MAI TAFIYA CHAPTER 7
Ashe tsakanina da ke wani alamari ne mai ban mamaki? Ashe tsakanina da ke ‘yanuwantaka ce? Ashe tsakanina da ke soyayya ce? Me ya sa abubuwa ba sa zuwa a daidai lokacin da ya kamata su zo? Me ya sa su kan zo a kurarren lokaci? Me ya sa????
Almustapha Iliyaso Tillaberi7
( you may need a tissue paper, this is going to be a tough ride. Going on a break i have exams to write. Do not conclude until you have read the last chapter, the last sentence, the last word. Few chapters to go inshallah)2
Hajiya Hadiza ke tafiya akan titin zoo road da ke kano. Tana hanyar zuwa wani biki diyar kawarta na nunawa sa’a. Nakasasshen mijinta ta bar shi a gida ko bi ta kan sa ba ta yi ba. Warin da ya isheta ne ma ya sa ta sa aka maida shi baskwata don ba zata iya ba.9
Kiri kiri abokiyar zamanta Khulsumou da ke Niamey ta ki zuwa sai faman aiken malamai ta ke. To ita ina za ta iya? Ta godewa Allah Almustapha dan ta shi ke kan komai da ina za ta sa kanta?
Ta san in dai ta khulsumou ne da ta wawure komai ta gudu ta bar ta da salallami.
A zuciyarta ta kagu maigidan na ta ya cika ko ta rabu da alakakai. Dama ai kowa ya debo da zafi bakinsa ya ke kaiwa. Ita ta aike shi ya zalunci jama’a ga shi nan abu ya dawo kan sa zai shafe su. Inaa…ba da ita ba.4
Wannan gidan bikin da zata je ta za ta hadu da matar mataimakin shugaban kasa dalilin ma da ya sa ta ci burin bikin kenen. Sun yi ajandar cewa za su hadu su tattauna kan batun ‘ya’yansu. Akwai diyarta Ramlat da take yiwa Almustapha hange. Ta san sun dace yanayin arzikin gidajensu ya dace da juna.
Idan ta biyewa Almustapha ta san ba zai tsaya yayi zabe yadda ya dace ba. Gwara ta zaba ma sa wacce ta dace da shi yadda sunansa zai kara daguwa a idon duniya.
Wani abun ma shi ne ba ta ma san inda dan na ta yake ba ko wani hali ma yake ciki. Kwana 2 ma ba suyi waya ba. Dama haka halinta yake in dai ba wai tana bukatar kudi ba ko wani abu da wuya ta neme shi don a ganinta kar ta katse ma muhimman aiyuka.1
Za ta neme shi da zaran ta gama da gidan bikin nan, dole ne ma ta neme shi. Tunaninta kenen.
Dama zaune take a bayan mota gefen mai zaman banza direba na jan ta. Da yake ma’abociyar karatun jaridu ce sai ta ce bari ta sayi jaridu akan juction. Ta siya aka ba su hannu suka wuce. Wani abu daya tak ne ya sa ma ta luguden zuciyarta. Labarin farko da ta gani a shafin jaridar daily news da kuma Nigerian ne ya girgiza ta. Ga abunda ta gani
7
5
STORY CONTINUES BELOW
Wani kara tayi ta ce
” Whattttttttt!!!”
“Karya ne wallahi! Sharri za a yiwa da na! Karya ne!”
Wani irin gumi ne ya fara tsattsafo ma ta ta koina. Ta shiga rudani. Amma wani sashe na zuciyarta na raya ma ta sharrin abokanan hamayya ne. To yaushe ma Almustaphan ta yayi aure? Yaron da aure ma baya gabansa.
Wani sashe na zuciyarta na so na yarda wani sashe ya hane ta. Ai daga gani ma kazafi ne, an ga danta mai karancin shekaru ya faso gari ana ma sa bakin ciki.
Ba shiri ta nemi wayarta tana ta gwada wayarsa. In dai an yi ne don a bata masa suna sai ta sa an tabbatar an kama su. Duk irin kiran da take wayar a kashe. Kanta ya kara daurewa.1
Daidai lokacin ta iso gidan bikin. Tayi sauri ta kama kanta ta mayar da nutsuwarta. Wannan ne damar da take da ita wajen ganin ta hadu da Hajiya murjanatu su kulla alaka. Ka da ta bari damar ta wuce akan wani zancen shafa labari shuni.1
Tana gamawa da gidan bikin za ta san yadda za ta yi a kama gidan jaridun nan. Yanzu haka ma labarin bai bazu ba. Za ta sa dan na ta ya je gidan radio da talabijin ya musanta ya wanke kansa tun kafin masoyansa su juya masa baya. Lokacin siyasa ya matso bata son abinda zai taba sunan danta.1
Kawai sai Hajiya Hadiza ta biris ta yi kamar bata ga jarida ba. Ta shiga gidan biki cikin taqama da izza. Amma zuciyarta fargaba ce da bacin rai. Tunaninta kawai ina Almustapha ya shiga, don tana so tayi magana da shi da gaggawa ta ji wacce a ciki.
Abun farko da ya sa jikinta ya fara yin sanyi bai wuce yadda uwar bikin Hajiya Hanne mai gwal ta karbe ta ba. A yadda suka saba kwata kwata sai ta ga ba wannan.
Yadda aka nuna ta a wajen matar mataimakin shugaban kasa ma bai mata ba, don ganin ai kamata yayi a ce su ne gaba gaba. Ba su san wacece ita ba?
Kawai sai tayi gaban kan ta. Ta fara shiga ana damawa da ita. Ta lura da gani ganin da wasu ke ma ta amma ta dauki hakan hassada kawai.2
Ba tayi kasa a gwiwa ba ta fara shigarwa Hajiya murjanatu batun da ke ranta. Ba ayi wata wata ba ta daka ma ta wata mahaukaciyar tsawa da ya bar Hajiya Hadiza cikin matsanancin mamaki. Ta ce
” Kina da hankali kuwa Hajiya Hadiza?! Ko kan ki ba daya ba? Ramlat din za a dauka a bawa sakaran dan ki manemin mata! Dan ta’adda! Ke idan kina cin kasa ki kiyayi ta shuri!”1
Wani irin abu ne ya daki kirjinta ba da wasa ba. Kafin ta ce wani abu Hajiya murjanatu ta wurgo ma ta wata jarida
3
” kin dauka mu mahaukata ne? Ko bamu san abinda duniya ke ciki ba? Lokacin da dan ki ya sha sarka, kya gane annabi ya faku”
Cikin gigita Hajiya Hadiza ke cewa
” karya ne Hajiya! Wannan aikin makiya ne”
Hajiya Murjanatu ta watsa mata banzan kallo ta ce
” Abin da ake bugawa a jaridu da gidajen talabijin shi ne karya?”
STORY CONTINUES BELOW
Kawai sai ta dauki remote ta kunna tv da tai tashar da take bukata ta ce , wanna ma karya ne?
Wani irin juyowa Hajiya Hadiza tayi ta kurawa Tv din kallo cikin matsanancin tashin hankali ta ji yawu ya kafe ma ta kaf ganin abunda take kallo
2
Ta kuma canja tashar talabijin din ta ce “wannan fa shi ma karya ne?”2
10
” lahaula wala kuwwata la haula wala kuwwata”
Su ne kalaman da Hajiya Hadiza ta samu furtawa cikin dimuwa. Wani irin abu take ji a kirjinta, wani irin faduwar gaba.
Rokon Allah take so tayi ta rasa takamaimai me zata roka saboda rudani. Kawai sai ta zari jakarta da mayafi ta fita bazar bazar kamar mahaukaciya sabon kamu.1
Wayarta ta dauko tana ta rusa masa kira amm bata shiga. Daga karshe ta tuna wani private layinsa na etisalat ta gwada kira ko za a dace. Tana fara bugu ta ji gabanta na bugawa wayar har zata tsinke ta ji an dauka. Cikin sauri ta ce
” Almustapha!! Me ke faruwa ne? Menene yake faruwa? Wasu irin munanan labarai nake ji?”
A wata irin murya a kasalance ya ce
” Mummy…! Mummy ina police station… Mummy ki taya ni addua!”
Tun da take da Almustapha bai taba yi mata magana a irin wannan muryar ta nuna sarewa ba. Sai ta ji wani abu ya daki kirjinta, ta ji wani yarr a jikinta.
Almustaphan ta! Gudan jininta! Shi ke nan guda daya tilo gurinta.
Akwai matsala, akwai babbar matsala.
K
awai sai ta tsugunna a wajen ta fashe da kuka cewa take
” Innalillahi..wa innailairrajiun”4
*********************************
Wani irin ciwo kan sa ke yi kamar zai rabe biyu. Tun da yake a rayuwarsa bai taba shiga tashin hankali irin na yan kwanakin nan ba.
Ya wayi gari da wani mummunan al’amari mai ban alajabi da kusa sa kwakwalwarsa tarwatsewa. Wai an kashe Rebecca a cikin gidansa kuma wai Rukky ita ce da wannan aiki.
STORY CONTINUES BELOW
Tunaninsa ya kara daurewa ne ganin yadda suka rabu da Rebecca a cikin gidan lafiya lafiya kafin ya fita. To har yaushe Rukky ta shigo ta kasheta ta dauki gawarta ta saka a boot ta tafi? Wani irin rikitaccen al’amari ne wannan?1
Ganin irin labaran da ke yawo a jaridu da gidajen talabijin na gari ya gane cewar akwai wata a kasa. Kamar wani shiri ne da aka yi shekara da shekaru da shiryawa aka tanada daidai wannan lokaci domin a tarwatsa shi.
Bai san ko waye ba amma yana tabbatarwa da kan sa akwai hada hannu da jamiyyar abokanan hamayya.4
Almustapha ya san yana da makiya, makiya ba na wasa ba amma fa bai taba zaton kiyayyar ta kai haka ba. Sai yake ganin kamar an yi anfani da Rukky ne domin a cimma buri akansa.2
Amma da gaske Rukky ta kashe Rebecca? Zancen da ya kasa kwanta ma sa a rai kenen.1
To idan ba ita ta kashe ta ba ya aka yi gawarta ta zo boot din motar ta? Zai bincika sai ya gane inda laujen yake a cikin nadi.
Ya wayi gari yansanda sun tafi da shi kan cewar za suyi masa tambayoyi. Maganar da sa hannunsa a kisan Rebecca ya sa ‘yan gari babu abunda suke masa shi da Rukky sai tofin Allah tsine.
Babu wani labarin sirrinsa da bai gani yana zaga gari ba. A halin da ake ciki investors din su dayawa ne suke zare hannun jarinsu daga kamfanin I and A. Tsoronsu kar a maka shi a kurkuku dukiyarsu da suka dulmiya a kamfaninsa ya salwanta.1
Hatta faifan video din da ke yawo na fadan Rebecca da Rukky ya sa kan sa kara daurewa. To wa ya dauka? Wannan alamarin ya sa ya zargi akwai wata manakisa.2
Tambayoyi ake ta jero masa, ya kuma gaya musu iya gaskiyar abunda ya sani.
Ya bar gifan ne da dare misalin karfe bakwai na dare ya fita wani mitin. Kuma shi rabonsa da yayi magana da Rukky ma ya manta. Domin daga ranar da aka yi fadan nan ma bai kara contacting din ta ba.
Bai kara jin wani labari ba sai kiransa da aka yi daga police station na mummunan abunda ya faru.
To zarya dai aka cigaba da yi da cike ciken takardu amma ba su da wata hujja kwakkwara da za su daure shi da ita.
Zarge zargensa da ake yi a gari kuwa ya zaga ya karade koina. Yawa yawan masu zaginsa mutane ne da ya taimakawa mutane ne da yake lullube fuskarsa don su ga mutuncinsa. Amma a yanzu sai a sayi lokaci a gidan radio ma a zage shi tas! A tsine masa.3
Babu abunda ya fi kona masa rai irin watsi da jamiyyarsu ta NPN ga masa. Jamiyyar da ya sa komai nasa da yake tunanin ita ce silar daukakarsa. Sai ga shi ba a je koina ba sun nuna ba sa yin sa. Saboda kar ya bata musu suna.1
Ashe dama haka duniya take? Shi din da mutane ke haba haba da shi suna marmarin su kusance shi su rabe shi sai ga shi a kwanaki kalilan kowa ya guje shi?1
Idan ya tuna Rukky na garkame a cell kafin ayi shirin zuwa kotu sai ya ji wani abu ya sari kan shi. Menene gaskiyar lamari? Ya kamata ya gan ta. Dole ne ma ya ji daga bakinta.
Da lauyansa wani barrister kabir tukur yayi magana. Ya kalle shi da alamar gargadi ya ce
” Almustapha ya kamata ka gane cewar yanzu duniya idonta akan ka yake. Ka ga maganar siyasarka ta riga ta rushe. Mutane dayawa na zargin da sa hannunka a kisan nan. Matarka ce Rebecca aka kashe, kai ne kuma ya kamata a tsaya tsakin daka ka bi ma ta hakkin jininta.
Yaya za a ji labarin kana neman haduwa da wacce ake zargi da kashe matarka? Ba ka tunanin za a kara tabbatar da cewar bakin ku daya?
Kar ka manta zance na yawo a gari cewa karuwarka ce ba ka tunani ya kamata ka musanta hakan? Abun da nake shawartarka shi ne lokaci yayi da za ka nuna baka san ta ba!”1
STORY CONTINUES BELOW
Wani irin kallo ya dago ya qurawa barrister gabansa na lugude. Eh ya san cewa rayuwar da suka yi da Rukky ta haram ce shi yasa abubuwansu ba ko digon albarka a ciki. Amma ya ce bai san Rukky ba? Ya juya baya zai iya kuwa ? Anya?1
Barrister ya cigaba da cewa
” kar ka manta wannan babban case na kisan rai, ka san kuwa ba adauki rai da wasa ba. Kar kuma ka manta wannan wacce aka kashe din mabiya addinin kirista ce. Kungiyar kare addinin kirista a yanzu kai take kallo kai kuma ta saka a gaba. Motsi kadan za ka yi su sako ka gaba. Kar a manta ana zarginka da sa a hannu a kashe Rebecca ne don ka boye sirrin dan ku da aurenku.
Da ni ne kai ita wannan yarinyar da ake zargi da kisan zan cinnawa karnuka. Ba karuwa ba ce? Ka game kai ma da hukuma ku yake ta.Yanzu fa ka san lauyan gwamnati ne akan lamarin, wannan yarinyar ce vs kano state. Ka san a kotu sai an kira ka ka bayar da bayani. Ka san fallasar da hakan zata jawo?
Hakan da za ka yi shi kadai zai sa ka tsira da kan ka. Ka nuna cewa ka tsaya tsayin daka wajen bi ma Rebecca jininta . Ka tabbatar Rukky tayi shekaru aru aru a gidan yari!”
Wani irin yarr ya ji jikinsa yayi wata irin zufa tana karyo ma sa. A hankali ya ce
” To idan ba ita tayi kisan ba fa? Sai a bar ta ta kare a gidan yari?”
” Toh ba karuwa ba ce!” Cewar barrister a fusace ” ko bata kare yanzu ba dole wataran zata kare. Dama iyakacin makomarta kenen. Ya kamata ka gane fa karuwa bata da daraja bata kuma da wata rawar takawa mai amfani a rayuwarka. Amfaninta daya ta zame maka abun nishadi a rayuwarka. Kuma ta ri ga ta zame maka. Abunda yayi saura kawai ka yar da kwallon mangoro ka huta da kuda”5
Tayi ikirarin zata kashe Rebecca da fatar bakinta, ga shi video ya nuna sun yi fada. Ka ga akwai motive na kisan kenen.
Kar ka manta bincike akan gawar Rebecca ya nuna karfe 8 na dare zuwa karfe 9 aka kashe ta. An samu shaidu cewar Rukky ta shiga gidanka a tsakanin wadannan lokutan. Me ya kai ta?
A kama ta ra’ayul aini da gawar matar a boot din motar ta! An ce fa ganin za a bude boot ya sa ta zaro kudi za tayi bribing din su. Bayan an kamata da a kayan maye a tare da ita. Shin wata shaida ka ke bukata?
Shiru Almustapha yayi kan sa yana juyawa. Me yasa yake ji ba ita ba ce? Inaa..dole akwai wani abu. Ya ce
” Ya kamata ka gane barrister wannan alamarin yana cike da rudani. Akwai wasu behind this! Waye ya dauki wannan faifan videon? Kuma wanene yayi leaking video din? Wa ye behind watsa labarai na? Kana ga yadda kowane kamfanin jarida da tashar talabijin suke watsa labaran nan, a tunaninka yin kan su ne? Ko saka su aka yi?”
Barrister yayi shiru ya ce
” Alamari irin na kotu shi ne, duk lokacin da kake so ka dauke laifi akan wani to dole ka samu wani da za ka daurawa. Abun tambaya anan shi ne idan ba ita Rukky ba ce tayi kisan wanene yayi? Yanda za ka fara kafa hujjojinka akan wancan yadda alkali zai karba ya aminta da su”
Wani irin numfashi Almustapha ya saki kan sa ya gama daurewa. Ko ma dai menene ya zama dole yayi magana da Rukky. Ya ce
” Ina ga barrister ya zama dole nayi magana da yarinyar nan Rukky”
Wani irin kallo barrister ya watso ma sa cikin tuhuma ya ce
” Ka san me kake yiwa rayuwarka kuwa? Na ga kamar duk bayanan da nake maka basu gamsar da kai ba, ko baka gane don kai nake yi ba? Mu’amalarka da yarinyar nan Ruky dole ne ta tsaya. Dole ka ma ta matsaya.”
Wani irin huci Almustapha ke fitarwa daga bakinsa. Barrister ya tatttara ‘yan takardunsa zai fice. Ya juyo a hankali ya kalli Almustapha ya ce
” Ka da ka yarda da kowa, ka da kayi wata magana da
ya danganci shariar nan da kowa. Babu wani abun yarda da. Mutane ne suke farautarka ya kama ta ka zama very careful”
STORY CONTINUES BELOW
Gyada masa kai kawai yayi suka rabu.
Tunani ne fal zuciyarsa Amma ya rasa yanda zai yi. Wai wanene masoyinsa na gaskia? So yake ya samu lauya a asirce ya tsaya akan case din Rukky..To amma hakan ba kuskure ba ne? Hakan ba cakawa kai wuka ba ne?
Har ya daga waya zai kira sadiq sai kuma ya ajiye. Maganar barrister ya tuna2
” ka da ka yarda da kowa…”
Yanzu shikenen mafarkansa sun tafi? Yanzu shikenen siyasar sa ta kare? Mutuncinsa ya gama zubewa? Sirrikansa an watsa su a duniya. Wani irin ibtila’i ne?4
A lokacin ya tuna da wani shahararren lauyan babansa. Barrister Kamal Dauda. Duk halin da babansa ya shiga bai saka kamal dauda mantawa da shi ba. Watakila a wajensa zai iya samun amsoshi. Watakila ya samu ya tsaya ma ta a kotu a sirrance ba tare da an gane da sa hannunsa ba.
Washegari suka hadu da shi. Bai boye masa komai ba ya gaya ma sa. Ya ce zai bincika komai akan case din ya sha kuruminsa zasu bari sai kafa ta dauke da daddare za su je wajenta. Yana da mutane a police station din da aka tsare ta zai san yadda zai yi.
Washegari da dare misalin karfe 10 ne suka bayyana a police station na hotoro.
Lokacin da ta fito kallo daya Almustapha ya yi ma ta ya dauke kai saboda tsananin tashin hankali. Me ya sa suka sa kan su a irin wannan rayuwar?
Ko da ta gan shi kuka take ta ce
” Almustapha dama za ka tuna da ni? Na dauka kai ma ka yarda da zargin da ake min…na shiga uku na. Ban san ya aka yi na samu kaina a cikin wannan rayuwar ba. Ina ma..ina ma na mutu tun da dadewa na hutasshe da kaina fadawa cikin wannan hali. Wallahi ba ni na kashe ta ba, sharri ne ake son kullamin”
Kallonta kawai yake. Ya kasa cewa komai. Kallon komai na ta yake, yanayinta ya canja kamar ba yar gayen nan Rukky ba.
Anan Barrister Kamal ya nemi ta ba shi bayani daki daki game da abu da ya faru. Ta kuma ba shi. Ya dubi ta ya ce
” ke a ran ki wa ki ke zargi da kulla wannan kullalliyar?”
” Luba”!! Ta ba shi amsa8
” Dama na san wani abu dole zai biyo baya ganin yadda muka ci amanarta. Yanzu na gane ita ko wani da ke ma ta aiki ne suke turomin sakonnin nan. Musamman na in zo gidan Almustapha yana nema na.
Ya ce
” Da ki ka fito ba ki lura da canji ba a motarki na kamar an taba ta?”
Ta ce bata lura ba. Ya ce
“Da kika shiga gidan kin hadu da Rebecca”
Ta ce bata hadu da ita ba sai dai amma ta tambayi kuku ko tana nan.
Ya ce
” wannan hanyar da kika bi kin saba bin ta dama? Idan kin saba kin taba ganin check point na yansanda a wurin”
Ta ce
” Eh na saba bin ta amma ban taba ganin check point ba”
Ya sake tambaya
” Me ya sa kike zargin Luba?”
” saboda ita ce mu ke gaba da ita ta kuma ce zan ga abunda zai biyo baya.”
” Banda Luba wanene ki ke zargi?”
Ta ce
” Gaskiya a raina babu kowa”
Ya ce
” A report din da aka bani na post motem na gawar Rebecca ya nuna cewa lokacin da aka kasheta yayi daidai da lokacin da kike cikin gidan. Ba ki ji wani ihu ba? Ko sauti?”
STORY CONTINUES BELOW
Ta ce
” Ban ji ba gaskiya. Domin gidan fafadan gida ne mawuyaci ne aji hakan”
” Ban da Luba wanene ki ke zargi kuma?”
Ta ce babu
Ya ce
” A cikin binciken da na karba daga yansanda a gano cewar wukar da aka kashe rebecca da ita tana dauke da finger print na mutum biyu. Daya daga ciki wanda na ki ne!”
Wani irin abu ne ya dake ta ba da wasa ba. Ya dora da
” Malama Rukky shin kin san cewa yansanda sun kai bincikensu gidanki sun tarar irin wukar da aka kashe Rebecca da ita tana cikin set din wukake da kike da su a gidanki? Kamanin wukar da irin ta gidanki iri daya ne!”
Wani kuka ta fashe da ta ce
” wallahi ni ban san yanda aka yi ba. Ni ba ni na kashe ta ba. Amma…”
“Amma me?” Ya ce da ita
” Ina zargin ‘yar modu bakinsu daya da Luba”4
“Me yasa kika ce haka?” Ya tambaya
Ta ce
” Shi ya zo gidana ya kawo labarin Almustapha. Kuma da ya zo na yanka mana lemo da kankana. To ina ga anan ya ya dauki wukar ta hanyar amfani da hankici ko abun rufe hannu.
Sannan shi ya ziga ni ya dun ga dirka min kayan maye akan na je na watsa taron nan. Ina zargin shi ya dauki faifan video din nan.”
A hankali bartister kamal dauda ya cigaba da gyada kai ya xe
” hakan ma zai taimaka. To amma kar ki manta fadanku da rebecca da ikirarin za ki kashe ta shi ne ya bata komai. Domin kuwa kin ga kenen akwai motive na kisa”
Wani shiru ne ya ziyarci wurin na ‘yan daqiqu kowa na wassafa abubuwa da yawa a zuciyarsa. Ya ce
” Ina ga zan dawo gobe , za.mu kara tattaunawa kafin a shiga kotu”
Da wannan suka yi sallama. Almustapha mamaki ya shallake masa tunani. Wai Luba!
Ko da yake ya san Luba na aiki ne tare da makiyansa. Domin sirrikansa da ke fita dole sai wanda ya san shi ciki da bai.
Wayarsa ce tayi kara message ne ya shigo. Wani abokinsa ne ya turo ma sa wata jarida ce ta hausa me suna “Gaskiya da Gaskiya”. An rubuta
” Shin ko kun san Almustapha Tillaberi cikakken dan caca ne?”
Sai wasu hotunansa a la mirage , kazaman hotuna.
Yayi sauri ya rufe gaban sa ke dakan goma goma. Ya san duniyarsa ta ruguje rugujewar da ba za ta kara dawo wa daidai ba!
Bai gama tunani ba aka kira shi a waya. Daga ofis ne. Ya dauka. Daraktansa ne me kula da harkokin shige da fice na kamfanin I and A group of companies.
” Yallabai ka kalli labarai kuwa?”
Bai kai ga ba shi amsa ba ya cigaba
” Yallabai muna cikin tashin hankali. Baban kanfanin nan na Amurka KNEELS wanda da karfinsa muke tsaya a kafafunmu ya zare hannun jarinsa saboda wai bai yarda da authenticity din mu ba. Suna ganin wataran za mu iya zuba dukiyarsu a caca ta salwanta. A halin da ake ciki sun janye shares din su hade da bada shawarwari tsaurara a kafafen yada labarai na duniya akan duk kamfanin da zai hada kai da mu! Yallabai wannan shi ne kamfani na 20 kuma ma fi girma da suka janye tallafinsu daga I and A. Yallabai we are about to go bankrupt!!”
Shiru Almustapha yayi. Wani irin shiru.
Shin ko wannan ita ce ranar da ake gudu? Shin ko wannan ita ce duhun? Shin ko ita ce ranar nadama??6
STORY CONTINUES BELOW
****************************
Harabar kotun a cike take makil! Babu wanda bai halarci wannan sharia ba mai daukan hankali.
A gefe daya Luba ce zaune da yar modu tana karkade kafa. Daga gefe can hindatu ce a cikin matsanancin tashin hankali. Abubuwan da suka faru ba abubuwa ne masu dadi ba, ganin Rukky a cikin halin da take ciki ya sa jikinta yayi mugun sanyi. Tsoro take ita ma kar karshenta ya kare a haka. Sai sharar hawaye take.4
Bata da wata masaniya akan shirin Luba ko wata manakisa na ta. Ita dai kawai tana tausayawa Rukky.
Almutapha na wani gefe daban shi da mahaifiyarsa. Ta ji labarin komai a bakinsa sai a lokacin take Allah wadai da irin rayuwar da ta bar dan ta yana yi saboda son duniya. To amma yanzu wa gari ya waya?1
Lokacin da aka fito da Rukky a cikin sarka sai da wata kwalla ta tarar masa, yayi sauri ya dauke kai. Gabadaya komai na duniya ya sire masa a zuciya.
Rukky kallon kowa take daidai. Yanzu ga shi an hallara duk akan dalilinta. Ga shi an tara mutane ana zarginta da kisan kai. Shin ashe haka duniya take bata da tabbas? Ashe abubuwan cikin duniya yau
dararrun abubuwa ne? Ashe ma jin dadin duniya kalilan ne,?3
Ta yarda duk wanda ya bar Allah to ya bar komai. Yanzu ga inda rayuwa ta kai ta, ga shi ta baro ta. Lallai ba ta da makiyi a duniya irin zuciya!2
Lauyoyi suka gabatar da kan su. Lauyanta kamal dauda yayi ma ta tambayoyi shigen irin wanda yayi mata a police station ta kuma ba shi amsa daidai da yanda aka yi. Ya ce
” Ina fatan mai sharia zai duba cewar yanayin da abubuwan suka faru a tsare ya nuna akwai sa hannu a ciki. Daga lokacin da aka dauki faifan video na fadan rukky da rebecca ya nuna cewar akwai wani shiri da ake yi akan hakan. Ana so a lakaya mata wannan kazafin ne don wata manufa.
Ga waya waya da take nuna irin tasa tasan da aka aiko ma ta da sunan Almustapha. Har wanda aka ce ta zo gidansa da misalin wannan lokaci na kisan”
Ya mika wayar a matsayin shaida
Alkali ya ce
” Kana da shaidu da ka ke bukatar gabatarwa da kotu?”
Ya ce
” Ina da su My lord”
Ya ce
” To ka gabatar da su”
Almustapha ya fara kira. Ya kuma tambaye sa tsakaninsa da wacce ake kara ya fada ba wani boye boye. Abinda ya kawo cece ku ce a kotun kenen. Ya tambaye shi game da batun tura sakonni ya ce shi ba shi ba ne. Ya kara da cewa rabonsa da yayi wani contact da Rukky tun kafin aurensu da Rebecca.
Daga wannan aka kira maigadin gidan Almustapha. Ya tambaye shi abunda ya faru a ranar ya labarta shigar Rukky gidan da fitarta. Ya tamabaya
” shin ko ka ga alamu da ke nuna ta fita da wani abu daga gidan”
Ya ce
” Ni dai ban gani ba”
Ya sake tambaya
” Ka ga lokacin da take komawa mota ko ta saka wani abu “
Ya ce
” Gaskiya ni ban gani ba..ita kadai na ga ta shigo kuma ita kadai ta fita sai dai abinda ke boye , wannan kuma Allah shi ne masani”
Barrister ya ce
” to kana ganin kamar dai wani ya taba motar kafin ta fito ba tare da ta sani ba..”
“Objection my Lord” cewar lauyan Gwamnati. Bartister yana leading witness din. Yana saka maganganu a bakinsa”
“Objection Sustained. Ka kiyaye” cewar Alkali.
STORY CONTINUES BELOW
Daga nan aka kira kuku. Shi ma ya fadi abinda ya wakana. Barrister ya ce
” ka ga fitar ta lokacin da bata samu oganta ba?”
Ya ce
” kwarai na gani”
“Shin ka ga wani makami a tare da ita? “
Ya ce
” A’a”
Daga nan ya kare tambayoyi ya dubi Alkali ya ce
” Ina so mai sharia ya gane wacce aka kara Rukky ta taka sawun barawo ne kawai. Amma ganin yanayinta da karfin ta na diya mace ba zai iya yiwuwa har ta kashe mutum ta dauki gawarsa ta saka a boot din mota ba. Ya kamata kotu mai adalci ta zurfafa bincike ta gano gaskiyar lamarin. Nagode”
Ya koma ya zauna. Barrista yunus ya fito ya fara yiwa Rukky tambayoyi kamar haka
” Malama Rukky mecece sanaarki? Kuma wata alaqa ke tsakaninki da Almustapha?”
Ta yi jim kadan can ta ce
” Karuwa ce ni! Kuma muna dadiro da shi”
Wata irin hayaniya ta cika kotu. Baka jin komai sai tsine tsine. Ya ce
” ba ki da wace sanaa da ta wuce wannan”?
Ta ce ba ta da ita
Ya ce
” Irinku ne ku ke raba mutum da iyalansa? Dalilin kenen da ki ka yanke hukuncin kashe Rebecca”
” objection my lord. Ba muna sharia a yau ba ne akan tuhumar da ake wa wacce ake zargi da laifin karuwanci. Akan wani abu ne daban.Barrister yana kokarin laqabawa wacce ake tuhuma kisan kai ba bayan ba a tabbatar ba zargi kawai ake” cewa Barrister Kamal.
“Objection sustained. Korafi ya karbu. Ya kamata barrister Yunus ya kiyaye”
Ya gyada kai
Ya ce
” Faifan video din da ke yawo na ke da Rebecca kuna fada. Ya nuna inda kika yi ikirarin kashe ta. Shin wannan wani shiri ne kika dauka akanta?”
“Objection my lord”! Ya kamata Barrister ya daidaita tambayarsa” cewar Barrister kamal dauda
Alkali ya masa gargadi.
Ya cigaba da yi mata tsauraran tambayoyi. Daga nan aka kira mai gadi. Ya ce
” Shin ko ka lura da yanayin ita Rukky lokacin da ta zo ficewa daga gidan?”
Ya ce
” eh to, gaskiya na dan lura kamar akwai bacin rai a fuskarta don ina kokarin yi mata sallama ta figi mota ta fice”
Ya ce
” To kana ganin akwai wani yanayi da ke nuna sauri a tare da ita?”
Kafin ya amsa Barrister kamal ya ce
” objection my lord, yana leading witness”
” objection overrulled. Korafi bai karbu ba. Barrister yunus yana kan sharafinsa ne”
Ya kira kuku ya cigaba da yi masa tambayoyi. Ya ce
” Da ta leko wajenka me ta tambayeka?”
Ya gaya masa. Ya kara da cewar
” sai ta ce min ina madam..na ce tana side din ta”
Barrister Yunus ya dubi Alkali ya ce
” Hakan yana nuna cewar tana da wani shiri akanta tun da ga shi ta tambayeta don ta san inda ta ke”
STORY CONTINUES BELOW
Daga baya ya kira shaidu 3 abokanan Almustapha ne da suka halarci cin abincin nan. Suka bada shaidar fadan da kuma gaskiyar magana cewar Rukky tayi ikirarin zata kashe Rebecca.
Ya dubi Alkali ya ce
” Daga jin wadannan bayanai za a gane cewar Rukky da shirinta ta zo gidan Almustapha. Domin kuwa akwai jin haushin Rebecca a zuciyarta na ta raba ta da masoyinta. Duba da yanayi da cewar bincike ya nuna ko lokacin da aka kamata da gawar tana dauke ne da kayan maye da ke nuna ba cikin hayyacinta yake ba. Hakan ya na nuna za ta iya aikata kisan.”
“Objection my lord. Ya kamata barrister ya gane har yanzu zargi ake wa wacce ake tuhuma. Maganganunsa hasashe ne kawai.” Cewar barrister Kamal.
Korafi ya karbu. Barrister Yunus kotu na yi maka gargadi.
Da haka aka tashi daga kotu bayan an daga kara zuwa 10 ga watan gobe. Alkali ya yanke hukunci da cewar a mayar da wacce ake tuhuma gidan yari na kofar mata a dauketa daga police station na hotoro.
*****************************
An yi zaman kotu kamar sau uku kafin ayi wannan zaman. A tsawon lokacin nan ya zamana ko masallaci a bi jam’i Almustapha bai isa ya shiga ba ba tare da an zunde shi ba.1
Yawan yawan mutane hankalinsu ya fi raja’a akan Almustapha da Rukky su ke da alhakin kashe Rebecca. Da ba su ga yanda za ayi mutum ya bada shaida don taimakawa wacce ta kashe matarsa ba.
Sun fi gane cewar da sa hannunsa dumu dumu. Sai dai duniya yanzu da mai hannu da shuni ake yi, ya cika jamian tsaro da kuma alkali da kudi domin a wanke sa. Don haka ba su da wani abun da suke masa sai tofin Allah tsine.
A yau ma kowa ya hallara a kotu. A wannan lokaci Barrister kamal ya sare domin babu wasu kwararen hujjoji a kasa. Wacce su a rans u suke zargi luba ce, kuma babu wata dama da za su nuna hakan. Domin kuwa bata bar wata shaida ba da za a iya amfani da ita a ramfota.
Yar modu da yake tunanin da hannunsa idan ya dora shi akan stand kwabarsa zai sa tayi ruwa. Da farko ba zai fadi gaskiya ba. Illa ma ya bi ‘yan shaidar fadan da ya wakana. Kan sa ya kulle qam haka na Almustapha. Don shi numfashi ma da kyar yake fitarwa. Ya rame ya lalace sabida tsananin tashin hankali.
Wanan karin da fari yansanda aka kira, aka musu tambayoyi suka bada bayanin abunda ya faru. Barriater yunus ya ce
” Ka na nufin ga bude jakarta ta miko kudi a matsayin cin hanci?”
Ya ce hakane
Ya dubi alkali ya ce
” Shin wannan bai ishemu shaida ba, cewar akwai abunda take boyewa?”
Objection my lord. Ba ana zarginta ba ne akan bada rashawa da cin hanci” cewar barrister kamal
“Objection overulled!Korafi bai karbu ba. Ka kiyaye barrister kamal” cewar Alkali.
Yansanda suka bada shaidar cewa akwai shaidar yan yatsun hannun Ruky akan wukar da aka yi kisan.
Sa’annan Rukky ba ta da Alibi wato wajen da take a lokacin da kisan ya auku. Wajen da take bai wuce cikin gidan da kisan ya auku ba!1
Barrister Kamal shi ma ya tashi ya bada hujjojinsa da cewar. Wukar da aka yi kisan da ita akwai shatin yan yatsu na wani da ba a sani ba. Dole kenen akwai wata manakisa.
Da wannan kowa ya samu waje ya zauna alkali zai yanke hukunci. Ya yanke hukunci kamar haka
” Duba da irin hujjojin da aka gabatar a kotu, kotu ta kama wacce ake tuhuma mai suna Rukky da laifin kisan Rebecca! Kotu ta yanke ma ta hukuncin daurin rai da rai a gidan yari! Wanda hakan yayi daidai na sashe na 3** na pinal code. Wacce ake zargi tana da damar daukaka kara zuwa nan da 27 na watan gobe. Kooot!”
STORY CONTINUES BELOW
Wani kara Rukky ta saka mai gigita hankalin mai saurare. Numfashin almustpha yake neman daukewa saboda tsananin rudani har sai da ya dafa bangon kotun. Cewa yake
” innalillahi wa inna ilairrajiun.. Allah idan saba maka da muka yi wannan ne hukuncinmu ya Allah mun tuba. Ya Allah ka yafe mana. Ko a yanzu mun gane kai madaukaki ne mai buwaye ne, ba daidai ka ke da mutum danadam ba. Ka fi karfin kowa kai mai iko ne akan kowa! Astagfirulla ya Allah! Astagfirulla!11
Ya dago kai yana kallon Rukky ana janta za a tafi da ita wani irin kuka ta ke. Ta kwalla kara
” Almustapha!! Ka taimake ni!”
Kawai sai ya ji hawaye ya subuce masa. A hankali ya ce
” Allah ne zai cece mu! Zan kuma taimake ki da karfin kwanjina! Zan taimake ki da kwandalar da zata kare a aljihu na”!
Ficewa yayi daga cikin kotun zuwa harabar waje. Yana cewa
” Zan daukaka kara daga nan har sai na ga abunda ya turewa buzu nadi! Wasu abubuwan na duniya ba sa zuwa da sanyi. Wasu abubuwan sai an dage kafin a cimma buri!”2
Cin karo yayi da Luba da ‘yar Modu a tsaye suna kwasar dariya. Ta dubi shi ta ce
” Shin a tunaninka ka dauka shata layin gaba da Luba abun wasa ne? To bari na gaya maka, tamkar ka daga hannu ka zagi uwarka ne! Za ka daidai?
Na so ka fiye da yanda na taba son duk wani namiji na duniya amma ka juyo ka watsamin kasa a ido. To abun son naka na salwantar! Kai kuma na bata maka suna, dukiya ba dai ka ji ana lissafinka a masu mallakinta ba.Sai naga yadda za kayi.!Wanna shi ne daidai hukuncin da ya dace da maciya amana!6
A tunaninka zan kale ku? To mu muka shirya komai! Wanda na sa ya kai Rebecca barzahu ko ka neme shi ba zaka same shi ba! Shin ko ka san ya fi kwana 3 da kai a cikin gidanka yana kwana da matarka Rebecca baka sani ba? Hahahahha3
Kwarton matarka shi na saya na kuma saka ya sheka ta barzahu! Shin ka dauka kana da masoya Almustapha? Su waye su?”
Daga bayanta sadiq ya bullo yana kallon Almustapha yana murmushi. Ita ma dariya take ta ce
” Awww…kan ka ya daure ko? To ina muka san sirrikanka idan ba ta hanyar makusantanka ba? Bar zargin yan adawa Almustapha, mutanen jamiyyarka ashe makiyanka ne ai da su na hade baki aka watsaka a duniya akai maka daidai! Da su aka taimaka wajen kai rahoton cacarka dan a tarwatsa ka a hannun investors din ka! Kai da Rukky Almustapha sai dai ku hadu a jahannama! Don ita ce makomarku!!”7
Rintse ido yayi ya bude wani irin tiriri ke fitowa daga bakinsa. Kallonsu yake, musaman sadik ya zai ci amanarsa irin haka? Me duniya ta zama ne wai?1
Amma yayi wa kan sa alkawari daga yanzu ya zama jajirtacce. Zai iya fada da kowa kuma ya ci shi da yaki. Ya kalle ta a tsaurare ya ce
” Ki jiraye ni! Ki jira ranar da zan waiwayeki ko da kuwa shekara dari biyu ne masu zuwa!. In dai ina raye sai kin gane ba a taka ni a wuce. Ki cigaba da harkokinki amman a kasan ran ki ki raya cewa wani kasurgumin makiyinki yana take miki baya.1
Lokacin da zan bayyana gabanki, Allah ya sa kin gama cika burirrikanki domin kamar mutuwar bazata haka zan datse miki cikar buri!! Zamu hadu a ranar da ba zamu sake haduwa ba!!!!!
Ya bar su a gurin ya hau motarsa ya figa a guje zuciyarsa na tafarfasa. Ya rasa ina za shi. Wata zuciyar ta ce masa ya kamata ya gano wacece yarinyar nan Rukky. Ko dan ya waiwayi iyayenta su san halin da diyarsu ke ciki. Kawai sai ya dauke kan motarsa ya wuce gidanta.1
Budewa kawai yayi ya shiga yana da fan mukulli. Gidan yana nan yadda ta bar shi. Dakin kwananta ha shiga ya fara hargitsa komai.
Suk iya bincikensa bai ga komai ba. Ya bude drawer ya fara wurgo kayanta . Ya duba koina da koina. Har zai rufe ya hango wata karamar akwati ya janyo ta.
Tarkace ne a ciki, wasu abubuwan kamar sun dade. A fara binciko su bai gane komai ba.
Har zai rufe acan kasa ya ga wata envelop sai ya zazzage ta. ID card ne a ciki sai wasu takardu kamar na makaranta haka. Sai hoton wata mata da shekarunta ya ja haka.
Da ya kura mata ido sai ya ga kamar ya san ta, kamar kuma ya san hoton sai ya mayar kawai. ID card din ne da takardun makaranta suka dan dauki hankalinsa. Suna ne iri daya a jiki baro baro
ROKAIYATOU AHMADOU TILLABERI
E.S.A L’ ECOLE SEKANDARE DE NIAMEY1
Rubutun sunan iri daya ne da na jikin sakamakon jarabawar. Sai ya rufe zai mayar. Sai kuma yayi sauri ya bude yana kurawa id card din ido yana kara karantawa cikin rudani.
ROKAIYATOU AHMADOU TILLABERI
Gabansa ya ji ya bada dam!!!
Cikin azama yayi sauri ya zaro hoton nan sai a lokacin ya gane wacece. Hoton mahaifiyar Rokaiyatou ne sak irin wanda ya sata a dakin mummyn sa lokacin cigiyar nan!
Saboda tsabar tashin hankali wani amai ne ya taso masa, kawai sai ya ru ga bandaki ya dunga kwara amai ba da wasa ba.1
Da kyar ya fito ya fadi akan kafet na dakin yana birgima!! Birgima yake yana malelekuwa cewa ya ke
” wayyo Allah na..wayyo Allah. Allah na tuba ka yafe ni! Allah na tuba bazan kara ba! Da kanwata nake zina!! Rokaiyatou! Matar danuwana! Innalillahi! Innalillahi”10
Kuka yake, kuka kashirban na ban mamaki. A rayuwarsa bai taba kuka irin haka ba. Jikinsa karkarwa yake zazxabi ya rufe shi. Da kyar ya dauki I d card din da takardun ya tafi mota ya ja ta a guje.
Wani abokinsa mai aiki a prison din kofar mata ya kira. Ya ce ya masa hanya zai ga wata yanzu yanzu aka kawo ta. Ya taimake shi ko nawa ne zai iya biyansa. Ya ce ya karaso.
Haka ya karasa, ba a jima ba aka sada shi da inda zai gan ta.
Ta fito sanye da shudin yinifom idonta luhu luhu bata ko gani sosai. Jiki na karkarwa ya watsa takardun nan akan tebur ya ce
” Ki yi wa ubangijin da ya halicce ki ki gaya min ko ke wacece. Ke ce mamallakiyar wannan takardun? Shin kece mai wannnan sunan?”
A hankali ta gyada masa kai. Bai yi wata wata ba bai san lokacin da ya sharara mata mari ba saboda tsananin tashin hakali.3
Ta rike kuncinta cikin mamaki take kallonsa. Kuka ta ga yana yi kashirban. Ya ce
“Me yasa tun da wuri ba ki gaya min wacece ke ba? Me yasa kika boye? Kin ga abunda hakan ya janyo ko?2
Kin san wanene ni? Ni ne Almustapha! Almustapha danuwanki jininki! Ni ne danuwan momodou masoyinki! Ni na dan babban makiyinki! Ni ne masoyin da ba ki da tamkarsa a yau duk duniya! Da ni da ke muka yi zaman haram! Zaman haram din da ya kai ki gidan yari!Ni ne Almustapha”
Durkushewa tayi a gurin. Kuka take amma ba ya fitowa. Yanzu ta gane me ke faruwa. Yanzu ta gane dalilin da take jin Almustapha a ran ta. Ashe jininta ne? Shi ya sa kaunar tayi yawa?7
Ina ma ina ma..ina ma. Ina ma ana dawo da hannun agogo baya. Yau ta tsinewa karuwanci! Yau tayi Allah wadai da rayuwar bariki. Allah ta tuba, a yau tan
a cikin da na sani marar amfani.
Kawai bai san lokacin da ya daga ta ya rungume ba. Dukkansu kuka suke
” Tsakanina da ke ashe ‘yanuwantaka ne? Tsakanina da ke ashe kauna ce? Kauna irin ta jini! Ya za ki yi min haka Rokaiyatou? Yaya za ki yi min haka? Ki zo a sa’ilin da lokaci ya kure?2
Ashe zina da na sani ce? Ashe haka ciwon yake idan kayi da diyar wani? Ina ma ban yi ba! Ina ma na tuba kafin na hadu da ke!
Ina ma ..ina ma ina ma.akwai rabo, da an rubuta ke tawa ce! Da mun gyara kura kuren mu. Ina ma bamu tarwatsa rayuwarmu ba! Ina ma bamu sabi Allah ba. Zai karbi tubanmu kuwa? Kamar lokaci ya kure.”13
A hankali ya fara ja da baya. Ya san dole ya tafi.
Shin ko ka san irin son da ke tsakanin uwa da d’a? Shin da gaske za ka iya komai saboda wannan abu da ake kira d’a?+
Bayan shekara goma2
Ajiya..ina bekin cikin senar miki, kina doke da cutan kanjamau! But ya kamata ki gane cuta wannan ba mutuwa ba ne, mutane dayawa dayawa suna doke da ita but suna shan megani, ba a seni ba. so, if kana shan magani ake ake..babu damuwa..babu mesala..
Zaune take akan kujera ta zuba ido tana kallon bayeraben likitan yana idar mata da sako a cikin gurbatacciyar hausar sa. Wani irin abu ne ta ji yana mamaye mata zuciya na tsananin fargaba da bakin ciki.
Mace ce da ta haura shekara arbain. Baka ce mai jiki, wanda yake nuna alamun jindadi a tare da ita. Tana sanye da wani farin leshi qal mai manyan huda huda da aka yiwa ado da ja. ‘Yanyatsunta akwai zabban zinare guda biyu, fuskarta babu kwalliya sai dai kayan jikinta sun bayyana tsadarsu ta nuna cewa ita mai arziki ce.1
Dankwali ta daura akanta amma bata yafa mayafi ba, rabi rabin jikinta a waje ya ke. Komai kuma na jikinta abun shaawa ne, abun kallo ne. Tayi kama da wacce zata halarci wannan babban taro, to amma ga ta a gaban likita yana labarta mata mummunan labari.
Hindu ta hadiye yawu maqwat, zufa na tsatssafo ma ta ce9
“Ban gane bayaninka ba likita. Ni din ce naje dauke da kanjamau? Anya kuwa ka duba da kyau? Ni fa idan banda dan zazzabi zazzabi babu abunda nake ji. Sakamakona ne kuwa?”3
Ya gane a rude take. Ya kara kallon takardar ya karanta sunan jiki ya kuma tabbatar mata da cewar ita ce. Ya ce
” Ajiya, wannen fa ba abu tashin henkali ba ne. Me cutan nan ba shi da bebenci da kowa. Yenzu megani yayi yawa wanda za kana sha..cikenen! Dats ol. Kuma megani is free! Kawai za kana zuwa asibiti ake ake kana karba. Za muyi guiding na ka.”2
Ta cigaba da zuba masa ido kirjinta na lugude. Rayuwarta ce ta bayyana a idanuwanta. Kokari take ta danne firgicinta da bakin cikin da take ji amma ta kasa. Kawai sai ta fashe da kuka, wani irin kuka mai cin rai.17
Tun likitan yana ba ta hakuri har ya gaji ya daina. Ta fito daga ofishinsa ta wuce wata bakar hadaddiyar motarta kirar camry. Motar da idan ta kalle ta ko wanke ta ake sai taji wani nishadi ya lullube ta.
Sai take jin kan ta cewar ta kai inda ta kai, ta isa domin kuwa motar lokacin da aka siye ta ba ta fi wata shida da fitowa ba. Alhaji Awaisu ya siyo mata, ya dalle ta da ita a matsayin kyautar ban girma a lokacin da akai wani shagali na cikarta shekara 40 cif a duniya.4
Amma me sai taji bakin motar a rine a idanunta, sai taji bata son ko ganinta. Ba ta ma son wani ya mata maganar Alhaji Awaisu ballantana dalleliyar motar da ta dangance shi.2
Babu makawa Alhaji shi ya sanya ma ta kanjamau! Dama yana da ita bai gaya mata ba? Ita a iya saninta a ‘yan shekarun nan shi kadai take kulawa domin da shi suka kulla dadiro.2
Sama da shekara goma kenen Alhaji Awaisu na ma ta alkawarin aure, yau gobe , jibi ,gata amma shiru. Ta raba shi da matarsa da ‘ya’yansa duk don wai ta samu da shiga ta bararraje da nata ‘ya’yen amma batun aure shiru maqatau bulaguran lahira.6
Sai alkawurra na iska. Yau ya kai ta dubai, gobe tana ingila ta zame masa jaka duk inda za shi da ita zai je. Ya bude mata bakin aljihu wanda bata taba sanin ana budewa mace ba take wawasa iya wawasa.3
Shagunanta biyu na sayarda lesissika da kayan kitchen akan titin zoo road, business take yi ba na wasa ba. Alhaji Awaisu ne kuma ya tsaya tsayin daka.Duk da a boye dai ta kan dan kula manemanta amma jikinta ya fi ba ta cewar Alhaji Awaisun ne ya shafa mata wannan qajagar.3
Ta bude motar a hankali ta fada ciki, ta dafa kanta akan sitiyari kuka take rusawa babu ji ba gani. Ba ta da mai lallashinta. Sai a ranar a lokacin ta ji kewar wani na ta, shin wa zata labartawa wannan bakin labarin?
STORY CONTINUES BELOW
Uwarta mahaifiya har yau tana nan da rai, amma rabonda ta taka ta je ta manta. Haka kannenta ba ta zuwa inda suke suma ba sa zuwa. Ba wai dan komai ba sai dan kalar tata rayuwar da suke ganin ba ta mu su ba.
Babarta mahaifiya tayi fadan tayi fadan amma ko gezau, hindu ta yi nisa. Har ta kai bata son zuwa gidan don ta san karshen zancen fada ne. Da wayo da wayo ta fara janyewa, tunda dai yaranta ai ba sa gidan. Daga baya sai suka ji dif harkar gabanta kawai take.2
To yanzu da haka ta same ta wa zata je wa ya jajanta ma ta? Wannan zance ne ma na abun fada? To amma idan ta durkushe wa zai yi jiyyarta? Ta tuno ‘yan yaranta da suka girma yanzu, ba ta so su sani ba ta son duk wani abu da zai jagula ma su lissafi.
Rayuwarta ta fara dawo ma ta a idonta kamar majigi. Wata irin nadama tana hudo ma ta jiki. Da gaske tayi kuskure? Da gaske ne? Shin kuskurenta ne ya sa ta fada a wannan halakar ko kaddararta ce?4
Tsawon shekara sama da goma sha biyar kenen tana wannan rayuwa ta zaman kai, amma bata taba samun abunda ya dake ta irin na yau ba. Yanzu ya za tayi?
Da kan ta ta lallashi kan ta tayi shiru ba don ta so ba, ta kunna motar ta dau kan titi. Wata irin nadama ce take dirar ma ta, sai take ganin bai fi nan da sati 1 zata rasu ba to wai me za ta ce wa Allah?
Ta fada zurfin tunani tana tuno abubuwan da ta aikata a wannan doguwar tafiya ta shekara 15 sai ta ga gabadaya babu abun tsinta a ciki. To ita yanzu idan ta mutu ta cewa Allah me? Har me ta tanada da zata nuna?1
Har ta hau kan titi kuka take. Da niyyarta daga nan zata wuce shagunanta ta duba halin da ake ciki to amma ba zata iya ba.
Luba ce ta fado ma ta a rai. Tayi tunanin bari ta je wajenta ta labarta mata halin da take ciki. Suka dade ba su hadu ba saboda cewar Lubar yanzu ta kama kasa.
A shekaru goman nan abubuwa dayawa sun faru, a ciki har da auren Luba da mashahurin attajirin nan kuma tsohon sanata Alhaji Hamza Dala. Wani aure da ya zo a lokacin da Luba ke bukatarsa, auren da ya zame ma ta tsani na taka haye.
A halin da ake ciki yanzu takara take yi ta dan majalisar tarayya, matakin da Alhaji Hamza Mai Dala ya dafe ma ta. Burirrikanta suna neman ida cika, babu wani abu da take yiwa kallon nasara fiye da wannan kujera.3
Luba na son mulki tana kaunar ace yau ga ta a matsayin da ta isa ta taka uban kowa. Yau ga ta a asusun gwamnati tana yaftar abunda yayi daidai da raayinta, yau ga ta a duniya tana juyata a tafin hannu.3
Kiranta tayi ta gaya ma ta zuwanta, ba tayi wata wata ba tayi hanyar gidan. Kerarran gida ne , tamfatsetse na zamani. Tun daga gate aka bata izinin shigowa don dalilin cewa matar gida ta sanar.
A falo ta tarar da ita tana waya sanye da wata doguwar riga irinta larabawa. Akwai jaka akan karamin teburin da ke gabanta da alama bata dade da dawowa ba. Kafin ka ce me an cika gaban Hindu da kayan makulashe. Amma Hindu ba ta iya taba ko daya ba. Ta dube ta ta ce
” Hindu lafiya kuwa? Ni ko a waya sai naji muryarki wata iri..kamar ma kin sha kuka. Kamar dai kina cikin damuwa, da fatan dai ba ta kudi ba ce?”2
Wani abu ya tokarewa Hindu a wuya kawai sai ta fashe da kuka. Ina ma damuwar ta kudi ce! Yau ga damuwar da bata bukatar kudi,
wayyo Allahnta!Ina ma kudi zai iya gyara mata rayuwarta.2
Da can tana hangen kudi kare magana, yanzu kuma sai ta ga gashi tana cikin kudin amma matsala bata kare ma ta ba. Ashe dama haka duniya take. Ta ce
” Asibiti na je, aka ce wai ina dauke da cutar kanjamau”
Wani shiru ne ya gifta. Kawai sai ta ji Luba ta fashe da dariya. Wata irin mahaukaciyar dariya har da faduwa kasa.
Hindu ta zuba mata ido tana mata kallon mahaukaciya don tunanin da take ko shaye shaye ya taba ma ta kai. To amma sai ta ga ta dube ta ce
STORY CONTINUES BELOW
” Yanzu ke Hindu don cutar kanjamau shi ne kika zauna kina rusa kuka kamar an ce kudin hannunki sun kare? To mene a kanjamau idan dai ba an san cewa kana dauke da ita ba. Kin ganni nan na fi shekara uku dauke da cutar kanjamau, to amma me kika ga ya canja a rayuwata”15
Cikin tsananin mamaki Hindu ke kallonta, jikinta har karkarwa yake ta nuna ta da danyatsa ta ce
” Kina dauke da cutar kanjamau fa kika ce! Kuma shi ne har kika yi aure?”
Dariya Luba ta cigaba da yi tana yiwa Hindu kallin sakarci ta ce
” To Hindu sai kar nayi aure bayan ina bukatar amfanin da auren zai min? To a goshi na aka rubuta cutar? Ya kamata fa ki gane Hindu, ke ce za ki tafiyar da rayuwarki fa yanda kika so. Ai cuta ba mutuwa ba ce, a wannan zamani da magani ya yawaita ai kawai cigaba za kiyi da harkarki.”4
Hindu ta ce a tsorace
” kuma ba kya tsoron wataran ya gane kina da cutar. Shin Luba kina da labarin ko mijinki waye kuwa? Wanenne bai san shi ba akan harkar aiwatar da ta’addanci ga duk wanda ya sake ya shiga huruminsa”2
Luba tayi galala da baki ta ce
” To sai dai in ke za ki gaya ma sa!.shi Allahn musuru ne da zai sani? Ba a shafa kanjamau ni aka shafa min? Shi mata nawa yake bi da zasu iya shafa ma sa? Ya za a yi ya san ni ce?”
Ta rage murya a hankali ta ce
” Kuma ba ma shi kadai na shafawa ba, muna nema da kaninsa Alhaji Bilya Dala”8
Wata irin zabura Hindu tayi. Ta kankance idanuwanta ta ce
” Shin ko kin san Luba kina wasa da wuta? Shin kin ko san yanzu siyasa kike ciki dumu dumu ba ta kuma bukatar abun fada?”2
Luba ta ce
” Hindu ke kadai ce aminiyata ta tale tale, muna tare sama da shekaru 15. Ke kuma kadai na gayawa, idan magana ta fita ke ce. Ai ni ban taba kaunar Alhaji Hamza ba, dama can bilya ne manemi na..shi Alhaji Hamza ai tsani ne. Sai da shi zan samu cikar burina. Dalilin kenen da muka yi da Bilya din na auri yayan na sa, kin ga baya zabe kawai sai mu hadu mu salwantar da dan banza mu ci duniyarmu da bakin allura.”14
Jikin hindu har karkarwa yake, duk iya barikinta Luba ta shafa mata lafiya.1
Ta fara yi mata hirar fita wani kampen na siyasa da za suyi da irin yadda take so ta cimma burirrikanta sai Hindu ta mike. Ji take komai na duniya ya gundureta.
Sallama suka yi Hindu ta wuce mota da cewar bayan kwana biyu zata dawo su tattauna.
Daga nan gida ta wuce. A zuciyarta tana tunanin zata hadu da Alhaji Awaisu. Da tayi niyyar ta yi masa cin mutunci na fitar hankali, amma yanzu ta canja tunani.
Lallaba shi za tayi ya aureta ba zata nuna masa maganar cutar nan ba ko a ido. Ta san dai shi ya sa ma ta, za ta nuna kamar bata gane ba ta samu dai ayi auren ko ta tsira da wani abun.
Tana shiga farfajiyar gidan tayi hamdala ganin dalleliyar motarsa a fake a gurin. Wato ya zo kenen, faduwa ta zo daidai da zama. Ta fito jikinta ba laka ta shige bangarenta na gidan.
A falo ta tsaya dube dube bata gan shi, ta san watakila bandaki ya shiga. Sai ta zauna zaman jiransa. Amma me? Sai take jin wani irin kara haka kamar ihu. Me ke faruwa ne?
Abunda ya sa ta tashi zumbur kenen ta shiga daya bangaren zata tuntubi iya mai kula ma ta da gida ko lafiya.
Sai a lokacin ta ji ihun sosai daga bangaren. Da ta tsaya tsai sai ta gane kamar ihun budurwar diyarta asiya mai kimanin shekara 19 zuwa 20.
Sai a lokacin ta tuna ta ga motar ta da ta siya mata kwana 7 da suka wuce ta ke zuwa makaranta, Kano poly. Guda biyu ta siyo amma babu yanda bata yi da Abba ya karba ba ya ki, ta rasa kalar taurin kan da ke damun yaron.
STORY CONTINUES BELOW
Kawai banka dakin ta yi a gigice, a daidai lokacin ta ji ihun ya dauke. Numfashinta ne ya tsaya cak saboda abunda idanunta ya gane ma ta.
Alhaji Awaisu ne ya daure diyarta gudan jininta Asiya yayi ma ta fyade!20
Da alamu ma kamar a buge yake.
Shigarta yarinyar ta sume, ga jini nan male male a tile din dakin.
Tun da take a rayuwar duniyarta bata taba ganin mugun gani irin na wannan ranar ba!
Wani irin ihu ta kwalla
” Ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh”!
******************************
Wani saurayi ne fari dogo sanye da fararen kaya tazarce zaune a gaban ajin na makarantar islamiyya ta ” Riyadul Quran”1
Ba shi da wasu tarin shekaru amma sai zurfin ilmi. Malami ne a makarantar kuma shi ke daukan ‘yan babban aji saboda mahaddacin Alqurani ne. Ya sauke manya manyan littafan addini.
Dalibi ne a makaranta Bayero da ke kano, yana karatun injiniya. Da yamma yana koyarwa ne a wannan islamiyya ta “riyadul Quran”. Ranar asabar da lahadi da safe yana koyarda yan tahfeez.
Alashinsa duk wata bai taka kara ya karya ba amma ya gwammace wa hakan. Mutum ne mai kokarin neman na kai domin a lokuta da dama yakan je wani garejin mota yana taya su aiki nan ma yana samun kudin kashewa.
Abdulhakeem wanda aka fi sani da Abba mutum ne mai zuciya da sanin ya kamata. Zama daya za kayi da shi ya shiga ranka farat daya saboda hankalinsa. Yawa yawan yanmatan islamiyyar na yawan rubuto masa wasika na wai suna son sa saboda yanayin kyaunsa da hali irin na sa amma sai ya share. Shi ba wannan ne a gabansa ba.1
A yanzu ma sun kammala ajin, aji ne na mata da maza. A lokacin ne ya dago kai yana murmushi, ma’abocin murmushi ne Abba ya kalli ‘ yan ajin ya ce
” shin ko akwai wani mai tambaya kafin mu rufe da addua?”
Anan wata zaqaqura Hafsa ta mike, kallo daya ya ma ta ya dauke kai. Ta aiko ma sa wasika ya fi shurin masaki akan irin kaunar da take ma sa, ya share. Sai daga baya ya gane kamar wata gaba take yi da shi, wannan ma bai dame shi ba. Ta ce
” Malam ina da tambaya”
Ya ce
” bismilla malama hafsa”
Ta yi yatsina ta ce
” Allah gafarta Malam menene matsayin dan karuwa a musulunci?”5
Wani irin shiru ne ya ziyarci ajin. Wani abu ya tattaro daga zuciyar Abba ya zo ma sa maqoshi. Yayi sauri ya danne bacin ran sa, ya mamaye fuskarsa da murmushi ya ce
” Malama hafsa shin akwai wani banbanci tsakanin dan karuwa da ragowar ‘ya’yan duniya?”
Ya nisa ya ce yana mai duban ajin
” Abunda ya kamata ku gane shi ne shi Allah yana duba ne i zuwa aiyukanmu ba aiyukan iyayenmu ko ‘ya’yayenmu ba.
Da a ce sakamakon aiyukanmu na zuwa ne dangane da na iyayenmu ashe da Allah bai bawa Annabi ibrahim annabta ba! Domin kuwa ai mahaifinsa kasurgumin mai bautar gumaka ne. Da Allah bai alkarwantawa Asiya matar firauna aljanna ba domin kuwa mijinta kasurgumin kafiri ne! Shin ko kin san dan annabi Nuhu kan’ana bai yarda da shi ba? Shin kin san cewa da annabi Nuhu ya gayyace shi shiga jirgin ruwa bai shiga ba..domin bai bada gaskiya da shi ba?
Shin Allah ya hukunta wadannan bayin Allah don dalilin makusantansu?
Shin kin san cewa Allah ” Azza wa jalla ne? Madaukaki ne shi? Shi kin san Al Hakeem ne shi mai hikimar fidda baki daga fari, ya fidda fari daga baki?
STORY CONTINUES BELOW
To ko zina aka yi aka haifi mutum hakan ba yana nuna cewa shi batacce ba ne a musulunci, ba zai samu da Rahama
r Allah ba. Laifin iyayensa daban na sa daban.
Allah yana cewa
Duk wanda ya zabi ya bi hanya madaidaiciya, to yayi ne domin kan sa. Haka duk wanda ya zabi ya baude hanya , shi ma yayi ne domin kan sa. Babu wani wanda zai dauki nauyin zunubin wani. Suratul Israa (17:15)4
” Allahu Akbar” yan aji suka yi kabbara.
Ya sunkuyar da kan sa a hankali ya dago ya zuba wa hafsa ido ya ce
” Malama hafsa da fatan na amsa miki tambayarki?”
Ta gyada kai a sanyaye yan ajin suna watso mata harara.
Adduar rufewa yayi aka tashi. Allah Allah yake ya bar makarantar saboda tsananin bacin ran da yake ciki.2
Ya rasa yanda zai yi da rayuwarsa, yayi kuka ya gayawa Allah amma har yanzu bai samu sauki ba.
Kowa ya san babarsa karuwa ce wani abu da yake kwana yake tashi da shi a rai. Wani abu da ya zame masa abun tsayawa a rai tun yana karami.
Ya taso da wani irin kyankyami na halayyar mahaifiyarsa alamarin da ya sanya ko kusa da ita bai cika son zuwa ba. Yana rayuwar shi ne shi daya kuma yayi alkawarin sai ya inganta ta.
Zai zama jarumi jajirtacce mai tsantseni na addini. Talauci ba hauka ba ne da zai je ya sayar da imaninsa domin sa. Ko yaushe mahaifiyarsa zata gane? Sai yaushe?4
Haka ya taka a hankali ya soma fita daga harabar makarantar. Babu tazara sosai da gidan mahaifiyarsa inda bacci ke kai shi ya soma takawa.
A hanya ya hadu da wannan mutumin da ya zame ma sa sabo su gaisa. A wani benci yake zama kamar yana bara kamar baya yi. Kayan jikinsa babu na zaba, haka yake diki diki.
Yau ma da ya zo wucewa mutumin ya ce
” Ah yaro an fito, Allah ya albarkaci karatu”
Abba ya tsaya suka yi musabaha. Ya sa hannu a aljihunsa ya zaro dari biyu ya ba shi, dama haka yake yi. Ba su dade da karbar albashinsu na wata ba, shi kuma dama can mai yawan sadaka ne.1
Mutumin ya karba yana ta zuba godiya kamar yadda ya saba har ya kara da cewar
” Yaro Allah ya maka albarka! Allah ya kiyaye ka ya kare ka. Biiznillahi sai ka zame wa musulunci jakada. Sai ka zame wa iyayenka abun ceto!”
Tsayawa yayi cak!
Ya waiwayo a hankali ya cigaba da karewa mutumin kallo a tsanake wani irin farin ciki na fatattakar bacin ran zuciyarsa. Ba a taba adduar da ta zauna ma sa a rai irin ta yau ba.
Har akwai abun da ya fi ya zama jakadan musulunci, ya ceci iyayensa. Duk da cewa uwa gare shi yanzu kawai, mahaifinsa ya rasu a kullum dukkaninsu yana musu addua.
Dawowa yayi ya kara wa dattijon mutumin nan kudi ya juya yana murmushi. Zuciyarsa fes, watakila yau mahaifiyar ta sa ta samu tukuicin fara’a darajar wannan addua.
Haka ya shiga gida, ya ga motar kanwarsa Asiya abunda ya dada kara masa farin ciki kenen. Wato ta dawo daga makaranta, yana kaunar kanwar ta sa kamar ran sa. Allah Allah yake ya gama makaranta ko dan aiki ne ya kara samu, aure zai yi ya dauke kanwar tasa. Ba ya so ta taso a irin wannan rayuwar gidan na su. Ko da yake ita ma kanwar ta sa ai ta girma, Allah ya bata miji nagari da zai aureta yayi nesa da ita daga mahaifiyarsu.
Da wannan tunanin ya shiga gida. Wani abu ne ya sa ya tsaya cak. Karan ihun da mahaifiyarsa ta ke yi.
Abun ya ba shi mamaki don ita ba maabociyar shiga sashensu ba ce. Da sauri ya fada dakin Asiya ganin daga nan ihun ke fitowa.
STORY CONTINUES BELOW
Shigarsa kenen, abubuwa guda biyu suka sa numfashinsa yayi tafiyar wucen gadi.
Ganin kasurgumin makiyinsa kuma dadiron mahaifiyarsa Alhaji Awaisu cukwikwiye a hannunta kamar ba zata dake shi ba tana zabga kuka. Ya tsani ganin mutumin a rayuwarsa duk kuma duk yanda ya so ya danne kiyayyarsa ya kasa domin ko gaisuwa bata iya hada su.
Alhajin da kan sa ya ce zai biya masa karatu zuwa ingila, a ranar mahaifiyarsa da ta isar da sakon ba karamin haukarsa ta gani ba. Ya tsane shi tsanar da bazai iya kwatantawa ba domin ya taimaka kwarai wajen kara dulmiyar da mahaifiyarsa.
Na biyu sai ga Asiyan shi a yashe an yaga kayan jikinta kwance male male cikin jini, da alamar zubar jini har daga goshinta da ke nuna an doka ta da wani abu.
A cikin kankanin lokaci ya gane mummunan abun da ke faruwa. Bai yi wata wata ba ya daga hannunsa a dunqule ya dirkawa Alhaji Awaisu naushi ya kifa jini ta baki ta hanci. Ya hau kan ruwan cikinsa ya dunga kirbarsa kamar Allah ya aiko shi.2
Gani tayi zai kashe shi ta fara jan sa kawai sai ya wancakalar da ita. Kamar baya cikin hankalinsa ya dube ta idanunsa sun yi jazir ya ce
” Kar ki sake ki kara taba ni”!
Duk halin da take ciki sai da taji gabanta ya fadi. Kamar ba dan cikinta ba, kamar wani sabon mutum da bata sani ba.
Kinkimar Asiya yayi, ya nemi wani zani ya rufa ma ta yana kuka. Ya dauketa kamar bebin roba, da mukullin motarta, a lokacin Alhaji Awaisu ya samu kan sa ya fice a guje.
Hindu ta yo kan Abba tana kuka da nufin za ta taimaka masa da rike Asiya ya fincike. Cikin kuka ya ce ma ta
” Ita ma kar ki taba ta! Ya za ki haifa diya a cikinki ki tarwatsa mata rayuwa irin haka! Duk abinda ya same ta ke da shi kuyi kuka da kan ku! You have to pay for this!”3
Fita yayi da gudu ya bar Hindu kamar zata mutu da kuka. Ya dauki motar Asiyan ya wuce da ita asibitin da suke zuwa. Anan ma aka tsaya bata lokaci akan report na yansanda da sakaci irin na asibitin kasarmu.
Likitan da ke kan ta mamaki zai kashe shi. Ya dade a rayuwarsa bai ga mummuna case irin haka ba, dalilin ma kenen da ya dage sai an taho da yansanda. Jinin da ke zuba a jikinta ya ki tsayawa. Hakannan ta fara aman jini da ke nuna an dake ta sosai a ciki.4
Abba ke ta zarya a coridor har Hindu ta iso, da kyar take tafiya saboda bakin ciki. Tun da take a rayuwarta bata taba da na sani ba iri na yau.
Ashe Alhaji Awaisu azzalumi ne irin haka ta sa hannu ta gayyato shi rayuwarta ga shi ya tarwatsa ma ta ita. Da me za ta ji? Yau tayi Allah wadai da rayuwar karuwanci da ta fada domin kuwa bata kare ta da komai ba sai da na sani.1
Bayan awa kamar 2 likitan ya fito ya ce za su iya zuwa su gan ta, amma fa ba ai mata aiki ba domin yana jiran babban likita ya zo wanda yake kan hanya.
A sassarfa suka shiga su duba halin da take ciki, gabadaya kamanninta sun canja. Da sauri Hindu ta nufe ta zata kama hannunta yarinyar ta janye.
Ta tsirawa uwar ido da wani irin kallo a cikin wata irin siga ta ce a hankali
” Ki…n ..kash..eni mamah!way…yo mama..wa..yyo Alla..h.na“3
Hindu bata san lokacin da ta fada kan Asiya ba. Bata manta da cewar Alhaji Awaisu da yayi wa Asiya fyade na dauke da kanjamau ba! Da me za ta ji”
Kuka take ta ce
” Asiya kar ki min haka. Kar ki zargeni ba ni da hannu! Asiya ki yafe min..ki yafe min na zame miki sanadi”
Wani irin amai yarinyar ta fara yi na jini, likitan ya kora su waje. Abba baya iya cewa komai sai hadiyar zuciya yake. Rokon Allah yake ya sa a ce mafarki ne ina ma ba da gaske ba ne.
Ita kuwa Hindu jikinta gabadaya ba laka, don yadda ta ga Asiya ta san sai wani ikon Allah!
Likitan ne ya fito, cikin sharbar hawaye Hindu ta ce
” Yaya ake ciki likita?”
A sanyaye ya ce
” Ta zubar da jini dayawa…i am sorry..i am so so sorry Hajiya…we lost her!”8
Ta gane me yake nufi, ta san kawai Asiya babu!
Ji tayi kamar zata zube ta jingina da bangon gurin. Rayuwar ta ce take dawo mata a idonta kamar a mafarki. Ta tuna irin ranar da mutuwa ta warce nata jinjirinta muhammadu sabode tsananin talauci.
A yau ga ta a babban asibiti da kudi fal jakarta amma ba ta fi karfin mutuwa ta sure ma ta Asiya ba! Asiyar da ta zamo sanadiyyar da mutuwa ziyarce ta. Ashe sanadin da Alhaji Awa
isu zai zame mata kenen?
Ina ma ina ma, ina ma ta zauna a talaucinta da ya fiye mata wannan rana da dadironta ya haikewa diyar cikinta ta sheka har lahira! Wannan wani irin labari ne, labari mafi muni da bata taba jin ko makamancinsa ba a kafafen yada labarai ba.3
Ashe haka Allah yake hukuncinsa? Ashe kai bawa ba komai ba ne? Ashe baka isa da komai ba? Da me za ta ji? Ina zata je? Asiya kuwa zata taba yafe ma ta.4
Waji irin naushi Abba ya kai wa bangon da ta ke jingine da, karfin naushin ya sa ta gane tabbas ya targada daya daga cikin yan yatsunsa. Ta san ji yake kamar ya kashe ta.
Ta dube shi tana makyarkyata a idanuwansa ta hango wata matsananciyar tsana da bata taba zaton da yana iya yiwa uwarsa shi ba. Hawaye ne yake zubar masa kamar da bakin fanfo, yana so yayi magana ya kasa.
A hankali ta ji ya ce
” Ba zan yafe ba, tunda ku ka raba ni da Asiya”2
“Ba zan taba yafewa ba!”
Lokaci wani irin bahagon alamari…idan ba ka yi a sannu ba sai ya wuce ya barka! Ya kan tafi da abubuwa dayawa cikinsu har da raggon imani. Idan da rai da rabo, idan da yarda da aminci!
Cape Town, South Africa
Sauka yayi daga tasi ya shiga wasu runfuna na farmers market da ake siyarda kayan marmari.
Yawa yawan mazauna garin kan ji harshen turanci wasun su kuma yaren Afrikaans ko xhosa. Ya dubi dan tsamurmurin tsohon mai siyarda su inibi tufa da sauransu. Sai wani sikeli babba da karami na awo da ke gabansa. Ya ce da shi a yaren Afrikaans
Hallo! Hoe gaan dit? (Barka, ya ka ke)2
Dan tsohon ya washe hakora, na alamun farin cikin ciniki ya zo ya ce
“Baie goed, dankie” (kalau nake, nagode)
Mutumin ya ce da shi
“Praat jy Engels?” ( kana jin harshen turanci)
“n Bietjie “( kadan kadan) ya ba shi amsa yana murmushi, sa’anan yana nuna kadan din da ‘yanyatsun sa.
Murmushi mutumin ya ma sa. Ya nuna masa abubuwan da yake so da dan yaren afrikaans din da yake ji kadan kadan da kuma alamu irin na kurame.
Ya gama saya, ya biya shi a kudinsu da suke ce ma rand sannan ya ce da shi
“Dankie” (nagode)
Ya wuce.
Ya fara tunani, tasi ya kamata ya shiga ta kai shi summit clinic da ke Rondebosch medical center da ke nan capetown. Wani asibiti da ya kware wajen kula da duk wani abu da ya shafi kwakwalwa. Matar shi na can.3
Ya tsayar da tasi ya shiga. Ya cigaba da kallon ledar hannunsa yana tunanin ko zata so ci? Sun shafe watanni amma ya ga abincin bai dame ta ba.4
Ko ya zai gan ta yau? Lokacin ziyara yayi so yake ya leka ya gan ta ko da ba za ta ce komai ba.
Ya nisa ya nutsa cikin tunani na yadda lokaci ke tafiya babu kakkautawa. Shekaru goman da suka zo sun zo ma sa da wasu al’amura da baya ko son tunawa.2
Wai ashe dama haka duniya take? Haka lokaci yake idan duniya na yi da kai? Sai ta daukake ta daga ka sama ka ke jin kan ka a gizagizai? Lokacin da ta ga dama sai ta sake ka fado! Irin faduwar da ba lallai ka sake doruwa ba.
Shi Almustapha Iliyasou Tillaberi yana da labarun bayarwa game da rayuwa. Mamaki yake yi yanda a yau zai shiga Najeriya a garin kano amma ba lallai a samu mahaluki daya da zai daga ido ya kalle shi ya ma sa kallon sani ba. Rayuwa ta canja!4
An wayi gari babu I and A group of companies. Wani alamari da yake tunanin ba zai taba faruwa ba a duniya.
Tun bayan bata ma sa suna da aka yi investors dayawa suka janye hannun jarinsu, masomi kenen. Sai ya zamana cewa babu wasu manyan kamfanunnuka ko qungiyoyi da za suyi trusting din sa su saka dukiyarsu.
Sannu a hankali abubuwa suka fara ja baya. Ba a shekara 2 kwarara ba sai da kamfani ya rushe. Kamfanin da ya sha gwagwarmaya kafin ya tsaya da kafafunsa. To amma a lokacin ya san a halin da ake ciki ko da akwai investors ma kamfanin ba zai je koina ba.
Domin shi ma ai ba a hayyacinsa yake ba. Idan ya tuno mafi yawan dukiyar I and A haram ce sai ya ji babu mamaki da ya ruguje.
Dukiyar a cakude take da kudin caca! Sa’anan rabin dukiyar an ciwo ta ne ta haramun domin kuwa kashe Ahmadou Tillaberi aka yi aka handame.3
Bai kara tsorata da duniya ba sai da mutuwar mahaifinsa, mutuwar da aka rasa wanda zai yi ma sa wankan gawa!
Wai kamar mahaifinsa wanda ya girma ya daukaka a duniya aka rasa wanda zai sa hannu a wanki gawarsa saboda tsananin wari.3
STORY CONTINUES BELOW
A gaban idonsa mutanen da ke dafifi a gaban mahaifinsa lokacin da yana kan ganiyarsa suke sauri su yi gaisuwa su fice wasu ma ba su zo ba.
Haka mahaifin nasa yayi mutuwar wulakanci ba tare da ya tafi da ko sisin kwabon da ya handame ba! Wannan abu yana daga masa hankali. Wannan abu ya sa ma sa tsoron Allah. Ya gane dan adam a duniya ba komai ba ne illa wani abu da aka halitta daga tabo!3
Yana ji yana gani mutanen da ke rububinsa suka guje shi. Masu masa fadanci suka koma zundensa da kala masa wasu sharrikan da bai ji ba bai gani ba. Na kusa da shi aka hada baki da su aka cuce shi. Idan ya tuna da sadiq sai ran sa yayi baki kirin.4
Ba talauci ne yake damunsa ba, ya san ya fi karfin da a kira shi talaka futuk. Sai dai me? Zuciyarsa ke ciwo, ita ke tuno masa irin sanadin da ya jefa kan sa da masoyiyarsa.
Dukiyar da ya san tasa ce halak malak ita ya tattare, kawai ya san dole ya bar kasar don ta masa kunci dayawa.
Dama yayi karatun business har zuwa digiri na biyu. Kawai sai ya sa takardunsa ya fara neman aiki a wani kamfanin sayar da motoci da ke cape town a kasar Afrika ta kudu.
Cikin saa ya samu. Da yake dama can mutum ne mayen kasuwanci da sanin makamarsa. Bai wani dade ba yayi fice a kamfanin nasu wajen kawo musu sabbin ideas, nan da nan suka rike shi gam. Babu yadda mahaifiyarsa bata yi ba ya dawo gida, ya ki. Najeriya ta masa kunci.
Ya dauki kusan shekara goma yana wannan aiki kuma yana da arzikinsa daidai gwargwado,yana kuma kula da duk wanda ya dace. Watanni da suka shude ne ya kawo matarsa ya ajiyeta a asibiti, don abunda take bukata kenen a wannan lokaci.3
Shi ya san ba shi ne Almustaphan da ba. Mutum ne shi a yanzu da ya samu canji na rayuwa, mutum ne da ya kusanta kan sa da ubangijinsa. Shin me ya fi ma sa wannan alamari?2
Ya iso asibitin ya biya mai tasi ya shiga ciki.
Ya karasa , ya san inda zai gan ta. Wani dan daki da aka zagaye da gilashi ya karaso. A lokacin ya hange ta, zauna take tana fuskantar wani likita. Ya sha ganinsu a irin wannan zaman likitan yayi masa alama da zai iya shigowa.
Sai bai shigo din ba ba ya son ya katse su. Ta cikin gilas din ya zura musu ido.
Daga ciki likitan ya dube ta ya ce
“Yaya sunanki?”
“Sunana Rokaiyatou Ahmadou Tillaberi” ta ba shi amsa14
“Shekararki nawa?”
” Shekarata talatin da uku”
” Kin san cewa a baya kina fama da lalura ta shaye shayen miyagun kwayoyi?”
Ta ce
“Na sani”
Ya ce
” Kin san cewa zamanki na tsawon lokaci a gidan yari ya sa kin kamu da post traumatic stress disorder?”9
Ta ce
” Na sani”
” kin san cewa an kawo ki asibitin nan ne watanni da suka shude domin neman waraka ga matsalolinki?”
Ta ce ” Na sani”
Ya ce
” Kin san kin yi aure? Sa’anan mijinki shi ne ya kawo ki?”
Ta ce ” Na sani”
” Kin yarda kin amince cewar kina da matsala?”
Ta ce ” eh na yarda”
Ya ce ” Kin amince cewar za ki bar shaye shaye?”
Ta ce ” Eh na amince”
Ya ce ” Kin yarda cewar za a yi miki magani? Kin yarda za ki warke?”
STORY CONTINUES BELOW
Ta ce ” Eh na yarda”
Murmushi likitan ya ma ta, ta mayar ma sa.
Almustapha ya cigaba da kallonsu ta gilas yana tunano abubuwa da dama.
Fadar irin gwagwarmayar da ya sha da fadi tashi dangane da shariar Rokaiyatou wani abu ne da baki ba zai iya labartawa ba.
Arzikinsa sai da ya tasamma karewa amma sharia ta ki ci ta ki cinyewa. An daga kara an sake dagawa amma sharia ba ta kare ba. Dalili, saboda har a lokacin an kasa gano wanda yayi ainihin kisan kan.
Luba na da connections a sama yanda ba ya tssammani. Yawan yawan Alkalan da duk wasu wanda ke da hannu a shariar mutanenta ne. Ta siye ta handame koina. Amma ya san Allah ba azzalumin bawansa ba ne.
Haka ya tashi haikan ba shi south Africa ba shi Nigeria saboda ya samu ya fito da Rokaiyatou. Burinsa daya, in da zai samo douglas saurayin Rebecca da Luba ta ba shi kwangilar kasheta.
Neman douglas da ya kai shi ku san shekaru goma cas! Wadannan shekaru sun fi komai azaba da radadi a zuciyarsa. Ya shiga taskun da har ya fara ji dama ba a halicce shi. Duk sanda ya ziyarci Rokaiyatou sai ya ji komai na duniya ya fice ma sa fit a rai.
Kamar abun alamara aka kama douglas a wasu yan fashi da makami da ke hanyar legas. To dama yana da Yansanda a ciki wadanda ya dora akan case din shekara da shekaru. Ba shiri aka masa waya.
Tuni aka tado da shariar Rokaiyatou. Finger print din douglas dai shi ne wannan finger print da aka samu akan wukar da aka kashe Rebecca!
To shi douglas din ma bai wani damu ba. Ba wani boye boye ya ce shi yayi kisan dama wannan ba wani abu ba ne sabo a wajensa. Wanda ya sa shi yayi kisa bai dai fada ba domin shi ma akwai abinda ya kudurce a ransa.
Aka mayar da sharia kotu Almustapha ya tsaya tsayin daka har sai da aka wanke Rokaiyatou. Wankewar da ta dauki shekara da shekaru!4
Shi douglas ya fadi shi yayi kisa to amma ya ce hayarsa aka yi. Wanda yayi hayarsa bai fada ba. Shi a tasa zuciyar ya rike sunan Luba ne domin yayi garkuwa da hakan.
Zai yi mata aike na cewar ta zo ta san yadda za ta fitar da shi idan ba haka ba ya ambaci sunanta. Ya san a yadda ya san ta sai tayi yanda tayi ta fitar da shi. Da wannan qudurin yake taqama.
Duk yanda Almustapha ya so Douglas yayi maganar Luba bai yi ba, to amma zai waiwaye shi ba wannan ba ne a gabansa. Zai magance wata matsala tukunna kafin wannan. Zai ceci rayuwar masoyiyarsa.
A hankali ya ga ta fara zagwanyewa, a hankali ya ga ta fara fita daga Rukkynta ta koma wani abu da ban. Tsananin damuwa da illar shaye shaye ya shiga kwakwalwarta ya na neman ga buga.
Fitowarta babu dadewa ya sa aka daura musu aure. Bai yi wata wata ba ya dauke ya ajiyeta a asibiti domin a bata kulawa ta musamman dangane da halin da take ciki.
Da sannu ya fara waiwayar Luba, zai tabbatar ta kare a inda ya kamace ta.
Wayarsa ce tayi kara, wani inspecton dansanda ne da ya tsaya masa kan lamarin. Ya ce
“Hello, inspector”
” Douglas ya fara magana” ya ce da shi
Murmushi yayi ya ce
” Good, very good”
Ya cigaba da kallon matarsa ta cikin gilashi. Da yaren Afrikaans din da yake ji jefi jefi ya ce
“Ek het jou lief ” ( i love you)15
****************************
Zaune take akan kujerar falo, a cikin sati biyun da suka gabata ta shiga tashin hankalin da bata taba sanin akwai kamarsa ba.
STORY CONTINUES BELOW
Mutuwar diyarta Asiya ya tsaya ma ta a rai fiye da kanjamau din da take dauke da shi. Ta yi kuka ta yi kuka ta gode Allah har hawayenta ya kafe kaf!
Sai a lokacin ne mahaifiyarta da kanenta suka taba takawa suka zo gida yi mata gaisuwa. Tambayar duniyar nan me ya samu Asiya ta rasu ta kasa amsawa sai kuka. Suka gaji suka kyale.
Ita ta san abunda take ji a zuciyarta. Ta ji wani irin da na sani ya lullube ta. Kawayensu ‘yan bariki da manemanta maza su ne suka yi ta tuttudowa zuwa gaisuwa. Gabadaya sai ta ji kunya ta rufe ta.1
Haka aka yi makoki aka share. Gashi duk tsawon wannan lokacin Abba bai ce da ita kanzil ba.
Daki yake shiga ya kulle kan sa, babu inda yake zuwa. Komai na dakin Asiya muhimmi mallakinta ya kwashe ta rasa me yake nufi da hakan.
A safiyar yau ne ta cigaba da zama a wannan falo zazzabi ya rufe ta. Ta san ba komai ba ne sai don yanayin jikinta da kuma zuciya. A sati biyun nan wata rama ta yanyameta.
Dama tunaninta ta kai Alhaji Awaisu kotu to sai kuma wata zuciyar ta ce da ita ai kan ta zata tonawa asiri.
To amma ba ta kara shiga hankalinta ba sai da ta samu labari cewa fitar Alhaji Awaisu daga gidanta ashe hatsarin mota yayi. Dama a cikin maye yake.
Wai yana kwance asibiti rai a hannun Allah. Babu yanda ba a yi ba tsohuwar matarsa ta zo da yaran amma ta ce a je a nemi Hindu. Ai ita ce ta fi cancanta tayi jiyyarsa.13
Ba ta san mikin da ya aza mata ba! Nadama ta shige ta, ta rabo shi da iyalansa ga shi ta jawowa kan ta jangwam.
Numfashi ta saukar a hankali, rabonta da ta ci abinci ta manta. Fitowar Abba ce daga dakinsa dauke da jakunkuna irin na matafiya ya sa ta dawo hankalinta. Gabanta ta ji ya ba da dam!
” Abba ina za ka je?”
Bai kula ba. Fara fita yayi da wasu daga cikin kayan yana kaiwa bakin gate. Hindu ta tashi zumbur! Gabanta lugude yake ba dai Abba tafiya zai yi ya barta ba? Idan ya tafi ina zata sa kanta? Ta rantse da Allahn ta ba za ta iya rayuwa ba!
Tashi tayi ta fara bin sa a baya cewa take
” Abba ba da kai nake ba? Shin ba ka jin ina maka magana ne? Ina za ka tafi da kayanka duka? So ka ke ka bar ni ko?”
Wasu kayan ya kuma cicciba zai wuce ta ta cakumo shi.
” Abba kar kayi min haka. Ka san kuwa ni mahaifiyarka ce? Duk yadda na kai ga lalacewa ni ce nan dai na haifeka. Baka da wanda ya fi ni sa’anan ina da hakki akan ka”
Maganar da ta sa jikinsa yayi sanyi kenen amma bai fasa fita ba. Hawaye ne ya fara zubo masa ya ce
” Mama ki yiwa Allah ki wa Annabi ki kale ne. Ke uwata ce duk kuma yadda na so na yafe miki bazan iya ba. Duk yadda zan so abubuwan rayuwar mu ya wuce kamar ba a yi ba bazan iya ba! Gwara nayi nesa nesa da ke watakila hakan zai sa na ji sassauci game da yadda nake jin ki a zuciyata. Ba na so na aikata abinda Allah zai tsine min! Bana so!”
Fizge rigarsa yayi ya wuce waje. Wani dankwali ne a kanta sai gamun gambiza na zani da riga a haka ga biyo shi tana kuka
” Haba Abba, ya zaka min haka? Da me ka ke so in ji? Nayi nadama, duniya ta koyamin hankali”
Waje ya fice sai yayi kacibus da maigadi yake ce da shi
” Allah gafarta malam ai wani mai bara ne yake nemanka a waje. Wai ya ga ba ka wucewa yanzu, shi ne aka ma sa kwatancen gidan, ya zo”
Haushi ne ma ya kama shi ya fice wajen ya ga wa ke nemansa haka. Daga nan ma ya kirawo dan tasi ya kwashi kayansa.
‘Yan kudaden da ke hannunsa da ya kan samu na albashi da aikin kanikanci ya tatuke ya kama wani daki. Daga nan gareji zai wuce ya riga ya shawarta wa kan sa dagewa zai yi da aikin kanikancin nan. Da shi zai rike kan sa kafin ya samu ya karasa makarantar ya ga abunda Allah zai yi.
STORY CONTINUES BELOW
Zuciyarsa a dake take kuma ya qudurta aikin karfi dai ta hanyar halal zai yi ya samu kudi ko yaya ne. Babu maraya sai rago.
Fitarsa kawai yayi kacibus da mutumin nan da yake taimakawa a hanyar makaranta. Yana nan dai yadda ya san shi gaje gaje. Mutumin kamar zai durkusa ma sa, Abba yayi sa
uri ya ba shi hannu.
Ya ce
” Allah gafarta malam kwana biyu shiru ba ka wucewa. Na ce a min kwatance na zo na gaishe ka, na ga ko lafiya.”
Bai kai ga amsawa ba Hindu ta bayyana kamar mayunwacin zaki tana kuka.
” Kar ka min haka Abba , Ni mahaifiyarka ce ba ka da wanda ya fi ni”
Wani irin dagowa yagalgalallen tsohon yayi a firgice. Idanunsa ne suka yi masa tozali da abunda ya firgita shi. Ko a duhu ko a haske sai ya gane ta. Ya ce
” Hindatu”!!!!!
A cikin tashin hankali ta dago ta zuba masa jajayen idanuwanta, sai tayi turus.
Wani irin abu ya fara mamaye mata zuciya na tsananin bakin ciki ta ce
” Habu! Innalillahi…innalillahi wa inna ilarrajiun”
Kawai durkushewa Habu yayi a wajen yana hawaye
” Na shiga uku Hindatu! Kin ga yadda Allah ya mayar da ni ..kin gani ko? Hakkinki ne! Hindatu ki yafe ni”6
Abba ne kuma fuskarsa ta mamaye da mamaki. So yake ya san waye. Mahaifiyarsa ya ga fuskarta gabadaya ta canja, wani irin bacin rai da bai taba ganinta a ciki ba. Ta nuna wanda take kira da Habu da danyatsa a fusace ta ce
” Fice min daga gaban gidan kafin na sa yansanda su fice min da kai!
Jikin Habu har rawa yake zai kamo ta a rikice ta hankada shi.
Hankalin Abba ya tashi cewa yake
” Mama lafiya? Wanene haka? Me ke faruwane wai?”
“Ubanka ne!!”
Tsikar jikinsa ce ta tashi yarrr, amma bai yarda ba. Jikinsa kawai ya ba shi wani makircin ne take son kullawa. Shi da babansa ya dade da mutuwa!
Ransa ya fara baci, wai me ke damun mamansa da maza ne.2
Habu din ne ya dago ya kalli Abba a firgice hawaye na malala ya fara nuna shi da danyatsa. Cewa yake
” Hindatu..Abba ne wannan? Hindatu da na Abba ne wannan? Na shiga uku na..Hindatu ya zan yi na shiga ukuna”
Ya mika hannu yana so ya kama Abba. Hindatu tayi ta maza ta finciko Abba ta kankame. A fusace ta ce
” Ban ce ka bar gidan nan ba? Yanzu ka san dan ka ne azzalumi ma ha’inci! Kar ka sake ka taba mun da na! Kar ka sake ka zo inda mu ke. Yanda ka tafi ka bar mu haka yau zaka gan mu ka kyale. Get out!”
To a lokacin ne jikin Abba ya gama ba shi, ya tsirawa tsohon kallo. Daga gani ba wai tsufan ba ne yayi tsabar wahala ce da talauci.
Yadda mahaifiyarsa ke kuka ya sa ya ji ko wanenne mutumin ya tsane shi. Ya ce2
” Malam ka matsa ma ta daga kofar gida ka ji ko! Ya za ka zo har kofar gidan mace ka daga mata hankali, dan Allah dan annabi ka tafi”
Kamar Habu zai rarrafa ya kama kafafunsa ya ce
” kai ma ka manta ni ko? Kai ma ba zaka yafe ni ba ko? Ashe shi yasa na ji rana daya ina kaunarka? Ashe jini na ne kai! Wayyo Allah na Abba kar ka gujeni kai ma.”
Tuni Hindatu ta fizge Abba sun yi cikin gida tana fushi tana fidda numfashi. Abba ne ma ya rufo gate din don ya fara tunanin ko mutumin na da tabin hankali. Yadda mamansa ke yi ya ruda shi.6
STORY CONTINUES BELOW
Falo suka koma, ta samu kujera ta zauna dabas. Sai gumi ta ke zazzabi ya rufe ta. Tayi kuka a dan kwanakin nan ta gaji. Ta san da kyar ne idan aka auna jininta bai hau ba.
Abba ne ya tsaya a kan ta ya nuna kofa da hannu ya ce
” Mama wanene wannan mutumin da ki ka ce babana ne? Na gaji da wannan rayuwar, wanene shi?”
Ta dago kai a hankali a sanyaye ta ce
” Mahaifinka ne Abba! Wallahi shi ne uban da ya haifeka!”
Wani irin mugun kallo ya watso mata. Ya nuna kan sa da danyatsa cikin tsananin mamaki ya ce
” Ni? Ni mama? Mahaifina ni da Asiya? Shin ba kin ce mahaifina daga yayi tafiya aka aiko ya rasu ba. Shin ba ke kika ce min na dunga yi masa addua ba Allah ya jikansa. Kina nufin hakan ba gaskiya ba ne? “
Muryarta na rawa ta ce
” Abba ba zaka gane ba! “
Ya kankance idanunsa yana jin tsanar da ya soma cirewa game da ita a ransa na dawowa ya ce
” Ki boyemin mahaifina sama da shekaru sha biyar. Ki kashe shi da bakin ki sannan ki ce da ni bazan gane ba?! Shin mama idan za ki yanke hukunci kina kuwa tuna mu mu ‘ya’yanki? Shi mama kin san mu amanar Allah ne a gurinki?”
Ta kalle shi a tsaurare ta ce
” Duk hukunci da na yankewa rayuwata na yanke ne saboda ku! Saboda ku ji dadi saboda ku taso cikin kwanciyar hankali da wadata. Abba sanadin fadawa ta wannan rayuwar saboda kai ne! Ina ji a lokacin da na gan ka a mace gwara na sayar da jikina na samu abinda zan maka magani!1
Shin Abba ka san irin son da uwa ke wa da? Irin son da kan sa ta sadaukar da komai saboda d’a? Irin son da kan rufe mata ido ta mance imaninta?
Shin ka san yadda na wahaltu a rayuwa saboda ku? Saboda ku ci ku sha ku je makaranta.
Na san ban yanke hukunci mai kyau ba..na san wataran Allah zai tambayeni. Ga shi nan ma kafin na je ga ubangiji na na fara ganin sakamako. Abba kai ne me ilimi kana ganin akwai wani abu da zan fara yi Allah ya yafe min wasu daga cikin kurakurai na?”
Kuka yake hanyar kofa yayi kamar zai fita. Ya rasa ya zai yi da rayuwarsa.
Bude baki tayi ta ce
” Abba ka dawo! Kar ka gujeni. Ina dauke da cutar kanjamau!!”2
Wata irin mahaukaciyar juyowa yayi da sauri cikin tashin hankali. Jikinsa ya fara rawa kamar mazari. Wani irin tausayin uwar ya mamaye shi. Ya fara jin wani abu na yawo a makoshinsa, irin yadda ya ji sa’in da ya ga Asiya a yashe an mata fyade.
Ya dawo da baya ya zauna akan kujerar da take. Ta kura ma sa ido ta ce
” Zan baka labarin rayuwata zaka gane dalilin da yasa na kori babanka a yau. Zaka san dalilin da ya sa na amsa sunan karuwa a yau. Watakila dalilan ba masu karfi ba ne a idonka, watakila dalilin ka gan su da rauni.1
Amma Abba mutanen duniya sukan iya yanke hukunci a bisa kuskure, sukan iya yankewa a lokacin da suke ganin hakan ne kawai mafita. A wata safiyar laraba…”4
A ranar Abdulhakeem Abubakar ya san wacece uwarsa Hindatu.
A ranar ta labarta ma sa sirrikanta da kurakurenta!
Galala yayi yana kallon mahaifiyar tasa. Wani irin abu yake ji a jikinsa da bai san ko menene ba. Ashe lokacin da ya fada rijiya yana yaro uwarsa karuwanci tayi ta samo kudin asibitin sa?
Menene haka? Wani irin bahagon labari ne irin haka? Wani irin labari ne haka marar dadin saurare? Allah ka sa mafarki ya ke!
Komai na jinin jikinsa ya tsinke. Wani irin tsananin tausayi ya kama shi kallonta yake kamar ya maida rayuwarta mafarki. Muryarsa na rawa ya kama hannunta ya ce
STORY CONTINUES BELOW
” Mama ba zan taba barinki ba! Ko da ke kika fi kowani dan adam zunubi a duniya!…Mamah…ki ce ..As..tag..fi..rullah!”18
Hindu kuka take. Ta ce
” Abba kunyar Allah nake ji! Laifukana ba zasu yafu ba. Akwai hakkin mutane. Abba ba zasu yafu ba..1
Ta kara fashewa da kuka ta ce
” Abba!..mahaifiyarka ‘ yar wuta ce!!”6
Bai san lokacin da ya jawo ta ya kankame ba ya ce
Allah mai karbar tuba ne, ki tuba saura Allah shi ne masani. Ki tuba kafin lokaci ya kure miki. Mama ki ce Astagfirulla….Mama ki ce astagfirulla”2
Ta ce
” Abba na..ce…Abba na ce Astagfirulla..Allah na tuba! Abba ka taya ni rokon Allah ka ce na tuba! Kayi tawassali da kyawawan aiyukanka, da zuciyarka da alherinka ka ce Allah ya dube su ya yafe min!2
” Ba kyawawan halaye na ba ne ya sa ubangiji ya bani kai, da ni da mahaifinka bamu da wannan kyawun halin. Cewa yayi ka kasance kawai sai ka kasance. Ya halicce
ka ne don ka zame mani izina!”
Dagowa yayi ya kalleta. Ya kama hannunta ya kankame. Yana son uwarsa son da bata sani ba. Yana tausaya mata tun lokacin da ya gane irin rayuwar da take. Kullum yayi sallah yana yi mata adduar shiriya. Lokaci bai kure ba kanjamau ba karshen rayuwa ba ce. Ya ce
” Mama za ki iya barin duk wannan daular ki bi ni? Wannan haramtacciyar dukiya ce. Ko dako sai nayi na ciyar da ke!”
“Kin yarda?”
Ta gyada masa kai, wannan karin da murmushi a fuskarta.
Ya ce
” Ita zuciya ita ce mutum. Akwai wani hadisi na manzon Allah da yake cewa
Wa inna fil jasadi madhghatan, idha Salahat Salaha al jasadu kulluhu, wa idha fasadat fasada al jasadu kulluhu, ‘a la wa hiya al Qalb.4
A cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru kuma Idan ta baci dukkan jiki ya baci. Ku saurara, ita ce zuciya.
Akwai wani hadisin da manzon Allah ya ce Allah madaukakin sarki ya ce
” Yaa ibadii, khullukum dhallun illa man hadaytuhu, fastahdhunii, Ahdhikum
Ya ku wadanda ku ke bautamin, dukkanku batattu ne sai wanda na shiryar da shi. Ku nemi shiryarwata, zan shiryar da ku.3
“Kin san da wannan hadisin?”
Murmushi tayi tana mai kallonsa da girgiza masa kai ta ce
” Ban sani ba. Kai ne za ka sanar da ni Abdulhakeem.”
******************************
Sai kin yi!
Hajiya Lubabatu sai kin yi
Kujerar dan majalisa a kano kamar kin hau
Bi za til rasulillahi sai kin koma habuja
ANCC sak!
Kowa ya bi , daga sama har kasa
Wanda bai bi ba ma an bi mar dan uwatar!13
Wani dan daba ke wasa Luba, ba ta san lokacin da ta zaro kudi ba tana watsawa a sama yara na wawaso.4
Ranta kal kamar takarda. Taron jamiyyarsu ne ake yi, suke yawo waje waje na kamfen. Ita kan ta ta san ta kafu, ba gudu ba ja da baya.
Da tuno irin alkawurran da suka yi da Alhaji Bilya Dala kanin mijinta. Komai yana tafiya yadda ake so. Lokaci kawai suke jira.
Da kyar ta samu ta bar gurin saboda cikowar mutane. Farin jini gareta sosai saboda akwaita da wasa da kudi. Ga mijinta ya tsaya ma ta.
A hankali ta gangaro zuwa inda ta faka hadaddiyar motarta. Karar shigowar text ne ya ja hankalinta. Tana karasawa mota tana dubawa, ta karanta text din. Abunda ya sa ta tsaya cak
” Har kin gama cika burirrikan ki? Domin kamar mutuwar bazata haka duniya za ta datse miki cikar buri!”
Jujjuya wayar ta ke a hannunta cikin tsananin mamaki. Waye haka? Daga ina? Har ita akwai wanda ya isa da zai turo mata irin wadannan sakonnin?
Ta buga tsaki, za ta sa a bincika ma ta.1
Kokarin tayi na son bude motar tana kokawa da mukulli.
Wata sanyayyiyar murya ce ta katse ma ta hanzari.
” salamu alaiki ya umee! ana saeid liruyatik alyawm!”
( salam ya mahaifiyata, ina farincikin ganinki a yau!)4
Wani irin wawan juyowa Luba tayi, gabanta ya yanke ya bada dam!
Wani irin abu take gani a gabanta, tamkar fuskarta! Wata yarinya tamkar ita! Banbancin daya ne, ita wannan tamkar akwai sirki, barbarar yanyawa.1
Wani irin zabura tayi tana nuna ta da danyatsa bakinta na rawa ta ce
” min ant ,wacece ke? “
Dariya yar budurwar yarinyar ke yi. Idanunta na nuna yarinta da kuma hatsabibanci a tare.25
Ta ce tana mai nuna kanta da dan yatsa ta ce
” Ismee Nadhiya! ( sunana Nadiya)
Ta jinjina kai ta kara da
” Ni ce diyar nan da kika watsar a Karantina mundh sanawat eadida ( shekaru masu yawa da suka wuce). Na ji an ce kin yi kudi, shi ne na zo na karbi rabo na!24
Wasu sirrikan ba sa boyuwa..4
wasu sirrikan ba sa taba yarda zu zamto tarihi tono kan su suke..su tarwatsa mamallakinsu.