Makaranta duniya
New book
Chapter1
Wannan Al,.Ada Al.adace Mai kyau wacce alhaj abdurrasheed ya rayu akai kusan haka rayuwar kakanninmu DA iyaye ta kasance wajen tunani DA kaifin hankali.
DA zurfin tunani DA kawaici abin duniya bai taba rufe musu Idoba shiyasa sukeda tsananin taka tsantsan akan kyale kyalen dake cikinta dattijo alhaj abdulrrashid ya kwashi kashi Tasha,in DA biyar akan abinda muka lissafo bugu DA qari mutum ne Maison jama,a DA kuma alkhairi koda kuwa abinda yai saura masa kenan
Har gobe haka yake bai canja ga gurbatacciyar rayuwar zamaninnan ba kuma bata sauyashi ba
Wani abin Al,ajabi ga alhaj abdulrrashid baya iyacin abinci shi kadai dukda halin rufin asirin DA yake a yanxu tun sunaci tare DA aminansa wadanda suka taso tare har ya kasance basa Raye duk sun koma ga ubangijinsu
Hakan yasashi kame kamen masu sha,awar tarbiya irin tasa domin dai yanxu wannan kyakkyawar Al,Adar an watsar DA ita
Magidanta sun mance DA fa,idar wannan Al,Ada ta samun wani majalisi domain cin abinci baya ga samun albarkacin juna yana taimakawa matuqa wajen shaquwa tsakanin makwabci DA makwabci sannan ya taimakawa magidanta sanin matsalolin juna Dana iyalansu Kai harda na unguwar tasu kuma anan ne ake tattauna matsalar domain maganceta a nawa gajeren hangen kenan
Sai Na hango kamar DA wadannan tunanin magabatanmu sukai amfani wajen kulle kawunansu waje Daya tare DA so DA qaunar juna
Ta yaddah makwabci zai Iya hukunta dan makwabcinsa DA zaran yayI ba daidai ba
Babu raini ballentana ya nemi yin rashin kunya
SBD ya tashi yaga iyayensu cikin kauna DA takaiga har abinci tare sukeci lallai dole ya dauka babu banbanci tsakanin iyayensa DA duk Wanda ya gansu tare
Don kullun hannuwansu a kano daya yake cikin annashuwa uhmm
Inam a ace wannan Al,Ada zata dawo magidanta su daura a kanta mu gani KO Allah zaisa mu samu canji akan lalacewar tarbiya DA zamantakewarmu ta qasar Hausa?
Malam Sadiq yana Daya daga cikin mutanen da suke girmama alhaj abdurrashid ya daukeshi tamkar uba kuma abokin shawararsa
Duk DA cewa akwai yar tazara a tsakanim gidajensu Amman akoda yaushe tare sukecin abincin dare masallaci ta hadasu tun dawowar malam Sadiq anguwar shekara uku DA suka wuce sha,aware dabiun tsohon yasa malam Sadiq bibiyarsa har suka shaqu sosai
Yau laraba kaman kullun malam Sadiq yai sallama a bakin dakin Alhaj abdureashid babban falo ne Kuma dukda kayan dake cikin falon sun tsufa kwarai kana kallon falon zakasan ya Kama kudi a baya Alhaj na zaune akan wata dardumar dake kan tsohuwar kafet din data malale ilahirin dakin farin gilashine sama fuskarsa yana tilawar alqur,ani Mai firma
Ya amsa sallamar Kai tsaye malam sadiq ya shiga falon
Cikin girmamawa ya shiga falon ya samu waje ya zauna sukai musabaha dukkanninsu fuskokinsu kamar gonan auduga
Malam Sadiq ya iyali? Ya amsa qalau suke baba
Masha Allah yana rude baki akai sallahama a falon dauke DA tire Wanda aka daura kwanonin samira guda biyu tare DA kofin ruwa Mai matsakaicin girma
Duk suka amsa sallamar DA yay in sannan ya aje tiren abincin a gabansu sannan ya gaishe DA malam Sadiq malam Sadiq ya amsa Mai da Fara,a mudassir kenan ya karatu ya amsa DA lfy qalau sannan ya miqe ya koma Cikin Gida
Alhaj ya yawo tiren ya bude lafiyayyen tuwon masarane miyar kubewa bismillah malam Sadiq ya gyara zama KO wannensu ya Fara DA sunan Allah sundanyi nisa Cikin cin abincin tare DA hirarrkin duniya
Alhaj abdul ke cewa tafiya nakesonyi zuwa bauci in Allah ya kaimu ranan lahadi kuma zanso rakiyarka idan har ka samu lokaci yace nimako zanso na rakakan saidai kuma ranan lahadi kace har maje mu dawo a ranan kasan yanayin aiki
Alhaj yace hakane ba komai Ina Iya maida tafiyan ranan asabar
KO daman maganan yaronnan imam ce zata kaini badai har yanxu maganan yarinyarnan yakeyiba ya dubeshi sosai itace ya kwallafa rai a kanta na rasa yaddah zanyi dashi
Malam saddiq ya tsame hannuwasa daga Cikin abincin hava Mai yasa imam yakeda kafiya hakane? Shin yarinyarnan ita kadaice ya mace? YayI zuciya mana ya qyale musu yarsu
Alhaj abdul yai murmushi gamida cewa so yake yaga abinda ya turema buzu nadi domain ni kaina na bashi shawaran hakan Amman saidai na Lura kaman Dada ingizashi nayi
Jiya yake cemin nine banje bauchi DA kaina ba sai naga kuma yanada gaskiya maganar gaba Daya ta waya akeyinta mamansuma tace in kyaleshi kawai saidai ni zanso naje domin kwada sa,ar mu
Malam saddiq ya numfasa Shannan yace gaskiya ne kuma daman ance matar mutum kabarinsa Allah yasa a daidaita alhaj yace amin sukaci gaba dacin abincin suna tattaunawa har suka qare qarfe Tara DA rabi malam Sadiq yaima Alhaj abdul saida safe sannak ya nufi gidansa
Asiya na kwance a tsakar Gida ita DA yaranta sunashan iska yayI sallama ya shiga shima nan tsakar gidan ya samu waje ya zauna yaima Allah tasbihi an dawo inji asiya uhm. Ya amsa gamida miqo mata baqar ledar dake hannunsa ta karba tana tambayarsa Mai Kuma aka samo mana
Bai amsaba ta kwance ledar qaton kunshine ne a takarda yayinda manyan yaransa DA basuyi barciba sukai masa sannu DA zuwa ya dubi babbar cikinsu aidaman ke nasan ba zakiyi barciba suna daria tace yaushe zanyi barci bayan nasan zaka dawo DA kunshi suka qara kecewa DA daria yana fadin mayyah yarinya makar kura uwar tasu tace ai asma,u Allah ya shirya wannan bakin kwadayin naki
Ta qara matsowa gaban ledar tana gyara baki uwar tasu ta harareta gamida cewa daukomin filet uwar kwadayi ta miqe sauran suna mata dariya
Asiya ta zubama malam saddiq NASA tsirene DA gurasa Shannan suma yaran ta raba musu sunaci suna hirarsu cikin kwanciyar hankali
Shannan ne yake sanar DA ita tafiyan DA zasuyi rananr asabar shida alhaj abdurrashid in Allah ya Kai mu tace Allah ya Nuna mama asabar din lfy yace amin
……. …… …….
Ranan asabar DA sassafe malam Sadiq ya gama shiryawa tsaf bayan ya gama Karin kumallo asiya ta rakoshi har bakin zaure gamida masa fatan sauka lfy ya I so gidan Alhaj abdul ya iske shima ya gama shiri kusanma shi suke jira
SBD haka babu bata lokaci ya kwadama mudassir Kira babu bata lokaci ya fito shima yaci adonsa ya gaida malam saddiq Sannan yake tambayarsa au tafiyar Ashe hardakai Cikin murmushi yace ban taba zuwa bauci bane shine nakeson zuwa naga yaddah take yace eh ya kamata to Ina shi angon?yace yaya imam yace eh shi mana yace yananan Zuma shima shiryawan yakeyi yana shiru imam din ya fito farine Sol dashi Mai kyan sura
Sannan suka gaisa DA malam Saddiqa bayan sun gaisan ne suka rankaya domain yai musu rakiya Zuma tashar mota bayan wucewar minti ashirin mota ta gama cika suka daga imam kuwa saida yaga tashinsu yai musu fatan sauka lfy Shannan ya hayo acaba ya dawo Gida tare DA roqon Allah ESA a dace
qarfe biyu na azahar suka isa bauci lokacin kuwa Ana zabga uban Rana Mai zafin gaske babu bata lokacI malam Sadiq yai musu tashar taxi a aljihunsa ta kaisu anguwar DA zasu sauka
A qofar gidan sukai fakin Sannan suka doka sallama ba tare DA bata lokaciba akaxo aka bude musu kallon mamaki tai mush tare DA wani razanannen murmushi tace ah baba sannu DA Zuma yace yauwa murja Ku shigo mana mudassir hardakai ya amsa hardani wlh
Alhaj yace aiko tare muke DA baqo tace ya shigo mana tace sannunku DA Zuwa suka shiga suna amsawa DA murmushinsu
Wani katafaren falo ta kaisu an rufeshi DA wani koriyan kafet ga kayan kallo DA wani makeken flasma a liqe a jikin bango
Alhaj yace kun ganmu kamar daga sama KO Ina fatan dai sulaiman din nanan tana murmushi tace ai kuwa yananan Bari na tasoshi don yanxu ya kwanta yac to madallah Ina yaran? Tace suma yanxu suka tafi kitso nan makwabta ta wuce yana fading yayi kyau
Shi kuwa malam Saddiqa mamakine ya isheshi ya shigayima kansa tambayoyi daman can alhaj yasan iyayen jamila ne? DA alamun sun Saba DA juna to me zai kawo ja inja a tsakaninsu akan Neman aure ?yanatayima kansa wadannan tambayoyin
Murja ta fada dakin Mai gidanta
Kwance yake akan katafaren gadonsa DA alamun ya fara nisa a Cikin barcin DA yake
Ita kanta tayi shakkar tashinsa saidai ya zama dole tunda babban baqo yayi
Ta zauna a gefensa gamida bubbugashi firgiggit ya tashi Ido jajir
Ya bita DA kallo fuskar sa a yamutse Cikin sababi yace amman dai kinsan na tsani wannan iskancin KO? Ina zaune tun dazun bakiyi magananar DA zakiyiba saida barci ya daukeni ?
Yaja dogon tsaki yana qoqarin juyawa domin komawa barcin tace mada wuqar ranka ya Dade babane yaxo ya qara yamutse fuska wane Baban?
Face Baban Kaduna mana yai wuf ya tashi zaune ya qura mata Ido don rashin yarda hakan yasa tace masa harda mudassir DA wanI magidanci haka
WanI mutum to me Zan musu?ta tabe baki oho saika taso kaji KO meke tafe dasu ya qara zaRo tsaki wannan bala,I DA yawa yake kema kinsan maganan jamila sukaxo ni ban wuri in sauka yau za,a yita ta qare Domin banson baqin naci ta miqe a hankali tana karya wuya a.a Baban jamila……
Ya daga mata hannu ba ruwanki ta numfasa tana kallonsa ya qarqare ya sauka daga kan gadon jallabiya ya zaro ya saka
DA Fara,arta ta taho falon sannunkufa baba gashinan Zuwa yanxu barcinne ya Fara daukarsa Shannan ta wuce
Fuska daure ya fito babu KO walwala a tare dashi sannunku DA Zuma baba alhaj abdulrrashid ya bishi DA kallo a sanda yake amsawa yace an tasoka kana barci KO?yayi yaqe yace ai banjima Da Fara barcinba kunxo fly?bai gama amsawaba murja ta shigo DA ruwan sanyi bayan sunsha ruwan alhaj yace Yanxu sallah zanuyi don haka aka fito musu DA butoci a Cikin koridon gidan banyan sun kallama sallan ne SBD iskan dake wajen kawai sukai zamansu a wajen suleman ne ya sake fitowa ya samesu yaga KO wannensu sai uban hammah suke DA alamanu yinwane DA gajiya kawai me addabarsu Amman da alamar wannan tunanin bai zo zuciyar sulaiman ba domin zamansa keda wuya ya Fara DA cewa banyi zaton zuwankuba baba wani abune ya faru?
Alhaj ya gyara zama yace hakane Amman DA farko wanna shine malam Saddiqa zumunci Mai qarfi ya kullu a tsakaninmu Kuma nadaukeshi kamar DA a gareni shiyasa na nemeshi DA yaimin rakiya ba komaine ke tafe damuba illa maganar jamila
Inason sanin Ina ta kwana ne
Domin imam ya damu matuqa tun dawowarta baisan inda aka dosa ba dalilin DA yasa na taso kenan DA kaina domain jamila DA imam duk Daya suke a wurinmu
Ya muskuta gamidayin wanI banzan guntun murmushi Mai fassara Kala Kala kamin yace baba kamata yayI kamin Ku taso ace kun kirani a waya ka gaya m….. Kallon DA kowa yai masa ya sa shi gimtse sauran maganar dake baking NASA
Ya dubi alhaj din babu kunya bare shakkah yaci gaba ai gaskiyane Kumar kunso kusha wahalane kawai domin babu abinda imam din bai saniba jamila karatu zatayi
Baya ga haka Kumarl nida kaina na tuntubeta tacemin imam bai kwanta mata ba gaskia baba babu yar boye boye ni bazan yi mata dole ba duk Wanda ta kawo banyan ta kammala karatunta ni shi Zan bata SBD haka ni inabama imam shawara akan Kawai ya nemi wata zaifi masa daya tsaya yana bata ma kansa lokaci koba gaskia ba ya fadi yana duban malam Saddiqa
Ya kada Kai cike DA dumnin mamaki yace gaskiyane Allah ya hada kowa DA rabonsa aishi Al,amarin aure shirine na ubangiji Kamar kullun abinda yafi zama alkhairi mushi muke nema a wajen Allah
Alhaj abdurrashid ya sauke numfashi a raunane yace wanna haka yake Amman sulaiman Al,amarinka yaban mamaki ya kuma dauremin Kai fiye DA tunaninka saidai babu abinda Zan Iya face ince dakai rayuwace na jima Ina karatu a MAKARANTAR DUNIYA
Amman ban taba cin Karo DA darasin Daya gigitaniba irin nayauba
Babu komai kamar yaddah malam Sadiq yace alkhairi muke nema Allah yasa hakan shine farinciki DA kwanciyar hankalinmu
Kansa tsaye yace amin ya miqe ya shiga cikin Gida ya barsu nan jiki a mace
Ba Wanda ya sake cewa komai mudassir ya katse shirun DA fadin baba mu tashi mu tafi Gida kar dare yai mana
Malam Saddiqa yace kayi magana mudassir zamanmu anan baida wanI amfani
Alhaj bai furta komaiba sulaiman ya sake dawowa banyan ya sauya kayan jikinsa ya tsaya a Kansu yace baba ni an kirani a office Zan tafi saidai bakuyi waya zakuxoba shiyasa ba,ai abinci dakuba Amman zata Dora na dare dan anjima kadan na tafi saina dawo
Alhj yace dashI a dawo fly sulaiman ya amsa da Allah yasa Sannan ya dambara wani baqin Gilas dinsa Sannan ya nufi inda motocinsa ke ajiye har guda hudu ya bude wata civic Mai ruwan siminti ya bata wuta Sannan yabar harabar kwatas din
Lol
Naku had kullun
The. C. E. O. @littafan Hausa zallah