MAKARANTA DUNIYA CHAPTER 13

 MAKARANTA DUNIYA CHAPTER 13

Makaranta. Duniya

               Chapter13

MAkaranTA  DUNiya

  book2
washe garin ranar  kwana hudu da yin rasuwar. daidai da kwana biyar da rufe. su Alhaji Abdul- Rasheed. La’asar sakaliya. Ladan da Malam Kasim tare da Suleman ke zaune cikin zauran gidan, dun ci-gaba da amsar gaisuwa. Magaji ya yi fakin kofar gidan dauke da Alhaji cikin motar. cikin gaggawa duk suka fito, suka tarbe shi da murna. Suka yi musabaha. Ladan na ta faman fadin. “Lale marhabin!” cikin zauran suka ja birki, duk suka zauna aka gaggaisa. “Da fatan komai ya wuce Alhaji?” lnji Ladan, Yace. “lnsha-Allahu babu sauran wata matsala”. ya amsa “Alhamdulillahi! To Allah ya kara tsarewa”. Yace “Amin,
amin. Suleman!” Yace “Sannu Baba “. Yace “Yauwa. Me ya sa baka koma makaranta ba?”


Ya yi shiru yana shafar kai. Alhaji yace “Ya kamata ace ka koma gida jiya, yau ka je makaranta abinka. Shi karatu in ya wuce mutum, ya wuce. gashi anaso ka yi jarabawa wannan
karon”. Malam Lado yace. “Ai kuwa jiyan ma ya koma ya
debo kayansa. Yace har wajen ka yaje suka hana shi ganin ka”. Yace “Ko? Lallai ba ka yi sa’a ba, amma ba su cika hanawa ba. Har da kwaso kaya ka yi shirin zaman kenan?”. Ya kada kai yana ‘yar dariya. Alhajin ya mike. Yace “Bari in shiga mu gaisa da su Gwaggo. Suleman je ka dauko jakar
kaya na suna nan a mota . Ya shige‘gida. Suleman ya tafi
dauko masa jakar.
Yana rafka sallama, duk suka yo waje har da’Gwaggo dake kwance tana fama da jiri. “Alhajl! Saukar yaushe?” Ya nufi Gwaggo ya riko ta, don kallon farko ya gane bata da lafiya. “Yanzu yanzu muka iso.
‘ Yaya dai gwaggo? Ba ki da lafiya ko?” Tace “gani nan dai”. Ya ja ‘ta’suka shige daki. saura na biya. “da ganin _ yanayin ki ba kya jin dadi gwaggo, ko Suwaiba’?” –
Tace “Damuwa ce kawai Alhaji, ina fatan an kashe’ maganar?” Ya numfasa yace “Allah ya amshi du’ar muna ta zaman jiran sakamako daga hedlkwatar mu a can lagos tare da fargabar wata kila susa a kai mu can Lagos din.
‘ Sai ga takarda jiya da yamma cewar an kammala bin cike, ni da Alhaji’Bara‘u ba’a ‘taba kamamu da laifi ba, sai wannan karan. ‘ “
Amma Mr. Bulagun ya taba amsa‘ kwairi a waccan maaikatar da ya bari, dalilin yi masa canji kenan zuwa nan. To amma fa an sallemu daga aiki, an kuma bata takardun mu, babu sauran aiki a wata-hukuma ta gwamnati. Kin ji halin da ake ciki, sabuda haka mu kara wa Allah godiya, tunda maganar ta tsaya a haka”.
Suleman ya shigo da‘j‘aka ya ajiye, ya yin da suke ta sallallami, hawaye na’ bin fuskarsu, ya juya ya fita ya‘na waigensu. Gwaggo ta fara magana. “Saboda Allah wannan wane irin hukunci ne na zalunci? Bayan an kore ka, kuma sai a bata! maka takardu don mugunta’? To Allah ya isa”
Yace “Gwaggo wannan hukunci ya yi daidai. Kuma da ba’a hukunta masu laifi ko su wanene, da zalunci da cin amanar kasa sun yawaita. Al duk inda aka ce wasu jama’a sun gagari hukuma saboda kudin su ko mukaminsu. Wallahi wannan kasa ta gama lalacewa, ba kuma za ta rabu da masifa ‘ da bala’o’i ba. Allah ya yi mana tsari. Saboda haka gwaggo  mu rungumi wannan abu a matsayin kaddara kawai”.
Tace, “Ai makauniyar shari’a aka yi Alhaji, me ya sa ba za’a bin ciko gaskiya ba? Ai wannan bata suna ne!” Yace “Gwaggo kar ki dauki maganar nan kisa a ranki. Magana ina da hannu a ciki, ko ba ni da shi. duk ba ‘ta taso ba, tunda ga sa hannu na baro-baro ya isa shaida ga kowane Alkali.
Don girman Allah Gwaggo ki kwantar da hankalinki.  Wai yau ina Baba ? Ya fa bar mu har abada, kuma dole hakuri za mu yi balle wata kujarar gwamnati, wanda ka san dole” wata rana idan ba ta bar ka ba, kai’za ka bar ta. Menene abin damuwa? Kin ga kin rame kwarai gwaggo, ina ganin ki hankalina ya tashi. Ki taimake ni ki cire damuwa a ranki”.
Ta cire tagumi. Tace “Ai shi kenan, hankalinsa ya kwanta, sai dai kar’ su manta akwai Allah kuma shi baya yanke makauniyar shari’a”. Hajiya Suwaiba ta amsa “Baskiya ne gwaggo. mu mun bar‘ wa Allah,dun haka-“ki kwantar da hankalin ki kamar yadda yace. Kin ga shi ma hankalinsa ba zai kwanta ba, idan yana ganinki cikin damuwa”.- ‘
Ta sauke numfashi. Tace “Allah ya yi maku albarka, ya jikan Malam”. Duk suka amsa. ” da Amin summa amin”. Alhaji ya zarce da cewa. “Bayan anyi hakwai za mu kuma, don hada
kayanmu, za mu bar gidan gwamnati za mu koma Tudun
Wada”. lnna Maira Tace “Allah ma ya taimakeka  ka dan gina matsugunni Yaya”. Yace, “Wallahi Mairo, kamar wasa da’ taro da! sisis ina jefarwa har na kammala mun godema Allah, bari in yiwanka in koma  zaure”. _ . , . Hajiya Suwaiba ta mike tana fadin. “Bari in duba ko ‘
da ruwan dumi’. Yace “‘To ina Baba na ne?” Gwaggo tace
“Yana ciki yana barci’. “Ya yi kyau’a_:cikin dan lakaci kadan ya yi‘ wanka, ya sauya kaya ya koma zaure.‘Kafin wani lokaci‘ mutane suka dinga_zaryar_zuwa yima Alhajin jae kafin : magar’iba gida ya sake cika kamar’ yau aka yi rasuwar, ‘ Kullum kuwa haka kofar gidan yake. har aka yi bakwai. ‘ Washe gari da sassafa suka tafi, don shirya kayan su
kar wa’adin da aka dibar- masu ya cika. Tare da Inna Mairo
suka zo don ita ma ta taimaka masu aikin, aka bar Gwaggo da ’yan matanta Raliya da Asabe. . ‘ Watau kannen Suleman. Suna isowa Hajiya Suwaiba ‘ ta tura Magaji gidansu, don ya sanar’ masu cewa sun dawo kuma an saki Alhaji. Ba tare da bata lokaci ba, suka fara daura ‘ kaya. makwota suka rinka shigowa yi masu gaisuwa da jaje. ‘‘Shi kuwa Suleman bakin-ciki ya ishe shi, tun lokacin da‘yaji cewa Alhaji ya rasa aikinsa. Abubuwa da yawa suke ‘ bata masa rai, dunya.‘ San tabbas za’a‘fuskanci wata sabuwar rayuwa dakinsa ya nufa yana jan’ tsaki yana
qunqunai cikin,‘-ransa.» “Mutane‘, suna zaman zamansu. sun
jawa kansu. Yanzu idan ba ‘ayi hankaliba,  duk
talaucewa zasuyi Ya kuma jan wani tsakin. Inna mairo ta kwala masa kira, yana ji ya kyale, sai data kira na biyu, sannan ya amsa ya fito. Tace. “ga abincinka can a kicin. kaje ka dauka. kaci  ka yi sallah. sai kaci-gaba da aikin”. Yace “To”; Ya wuce ya ya dauko. ya ‘shiga da shi daki.
Duk sun yi sallah. sun fito falo suna cin abincin har da shi kansa Alhajin. Imam ke taya shi. Suleman ya fito yai
tsaye a kansu. Yace “Wai yaya za’ayi da kayan su Khalid _. ne?” Hajiya Suwaiba. Tace “Me kuwa za’ayi da su? Ka hada. ka yi ta sawa abinka”. Alhaji dake gefe, ya karba. “Bai kamata ba. kai masu kayansu za’ayi, tunda mallakarsu ne”.
, . Haushi ya kuma ta. Tace “Kai masu fa ka ce? To wa zai kai masu?” “Ni da kaina zan iya’zuwa in kai masu. Ka tara masu komai waje daya Suleman, idan aka natsa. zani
da kaina in kai masu
Hajiya Suwaiba ta kore shi da ido kafin. Tace
’ “Amma ka na ban Mamaki Alhaji, yanzu sai ka kwashi kaya ka
bisu da shi? Matar da ta yi mana tatas! Anan wurin ko gaisuwa ba ta yi mana ba! Haba Alhaji, ai sai ka sa ta
” tabbatar da maganar mijinta gaskiya ce”.
Yace. “Shine me? Ni ba zan yi gaba da Alhaji bara‘u ba. koda zai yanke zumunci da mu. kuma babu
abinda zai ragu a jiki na. Saboda haka ki daina kawo wannan
tunanin”. Ta yi’ shiru saboda takaici. A haka ma Inna Mairo duk haushi ya cika mata ciki. Shi kuwa Suleman. juyawa ya yi
dadi ya kama shi. Lallal zancen aurensa da Murja ba zai tashi ba.
Bada bayansa keda wuya aka murdo kofa aka shigo. “gafara dai!” Hajiya Aliyaa ta shigo, duk suka bita da kallo. “Menene gafara kamar gidan arna?” lnji Hajiya Suwaiba, Inna Mairo Tace “Ni ma dai shi na gani”. Alhaji yace “Allah ya yi mana gafara baki daya”. Sannan ta lura yana cikin falon.
Tace “Kai amma dai na yi sa’a tunda na same ka!  Dama na yi tunanin tunda anyi sadakar bakwai, yanzu kun dawo gida. To magana ce take tafe da ni akan Murja, ko kuma ince gargadi tare da fatan dukkan ku za ku ja kunnuwan ku, ku saurareni! Kafin nan bari in ba ki amsa Suwaiba, ai masu zuciyar masulunci akewa sallama…”
Ta katse mata hanzari. “A jahilcinki ba!” Alhaji ya  daga mata hannu. ta yi shiru. lta kuwa ta dauka. “Komai za ki ‘
fadi, ki fada, ba damuwata bane wannan. ehe Dalilin shiguwata gidan nan, na ke so ku sani!
Na samu labarin ranar lahadi Sulaman ya je wajan Murja, to ya kiyayeni, ya kuma fita idu na, tun muna shaida juna, idan ba haka ba. zai fuskanci wulakancin da har’ ya mutu ba zai manta da ni ba! Dakiki ne shi? Ko kuwa tumasancin ne na gado yake son ya nuna mana?
ldan mafarki yake  toya farka barcin sa. Murja ta yi . masa nisa kuma, karatu ‘yata, ta je yi makaranta, ba sayayya ba! Ina fatan an ji ni da kunnuwan basira? ldan kunne ya ji …… “,Fuu…. Ta fice, ta bugo masu kofa.
gaba daya tsit Suka yi na tsawon lokaci, kafin lnna Mairo. Tace “Caf! Yaushe wannan yaron ya je makarantar su Murja?” Hajiya Suwaiba ta amsa. “Ba ki ji tace ranar lahadi ba’? Ranar da yace zaizo ya debi kayansa kenan. Ashe da manufar’sa”. “Ranar da Baba ya yi uku?”
“Lallai Suleman ba shi da hankali Ana; tsakiyar’ jimami da tashin hankali, ya iya tsallakewa ya tafi yawon sa? Allah ya shir’ye shi! Yanzu haka idan ki ka bibiya, a ranar bai je wajen yayan ba, yace wai ya je, amma an hana shi ganinsa. Sakaran yaro kawai” Tace “Magana ai ta kare, ya ji wa kunnensa abinda uwar’ta tace! Ka gani ko Alhaji?”
Yace “Na ji na kuma gani, tabbas shaidan ya ribanci zuciyar’ta. Allah ya sa ta gane”. Haushi ya kume Hajiya Suwaiba, ta mike ta nufi dakin Sulaman. Inna Mairo ta biyo bayanta. Yana zaune bakin gado, ya yi sukuti da kai sunkuye. Hajiya Suwaiba ta tsaya gabansa.
Tace “Ba ka ji mur’yar‘ surikar ka bane? Me ya hanaka fitowa ka gaisheta?” Ya yi shiru kuma bai dubesu ba. “Ai ka ji sakon data aje maka ko? Bai sai na bata baki na ba. Yanzu me ye abin yi?” Inna ta karbe. “Don me zaki tambaye shi abin yi?” “To ba sakarai bane Mairo? Bari mu ji me zai ce?”
Kawai tashi ya yi ya bar masu dakin. Suka dubi juna baki sake. Inna Mairo ta zaburo ta biyo shi. “Sa’o’inka ne mu da ka fito ka bar mu, don ubanka?” Har ya kai kofa. Alhaji yasa baki ya kira shi. “Kai Suleman zonan”. Ya tsaya cak Hawaye suka cika masa ido  “Kazo:: nan nace”. Ya dawo
gabansa, ya zube hawayen har’ sun zubu bisa kuncinsa.
Alhaji ya zuba masa ido, ya tambaye shi “Menene ra’ayinka akan Murja yanzu?” Ya gage kwalla mur’ya na rawa. Yace “Ba na so a raba mu Baba. Akwai laifi, don na ja wajen ta na gaya mata kar ta yarda a raba mu, saboda’ wannan maganar‘?” Inna Mairo ta cafe “Tambaya ma ka ke yi’?” Alhaji ya dubeta.
“Ba ruwanki da maganar nan, ki yimin shiru kawai”. Ya juya kan Suleman. “Ba ka yi laifiba Suleman, sai dai inaso ka gane cewar’, dole mu bi a hankali tunda wannan sar’kakiyar ta’ ratsa. Duk da cewar Aliyaa itace mahaifiyar Mur’ja sam‘~ ‘ surutanta ba su firgitani ba, don na san ba itace abokiyar magana ba.
Shi yasama ban tanka mata ba. Ka kwantar da hankalin ka, idan Mur’ja rabonka ce, sai inda karfina ya kare. Amma ka yi min alkawari bazaka sake komawa makarantarsu ba, kamar yadda Ummanta tace. Saboda zaman lafiya da samun kwanciyr’a hankali.” Ya yi dan shir‘u jim, kafin yace “Shi kenan, ba zan sake zuwa ba”.
“Madalla. Tashi ka koma daki, ka ci-gaba da shirin ka”. Ya mike ya wuce su Hajiya Suwaiba ya shige daki. Shi kuma Alhajin kama hannun Imam yayi suka koma daki. Hajiya Suwaiha ta dubi Inna Mairo.
Tace “Mu je mu yi aikin mu Mairo”. Tace “Wai me Yaya ke nufi?” Ta ba ta amsa. “Ki sa ido mana, ke ba ki san Alhaji da daukar duman Magaji da nishi bane”. Ta kada kai.
Tace “Ai shi kenan”. Suka koma akin su. **************
Bayan kwana biyu su. Alhaji Bara’u suka gama shirin su tsaf! Na komawa Kankiya. Tun asuba motar’ kayansu ta yi gaba, su kuma suka biyo bayanta, a halin yanzu. Har a yau din nan Hajiya Aliyaa ba ta daina naci da surutal akan auran Murja da Suleman ba. Alhaji Bara’u ya murtuka fuska. Yace “Kin fiye ‘ mita‘ Aliyaa. Wai ita wannan maganar ‘bata karewane  Tafiyar ma fa bada izinina ki ka yi ta ba” Tace “Haka ka ke gani Baban Mansur. amma zaka ga muhimmancin maganganun nan gaba”. Mansur dake tare da Alhajin a gaba. Yace”gaskiya ne, ai gara tun wuri . ayi wa tufkar hanci, tun kafin ya zugata ta gagaremu.” Yace “Duk shirmen banza ku ke yi. Murja fa yarinya ce, meta sani .da za ku dami kanku?” ‘ Nasiru ya amsa. “Wallahi ba na son jin wadanann maganganun. Me zaisa ba za’a manta da su ba?” Tace “Ba na gaya maka idan muna magana, ka daina sa mana baki ba? ’Sakarai mara zuciya! Ai ni da ku ne, kai da Khalid za ku gane kuran ku,’ muddin ka ki daina goyon bayan macucin nan! Wawaye, kawai ni dama motar kaya kukabi
Khalid yace “Wai ni me nace Umma, ki ke sawa dani?” Tace “Ban sani ba!” Alhaji Bara’u yace “Kai! Ya isa  haka, kar in sake jin bakin kowa. Laifin nan dai ni akai ma wa, idan na gadama, sai ince na yafe”. Nasiru yace daKO ka ;; kyauta Abba, domin Allah yana son mai yafiya”.
Hajiya Aliyaa ta watso masa harara, A yayin da Alhajin ke fadin. “Ni kuwa zan yafe duk ranar da Alhaji Abdul-
Rashced ya nemi yafiyata”. Dadi ya rufe Nasiru da Khalid. Mansur kuwa shiru ya yi yana kallon gabansa. ;
A haka suka iso‘ Zariya, suka sauké Mansur a makaranta, sukaci gaba da tafiya. bab suke da shiga garin Manumfashi, ba hawa, ba sauka cikin wani hukunci na Ubangiji tayar gaba ta faShe. Motar ta kwacewa Alhaji Bara’u. ta yi daji ta daki wani dan matsashin dutse,ta yi
kuli-kulin kubura sau uku.
Sannan ta dire ta tsaya cak! Akan kasa. Tayoyinta na sama
“Inna-Lillahi’wa-|nna-|laihir-Raju’un! Jama’a ‘sunga
gagarumin tashin hankalin da suka jima ba su‘ga kamarsa ba. Domin nan take aka zaro gawar mutum biyu, sauran biyun
ma hasashen suna da rai KO basu DA rai akeyi  ”
Amma babu tabbas. ‘Yan-Sanda da Jaman  sun taimaka kwarai da gaska wajan binciko  su waya da kai su asibiti; A cikin motar aka samu muhimman takardun da suka bayyana Alhaji Bara’u da garinsu. ‘
Tuni aka kai gawawwakin guda’biyu mutuware. Yayin da biyun ke imajansi anan babban asibitin ABu na ‘Manumfashi. Musamman aka tashi wani bawan Allah ya tafi Kankiya, don binciko ‘Yan-uwansu Alhaji Bara’u.
Karfa takwas na dare, dan ‘sakon ya dawo tare da
manyan maza ‘cikin” mota fikof za’su kai mutum shida.
HankalinSu in ya yi ‘dubu, ya tashi. Abin tausayin ‘ma ‘sai ‘da “‘suka iso, aka nuna masu gawar mutum’biyu  Daga kuma wadanann magashiyyan.‘Babu wanda bai zubda’haWayeba. saboda tausayi. Anan sukakwana muhawarar yaddah
za’ayi’a karbi gawawwakin da sassafe, don yi masu sutura aka yi’ Shiwarar sanyin asuba, cikn yardar Uhangiji Aliyaa ta farfado. Kanta dum! Ta ji a dame, da kyar ta bude ido ta rasa duniyar da take. Da karfin tsiya takwala ihu mai tsanani, gaba daya ta firgita duk mahalukin dake wajen. lhun‘ ne ya jawo hankalin ma’aikatan lafiyar. suka yi caaa! Kanta. a gigice suka dafe ta, ita kuWa fadi take “A”‘ina na ke? Ina Baban Mansur? Ina su NaSiru’? Wai a ina na ke nace?” ~ ‘
guda cikinsu tace “Ki natsu Hajiya, kar ki’karawa kanki ciwon! Nan asibiti kike ~ldo a war‘waje‘tace’Me ya“faru? Ai Kankiya za mu, ba asihiti ba” “Hadari ‘kuka yi’ Hajiya, ki yi shiru ki kwanta, kin ga akwai rauni a kanki, kar ki ,_ sa zubarjinin ya dawo”.
‘ Ta fara kuka. “To ina ya’rana?‘ Ina Babansu? Ko sun
mutu ne?” Suka ce “Ba su mutu ba, suna can bangaren” maza”. “Zan iya gansu! Kumuje in gansu!” “Ba za ki ba Hajiya! Ki kwanta kawai!” Da kyar’ suka samu ta natsu, har ta far’a ba su haushi saboda kafiyarta Sannan ’dayadaga‘ cikinsu ta hanzarta taje ta nemu-‘yan uWanta;~-mutum biyu suka shigo suka zauna tare da ita. ‘ ‘ ‘ ‘ ~
A hankali ta sake bude-ido. ta dubi wadénda ke tare da ita. ganin mutan gidan sune yasata kara gocewa da kUka “Kun ga abinda ya samemu ko? Masifa iri iri?” Suka ce.””Ki’yi‘ hakuri Hajiya Aliyaa, haka Allah ya kaddara”Tace “Kun ga
su Baban Mansur? Su ma sun ji ciwo ‘sosai ne?” ” sukace “Ba sosai‘ bane”. Ba su‘kara ‘mata’ komai ba domin’ Nus din nan ta gargade su kar su gaya mata labarin rasuwan
a halin da take ciki yanzu. Ta matse ido. tace “Uh Allah! Haka kuma ka kaddaro mana” Daya cikinsu yace “Ki yi masa godiya ne, ki roke shi sauki, domin komai na gare shi”,
Ta ci-gaba da nishi, ba ta tanka ba. .Lukacin tafiya sallah ya yi. suka‘nufi masallacin asibitin, suka bada farali, suka dawo. Har zuwa lokacin .Alhaji‘Bara’u na cikin  halin, rai kwawai, mutu kwakwai. { ,.
Sai Hajlya Aliyaa takuqu tasan halin da iyalanta suke ciki. Ganin ta matsa Likita-,yasa akarakata ta gunsu: Nusis biyu suka .rirrike ta suka nufi inda Alhaji Bara’u ke kwance. Ta kalle shi, ta dube. su. “Bai farfado bane? Ko barci yake yi?”/’gaskiya bai farfado bane”. an daya ta bata amsa.
To ina yarana suke?” Suka danyi shiru jim, kafin ita Nus din tace. “Ki fa yi hakuri Hajiya, duk suna mutuware”. Ta zura mata ido tsawon lokaci, kafin ta yi’dan murmushin takaici.Tace.
“Baiwar’ Allah’ki daina maganar wasa mana, wane irin mutuware kaman sun mutu?” Tace “Duk wanda ki ka ji yana mutuware, tabbas Ai mutuwa yayi. Daga Allah ne Hajiya, ki yi hakuri ki dangana”.
‘ Ido waje tace. “Dukkan su’?” Ba su tanka mata ba. Ji suka yi ta tafi yuuuu! Za ta zube kasa. Suka yi azama suka kara rike ta, suka dawo da ita bisa gadunta
MalamSallau yana daya daga cikin mazan da su ka zu qani ne ga mahaifinAlhaji Bara’u, Shi ya tsaya tsayin daka aka ba su gawar‘ Nasiru da Khalid tare da sa hannun ‘Yan
San da suka kawo hadarin. Saboda ya kamata ayi masu sutura ne ba wai a bar su a mutuware  ba.
Karfe goma na safiyar suna shirin tashi, wasu mata biyu suka iso, guda matar Malam Sallau ce, guda kuwa Yayar Hajiya Aliyaa ce. Sun ci kuka, har suka godema Allah. Nan aka bar su tare da Aliyaa suna ta kwantar mata da hankali, dun tunda ta farfadu, rusar kuka take yi. tana sambatu babu dadinji.
Mansur, bai samu labari ba, sai da yammacin wannan ranar. Wani saurayi cikin ‘ya’yan Malam Sallau ya je makaranta ya neme shi ya gaya masa wannan mummunan labari. Take nan ya kusan zarewa.
A daddafe suka iso Manumfashi. Kamar ransa zai fita saboda kuka, duniya ta yi masa bakikkirin! Ya rinka jin duk duniya babu wanda ya kai shi bakin-ciki a Wannan rana.
Babban abinda ya fi daga masa hankali, shi ne sun tarar’ Alhaji Bar’a’u ya farfado. Amma baya iya magana. kuma ilahirin jikinsa babu inda yake iya motsawa. binciken Likitoci ya nuna kashin hayansa ne ya karya, watau sifainal kud. Subhanalillahi. Hasbinallahu’wa-Ni’imal-Wakil! Rayuwa kenan,
shi ya sa aka ce aikata alheri, don ba ka san ta yadda za ta zo
maka ba. Nan Mansur ya kwana babu barci, sai don ance
barawone. da safe suka karasa Kankiya, aka kai shi makabarta ya isa kabarin ‘yan-uwansa, ya yi masu addu’a. Suka bar makabar’ta yana kuka sosai. Ko da suka dawo inda ake zaman makoki. wanda shi ne babban gidansu na gado
nan ma zaune yake kawai,‘ yajima yana sharar’a kwalla kaf suka kafe.  Zuwa la’asar ya sake dawowa Manumfashi ya zauna wajen Abbansa, damin hankalinsa ya fi karkata a kansa, saboda ita Hajiya Aliyaa ba ta samu manyan raunuka ba, illa
kanta da wuraren da ba’a rasa ba. ************
Hankali kwance Alhaji Abdul-Rasheed da iyalansa suka tare
sabon gidansu .da ke Tudun Wada. Duk da ba’a zuba masa wasu sababbin kayayyaki ba, sai wadanda suka je da su. gidan ya’yi kyau, saboda tsarinsA mai kyau né irin na zamani. Kuma da yake ana samun wutar lantar’ki sosai, koda yaushe gidan cikin karatun qur’ani yake don kore shaidanu.
Kwana daya Inna Mairo_ta kara yi, ta koma. ga shi wasa WaSa sun kwashe‘ kwanaki goma sha biyu ba tare’da ‘ sun samu labarin abinda ya faru ga Alhaji Bara’u da iyalansa
‘ba.
Yau asabar Alhaji ya kira Direbansa Magaji a falonsa. Bayansun gaisa. Alhaji Abdul-Rasheedya ya dube ‘shi. Yace‘ “Magaji na San mun dade tare, cikin lumanamun yi zama na amana da kwanciyar hankali’. Sai dai ina ganin lokaci ya yi daya zama dole mu rabu…;..”
. Da sauri ya katse shi. ’sbd me Alhaji? In dai tuki ne,‘ na yi alkawari zan tuka ka har karshen rajuwata Alhaji”. Ya yi dan murmushi.
‘Yace “Na san za ka iya Magaji, amma da me‘zan biya ka? Ba ka ganin rayuwa ta sauya? Ka na da iyali Magaji. gaba daya hakkinsu rataye, yake a wuyanka. ashe wajibinka ne ka ‘ je neman halali. Ba zai mana kyau ba, idan kaci-gaba da zama tare dani, alhalin ni din nan ba zan iya daukar nauyinka , ba a halin yanzu. ‘ : .
Dukkanmu hakuri zamuyi, mu bar wa Allah. Abinda na ke son ka da shi, shine ka’ laluba wani wuri ka samu wani aikin. don kai ma ka ji da‘din tafiyar da rayuwar iyalanka”.
Jikinsa‘ya yi mugun sanyi, tamkar zai yi kuka yake fadin. “Alhaji mun saba da juna, shekaru‘ sama da talatin muna tare, ai ’ba wasa bane. baka taba kyara ta ba ko ka hantareniba Samun irin ka zai yi wuya Alhaji. Da za kai min
‘ hakuri, da ka bar ni tare da kai, mu tashi tare, kamar’ yadda muka fadi tare”.
Kai tsaye ya ba shi amsa. “Ba zai yuwu ba Magaji! Kamar yadda na gaya maka, ‘ka dauki umarni na akan hakan, koda dadi ko babu’dadi! Ka ji abinda nace?”Ya yi kasa da ‘ fuska. yana gage kwalla. Alhaji ya laluha aljihu‘ya daukl kudi dubu biyu da dari biyar.
” __ Yace “Ungu wannan ka sa aljihu, ka dan taba cefane kafin wani aikin’ ya ‘samu. Ga masara da shinkafa tiya hiyar‘~ biyar da rabin katun din’Taliya  in za ka wuce ka tafi da su a ‘ yi maneji. Karbi nan!”
. Ya mika hannu da kyar ya karbi kudin Yace”Na -_ gode Alhaji. Allah ya‘saka da alkhairi‘. Amma ina son in roki alfar‘maf da ka bari in rinka tuka‘ka har-zuwa lokacin da zan
‘ samu wani aikin”. ,
‘Yace. “Ban amince ba Magaji ka san dalili? Hakan- zai sa kashentake‘. ka kasa neman‘wani aikin, tunda ranka yana son’zama da ni. Ba ma wannan ba, shin ina 2a ni, da zaka’rinka tuka ni? Babu Magaji”.
‘ Ya numfasa. Yace “To ka yi hakuri. gobe! in tuka ka zuwa Kankiya, idan muka dawo sai mu yi bankwana Alhaji”. Ya dan kada kai cike da tausayin Magaji. “Shi kenan. Allah ya nUna mana guben lafiya”. Yace “Amin”. Sun jima “suna‘ta
hirer duniya har zuwa kiran sallar la’asar. suka yi alwala
suka shiga masallaci. ‘
Washe gari safiyar lahadi. Alhaji shirya ‘tun kafin takwas na safiya. Suleman Imam kawai yake jira. take da isowar Magaji. Ba’a jima ba Magajin ya iso, yayin da su Suleman ke karyawa. Suna kammalawa. babu bata lukaci aka fito da jakukkunan kayansu Nasiru -da sauran ‘yan tsirarun na. Mansur: ‘
Magaj‘i ya sa a but. Hajiya Suwaiba ta rakosu’tana masu fatan sauka lafiya, dukda cewar bada son ranta za’ayi tafiyar ba.cikin ikon Allah  suka iso har’ Kankiya da tsakar rana. Alhaji ya fito ya Shiga. zaure ya yi sallama sau uku, sannan aka amsa. Malam Sallau ne ,ya’fito. Yana ganin Alhaji Abdul- Rasheed ya fara ‘yar fara’a; ‘
“Ah! Alhaji! Sannu da zuwa”. Ya mika masa hannu.
“:bari  “Bari a kawo tabarma”. Ya juya da sauri ya dauko tabarma, ya fita da ita. Ya shimfida yayin da Alhajin ya
leka, ya kirasu Suleman. ‘Ashe har da yara?” ‘
“Eh Wallahi”. Suka zauna, Saunan suka gaisa gaba ‘
‘ “dayansu. Magaji ya tashi ya koma cikin mota. “Sai ku ka ji abu
babu dadin ji ko Malam’?” . –
Yace. “To yaya za’ayi da abinda Allah ya kaddaro? Dama ana ta tararrabin abinda ya faru, Sai kuma ga wani. To yaya za’ayi? Sai hakuri, ajalin na su ne ya zo daya. Shi kuma Allah‘ya ba shi lafiya”.
Duk suka zubo masa ido. “Ajali? Ajalin we?” Yace._ ~ “Ah! Baka da labarin Hadarin da ya faru ne?‘ Ai na zaci gaiSUWa ka zo Alhaji. Nasiru da Khalid Sun rasu Alhaji, shi
kuwa Bara’u yana asibiti, ya samu matsala sosai, don ance kashin bayan sa ne ya karye. Aliyaar ce kadai ke da dan dama-dama”.
Tuni gaban su ya fadi, ldo waje. Yace “Me? Yaushe wannan abu ya faru?” Ya amsa “Yau kwanan su goma sha uku”. “lnna _-l.illahi‘wa—lnna-llaihir-Raji’unl Ya maimaita sau uku. kafin ya ci—gaha da fadin. “Kun’ ga tashin hanakli Malam Wallahi ban sani ba. kawai na kawu masa ziyara ne, sam ban san abinda ya faru ba.
Ka san abin wannan da ya faru, mun dan samu
sabani har ran ita Aliyaa ya baci, ta je ta kwashe yaran daga , ‘
gidana. Ashe ajali ke kiransu.Allahu-Akbar Allah ya yi masu rahama”
Yace “Amin, amin”. Suleman ya sauke numfashi ido jajur! Yace “Yanzu shi kenan sun mutu Baba?” Ya kada kai.
Yace “Babu wai Sulaman. Kai rayuwa kenan . Suleman yaCe 
“Allah ya jikansu, shi kuma Abba Allah ya ba shi lafiya”. Duk suka amsa. “Amin summa amin”. Alhajin yace “Bari mu yi .masu addu’a”. Shi ya jagoranci addu’ar mai .tsaWo, suka shafa,. ka na ya tambaya. “Shin Alhaji Bara’un yana wane asibitin ne?”
Yace “Babban asibitin ManumfaShi,Amman sunce
za su tura’su Zariya gobe litinin, Yanumfasa.‘ Yace “Allah
ya ba shi ‘lafiya”. “Amin”. Bari mu za mu koma, daga nan mu biya asibitin mu duba shi”. Yace'”Hakan yayi kyau, amma ku tsaya ku sha ruwa, akwai fura  sai a dama maku,‘ ku sha”.
Alhaji yace “Babu yunwa a tattare da mu, kar’ ka?!“ damu Malam. bari mu hanzarta don gaba daya hankali na ya koma gare shi”. “To shi kenan. Allah ya kai ku lafiya”. Suka . mike, ya jagorancesu zuwa cikin gida, ya yi wa mutan gidan gaisuwa.
Magaji ya kwaSo jakukunan kayayyakin su Nasirun. Alhaji yace “A ajiye cikin kayan su, ko sadaka ayi dasu”. Bayan sun sallami juna. Suka mika hanya, hankalin su a tashe, har basu yiwa juna maganar kirki.
A hanya suka yi sallar azahar, sannan suka karaso cikin asibiti. Suna isowa kofar emajansi da Hajiya Aliyaa suka fara arba, suna zaune bisa tabarma da wasu bakinta suna shan iskar bishiyar dalbejiya. lta kam ta ji sauki, don an kwance mata rawanin bandejin da ke kanta, sai filasta.
Tana hango motarsa na tsayawa wajen aje motnci. Ta yi wuf! Ta taso da saurin ta, ta iso gunsu, sai dai ganin ta suka yi a gabansu. “Hajiya Aliyaa!”
lnji Alhaji yana budo kofa. Ta tuge jikin kufar ta hana shi’fitowa. Ya bita da kallo yace “Ba tashin hankali ya kawo ni ba Hajiya Aliyaa. Ya kamata ace ayoyi sun bayyana a garemu, mu gane cewa wannan rayuwar’ ‘yar kalilan ce a garemu. Ki yiwa girman Allah kar ki dauki wannan maganar ta zama silar’ gaba a tsakaninmu. Ba ki ji yadda zuciyata ke
suya ba, sakamakon labarin da na ji. Tace “Saurara min Alhaji Abdul-Rasheed! Babu abinda 2a ka gaya min, wanda zai gage dafin daka zuba min
cikin zuciya! Saboda haka gaba mu da ku yanzu muka kulla ta. har abada bazan taba’ yafe. maka ba Alhaji Sannan ina so in
tabbatar maka cewa daga yau kar ka sake tako kafar ka inda ” muke. da yaradar Allah Baban Mansur zai tashi ya yi rayuwa kamar kowa”.
Ya kada kai tare da nisawa. Yace “lna masa fatan hakan. kuma ina rokon ki da ki bar ni in je in gan shi mu yi musabaha”. Tace “Allah shi kyauta! Baya bukatar ganin ka balle musabahar kai Macuci, azzalumi! Bakin mugu zakaga karshen ka kai ma.

Complete 13 na cikin www.littafanhausane.com.ng

Tunda ka yi sanadiyar tarwatsewar cikin gidanmu! Bakin-ciki da tunanin cin amanarda,kayiwa Baban mansur  shiya jefa Bahan Mansur wani hali, har sitiyari ya kwace masa ya fada daji! Ina ribar alakar mu da dakai? 
Dama can ba mu hada komai ba, l<a gane? Haduwar bariki ce kawai. saboda haka rabuwar hariki itace amsar. Amma kafin nan. ina kara jaddada maka cewar har abada, ba zan taba yafe maka ba
Ta buga masa murfin mutar, ta yi gaba abin ta. Saura kiris! Ta datse hannunsa da kufar’ motar.
Ya talalbe goshi, yana yi wa Allah tasbihi. Shi kuwa Suleman tsintar kansa yayi cikin rudu mai tsanani. ldanuwansa suka kada, ya zubawa Alhaji su’, ya rasa me zai ce Muryar Magaji ta dawo da hankalin Alhjin cikin motar. “Ya kamata ka kyale mutanen nan Alhaji.
Bai kamata kamar Hajiya Aliyaa ,ka zauna tana dankara maka maganganu ba. Ai Allah ya gazuciyarka game da wannan al’amari. lta da mai hankali ce da ta: gane tarkun
amanane Alhaji Bara’u ya fada”

hmmmmmm jama,a ni nama rasa me zance Ina fatandai kuna fahimtar inda labarin ke dosa?

DA kuma darussa masu dama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *