..ta yo shegen mana.. Asabe ubanki ne ya ma ta?”

Ta juya za ta shige daki Iya Asabe ta fizgo ta wai ta zageta aka fara damben alkafira. Har makota sai da suka shigo sannan aka raba su suna takaicin wannan gida mai kama da filin daga.4

Sabuwa ta dauki zaninta da aka tumurmusa a kasa tana ta dure duren ashar ta ce wa Iya Asabe

” To ni ban kar zomon ba da zaki fizgoni ki daka. Ni nayi shegen ko kuwa uwata? Ki samu wacce tayi shege ki daka mana. Muguwar mace kawai danginsu fir’auna” tayi daki da sauri tana kullo kofa.3

< br />

” Au matsoraciya ki tsaya ki ga yadda zan saba miki kamanni , wanda ya ajiyeki ma ba lallai ya gane ki ba” cewar Iya Asabe

Duk wannan badakalar da ake Iya Tamadi ba ta daina sharar hawaye ba tashin hankalinta shegen da aka ce Luba ta haifa. Ita ma da ta kare ma ta kallo sai ta ga kamar akwai alamun haihuwa a tare da ita.

Ita kuwa Luba ko a farcenta taunar cingam ma take tana yatsina tana kallon kowa daidai. Sabuwa da Iya Asabe dabbobi ta dauke su wadanda ba su san inda yake musu ciwo ba. Ta buga tsaki ta shige dakin uwar bayan ta ce musu

” Antuma….Majnutani!!”

( ku mahaukata ne)

Tana mai takaicin rashin canjawar rayuwar gidan.

Ta samu waje akan yaloluwar katifar uwar ta zauna. Iya tamadi da ta biyo bayanta ta ce

” Yanzu auta da gaske haihuwar kika yi? Za ki kara jawomin gori a sakani a waka cikin unguwa. Kina ganin guduwar da kika yi daga gidan Alhajin Kyalli dan kosan da nake yi sai hakura nayi saboda gore gore. Auta yaushe za ki bari raina ya huta ne?”

Luba ta galla ma ta harara ta ce1

” Wai ke Iyannan yaushe za ki bar tsegumi da kananan maganganu? Daga dawowata an kafa min kahon zuka. A gabanki na haihu? Ko kuwa wani shegen ne yace muku ya ganni da goyo? Idan kina min irin haka yaya zan ji dadin nuna miki arzikin da na yo? Mutane suna so su raba mu kiri kiri amma ke kin kasa ganewa.”1

Iya Tamadi tayi shiru taji batun arziki. Luba ta gama ‘yan fadace fadacenta kamar ita ce uwar kana ta zuge yar jakar da ta zo da ita da lalitarta ta fara ciro kudade. Riyal riyal ne da dalolin Amurka da Abu Khalifa ya sha wanketa da su. Iya sai zazzaro ido take tana washe baki

” Na shigangada ni Tamadi auta me zan gani haka?

Luba ta ce

” To ba na gaya miki ba ki ka tsaya mita. Yanzun haka wannan kin ga ba kudin kasarmu ba ne. Zuwa gobe idan nayi wanka na huta sai in je in canjo su zuwa naira na fitar miki da naki.”1

Iya tamadi ta ce

” Allah auta? Yanzu duk kudin nan naki ne? Tabdijam lallai Saudiyya ta karbe ki..da gangan ma ake zaginki”

Luba ta ce

” Au dama ba na gaya miki ba. To bari ki ji har sarkar zinare zan siya miki”

Iya ta buga kirjinta da karfi ta ce

” sarkar zinari! Ni auta? Kamar wata matar gwamna?”

Luba tayi dariya ta ce

” tukunna ma iyannan idan na canzo kudin nan har jari zan ba ki ki sayi injin markade. Abinci sai wanda kika zaba. Na kai ki goron dutse ki zabi gado da kabet dan ubansu!”

Iya tamadi ta mike tsaye jiki na rawa don tsabar murna kawai sai ta karkace ta rangada guda. Ta ce

” yayi auta..duk cikin ‘ya’yana ba mai kaunata irinki. Allah dai ya karo arziki”

Suka cigaba da hirarsu.1

Ita kuwa Luba ga shi dai tana murna ta rabu da kajaga amma zuciyarta cike take da tunanin jinjirarta. Idan ta rufe ido sai ta ga lokacin da diyar ta bude idonta masu tsoratarwa ta kura ma ta su. Sai ga ji gabanta na faduwa, ko yaya aka yi da jinjirar? Ta ma san ta mutu don ba yadda za a yi ta rayu ba ruwan nono. Da wannan ire iren tunanin ta yakice abun a ranta ta cigaba da harkokinta.6

Bayan dawowarta da yan kudadenta sai ta zamo tamkar tauraruwa a gidan. Komai na ta daban ne ci , sha , suttura. Wataran ma kafin ta tashi daga bacci Iya Tamadi ta dafa ma ta ruwan wanka ta kai mata bandaki…wata irin rayuwa take yi tsadaddiya. Tuni ta karawa babanta jari har yake gani duk cikin ‘ya’yansa ba mai kaunarsa kamar ita.2

Son zuciya irin na wasu iyayen kan zama abun mamaki. Daga baban yara har iya tamadi sai ya zamana ba wanda ke ganin laifin Luba. Ta girgije ta gyatse ta cigaba da harkokinta, iyayen suna kallo ba wanda ya isa ya ce da ita kanzil.5

Har a wannan lokaci ba ta tunanin aure, sai ma take hangensa a matsayin wata hanyar tukurawa. Kullum hange ta ke akwai inda ya kamata ta kai wanda ba ta kai ba. Ta sawa ranta cewar in har za tayi aure to sai namijin da ya ci ya tada kai da nera.

Wata shida bayan dawowarta sai rayuwa ta soma yi mata matsi, ta kudurcewa ranta zama ba na ta ba ne.

A safiyar wata alhamis ta rangada kwalliyarta ta shiga wani tsadadden saloon domin a wanke mata kai. Kawai sai tayi kacibus da wata yarinya da suka yi sakandare tare mai suna Sadiya indiyar daji. Daga ita har luba dama can halinsu daya suka tafa Luba ta ce

” Sadiya kin buya kwana dayawa..khaifa haluk?”

Sadiya ta ce

” Shegiya Luba haka kika koma? Kwanakin baya an ce min kina saudiyya lallai ta karbeki”

Luba tayi galala tana kallon sadiya cike da tsananin mamaki. Ko da can ta san sadiya na tsalle tsalle amman kwata kwata baga goge irin haka ba. Yanzu Sadiga ta zama yar gayu komai na jikinta mai tsada ne. Wayar hannunta ma ba a gani sai a hannun wane da wane. Balle kuma uwa uba galleliyar motar da ta hawo ta zo saloon din da ita. Luba ta kama baki ta ce

” Aiwa..Sadiya haka duniya ta miki wankan albarka? Mashallah..mashallah. wa kika samu ya rike miki kan maciji ki ke wasa da jelar?”9

Sadiya ta kyalkyace da dariya tana kada ‘yan mukullin mota ta ce

” Duniya ai ba gidan zama ba ce Luba sai ka tashi ka nemi sa’a tukunna.”

Luba ita ma dariyar tayi ta ce

” Aiwa..da gaskiyarki. Wallahil Azeem sadiya arziki ya karbeki. Nima ki min hanya mana in daina rabe rabe. Tun dawowata daga Saudiyya al’amura suka tsaya cak ba kamar da ba. Ga shi na tsani rayuwar babu wallahi.” Suka tafa.

Sadiya ta ce1

” To in kina so sai in kai ki amma fa sai kin jajirce”

Luba tayi caraf ta ce

” Ku ji mu da Sadiyan nan ai ni duk inda kudi yake to ina nan. Ko ina ne ma kai ni..menene a cikin ido in ban da ruwa?”

Sadiya tayi dariya ta fara cewa

” Akwai wata kungiya…….”10

Babu wani sashe na zuciyar Luba da ya taba tuna ma ta ranar nadama.

Kun ji masomin labarin Lubabatu.Mutuwa mai yankan kauna, bakin takobi mai raba soyayya!5

Niamey, Niger Republic

A shekara 18 babu wani namiji da zai daga ido ya kalli Rokaiyatou ba tare da bukata daya ta mamaye ran sa ba, na ya mallaketa har abada. Amma a zuciyarta mutum guda ne kacal! Frère Momodou. Idan da shi a duniya to ba ta ki sauran maza duk a hada ayi jana’izarsu ba wannan ba matsalarta ba ce!1

Sau da dama takan yi tunani a duniya akwai irin Frère kuwa? Dan adam guda daya tal da zai iya maye gurbin dangi guda ya zama kamar uba? A so da kauna, tausayi da jin kai babu ya Frère duk duniya a hasashen Rukaiyatou. Shin wai da babu shi wata irin rayuwa za ta yi ita da Momma. Shi ya tsaya tsayin daka cin su, shan su, karatunta tun daga Ècole Elementaire har Ècole Secondaire.3

A halin da ake ciki yanzu Momodou yana kasar Faransa a wani gari mai suna Montpellier. Ya gama digirinsa na biyu da dadewa amma fafur mahaifinsa ya ki ya dawo gabadaya. Ya dora shi akan al’amuransa na kasuwanci ba shi Faransa, ba shi Nigeria ba shi Niger.

Da gaske mahaifinsa yake bai son ya dawo, tsakaninsa da Niamey sai dai idan ya zo ziyara. Ya gama gane cewa duk kan maganar Rokaiyatou ke ya sa yake ma sa walagigi da rayuwa na kusan shekara biyar. Ko son yayi maganar aure ba ya yi ga shi shekarun sa sun ja. Da wannan aniyar ya dawo gida wannan shekara. Rokaiyatou ta gama Ècole Secondaire aurenta a yanzu ba gudu babu ja da baya!

Da wata safiya ne Rukaiyatou na tsakar gida tana tankaden garin tuwo yayin da Momma ke dinkin hula akan tabarma. Ta dube ta cikin farin ciki ta ce

“Momma sakamakon gwajinmu ya hito kuma na kokarta na san Frere zai nema mun Universete ko amren namu za a yi?”

Momma ta buga tsaki ta nuna ta da dan yatsa ta ce

” ke ki fita idona, ni ki ke yiwa maganar aure?”3

< p>Rukaiyatou ta kwashe da dariya ta ce

” To gwada mini wa nake da shi baya ga ke?”

Momma tayi dariya suka cigaba da hirarrakinsu a ran Rokaiyatou fal tunanin Momodou

A lissafinsa satin da wuce ya kamata ya zo, to amma har yanzu shiru. Sai ta yini sukuku ko me ya rike shi ga Faransa? Ta kwaso kwanukansu ta kawo bakin rijiya don ta wanke, ta hado da wata tsohuwar rikodar momma ta kamo gidan radio. Ta fara wanke wanke ta ji sun sako wakar Sogha Niger, wayyo dadi zai kasheta don tana son wakar dankwali. Ta fara bin wasu baitikan tana aikinta kamar da ita aka rera

A can da dauri,

An ka je yin wasa

‘Yanmata su sanyo kwalli,

Sauran sai su sa janbaki,

Sai a taru hilin wasa

Samari sai suna wilgawa,

Ka ga wacce ranka yake so

Hitilla ce ka ke matsawa

Rawa da waka rannan sai sahe….2

Duk sallamar da ake yi ba ta ji ba, sai kamar daga sama ta ji an ce

“Bonjour!”

( ina kwana/ ina yini)

Ta dago da sauri tana mai kashe rikodar jin muryar Momodou. Kawai sai ta sa dariya cikin wata murya ta ce

“Frère!”

(Danuwa)

Shi ma ya sa dariya. Ta dago ta kare ma sa kallo ya sa riga mai dogon hannu fara tas da bakin wando. Takalminsa ma baki ne sau ciki daga ganinsa fes fes. Jikinsa ya nuna alamar hutu, da wata karamar jaka a hannunsa daga alamu ko gidansu bai shiga ba dirowarsa kenen. Da ta kare ma sa kallo sai ta ji gabanta ya fadi sai take ganin kamar ya fi karfinta.

Murmushi ya sakar ma ta ganin kamar ta fada tunani ya ce

“Comment allez-vous”

( ya ki ke)

STORY CONTINUES BELOW

“Je vais bien. Merci”

(Ina nan lafia.nagode)

Daga nan ta wancakalar da kwanunkan tana kwallawa Momma kira cikin murna. Ta fito tana kokarin daura dankwali tana yiwa Rukaiyatou fafan kwada mata kira sai tayi ido biyu da Momodou. Duka sai suka kwashe da dariya. Ya tsugunna a gabanta yana gaisheta ta dafa kan shi cikin farin ciki ta ce1

” Mon garçon, saukar yaushe?”

Ya ce

” yanzun wannan tsal na zo”

Ta kama baki ta ce

” Ba dai ko gida baka shiga ba?”

Murmushi kawai yayi.

Ta ce

” A’a Momodou ba a haka, maza je ka gida su gan ka su ji dadi kai da ka dade baka zo ba? Ma za je ka abunka idan ka huta sai ka dawo mu gaisa a tsanake. Ai maganganunmu dayawa ko?” Ta karashe tana dariya

Shi ma dariya yayi ya ce “To”

Juyawa yayi zai tafi ya zo daidai kunnen Rokaiyatou ya ce a hankali

” ki tsumayi zuwana anjima, Au revoir”

Sai ta ji kamar ta bi shi don farinciki!7

Momodou ya dawo bai dawo ba har kwana biyu shiru sai kan ta ya daure. Ita ba ta isa ta je gidan nan neman shi ba, ba za ma ta fara ba, wacece ita? Da kwana uku tayi shiru kawai sai ta dauki sakamakon jarabawarta ta mayar karkashin akwatinta.

Sai a kwana na hudu tana shara ta jiyo sallamarsa sai kawai ta share. Momma ce kawai ta amsa ta ce ya karaso. Ya karaso yana satar kallon Rukaiyatou ta dauke kai ya isa wajen Momma ya durkusa ya ce1

” Kuna lahiya”

Ta amsa ma sa. Daidai nan sharar da Rokaiyatou ke yi ta isko inda suke zaune kawai sai ta sa tsintsiya ta sharo kafafunsa. Momma ta daka ma ta tsawa ta ce6

” Menene haka? Ji min rashin hankali fa ni Ramlatu”

Rukaiyatou ta tsaya tayi sororo. Momma ta cigaba da fada

“Momodou ki ke sharewa? Wai duk haushin bai zo ba ne? Ko zamanki yake? Ku ji ni da ‘ya”

Idonta ya cicciko da hawaye ta dalla ma sa harara wani murmushi ya kufce ma sa ta kara kulewa. Maimakon ya kula ta sai ma yayi wa Momma sallama ya fita yana dariya.

Wai mai ma yake neman maidata? Sakarya ko? Kawai sai ta jefar da tsintsiyar ta shige daki a guje tana kuka. Momma ta kama baki ta na cewa

” hauka kawai”7

Sai da daddare bayan sallar isha Momodou din ya shigo, ya tarar da su a zaune Rokaiyatou na cin tuwo. Sai suka dan fara hirarrakin yaushe rabo da Momma yana tambayar makarantar Rokaiyatou, ita dai bata saka musu baki ba. Can Momma ta ankara ta ce

” Ni ke kadai za ki ci ne ba zaki zubowa Momodou ba? Wani kalar bakin hali ne haka kika koyo?”

Kawai sai ta turo baki. Momma ta dauki mahuci ta kwada ma ta kafin ta kara ta gudu daki. Momodou dariya ya kama yi ya ce

” Momma ki bar ta ta ci tayi jiki”

Ta yi tsaki ta ce

” yarinyar nan ban san me ke damunta ba kamar mai aljanu”

Ya ce

” kale ta Momma shagwaba ta ka ji”

Ta kama baki tace

” Hauka dai”

Budar bakinsa sai cewa yayi

” um..um Momma Rokaiyatou ai bata hauka”

Tayi dariya ta ce

” Au shigar ma ta zaka yi, kun fi kusa ko? Ku yanuwan juna”

Yana dariya dariya yayi hanyar waje yana cewa

STORY CONTINUES BELOW

” Hakuri za ki Momma, kuskure an ka yi”

Kawai sai Momma ta shige daki ta tarar da Rokaiyatou tana cika tana batsewa ta sakar mata rankwashi ta ce

” ki je na san yana jiranki a waje. Don rashin ta ido shi za ki wa rowar abinci? Don iyayenki wa ya kawo?”

Tayi rau rau da ido ta ce

” gori ne?”

Ta ce

” An miki gorin ke ai ba ki da dubara. Don bai shigo ba ki ke fushi? Kin ga yaron nan abinda zai hana shi shigowa sai Allah. Daga ganin idonsa akwai damuwa bana son takura shi ne ga fada. Amma ke dan rashin hankali kin dau fushi. Ba za ki tashi ki je ki jiyo ba ko sai na yo kan ki?”

Rukaiyatou ta fice tana dariya.

Dama soron na su akwai duhu, ta fara wucewa sadaf sadaf. Kawai sai ta ji an kurma wani irin ihu, ai fa nan ta zubar da takalmanta ta fice waje a guje ciki rudu. Tana isa waje ta ga Momodou a bakin kofar ya rike ciki yana dariya, nan ta gane shi ne sai tayi murmushi. Ta ce

” Wannan ai zalumci ne”

Ya nemi wani dan dakali ya share ya zauna yana karasa dariyarsa daga karshe ya ce

” pardonnee-moi!”

( ki yafe ni)

Ta samu waje ita ma akan dakalin ta ce

“Je pardonne”

(Na yafe)

Sai yayi shiru na wasu dakiku sannan ya ce

” Akwai damuwa Rukaiyatou, akwai damuwa”

Gabanta ya fadi ta tuna da maganar Momma ta ce

” Me shi faru Frère? Zucciyata bugu takai!”

Ya kama kan shi ya sake sannan yayi murmushin dole ya ce

” Dauko sakamakon gwajin naku tukunna in soma da wannan duk da dai na san abunda ke ciki akwai”

Da saurinta shiga ta dauko ta kawo ya duba cikin farin ciki. Ya ce da turanci

” Excellent! Thats my girl. Yanzu sai universete kenen ko?”

Ta yi rufe fuska tana dariya ta ce

” Ai Abdou Moumoni universete zan ke zawwa ko?”

Ya kalle ta sakaka ya ce

” Wa ya hwadi miki?”

Ta ce

” Ai ka shina dai ina sha’awal aikin jarida”

Yayi murmushi kawai yana nade takardun ya ce

” Ai ba a garin ga ma za ki yi ba Rukaiyatou”1

Ta kura ma sa ido tana kokarin gane manufarsa. Ya ce

” Na samu wani aiki a Nairobi bar musu komai zan yi Rokaiyatou. Mu yi amre mu tai abinmu a can za ki karatu. Buri hwa gareni kan ki!”

Tayi sauri ta dube shi maganarsa na taba ranta jikinta yayi sanyi. Ta ce

” Haka ni kwanta ma cikin zucciya?”6

Sai ta sunkuyar da kan ta. Me gareta cikin mata da Momodou ya ware ta ya daukaki rayuwarta haka? Allah Al Hakeem Allah Al Kareem.1

Ya dawo da ita daga du
niyar tunani ya ce

” Daga ke har Momma dauke ku zan na bal Niamey da ku. Momma zan maisheta gurin danuwanta, a shiryasu ina ga hakan zai fi. Shekarun dayawa, Na gaji da ganinku a wannan rayuwar. Ban san me Abba ke nuhi game da ku ba. Ashe dan danuwanka ba da yake gareka ba?Ashe haka amana take a zuciyal mutane? A ce ke kike yin kwana a wanga kangon gida mu kuma muna kwamci cikin kayataccen gida irin wanga? A ce ke ki kan yi cima irin wacce ki kayi mu muna cikin wadata sai wacce mun ka zabi? A ce yawo kika yi ba wanda zai nasa ki ga Lècole?”3

STORY CONTINUES BELOW

Nisawa yayi muryar shi na rawa zuciyarsa na mamakin mahaifinsa. Momodou mutum ne mai tsantseni zuciyar shi mai kyau ce ba ya son duk wani abu na zalunci. Bai taba goyon bayan mahaifinsa ba kuma yana gaya ma sa gaskiya sai ya shure. Amma yanzu dai ya ri ga ya yanke hukunci game da rayuwarsa ,lokaci yayi.2

Ya cigaba da cewa

” Na sha kai kararsa ga Baffaninsu na Tillaberi, sun yi sun yi ya ki ji. A tammanina yanzun ga idan ubanki ya hito kabari zai yahewa Abba? Dukiya ya danne wannan shi a amana? Tausayim shi nikke, ina ya ka zuwa da hakkinki?”1

Gani tayi idonsa ya cika da kwalla sai ta ji kamar ta sa kuka. Ta ce

” Frère, yazunga ban yi butulci ga

Allah ba idan na hidi ban yahewa Abba ba bayan shi ya haihe ka? Babu wani mutum bayan uwata da ya darajantani kamal kai. Idan Allah bai nihe ni da yin uba ga Abba ba ga tammanina ai ya maishe mini da kai! Momodou rayuwar duniya hwa ba komi ba ce, watarana hwa sai labari!”

Ya mike tsaye a dake kamar ba shi ne idonsa ya kawo ruwa ba dazu. Ya ce

” Inaa..inaa Rukaiyatou wannan ba batu ba ne. Lamarin akwai zalumci ciki. Dole ne na sama miki mahita shi ya sanya kwana biyu ba ki ganni ba. Na riga na budewa iyayena zucciyata. Je suis amoreux! I’m in love! Yanzun ga rikici ne a gidanmu. Wai mi ne tattare da ke da anka hwadin bazan amre ki ba?”

Sunkuyar da kan ta kawai tayi. Wasu abubuwan duniya ba su da cikakken bayani. Suna nan ne kamar yadda suke, kamar yadda aka halicce su su zama!

Ya ce

” Ko da yake duk yanzun ba wannan ba ne. Amre kam sai an yi karshen satin ga. Nijeriya zamu wuce, mu kai Momma gida. Na yi wa Mustapha magana za a je ai maki fasfo a sanya visa da sauransu. Ta Najeriya zamu tahi shi zai kula da komai”

Ita ma tsaye ta mike cikin damuwa ta ce

” Ni dai bani so ka samu sabani da uwayenka”

Cikin zafi ya ce ma ta

” ke kin ga babu wanda ya ce ke zaki shiga. Kawai suna da akidojin da ni ban aminta da su ba. Abba na yana matukar kamnata ko ya yi hushi zai sabko!”

Ta jinjina kai. A ranta akwai tsantsar tsana ta Iliyasou Tillaberi amma sai ta share ko a fuska bata nuna ba. Sai tayi murmushi, kai a rayuwa tana kaunar Momodou ta ce

” Toh shikenen Frère yanzunga ta ina za a fara?”

Yayi dariya yana kallon cikin idonta sa’annan ya ce

” On se marie Rukaiyatou!!”

( Aure za mu yi Rukaiyatou!!)4

Kamar wasa rigima ta balle a gidansu Momodou. Duka ‘yan gidan suka juya ma sa baya ba su son aurensa da Rukaiyatou. Hajiya Khulsomou ta dau zafi ta zage shi tas sannan ta ce za ta iya tsine ma sa idan bai yi hankali ba. Abba Iliyasou kuwa cewa yayi idan shi ne zai daura auren to kuwa har abada ba zai daura ba.

Abinda ke ran Iliyasou Tillaberi guda daya ne. Tun yanzu Momodou na ma shi fito na fito akan yarinyar ina ga idan ya aureta? Ya san babu dadewa yarinyar za ta hure ma sa kunne ya karbo ma ta dukiyarta. Momodou zai iya juya ma sa baya zai iya rusa ma sa ajandarsa na girma da fadadar dukiyarsa da bude kamfanunnuka da zasu girgiza duniya.

A halin da ake ciki yana kokarin bude hedkwatarsu a Najeriya. Muddin ya samu ya cimma burinsa to za a fara ambaton I.A and son’s a mujallu ma su kawo rahotani na masu kudin Afrika! Ba wuya zai fada nan. Yana bukatar ‘ya’yansa biyu su taimaka su talkafi burinsa. Idan aka zare gadon Rukaiyatou to ai ya koma baya shi da Ahmadou 50-50 suka yi amma wa ya sani idan banda shi? Idan yarinyar nan ta so ta fara bata ma sa burika to lallai zai iya sa a batar da ita!!

Kan momdou ya dau zafi yana ganin kamar ba ai ma sa adalci ba. A cikin satin ya shigo gidansu Rukaiyatou da shirin tafiya ta ce ma sa

” Frère ina ka ka zawwa?”2

STORY CONTINUES BELOW

Ya ce

” Nijeriya “

Ta ce

” Ikon Allah ,wajen wa?”

Ya balla ma ta harara ya ce

” Ba ki min kara ko? Ina da uwa can da soba amma ba ki cewa na gaishe su. Ba ki neman ‘yanuwanki”

Dariya tayi ta ce

” Ni fa baki nake jin su, ban ga suna zawwa ba”

Ya ce

” Gaskiya ne. Kin san tsakanin uwata da uwal Mustapha akwai rikici tsakani. Da muna kankana kowa yana zawwa, sa’ilin kina kankanuwa sosai. Amma yanzun ga lamarin ya baci. Amma fa ni Hajja Hadiza bata nunamin kiyayya. Shi ya sa ma na kan je. Mustapha soba na ne, aminina duk ‘yan gidamu wa wanda nake kamna kamar sa. Da shi ni ke shirin komai. Sau biyu fa yana zawwa Montepillier ko iyayenmu basu so mu kuwa ma yi zumunci. Labarinki ba wanda bai sani ba. Yanzu zan je Nijeriya tare muka dawowa. Bari ma ki ji na kiraye shi a tarho”

Sai ya dauka waya a aljihunsa. Rukaiyatou ta bi shi da kallo tana mamaki. Tana dai ganinta hannun mutane ta baza gari amma bata taba magana a ciki ba, to ita a wa? Ita abun ma tsoro yake ba ta. Ta ji momodou ya ce

” Alo..ga kamnata ku yi magana”

Yana sa ma ta a kunne. Ta ji an ce

” Hello..Helloooo”

Ai kawai sai ta wurgar da wayar ta fyalla daki a guje! A irin labaran da suke ji wani an ce daga wayar nan aka zuke ma sa jini. Nan ya fadi matacce. Momodou yayi ta ma ta dariya yana cewa

” Wanga yarinya… an yi ‘yar kauye. Bari goben wannan tsal na sai miki tarho”

Kwanan Momodou uku a Nijeriya ya dawo, daga isowarsa gidansu ya shigo. Ta ji yana gaisawa da Momma sai ta fito da sauri daga daki ta ce

” Ina bakon namu shi ke?”

Momma ta ce

” ya tai koyo gaisuwa”

Suka sa dariya Rokaiyatou ta ji kunya ta koma daki. Ya fita waje sai ta bishi daga baya. Tana leke leke yayi dariya ya ce

” Za shi zo cikin sati. Mun yi wata shawara ne zan dawo gobe ni gaya miki.”

Ta ce

“To”

Suka yi sallama.

Shigarsa gidan ya tarar da iyayen na sa zaune a falo. Uwar ta cika ta cika tayi fam. Ta fara bala’i

” Ka tahi gurin uwal taka ko? Momodou kahiya gareka. Su wadannan din su sunka lashe kurwar kanin mahaihinka. Sai sun lashe min kai Momodou..Maita ke gare su!”3

Cikin bacin rai ya soma cewa

” Habaa…”

Ta katse shi da salati

“Sun baka cikin ruwa ka sha ko? Oh ni Khulsomou na haihwa wa Ramlatu da, wani irin bala’i ne haka?”

Uban take kallo kamar ya samo mafita. Ya kurawa Momodou ido ya ra sa yanda zai yi da shi. Yaron ya cika taurin kai. Tabbas wadannan mutane suna da siddabaru kar su je su lahanta mishi da a banza, amma shi ya kasa ganewa.

Cikin wata irin murya ta isa ya daure fuskarsa tamau ya ce

“Momodou”

Ya amsa da

“Iye”

Ya ce

” Ban san ga ina ka sami kahiya ba. Da tammanina da fari kana zuwa gidan ne don kana tausaya musu. Ni ban taba tammanin wai amren yarinyar ga ka ke bida ba. Wace tsiya ke ga zuriyar Ahmadou? Hakkina ke wahal tasshi .Da zan gaya maka tsakanina da shi da sai ni gaya maka hakki na ne ya dauke shi. Mutum ne mai tulin zalumci. Ka ga wannan mata tasa da kake gani ai shedaniya ce danginsu dangin maita ne. Idan ba ka yi a hankula ba yarinyar ga sai ta zamo ajalinka! Kamal yadda tayi ajalin ubanta! Ka shiga hankalinka fa Momodou!”

STORY CONTINUES BELOW< /p>

Takaici ya cika shi amma sai ya hadiye cikin murya mai tausayi ya ce

” Abba ka dubi girman Allah ka dubi zumuntal da ke tsakaninku da mahaihinta ka yi hakuri. Jininmu ne su ko me suka mana mu yahe. Shi kan sa ubanta yau ina shi ke? Idan ba ma yahiya ya Allah zai dube mu ya yahe mana?”

Kawai Hajiya Khulsomou sai ta fashe da kuka ta mike tsaye ta ce da uban

” Wallahi Alhaji kar ka aminta da amren nan don wataran sai Momodou ya hi karhinka. Shikenen na shiga uku da dayan nawa namiji tilo za a salwantal mun da shi”

Ran Iliyasou Tillaberi yayi masifar baci. Zance daya ya ki ci ya ki cinyewa? Shi za a tsaya ana yiwa gardama? Fuskarsa a murtuke kamar hadari ya karashe zancen da cewa

“Kai tsaya ka ji ba lallashinka nake ba da zaka nuna min iyawa. Na rantse da kur’ani izifi sittin idan dai ni zan damra maka amre da wanga yarinya wallahi ba zaka amre ta ba. Daga kai har ita ai kalkashi na ku ke. Idan ta samu miji za a damra mata amre amma ba da kai ba. Lalataccen yaro kawai!”

Daga nan ya fice ran sa yana raya ma sa dole ya kora shi wata kasar su kuma ya dauki mataki akan su. Hajiya khulsumou ta kudurta a ranta abun nan ya zo karshe , dole ta yi musu gargadin karshe. Da haka aka bar Momodou cike da tunanin zuci.

Washegari kuwa Hajiya ta yiwa gidan na su dirar mikiya. Ba tayi sallama ba wasu kwanuka ta tarar a gefe tayi ball da su. Hakan ya fito da Maman da sauri sanin ba kowa ta aiki Rukaiyatou. Sai suka yi ido biyu.

Kowa na kallon kowa. Mamma na kallon irin shigar alfarmar da Hajiyar tayi ta nunawa sa’a. Tana tuno irin dadin da Ahmadou ya jiya ma ta amma yau saboda wadannan azzaluman ji ba yanda rayuwarta ta koma.

Hajiyar tayi ma ta kallo makaskanci ta ce

” Ramlatu kar ki min iya shegenku na Ingilishi gargadi kawai na zo in ma ki. Da ke da diyarki ku nisanci Momodou. Ko ya rasa mace kasar Niger ba zai amri wacce ta kashe ubanta ba!”

Hakurin Momma ya kare ta ce

” Yanzu ke Hajiya duk hakkinmu da kuka danne na shekara da shekaru ni ban je na ni ban je na tsare ki na ci mutuncinki ba sai ke za ki tako har gida ki zage ni?”

” To mi ne in an zage kin? Ke nan har wata abu ce muguwal mace kawai mai nacin tsiya. Da kina da zucciya da tuni kin koma kasal ku. Kurwar Momodou ba zata lasu ba, ‘yan kaniyal uwa!”4

Har ta fita tana zage zage. Momma ta zauna kan tabarma tayi shiru tana tunanin wacce zata fissheta. Gorin da aka yi ma ta yau ya taba ta. Najeriya za ta koma!

Momodou da Rukaiyatou ne suka shigo suna dariya ganinta tana hawaye ya sa jikinsu yayi sanyi. Suna ta tambayarta me ya faru. Ta gaya musu abinda ya faru ga kara da

” Momodou ina so na gaya maka wata magana, ka hakura da Rokaiyatou. Iyayenka sun dage ba sa so, gwara duka mu hakura. Najeriya ma zamu koma, gwara na je duk abinda danuwana zai min ya min. Wannan rayuwar ta isa haka. Gorin da aka min yau ya sa na ji dole na kima kasata ko da ba za a karbeni ba son nan ne asalina.”1

Ta share hawaye

” Kayi hakuri Mommodou wani lokacin ba mutuwa ce kadai take yankan kauna ba duniya ce take raba masoya. Ko babu mutuwa wataran sai ka ga an raba wajen zama!”

Rukaiyatou ta fashe da kuka ta rungume Momma. Shi kuma ya kura musu ido, zuciyar shi sai bugawa take. Ya daure ya ce

” Najeriya ko? Ita kike so? To ku tashi ku hada kayanku.” Ya ciro wasu kudade a aljihunsa ya ajiye ya ce ” ku sayi abinda kuke da bukata yanzun tsal zan je na dawo”

A guje ya fita Momma na kwalla ma sa kira bai waiwayo ba.

Rukaiyatou ce ta fita a guje ta bi shi daidai lokacin da yake kokarin jan motarsa ya dakata da ya ganta. Ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” Frère ina za ka?”

Ya kalleta a tsanake kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce

” Amre za a damra mana”5

Ta kura ma sa ido ta ce

” Aa ba za a yi haka ba. Momodou kar mu zo mu janyo abunda Abba zai yi hushi da kai. Idan mu ka dangana gaba idan Allah ya rubuta da amrenmu sai ka ga mun yi”

Wani duban takaici ya ma ta, ya fito daga motar a fusace ya ce

” Ashe ba ki hankali? Ni ne zan zauna jiran tammani akan amrenmu? Yanzu na hwahimce ki. Dama ba kamnata ki ke ba. Ni ne dai nake shiririta ta. Don mai kamnalka mai hwatan kuyi rayuwa tare ba zai ce ka tsimayi dogon lokaci ba kahin kuyi amre.”2

Ya buga wani uban tsaki zai wuce ta kamo shi tana kuka ta ce

” Haba Momodou ya zaka min mummunal hwahimta irin haka. Wa nake da alaqa da shi kamal kai. Ina guje maka hushin iyaye ne wanda duk mai kamnal ka ba zai taba kamnal ka hwada halaka ba”.

Sai yayi dariya ya bubbuga kafadarta ta dama ya ce

” kwantar da hankalinki kamnata, babu abunda zai faru. Duk wata mishkila da zata faru bayan an damra amren nan ne. Yanzun tsal daga nan tillaberi zan shige. Ai ba su suka haihi kan su ba, baffaninsu na raye. Tunda ni da ke tushe daya ne, kin ga abun ya zo da sauki. Su zasu yi mana walittaka su damra mana aure. Wuyalta in dawo komi dare zamu bar garin ga Nijeriya zamu shige.”

Sai ta kura ma sa ido, sai ta ga kamar ya canja ma ta. Wani irin farinciki yake ciki marar misali. Wai kuwa a duniya akwai mai kaunarta kamar Momodou?2

Ya katse ma ta tunani da ya daka wani uban tsalle ya ce5

” Yau zan zama angonki Rukaiyatou!

Suka fashe da dariya

Sai ya fara ja da baya yana karkada ‘yan mukullayensa cikin farin ciki ya ce

” Tu es la femme de mes revès Rukaiyatou”

( ke ce macen rayuwata Rukaiyatou)4

” Je ne peux vivre sans toi” ( bazan iya rayuwa babu ke ba)

Sai ta kama dariya ranta fari kal! Ta ce

” Nima, je ne peux vivre sans toi momodou! Kai ma ka sani”

Ya daga ma ta hannu ya shiga mota sauri sauri gudu gudu. Har ta juya za ta shige gida ya kwalla ma ta kira

” Rukaiyatou!!!”

Ta juyo da sauri. Sai ya fada ma ta wasu kalmomi da masoyan faransa kan fadi

” Je suis amoreux!”

(Ina cikin so/ im in love)

Rukaiyatou ta shiga gida da gudu cikin farin ciki ta tadda Momma har yanzu a zaune.

” Me yayi miki dadi haka?”

Ta tambaya ganinta cikin annashuwa. Sai ta labarta ma ta yanda suka yi da Momodou. Momma ba ta kasa cewa kkmai sai maimaitawa take

” Mommodou yaro ne, Mommodou yaro ne”2

Jikin Rokaiyatou yayi sanyi ganin yadda Momma ta yi. Sai kawai Momman ta tashi ta soma tattare kayanta. Rokaiyatou ta kwashi takardunta na makaranta da yan kayanta kadan ta hada a waje guda. Suka zauna jiran Momodou. Wani jira mai tsawo irin na daren mutuwa!1

An dauki tsawon lokaci tun Rokaiyatou na lissafin dawowar Momodou har ta bace wajen lissafi. Ina angonta ya shiga? Ta san i yanzu dai an daura. To ko a Tillaberin ne ba a yarda ba, gabanta ya bada dam!

Hankalinta gabadaya ya ki kwanciya ta fita leko waje ya fi a kirga. Dare ya fara yi Momodou shiru dukkaninsu sun yi cirko cirko. Suna zaune nan kan tabarma ta fara gyangyadi ta ji wata gigitacciyar hayaniya ta ban al’ajabi.

STORY CONTINUES BELOW

Dukkansu tsayuwa suka yi firgigit. Momma ta ce

” Ba lafiya ba, daga ji ba lafiya ba”

Ba ta rufe bakinta ba aka wurgo wani katon icce tsakar gidan yana cin wuta. Ai sai syka samu kan su suna falfalawa fa gudu waje irin na ceton rai.

Abinda ya gigita su ya kuma daure musu kai shi ne dandazon da suke jiyo hayaniyarsu ba fa a koina suke ba sai a kofar gidansu. Taron mutane ne wanda fadar adadinsu sai dai kayi karya. Kowanne rike da makami da itatuwa suna cin wuta.

Rukaiyatou ta kankame Momma da kokarin janyota su koma cikin gida sai din hakan y
a gagara inda ba tayi aune ba ta ji an yi musu wata fincikar alkafira an wurgo su tsakiyar taron.

Ba su san yanda aka hau ba ballantana yadda za a sauka aka rufe su da wani irin duka ta ko’ina. Maganganun da mutanen suke fada Rukaiyatou ta kasa tantance su sai dai jimla daya

” galla mayu ne, ku kar musu”4

Sai da aka yi musu ligi ligi don momma ma ta ri ga da ta sume. Rukaiyatou ta cigaba da ganin dishi dishi har ta gano surar Abba Iliyasou yana sharbar kuka a gabanta. Hajiya Khulsomou na birgima a kasa tana ihu da kuka tana tsinewa Rukaiyatou.

Iliyasou Tillaberi ya cakumota kamar zai balla ya kifa ma ta mari. Ya ce cikin kuka

” Ki ka kashe mun diyana ? Ki ka kashe min Momodou kamar yadda uwalki ta kashe Amadou. Allah shi tsine muku!”13

Duk da Rukaiyatou ba wai ciki hayyacinta take ba ta gano maganganunsa. Abinda ya cigaba da daure ma ta kai bai wuce jin cewar wai ta kashe Momodou ba. Wani Momodou din wai? Na ta? Momodou mijin aurenta? Ba dazu suka rabu ba ya tafi a dauro musu aure? Shi ne za a ce ya mutu? Ba ta kara gane wa komai sai da taji muryar Abba Iliyasou yana gaya wa taron cikin kuka2

” Mayyu ne! Su sunka kashemin danuwana. Ta dage sai ya amreta a hanyal bidar amren ya mutu”!1

Sai a lokacin kwanyar Rukaiyatou ta dawo da doka da oda kawai sai jin ta tayi ta tashi ta ruga a guje ba don ta san dalilin yin hakan ba. Wani ne ya fincikota.

Wata hauka ce take ji a kanta ta wucin gadi. Sai ta ji tana so tayi kuka

tana kuma so tayi dariya. Wata gigita ce ta shige ta ta jin wai Momodou ya mutu. Kuma wai ita ake zargi saboda ana musu sharrin su mayu ne.4

Bata san ko ita mayya ce ko ba ita ba ce amma fatan da take shi na ka da a sassauta ma ta. Ta dalilinta Momodou ya rasa ransa ko da ta lashe kurwarsa ko bata lashe ba don haka ya cancanta ta mutu. Wai me yasa ake gudun mutuwa? In dai a irin rayuwarta ne da babu Momodou to kuwa mutuwa abun ai wa lale marhabin ce! To ta zauna duniya tayi me?3

Mutuwa mai tonin asiri, dama haka take? Haka dacinta yake? Ta ji wani abu yana yawo tsakanin makogwaronta da kirjnta ko makiyinta ba ta fatan ya ji. Ina ma daya daga cikin masu hayaniyar nan ya daga takobi ya caka ma ta. Ko ta je ta hadu da Momodou a wata duniyar!4

Hayaniyar ta cigaba da juya ma ga kai. Can sai ta ji ta dauke wuta dif.!

Ta bude idonta a hankali bata gano inda take ba sai ta mayar ta rufe. Ko bata tambaya ba ta san nan ne lahirar da ake ambato. Ta kara bude au sai anan ga lura aahe ba ita kadai ba ce mutane biyu ne tsaye a kan ta. Daya yana sanye da kayan likitoci daya kuma irin na masu aikin hukuma.

Suka ma ta sannu ta amsa a hankali, likitan ya fita dayan ya ce

” ya jikin na ki?”

Ta kalle shi sosai amma ba ta gane shi ba. Amma ta gane ba dan kasar su ba ne saboda yanayin hausarsa. Ya ce

” Mamanki ma tana kwance ta samu bacci “

Aai a lokacin ta ji hankalinta ya kara kwanciya. Kamar ya san abinda take tunani ya ce

STORY CONTINUES BELOW

” Nan asibiti ne ni ne na dauko ku na kawo ku. Ki kwantar da hankalinki. Ta kasa cewa kanzil illa dai ta kura ma sa ido. To idan nan asibiti ne kenen ba ta mutu ba? Kenan ba zata je ta tarar da Momodou ba? Shikenen labarin ya kare an rufe littafin kaddar. Kawai sai ta soma kuka, kuka mai yawa da ba ta fatan ta sake irin shi a duniya.2

Mutumin nan ya tsaye a kanta har ta kare kukanta ba tare da ya ce ma ta kanzil ba. Ya cigaba da latse latsen waya a hannunsa. Kwanansu biyu a asibitin ya zo ya dauke su ya kai su wani gida. Ya tara su ya ce1

” Ni sunana Asp Mukhtar Badamasi. Ni mutumin kasar Nijeriya ne. Na san za kuyi mamakin ganina cikin lamuranku bayan ba ku sanni ba. Ina karkaahin wata kungiya ne ta kare hakkin dan adam sai bincike da sanin makamar aiki ya kawo mu kasar Niger.

Kwanana uku a garin nan aka kawo mana rahotan da aka yi don neman tozarta wasu abun har yana nema ya zarce da kisa. Allah ya taimaka muka iso duk da dai an kusa makara. Amma so nake mu san menene ainihin matsalar because saboda irinku irinku muka bude wannan kungiya. So nake na san gundarin al’amarin don mu san yanda za a shawo kan matsalar.

Momma ce ta kwashe labarin komai ta gaya masa tana kuka. Ta karasa da

” Na rasa tun farko abunda muka yiwa Iliyasou mai zafi..na rasa wannan kiyayya”

Wani mamaki da ban haushi ya mamaye zuciyar Asp Mukhtar a fusace ya ce

” In this era? A wannan zamanin a wannan lokacin da ilmi ya shigo a ce har akwai still masu duhun kai da canfe canfe da zasu tara mutane wai duk dalilin maita? This is absolute nonsense! Za mu neme shi yanzun zai ga sammaci sai an bi muku hakkinku.”

Momma ta girgiza kai tana murmushin takaici ta ce

” Ka san wanene Iliyasou Tillaberi kuwa? Kar ka soma dan ba zan iya yaki da shi ba. Yakin da ba shi da amfani mu zo muna wahalar da kan mu daga baya ya zo ya sa a daure mu ko kashe mu. Ka bar shi ma ya ji da mutuwar gudan jininsa..innalillahi wa in a ilaihirrajiun Momodou ka bar ni da miki!”

Tayi kuka tayi kuka har ta gaji sannan ta ce

“Ni yanzu taimako daya za ka min ka mayar mu gida Najeriya in roki danuwana gafara. Zaman Niger ba na mu ba ne!”

Rukaiyatou ba ta ce komai ba magana wahala take ba ta. Tunaninta daya ne

” Za ta dau fansa, ga mutumin da yayi wa rayuwarta kisan gilla, yayi mata kaca kaca saboda fin karfi. Ya handame ma ta dukiya ya bar ta tana watangaririya a duniya babu gata. Tana jiran wata rana ta daukar fansa akan Iliyasou Tillaberi.1

Asp yayi iya yanda zai yi ya roke su su amince da shawararsa suka ki. Ya alkarwanta musu mota da zata kai su har cikin garin kano a haka aka kwana.

Washegari mota ta iso ya rako su har bakin motar. Ya ce a raka su tsohon gidansu su dauki abubuwansu masu muhimmanci wanda ba su kone ba. Har suka ce aa sai Rokaiyatou ta tuno takardunta na makaranta, ta ce a biya zata dauka. Duk abunda ake idonsa na kan Rokaiyatou. Sai yakan lalace a kallonta yana tunanin idan ta samu ingantacciyar rayuwa yanda za ta koma. Sai ya raya a ran sa cewa ina ma zasu yarda ya taimake au irin taimakon da yake niyyar ba su. Yana kallo suka kama ganya bayan ya taimaka musu da kudin guzuri.

Cikin ikon Allah suka biya ta tsohon gidansu takardunta da ta hada waje daya suna nan ba abunda ya taba su. Ta dauka tana mai fatan kar Allah ya kara dawo da ita garin Niamey.

**********************************

Kano, Nigeria.

Sai da suka kwana suka yini sannan suka shigo birnin kano. Jalla babbar Hausa, kano tumbin giwa yaro ko da mai ka zo an fi ka!

Momma ta kwatanta gidansu wanda ya zamo gadonta ita da yayanta a unguwar kawo. Har ta mutu ba za ta taba mantawa ba duk da sauye sauyen da aka samu.

STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da suka iso kofar gidan sai jikin Momma ya kara sanyi tana fargabar shiga saboda abubuwa da dama. Na farko irin rabuwar baram baram da aka yi, na biyu gidan ta ga ya kara lalacewa. Tun da can yayan na ta a saninta ma’aikacin wani kamfanin inshora ne, ta san yana cikin rufin asiri. Amma shekaru sun ja komai kan iya faruwa.

Ta fito daga motar da kyar saboda ciwon da ke kafarta Rokaiyatou na bin ta a baya. Akwai wani shago a kodar gidan wasu na zazzaune akan benci tsayuwar motar ya sa hankulansu ya dawo kan su. Momma ta dingisa kafarta tana dosar gidan sai ta hango wani shi ma yana kokarin shiga sai aka yi cirko cirko kowa yana yiwa kowa kallon sani. Ya nuna ta da danyatsa cikin mamaki ya ce

” Wa nake gani kamar Ramlatu?”

Maimakon ta ba shi amsa sai ta fashe da kuka tana mai durkusawa daidai kafarsa ta ce

” Yaya ni ce..ni ce Ramlatu ..ka yafe min..innalillahi wa i
nnailairrajiun!”

Tana kuka yana kuka ya mikar da ita ya ce

” Tashi mu shiga ciki yau ai ranar farinciki ce”2

A tsakar gida matarsa Harira ce ke alwala a bakin famfo ta gama tana kokarin daura dankwalinta maigidan ya shigo yana sharbe. Gabanta ya yanke ya fadi ta dafe kirjinta ta ce

” Baban Ali lafiya?”

Ya share hawayensa ya ce

” Addu’ata ce ta karbu yau, Allah ya dawo da Ramlatu gida. Allah nagode maka”

Harira ta bi su da wani lalataccen kallo na kaskanci sannan ta ja wani matsiyacin tsaki ta ce1

” Amma baban Ali ka dau alhaki na, ni na zata wani babban alamari ne ya faru nake kokarin jajanta ma ka. Sai ka ce fitsararriyar kanwarka da ta guje ka akan auren mai kudi, ta kare mata ta dawo gida. Ai mu tuni muka samu labarin miji ya mutu bai bar mata ko sisin kwabo ba. Shi ne yanzu ta dawo? Har da guzurin ‘ya? Gaskiya Ramlatu kin yi karkon kifi daga ruwa kin koma wuta!”

Wani abu marar dadi ya saukarwa Momma a rai. Harira ba bakuwarta ba ce ta san ta sarai, sai ta sunkuyar da kai. Ba ta ce komai ba.

Baban Ali ya dubi Harira cikin in ina ya ce

” kin..ji..kin.ji..ko Harira bana son diban albarka. Mutane sun diro yanzu sai ki sauke su da rashin mutunci. Haba Harira..Haba.”

Ya shigar da su wani falo jikinsu a sanyaye. Rukaiyatou sai rarraba ido take gani take matar nan za ta musu duka. Shi ya kawo musu ruwa ya sa aka siyo musu abinci don babu a gidan, Harira na tsakar gida tana habaice habaice.

Bayan sun nutsu ne aka yi hirar yaushe gamo. Suka yi labarin rabuwarsu aka yi kuka aka share hawaye aka yafe wa juna.

Yayanta na ta ya labarta ma ta shekarun baya aka kore shi daga aiko ba fansho ba garatuti. Yanzu ma gidan naau ya raba shi kashi uku ya bada hayar kashi biyu. Baya aikin komai sai buga buga Harira ce kashin baya gida don iga ke sanaar waina take kuma sayarda kayan masarufi. A haka har aka samu aka tura babban dan na sa Ali zaria yake karatu. A ranar dai a wannan falon suka kwana.

Dakin da ke tsakar gidan anan Harira ta zuba kajinta take kiwo. Baban Ali ya sa kafinta ya nemo tsohon silin ya raba daki biyu domin Harira ta ce ba ta ga uban da ya isa ya kwashe ma ga kajinta ba. A wannan rabin dakin anan Momma da Rokaiyatou suka koma zama.1

Wata irin rayuwa suka fara marar kan gado. Sai Rukaiyatoh ta kasa ganewa shin acikin halittu akwai marar imani irin mutum dan adam? Ita dai Momodou kadai ta sani mai imani shi kadai ta sani mai taimako amma ragowar duk kyamatar talaka garesu. Wai shikenen idan baka da shi da kai da banza duk daya? Mutane suna tuna lahira kuwa? Inda za ka je kai daya sai dai halinka ya cece ka. To menene duniyar kai da zaka tafi ka bari?1

STORY CONTINUES BELOW

A gidan Baban Ali a tsangwame suka abinci ma sai an damar ba su. Duk wata kyautatawa da za suyi a banza a wajen Harira. In ka gansu kamar almajirai babu kulawa. Babu abinda ke dagawa Rokaiyatou hankali irin ciwon uwar da ke kafarta har yanzu ya ki warkewa. Sun je asibiti amma abun har yanzu shiru.

Mutane biyu ke haya a gidan. Akwai wata mata da mijinta yan jihar Naija. Sai kuma wata baba yar tsohuwa da mai kula da ita a wani bangare. Amma duk tsakar gidan daya ce.

Wani abun al’ajabi shi ne duk tsangwamar nan da raahin gata da suke ciki sai ya zamo Rukaiyatou tana da matukar farin jini. Samarin unguwar kamar an sa musu ita gasa daga wannan ya yiwo sallama sai ka ji wani ma. Wannan abu yana konawa Harira rai ita me yanmata a gida. Gabadaya sai ka va annurin fuskarta ya canja don tsananin cin fuska sai ta cewa san aiken

” ka cewa abokin zinar tata tana can dakin kaji ya shigo ciki su tsadance”1

Wannan magana tana bakantawa Rukaiyatou da Momma rai. Rokaiyatou ta kan yi kuka tana kallon mutuwa a matsayin babbar abar tona asiri. Oh rayuwa yau ina babanta? Yau ina Momodou?

Harira mai waina wata irin mace ce marar dadin zama. Ko mijjnta bai isheta kallo ba saboda yanzu ba shi da shi. Idan ta zauna suyar wainarta kuwa ko sallah ba ta tashi ta fi ganewa idan ta gama sai ta jero su.

Ranar wata asabar tana cikin suyarta sai aka doko sallama. Ta leko daga ‘yar langa langa da ta kewaye ta sai gayi ido biyu da Anti Saude. Ai kuwa tayi zumbur ta mike tana kwalawa diyarta bilki kira kamar zata fasa musu dodon kunne

” Dan ubanki fito ki taya ni suya, kin nannade a daki kamar macijiya wato ni wuta ta karasa ni ko? To don iyayenki idan na mutu zan ga uban da zai ciyar da ku tunda naki uban ya zama Allah zi wahidin”

Ta tafi da sauri ta je ta taro bakuwar da ba tata ba.

” Anti saude..Yau kike a gari in ji maki bako”

Anti saude jikar Baba yar taohuwa ce ta gidan. Yar gayu ce ta kin karawa za ta kai shekara talatin da biyar. Bata da aure ba kuma ta taba aure ba. Gogaggiyar yar duniya ce mai tashe da Naira son motar hawa ma biyu gareta.

Marainiyace gaba da baya don Baba yar tsohuwan nan ita ta haifi babanta kuma ita kadai ta rage ma ta. Babau wanda ya san takamaimai aikin me Anti saude take amma kudi ba sa yanke ma ta. Zama take a gidan kan ta sai dai takan zo wa kakarta ziyara akai akai har ta dan kwana biyu tana mai kawo mata abun bukata. Kudin hayar gidan ma ita ke biya. Tsohuwar nan tayi tayi ta dawo da ita hanya abun ga faskara sai kawai ta bi ta da addua.

Anti saude mutuniyar Harira mai waina ce saboda akwai sakin hannu kamar bata san ciwon kudi ba. Da yake kuma ita harira kaska ce rabi mai jini sai ta manne ma ta.

‘ Yar gajeruwa ce mai dan kauri ba dayawa ba, fuskarta kadaran kadahan. A ranar ta yi shigar wani leshi fari tas mai manyan huda huda kuma ba ta yi masa shafi ba don haka ana hangen ma fi akasarin halittar jikinta. Ba ta yafa mayafi ba dama haka take yawo.

Harira tayi sauri ta dauko kujera yar tsugunno. Ta aiki dan ta isyaku ya siyo mata lemon roba coca cola. Harira ta ce

” Lafiya kuwa Anti Saude. Nayi cigiyarki har na gaji.”

Fuskarta fal faraa ta ce

” wallahi Harira wata yar tafiga ce ta kama ni amma yanzu na dawo har sai kun gaji da ganina”

Harira ta ce

” Haba? Ko da na ji bari na dan debo miki wainar ki dan taba”

Sai a loakcin ta kura ashe bilkin bata kama ma ta suyar wainar ba har fa kan tandar ta soma konewa. Ta kwala ma ta kira, Bilkin ta fito tana yatsina ta ce

” Wai ke umanmu mutum na barcinsa ba za a bari ya huta ba?”

Harira ta aiko ma ta da tagwayen dakuwa da yatsunta goma ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” Ubanki! Ubanki na ce. Idan baccin rana abun yi ne ni uwarki in zauna in yi mana amma idan nayi ke hanjin cikinki zai bari ki runtsa? Tunda ubanki bai san ya nemo ba kin ga ai ni dole na hana idon nawa bacci. Za ki karasa ki zubo ma ta ko sai na zo nan na maida ke abun kwatance?”

Bilkin ta karasa tana gunagunai. Ba a dade ba Rukaiyatou ta fito daga dakinsu fitsari ya matse ta za ta je bandaki. Sai ta dauki buta Harira ta daka mata tsawa ta ce

” Ke! tinkiya uwar tambele..ina za ki?”

Ta ce

” Sabani naka bida zan yi sayi”

Ta yi mata dakuwa ta ce

” Sahanin daga lahira ubanki ya aiko? Ajiyemin butata ‘yar Allah bani kawai!”

A sanyaye ta ajiye ranta a bace ta koma daki. Ba a taba yi ma ta irin wannan zagin ba a duniya.

Anti saude tana kallonsu ranta bai ma fa dadi ba. Ta share ta ce

” Ina kuma kuka samu ‘yan Nijar?”

Ta ce

” Wasu ‘yan alakakai ne talauci ya koro su suka zame mana karma karma. Tunda uwata ta halicceni ban taba ganin masu daudar talauci irin wadannan yan hauren ba”

Anti saude ta gyada kai ta ce

“Amman kuma yarinya
r kyakkyawa da ita daga gani za a ci kasuwarta musamman a kano. Bakanon mutum da son farar mace..’

Ran Harira ya baci amma bata nuna ba ta tsani ta ga ana yabin kyawun yarinyar.

An yi wajen tsawon wata takwas suna zaune a gidan da dadi ba dadi.

Sai dai Momma bata cika lafiya ba, sai Rokaiyatou ta fito ma ta da tabarma tsakar gida ta sha iska. Harira a ranar ta gama suyar wainarta tana zaune a kofar falonta tana zukar madara peak sabida aikin gaban wuta. Ba ta ce musu ci kan ku ba illa ma ta ware rikodarta da ta sa kaset din waka na barmani coge. Sai abun kuma ya zama habaici ta fara bin wakar a shagubance

Kai ku kama sana’a mata ko don ku huce takaicin zamani…lale lale maraba da ke zinariya

Kai ku kama sana’a ayye..ai kuli kuli ko ai kosai, ai furar madu ko dan wake ko da dako aka samu ma ayi

(Amshi)

Ayye kida na sanaa mata macen da bata sanaa ta bani…

Banda sakarai bankaurar banza ,mata suna ta sana’ar nema, ta sai da gulma ta sai tabarma, kullum asin da asin sai ta ara…..

Su dai ba su ce komai ba. Ba ta kai ga ajiye gwangwani ba yara suka shigo suna oyoyo yaya Ali ya dawo. Harira ta biye musu cikin farin ciki, tana kaunar dan na ta Ali. Suka gaisa tana ta mai korafin bai kira a waya ba an shirya ma sa abun sauka, an kuma gyara ma sa daki.

Sai a lokacin ya lura da bakuwar fuska suka gaisa. Uwar ta masa bayanin su a wulakance ya kara gaida Momma ya ma ta sannu da kafa.

Washegari ya fito daga daki Rokaiyatoh na zaune kan turmi ta gaishe. Ya gaida Harira ta ba shi karin safe. Abinci yake ci amma kamannin yarinyar sun dauke ma sa hankali. Wannan da a makarantarsu take ABU Zaria da yanzu ya san an sa gasa a kanta. Ai ‘yan clique din su kadai sun isa suyi fada akanta. Da zai wuce ya ce ta zo ta gyara ma sa daki. Ta ce “to”

Dakin na sa ba wani babban daki ba ne, irin dai na samari masu son gayu. Fastoci ne a manne a bangi manya manya na ball na club din real madrid. Sai katifa sai kayan kallo.

Ta gyara koina fes fes. Wajen gyatan kayan kallon ne ta ci karo da fina fina batsa kala kala. Gabanta ya fadi ga shi mai kirki a fuska, tai sauri ta mayar. Ta bar dakin.

Wata irin yunwa harira ke barinsu da ita. Su rasa unda zasu sa kan su. Momma ta fi dagawa Rokaiyatou hankali saboda ita ba lafiya ba..kafar nan ta matsa ma ta. Momma kan yi kuka ta ce

STORY CONTINUES BELOW

“Rokaiyatou bango ya fadi, Momodou babu ko gawarsa ban sa a ido na ba”9

Irin wannan maganganun kan sa su shiga tashin hankali.

Ranar da yunwa suka kwana. Da daddare Rokaiyatou ta kasa bacci tana ta murkususu. Sai ji an budw kyauren daki ta tashi zumbur! Ali ne.

Yayi ma ta magana rada rada

” ba kiyi barci ba kina jin yunwa ko? Ta gyada ma sa kai kamar kadangaruwa a tsorace. Ya ce ta biyo shi ta karba. Ta bi shi. Abincin ya ba ta ya ce

” Duk sanda kike jin yunwa kizo ki gayamin kin ji?”

Ta ce “toh” cikin murna

Ta kaiwa Momma suka ci suka koshi sukai kat! Tunda ta zo kano bata taba cin abinci ta koshi irin ranar ba. Wani irin dadi ya mamaye ta taji kaunar Ali a ranta. Har da nama!Dama a kano akwai mutane ma su kirki da za su bawa mutum abinci? Duk gidan ta daina ganin mutuncin kowa sama da Ali.

To sai halayyar lallabowa ya bawa Rukaiyatou abinci ya zamo wa Ali farilla. A lokuta da dama kuma sai yace ta zo ta gyara ma sa dakin sa. Ko kuma ya kira ta ya ce auyi hira. A lokuta da dama sai hakan kama hannunta ko ya ce zai taba nannadedden gashinta marar gyara sai yace ba ta son kulawa da shi. Ranar har sabulu ya siyo ma ta wai ta wanke, tayi ta murna. To ita bata saba da hakan ba sai takan nuna ma sa bata so ya taba ta. Sai yayi fushi ya ce bata dauke shi danuwanta ba.

Da yake ita ba wai tana da wayo ba ne ba ta dau hakan a matsayin gagarumar matsala ba. Ita dai tsoranta sau da dama kar ta je ta bata ma sa rai ya hana su abinci. Saboda irin gigitar da yunwa take jefa su ciki.1

Momma bata kawo komai ba sabida yanzu ta lafiyarta ma take. A asibiti an dora ta akan magunguna ba su sa bacci da kasala. Komai yanzu Rokaiyatou ke ma ta.

Ali ya gama gajeran hutunsa a ciki yayi wa Rokaiyatou alkawurra da dama. A ciki har da yana son ta kuma ba zai dade ba zai dawo. Rokaiyatou ba wai son Ali take ba, a zuciyarta babu wani gurbi da ta bari na so. Ka wai dai Ali ahi kadai ha nuna musu kauna tun dawowarsu hakan ya sa ta ba shi matsayi daban.

Bayan tafiyar Ali da sati 4 ya dawo. Wannan dawowar ta Ali ita ta canza salon rayuwar Rokaiyatou. Dama an ce Hau ba ta wuce ranarta.

Harira ce ta jefi Rokaiyatou da kalmar ” karuwanci” Momma ta gaji ta tanka suka yi cacar baki. Cikin kuka Momma ta ce

” Ni ban san me nayi wa mutane suka tsane ni suka tsani ahalina ba. Wai Rukaiyatou ce karuwa??? Karuwa fa?2

Don tsabar bakin ciki kawai sai tabyanke jiki ta fadi. Fadar irin tashin hankalin da ya biyo baya daga Rokaiyatou , Ali har baban Ali zuwa zaryar asibiti abu ne da bazai labartu ba. A asibiti aka gano tana dauke da cutar diabetes aka ba ta gado sai cacar kudi ya biyo baya.1

Rokaiyatou bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba ga shi zaman asibiti yana neman gagararsu. Baban Ali da Ali suke buga buga. Kullum zarya tsakanin gida da asibitin. A lokacin ne Ali ya cimma burinsa akan Rokaiyatou.

Ya nuna mata cewar babu mai kaunarsu kamar shi kuma bata da danuwan da ya wuce shi. Shi ke ba ta kudin abincin da zata kai asibiti da kuma na mota. Da hilata da yaudara irin ta tashi ta dan boko sai da ya san yanda yayi ya ci galaba a kanta. Sai ya lallabata da tayi shiru kar ta gaya ma kowa, don idan ta fada ba zai kara bata kudin zuwa asibiti ba.2

A wata rana aka rubutawa Momma allurar insulin da za a mata babu kudi babu dalilinsu. Haka ta garzayo gurin Ali yayi amfani da ita ya bata kudin a hannu N2500. Ranar ta ji kamar ta mutu don bakin ciki. Ji tayi ina ma ba a halicce ta.9

Haka ta isa asibitin a galabaice. To amma abunda ya fi ruda ta shi ne Momma bata kan gadonta. Da ta tambaye na kusa da gadon ina mai gadon. Sai aka ce mata ai bayan fitarta kadan matar ta cika!3

STORY CONTINUES BELOW

Wani abu ne kamar walkiya ya gifta ta idonta, daga nan ta ji dif! Wadanda suka yi zaman makoki su ne suka bada labarin cewa kwananta bakwai ba ta san inda kan ta yake ba.

Tana ta kirga kwanakin da zata mutu ba ta mutu ba. Sai take kallon mutane wai kuwa suna jin yanda take ji kuwa? Amma me? Ta san ba zata zauna a gidan nan ba dole ta samo mafita. Momma na da kwana 60 a kasa, sai ciki ya bullo ma ta.8

Abin ya faro ne kamar abun al’mara. Tunda aka yi mutuwar nan bata fitowa. Ali ya dawo hutunsa ta kura ko harkarta ba ya shiga. Ba ta wani damu ba.

Baban Ali ne ya shigo bazar bazar a fusace ya tarda harira tana kullin sikari ya ce

” wai ke harira yaushe za ki saka ido kan ‘ya’yanki? Wannan yarinyar Bilki daga yau wannan ya zo sai wani. Tunda ba karatun za tayi ba ki ce na ce ta tsaida miji. Sau biyu tana rubuta jarabawar fita daga sakandare ta kasa tabuka abun kirki..ki gaya mata aure zan ma ta wallahi”

Abun ita ma yana damunta yau sai aka dace ta ce

” Wannan alamari na bilki akwai sa hannun makiya. Ji fa yaron nan kwanaki dan gidan Alhaji ya zo kanar gaske. Amma daga cewa ya fito ba amo ba labari”

Ya ce a fusace

” kin bar su suna yawon ta zubar ya kuwa zai aureta? Sai nayi magana ki ce ke kike ciyar da gida ni menene ban miki ba lokacin da ina da shi? Wallahi tallahi in dai haka arzikin mace yake to Allah wadaransa. Ki ce nace ta fidda miji..atoh”2

Kafin ta ba shi amsa sai Anti saude ta fito dama ta zo jiya. Aka gaisa. Auna cikin gaisawar ne Rokaiyatou ta fito ta gaishe su ta shiga bandaki. Baban ali ga bi ga da
kallon tausayi, yana kaunar yarinyar yana tausayawa maraicinta. Ya kudurce a ransa inahallahu sai inda karfinsa ya kare, zai kula da ita.

Anti Saude ta bi ta da kallo har ta bace. Cikin sauri ta ce da Harira

” wai me yasa ba ki da lura ne? Yarinyar nan ciki gareta”2

Harira da ke zaune ta mike ta ce

” wani irin ciki kamar a wasan kwaikwayo?”

Baban Ali sai ya ji ya gagara tsayuwa gabansa yana faduwa. Ya kalli anti saude rai a bace ya ce

” Haba saude kamilar yarinya kamar wannan ko fita ba ta cika yi ba”

Ta katse shi da” cewar wallahi baban Ali yarinyar nan ciki gareta, amma bari ta fito.”

Kawai sai harira tavrangada guda ta ce

” Ahayye abun boye ya fito fili. Har aka dunga zagi na wai bakin cikina ya kashe Ramlatu don na ce da diyarta karuwa. To ai ga shi nan”

Baban Ali gabadaya jikinsa a sanyaye yake ba don komai ba sai don ya ga yarinyar suna mutunci da Ali. Ranar har ya ga ta fito daga dakinsa wai ta je gyara har ma ya tsawatar ma sa akan hakan. To tunda aka ce ciki sai zarginsa ya darsu kan Ali don yarinyar ba wani fita take ba. Amma dai ya zuba ido.

Rokaiyatou na fitowa harira ta rufe ta da duka. Ta ce

” uban waye yayi miki ciki?”

Baban Ali ya finciketa ya ce

” dalla malam ki bari a bincika mana, yanzu haka ma abun a gindinki ya ke”

A fusace ta ce

” Ban gane wannan bakin da ka ja ba fassara min. Yarinyabta yo ciki kwararo ka ce ba za a daketa ba. Na tabbatar da bilki ce da yau sai dai na dau ciki nayi goyonsa wata tara idan na haihu na sa ma ta bilki, domin kuwa ka kasheta!

A nan Baban Ali da Anti saude suka lallaba Rokaiyatou har ta fada musu cewa Ali ne.

Baban Ali ya jingina da bango hasashensa ya zamo gaskiya. Ya sa a kira ma sa Alin. Harira tana cewa

” ji munafukar yarinya algunguma abun a kaina zai kare? Dan nawa za ayi wa sharri”

Ali yan zuwa babansa bai wata wata ba ya kwaahe shi da mari guda biyu. Ali ya ce fafur ba shi ba ne. Ai fa gida ya rikice. Kan ka ce kwabo harira ta zari mayafinta akan igiya ta tafi kawo police starion ta taho da ‘yansanda mata biyu wai au kama Rokaiyatou ta laqa wa dan ta sharri.

Baban Ali ne don bakin ciki ya ce

” Harira wallahi idan kika yarda matar nan ta tafi da Rokaiyatou to ke ma ba zaki zauna mun a gida ba. Sakin ki zan yi. Aure da Rokaiyatou da Ali ba fashi!”

Kawai sai Harira tayi zaman ‘yan bori tana birgima a kasa tana kuka

” shegiyar yarinya ta zame min kadangaren bakin tulu, in kar ta in fasa tulu in barta ta bata min ruwa. Auren nawa na shekara aahirin da biyar za a min kandagarki da shi akan na sa a fitarwa da na hakkinsa?” A daren ranar ba wanda ya runtsa.1

Da tsakar dare Rokaiyatou ta sadado ta fito daga daki, lokaci yayi ta gayawa kan ta. Za ta taba kofa kenen ta ji an ce

” ‘yar Nijar”

Ta waiwayo tayi ido biyu da Anti saude. Ta ce da ita kai tsaye

” ka da ki fita wahalar banza za ki sha ki zama karamar karuwa abunda zai raba ki da namiji bai fi kudin abinci ba.”

Rokaiyatou tayi shiru tana kallonta

Ta ce yar nijar ki yarda da ni. Rokaiyatou nan take ta yarda da ita, wa zai taimake ta in ba ita ba? Daga ranar ba ta kara kwana a gidan baban Ali ba!

Anti saude ita ta tsaya tsayin daka akan Rokaiyatou ta gudu da ita. Ta kai ta asibiti aka cire ma ta cikin jikinta. Sai da Rokaiyatou tayi tsawaon wata tara a gidan Anti saude idan ka gan ta ba zaka taba zaton ita ba ce. Ta bata cima mai kyau ta ba ta kulawa. Tayi bulbul ta zama wanke hannu ka taba. Ba abunda ba a koya ma ta ba, yanayin cin abinci, tafiya, magana uwa uba kwalliya!

Anti sauden kan ce da ita

” wannan hausar ta ki ki gyarata ki daure ki iya hausar kanawa. Ba a cika so farat daya a gane mace daga inda ta fito ba. Ki koyi canja harshenki, ki koyi wayo da hilata ta yanda zaki gwanance a yaudarar da namiji!”

Rokaiyatou ta kan yi murmushi . Ita kan ta ta san ta goge kuma ranta a kekashe yake. Kudi za ta nema don ba ta ga amfanin zama da babu ba!

Watarana da daddare Anti saude ta ce

” yar Nijar saurareni da kyau. Yanzu na miki iya panel beating din da ya dace kin fara zama irin macen da maza zasu gani su saka gasa akanki. Kar da ki sake ki manta jikinki shi ne jarin ki, shi maza za su dakawa wawaso. Ina so ki daukaka, ki fi haka…kina ji na ko?… akwai wata kungiya……”4

Wani sashe na zuciyar Rokaiyatou yana hango ma ta Momodou ya na yi ma ta bye bye.

Kun ji masomin labarin Mai Tafiya

Mai Tafiya…wani guzuri ka tanada??????

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *