MAI TAFIYA CHAPTER 7 KARSHE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Karshen alewa kasa!+
With a heavy heart i conclude the last 2 chapters of Maitafiya. Ya Allah ka karbi ranmu muna mai tuba a gareka. Ya Allah ka sa mu gane girmanka da daukakar ka tun kafin lokaci ya kure mana. Allah ka sa mu gyara kurakurenmu tun kafin mu fuskance ka dan darajarka dan darajar fiyayyen halitta. Allah ka raba mu da dattin zina, ka sa mu nisance ta ka sa mu bayyana a gabanka muna tsarkakakku, masu tuba, masu nadama! Ya arrahmar rahimin ya Alkhramal Akhrameen ya zhul jalalu wal ikram.19
Kano, Nigeria
Tsaye yake yana kallon agogon hannunsa sanye da farin yadi da takalmi sau ciki. Haka yake yawancin shigarsa yanzu, tsadaddun abubuwa ba su cika damunsa ba.
A makarantar yara ta Lufaloy yake, karfe biyu daidai na rana yana hange hangen ta inda yaron zai fito.
Yaran ga su nan birjik cikin yinifom, sai ya ga kawai su na yi masa kamanni shigen daya. Bai daina hange hangen ba kawai sai ya ji an ruqunqume shi.
” Oyoyo…Daddy! Yaushe ka dawo? Shi ne ka zo daukana a school?”
Shi ma rike shi yayi, kana ya mika masa hannu suka gaisa ya na cewa
” Ka ga Malam ALMUSTAPHA..kananan ‘yan makaranta..ah..ah..Allah sabbinani!”2
Turbune fuska yaron yayi ya ce
” Daddy mu fa mun girmi kanana, yanzu fa muna sacondary section ne.”
Uban ya ce
” Au..au..yallabai ai na manta. Kamar ma ka ce min kai ne monitan ajinku ko?”
Dariya yaron ya saki ya ce
” Habaaa…Daddy cewa nayi assistant fa”!
” Au ..au..ka ga assistant..to.menene banbancin? Ai aikinku rubuta masu surutu. Shi ne fa!”
Ya tallo keyarsa ya ce
” wuce mu je kar mommy ta cinye tuwonta babu kai”
Wani irin qura ma yaron ido yake, tsananin kamanninsu na ba shi mamaki. Ko dariya yaron yayi kamar shi, babu abinda ya biyo na uwarsa.5
Har yanzu ya kasa kallon dan sa Almustapha da wata siga da ta wuce wacce take akwai. In yaron ya girma me zai ce ma sa?
Yanzu kowa ya sani a duniya yana da dan shege wannan wani kazamin alamari ne a yankinmu.
Ana kyamatar yaran da aka haifa ba tare da aure ba, a kan yi musu tofin Allah tsine. Yaran ba su ji ba ba su gani ba amma kuma ba su da yadda za suyi.
Ya kan kalli Almustapha cikin jin kunya cikin dana sani. Ya kan kalle shi cikin jin nauyi da tunanin gaba.
Yanzu mai zai ce ma sa idan ya girma? Ya yaron zai ji idan ya fahimci yadda aka same shi? Ya zai ji idan ya san kashe uwarsa aka yi?!2
Almustapha iliyasou Tillaberi kan kwana da wani nauyi a kirjinsa da ke danne shi ya hana shi numfashi. Ya san da wannan nauyin zai koma ga Allah.
Shigowar Almustapha karami rayuwarshi ba karamar kaddara ba ce. Babu irin zagi da aibatawar da ba a yi ma sa ba.
Ido da ido an kira daniska, azzalumi, dan caca. Yawa yawan mutane na bin sa da cewar da sa hannunsa a kashe Rebecca. Har yau a kano cikin mutanensa na da can baya, bai isa ya shiga ba. Masu mutunci ba su so a gan su da shi.
Sukan ce wai nauyin zunubinsa ma kadai ya isa ya shafe su. Amma me?4
Almustapha ya san duk duniya babu ya ubangijin talikai, kuma a wajensa yake neman rahama.2
STORY CONTINUES BELOW
Tuban da yayi ya sa ya karbo dan sa wanda ya haifa ba tare da aure ba Almustapha junior. Ba zai taba bari rayuwarsa ta lalace ba saboda kawai yana jin kunyar kar a jefe shi da kalmar uban shege. Da kunyar lahira gwara ta duniya!9
Ya kan shiga da dan sa koina, ya kan dauki Almustapha junior a matsayin kaddara. Babu wani bawa da ya fi karfin kuskure, babu wani bawa da ya fi karfin rubutacciyar kaddara.1
Ya so ya tafi da shi cape town suyi rayuwarsu a can, amma mahaifiyarsa ta ki. A wajenta yaron yake domin a halin da ake ciki yanzu ai ba ta da kowa. Rayuwar da can din dai ba daidai take da yanzu ba, suna cikin halin da a yanzu dukkansu sai sun tashi sun nema ne. Don haka tana aikin koyarwa a legal.
Almustapha ne ya nema ma ta wani madaidaicin gida bayan an siyar da ragowar dukiyarsu an raba gado. Hajiya khulsumou ita ke da yawan ‘ya’ya haka ta dun ga zalama ta na zuba rashin mutunci.
Daga karshe ya tattara komai ya ba su. Abinda ya san na shi ne ya dauka, da su zai yi al’amuran gabansa.
Samun aikinsa ba karamin sauki ya kawo ba. Ga shi yanzu duk wadanda suke karkashinsa yana daukan nauyinsu.
Ya shiga da junior mota har gidan Mummy. Jiya jiyan nan ya dawo daga capetown, akwai wani case musamman da ya dawo da shi. A mota yaron na ta mishi surutu, da cewar in zai koma zai bi shi. Ya ji yana so ya tafi da shi amma ya san sai dai a gaba.
Mahaifiyarsa ta kwallafa rai akan yaron, gani yake kamar shi ne yana karami. Saannan Rokaiyatou ba mai lafiya ba ce kula da shi zai zama wani aiki babba. Shi kuma kullum aiki ya masa yawa, ya ji da marar lafiyarsa ya ji da aiki.
Ya sa a ransa dole ne shi da Almustapha junior su rayu wataran a bigire guda daya. Yana so ya san dan shi yana so ya ja shi a jiki. Ya kan kalli Almustapha tun yana dan kankani ya ma sa addua
” Allah ya sa kai tsarkakakke ne. Allah ya sa ba za ka biyo halayen mahaifanka ba! Allah ya kare ka daga dattin zina. Bi za tul rasulillahi sai ka zama abun kwatance, sai ka ceci alumma.”2
Suna shiga gidan tana fitowa daga kitchen da wani dan karamin kwano na alamun ita ta dafa.
Sau da yawa a yan shekarun nan yana mamakin mahaifiyarsa, yadda ta sauko. Saukowa irinta dolen dole domin kuwa babu wadatar da za a dauko masu hidimta ma ta.
A tun tasowarsa bai taba ganin mummynsa a kicin ba wai don girki sai ga shi yau kamar ba ita ba. Duniya juyi juyi.11
Suka yi hirarrakinsu yadda suka saba, tana ta nan da nan da shi. Duk abunda a ke yaron na sa na makale da shi, ya kankame shi. Ta kara tambayar jikin Rokaiyatou ya ce ma ta da sauki.
Bayan ya ci abinci ya fita da niyyar zai dawo.
A mota ma tunane tunane yake yi, yana Allah wadai da shaye shayen miyagun kwayoyi. Shaye shayen da ya janyo Rokaiyatou ta kasa samun kan ta har yanzu.
Shin ko wata kungiya zai bude ta yaki da miyagun kwayoyi? Ya lura babu wani abu da yake tarwatsa al’umma irin qwaya. Da mutane sun san illar da suke yiwa rayuwarsu da basu fara ba.
Ya tarwatsa maka rayuwa ka zama marar mamora. Ya jirkita maka tunani ka zama marar nazari. Daga karshe yawa yawansu su kare a hauka. To wa gari ya waya?
Banda lalurar PTSD da ta kama ta kwayar da sha ta taimaka wajen birkita mata tunani. Har yanzu ba ta ji sauki yanda ake so ba, to anya ma za a samu yanda ake so kuwa? Wasu abubuwan ya san za su gyaru,wasu
kuwa sai dai hakuri. Ba a bari a kwashe daidai.2
Ya daga waya ya kira Barrister suka yi magana kamar yadda suka saba. Ya dora da
” Yallabai ai kar ka damu, case yana kotu a yanzu haka. Za a zauna ranar sha shida ga wata. Mun yi magana da douglas a matsayin mu ne lauyoyin da zamu kare shi. Mun kuma yi masa gadar zare na cewar idan dai ya fadi gaskiya hakan zata samar ma sa da ” immunity” a kotu. Wato za mu wanke laifukansa ya koma kan luba gabadaya. Komai is under control, babu matsala.”
STORY CONTINUES BELOW
” Gaskiya na ji dadin hakan” ya ce da shi. Barrister ya cigaba da cewa
Sannan mun nemo wannan abokin aikin na ta, dan daudun nan ‘yar modu. Acan wani kauye cikin karamar hukumar doguwa muka samo shi. Ashe shekaru da dama ya sha fama da ciwon hanta, komai na sa sai da ya kare.12
To a lokacin ne ita Luban ta guje shi. Babu yanda bai yi ba don ta taimaka masa domin ciwon ya dau shekaru ba a gane asalin menene matsalan ba.
Da ta ga zai dame ta sai ta daina daukan wayoyinsa. A lokacin da muka je kwata kwata idan ka san shi a da can ba zaka ce shi ba ne.
To sai mu ka so jin bayanai daga bakinsa dangane da case din muka hada da yi masa alkawurra na nemar ma sa magani.
To ashe shi ya fi mu kulewa ganin yadda ta masa butulci. Ya lalace abun babu kyaun gani. Kai! Ni ina tunanin ma da kyar idan ba sida ce ta ci ta cinye shi ba. Domin har ina tarin nan yake yi kamar na masu tarin fuka.
Ya ce zai tsaya shaida a kotu ko zai samu sassauci wasu zunuban. Sannan ya ce yana da shaida na transaction na kudi da ta yiwa douglas da wanda ta yi masa. Akwai wasu faya fayan video ma da ya ce ya dauka bai taba tunanin za suyi masa amfani ba sai a rana irinta wacce muka je.
Komai yana tafiya ne yadda ake so, babu wata matsala.”
Da haka suka karashe wayar Almustapha na cewa
” Good, very good”
Ya kashe. Sa’annan ya danna kiran da yake so. Ya shiga ta fara
” dit…dit”
Alhaji Hamza Mai Dala ke zaune a office din sa. A gaban teburinsa takardu ne baja baja. Tsohon dan siyasa ne haka barawon gwamnati na kin karawa.
Wani irin murdadden mutum ne cikakken dan ta’adda. Kana shiga gabansa sai sa a dauke ran ka daga doron kasa wannan ba matsalarsa ba ne.
Sai dai a fili idan ka kalle shi ba zaka kawo hakan ta farat daya ba domin kuwa yana da fuskar kadaran kadahan. Yana da taimakon wanda ya so ya taimaka musamman kaninsa uwa daya uba daya Bilya.
Allah ya jarabce shi da son Luba tun ba yau ba, don haka yayi amfani da dukiyarsa wajen farauto ta. Ya zuba ma ta duk wani abu na jin dadi na rayuwa da tunanin wannan shi zai rike ta ta daina yawon dandi.
A ganinsa ya kama Luba ram tunda ya ajiye ma ta kudade. Da kuma bazarsa take rawa domin kuwa shi ya tsaya tsayin daka game da siyasar ta.
Ya ri ga ya tsara duk yadda abun zai kasance. Ita ma za ta zame ma sa wani tsani ne na farauto kudin jamaa, na waso asusun gwamnati. Gaba gaba fatansa yayi takarar gwamna domin kuwa har yayi sanata sau biyu.
Wayarsa da ke kara ya daga. Daga daga dayan bangaren aka yi masa bayani kamar haka
” Sunana Almustapha Iliyasou Tillaberi. Na san ina magana ne da Alhaji Hamza Mai Dala. A wajen sakatariyarka na bar sako a ba ka. Wani lamari ne da ya shafi matarka Lubabatu. Duk abinda ka gani a cikin wannan sakon gaskiaya ne, idan kuma har baka yarda ba akwai wasu hujjoji masu karfi da zan iya gabatar ma ka daga baya ko kuma ka tuntubi matarka don karin haske. Na bar ka lafiya.”
Kit! Ya kashe wayar
Bakin Alhaji a sake ya cika da mamaki. Wani irin mugun sako ne haka. Bai rufe baki ba sakatariyarsa ta shigo ma sa da sako ya karba jiki na rawa. Wata zungureriyar ambulan ce fara kal! Sai da ya ji gabansa ya fadi domin ya san ba alheri ba ne.
Ambulan din ya fara zazzagowa hotunan ciki suka fado. Sai wata zungureriyar takarda. Kallo daya yayi wa hotunan numfashinsa ya dauke na sakan 5.
Wasu irin kazanman hotuna ne na matarsa Luba da kaninsa Bilya, sun fi kala goma sha biyar. Wasu hotunan saboda kazantarsu bai ma san ya aka yi aka dauke su ba.8
STORY CONTINUES BELOW
Sai yanzu ya gane yawan shirin matarsa Luba da kaninsa, ya zata irin wasan nan ne na kanin miji. Ashe cin amanarsa suke!
Ya tuna lokacin da tayi tafiya kasar faransa Bilya kuma ya ce ma sa zai je wani aiki ingila ashe karya suke hadewa suka yi? Ga hotuna nan birjik a wajejen shakatawa sun rungume junansu.
Hankalinsa bai fita a jikinsa ba sai da ya warware wannan takarda ai sai ya ji duk duniya babu wani mahalukin da ya tsana irin Luba. Sakamako ne na cewar wai ita Luba din tana dauke da cutar kanjamau!4
Wata irin zabura yayi! Gumi ya jike shi sharkaf! Har makyarkyata yake. Babu abinda yake yi sai salati. Ransa yana raya masa shartin makiya ne amma ya ka sa yarda.
Cewa yake
” Ta kasheni! Yarinyar nan ta cuce ni! Innalillahi! Yau na shiga uku na!8
Ya wawuri wayarsa ya kira kaninsa Bilya. Bai ko bari ya gaishe shi ba ya ce
” Dakata! Me ke tsakaninku kai da Matata Luba?”
Ya fara ma sa rantse rantse ya ce
” Ka fada min gaskiya kawai domin ka san tukwicin da nake yiwa wanda ya min karya akan laifin da ya min! Abunda aka aiko min a tsakaninku gaskiya ne ko karya?”
Ba wata kwana kwana Bilya ya ba shi amsa da ” Gaskiya ne” don ya san karyar ma ta banza ce. Dole sai ya gane, yana gano karya ya masa kashinsa ya bushe. A lokacin ya fara tunanin harhada kayansa ya bar kasar. Idonsa idan Hamza Dala ya san ba zai kai labari ba.
Wani abu ya caki zuciyar Alhaji Hamza. Ya sha kwana da matan mutane, ya sha yin yawon ta zubar din da matan aure masu ‘ya’ya. Amma bai taba zaton haka ake ji ba. Dama haka suke ji? Kaninsa uwa daya uba daya!15
Lallai za a sha artabu! Kawai sai ya ji wata kwalla ta tarar masa a ido. Ya bude baki ya ce
” To ka shirya domin kuwa kana dauke da cutar kanjamau”
Yana jiyo kurma ihun da Bilya ke yi ya datse wayar. Za su sha mamakinsa, sun manta ko shi waye! Ba a taba shi a kare kalau!
Daga dayan bangaren Almustapha ke zira wayarsa a aljihunsa. Fuskarsa babu annuri kwata kwata. Ya ce
” Wasu mutanen ba su san lokaci yayi ba. Wasu ba su san ya kamata su tsaya haka ba. Dole sai an tsayar da su, dole sai an dakatar da su!4
Da sannu kowa zai karbi sakamakon da ya dace da shi!1
******************************
Karantina ,Jedda saudia
Shekaru da suka wuce
“Yau me zan gani ni Aisha indo! Lahaula wala kuwwata….hanak mushkilatan ( akwai matsala). Wanan jinjira ni Indo ina zan kai ta?”
Jinjirar da Luba ta bari ta kura wa ido da ta gane lallai ta gudu ta bar ta ne da gangan. Nan zargin da take yi n cewar labarin kanzan kurege suka shirya ita da munari na cewa mijinta aka kama don su karbeta karya ne kawai.
Nan da nan ta aika wani yaro ya kira ma ta munari da yake gidan ba nisa. Tana hada ‘yan komatsanta na talla ta samu kira ta bazamo a guje.
A cikin sakan talatin indo ta labarta ma ta abinda ke ciki akwai, bata yi wani dogon tunani ba ta gane da gangan kawai Luba ta gudu ta bar su da kajaga. Cikin takaici ta ce
” Wannan Luba ..wannan Luba ya salaam ta cuceni! Idan don Riyal dubu biyun da ta bani ne ai da sai na maido ma ta akan ta bar ni da wannan qajagar! Ashe shi yasa ta lallaba ni akan na nema mata wajen buya? Yau na ga ta kaina Indo ya za muyi da jinjira”
Indo ta wani ja da baya ta ce
” Ya za muyi da jinjira ko ya za ki yi da ita? Kwarankwatsa dub
u munari kin yi kadan ki shafa min kashin kaji! Wallahil azeem tun da naga matar nan idonta a soye nayi zargin karya ku ke. Amma kar a ce ka fiye siyar da halin dalilin ke nan da na sa na kulle bakina. Ai daukan jinjira ki tafi da ita ya kama ki, tun da kowa ya san ke kika kawo wannan Luba karatina. Bakinku daya. Baki barinta anan wallahi bamu ji ba bamu gani ba la zarara wala zirar (babu cuta babu cutarwa)”
STORY CONTINUES BELOW
Kawai zaro ido munari ke yi tana tsinewa kwadayinta da ya kaita janyo luba. Ta kalli indo ta ce
” Ma….dha af’a….lu? ( ya zan yi?)
A fusace indo ta ce
” La..’aarifu!” ( ban sani ba!)
Sai ma ta dauko jinjirar ta dangwara ma ta. Munari kuka take hankalinta a tashe. Ta tafi da jinjirar gidansu tana tsala kuka. Abinda ha kara rikitata kenen.
Ta samu wani guntun ruwan zam zam ta ba ta ta sha. Yarinyar na ta lashe baki. An samu tayi shiru, ta kura ma ta ido. Ta fara tunanin inda za ta je ta jefar da diyar, ko bola za ta?
Sai ta tuna cewar a cikin watannin nan an tsananta tsaro saboda tsintar jira jirai da aka dunga yi a bola a karantina. Wata da aka kamata aka tafi da ita har yau babu labarinta. Abinda ya kara tsoratata kenen.
Tayi tunanin ta tashi haikam neman Luba, amma ta san dolenta sai ta nemi fida da madarar da zata ba yarinyar.
Bayan ta siyo komai ta ba ta ta koshi, sai ta saba ta a baya ta bazama neman Luba. Layi layi lungu lungu duk inda ta san za ta iya samunta a jedda amma babu labari.
Washegari ta kuma sabar kafa ta tafi Makkah. Tana neman ita ko Hajiya yar sokoto tun da tare ta gan su amma babu saa. Ta gaji da yawonta don kan ta ta dawo gida.
Ta tsinewa Luba ya fi cikin masaki tayi Allah wadai da haduwa da ita. Yan kudadenta kaf yarinyar ta soma lashewa. Ta kan yi tallar ta ko soye soyenta ta hada wataran da yawon ta zubar ta samo yan kudadenta.
To yanzu kiri kiri yawon ma ya gagara domin ga jinjira kunshe a bayanta wa zai kula ta?
Ga yarinya sai shegen kyau, ta kura ma ka ido tana kallonka kamar tana ganin hanjin cikinka. Sak uwar sai yanayinta da ya nuna uban balarabe ne.
Yawan kukan da Munari ke yi kullum ya sa wata Hajiya Mairo a dakin ta kira ta tace da ita.
” Ke ji ni nan Munari. Ta yaro kyau ta ke bata qarko. Dama kale ki nayi in ga iya gudun ruwanki da kika fara neman uwar yarinyar nan. To idan banda abunki ya za ayi ta tsaya inda zaki same ta? To ai tunda ki ka ga diyar nan to ta gudu ta bar kasar.
Ke da Allah ya baki kyautar dan mutum sukutum! Jinjirar nan ai jari ce! Wannan kudin madarar da kike kashe ma ta har kika zubda hawaye wa billahillazi sai ki ninka shi!”
Ta mayar da numfashi saanann ta ce tana mai dauko wani yamusasshen tsumma a gefenta.
” Kin ga wannan kyallen shi za ki samu ki jika a jan zobo ya kama jikinsa sai ki kamar kafarta daya haka. Daidai agarar ki daure ta kamar ciwo. Sai ki daidaici lokacin zuwan larabawan nan masallaci ki kafa bara. Kina daga yarinyar nan kina kuka kina cewa
” dhafalee..mureeda! Dhafalee mureeda ( ‘ya ta bata da lafiya/’ya ta na ciwo)….innaha..jaa’i’a (tana jin yunwa)
Suna da tausayi, ga tsananin kyauta. Za ki ga ruwan kudin sadakar da za a baki. Ba sadakar kudi kawai ba har da ta kayan sawa da na abinci.
Idan kin so ma takanas za ki tafi Makkah ki je harem domin yin barar. Kudin da za ki samu ya fi kudin da kike samu toye toyen nan. Kya ce na gaya miki!”4
Wani irin farinciki ya mamaye munari ta ji kamar ta rungume Hajiya mairo. Tayi ta mamakin yaya aka yi tuntuni bata yi tunanin hakan ba? Tayi ta zuba ma ta godiya. Hajiya mairo ta gyara zama ta ce
” Yo in ban da abunki wa ke kuka yanzu ga haihuwar diya mace? Ai diya mace ita ce riba. Yanzu wannan yarinya tana dan tasawa za ki fara nunawa maza ita. Kin san larabawan garin nan mayun mata ne.
Daga baya idan ta girma sai ki fara nunawa Alhazanmu na Najeriya masu shigowa ita. Musamman kanawa! Shin kin mance da kanawa mayun fararen mata? Da sannu za ya zamo kudi ba su karanci a hannunki. Wa ya sani daga nan cikinsu ko a sami wani dan kankanbar ya ce zai aureta, sai ki tsabg ma ta sadaki tsababa ya tafi da ita ke ma kin huta. Shin kin manta yadda aka yi da diyar Hajiya Ladi da ta haifa da wannan balaraben ba. Ina nan nan wani dan Nijeriya mutumin sakkwato ya aure ta bayan ya zabgowa Ita Hajiya ladin dukiya?”
STORY CONTINUES BELOW
Gyada kai kawai munari keyi tana murmusawa. Labarin Hajiya Ladi tas ba wanda bata sani ba. Kuma a gabanta aka yi auren wannan shegiyar yarinyar suka ci suka sha.
Daga wannan magana sai ta ware abunta zuciyarta fes. Ta kalli yarinya ta rada mata suna NADIYA.
Rainon Nadiya zuwa budurci bai zo wa Munari kamar yadda take tsammani ba. Domin kuwa hatsabibiyar yarinyar ta jawo mata shiga jafa’i ya fi kudin kwabo.
Ba a rana a kare ba ta janyo fada ba, ko ta dau kayan wani. A irin wannan takaicin ne Munari ke tsine mata da uwarta tana jawo mata alkaba’i. Ba a wani dade ba Nadiya ta gane munari fa ba uwar ta ba ce. Uwarta sunanta Luba a yar Najeriya amma ba a san ubanta ba.
Nadiya ta taso yarinya ‘yar kan ta mai tsananin son abun wani. Ita dai idan ta gani a ba ta ko ta dauka. Tun ana tuhuumarta da sata munari na karyatawa har ta hakura. Ya zamana cewa ko abu aka rasa ba a cigiya sai dai a nemi Nadiya.8
Shekaru suka ja masu tsayi Munari bata yar da Nadiya ba saboda kudin da take samu da ita. Shekarunta sun ja ita, yanzu karfin nema ba irin na da ba.
Wata shekara tafiya ta kai su makkah bara kwatsam sai Munari ta yi kacibis da Hajiya ‘yar sakkwato. Ta tsufa ta yankwane sai wata shirgegiyar kafarta ta hagu da tayi biyun kanta a tsammanin Munari ciwon daji ne. Lalacewar Hajiya yar sakkwato ya matukar ba ta mamaki domin yanayin da ta gan ta sai wanda ya yi mata kyakkyawan sani zai gane ta.
Bata gane.munari ba sai da ga ma ta bayani. Ta kama baki ta ce
” shin munari dama kina garin ga ba ko leke? Shekaru kusan 17 kenen rabonda na sako ki cikin idaniyata. Ai da dadewa na koma wani kauyen Taif. Wannan ciwon nawa ai bai hi shekara biyu ba amma kin ga dai yadda ni kkoma”
Munari ta ce
” To Hajiya ki koma gida najeriya mana. Watakilla a samu mai jinyar ki tunda da yan kudinki. Yaranki ai ba za su bar ki haka ba babu kulawa”
Ta kama haba ta ce
” wani yara kin ka nuhi? Yaran da ni wwatsar da su sa’ilin da sunke bukata ta? Ban ko bi ta kan su ba. Babban cikinsu babu irin rokana da bai yi ba kan ni ddawo ni zzauna gida dogon daji ni kkiya. Sai yanzu? Bani komawa makiya su min dariya”
Sai a lokacin ta lura da yarinyar da ke tare da munari tana ta wani yatsina ta ce
” Munari har diya ki ka haihwa ban sani ba? Assha lallai lokaci shi jja. Ga ta har ta tasamma zama budurwa!”
Munari ta kama baki ta ce
” Ni?!Ai ban ajje ko kwan zakara ba! Wannan diya ai ta Luba ce. Daga taimako ta gudu ta bar ta. Shi ne na dauke ta kafin mu ga abunda Allah zai yi”
Hajiya tayi salati ta sanar da ubangiji ta ce
” Haba! Ko da na ji! Ga idanuwan nan na ta a soye irin na uwar. Awo wallah sai yanzu nigga kamanni da gyatumar! Oh yarinya ba kiyi sa’ar uwa ba, Luba kwai tsinaniya! Yarinya kamar renon tinkiya ba kai ba kawhahuwa. Ai ita wannan diyar babu yadda ba a yi ba a zub da cikinta abu shi ggagara. Ashe ashe sai ta diro kasar ga! Wannan ma aya ta! Alkawarin Allah ba shi tashi! Uhm uhum”6
Wata irin harara Nadiya ta galla mata jin ana antayawa uwarta zagi. Ba wai wani haushi can can ta ji ba kawai tsabar fitsara ce. Domin ita ma tana so Allah ya hada ta da uwar nan ta ta wataran ta ga tijara. Ba ita ga haifa
ta jefar ba? A kanta za a daina jefar da ‘ya’yan titi”
Caraf Hajiya yar sakkwato ta gan ta tace
“Au! Au! Wa billahillazi diyarta ce! Yarinya kin sha a ruwan mahaifa. Gado ba karambani ba. Na kara da uwarki ma ta bar ni don buhun ubanki!”17
Munari ce ta shiga zancen jiki na rawa ta ce
” To Hajiya kin san ubanta?”
Hajiyar ta girgiza kai
STORY CONTINUES BELOW
Ta ce “ko daya wallahi!”
Munari ta ce
” To amma ai ke kika dauko Luba daga kano za ki iya sanin gidansu”
Tayi jim can ta ce
” Ai ita uwar Lubar Tamadi tare munka yanmatanci. Wancan karun dai gidansu ga birget shi ke layin ‘yan mana. Uban shi anka kira baban yara. Yanzun kuma shekaru sun ja babu tabbas luba ta koma Najeriya. Sa’annan kin san halin rayuwa ta yiwu sun tashi ma. Au..au..na tuna ina sun ka koma in sun tashi? Uban na fama da bakin talauci baya da komi sai annakiyar daudar da ta mamaye masa hula!”5
Munari tayi shiru, tana so a ce ko yaya ne ta san inda luba ko dangi ta suke saboda halin rayuwa. Ita ma tana zama a kano da watan wataran ta neme ta. To ga shi an ce ba tabbas tana Najeriya.
Jiki a sanyaye suka yi sallama.
Ba ayi wata shida da hakan ba tsautsayi ya ritsa da munari da Nadiya aka kama su aka watso su Najeriya a garin kano. Ba su tsira da komai ba sai lalitarsu da ke qugunsu.2
Anan wani gidan yanuwan munari suke zaune zaman maleji. Dan kudin da suka zo da shi sun kusan cinyewa ga gidan rayuwar ta kai ta kai ake. Tana ta yi musu fafutuka su koma saudiyya babu isasshen kudi. Wani abu ya fadowa munari
Me zai hana ta nemi ko gidansu Luba ne ta yar da kwallon mangwaro ta huta da kuda? Iya moriya ta mori Nadiya, ta ga alamar tana neman zame mata kaya. Ko babu Luba sai ta yasarwa uwarta ko ta samu sa’ida.
Sai dai me?
Ba a yi kwana 2 da wannan tunani na ta ba wani yaro saurayi a gidan Kamalu ya shigo da fastoci yana mannawa na jamiyyarsu uwarsa na zabaga balai kamar zata ari baki wai ya lalata musu bangon gida.
Fasta guda daya ce ta dauki hankalinta ta girgiza ta.
Duk da akwai canje canjen lokaci na shekaru masu tsayi. Ko luba shekara nawa zata yi ba zata kasa gane ta ba, ga kuma sunanta baro baro a jiki. Sai ta ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha.
Ba shiri ta kwashe labari ta zayyanawa kamalu da Nadiya.
Ba shiri Nadiya ta sungumi fasta tana tika dariya. Ashe ma uwar tata da ake zagi hamshakiyar maikudi ce, ta je can tana rayuwa a wahala. Dole ta rabe ta ta samu abunda zata dangwala.
Kamalu wani tambadadden yaro ne marar mafadi. Tunda suka zo ya fara jin son Nadiyar sai ya ji wasai a ransa. Ashe ma yarinyar zata iya masa silar kudi. Ya dube su yace
” Faduwa ta zo daidai da zama. Kun ga wannan matar wallahi kudi gareta kamar su kasheta. Ko ni nan sai na samu mota idan ta so ta dalilin Nadiya balle ita kan ta Nadiyar.
Amma fa kun san yan siyasa suna da matsala. Idan dai ba ka yi musu jan ido ba ba sa russuna. Yanzu haka ba lallai ta yarda da ke ba saboda gudun mutuncinta.
Abinda za a yi shi ne, mu je na raka ki gidanta ki gaya mata. Idan ta amince shi kenen, na san zata bada toshiyar baki ki rufe zancen. Idan ta ki daga nan gidan radiyo za mu wuce. Ki fara bada labarinki . In ta kama ma sai a je har da gwaggo munari tunda ita ce shaida ita ma ta bada na ta labarin. Ki nuna irin wahalar da kika sha ba uwa ba uba.
Idan aka fara yadawa ko sau daya ne ta ji to hankalinta zai tashi. Maza maza zata hana yadawar ta neme ki ido rufe don ta baki tosshiyar baki. Kin ga ko bata karbe ki ba ai kin tsira da wani abun.
Dalilin da ya sa nake ba ki wannan shawarwarin shi ne matar nan fa tero ce. Wallahi idan ba ki ma ta jan ido ba, kin ma ta fito na fito ba za ki mori komai ba!
Kin ga idan ta sallame ki daga baya za a iya korar zancen a ce sharrin ‘yan adawa ne. Ina fatan kun gane?”
Suka gyada kai ran su fes. Kuma sun gane din. Nadiya doki ta ke, ba don ta ga uwarta ba sai don ta samu abunda zata samu. Suna samu ma saudiyya zasu koma inda suka fi wayo. Ba ta jin kaunar uwar ko dis a ranta bata jin ma zata iya son kowa a duniya.1
STORY CONTINUES BELOW
Kamalu ya ce
“Don haka kawai gobe ki shirya na san har gidanta. Idan ba ta gida na san duk inda muke taron siyasa ba ta wuce nan sai muje. Duk yadda ta karbeki mu ma muna da hanyar bullo ma ta.”
A haka aka kwana
********************************
Kallon galala Luba ke bin yarinyar da ta kira kan ta da Nadiya. Kanta ya daure gabanta yana fat fat.
A kallon farko ta gane ko karya ne tabbas wannan yarinyar sun hada jini to amma daga ina? To ko dai diyarsu hafsy ce yayarta?1
To amma ta ce karantina, ke nan diyar da ta bari ce yar Abu maaruf?
Ya aka yi ta san ita ce uwarta ya kuma aka yi ta san inda take. Shekaru aru aru ya aka yi ta nemo ta?
Tambayoyi ne fal ranta amma bata furta ba. Ta tsuke fuskarta tamau ta nuna yarinyar da dan yatsa ta ce
” ke ban son sakarci! Diyar wacece ke? Za ki zo ki tsaya gabana kina batun banza! Yanzun nan na sa a daure ki! Ku mutanen gari da kun ga mutum ya fito siyasa shikenen kun samu sharri kala kala da za ku laqa masa.”
Babu abunda ke ran luba sai tunanin makomar siyasarta. Yaushe za ta bari karamar yarinya irin haka ta bata ma ta suna.
Ta dai gane diyarta ce, a ranta ta raya cewar bayan zabe za ta neme ta ko a sirri ne. Amma yanzu ba zai yiwu ba.2
Wani irin abu ne ya doki kirjin Nadiya. Duk yadda ake bada mugun labarin uwarta ashe ta wuce nan? Allah ya ba ta abun duniya ta ja ta jiki ta dan san ma ta ma ya gagara? Ashe muguntarta ta kai haka?
Ji yadda ta nuna bata santa ba , bayan an ce suna muguwar kama. Ta ce
” Umee, kowa ya san ni diyarki ce. Ammi ma da ta rikeni ta ga hotonki ta ce ke ce ummi na! Anta amee (ke uwata ce)!
” ana last ‘umuk…. ana last ‘umuk” ( ni ba uwarki ba ce)
Abunda Luba ke maimaitawa kenen tana girgiza ma ta kai. Ta dora da cewar
” Ki zo ki fice daga gurin nan kafin na sa a fitar min da ke! Ant..majnuun (ke mahaukaciya ce)
Wani irin kallo Nadiya ke ma ta. Ta ce
” Kin yar da ni ba ki taba tuntubar abincin da na ci ba balle ruwan da na sha balle suturar da na sa. Yau Allah ya hada mu shi ne za ki guje ni ko?”
Sakaka Luba tayi gabanta na fat fat. Sai ta ji kamar tana tsoron yarinyar, zuciyarta na neman karyewa. To amma kujerarta take dubawa. Ta danne ta ce
” Masharranta kawai! Za ki fice ko na zo na saka a fitar da ke?”
Wani irin kallon murmushi Nadiya ta ma ta ta juya. Tana ji a zucuyarta babu wacce ta tsana irin wacce ake kira da uwarta.
Fitarta ta gamu da Kalamu har da guntun hawayenta na. Ta ga samu ta ga rashi. Ta labarta ma sa yadda suka yi ya ce
” Ahaf! Wai bana gaya miki ba? Ai na gaya miki ita uwartaki karfe ce sai da wuta. Akwai wani abokina ma’aikacin gidan radio ne. Yana daukan wani shiri “siyasa a yau”. Wajensa za mu je ki fadi labarinki ya nada. Rana irinta gobe yake watsa shirin, kawai sai ya saki labarin.6
Akwai wani abokina da yake ma ta aiki sosai akan siyasar nan shi za mu sa ya kira ta ya gaya mata ta saurari abinda ake yi a radion a lokacin. Tana ji za ta bazama nemanki domin kar a kara watsa labarin.
Daga nan sai ki yanko kudi ki gaya ma ta, ki ce ma ta ifan ta kama ma za ki je ki karyata zancen. Ina shikenen. Ke dai ba ga kudinki a mararki ba?
STORY CONTINUES BELOW
Ki sallame ni ki sallami gwaggo munari. Amma fa ba zaki koma saudiyya ba aure za muyi.”
Dariya ta sakar ma sa ta rainin hankali amma bata bari ya gane ba ta ce
” Ta ce sosai! Ai na ga wajen zama me zan koma saudiyya na yi? Ai ni bani da abun ce maka. Ka nuna min kauna!”3
Washe baki ya dunga yi yana mamakin yadda ya tsinci dami a kala. Tsaleliyar yarinya irin haka rana tsaka? Nan da sati biyu zai hura mata wuta a daura aurensu suke cin dukiyarsu a hankali. Ba zai yi sake Alhazawan kano su kyalla ido su gan ta ba, yanzu labari zai sauya.2
Ita kuma can cikin zuciyar Nadiya sakarci ta ke gani irin na Kamalu. Ya za a yi kamar ita matar manya ta kare da dan bangar siyasa irin kamalu? Me na sama ya ci ballantana ya ba na kasa?5
Amfani take da shi kawai ta samu ta warci wani abu wajen Luba, ai sai da dan gari a kan ci gari. Shi yasa take bin sa a sannu.4
Tana jin kudadenta kwashe su za ta yi kaf ta calle saudiyya!
Amma kafin nan sai ta zame ma Luba saniyar tatsa. Barazana za ta dunga yi ma ta tana karbar kudi akai akai. Da ita ake zancen!
Daga nan gidan radion suka wuce. Mai watsa shirin Sani jimeta murna kamar ta kashe shi samun wannan daddadan labarin da zai kawo masa kaurin suna.
Suka yi duk abinda ya dace. Ya gaya musu gobe da yamma za a watsa. Sannan zai bar namba da za a tuntubi yarinyar.
Wannan kenen.
Shigar Luba mota bayan rabuwarta da Nadiya ta ji kirjinta na fat fat. Wani irin tsoro ya fara shigarta. Wai wannan diyar da ya yasar a karantina ita ce ta biyo ta yau? To ya aka yi ta san ita ce uwarta?
A tsammaninta ta mutu tuntuni, to wa ya raine ta har ta rayu?1
Jikinta ya fara yin laasar da ta tuna kamannin fuskar yarinyar kamar na ta. Tsarin jikinta kuwa tamkar na Abu Maaruf!
Ta kudurce a ranta cewar idan ta hau kujerarta za ta aika yarinyar ta zo, ko dan wani abu ne ta ba ta. Amma sai tayi mata alkwarin fita daga rayuwarta. Don ko gaba tana son yin takarar sanata bata so sunanta ya baci. Ba son komai ba sai da makiyanta, suna ji ana cewa tana da shege za a dauko wani sharrin a laqa ma ta. Waau ma su ce tayi yunkurin kasheta Allah ya cece ta. Da wannan tunanin ta wuce gida.1
Ko a ranar mijinta Alhaji Hamza Dala bai dawo gida ba , bata yi mamaki ba don ba kullum yake kwana gidan ba saboda alamuran siyasa. Babu irin kiran da bata yiwa Bilya ba amma wayarsa a kashe, mawuyaci ne yayi hakan.
Washegari ta tashi ta fesa wanka da kwalliya. Bata damu da bata ji da maigidan ba domin kuwa ba a gabanta yake ba. Ta gama shiri tsaf zata fice sai ka kiran ‘Dan gujungu” yaronta. Ta san dole wani cigaban aka samu tayi sauri ta dauka
” Ran ki ya dade…ma..za maza ki bude gidan Radion haske shirin nan na siyasa a yau! Akwai wani mugun labari akan ki! Ya kamata ki tari abun!”
Cikin rawar jiki ta yi amfani da wayarta ta kunna. Wasu irin maganganu ne suka dira a kunneta
” Kamar yadda na ce da ku sunana Nadiya. Ni diya ce ga Lubabatu Hamza Mai Dala. An haifeni ne ba tare da Uba ba. Uwa ta Lubabatu ita ta haifeni a saudiyya a garin Jedda wata unguwa mai suna Karantina.
Wadanda suka tsince ni sun ce sun tsinceni ne a bola ko cibiya ba a yanke min ba. Bana rayuwar komai sai bara. Kamo ni aka yi aka jeho ni kano. Shi ne nake neman mahaifiyata ganin kowa ya san ta da ta taimakawa rayuwata ta yi min gata. Ga wanda yake tantamar labari na zai iya kaimu gwajin jini ni da ita. Ko kuma…..”3
Wani irin kara Luba ke yi ta wurgar da wayar gumi na tsattsafo ma ta!
Menene haka?
Dama abunda yarinyar nan ta so yi mata kenen? Ita za a ci wa mutunci da zancen banza a bata ma ta siyasa? Da sake!
STORY CONTINUES BELOW
Kira dan gujungu ne ya shigo. Ta dauka jikinta na bari. Ya ce
” Hajiya kin ji ko? Idan kin tabbata sharrin yan siyasa ne to zamu dauki mummunan mataki. Idan kuma har kin san da gaske take to kawai ki bata ‘yan kwabbai ki sallame ta mu samu tarzomar nan ta kwanta. Allah ba shi idan abu ya lafa ko batar da ita ne sai a yi. Amma a halin yanzu mutane dayawa sun saka mana ido, bana so muyi abunda zai taba siyasarki. Sannan mu tabbatar shi kan sa gidan radion mun siye shi an daina watsa labarin. Za mu iya cewa sharrin makiya ne”
Ta amince da zancensa ta kuma sa shi ya je gidan radion ya tuntubi nambar yarinyar. Ya tura kudin da ya kamata ya tura musu. Ta bar komai a hannunsa. Ita za ta ji da abunda ke damunta.
Abinda Nadiya tayi yayi matukar bata wa Luba rai, amma bari ta ci zabe za ta samu lokacinta. A yanzu Zunzurutun kudi har naira miliyan goma tace a tura mata. Ta san dan gujungu ba wasa zai kula da komai kamar yadda aka saba.
Washegarin rana aka tura wa Nadiya makudan kudaden rufe baki. Kamalu ne ya nemo wani account aka tura. Murna a wannan gida ba magana!
Daga nan Nadiya ta fara tunanin yadda za ta koma saudiyya da dukiyarta.
Watarana za ta yiwa Najeriya dirar bazata. Za ta zo da zummar fito na fito da Luba!
Sai dai me?
Tunaninnikanmu suna tafiya ne da burirrikanmu.
Kana taka, Allah na tasa!3
*****************************
Alhaji Hamza Mai Dala ne tsaye yana muzurai. Illahirin fuskarsa babu abunda take nunawa sai tsananin bacin rai da bakin ciki.
Tsawon kwana biyun da yayi bai dawo gida ba na tsantsar bakin ciki ne. Ya je an yi masa gwaje gwaje an kuma ga yana dauke da cutar kanjamau.
Watsa ma ta hotuna yayi gabanta cikin karaji ya ce
” Wacece wannan?”
Wani irin murdawa ciki Luba yayi cikin tashin hankali. A duk al’amuranta na duniya ta kan yi su ne cikin sirri. Shige da ficenta da Alhaji Bilya gani take wani abu ne na sirri.
Ta mugun tsorata, amma da yake ‘yar kanta ce sai ta wayince ta ce
” Au au, irin sharrin da aka saba yiwa mutane na hada hotuna shi ne aka dawo da shi kaina? Lallai na yarda babu abunda siyasa ba ta jawowa!”
Sai ta kwashe da dariya.
Bai yi wata wata ba ya kifa mata mari biyu!2
Shako ta yayi ya manna ta a bango tana kakari ya ce
” Ni za ki maida sakarai? Ashe cin amanata ku ke ke da Bilya? Ke yanzu ko da kudi aka baki aka ce ki ci amanata sai kiyi? Kin manta ko ni wanene? Bana baki tsoro? Yanzun ina kwarton naki? Shin ba kiyi mamakin ko wayarsa ba kya samu ba?”
Wani irin kakari take na mutuwa, ya sake ta ta fado him!
Ta matukar galabaita don ko numfashi sama sama take. Tana so ta ce masa karya ake ma ta amma ta kasa.
Ya warware mata takardar hannunsa ya kawo mata fuskarta ya ce
” Kin sa kina da kanjamau ashe kika aureni ki ke kuma nema da kanina? Ni za ki shafawa kashin kaji Luba saboda ke tsinanniya ce!”
Wannan karin kuma kuka yake yana tuna barin duniya da tikitin zuwa lahira da Luba ta saya musu duka.
Kuka yake kashirban!
” kar..ya ake min…Al..haji…karya ne!”
Abunda kawai take kokarin fada masa kenen. Kalaman da suka kara fusata shi kenen. Bai yi wata wata ba yayi bal da ita, bal din da ta san dole ya karya mata wani sassan jikinta.
STORY CONTINUES BELOW
Tana so ta gudu ta kasa, mirgina kawai take ta iso har bakin bene.
Bai yi wata wata ba ya daddage ya haureta a ciki ta wuntsula!
Tun daga farkon benen sai da ta kai kasa. Ta kwalla wani mugun kara, sai tsit.9
******************************
Shesshekar kuka ita ta tada Luba daga mahaukacin ciwon da likita ya sa ta barcin dole.
Iya tamadi ce akanta take wannan kuk
an, sai kafarta da ke rataye irin ta masu karaya. Duk jinkinta tabon duka ne na Alhaji Hamza. Bato so ta tuna irin azabar da ya gana mata, amma da ita yake zancen.
Ta dago luhu luhun idonta tana kallon iyannan da take zaton kukan jimami take ma ta. Ta ce
” Iyannan kiyi hakuri mana ai zan samu sauki”
Wata irin muguwar harara ta doko mata tana mai dakatar da zubar hawayenta. Kawai sai ta dauki hannunta na dama ta danqarawa Luba dakuwa ta ce
” Ubanki! Ka ji min yar buhun butar shayi! Ni za ki cewa nayi shiru bayan irin masifa da balain da kika jefa ni a ciki! Zaman gidan da nake ma ya gagare ni saboda tashin hankali!2
Ubanki kuwa duk inda ya bi jifansa ake! Jiya kuwa da aka yi rashin saa aka saita idonsa sai da ruwan idon ya tsiyaye kaf! Aka yi masa mutuwar zaune. Duk don saboda ke annamimiya! Da haihuwarki Luba gwara barin ki”6
Ta sake barkewa da kuka.
Kallon galala Luba ke mata, ta san bai wuce Alhaji Hamza ya yada ta cewar tana kwartanci ba. To shi ne Iyannan zata kare mata tanadi? Don an gan ta ta nakasa ko? To wai ina ruwan wani da rayuwarta?
Ta dago a hankali ta ce
” Wai iyannan don Alhaji ya yayata labaran karya akaina shi ne kuka hau kuka zauna? Shi ne har ki ka tasamma tsine min? Da me kuke so na ji wai?”
“Da ubanki za ki ji!” Iyannan ta fada a fusace! ” Daga haihuwarki nayi kuka ya fi cikin masaki! Ni ce gorin kishiya ni ce ta yan unguwa ni ce ta ubanki duk dan na dadada miki ashe ni gari na za ki zubawa ruwa! Da a ce labarin da Alhaji yake yayatawa a gidan radio akan ki na kwartanci da kaninsa ne kadai labari to ai da da sauki! Luba kin cuceni.” Kukan dai take4
Wani irin bakin ciki ya ziyarce ta. Wato Alhaji yayatata ya ke yi don hassada da son bata mata siyasa? Shikenen ya jaza ma ta mutane ba zasu zabe ta ba!
Wato ita iyannan za ta sa a gaba ta ci fuskarta don ta gan ta a kwance. Alhalin duk abunda ta samu duniya da ita ake lasa. Da kyau!
Ta ce
” Iyannan ki fa daina jifa na da alkaba’i, na menene wannan jinini haka!? Ki bar ni in ji da ciwon jikina ni da Alhaji muyi fito na fito. Daga nan za a gane me gaskia. Da zaki ce da haihuwata gwara bari, amfani nawa haihuwar tawa ta miki?”1
Ai iyannan ba ta yi wata wata ba ta tsinka luba da mari ji ka ke kau! Wani abu da bai taba faruwa ba a tarihi. Luba ta rike kuncinta cikin tsananin mamaki. Iyannan ta ce3
” Za ki gane marin nan na menene. Gaban kofar dakin nan yansanda ne, yau kwanansu uku suna gadi. An fara wata sharia ta kisan wata, kuma wanda yayi kisan ya ce ke kika biya shi yayi! Alkali yace ya kawo masa ke! Don haka yanzu a karkashin matakan tsaro kike!!!”
Wani irin abu ne ya daki zuciyar Luba ba da wasa ba..wato abunda ta binne an tono kenen. Da sake! Ta dubi iyannan ta kwashe da dariya irinta yan kwaya. Iyannan ta tsira mata ido a tsorace. Luba ta ce
” Sai yanzu ne iyannan kike da na sani? To laifin waye? Tun da na taso ke da baban yara akwai wanda ya taba taimaka min? Ya za ayi na taso bazan nemi taimakawa kaina ba?4
STORY CONTINUES BELOW
Kan ku kawai kuka sani ba ku famu da ‘ya’yan da kuka haifa ba. Lokacin da nake samun kudina nake kawo muku mai yasa ba ku tambayeni inada nake samu ba? Mai yasa da na ba ku kuka karba?
Ku iyayena ku ne baku min adalci ba don haka duk abinda na zama a duniya ku ne! Na nutsa cikin alamuran duniyar da bazan koma baya ba! Ba gudu ba ja da baya!”
Wani irin kuka iyannan ke yi ta durkushe a haka. A tunaninta gata take wa luba autarta, shalelenta. Bata taba tunanin zata juye haka ba. Ashe hakane, idan ka so dan ka duniya kin sa za tayi? Ashe a kwabi yaro ba kiyayya ba ne? Ashe gyara kayanka ba laifi ba ne? Ga dukiya nan a wajen diyarta sai dai babu kwanciyar hankali. Wannan wani irin balai ne?”
A lokacin Luba ta fara tunanin mafita. Tana zuwa kotu ta san an daureta an gama. Ya za a yi ta kubuta daga shariar nan? Ba za ta je shariar nan ba, dole ta san yadda za ta yi!1
Ba zata zauna a kurkuku yanzu ba, dadin duniya bai isheta ba tukunna. Da saura, labarinta bai zo karshe ba.13
Tunani daya ne a ranta, dole ta bar kasar. To amma ta yaya?
Washegari akwai shiga kotu haka aka dauke ta aka ciccibeta aka kai.
Duk wasu abubuwa da aka tuhumeta da musawa tayi. Alkali yace a cigaba da tsareta a asibiti saboda ciwonta kafin shariar gaba.
An fito da ita tayi ido hudu da Almustapha. Daga nan ta gano bakin zaren.
Fuskarsa babu alamar farinciki ko bakin ciki ya ce
” Shin ban gaya miki ki tsammaci zuwana ba ko da sama da shekara dari biyu ne masu zuwa? Ba nayi don zalunci ba ne, nayi don ki gane ba ki yi daidai ba. Alkawarin Allah baya tashi, yau Rukky matata ce. Dalili saboda mun bi Allah mun tuba. Shin ke menene makomarki? Kin yi tunanin ki tuba ko azabar Allah zata ragu akan ki? Shin kin yi?5
Da wannan ya zame ya bar ta wajen. Wani kululu ne ya tsaya mata a makogoro. Wato duka rayuwarta ahannun Almustapha take ashe, bibiyarta yake. Tabbas shi ya san yadda yayi ya fasa ma ta sirri a wajen Alhaji. Ga shi sai da ya sa yadda ya tono wannan case. To ya sani ko me za a yi ba za tayi zaman gidan kaso ba!
Tunaninta guda daya ce , ya san yadda za tayi ta fice daga kasar. A neme ta a rasa.
Alamarin farko data fara yi shi ne hada baki da daya daga cikin masu tsaronta. Tashin farko ya bata aron waya.
IG of police gabadaya ta kira, mutumin ta ne ba tun yau ba. Ta labarta masa abinda take so. Ya ce yi mata visa zuwa wata kasa a yanzu da aka saka ido akanta da matukar wuya. Abu daya shi ne a dauketa a mota a kai ta Niger. Daga nan sai ai mata fasfo na Niger ta fita kasar Amurka ko ingila abunta ta ba tare da an gane ba.
A yanzu case din ta yana idon duniya gabadaya, don haka ayi magudi a kori case din zai jawo hankalin jamaa gabadaya.
Zai aiko da takardar bogi da zata nuna hukuma ta ce a mata transfer zuwa wani asibitin. Da motar yansanda za a zo kamar gaske. Daga nan inda suka dauketa zai sa su wuce da ita kawai. Duk inda aka gansu ba mai tsaida su. Idan sun kai ta Niger daga nan zai karbi aikin.
A ranar Luba tayi wani irin kwanan farinciki da annashuwa. Ranta kal! Ita dama ta san ta fi gaban a kama ta ai mata hukunci. Ta kubuta ta gama kawai.2
Hakan kuwa ce ta kasance. Dansanda da ke tuka katuwar hilux ta yansanda shi ke sharara gudu yana mata kuri. Cewar duk wanda ya san IG ai ya gama. Wani ma da aka kama shi da laifin kisa kiri kiri sai da IG ya sa aka kubutar da shi balle ita.
Wani farinciki ke mamaye zuciyarta tana jinjinawa kanta akan dubarunta. Da kuma hikima irinta ta IG of police.
Idan ta je Niger din ma ko tsaya jinyar kafarta ma ba zata yi ba. Cewa za tayi a buga mata biza ta mararsa lafiya, daga nan idan ta cale sai an gan ta.1
Sun zo wata mararraba kenen direban motar na sharara gudu bai ankara ba wata motar tirela ta shanu ta taho a guje.
Duk yanda ya so ya ci burki abun gagara yayi . Ya taka wani birki kiiiiiiiiiiiiiiit!
Amma hakanbai hana tirelar yiwowa ta kan su gadan gadan ba. Luba ta ga lokacin da tirelar shanun ta yiwo kan su wani irin abu ta ji ya daki kirjinta ganin mutuwa a zahiri.
Ciki yayi da su inda motar ta wuntsula sama ta dawo ta daki kan titi sai da ta juya sau uku sannan ta fadi ta kama da wuta. Wata irin wuta mai ban mamaki!
A cikin wani irin tashin hankali Luba ke ihu ganin dukka yansanda sun mutu jini ke malala daga kan su. Wuta ke cin ta ba da wasa ba, ta san mutuwa za tayi.
Ai ta zata ta kubuta!
Ashe da gaske shi Allahn nan ba za a iya kubuta daga shi ba?3
Ashe shi ba a guje ma sa?
To idan da ta san haka ne ai da ta tuba!4
Kamar tana jin wani matsanancin ciwo…
Kamar mutuwa fa za tayi,
Kamar karshenta ya zo.
Yanzu ya za tayi da dukiyar da ta tara?
Ya za tayi da mukamin da take nema?
Shikenen za ta bar duniya bata cika burrikanta ba?6
Wannan tafiya tana da rikitarwa, Tafiyar tana da rashin alkawari!
Karshen Alewa kasa!
Haske maganin duhu. Haske ya bayyana, duhu ya yaye.+
( last chapter)
Kano, Nigeria
Shekaru dayawa sun ja dauke da abubuwa daban daban.
Tsaye suke a gaban sasshen SS wali na Asibitin AKTH inda ya danganci kula da masu cuta mai karya garkuwar jiki.
Abba ne da mahaifiyarsa Hindatu, hannusa rike da ledar magunguna. Shi ne ya kawo ta kamar yadda ya saba, suka doshi wata jaramar mota kirar starlet. Fuskarsu kadaran kadahan suka shige suka fice daga asibitin.
Abban ne ke cewa
” Ai mama, idan na samu na ajiyeki. Yanzu yanzun lodi zan yi na je Dutse na dawo kafin la’asar. Sai ki ga wasu ‘yan kwabbai sun shigo hannuna.”
Wani irin kallo Hindatu ke masa tana son yin dariya tana kunshewa. Cikin mamaki ta ce tana mai nuna masa dan yatsa
” Anya Abba! Anya kuwa nan kurkusa akwai mai son jarabar neman kudi irinka? A kofar gida ka kafa tireda, kana kanikanci, kana koyarwa a islamiyya, yanzu juma ka tsiri lodi zuwa jigawa. Dazu dazu aka kira ka wai interview din da kuka yi ka ci, an dauke ku aiki. Wannan neman kudi da me yayi kama?”5
Wata irin dariya ya kwashe da ita har da buga sitiyari ya ce
” Ka ji mama! Na san babu wani abu da ya fi ba ki haushi irin tiredar nan. Mama kin raina tiredar nan. To jiya jiyan nan da aka siyo miki zabuwa kika sashe baki da kudin tireda ne!”2
Dariya take, ta kama baki ta ce
” tiredar?!
Ya ce
” Ahaf mama! Ai ku ne kuka raina sanaa. Mutane sun fi so su jira aikin gwamnati to ina aikin gwamnati yake? Yanzu wannan tiredar da kudin bautar kasata na kafata. Da a ce mutane za su dauki hanyar rashin dogaro ga aikin gwamnati su kafa kan su da kansu ba tare da sun sa girman kai ba, to da an yaki talauci. Yanzu da kudin wannan tiredar sai ki ga an dallo miki suruka!”6
Ware hannayenta tayi guda biyu ta masa dakuwa ta na cewa
” uwaka! Ka ga marar kunya, ni kake wa maganar suruka. Ka mai da ni kakar ka ko”
Suka kwashe da dariya
Ran Hindatu wani farin ciki ne jin ya ambaci aure. Tana fatan ta ga auren Abbanta. Ko za ta kai?
Ya ce
” Ba ga shi ba yanzu aikin ya samu daga Allah. Kafin ya samu fa ai da sai mu zauna mu nade hannu muyi maula? Allah ya ce tashi in taimake ka. Babu maraya sai rago mama!”2
Shiru tayi tana nutsar da maganganun Abba. Ya lura zata fada tunani ya ce
” Ehem..ehem”
Ta ce” ya dai?”
Ya fara shafa keyarsa yana cewa
” Yau ma fa na ga mutumin naki a kofar gida kafin mu taho. Allah Mama yana wahala”
Take annurin fuskarta ya gushe, ta san maganar mahaifinsa yake. Mutumin da ba shi da wajen ziyara sai kofar gidansu idan ya bushi iska, duk wai don ta yafe masa.
Ya lura da daurewar fuskarta ya ce
“Mamah…”
Ta dakatar da shi da sauri idanunta fal kwalla
” Abdulhakeem!….ka da ka ce Allah ya ce na yafewa mahaifinka! Dan Allah kar ka ce!”
Ya ga yadda hankalinta yake neman tashi ya dafa kafadarta ya ce
” To shikenen. Ka da ki damu. Yafiya abun so ce amma ba tilas ba ce. Allah ya ce ayi koyi da hakan amma ba dole ba ne. Ita wata aba ce da kan zo daga zuciya. Idan har bata zo miki zuciya ba sai a hakura.”
STORY CONTINUES BELOW
Motar tayi shiru, a lokacin ya zo wani shatalele. Ya kalle ta fuska a sake yace
” Ai kuwa kamar kin dan dade ba ki je kofar wambai ba, ya kamata ki dan yini acan yau ku sha hira. Alabashi idan na dawo daga dutse sai na biyo na dauke ki.”
Bai jira amsarta ba ya karya kwana ya dau hanyar gidan kakarsa. Murmushi tayi. Abba ya dage sai ta shirya da yanuwanta. Haka ya tara su yayi musu nasiha akan zumunci. An samu abun ya dan daidaita.
“Uhum Mama”
Me ne kuma! ” ta fadi ta san abba ba zai bar zancen ubansa ba sai ya bibiyeta da waazi
” Mama kin ga ita duniya mafi yawanta jarabawa ce. Shin za ki iya tuna tarin laifukan da kike ganin kin yiwa Allah? Amma kika iya ki roke shi gafara? Shin ya kai tarin laifin da babana ya miki?
Mama da a ce mu fa mutanen duniya mun san irin abunda za mu fuskanta ranar gobe kiyama da mun daina wahal da kanmu akan duniya ba.
Shin kin san suratul “zalzalah” da Allah yayi wa laqabi da “girgizar kasa” wato ranar karshe. Allah ya ce a ranar kasa za ta fitar da duk wani abu da ke cikinta mai kyau da marar kyau saboda shi zai umarceta tayi hakan. A ranar mu halittu za mu tarwatse mu rikice muna rokon a nuna mana ayyukanmu. Sai Allah ya ce1
Faman yaAAamal mithqala tharratinkhayran yarah
Duk wani wanda ya aikata wani abu mai kyau ( alkahairi) ko da kwayar zarra ne, to zai gan shi
Waman yaAAmal mithqala tharratinsharran yarah
Haka duk wani wanda ya aikata abu marar kyau (sharri) ko da kwayar zarra ne, to zai gan shi.
Mama so nake ki wayi gari a ranar alkhairinki ya fi duk wani sharrinki yawa!”2
Kwalla ta cika mata ido amma murmushi take. A daidai lokacin sun iso lungun gidan. Ta goge idonta ta ce
” To na ji, na yafe”
Dariya yayi ya ce
” To a ce ya zo kenen, a daura”4
Da sauri ta karo sako masa dakuwa ta ce
” Abba ka ci kaniyarka”!
Dariya yake kyalkyata ma ta ya ce
” Au ba za ki yi auren ba kenen? Ko za ki aure shin?”5
Fita tayi daga motar cikin sauri ganin Abba na neman maidata kakarsa. Irin wannan wasanni ya fi jan ta da su don sanin tana cikin damuwa game da ciwonta.
Bayan ta fita ne ta nuna masa danyatsanta alamun gargadi ta ce
” Banda gudu, ka ji na gaya maka.”
” Inshallah” ya fada.
Yayi ribas alamun zai tafi. Ya leko ta window ya ce
” Mama zancen nan fa da gaske nake. Na surukar nan”
Ta ce
” Ho dan nema! Allah ya nuna mana”!
Yana dariya ya ce
” Amin!”
Sai ta ji ranta fes! Tana mai son ganin wannan rana da za a kawo mata suruka.
Motar ya ja yana daga maga hannu, ita ma tana daga masa.
Ba ta bar wajen ba har ya kule. Ba ta gajiya da kallon gudan jininta mai tarin ilmi da hangen nesa.
Ta san tana cikin kwanciyar hankali, amma ciwonta na bata tsoro. Shekaru na ja wasa wasa cin jikinta yake.
Ta san ko ta mutu Abba zai mata addua. Abba ba zai daina roka mata rahama ba.
Shin ko za ta ga auren Abbanta?
STORY CONTINUES BELOW
Ta ce
” K’….Allah masani”
*******************************
Cape town
Tsaye yake yana daura agogo a hannunsa na hagu wani abu da ya zame masa halayya. Hankalinsa ya rabu kashi biyu.
Wasan kallon kafa yake kallo, saannan hankalinsa na matattakalar bene inda yake jiran Rokaiyatou.2
Zuciyarsa ta wani bangaren tana tunanin ko zai fara neman wata hanyar samun kudi ne? Ba wai dogara da aiki kawai ba. Ya fara shawarar kai ” spare parts” na motoci kasarmu ta najeriya.
Hakan yana da nasaba da cewar kwanan nan ya ji asusun bankinsa yayi kasa saboda hidindimu.
A halin da ake ciki ya biyawa mahaifiyarsa da Almustapha junior su kawo musu ziyara. Shi
rin da yake na zuwa tarbo su ne. Amma kuma ga shi Rokaiyatou ba ta sauko ba.
Ya gama daura agogon, saannan ya kara kallon bene, lokacin ya ga tana saukowa.
Shigar hausawa tayi na wata koriyar atamfa mai ratsin fari da aka yiwa dinkin siket da riga. Har ta karaso ta zauna bai dauke idonsa akanta ba.
” Frere yi hakuri kana ta jira na ko?”
Almustapha ya dago ya kalleta ba tare da ya bata amsar tambayarta ba ya ce
” Kin sha maganin ki”?
Har yanzu tana gwagwarmaya da cutar da ta shafi kwakwalwa. Har yanzu tana kan magunguna ne. Tana fuskantar matsaloli irin na masu lalurar, sai dai magungunan da take sha suna matukar taimakawa. Shi ya san ba lallai Rokaiyatou ta dawo daidai ba amma wanda aka samu ma an gode Allah.
Murmushi tayi tana mai jinjina damuwarsa akan harkokinta ta ce
” Na sha”
Ya ce
“Abinci fa?”
Ta ce
” Na ci”
Hannunsa ya dauko guda biyu ya ritsa kugunta daidai tunbinta. Ta zame tana dariya ta ce
” lafiyarka kuwa?”
Ya ce shi ma yana dariya
” so nake na auna ko kin ci din kin kara kiba”
Bai bari ta amsa shi ba ya ce
” wato ke a dole bahaushiya ko? Kin dauki hausar kanawa karfi da yaji kin dorawa kan ki. Hausar Niger ma yanzu kin manta”
Kama baki tayi ta ce
” Ni mmanta mi? Ya za ai mutum shi manta tushe nai! Ai niger ba ta gushemin cikin zucciya!”
Dariya suka yi. Ya ce
“Ah! Kwarai ke ‘yar gado ce. Ni ma Niger ita attushe na. Mutumin arziki ba shi manta tushe nai. Allah shi hobbaka Niger da Nijeriya gabaki daya”
Tana murmushi ta ce “Amin”
Ya ce da ita yana dube dube
” Ina Momodou ne?”
Ta daga kai a hankali ta kalli benen kana ta ce
” Bacci yake…sai nace bari lokacin tafiya yayi sai na dauko shi”
“Dauko shi” haka kawai yace da ita yana duba agogon hannunsa.
Ta tashi a hankali ta hau benen ta dauko dan jinjirin a farin shawul. Ya karbe shi yana tsaye ya fara jijjiga shi ba don yana kuka ba. Yaron da bai fi wata uku ba ya bude idonsa tar uban ya ce3
” wakie..wakue” ya juyo yana kallonta ya ce
” Allah yaron nan da ni yake kama”
Ta ce ” wannan zance ai na haddace”
STORY CONTINUES BELOW
Ya cigaba da kallonsa yana tuno irin adadin gwagwarmayar da aka sha kafin ya zo duniya.
Samun yaron da sai da yayi sanadiyyar da aka cirewa uwarsa mahaifa. Ta sha magunguna na hana daukan ciki har suka yi mata lahani. Allah ne kawai ya kadarta yaron zai zo duniya. Kallo daya yayi masa ranar farko ya san ya dace da sunansa.
” Momodou”
Kaunar yaron na shiga ransa yana kara godewa Allah.
Ya mayar da shi dan wani gado a falon.
Ya dauko wani zane yana nuna ma ta. Ya ce an kawo fa
Cikin tsananin doki ta karba. Zanen Momma ne. Wani tsohon hoton ta ne ya bayar aka yi zane da shi.
Tana ta kallon hoton kwalla ta cika mata ido. A shekaru da dama tayi kewar momma. Momma ta tafi a lokacin da ya kamata ta ji dadi. Shin ko za ta yafe mata? Ta kan ji wannan nauyin na damun kirjinta , kamar ta ci amanarta.
Ya karbi hoton ya sakala a wani bangon falon. Ya dawo yana cewa
” Mu anan gidan ba a kuka…huh..mutum daya aka yarjewa yayi kuka. His royal highness Momodou!”2
Dariya take yi sosai ta ce
” wannan dole ne ai! Kuka har da na gyara akwai shi. Ai kai ya biyo, kana yaro kai ma an ce ba dama!”
Ya zaro ido da mamaki ya ce
” waye ? Ni? Ni da ina jinjiri aka ce min damo sarkin hakuri. Ai sai na kwana na yini ba a ji kuka na ba” ya kashe idonsa guda daya
Ta ce
” Au haba? To tunda mummy yanzu zata iso sai a tambayeta labarin damon nan….”
Ya nuna mata danyatsa da sauri yana cewa
” ke..! Ke! Wallahi ki kiyayeni”
Dariya suke. Ya maida idonsa kan hoton momma ya ce
” iyayenmu, da yanuwanmu da suka riga mu gidan gaskiya Allah ya jikansu ya musu rahama ya yafe musu”
A sanyaye ta ce ” Amin”
Wannan karin agogon bango ya kalla ya ce
” Ina ga lokaci yayi, ya kamata mu tafi. Kar suyi ta jira. Da fatan kin tanadi cakulet din da aka ce miki na mutuminki”
Ta kama baki ta ce
” Ni na isa na manta? Abinda aka fi sati biyu ana jaddamin”
Ya ce ” Ah lallai kam” yana dauko jinjirin daga kwandon da aka kwantar da shi. Ya cigaba da cewa
” Ai kin gama siye yaron nan da abun duniya, baya ji da kowa sai ke”
Ta ce
” Frere kamar kana kishi”!
Ya ce
” Nahh..ni.ma ni da danuwana za muyi building team guda agaisnt you two!”
Sai kuma ta ga ya dan canja fuska ya ce
” Idan suka gama hutunsu tare zamu koma gida Najeriya. Da ni da ke za mu je gidan Baban Ali. Bai kamata a yada shi ba”
Tayi shiru kamar wutar nepa ta dauke. Tana tuno irin balain da ta shiga a wannan gida, da irin silar da ya janyo ma ta. Ya kamo hannunta ya ce
” You have to be strong, duniya ba ta ragwage ba ce”4
Ta gyada masa kai, sai kuma hawaye ya cigaba da zuba daga idonta. Babu wani abu da zata iya ce masa ya riga ya gama ma ta komai.
Dama ta hadu da shi da wuri, dama abubuwan da suka faru ba su faru ba. Ta tuno labarin da ya zo musu na mutuwar Luba, sai jikinta ya kara yin sanyi. Ya ce
“Yaya dai?..huh?
Ta ce a sanyaye
” Kana ga zan warke watarana? Kana ga zan zamo mai hankali kamar kowa ba tare da na sha magani ba?”
“Ina ga za ki rayu ki fi haka wataran Rokaiyatou!”
Ina ga wataran komai zai zamo labari,2
Ina ga wataran za ki zama malama ki bawa wadansu labarin rayuwarki,
Ina so wataran ya zamana wata ta shiryu ta dalilinki,
Watarana labarinmu zai zame wa wasu izina!
Kuka take ta rukunkume shi ta ce
” Ni baza…n zam….o ni ba idan ba..bu kai, shin baka gane haka…n ba!”
Bubbuga bayanta yayi ya ce
“Shhhiit!..shin ban gaya miki mutum daya aka yarjewa a gidan nan yayi kuka ba? Ran shi ya dade…”2
Ta zame tana dariya ta ce “ohhhhh!”
Ta sa hannu ta dauki jakarta, Ya dauki dan mukullin mota. Tana dariya ta bi shi a baya.
Tsaye suke a harabar airport din , wajen karbar wadanda suka iso. Can suka hango Mummy da Almustapha junior. Da gudu ya saki hannun kakarsa ya taho gun Rokaiyatou yana cewa
” Mammah”!
Ta rungume shi tana cewa
” Mon garcon..!”
Almustapha ne ya janye shi yana cewa
” Kai, sakar min matata”
Dariya suka ta mishi
Mummy ta ce
” Allah ya shirye ka”
Suka gaggaisa cikin annashuwa da farin ciki ana ta hayaniyar yaushe rabo. Mummy tana dungure kan momodou wai bai biyo dan ta mai sunansa a kyau ba.
Mummy ta karbi babyn suka fara fita daga harabar gurin. Almustapha yace suyi gaba ta ba shi passport din su a dauki kayansu. Rokaiyatou zata bi su ya fincikota
” ke malama waye dan dakon ki?”
Dariya tayi, hakan ta kan yi don bata fiye yawon magana ba.
Shirgin kaya mummy ta jibgo, ya san bai wuce ta yo musu kayan abincin Najeriya ba.
Kafin ya ankara ta tsinci yan kananan kayan ta dora a keken tura wa tayi gaba. Sai a lokacin ya lura manyan jakankunan ne a gabansa.
Ya dago da sauri ya ga tayi gaba tana dariya. Ya kwala mata kira yana ma ta alamu da hannu na kama kunne da shauda bulala.2
Sai ma ta tabe baki alamar oho masa
Dariya suke a yana cewa ” zan kama ki ne”
Ya loda kayan yana murmushi ya ce
” je suis amoreux”!
Ya bi ta a baya, doguwar tafiyar da ta zame musu tattaki a cikin HASKE.23
KARSHE