MAIMOON COMPLETE BY MAMAN MAAMA

 MAIMOON COMPLETE BY MAMAN MAAMA 

Shin ta ina zan fara ne, in fara ta haduwa ta da Ibrahim ne ko kuma ta haduwa ta da Sultan? Ko kuma in fara da baku tarihi na ni kaina? Sunana Maimuna

 Muhammad Dikko. An haifeni kuma na tashi garin Abuja, Nigeria. Mahaifina Alhaji Muhammad Dikko bafulatanin garin ‘yalleman ne dake jahar Jigawa. Garin ‘yalleman garin Fulani ne kyawawan gaske wadanda kuma Allah yayi musu arziki sosai har suka watsu a duk fadin Nigeria, musamman garin Lagos da port hercourt tunda yawancin arzikin su na chanjin kudi ne. Mahaifina bai bi family tradition ba saboda shi ya kasance dan boko ne. Yayi primary school dinsa a nan garin ‘yalleman tamkar sauran ‘yan uwansa amma saboda hazakarsa sai head master dinsu ya bawa mahaifinsa Alh Lawan Dikko shawarar in dai da hali gwara a tura shi kasar waje Dan ya fi samun karatu mai kyau. Da yake kakan mu mai hali ne tun a wancan lokacin, sai ya tattara makuden kudade ya dauko yaro ya tafi dashi Lagos, da taimakon ‘yan uwansu da suke can aka samar wa Muhammad biza zuwa England inda a can ne aka samar masa admission a makarantar Gifted International College inda ya fara karatunsa na secondary school.Duk bayan shekara ake basu hutun session, Muhammad yakan zo Nigeria ya ga iyayensa da ‘yanuwansa ya koma, shi kuma Alh Lawan duk sanda Muhammad zai koma sai ya hada kudade masu yawa ya bashi saboda harkar registration da kuma bukatunsa na yau da kullum. Mahaifiyar Muhammad ma Hajiya Adama ba’a barta a baya ba domin tana iya kacin kokarinta dan har shanun ta na gado take sawa a sayar mata a boye bada sanin mai gidanta ba ta tattara kudi ta bawa Muhammad. Kwanci tashi har Allah yasa ya gama sec sch dinsa kuma a take ya samu scholarship na karatu a Oxford University inda ya karanci business administration saboda burinsa na ganin ya gama karatu ya dawo gida yana taimakawa mahaifinsa a harkar kasuwancinsa. Daga lokacin ne ya gayawa mahaifansa cewa babu zancen biyan kudin makaranta kuma tunda yanzu he is on scholarship, amma duk da haka Alh Lawan yakan aika masa da kudade dan ya biya bukatunsa. A lokacin da ya gama first degree dinsa ne ya dawo gida da niyyar cika burinsa na karbar garkar business din mahaifinsa amma hakan bai samu ba saboda rigimar data barke a familyn su inda kishiyar mamansa wacce ake kira da Hajja tayi tsalle ta dire tace sam ba zata sabu ba bindiga a ruwa. A cewar ta duk wahalar da aka sha da makudan kudaden da aka kashe akan karatunsa sannan ya dawo kuma yace zai karbi dukiyar gida? Ta kara da cewa” inace cewa a kayi shi mai kwakwalwa ne ba zai yi kasuwanci ba karatu zai yi, sai da aka gama kashe kudi a karatun nasa sannan kuma zai zo yace zai yi kasuwancin to ba’a isa ba wallahi, suma sauran yaran gidan ai ‘ya’yane”. Da wannan Muhammad ya tattara ya koma England ya dora karatun masters dinsa, yana gamawa ya wuce pH D. Bayan ya gama ne kuma ya karbi aikin lecturing a makarantar. Shekarunsa biyar yana lecturing a Oxford  aka bashi award na professorship. A shekarar ne kuma mahaifansa suka dage akan lallai ya dawo Nigeria yayi settling down kaman sauran ‘yan uwansa. Saboda gogewarsa a harkar ilimin kasuwanci da mu’amala da kasashen waje yasa yana dawowa Nigeria government din wancan lokacin ta bashi mukamin ambassador. Kasar da aka fara turashi itace makociyar mu, Niger. 

DOWNLOAD HERE 👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *