MAKIRCI KO ASIRI CHAPTER 2

MAKIRCI KO ASIRI.
CHAPTER 2

Shiru Ramlah tayi dan tabbas tasan Haneefa gaskia take fad’a mata dole ta tashi tsaye da adu’a dan matar nan da alamun batazo da zaman lafiya ba, ita har mamakin Haneefa takeyi a iya shekarunta amma tasan ama wani abinda bai dace ba….
    Tana shiga d’aki tajawo waya ringing biyu aka d’auka
“Hello Lash kina ina?”
Banji mi akace ba,
“Ok kizo gidana yanzu ina san ganinki”, tana fad’ar haka ta datse call d’in, tashi tayi ta dinga zurga zurga cikin d’akin
“Hmmm Ramlah zaki raina kanki dake da marar kunyar d’iyarkin nan zaku san wacece Mufeedah yar ruwan zafi baka tab’ani bama na k’ona ka bare ka tab’ani da nayi niyar in d’an barku amma naga d’iyarki tsaye take to dole zanyi maganinku da wuri sai na mai daku abun tausai a gari…
    Haka ta dinga zagaye d’aki tana sabbatu ita kadai..
                        *******
     Banko k’ofa tayi ta shigo ko sallama babu
“Lafiya Mufeedah?”
Sai a sannan ta juyo, murmushi tayi taja hannunta suka zauna bakin gado…
    “Ina jinki fad’aman ko hankalina ya kwanta”
Dafa kafad’arta tayi tace
“Akwai matsala”
“Matsala?”
“Eh matsala”
“To matsalarmi ke da aka kawo jiya wace irin matsala kenan kodai ya gane ba budurwa ya sameki ba ya maki wulakanci?”
Dariya tayi tace
“Tabbas ya gane ba cikakka nake ba sai dai kinsan baida hurumin ya man maganar ko ya canjaman saboda boka yaman aiki akan haka…”
  Numfasawa tayi tace
“To kodai kin had’u da hatsabibiyar kishiya wadda tafiki MAKIRCI?”
Wata dariya ta saki tace
“Kina tunani akwai wadda zata fini makirci kuwa? Toh in gaya maki ba haka Ramlah take ba in gaya maki kwana d’aya nayi da ita amma nasan wacece ita mace ce mai hak’uri da kawaici.”
   Kallo ta bita dashi tace
“Ramlah ki fitoman a mutum ban san inda kika nufa ba…”
    Gyara zama tayi tace
matsalar daga d’iyarshi ne”
“D’iyarshi?”
“Eh”
“Dama yana da d’iya babba ne?”
   Girgiza kai tayi tace
Bazata wuce shekara goma ba”
Dasauri Lash ta mik’e tace
“Shekara 10?”
“Eh”
“Ke ko wace lalacewa tazo maki da yarinyar cikinki zata tada maki hankali?”..3
    Zaunar da ita tayi tace
“Kinfi kowa sanin wacece Mufeedah yar ruwan zafi ban da tsoro ko kad’an baka tab’ani ba na k’onaka bare ka tab’ani, kinfi kowa sanin dalilin dayasa na shigo rayuwar Imran na shigone dan na rabashi da farin ciki in tarwatsa gidanshi, da nayi niyar in d’an d’aga masu k’afa amma wannan mara kunyar yarinyar tasa dole zanyi maganinsu da wuri….”
  Ajiyan zuciya tayi tace
“Naji amma mi yarinyar ta maki?”
   Zama ta gyara ta kwashe komai duk abinda ya faru ta gaya mata…
   Dariya Lash tayi tace
“To yanzu miye abinyi?”
     Murmushi tayi tace
“Yauwa yar gari yanzu kikayi magana, wajen boka nake san kije ki gaya mashi komai karki rage komai kice nace so nake ya tarwatsasu ya hana masu farin ciki ya dasa masu bak’in ciki har k’arshen rayuwarsu kingani yanzu babu yanda za’ayi na fita tun da jiya kuka kawoni..”
   (Wa iya zu billahi mi mutane suka d’auki duniya? Shin ko sun manta ana mutuwa ne? Idan ka hana wani farin ciki ribar mi kaci? Kar mu manta akwai ranar sakayya ko Allah bai saka ma wanda ka cuta duniya ba wallahi sai ya saka mashi ranan gobe k’iya, Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu..)
   Wata irin dariya Lash tayi tace
“Buk’atarki ta biya, sai dai kinsan saikin kashe kud’i ko?”
Dariya tayi tace
“Kud’i ba matsala ta bace ba ke kin sani”
  Tana gama fad’an haka ta mik’e ta nufi wardrobe d’inta kud’i ta d’auko rapper 1k guda biyu ta wurga matasu tace
“Nasan zasu isheki”
Dariya tayi tace
“Harda canji ma kuwa.. “
     Shewa sukayi suka tab’a…
Kallonta Lash tayi tace
“Bari na wuce kinsan da safe ake kamun fara dan haka yanzu daga nan can na nufa..”
  Rungemata Mufeedah tayi tace
“Shiyasa nake sanki Aminiyata samunki a rayuwata babban alkairi ne…
    Jakarta ta d’auka suka fito bakin kitchen suka had’u da Ramlah tana ganinsu ta washe baki kallon Mufeedah lash tayi tace
“Kar dai kiceman wannan ce kishiyar taki?”
   Tab’e baki tayi tace
“Itace”
Dariya Lash tayi tace
“Bakida kishiya wannan ay bata da maraba da mai aiki”
Shewa sukayi suka tab’a
   Lash takai dubanta ga Ramlah tace
“Hajiya ina fatan kin shirya kishi damu danmu kishi damu sai mutum ya shirya…”
Tana fad’an haka suka wurga mata harara suka fita..
  Jiki sanyaye Ramlah taja jiki ta koma kitchen..
   Suna fita ta kalli Ramlah tace
“Amma matar nan akwai kyau”
Tab’e baki tayi tace
“Tana da kyau”
  Dariya tayi tace
“Dakyar na iya kallonta na gaya mata magana dan kwarjini taman wallahi”
   Harararta tayi tace
“Malama ki wuce dan ki dawo da wuri”
   sallama ta mata tayi gaba….
                         ********
    Tafiya takeyi ciki  k’urmin daji ba gida gaba ba gida baya sai da tayi tafiya sosai kana ta iso bakin wata bukka, ita kad’ai ce bukka a wajen.
  “Gafaranku dai”
Abinda tace kenan
   Shigo daga ciki, shiga tayi tana kirari, takai minti goma da shiga kana ya mata izinin zama, waje tasamu ta zauna..
   “Allah ya taimaki boka”
Mutum ne bak’ik’irin idanuwanshi jajaye ya daka mata tsawa yace
“Ba’a kira mana Allah anan ko kin mance dokar wannan bukar ne?”
  Jiki na kyarma tace
“Aiman afuwa boka na mance ne”
  Kai ya d’aga mata batare da yayi magana ba..
  “Mike tafe dake?”
Zama ta gyara tace
“Boka ba zuwan kaina bane ba zuwan Mufeedah ne..”
Hak’oranshi ya washe wanda sukayi jawur yace
“Amarya zakice man lafiya take ko?”
Dariya tayi tace
“Lafiya lau”
Dama boka so take… ta kwashe komai ta gaya mashi…
   Wata irin dariya ya kwashe da ita yace
“Aikinta mai sauk’i ne ita kuma Haneefa ba zamu kasheta yanzu ba sai sun d’and’ani wahalar rayuwa kana daga baya zamu kaudasu d’aya bayan d’aya..”
  Baki Lash ta lashe tace
“Godiya muke boka”
    Wani magani ya d’auko a wata kwarya yace
“Kice mata wannan ta wanke gabanta dashi idan ta wanke ruwan ta mashi girki ta tabbata daidai shi tayi girkin dan ba’a buk’atar wani yaci girkin sai shi idan tayi yanda mukace to sai yanda tayi dashi, wata kwarya ya d’auko yace wannan kuma kwaryan ta saka a k’ark’ashin gadonshi to zai tsani Matarshi da yaranshi zaiji bai san ganinsu..”
    Godiya Lash ta mashi ta karb’a ta aje mashi rapper 1k guda yana gani ya washe jajawur d’in hak’oranshi..
   Sallama ta mashi ta fita, saida tayi tafiyar awa guda kana ta iso bakin titi mai napep ta tsaida tace
  “Katsina zaka kaini”
Kallonta yayi yace
“Hajiya katsina fa maimakon ki hau mota ko kin manta daga inda kike in kin manta bari na tuna maki charanci kike kuma da alama daga k’auyen d’an turu kike”
   Dariya tayi tace
“Ka kaini in baka dubu biyar..”
Baki ya washe yace
“Shigo muje..”
Shiga tayi suka tafi….
   Sai da yahau titi sosai ya juyo ya kalleta yace
“Amma malama mi yakaiki k’auyen d’an turu? Nidai a sanina babu gidaje sai bukkar boka dumbus kuma da alamu ke macen arzik’i ce nayi mamakin dana ganki kin fito daga k’auyen”
  Tsawa ta daka mashi tace
“Idan tambayoyi zakaman ajeni in sami wata..”
“Allah ya baki hak’uri”
Abinda yace kenan yaja bakinshi yayi shiru….
11
Ana wata ga wata shin Mufeedah zatayi nasaran raba Ramlah da farin cikinta? Dagaske Imran zai juyama Ramlah baya da yaran da yafiso a rayuwa? Ya makomar Mufeedah daga k’arshe? Ku cigaba da yar mutan katsinawa dan jin amsoshinku…
   Mik’a mata magungunan tayi ta mata bayani yanda boka yace, kallonta tayi tace
“Mufeedah abubuwanan suna da had’ari sai kin kiyaye dan karmu samu matsala.”
   Dariya tayi tace
“Kinsan yanda nake bin dokar boka ko ta maifiyata banabi so karki sa damuwa ba wata matsalar da za’a samu saboda ni kullum mai sa’a ce…”
   Jinjina kai Lash tayi dan tasan makircin Mufeedah duk abinda tasa gaba to sai tayi nasara, a kullum ita mainasarace…
   Jakarta ta d’auka tace
“Bari na wuce gida kar dare yayi..”
   Tare suka fito, parlour sukaci karo da Imran na shigowa daidai Ramlah na jera abinci a dainning, dasauri Mufeedah ta isa wajen Ramlah tace
“Haba Anty da kin barshi na k’arasa jerawa ai bak’uwar ba dad’ewa zatayi ba”
Mamakine ya kama Ramlah
“Tabbas duk inda Makira takai yarinyar nan takai.”
A zahiri kuma tace
“Kibarshi na k’arasa kinsan ke amarya ce..”
   Dariya sukayi baki d’aya dai dai Imran na k’arasowa wajensu tare da washe baki ganin yanda Mufeedah kesan Ramlah…
   “Sannunku da gida”
“Yauwa suka amsa dashi”
  Kitchen ta nufa da sauri ta d’auko sauran warmers d’in, ta aje a dainning, binta da ido Ramlah tayi tana mamakin yanda take rawan kai kamar ba ita ke gasa mata magana ba, da kyar tace
“K’awarki na jiranki”
  Juyawa tayi inda Lash ke tsaye ta kashe mata ido, Lash kuwa ta daskare dan mamaki tace
“Harna manta da ita”
Tana fad’an haka ta k’arasa wajen Lash taja hannunta suka fita….
  Suna fita Lash ta kalleta
“Mihakan ke nufi? Nasan dai wani sabon abun ne zakiyi”
Dariya Mufeedah tayi tace
“Dad’ina dake saurin ganewa dole sai na had’a da kissa da MAKIRCI ai asiri kad’ai bazaiyi tasiri ba dole sai na had’a danawa to gaban idan mijin zan nuna nafisan su akaina kinga bayan shi in gasasu yanda raina keso ko fad’a mai tayi bazai yarda ba…”
  Dariya Lash tayi tace
“Nikaina ina tsoronki”
Tafawa sukayi ta mata sallama ta tafi ita kuma ta koma cikin gida….
   Tana shiga parlour idanta yakai kansu, rungume take jikinshi yana shafa kanta, wani bak’in ciki ya taso mata amma ba yanda zatayi
  “Nan da wasu yan lokaci zan maidaki abin tausai zai tsaneki fiye da komai a duniya…”
  K’arasawa tayi ciki da sallama, saurin sakin Ramlah yayi ya juyo yana mata murmushi, itama murmushin takeyi ta isa wajen Ramlah tace
“Anty baki buk’atar komai?”
  Daskarewa Ramlah tayi da kyar ta tattaro kalaman bakinta ta had’a tace
“Bani buk’atar komai nagode”…
  Imran ya kalli matanshi yace
“Nagode sosai yanda kuka had’a kanku Allah ya maku albarka”
“Amin”
Mufeedah ta amsa, ita dai Ramlah ta zama yar kallo..
  “Kuje kuyi sallah nima masallaci zan wuce”
  Yana fad’an haka ya juya ya fita
   Kallonta Mufeedah tayi tace
“Kin kusa raina kanki a gidannan sai na zame maki k’adangaren bakin tulu”
Tana fad’an haka ta buga mata tsaki ta wuce d’akinta….
   Kai Ramlah ta girgiza tace
“Allah ya fiki”
Tana fad’an haka ta shige d’akin yaranta…
   Tana shiga suka taso da gudu sukayi kanta, rungumesu tayi wasu kwalla na gangaro mata, Haneefa na kallonta, sallah da aka kira ne yasa ta sakesu tace
“Kuje kuyi alwalla kubi Daddynku masallaci Haneefa ke kuma ki tashi kije kiyi alwalla…”
  Ba musu suka tashi sukayi alwalla suka fita dan tafiya masallaci..
  Juyawa tayi zata nufi d’akinta
“Ammi”
Haneefa ta kirata
   Juyowa tayo da fara’arta tace
“Yadai princess?”
   Takowa tayi ta k’araso wajenta tace
“Ammi kina cikin damuwa ki dage da adua in shaa Allah, Allah na tare damu..”
   Duk’awa tayi ta rik’o hannunta tace
“Ina alfahari da samunki a matsayin d’iyata Allah ya maki albarka..”
“Amin”
   Tace ta wuce ta tada sallah..
   D’akinta ta nufa tana shiga ta fad’a toilet tayo alwala tana fitowa ta tada sallah tana idawa ta d’aga hannunta sama tana adu’a bata tashi daga kan carpet ba sai da tayi sallah isha kana ta tashi ta ninnike abin sallah…
                         *******
   Parlour suka had’u gaba d’aya suka nufi dainning table suka zauna su Haneef suka gaida ko da kyar Haneefa ta iya gaida Mufeedah, Ramlah ta mik’e zata zuba masu abinci dasauri Mufeedah ta amshe serving spoon d’in   tace
“Anty gani zakiyi aiki”
  Binta da ido Ramlah tayi  dan yanzu abun nata ya daina bata mamaki, yak’e tayi ta zauna, da kanta ta zuzuba masu kowa ta aje mashi gabanshi, abinci suka faraci bamai magana har saida suka gama, Haneefa ta mik’e zata wuce, hannunta ya rik’e yace
“Princess anya kina da lafiya?”
   Yak’e tayi tace
“Daddy lafiya lau”
  Murmushi yayi ya saketa…
  “Amm Anty kibari gobe zanma Baban Haneefa abinci da kaina so ke sai kiyi namu kar abun ya maki yawa..”
   Bata kawo komai a ranta ba tace
“Shikenan Allah ya kaimu..”
   Wani farin ciki ne ya lullubeta na samun nasara..
   Kallonshi tayi tace
“Honey bari naje nayi wanka kafin ka shigo”
  Tana kaiwa nan ta tashi tabar parlour’n..
   Dasauri ta isa d’akinta ta d’auki kwarya ta d’an corridor tabi ta shiga d’akinshi, saida ta saka key a k’ofar kana ta dawo ta d’aga katifan da kyar ta iya d’agata ta saka kwaryan ta mai da katifan, ta gyara gadon kamar ba’ayi komai ba, ta lallab’a ta bud’e k’ofan kana ta wuce d’akinta tsalle ta buga na samun nasara tace
   “Saura kaci abincin gobe..”
   Juyi tayi tace
“Kullum ni mainasara ce kuma zan cigaba dayin nasara, Ramlah namaki alk’awarin tarwatsa farin cikinki kuma nasan nike da nasara…”
  Haka ta dunga surutanta tana murna ganin ta kusa nasara….
K’arfe bakwai ta tashi ta nufi d’akinta, tana shiga ta wuce inda ta aje maganin d’auka tayi ta nufi toilet wanke gabanta tayi tas kana ta d’auki ruwan maganin ta nufi kitchen dashi, tana isa k’ofar kitchen taci karo da Ramlah na shirya breakfast, wani takaici taji, komawa tayi d’akinta ta adana ruwan, saida ta tabbatar Ramlah ta gama ta koma wajen yaranta dan suyi shirin makaranta, da sauri ta nufi kitchen ta d’ora taliya dan danan ta had’a taliya, tuni kitchen ya d’auki k’amshi dan ta saka kayan k’amshi sosai yanda bazai gane akwai wani abu….
Mintuna kad’an ta juye taliyan cikin warmers ta ta had’a mashi tea da yaji kayan k’amshi shima tea sai data zuba ruwan tsarkinta, komai na mutum guda tayi kana ta kwasa ta nufi d’akinshi dashi tana mai neman Allah ya bata nasara yaci abincin nan…+
Tana shiga d’aki ta tar da yana bacci, a hankali ta yaye blanket d’in daya rufa, iska take hura mashi a gashin kanshi har sai daya bud’e idonshi, idonshi bisa fuskarta tana sakar mashi murmushi, shima murmushin yake mata, hannu ta mik’a mashi ba musu ya mik’o mata ta kamashi, bakin toilet ta kaishi ta kalleshi tace
“Kayi wanka kazo ga breakfast d’inka yau girkina zakaci..”
Tana magana tana kashe mashi ido..
“Angama amaryata”
Ya fad’a yana dariya…
Fitowa yayi yana tsane jikinshi da towel k’arasowa tayi ta k’arba ta tayashi gogewa, da taimakonta Imran ya shirya, yana gama shiri tace
“Ga abinci”
Kallonta yayi da mamaki yace
“Abinci kuma? Ayba nan nake cin abinci ba”
“Nasani amma yau nan zakaci”
Ta fad’a tana b’ata rai, babu yanda ya iya illa yabi umurninta…
Zama yayi ta zuba mashi taliya, ta had’a mashi tea ta mik’a mashi gabanshi, ba musu ya faracin abincin yanaci yana zuba mata santi saida ya cinye tas ya sha tea, wani irin farin ciki Mufeedah take ciki wanda bata iya misaltashi…
Yana gama cin abinci yaji kanshi yayi nauyi jikinshi duk ya mutu kallonta yayi yace
“Bari nad’an kwanta”
Kafin ta amsashi har ya fad’a kan gado..
Mik’ewa tayi tazo wajenshi ta tab’ashi amma ina yayi nisa, tsalle tayi tana rawa tace
“Yau zan fara aikina da alama maganin nan yayi aiki..”
*******
K’arfe shida ya tashi ji yake jikinshi duk ya mashi wani iri toilet ya shiga yayi wanka ya d’auro alwalla, zuwa yayi ya tada sallah sai da yayi azahar kana ya maida la’asar, shigowa tayi cikin k’ana nan kaya riga da wando (kamar sanda ta sa wando lolzz), yana ganinta yaji duk k’uncin da yake ciki ya yaye, ware mata hannu yayi da yar kisisinarta ta isa wajenshi rungumeta yayi tare da a jiyar zuciya..
“Shine baki tadani nayi sallah ba”
Cewar Imran yana d’ago Mufeedah daga k’irjinshi
Fari ta mashi da ido tace
“Kasan idan mutum na bacci ba’a ta dashi”
(Niko nace inji wane malamin ya gaya mata haka ai sallah na gaba da komai..)
“Bari naje naga Ahmad”
Shagwab’ewa tayi tace
“Nidai ba inda zaka”
Jawota yayi yace
“Ba dad’ewa zanyi ba yanzu zan dawo kinji my babe..”
D’aga mashi kai tayi…
A tare suka fito a parlour suka had’u dasu Ramlah ji yayi gabanshi ya fad’i wani irin tsanarta yaji da yaran kwatakwata bai san ganinsu, d’auke kanshi yayi daga inda suke..
“Sannu da fitowa”
Cewar Ramlah
Shiru yayi bai tanka ba kuma bai kalli inda suke ba, murmushi Mufeedah tayi tace
“Baby ana magana fa”
Naji abinda yace kenan
Mukhtar ne ya ruga wajenshi ya rungume shi yana Daddy, jefar dashi yayi kan carpet har saida kanshi ya fashe yana huci…
Dasauri Ramlah ta k’araso tace
“Imran lafiyarka kuwa?”
Harara ya wurga mata yace
“Natsaneku dagake har shegun yaranki, ki gaya masu su daina shiga harkata kuma kada ubanda ya k’ara kirana Daddy Wallahi na tsani ganinku gidannan ji nake kamar in bud’e idona inga kun mutu..”
Wani irin kuka Ramlah ta saki tare da rungume Mukhtar shima kukan yake, ganin haka yasa Haneef fashewa da kuka..
K’arasowa Haneefa tayi tace
“Daddy mikake shirinyi? Kamanta suwaye mu? Yaranka ne dakafi k’auna sai kuma Ammi da duk duniya kake cewa baka da kamart….”
Tsawar daya daka matane yasa sauran maganar tamak’ale..
“Nace na tsaneku bansan ganinku ko bakiji bane ba?”
Gabanshi Mufeedah ta k’araso tace
“Calm down my baby abun duk bai kai haka ba, kayi hak’uri inma wani laifin suka maka kayafe masu…”
Hararta yayi yaja hannunta suka fita suka bar parlour’n, rungume yaranta Ramlah tayi tana kuka suma kukan sukeyi banda Haneefa da idonta yayi ja kamar garwashi saboda tsananin b’acin rai…
annunta ta fizge tace
“Miye haka kakeyi? Mi suka maka idan wani laifin suka maka ai ba haka zaka hukun tasu ba ji yanda ka fashema Mukhtar kai..”
Baki ya tab’e yace
“Ni basuyi man komai ba kawai natsanesu bank’i in bud’e idona inga basu gidannan ba..”
“To ka saketa mana basai su barma gidan ba”
Ido ya zaro yace
“Ban iya sakinta bansan miyasa ba amma bansan ganinta..”
“Ina da aiki gabana”
Abinda ta fad’a a ranta kenan, murmushi ta mashi tace
“Ya kamata ka tafi kada ya dinga jiranka..”
Ba musu ya mata peck ya juya ya tafi, ita kuma ta koma cikin gida…
Shiga tayi tana wak’e wak’e wuce su tayi takai k’ofar d’akinta ta dawo duk’awa tayi gaban Ramlah
“Dama nace zaki raina kanki kad’an kika gani daga aikin Mufeedah yar ruwan zafi kinga wannan gidan da kike tak’ama dashi sai kin fita kin barshi..”
Tana fad’an haka ta mik’e tana dariyar mugunta..
“Ke baki isa ki mana abinda Allah bai mana ba kuma gidan da kike tak’ama zamu bari ke zaki barshi da izinin Allah muda Allah muka dogara kuma shi zai mana maganinki cikin ruwan sanyi..”
Haneefa ce ke magana tana huci…
Juyowa tayi ta kalleta tace
” kina burgeni saboda kwazonki amma kwanannan zanyi maganinki dan na lura kece matsalata..”
D’agowa Ramlah tayi ta kalleta sannan tayi magana
“Baki isa ki mata abinda Allah bai mata ba da Allah muka dogara kuma yana tare damu…”
Dariya ta kwashe da ita tace
“Zan gani ni daku wanda zaiyi nasara”
Tana kaiwa nan ta shige d’akinta…
Rungume yaranta tayi ta fashe da kuka..
“Ammi yanzu ba lokacin kuka baneba lokacin da zaki kwaci gidanki ne da martabarki idan kikace kuka zakiyi bazai amfana mana komai ba muna gani zatayi galaba akanmu kamar yanda ta fad’a..”
Tana kaiwa nan ta mik’e ta wuce d’akin Amminta..
“Tabbas maganar Haneefa gaskiya ne yanzu ba lokacin da zanyi kuka baneba lokacin da zan dawo da martaban gidana da mijina ne hannuna amma taya?”
Duk a zuciya take wannan tunanin..
Haneefa ce ta fito da first aid box ta gyarama Mukhtar inda yaji ciwo, ta kwashe kayan da tayi amfani dasu ta maida d’akin Ammi..
Tana shiga d’aki ta dinga zagaye zagaye
“Dole nad’auki mataki kan Haneefa dan zata kawoman cikas..”
Wayarta ta jawo ta kira Lash, saida ta kusa tsinkewa kana ta d’auka
“Hello Lash akwai matsala”
Banji mitace mata ba tace
“Inasan ki koma wajen Boka Dumbus a kauda man da Haneefa daga duniya saboda tana kawoman matsala yariyar na tsaneta kawai ya kasheta…”
Tana gama fad’ar haka ta katse wayar ta cigaba da zagaye d’aki burinta kawai taga Haneefa tabar duniya to komi zaizo mata dasauki…
******
Rungume take da Mukhtar wanda yayi baccin wahala gefe Haneef ne shima yayi bacci, zuwa Haneefa tayi ta kwashesu ta kaisu d’aki ta kwantar dasu, kitchen taje ta had’oma Ramlah tea ta kawo mata tace
“Ammi gashi kisha”
Karb’a tayi ta mata yak’en da yafi kuka ciwo
“Nagode Allah ya maki albarka ya rabaku da sharrin mutum da Aljan Allah ya karemanku..”
“Amin”
Haneefa ta amsa
Kafa cup d’in tayi bata ajeba saida ta shanye tayi hamdala, juyowa tayi wajen Haneefa ta rik’e hannunta tace
“Haneefa kidaina ma Mufeedah rashin kunya ina tsoron karta maki wani abu kinji kalamanta bansan yanda ta rabamu da Imran ta maki illa kema dan Allah kidaina shiga harkanta duk abinda zatayi kidaina tanka mata ina tsoron ta illatamanke bansan ta rabani dake kune farin cikina yanzu..”
Kukan da yaci k’arfinta ne yafito. Dakyar Haneefa ta lallasheta tayi shiru..
“Ammi kidaina sakawa a ranki zataman wani abu Wallahi babu abinda zataman duk abinda kika ga ya sameni to dama can Allah ya rubuta zai sameni, kedai ki cigaba da mana adu’a saboda adu’arki takobi ce ga duk mai binmu da sharri..”
Rungumota Ramlah tayi ta k’ank’ameta kamar wani zai kwace mata ita, sabon kuka ta fashe dashi mai tsananin damuwa, duk dauriyan Haneefa saida tayi kuka itama sun dad’e haka kana Ramlah ta saketa ta tashi ta nufi d’akinta…
Tana fita ta had’u da Imran yadawo sauri yayi ya k’auda kanshi.
“Sannu da zuwa”
Shiru yayi ya cigaba da tafiya, sauri tayi tasha gabanshi tace
“Dan Allah idan laifi na maka kayi hak’uri kada ka hukunta ni da abinda bansan na aikata ba kuma laifina bai kamata ya shafi yaranka ba kaga yanda kajima Mukhtar ciwo yaro ne baisan komai ba..”
Hannu ya d’aga mata
“Ba abinda kuka man kawai na tsaneku da zaki taimaka keda yaranki kun fita harkana ko gaidani kada ku sakeyi Wallahi na tsani ganinku..”
Yana fad’an haka ya rab’ata ya wuce, duk’ewa tayi k’asa tana kuka ganin kukan ba maganin da zai mata yasa taja ka’afafuwanta ta wuce d’akinta…
Duk abinda yafaru kan idon Mufeedah murmushi tayi mai k’unshe da ma’ana kala kala kafin ta koma d’aki…
K’arasowa wajenshi tayi yana ganinta ya saki murmushi, rungumeta yayi ya saki ajiyar zuciya, janshi tayi ta kaishi d’aki.
“Had’aman ruwan wanka”
Cewar Imran yana kallon Mufeedah
Turo baki tayi tace
“Gaskiya nagaji kawai kaje ka had’a nifa bazan iya yan had’e had’en ruwan wankan nan”
Babu yanda ya iya ya tashi ya nufi toilet…+
Fitowa yayi ko inda yake bata kalla ba sai cika take tana batsewa haka ya shirya kanshi yazo ya zauna kusa da ita
“Miyafaru ne?”
Naga kamar kina cikin damuwa, fashewa tayi da kuka tace
“Bayan ka fita Ramlah da Haneefa suka tusani gaba suna zagi kamar ni nace ka tsanesu Ramlah harda marina ita kuma Haneefa tana cewa wai karuwace ni har ciki na zubar kana nazo na aure ka..”
Bata k’arasaba ya tashi yana huci ya nufi d’akin Ramlah
“Ramlah! Ramlah!! Ramlah!!”
Kwalamata kira yakeyi kamar zai tada gidan, k’arasowa tayi dasauri tace
“Lafiya Imran?”
Saukar mari taji a kuncinta kafin ta ankara ya k’ara kwasheta da mari sai da ta saki k’ara d’agowa tayi tace
“Imran mina maka?”
“Aww baki masan mi kikayi ba?”
D’aga kai tayi alamar bata sani ba
“Ubanwa yace ku zagar man mata keda d’iyarki? Har d’iyarki na kiranta karuwa to sai dai idan kece karuwa”
Dasauri ta kalli inda Mufeedah ke tsaye ta hard’e hannuwa tana murmushi, kashe mata ido Mufeedah tayi tana dariyan mugunta. Girgiza kai tayi tace
“Wallahi ba abinda mukayi mata”
“Aww k’arya zata maki lallai Ramlah kin cika annamimiya..”
Hawaye suka kwararo mata tace
“Iya gaskiyata na fad’a maka..”
Cakumota yayi ya d’aga hannu zai k’ara marinta
“Daddy”
jin muryan Haneefa yasa ya kasa k’arasa marin Ramlah wanda takai k’asa sanadiyar hankad’ata da yayi…
K’arasowa tayi inda yake tsaye yana huci, kallonshi tayi tace
“Daddy ka canja ba haka ka saba mana ba baka tab’a yima Ammi fad’a a gabanmu ba, yau gashi kan wata ta nuna Mufeedah tace ka d’auki hannu ka mareta ka jefeta da munanan kalamai akan abinda bata sani ba shin baka gudun Allah ya mata sakayya?” Wallahi Daddy Ammi bata tab’a d’aga ido ta kalli matarka ba da sunan cin fuska amma yau an gaya maka magana ba bincike ka d’aga hannu ka mareta ka aibata ta wanda kafi kowa sanin halin matarka kasan abinda zata iya, ka d’auki hannu ka mareta duk akan wannan munafukar matar taka…”
D’agowa yayi da sauri zai kai ma Haneefa mari sai kuma ya fasa dan duk cikin yaranshi yafisan Haneefa bai san abinda zai tab’ata..
Murmushi tayi tace
“Ni yaka mata ka mara ba Ammi ba saboda Ammi bata da laifi nike gayama matarka magana a yayinda taci fuskar mahaifiyata kuma kasan duk d’an halak bazai bari aci mutuncin mahaifiyarshi ba kuma ban tab’a kiran matarka da karuwa ba kafi kowa sanin irin tarbiyan da kuka bamu…”
Tana fad’an haka ta d’aga Ammi dake ta hawaye suka wuce har sun kai bakin k’ofa ta saki Ammi ta juyo wajen Imran ta duk’a tace
“Daddy idan maganganun dana maka sun b’ata maka rai dan Allah kayafeman, idan wani laifi muka maka muda mahaifiyarmu dan Allah kayi hak’uri kuma da kace baka sanmu ka tsanemu Wallahi mu munasanka muna fatan kadawo Daddynmu nada mai wasa damu mai maida damuwarmu damuwarshi wanda yafi sanmu a kanshi wanda bai iya cin abinci sai muna gabanshi, juyawa tayi wajen Mufeedah tace kinyi nasara amma kijira ranan sakamako Wallahi k’arshenki bazaiyi kyau ba…”
Tana gama fad’an haka ta mik’e takama mahaifiyarta ta kaita d’aki…
Huci Mufeedah keyi tace
“Kanajin yanda d’iyarka ke gayaman magana amma ka kasa d’aukar mataki”
Kallon ta yayi yace
“Bansan miyasa bazan iya bugun Haneefa ba bazan iya aibatata ba Haneefa d’iyatace bazan iya yi mata komai ba kawai dai nasan natsanesu amma bazan iya dukanta ba..”
Harararshi tayi ta buga tsaki ta nufi d’akinta binta yayi yana kira amma bata tanka ba tana shiga ta maida k’ofa ta rufe tanaji yana magiya yana rok’onta amma tak’i kulashi….
K’afafuwanshi yaja ya nufi d’akinshi yana zuwa ya fad’a kan gado yana juyi shi kanshi yasan akwai abinda ke damunshi amma bai sani ba haka ya dinga juyi har bacci ya d’aukeshi..
B’an garen Haneefa kuwa suna shiga d’aki ta fad’a kan Ramlah tana kuka cikin kuka tace
“Ammi kinga abinda nake gaya maki ko? Nace maki matar nan ba matar arziki baceba amma kika kasa yarda da maganata to wallahi idan baki tashi da adua ba nan gaba gidan zata rabaki dashi kamar yanda take ikirari kinaji kina gani zata rabaki da gidanki..”
Jawota Ramlah tayi jikinta suka cigaba da kuka saida sukayi mai isarsu kana sukayi alwalla sukazo suka fara sallah suna kaima Allah kukansu….
Mufeedah na shiga d’aki ta saki uban kuka tace
“Yau ni Mufeedah yar ruwan zafi ake gaya ma magana ban d’auki mataki ba dole in kauda Haneefa daga duniya dan itace babbar matsalata yanzu..”
Haka ta dinga sak’awa da warwarewa daga baya bacci yayi gaba da ita….
BAYAN KWANA UKU
Zaune take gaban boka dumbus tana gaya mashi matsalolinta saida ta gama kaf yayi dariya ya d’ago yace
Mufeedah amarya yanzu mi kikeso ayi masu ne?”
Zama ta gyara tare da jin dad’in yin nasara tace
“Boka so nake ka kauda Haneefa daga duniya ita kuma Ramlah ka saka Imran ya saketa ya koreta ita da yaranta subi duniya daganan gida ya zama nawa nikadai sai yanda nayi..
D’agowa boka dumbus yayi ya kalleta sai kuma ya fashe da wata irin dariya, wadda koni bansan ma’anarta ba…Dariya yayi mai isarshi yace
“Wannan aikin mai sauki ne amma bari na duba nagani..”
Dariya tayi dan dama tasan duk idan tazo nan to buk’atarta ko wace iri ce zata biya…
Duk’ufa yayi yana bincike tunda ya duk’a bai d’ago ba sai k’asa da yake bugu yakai kusan minti talatin yana abu guda duk ya had’a zufa…+
D’agowa yayi dasauri ya kalleta yace
“Akwai matsala”
Dubanshi tayi da alamar firgici a ranta tace
“Bangane mi kake fad’a ba..”
Zama ya gyara yace
“Gaskiya kashe Haneefa zaiyi matuk’ar wahala saboda duk abinda nayi sai inga wani haske na binta kiyi hak’uri kasheta zai iya zama barazana akanmu….”
Shiru tayi a ranta tana cewa
“Wannan wace irin yarinya ce haka?”
A sanyaye ta kalleshi tace
“To raba auren Ramlah da Imran fa?”
K’asa ya cigaba da bugawa dasauri ya kalleta yace
“Wannan wane irin aiki ne kika kawoman? To bari kiji auren Ramlah da Imran bazan iya kasheshi ba saboda tafimu bata bacci ita da d’iyarta suna kaima Allah kukansu idan har na matsa to nidake zamu rasa ranmu na gaya maki…”
Cikin tsananin firgici tace
“Katai makeni kasan dakai na dogara ko nawane zan biyaka indai buk’atata zata biya..”
Tsawar daya daka matane saida ta kusa sakin fitsari yace
“Bakiji mi nace maki ba? Idan muka matsa zamu iya rasa ranmu, basu barci kullum suna kaima Allah kukansu, shima Imran abinda yasa mukayi galaba akan shi saboda bai damu dayin azkar ba dan haka tashi kiban wuri ni inasan rayuwata….”
Kallonshi tayi da b’acin rai tace
“Kaban kunya ashe akwai abinda zai gagareka to in kai ya gagareka ni bazai gagareni ba namaka alk’awarin saina kashe Haneefa da hannuna na raba auren Imran da Ramlah…”
Tana kaiwa nan ta mik’e ta fita rai b’ace….
******
Yamma lik’is ta shigo gidan, bata tarda kowa parlour ba dan haka d’akinta ta nufa tana shiga tai wurgi da jikar hannunta ta fad’a kan gado, bata damu da tayi sallah ba, haka ta dinga juyi kan gado tana neman mafita dan gaskiya barin Haneefa a duniya ba babbar barazana bace ba a rayuwata…
Aiki suke ita da Haneefa a kitchen, dan yau zata karb’i girki suna aiki suna fira..
“Ammi mi zamu dafa ne yau?”
Murmushi tayi tace
“Favourite food din babanki”
Tab’e baki tayi tace
“Jallof rice ryt?”
Murmushi tayi tace
“Eh Mamana”
“D’auko kaza a fridge ki gyara kiyi pepper chicken”
Kazar ta d’auko ta wanke tasa a wuta, suna girki suna fira, dama kullum idan Haneefa tana gida to tare suke shiga kitchen dan tana koya mata abinci…
Guava juice suka had’a dayake fav drink din Imran d’in kenan, kafin kice mi gidan ya d’auki k’amshi, suna gamawa Haneefa ta jera komai a dainning table, shafa kanta Ramlah tayi tace
“Allah ya maki albarka”
“Amin”
Ta bata amsa…
“Bari naje nayi wanka”
Cewar Ramlah tana fad’an haka ta nufi d’akinta itama Haneefa d’akinsu ta nufa….
K’arfe takwas daidai ya shigo gida da sallama, tashi tayi da sauri taje ta tareshi da fara’a shiko ganinta ji yayi kamar an buga mashi guduma a k’irji…
“Sannu da zuwa Hayatee”
Yauwa ya fad’a kanshi gefe, jakar hannunshi zata karb’a ya dakatar da ita..
“Bawai na hanaki shiga harkata ba?”
“Kayi hak’uri”
Cewar Ramlah
“Mizaka farayi wanka ko abinci?”
Tsawa ya daka mata yace
“Waike dak’ik’iyar inace? Bakiji mi nace ba? Nace maki natsaneki bansan ganinki..”
“Kayi hak’uri naga yau aiki nane”
“Eh aikinki ne amma ki sani bazanci abincin naki ba…”
Zuciyarta wata k’una takeyi, daurewa takeyi take magana dan gab take da fashewa da kuka..
Duk’awa tayi ta rik’e k’afafuwanshi tace
“Dan Allah idan laifi na maka kayi hak’uri bazan iya d’aukar hukuncin daka yanke akai na ba yaman tsauri Imran..”
Tana fad’an haka ta fashe da kuka..
Hankad’eta yayi sai da kanta ya bugi tiles d’in parlour’n yace
“Ramlah ki fita harkana natsaneki bansan ganinki…”
Yana fad’an haka ya rab’ata ya wuce, ya nufi wajen Mufeedah wadda tun da Imran ya dawo ta fito, yana isowa wajenta ya rungumeta yace
“I miss you my babe”
Rungumeshi tayi tace
“Miss you more honey”
“Mi kika dafaman? Yunwa nakeji”
Tab’e baki tayi tace
“Ba abinda na dafa dan gaskiya bazan juri yin girki ba dan bashi nazoyi ba…”
Rungumeta yayi yace
“My babe duk yanda kikeso haka za’ayi, yanzu muje ki shirya muje muci abinci a restaurant ..”
Da tsallenta ta shiga d’aki, binta yayi d’akin, can suka fito cikin shirin riga da wando, Mufeedah ta zubo gashin attach d’inta kai ko d’an kwalli, rab’a Ramlah sukayi suka wuce suna rungume da juna..
Har sun wuce Mufeedah ta dawo ta duk’a gabanta…
“Yakamata ki sassauta ma kanki ki kwashe kayanki kibar gidannan dan mai gidan yatsaneki..”
Murmushi Ramlah tayi tace
“Burinki kenan ko? To bazaki tab’a yin nasara ba in shaa Allah..”
Tana fad’an haka ta mik’e ta nufi d’akinta, k’afafuwanta Mufeedah taja tabi bayan Imran dake tsaye bakin mota yana jiranta….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *