Makaranta duniya
Chapter4
Cikin tashin hankali ya Fara Neman taimako wajen jama,a cikin ikon Allah kuwa jama,a suka taru nan suka taimaka masa aka daura alhaj din akan mashin wani ya tarbe masa Shi ta baya shi kuma muhsin din ya tuqa mashin din suka nufi Gida isansu keda wuya ya Kira malam saddiq a waya gamida shaida masa abinda ke faruwa ba tare DA bata lokaciba ya nemi izini daga wajen aikin nasu aka barshi yana isowa ba tare DA bata lokaciba ya nemi dan taxi sai asibity bayan sun isa ne akai gaggawan basu gado mudassir ya Kira mamansa cikin kuka yana sanar DA ita abinda ke faruwa gocewa tai DA kuka tana Neman sauqi wajen Allah tace yanxu muda ya zamuyi kenan wlh ba kudi a wajena yace ai na Kira malam saddiq a waya yanxu hakama muna asibity an bashi gado
Nannauyan numfashi ta sauke gamida cewa to Allah e saka masa DA alkhairi Amman muda ka dauki number lado Mijin innarku ka sanar dashi abinda ke faruwa don a sauu Wanda zaizo kula dashi don karka samu matsala a skul dinka yace to shikenan mama Zan duba yanxu a wayar baba na dauki number saina kirashi sannan ya kashe wayar ba tare DA bata lokaciba kuwa Allah yasa wayar ta shiga ya kirashi gamida shaida masa abinda ke faruwa a take kuwa ya isar DA saqon washe gari DA sassafe mairo qanuwar alhaj abdurrashid tasa lado mijinta Daya kawota asibitin DA aka kwantar DA imam domin taga yaddah jikin NASA yake aikuwa hakan akai Inna mairo had kukan takaici tayi tace yanxu SBD Allah ace dan dan,uwana DA dan uwan nawa kansa basu DA lfy Amman a kasa sanar Dani yanxuma to meye ta ka maiman abinda ke faruwa ba tare DA boye boyen komaiba hajiya suwaiba ta zayyane mata duk iron wulaqancin DA sulaiman yaima su alhaj akan jamila dalilin hakane yasa imam zuwa ya banki kwayoyin DA sukafi qarfin kwakwalwarsa sannan baqincikin abinda sulaiman yaima alhaj DA tashin hankalin halin DA imam ke ciki yasashi yanke jiki ya fadi a ranan DA sukaje zagaye a gonarsa ta Dade sosai tana kukan baqin ciki DA sake tsanar wannan irin hali na sulaiman ace ka haifi DA DA cikinka Amman ka kasa tankwarashi Amman ba komai zai gwauraya Dani sannan sukai sallama DA fadin in Allah ya yarda yau zata gama duk shirin DA zatai gobe taje ta tare a Kaduna domin yin jinyar dan uwarta bayan sun isa Gida tasa lado ya latso mata number sulaiman ya Kira number saida tai ringin har ta kusa katsewa sannan aka dauka ya miqa mata gamida cewa ta kanga a kunnenta
Salamu alaikum ya fada cikin ji dakai wa alaikumussalam Inna mairo tace wai sule Mai kakeson zamane kana Neman albarka kuwa?
Ya qara murtuke fuska DA murya
Me kuma akace miki nayi inna? Nifa banason qananun maganganu irin nakunnan
Tace baka DA kunya sule kuma ban taba sanin butulcinka yakai ga haka ba kamar alhaj to ina Mai tabbatar maka DA nikai mawa kuma wlh idan baka zauna kayi tunani Kama ka daidaita hankalinkaba
Nayi rantsuwa kana tare DA Dana Sani baya ga haka inason shaida maka dagashi har imam suna kwance a asibity basu DA lfy don haka duk halin DA kake ciki ka samu lokaci kaxo ka dubasu
Yace Inna DA farko inason in fadamiki Ki daina biyema KO wacce magana DA aka kawo miki
Maganar jamilace kawai yarinya Kuma tace bataso to Mai zaisa ai mata dole tace wannan ya rage naku tunda bata game Mai sontaba a Halin Yanxu nan gaba ai zata game
Yadan murmusa inna kenan mubar wannan zancen ciwon me suke?tace ciwon baqin ciki mana kwayoyifa akace imam ya bankada sukafi qarfin kwakwalwarsa ya zare kamar Mai hauka
Shi Kuma Alhaj a gonna ya fadi ba qafa ba hannu Sannan babu baki dun wannan ba matsalar baqinciki bane?
Yace babu matsalar jamila a cikin shaye shayen kwayoyinsa daman can yana shaye shayensa shi yasa dun abinda kikaga hankali bai kwantar dashiba to akwai matsala…
Ta katseshi qarya kake sule yaran Alhaj basu da wani Matsala kaidai kawai kace bakason hadin zuri,a dashi abarshi a haka
Rai a bace yace to a barshi din mana Inna zancen zuwana Kuwa banajin Zan Iya dan inada aiyuka a gabana DA yawa
Tace sule sule kaji tsoron duniya ka gyara halinka
Kai bakajin kunyan ace sai ankiraka an fada maka abinda ya kamaceka yace nima abinda na Dade Ina mamaki kenan kullun saidai a kirani Ana fadamin yi wanna yi wancan kaman qaramin yaro ummar tasa ta numfasa yace magana ta qare nidai na fada miki bazan samu zuwaba tace to ka samu wani Abu ka turo musu domin a rage dawainiyar asibity ni koda baka turominba don bana jin dadin butulcin DA kake nunama Alhaj
Guntun tsaki yaja mtwssss sai anjima Inna insha allahu kuma Zan turo muku DA abinda ya samu ba tare DA wani qarin bayaniba ya qatse wayar
Lol
Naku har kullun
Www.Facebook.com/abdullahi.Ismail.salanke