MAKIRCI KO ASIRI
CHAPTER 4 KARSHE
Bata tashi daga bacci ba sai k’arfe shidda na dare, da sauri ta diro daga kan gado ta nufi toilet wanka tayi tare da alwalla sai da ta gabatar da sallah la’asar kana ta nufi dressing mirror, kwalliya ta tsantsara kana ta nufi gaban wardrobe atamfa ta d’auko holland lemon green ta saka, d’inkin doguwar riga ya zauna d’as a jikinta. D’aurin d’an kwali ta kata kamar ta nad’a gwargwaro k’ara feshe kanta tayi da turaruka kala kala, kallon kanta tayi cikin madubi Wani irin murmushi ta saki wanda ita kanta bata san ta iyashi ba….
Zaune take bakin gado aka kira sallah magrib tashi tayi ta kabbara sallah, tana gamawa tayi adu’onta ta Shafa tana nan bisa carpet wayarta tayi ringing alaman sak’o ya shigo. Bud’awa tayi dan tasan daga inda sak’on ya fito.
“Ina d’akin Ahmad”
Abinda yace kenan, tashi tayi ta d’auki mayafinta ta nufi d’akin Ahmad, a corridor suka had’u da Ahmad kallonta yayi sama da k’asa yace
“Wannan kwaliyan fa? Duk Imran aka mawa?”
Zumb’uro baki tayi tace
“Wallahi yaya Ahmad ni bashi namawa ba kaina namawa”
Dariya yayi tare da Jan hancinta yace
“Wuce kije amma nasan karya kikeyi”
Dariya tayi ta yi gaba. Tana isa k’ofar d’akin Ahmad taji gabanta yana fad’uwa daurewa tayi ta shiga da sallama, juyowa yayi tare da amsa mata sallama yana jifarta da wani murmushi..
Ji tayi k’afafuwanta sun kasa d’aukarta dan wani kyau da kwarjini da ya mata yau bata tab’a tunanin yana dashi ba.
A b’an garenshi shima gani yayi ta canza ta mashi kyau fiye da sauran lokutan da yake ganinta. K’arasowa yayi inda take tsaye, iska ya hura mata a hankali tayi Ajiyan zuciya tare da kallon k’asa..
“Irin wannan kyau haka da kikayi”
Cikin kwanyar kanta ta jiyo muryanshi yana magana. D’agowa tayi ta turo baki kamar zatayi kuka, hannunta yaja ya zaunar da ita saman kujera dan bai iya jure shagwab’an da zata mashi. Kusa da ita ya samu ya zauna, sun kai kusan minti biyar babu wanda yayi magana. A hankali ya kira sunanta
“Ramlah”
Wani iri taji har cikin zuciyanta ji tayi babu wanda ya iya kiran sunanta irin Imran ko dan bai tab’a kiranta da sunan ta ba sai dai angel. Kasa d’agowa tayi ta kalleshi bare kuma ta amsa. Sake kiranta yayi d’agowa tayi suka had’a ido ganin yanayin da yake ciki yasa tayi sauri tayi k’asa da idonta. Bai damu ba ya cigaba da magana
“Ramlah tun randa aka haifeki Allah yasa man sanki a lokacin bansan miye so ba amma nasan dai Ina sanki, Ina girma sanki na k’ara girma na d’auka shak’uwa ce da mukayi sai daga baya na gane sanki nake kece mahad’in rayuwata a yanzu na gane bazan iya rayuwa babu ke ba, Allah ya kawoki duniyata danni kad’ai a yau zan gaya maki abinda ke raina Ramlah Ina sanki san da bazan iya misalta shi ba Ramlah kece rayuwata kece komai nawa inasan ki taimaka ki zama abokiyar rayuwata.”
Tunda ya fara magana kanta yake k’asa tabbas itama sai a yanzu tasan bata iya rayuwa babu Imran kusa da ita duniyarta bazata zama daidai ba sai tare da taimakon Imran.
Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ya kira sunanta nan ma shiru tayi bata amsa ba, jikinshi yayi sanyi yana tunanin kodai Ramlah bazata amince dashi ba. D’agota yayi yace
“Kiyi magana please”
A sanyaye tace
“Kaban lokaci zanyi shawara”
Murmushi yayi wanda bai kai ciki ba yace
“A iya sanina ba kida abokin shawara sai ni? Dan haka gani kiyi shawara dani”
Zumb’uro baki tayi
“Ni dai gaskia sai nayi shawara yanzu ba zanyi shawara da kai ba”
Dariya yayi yace
“A yau nake san naji matsayina wajen angel.”
Tashi tayi tsaye ta kalleshi
“Ya Imran duk abinda kake ji dashi game dani haka nima nake ji game da kai kasani zuciyan Ramlah ba kowa sai kai kaine sarki cikin zuciyan Ramlah na baka ita kayi duk yanda ka gadama da ita a yau na tabbatar ma kaina bazan iya rayuwa ba batare da kai ba ya Imran I love you more than you love me (ya Imran Ina sanka fiye da yanda kake sona).” Tana gama fad’in haka ta ruga da gudu cikin gida, karo sukayi da Ahmad yana daidai shigowa har ta yarda mashi tray d’in da ke hannunshi, bata ko tsaya bi ta kanshi ba bare tasan ta mashi barna…..
Girgiza kai yayi ya kwashi tray d’inshi ya kutsa kai cikin d’aki, yana shiga ya samu Imran yana surutu shi kad’ai
“Ramlah Ina sanki kamar yanda uwa ke san d’anta Ina sanki fiye da komai a duniyar nan a yau nasan nafi kowa sa’a a duniya tabbas zan zama fitilar da zaki dinga gani a duniyarki.” Haka ya dinga surutai shi kad’ai
Zama Ahmad yayi kusa dashi, dafashi yayi tare da cewa
“Yadai malam Imran? Kodai ka tab’u ne?”
Bugu ya kai mashi yace
“Akan Ramlah abinda yafi tab’uwa ma zanyi”
Tab’e baki yayi yace
“Ai naga duk kun tab’u ita kanta ban kad’eni tayi bata ko tsaya ba bare taga b’arnar da taman.”
Dariya Imran yayi yace
“Malam bazaka gane miye so ba sai ka fad’a tarkonshi, a yanzu gani nake nafi kowa sa’a a duniyar nan.”
“Aiko kafi kowa sa’a dan abincinmu da na d’auko Ramlah ta kifar dashi kuma wallah sai dai yunwar da kakeji ta kashe ka dan bazan koma kitchen ba.”
“Dariya Imran yayi yace
“Kafin inga angel nake Jin yunwa amma wallahi yanzu ganinta yasa na k’oshi”
Tab’e baki Ahmad yayi yace kunji dashi ni kaga natafi masallaci, tare suka mik’e suka nufi masallaci..
Tana fita ta nufi d’akin mamarta fad’awa tayi kan cinyarta, d’agota tayi tace
“Ramlah karki karyani”
K’ara shiga jikinta tayi tana dariya, murmushi tayi tace
“Miya saki farin ciki haka? Kodai kyauta Imran ya maki?”
Sunne kanta tayi jikin Mamarta tana dariya, d’agota tayi tace gayaman mana, kafin ta bata amsa Ahmad ya shigo da sallama. Tashi tayi daga jikin mamanta tace
“Please big bro don’t say anything (dan Allah babban yaya karka ce komai)”
Harara ya b’alla mata yace
“Sai na fad’a”
Murmushi maman tayi tace
“Son mike faruwa?”
“Mama yarinyar nan tana ganin yanda muke jin yunwa ta taho da gudu kamar mahaukaciya ta b’are mana abinci kuma ko ta tsaya sai ma kai da tasa tayi gaba.”
Kallonta tayi tace
“Garin ya haka ta faru?”
Turo baki tayi tace
“Bangani ba fa Mama”
“Eh nasan baki gani ba amma miye saki gudu”
“Bakomai”
Zaro ido yayi yace
“Bakomai?”
Shiru tayi, dariya yayi yace Mama ni zan gaya maki komai kuwa, marairaicewa tayi, dariya yayi yace
“Wallahi sai na fad’i”
Zama ya gyara, kafin ya fara magana sukaji ance
“Nima Bari in shigo ayi dani”
Ganin Alhaji Habeebu yasa Ramlah ta tashi ta ruga d’akinta.
Zama Alhaji ya gyara yace
“Son mike faruwa?”
Murmushi yayi ya kwashe komai ya gaya masu, ba abun mamaki baneba dan ganin yanda shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran, dukansu sunyi murna da jin wannan maganar dan sun San Imran yana da halin kwarai kuma sun San ko bayan ransu zai rik’e masu Ramlah…+
**********
Soyayya mai k’arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran kowa burinshi ya kyautata ma d’an uwanshi yake, tsaftatacciyar soyayya sukeyi babu mai San yaga d’aya cikin damuwa, soyayyan Imran da Ramlah ta zagaye dangi babu wanda bai san da wannan soyayya ba….
Imran na aji uku jami’a Allah yayi ma mahaifiyarshi rasuwa, yayi kuka kamar ranshi zai fita, ya daina cin abinci sai idan Ramlah ta tsareshi watarana ma sai ta sa mashi kuka kana yakeci, bayan bakwai Alhaji Habeebu ya nemi Imran da ya dawo gidanshi tunda dama bacci kawai ke baiyi gidan, bai musa ba haka ya tattaro ya dawo gidan Alhaji Habeebu, tun da ya dawo gidan gaba d’aya komai na Imran Ramlah ke mashi, kullum cikin yi mata gori ahmad yake, idan ya ishesu sai Mama tace
“Kaima ka samo mata”
Da an fara fad’a mashi haka sai yayi shiru saboda tsoron mata yakeyi shi gani yake soyayya b’ata lokaci ne….
********
Su Imran sun k’are karatu cikin sa’a bayan result ya fito Alhaji Habeebu ya samo masu aiki a company d’inshi. Tun da Imran ya fara aiki, ya fara maganar aure anso ya bari sai Ramlah ta shiga aji uku dan A lokacin tana aji d’aya jami’a Amma ya dage shi dai lokacin yakeso ayi komai, bayan da Alhaji Habeebu ya iya dole yasa aka saka biki, anso a had’a da na Imran to shi ko budurwa bai da ita.
Alhaji Habeebu shi yayi komai b’angaren ango da amarya dan yace “shima Imran d’anshi ne, haka akayi biki aka gama cikin jin dad’i, inda amarya ta tare a gidanta dake barhim…
Zaune suke cikin so da k’aunar juna babu maisan yaga ran d’an uwanshi ya b’aci, randa suka cika shekara da aure ranan Ramlah ta haihu ta samu d’iyarta mace, zo kaga murna wajen Imran, ranan suna yarinya taci sunan maman Imran Ameena amma suna kiranta da Haneefa….
Haihuwar Haneefa da wata uku Allah yama mahaifan Ramlah rasuwa, sakamakon had’arin Jirgin sama da sukayi. Tayi kuka kamar ranta zai fita, daga k’arshe ta dangana, tun daga lokacin Imran ya k’ara jin tausayinta dan gani yakeyi yanzu bata da kowa sai shi mijinta Sai kuma d’an uwanta Ahmad…
Haka zaman Imran da Ramlah ya kasance cikin so da k’aunar juna, kullum tattalinta yakeyi, duk abinda Ramlah keso shi Imran keyi baiso ko kad’an ya ganta cikin damuwa. Shekaran Haneefa uku Allah ya k’ara azurta Ramlah da haihuwa inda ta samu namiji, ranan suna yaci suna Alhaji Habeebu amma suna kiranshi da Haneef, haka suka cigaba da kula da yaransu sun basu tarbiya daidai gwargwado, Haneef na da shekara biyu ramlah ta haifi Mukhtar murna waje Imran ba’a magana, yaso ya saka sunan Ahmad sai Ahmad yace mukhtar za’a sa mashi saboda sunan babanshi ne kuma baza’a b’oye mashi ba.
Haka yaran suka taso cikin so da k’aunar iyayensu, duk abinda suke so iyayensu zasuyi masu muddin bai kauce ma fad’ar Allah ba. Kullum cikin yima Ahmad gori Imran yake dan yayi aure, sai dai yayi murmushi yace
“Ina ga matata bata duniya”
Tun rashin auren Ahmad na damun Imran da Ramlah har suka hak’ura suka sa mashi ido, idan Imran ya matsa mashi da cewa ko dan ka haihu ya kamata kayi aure sai yayi dariya yace
“Tunda kai da Ramlah kun haifaman Ai kamar ni na haifesu ne.”
Dan dole suka sa mashi ido suka daina mashi maganar aure sai dai kullum suna mashi adu’a Allah ya bashi mata ta gari..+
************
Zaune suke parlour suna fira, Mukhtar na saman cinyarta yayi bacci Haneefa da Haneef suna kallon cartoon, kallonshi tayi tace
“Hayatee yau zamu je yawo after isha”
“Ina zamu je?”
Abinda yace mata kenan, murmushi tayi tace
“Wait and see (tsaya ka gani)” girgiza kanshi yayi alamar “to…”
Shirya yaranta tayi cikin shigar k’ananan kaya, Itama shiryawa tayi cikin bak’ar abaya, parlour suka fito inda yake zaune, kallonsu yayi da mamaki
“Wai dagaske kike fita zamuyi?”
Zumb’uro baki tayi tace
“Bana gaya maka ba”
Murmushi yayi ya tashi zuwa yayi daf da ita, ya kama bakin ya murd’e yace
“Sai yaushe zaki san kin girma harda yara uku? Amma kullum k’ara shagwab’a kike”
K’ara ta saki dan bakin har zafi yake mata, sakinta yayi yana dariyan mugunta ya wuce d’aki da gudu ta bishi, suna shiga ya janyo ta da k’arfi ta fad’o jikinshi, marairacewa ta farayi tana ta tuba. Hancinta yaja yace
“Matsoraciyya”
Ita ta taimaka mashi ya shirya shima cikin k’ananan kaya. A jere suka fito kamar sabbin aure, k’arasowa sukayi parlour d’aukar Mukhtar tayi shikuma ya d’aukar mata handbag d’inta ya kama hannun Haneef suka fita.
Suna isa parking space ya bud’e mota Haneef da Haneefa suka shiga mik’a mashi Mukhtar tayi tace
“Bani key”
Ba musu ya karb’i Mukhtar ya mik’a mata key ya shiga mota itama shiga tayi tama motar wuta suka bae haraban gidan….
Basu tsaya ko Ina ba sai wajen salah, suna zuwa tayi parking duk suka fito, sukayi ciki suna isa aka kawo masu menu mik’ama Haneefa tayi ta zab’i abinda zataci, shawarma ta zab’a shima Haneef shi ya zab’a. Kallon Imran tayi tace
“Kai kuma sai abinda na zab’ar maka.”
Murmushi yayi yace
“An gama madam”
Dariya tayi ta zab’ar mashi fried rice nd coslow sai ferfesun cow leg, itama shi ta zab’a ta bada order, jim kad’an aka kawo masu suka faraci suna ci suna fira kai da kagansu kasan akwai soyayya mai k’arfi tsakanin wannan familyn. Suna gama ci aka mata bill ta biya tashi sukayi suka fita…
Tunda suka iso hankalinta gaba d’aya ya koma kansu, duk Abinda sukeyi akan idonta gaba d’aya sun gama tafiya da imanin ta ,duniya ji tayi babu wanda ya mata irin Imran lokaci guda kuma taji ta tsani matarshi zata iya komai dan ta rabasu ita kuma ta samu shiga, suna tashi ta tashi ta bisu, daga nesa ta dai dai ta camera d’inta tayi zooming ta d’auki number motar hoto ta koma ciki….
Tana shiga ciki, k’awarta tace
“Mufeedah Ina kikaje?”
Dariya tayi tace
“Sabon kamu nayi”
“Sabon kamu?”
Ta tambayeta dan bata gane maganarta ba. Dariya tayi tace
“Haka nace”
“Ayna kenan? Nidai naga muna nan kuma babu wanda yazo wajenmu.”
Murmushi tayi tace
“Baki ga wanda suka zauna nan ba?”
“Nagani”
“To shi naji inaso kuma san da zan iya kauda ko waye ya nemi hanani tarayya dashi..”
Ido ta zaro tace
“Ba gaskia bane ba akwai dai abinda kika hango a wajenshi.”
Dariya tayi tace
“Kina da ganewa gaskia ne daga ganinshi yana da abun hannunshi ni kuma kinsan duk hannu mai maik’o shi nake bi..”
“Amma Mufeedah kina ganin zaki samu shiga wajen shi? Jifa yanda yake tarairayan matarshi da d’iyanta.”
Dariya tayi tace
“Lash kin manta wacece Mufeedah kenan kin manta Ban tab’a neman abu na rasa ba, Bari in gaya maki tunda na kalli matarshi naji na tsaneta dan haka ko ta halin k’ak’a Sai na shiga gidan mutumin nan sai na tarwatsa gidanshi na dasa masu bak’in ciki daga nan nikuma in kwashe kud’inshi in k’ara gaba, shiyasa na bisu na d’auki number motarshi hoto dan gobe asuba gurin boka na kan dumbus zataman..”
Dariya Lash tayi tace
“Nasan zakiyi fiye da haka akan abinda kikeso to banda shakku akanki.”
Tab’awa sukayi suna dariya….
STORY CONTINUES BELOW
*********
Tunda asuba ta tashi dan tafiya wajen boka, k’arfe bakwai dai dai tana zaune gaban boka Dumbus, tana mashi bayani. Dariya yayi yace
“Tun kafin kizo nan an man bayanin zuwan Ki.”
Wata kwarya ya jawo gabanshi yayi siddabarunshi kallonta yayi yace
“Matso nan”
Tana matsawa ta kai fuskan ta wajen kwaryan da sauri ta d’ago dan ganin wanda Ke jikin kwaryan.
“Imran ne jikin kwaryan.”
Wata irin dariya boka ya saki yace
“Ko bashi bane?”
D’aga kai tayi alama shine, dariya boka ya saki yace
“Daga yau ki fara d’aukar kanki a matsayin matar Imran, kuma idan kika bi abinda nace to sai yanda kikayi dashi, wani abu ya d’auko d’aure yace kisan yanda zakiyi kin saka wannan layar cikin gidanshi idan kika saka to bazai tab’a maki gardama ba akan aurenki ke sai yanda ma kikayi dashi.”
Zaro ido tayi tace
“Boka Taya nida ko sunanshi bakinka naji bare har nasan gidanshi.”
Hak’oranshi ya washe yace
“Da kanki kuma zaki saka akwai ruwan maganin da zan baki da kin kusa shiga gari ki shafashi ki kira sunanshi sau uku kije titin barhim da k’arfe shida zaki had’u dashi.”
Murmushi ta saki dan tasan halin boka zaiyi fiye da haka, kud’i ta aje mashi ta mashi ban kwana ta fito….
***********
Biyar da rabi ta isa cikin garin katsina, ruwan maganin ta d’auko ta shafa tayi duk yanda boka yace mata.
“Titin Barhim zaka kaini”
Abinda tace ma mai napep ke nan, titin barhim ya kaita ya ajeta, ta kusan minti sha biyar tsaye ba taga alaman Imran zai zo ba har ta fara sarewa. Daga nesa ta hango motarshi wata Ajiyan zuciya ta saki dan ko mafarki ta tashi zata gane number motar. Yana k’arasowa daidai wajenta, juya kai tayi kamar bata san ya iso ba..
“I found my missing rib”
Abinda taji yace kenan, shiru tayi kamar ba taji shi ba, k’arasowa yayi kusa da ita yace
“Malama ina magana”
Kallonshi tayi sama da k’asa ta watsar.
“Wow Allah yayi halitta nan”
Kallon kanta tayi dan tasan ya dai fad’a ne amma bawani kyau ne da ita ba….
“Dan Allah kiman magana ko naji sanyi”
Kallonshi tayi tace
Mizance maka?”
“Komai ma kifad’a”
“Ni dai sunana Imran”
Abun ba k’aramin mamaki ya bata ba dan tun tana wajen boka ya gaya mata sunan shi, amma wani lokacin tasan boka Dumbus zaiyi abinda yafi haka.
“Ina magana kinyi shiru”
Ajiyan zuciya tayi ranta fes ta ya tsina fuska tace
“Mizance?”
“Komai ma kice
“Sunana mufeedah”
“What a nice name”
Murmushi tayi da bai kai ciki ba, yace
“Muje in kaiki inda zaki “
“Karka damu ka barshi”
Haka ya dinga mata magiya amma ta kafe, dan dole ya hak’ura amma sai da sukayi exchanging phone number. Yana tafiya ta tsaida napep cema mai napep tayi ya dinga binsa a baya amma a hankali karya gane suna binshi, haka kuwa akayi suka dinga binshi har suka iso gidan, tana ganin gidan yasa tayi dariya ta cema mai napep su tafi….
K’arfe 8:00pm dai-dai ta dawo k’ofar gidan Imran, knocking tayi mai gadi ya lek’o gaidashi tayi tace
“Nazo wajen matar gidan ne, mu bak’i ne bayansu muke shine nake shiga muna gaisawa..”
Mai gadi najin haka ya bud’e mata gate ta kutsa kai cikin gidan.
Wata hanya ta gani, hanyar tabi cikin ikon Allah tana isa taga wani d’an wuri da k’asa tona wurin tayi ta binne layar ba tare da wani ya ganta ba, tana gamawa ta mik’e cikin farin ciki ta nufi hanyar fita, bankwana tama mai gadi ta fita ranta fes da tabbacin zatayi nasara…
Tun randa Mufeedah ta binne laya, Imran ya kasa zaune ya kasa tsaye burinshi dai ya auri Mufeedah, ita kuma sai yawo take mashi da hankali, da kyar ya samu ta amince zata aureshi….
Ahmad ya samu da maganar k’ara aure ba k’aramin tashin hankali Ahmad ya shiga ba sakamakon bincike da yayi akan wacece Mufeedah, da kuma irin rayuwar da takeyi, koda ya zoma Imran da maganar ya janye auren Mufeedah saboda ba d’iyar kirki bace ba bama a gidan iyayenta take zaune ba wajen saurayinta take zaune. Ba k’aramin fad’a sukayi ba dan Imran cewa yayi sharri ne ake mata amma mufeedah natsattsa ce. Da yaga ba yanda ya iya dole ya saka mashi ido dan Imran baijin maganar kowa akan auren Mufeedah. Haka akayi bikin Imran da Mufeedah babu wani danginta sai abokanta yan bariki. Ba yanda Ahmad ya iya haka ya shiga cikin hidima dole aka dinga komai dashi….
CIGABAN LABARI
Tafe yake yana tuk’i cikin kwanciyar hankali, bakajin komai sai k’arar karatun al qur’ani. K’arfe shida (6:00pm) ya isa daura da kwatance ya gane gidan Malam Andu. Zaune yake k’ofar gida yana karatu.
Sallama ya mashi, d’agowa malam Audu yayi da fara’arsa ya amsa tare da mik’a mashi hannu sukayi musabaha….
“Malam wajenka nazo”
“Bismillah ka zauna to”
Wuri ya samu ya zauna tare da tan kwashe k’afa.
“Malam mike tafe dakai?”
Zama ya gyara yace
“Ni dai sunana ahmad kuma wani bawan Allah ne yaman kwatancenka saboda Ina cikin matsala yace idan nazo wajenka in shaa Allah komai zai zo da sauki, to shine nazo yau danni mutumin katsina ne..”
“Allah sarki”
Abinda malam yace kenan
“To malam Ahmad Ina jinka mike tafe dakai?”
Zama Ahmad ya gyara ya warware ma malam komai tun daga farko har yanzu ba abinda Ahmad ya rage ma malam…
Shiru malam yayi na d’an wani lokaci kana ya maida dubanshi ga Ahmad yace
“Ina zuwa”
Tashi yayi ya shiga gida, jim kad’an ya fito daga gidan…
Zama yayi yana mai kallon Ahmad yace
“Gaskia asiri ne aka mashi kuma muddin ba a karya asirin ba to bazai tab’a komawa daidai ba kuma wadda ta mashi asirin bata aure shi dan tana sanshi bane ba ta aure shi ne dan ta rabashi da iyalanshi kuma ta cinye mashi dukiya, kuma asirin da aka mashi yana nan cikin gidan ba wani wuri aka kai shi ba cikin gidan aka binne koma miye, dan haka sai kun tashi tsaye kun cire komai kana, Kuma duk ruwan shanshi ya zama akwai adu’o’i ciki to in shaa Allah za’ayi nasara kuma dole sai ya dage da yin azakar saboda akwai sakacin Adu’a tare dashi, amma in shaa Allah komai yazo k’arshe, yanzu akwai wani ruwan magani da zan baka sau uku zai wanke fuskarshi dashi sai kuma ya kurb’a ma’ana na kwana uku he duk sanda zai wanke fuskanshin ya kurb’i ruwan to duk wani sammu da aka mashi wanda yaci zai karye idan akayi wannan kuma aka cire layun dake cikin gidan to komai yazo k’arshe dan zai dawo cikin hayyacinshi”
Tashi malam yayi yaje ya kawo ruwan magani ya ba Ahmad, godia Ahmad ya mashi tare da aje malam rapper 200. Godiya malam ya ma Ahmad.
Sai da sukayi sallah magrib kana Ahmad yama malam bankwana ya kamo hanyar katsina…
Tafiya yake yana tunanin ta Ina zai fara baisan ta inda zai fara neman layun ba amma koma dai yane in shaa Allah sai yayi iya k’ok’arinshi ya karya asirin nan ko dan k’anwarshi da amininshi su koma masoyansu nada, Sai da yay tafiya mai nisa kana ya kira Imran dan Sai da ya kusa shiga katsina kana ya kiranshi, bugu uku ya d’auka gaisawa sukayi Ahmad yace
“Ina kan hanya zan dawo yanzu”
“Allah ya maidoka lafiya d’an uwana”
Kashe wayar yayi sakamakon kanshi da yaji yana juya mashi, ji yayi idonshi na rufewa alamar yana jin bacci, ga kuma kanshi da ke sara mashi kamar zai b’are biyu..
Gani yayi wani abu ya gifta mashi kamar mashi, gaba d’aya ya saki sitiyarin yayi cikin daji wani icce ya buga sai da motar ta lotsa….
Wasu ne dake gefen titin sukayo kanshi da gudu, dan duk abinda faru akan idonsu ya faru.
Dakyar suka jawoshi daga cikin mota, ganin baya numfashi yasa suka tsaida wata motar suka kwashi abubuwanshi masu amfani suka nufi cikin gari dashi dan kaishi asibiti….
Medical center suka nufa dashi, suna zuwa akayi emergency dashi. Likitoci uku ne kanshi da kyar suka ceto numfashinshi ya koma daidai. Allura aka mashi aka d’aura mashi k’arin ruwa, ga kanshi da aka d’aure saboda jini dake zuba….
Zaune yake yayi tagumi ya rasa Abinda ke mashi dad’i. Haka b’angaren Ramlah abun yake, tun da marece take jin gabanta na fad’uwa ta rasa dalili.
Wayar Imran ne tayi ringing kamar jira yake da sauri ya duba ganin waye ya kira yasa ya saki numfashi.
“Hello dan Allah Imran ne?”
“Eh shine ya amsa da kyar gabanshi sai fad’uwa yakeyi.”
“Dama mai wayar nan ne yayi accident yana medical center nan emergency, mun duba munga kaine mutum na k’arshe da kukayi waya da shi shine muka kiraka.”
“What?”
Ya mik’e tsaye ga zufa na karyo mashi.
“Ai na yayi accident d’in?”
Basu bashi amsa ba suka kashe waya, dai-dai Ramlah ta fito daga d’aki.
“Imran lafiya?”
Ta tambaya, baiko kalli inda take ba haka bai bata amsa ba yasa kai ya wuce, sai da ya kai bakin k’ofa kana yace mata
“Ahmad ne yayi accident yana medical center a nan emergency.”
Yana fad’ar haka yayi waje..
Kuka ta fashe dashi tayi d’akinta da gudu, hijab ta d’auko da key d’in mota tayi waje, tana shiga ta tada motar horn ta dinga ma maigadi kamar zata b’alle gate d’in da sauri ya wangale mata gate tayi waje. Gudu take sosai kamar zata tashi sama, Allah ne kawai ya kaita asibiti lafiya…
Kusan tare suka isa asibitin ita da Imran, a tare suka shiga emergency Amma babu wanda kema d’an uwarshi magana. Basu sha wahala ba suka gane inda yake, kallo d’aya zaka mashi kasan yana jin jiki, k’arasawa sukayi wajenshi gaba d’ayansu. Hawaye Imran yakeyi
“D’an uwana haka ka koma? Duk dan kasama man farin ciki miyasa ban hanaka tafiya ba a lokacin da kace man zaka tafi miyasa ban bika ba miyasa kullum burinka ka faranta man koda kai zaka k’untata.”
Haka ya dinga surutu yana kuka, fad’awa Ramlah tayi jikinshi tana kuka sosai.
“Ya Ahmad please ka tashi kada Kaima ka tafi kamar yanda Mama da Baba da Haneef suka tafi dan Allah ka tashi kai kad’ai kaman saura kaine gata na idan ka tafi bansan inda zan saka kaina ba ya Ahmad ka tashi nasan kana jina, na yafe zan zauna da Imran cikin k’unci basai ya kulani ba indai zan dinga ganinka kusa dani yafi man komai..”
Kuka take tana sabbatu kamar zararra, Imran ne yazo kusa da ita ya janyeta fizgewa tayi ta koma jikin ahmad tana kuka. K’ara ta kowa yayi yazo ya janyeta ya k’ank’ameta jikinshi, ji yayi wani abu na mashi yawo cikin kanshi da sauri ya ingijeta gefe guda yana huci..
Fashewa tayi da sabon kuka ita kad’ai tasan halin da take ciki, tabbas tasan tayi missing d’in mijinta har dai yau da ya had’a jikinta da nashi, ita kanta tasan tana kewarshi…
Ganin kuka bai mata ta shiga toilet ta d’auro alwalla zuwa tayi ta kabbara sallah tana neman ma Ahmad sauk’i. Shiko Imran yana kusa dashi zaune ya kama hannunshi ya rik’e kamar wani zai kwace shi…
Tana nan zaune bisa sallaya har aka kira sallar asuba tashi tayi ta gabatar da sallah, shima Imran masallacin dake cikin asibitin ya tafi…+
K’arfe bakwai ya dawo in da Ahmad yake, tana nan zaune inda ya barta, kallon gefen da Ahmad yake yayi
“Yakamata kije gida”
Batace mashi k’ala ba ta tashi ta d’auki jikarta ta fita…..
Cikin gida ta nufa bakowa parlour d’akin yaranta ta nufa zaune ta gansu sunyi tagumi, d’agowa sukayi dan suga waye zai shigo suna ganinta gaba d’aya sukayi kanta.
“Ammi Ina kikaje?”
Cewar Haneefa data rik’e hannunta, shiru tayi taja hannun Mukhtar suka zauna.
“Ammi talk to me please (Ammi kiman magana dan Allah).” Hawaye ta share tace uncle Ahmad ne yayi accident yana asibiti. Dasauri Haneefa ta mik’e
“Ammi tun yaushe?”
“Jiya ne “
Tashi tayi tace
“Kima Mukhtar wanka kema kiyi zanje na had’a breakfast mukoma asibiti.”
Tana fita ta nufi kichen dan shirya kalaci. K’arfe tara dai-dai suka gama shirinsu, basu tsaya kalaci ba suka nufi asibiti cikin motar ba mai magana sai karatun alqur’ani dake tashi k’ira’ar sudais. Koda suka shiga asibitin basu tsaya ko Ina ba sai d’akin da Ahmad yake, da sallama suka shiga. Amsawa yayi batare da ya kalli inda suke ba.
K’arasawa Haneefa tayi wajen Imran tace
“Daddy Ina kwana?”
“Lafiya”
Ya bata amsa, shima mukhtar gaidashi yayi ya amsa ba yabo ba fallasa. Gaidashi Ramlah tayi a dak’ile ya amsa, wuri suka samu suka zauna…..
STORY CONTINUES BELOW
A hankali ya fara bud’e idonshi har ya gama bud’esu gaba d’aya. Tuna Abinda ya faru dashi jiya yayi, dafe kanshi yayi tare da fad’in
“Wash”
Dasauri Ramlah tayi inda yake, shima haka Imran ya tashi ya nufi bakin gadon, sannu suka fara mashi. Murmushi ya masu tare da karkad’a masu kai…
Kallon Imran yayi ya fara magana
“Imran ga Ramlah nan amana kasani daga randa zan barku daga rannan ta koma bata da kowa sai kai ka tuna halaccin da iyayenta sukayi mana ka rik’e ta amana, naso na ida aiki na akanka amma Allah bai nufa ba, nasani ko da na mutu a yau nasan akwai wanda zai ida abinda na fara dan Allah ka dage da adu’a.”
Hawaye ne suka fara sintiri fuskan Imran tare da rufe mashi baki.
“Ka daina fad’an haka d’an uwana zaka tashi zakaji sauk’i ciwo ba mutuwa ba.”
Girgiza kai yayi yana cije leb’e, hannunshi Ramlah ta damk’e tana kuka.
“Dan Allah ya Ahmad ka daina magana irin haka, kasani bani da kowa sai kai kasani na rasa iyaye na na rasa d’ana na rasa farin cikin mijina na rasa komai nawa k’unci yaman yawa kai ne uwata kaine ubana gashi kaima kana niyar barina dan Allah kayi hak’uri ka tsaya dani zuciyana zata iya tarwatsewa a yayin da naga babu kai kusa dani kaine gatana yanzu..”
Rik’e mata hannu yayi
“Naso in zauna daku naso in sama maki farin ciki kamar yanda iyayenki suka bani farin ciki amma hakan bazai samu ba, baki rasa komai ba ni nasani Imran na sanki kuma kema kinsan haka daga randa nabar duniya daga rannan za’a cigaba daga inda na tsaya ki dage da adua a yanzu mijinki adu’arki yake nema In shaa Allah watara sai kunyi dariya..”
Kuka take sosai, Haneefa da Mukhtar suna gefensu Mukhtar kuka yake yayin da Haneefa ta kasa kukan sai dai idonta da yayi ja kamar tarugu. Hannu ya mik’a ma Mukhtar yace
“Babana zo nan”
Ba musu mukhtar yaje gabanshi shafa kanshi yayi yace
“Allah ya raya ka kaji babana kasani ina sanku sosai.”
Hawaye ya share
“Muma muna sanka Papa.”
A hankali ya d’ago ya kallesu
“Kubani wuri ina san inyi magana da princess”
Ba musu suka fita, mik’a mata hannu yayi ta k’arasa kusa dashi….
Murmushi ya sakar mata
“Shekarar ki nawa yanzu?”
“Sha biyar”
Ta bashi amsa, gyad’a kai yayi yace
“Nasan kinyi k’ank’anta amma sanin da na maki zaki iya nasan zaki iya aiki zan baki naso inyi da kaina amma hakan bazai samu ba, nasan ke kad’ai zaki ida man shi, Haneefa sai kin daure sai kinyi hak’uri aikin akwai wuya Amma nasan zaki iya Allah na tare dake.”
Nan ya kwashe duk yanda sukayi da malam ya gaya mata ya k’ara da cewa
“Amma sai kinbi a hankali saboda Mufeedah ta wuce yanda muka d’auketa, inasan ki tone duk wani asiri da ta binne a cikin gidan nan inasan ruwan Imran na sha ya zamana akwai adu’a ciki, a mota na da nayi accident nasan za’a d’auko ta akwai ruwan magani ya wanke fuskanshi sau uku ya kuma sha, rana uku kenan, ki taimakeni ki ci kaman buri na ki dawo da farin cikin iyayenki nasan zasuyi alfahari dake…”
Hawaye ta share tare da fad’in
“In shaa Allah Papa zan cika maka burinka duk wuyarshi I want you to be proud of me Papa, zan dawo da farin cikin iyayena no matter how long it will take me, sai na cika maka burinka sai kayi dariya zan daure duk wahalarshi na maka alk’awari.”
Murmushi yayi
“I trust you my princess kuma inasan abun nan ya zama sirri har sai kin gama aikinki saboda bansan kema a halakaki.”
“D’aga mashi kai tayi alamar to, hannunta ya rik’e yana dariya, motsi bakinshi ya farayi yana salati daga baya kuma yayi shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta d’auka bacci ya samu….
Lura tayi kamar baya numfashi, kanta ta kai wajen k’irjinshi Amma da alamu baya numfashi, da gudu ta fita ta nufi waje dai-dai likita na tahowa rik’eta yayi tare da tambayar
“Lafiya?”
D’akin ta dinga nuna mashi da hannu dan bata iya magana shiga yayi cikin d’akin, ganin haka yasa Imran da Ramlah suka bi doctor d’akin. K’arasawa doctor yayi tare dayi mashi aune aunen, d’agowa doctor yayi ya kallesu
“Am sorry to say he’s gone”
“What?”
Cewar Imran tare da shak’e doctor
“K’arya kake bai rasu ba bamuyi dashi zai rasu yanzu ba munyi dashi zamu rayu tare taya zai mutu yabarni.”
Da kyar doctor ya kwace kanshi wajen Imran.
Kanshi Ramlah tayi da gudu tana fad’in
“Ya Ahmad katashi please kada kaman haka kada ka mutu kabarni taya zaka barni cikin Wannan duniyar mai cik’e da rud’ani dan Allah ka tashi ka tausayaman kaine gatana bayan na rasa mahaifana Ina kakeso in saka kaina? Mutuwa Taya zaki man haka wane irin jarabawa ne wannan mai wuyar cinyewa.”
Kuka take tana surutu, Haneefa ce tazo kusa da ita ta janyeta, ita kanta kukan takeyi ta kasa magana sai kuka.
Imran kuwa kusan zarewa yayi gaba d’aya kuka suke babu mai ba wani hak’uri….
Ganin kukan bai mashi yasa yaje ya biya Bill aka bashi gawan Ahmad sukayo gida da ita, kafin kace mi mutuwar Ahmad ta zagaye dangi da yan unguwa da abokin arziki, gidan Imran tun kafin ya baro asibiti yafara cika, wanka akama Ahmad aka shiryashi aka d’auke shi aka nufi dashi gidan shi na gaskia, sai dai muyi mashi fatan Allah yasa ya huta…
Duk wanda ke gidan Imran sai da ya zubda ma Ramlah Hawaye ganin yanda ta koma ta lalace ta fita hayyacinta..
Kowa na zaune parlour ana karb’an gaisuwa ban da Mufeedah da tunda taji labarin mutuwa ta koma d’aki bata fito ba…
ABINDA YA FARU
Shigowar ta gida kenan taji Ahmad nama Imran magana akan magani, komawa tayi da baya dan ta gama razana tabbas tasan idan tayi sake Ahmad sai ya ruguza mata shirinta. Ita kuma duk wanda yayi yin k’urin b’ata mata shiri sai ta ga bayanshi…
Tana shiga d’akinta ta fara zarya cikin d’aki. Boka Dumbus tayi tunanin zuwa wajenshi, tuna yanda sukayi dashi ta tuna tasan ba halin komawa dan bazai saurareta ba. Waya ta jawo ta kira Lash bugu d’aya ta d’auka
“Lash Ina cikin matsala”
Cewar Mufeedah dake had’a gumi.
“Lafiya Mufeedah?”
Kwashe komai tayi ta gaya mata ta k’ara da cewa
“Lash idan Ahmad yaje daura komai nawa zai warware inna ce komai Ina nufin komai da kika sani duk shiri na wallahi zai lalace, kuma kinsan yanda mukayi da boka Dumbus bazan iya komawa ba zuwan Ahmad daura barazana ne daga dukkan komai nawa, kuma duk wanda yayi yunk’urin tsaida man aiki na sai na halakashi, dan haka ki samo mana mafita..”
Numfasawa Lash tayi
“Karki damu Mufeedah k’arya Ahmad yake yace zai b’ata mana shiri, yanzu ki shirya gobe akwai wani boka dake malumfashi kuma shima aikinshi kamar yankan wuk’a yake sai muje..”
Sai a sannan Mufeedah ta samu d’an kwanciyar hankali dan tasan Lash da kutse kutse….
K’arfe goma bukkan boka ta masu, gurfana tayi gaban boka ta warware mashi komai, ta k’ara da cewa
“Boka so nake a kasheshi inasan a datse mashi numfashi dan muddin yana numfashi to zai b’ataman aiki nikuma alk’awari nayi duk wanda ya nemi b’ataman aiki sai na kaseshi…”
Dariya boka ya saki yace
“Tashi kuje aikinki ya biya”
kallon boka tayi da mamaki tana neman k’arin bayani. Dariya yayi yace
“Kina tunanin abinda Zanyi ko? To aljani zan tura mashi idan yana hanya shi zaiyi komai kedai ki saurara zakiji ance maki ya rasu..”
Godiya sukayi ta ajema boka kud’i suka tashi suka bar wajenshi, Lash na k’ara kuranta mata boka….
Tunda Ahmad yayi tafiya take sauraran taji ance ya rasu, tana mak’ale bakin k’ofa taji wayar Imran tayi ringing da kuma amsar da Imran yaba Ramlah ba k’aramin dad’i taji ba..
Komawa d’aki tayi da gudu ta d’auki waya ta kira Lash, ta gaya mata komai nan suka shiga murna. Koda aka shigo da gawan Ahmad wani irin dad’i ne ya rufe ta ganin wanda ke neman kawo mata cikas ta kaudashi. Sai dai Mufeedah ta manta da tayi tuya ta manta da albasa…..
Bayan kwana biyu, Haneefa ce zaune d’akinta tayi tagumi ta rasa taya zata fara aikinta da ta d’aukar ma Papa Alk’awari tabbas tasan aikin akwai wahala amma sai ta cika mashi burinshi tasan zakiji dad’i ko da yana kabari ne, amma ta rasa ta Ina zata fara. Ramlah ce ta shigo da sallama, Haneefa bata san shigowarta ba. Hannunta ta janye daga tagumi ta samu wuri ta zauna kusa da ita. Murmushi tayi tare da fad’in
“Ammi yaushe kika shigo?”
“Ina zaki san nashigo kin tsunduma cikin tunani”
Dariya tayi tace
“Wallahi ina tunanin Papa ne “
“Kina tunani Papa ko kina tunanin maganar da kukayi dashi? Wai miye ya ce maki ne ko Allah yasa ina da abinda zan taimaka maki nima dashi..”
Dariya tayi tace
“Wannan yak’i nane Ammi, and I have to fight it alone, kedai ki tayani da adua, sai na dawo maki da farin cikin ki koda zan rasa nawa farin cikin I want you to be proud of me Ammi.”
Shafa kanta Ramlah tayi tace
“Ina alfahari dake d’iyata kuma In shaa Allah zakiyi nasara kuma adua ta tana binki koda yaushe, kedai kiyi a hankali bansan kema in rasaki, kamar yanda na rasa d’an uwana da D’ana..”
“Kisa a ranki ba zaki rasa ni ba Ammi In shaa Allah..”
Jawo ta Ramlah tayi ta rungumeta tana k’arajin k’aunar d’iyarta har cikin ranta….
Ana wata ga wata, shin Haneefa zatayi nasara akan Mufeedah Ko kuma Mufeedah zata hallaka Haneefa kamar yanda ta hallaka Ahmad? Duka amsoshinku suna tare dani kudai ku cigaba da bina kuma da bani had’in kai wajen danna Yar tauraruwar nan da kuma shiga d’an akwatin nan dan aje ra’ayoyinku, inasan inga comment yau 1k shi zai saka inji dad’in maku typing har kuzo inda kukeso azo…. thnx y’all….
BAYAN KWANA BIYU
Zaune take d’aki tayi ta gumi duk abin duniya ya isheta ta rasa taya zata fara aikin da Papa ya sakata, ita kanta kwakwalwanta ta cunkushe.
“Anya zan iya kuwa?”
Tambayar da tama kanta kenan. “Zaki iya kisa a ranki zaki iya kin d’aukar ma Papa alk’awarin zaki iya komai dan kiga burinshi ya cika, kuma ko ba komai zaki dawo da soyayyar iyayenki wanda suka gina tun da dad’ewa rana guda aka tarwatsasu.”
Wata zuciya ce ke fad’a mata haka. Mik’ewa tayi da sauri tare da fad’in
“Zanyi komai akan Ammi da Daddy dan ganin nadawo masu da farin cikinsu koda kuwa haka na nufin rasa nawa farin cikin…”
Tashi tayi ta dinga kai komo cikin d’aki ita kad’ai tana sak’awa da warwarewa, k’arasawa tayi jikin window ta yaye labulen window d’in…
“Akwai ruwan magani a mota na inasan Imran yasha ya kuma wanke fuskanshi na kwana uku ne ki taimakeni ki ci kaman burina ki dawo da farin cikin iyayenki nasan zasuyi alfahari dake” tunawa tayi da maganar Ahmad yayi mata da ta ga motarshi anyi parking d’inta…
Da gudu ta nufi waje, cikin ikon Allah bata tarda kowa ba. Tana bud’e k’ofar motar taji ta bud’e shiga tayi inda direba ke zama ta fara dubawa ba taga komai ba haka ta dinga bin motar tana dubawa amma ba taga komai ba takai kusan minti ashirin tana dubawa amma ba abinda tagani, a kasalance ta fito jikinta duk ya mutu, hawayen da suke mak’ale da ita suka gangaro mata. Goge hawayen tayi cikin kuka take furta.
“Kayafeman Papa na kasa cika maka alk’awari bansan ta ina zan fara ba abun nan yafi k’arfina naso kana raye da komai yanzu yazo k’arshe.”
Kuka takeyi sosai tana surutu.
Magana taji ta rasa ta in maganar ke fitowa duba wa tayi ko ina amma bataga mai maganar ba sai dai ko mafarki ta tashi bazata mance muryan Papa ba.
“Kiyi hak’uri nasan zaki iya nasan akwai wahala amma nasan ke zaki iya ke kad’ai nasan zakiman yanda nakeso ki taimakeni ki dawo da farin cikin ma’auratan nan..”
Wani k’arfi taji yazo mata, adu’a tayi ta juya ta nufi gida taku biyu tayi ta juyo, cikin motar ta koma ta fara dubawa a hankali. Wata leda taji a k’ark’ashin sit d’in kusa da direba jawota tayi a hankali tana fito da ita, ta bud’e ta ruwa tagani cikin kwalba, ko tantama baza tayi ba tasan wannan sune ruwan da Papa yake nufi.
Fitowa tayi tana mai hamdala ga Allah ta nufi cikin gida, d’akinta ta nufa ta b’oye ruwan maganin tana ma Allah godiya….+
Fitowa tayi parlour abinda ta tarda bai bata mamaki ba dan ba sabon abu baneba
“Ramlah wallahi na tsaneki na tsani ganinki da zan iya rabuwa dake dana rabu dake dan Allah ki taimaka ki tattara kayanki ki koma BQ Idan na daina ganinki kusa dani zan daina jin rad’ad’in dake damuna..”
Magana yake yana huci, Mufeedah zaune bisa kujera ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya tana murnushi.
Hawayen da suka gangaro mata ta share tare da fad’in
“Karka damu indai ganina ne ke sa kanajin wani iri a rayuwanka zaka daina ganina Daga yau wallahi da zaka sakeni dana fi buk’atan haka dan yanzu nafisan nayi rayuwa ni kad’ai.”
“Darling ka saketa mana tunda ta buk’aci sakin da kanta..”
“Wallahi da zan iya sakinta dana saketa to sakinta wani baraza nane ga rayuwata amma ta tattara tabar cikin gidan nan bana buk’atar ganinta..”
K’arasowa Haneefa tayi inda Ramlah take duk’e tana kuka, kamata tayi ta tashi, dubanta ta kai wajen Mufeedah tace
“Ki guji randa asirinki zai tonu nayi alk’awarin sai na tona duk wani asiri naki…”
Tana gama fad’in haka taja mahaifiyarta suka bar parlourn, mik’ewa Mufeedah tayi kamar zaki tayi hanyar d’akinta tana shiga ta lailayo ashariya ta d’urama haneefa
“Kafin kiga bayana ni zan ga bayanki yarinyar nan kin zak’e da yawa amma zanyi maganinki zaki raina kanki wallahi namaki alk’awarin kema sai naga bayanki…”
Haka ta dinga surutai ita kad’ai…
Suna shiga d’aki ta share hawaye tace
“Ki fara had’a kayanku zamu koma BQ”
“Akanmi?”
“Hakan mahaifinku ke buk’ata”
“Wannan ba hujja baneba babu inda zamu”
Dafa kafad’arta tayi tace
“Dole muyi biyayya ga Imran gaba d’aya nidaku k’ark’ashinshi muke dan haka dole muyi abinda yake so..”
Tana gama fad’an haka ta tashi tafara tattara duk abinda take buk’ata ba yanda Haneefa ta iya itama tashi tayi ta nufi d’akinsu ta had’a masu kayan buk’ata. Da taimakon Haneefa Ramlah ta gama shirya kayansu a BQ dan dama BQ d’in akwai komai d’aki biyu ne kowane d’aki a kwai toilet kuma akwai gado sai parlour mai d’auke da set d’in kujeru da kayan kallo, sai kitchen haka dai suka gama shirya ko ina yayi tsaf…..
STORY CONTINUES BELOW
BAYAN SATI D’AYA
Tun da Ramlah tabar cikin gidan yaji kamar an sauke mashi wani dutse dake kanshi, duk abin buk’ata na game da abinci ya aje mata shi a BQ sai dai duk hanyar da zata had’asu ya toshe ta dan yanzu rayuwarshi yake hankali kwance shida Mufeedah, har mancewa yake da Ramlah.
Itama b’an garenta hakane duk wata hanya da zata had’asu ta toshe ta dan ganinta shike saka shi damuwa ita kuma tayi alk’awarin ya gama ganinta dan ya dawwama cikin farin ciki, sai dai kullum tana adua Allah ya dawo dashi hayyacinshi…
****************
A hankali ta shiga parlourn dubawa tayi ko ina taga ba kowa, Jin shirun ya tabbatar mata da Mufeedah ta fita kamar yanda taji tana waya d’azu da take lab’e, k’arasawa tayi d’akin Ahmad tana tura k’ofa taji ta bud’e hamdala tayi tare da fad’ad’a murmushinta alamar cin nasara. Fridge d’in dake d’akin ta nufa bud’e waa tayi duk ruwan dake ciki sai da ta bud’e ta tofesu da adu’a kana ta rufe ta maida fridge tare da fitowa, kitchen ta nufa nan ma ruwan dake cikin fridge d’in haka ta tofesu da adu’o’i. Tana gamawa ta fito fuskan ta cike da murna tare da yima Allah godia yanda ta fara aikinta batare da tasamu tan gard’a ba…
Tana shiga cikin BQ da sallama Ammi ta gani tare da Mukhtar suna fira, wuri ta samu ta zauna kusa da Mukhtar. K’ura mara ido Ammi tayi can ta nisa tare da fad’in
“Daga Ina kike?”
“Cikin gida naje”
Ta bata amsa, ido ta zaro
“Mi kika je yi cikin gida? Kinga Haneefa bansan d’aukar magana kibar ma Allah komai shi zai mana maganin duk wani abu dake damunmu indai maganar da kukayi da Papa ne nikam na yafe nafisan mu zauna haka da kema In rasaki.”
Dafa kafad’arta tayi ta sakar mata murmushi
“Bazaki tab’a rasani ba In shaa Allah kedai ki bini da adua”
Tana fad’in haka ta mik’e ta nufi cikin d’akin Ammi….
Da sallama ya shiga cikin gida ganin ba kowa yasa kai ya nufi d’akinshi, fridge ya bud’e buttle water ya d’auko ya bud’e d’aga kai yayi bai aje ba sai da ya shanye gaba d’aya ya ajiye roban ji yayi wata natsuwa ta diran mashi, k’ara d’auko wata roban yayi ya bud’e rabi yasha kana ya maida a fridge tare da rufewa…”.
Haraban gidan ya fito yana fitowa yaci karo da Haneefa rik’e da cup. Murmushi ta sakar mashi, shima kuma murmushin ya mata dan gaskia yan san yaranshi har dai Haneefa .
“Ina wuni”
Muryanta ya tsinkaya tana gaidashi. Amsawa yayi da
“Lafiya lau”
Yana mata murmushi…
Cup ta mik’a mashi tana fad’in
“Gashi kayi bismillah kasha sai ka rage d’an kad’an ka wanke fuskanka dashi.”
Kallonta yayi ya kalli cup d’in yace
“Nasha ruwa cikin gida banjin zan k’ara shan wani abu yanzu.”
Murmushi tayi da taji yace ya sha ruwa kuma ta tabbata ruwan da yasha akwai adu’o’i ciki.
Tab’e baki tayi tana fad’in
“Wancan ruwan da kasha daban wannan kuma daban dan haka Daddy ka karb’a please kasha ko yanzu in maka kuka.,”
Ba yanda ya iya dole ya karb’i cup d’in yayi bismillah yasha ya rage ya wanke fuska, tsalle tayi tare da fad’awa kanshi tace
“Allah ya bani ikon k’arasa abinda nayi niyya..”
Kanta ya Shafa yana maijin nishad’i kasancewar yaji jininshi a jikinshi…
Duk abin nan da ya faru akan idon Ramlah, hawayen da suka zubo mata ta goge tare da wani farin ciki ko ba komai tasan Haneefa zata dawo mata da martabanta gidan mijinta, a yau yafi mata komai dad’i yanda taga Imran ya nama Haneefa dariya har ya rugumeta koba komai yau ta kasance rana mai tarin abubuwa da dama wanda bazata iya manta dasu ba. Dasauri ta juya ta nufi cikin gida dan kar Imran ya ganta ranshi ya b’aci ta salwanta mashi farin cikin shi…
WASHE GARI
Fitowa yayi zai tafi wajen aiki, hannunshi rik’e da jaka d’ayan hannun kuma Mufeedah ya d’an rungumo jikinshi har suka iso bakin mota, sakinta yayi ya bud’e mota ya saka jikarshi, juyowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi yace
“Dan Allah ki daure yau ki mana girki nagaji da sayen abincin waje.”
Murgud’a baki tayi tace
“Wallahi bazan girka maka abinci ba dan banma iya ba ka kuma sani kawai ka tsaya ka mana take away.”
Tana fad’an haka ta juya ta nufi cikin gida tana gunguni. Girgiza kai yayi tare da shiga mota.
Inda ta b’oye ta fito da sauri wajenshi ta k’arasa yana k’ok’arin tada mota, kwankwasa mashi glass tayi, ganin wacece yasa ya bud’e yana dariya.
“Good morning Daddy”
Good morning princess “
Murmushi tayi ta mik’a mashi cup d’in ba musu ya karb’a yayi yanda yayi jiya, yana gamasha yaji wata natsuwa ta sauko mashi. Mik’a mata cup d’in yayi ta karb’a.
“Miya hanaki zuwa makaranta?”
“WAEC mukeyi kuma yau banda paper”
Girgiza kanshi yayi tare da wata kunya da ta sauko mashi dan baisan yaranshi ko aji nawa suke ba a makaranta.
“Allah ya bada sa’a”
Ta tsinkayi muryanshi yana fad’a jiki sanyaye.
“Ameen Daddy”
Ta amsa, kud’i ya zaro cikin Aljihu ya mik’a mata, hannu biyu ta saka ta karb’a tana mai godiya, motarshi ya tada ya bar haraban gidan, d’aga mashi hannu ta dingayi har sai da taga yabar gidan kana ta nufi BQ da gudu tana kwalama Ammi kira…
STORY CONTINUES BELOW
Dasauri Ammi ta tare ta tana tambayarta
“Lafiya?”
Dariya tayi taja hannunta suka zauna, ta gaya mata duk yanda sukayi da Imran ta bata kud’in. Rungumeta tayi tace
“A kodayaushe Ina alfahari dake ina k’ara godema Allah da yabani ke a matsayin d’iya, Allah ya k’ara taimakonki adu’ata tana biye dake ke dai kiyi a hankali ina tare dake In shaa Allah.”
“Ameen Ammi”
Ta fad’a ta tashi ta nufi d’akinta..
Tun safe take lab’e dan taga fitowar Imran amma har yanzu shiru, agogon hannunta ta kalla taga 12 saura d’an guntun tsaki taja tare da juyawa zata nufi BQ. Muryanshi ta juyo yana waya da sauri ta juyo, ganin shine ya sa ta saki murmushi wanda itama bata san tayi shi ba.
K’arasawa tayi gabanshi da cup a hannu, tun kafin tayi magana ya gane mi take nufi karb’an cup d’in yayi kamar yanda yakeyi kullum haka yauma yayi. Yana gamawa ya mik’a mata cup d’in tare da murmushi.
“Nagode duk sanda na sha ruwan nan ina samun natsuwa.”
Fad’awa tayi jikinshi tana fad’in
“Zanyi komai dan ka samu farin ciki Daddy idan ruwan fridge d’inka ya k’are kaman magana zan kawo maka wasu amma inasan ya zama sirri bansan matarka tasani.”
Dariya yayi yace
“Angama zanyi duk yanda kika ce”
Haka kawai yaji ya bata amsa batare da ya mata gardama ba, kuma kullum idan yana ganin Haneefa yana k’arajin k’aunar ta da sabuwar natsuwa da ke kamashi. A haka ya mata sallama ya fita, da murna ta koma cikin gida, duk abinnan da akeyi Mufeedah bata sani ba a tunaninta ta gama dasu tun da ya Koresu daga cikin gidan nan gaba kad’an ma zai rabasu da gidan, alk’awari ne da ta d’aukar ma kanta. kuma shima bai gaya mata Haneefa na bashi ruwa ba. Tana shiga d’aki ta fad’a kan gado.
“Na gama wannan cikin nasara Allah ka bani ikon aikata sauran suma cikin nasara batare da wata matsala ba.”
Ji tayi An karb’a da
“Ameen”
Juyawa tayi Ammi taga ni tsaye da gudu ta tashi ta rungumeta tana dariya. Itama rungume d’iyarta tayi tana shi mata albarka.
BAYAN SATI BIYU
Zirga zirga ta keyi cikin d’aki ta rasa abinda za tayi tafara komai a sa’a amma tana ganin abun kamar ba zaizo mata da sauk’i ba, tun da ta gama ba Imran ruwan magani ta rasa abinyi, sai dai tayi imani ruwan shanshi akwai ayoyin Allah wanda ita da kanta take mashi kuma ta tabbata yana sha dan ta fara ganin canji daga gareshi. Sai dai ta rasa ta ina zata fara bincike cikin gidan har ta gano asirin da ta binne. Haka ta dinga zirga zirga cikin d’aki tana tunani, wata zuciya taji tana k’arfafa mata guiwa akan zata iya kuma komai zai zo mata da sauki.
Dasauri ta zuri hijab d’inta tayi hanyar fita, a bakin k’ofa sukayi karo da Mukhtar yana daidai shigowa
“Adda Haneefa Ina zaki haka kike sauri?”
Murmushi tayi ta duk’a daf dashi, dafa kafad’unshi tayi tare da fad’in
“Zanje in ida aikin da Papa ya sani kaji, Kai dai kawai ka bini da adu’a”
Tana gama fad’in haka ta tashi tayi hanyar fita. Muryanshi ta juyo yana mata adu’a
“Adda Allah ya baki sa’a ya tsareki ya kare mana ke.”
Juyowa tayi tana murmushi
“Ameen Auta nagode kaji”
Tana fad’in haka ta juya ta nufi hanyar fita….
Tana fita tayi hanyar lambu, magana taji ta window Mufeedah lab’e wa tayi dan taji maganar mi takeyi.
“Lash Ina cikin matsala”
“Matsalar mi?”
“Imran ya fara canjawa ban isa in sakama Imran doka yanzu ya biba na d’auka na gama da matsalata tun da ya raba Ramlah da cikin gidan kuma na kauda Ahmad dake kawo man matsala, sai gashi wata matsalar babba na neman faruwa, kodai asirin da nayi yafara karewa ne. wallahi Lash a yanzu san Imran nake dagaske amma yana neman ya canja man bansan ya zanyi ba ki taimakeni kiban shawara.”
Numfasawa Lash tayi tana fad’in
“Hanya d’aya ce zamu bi shine mu koma wajen boka Dumbus shi zai warware mana komai.”
“Zuwa wajen boka bashi bane mafita ke kanki kinsan yanda mukayi dashi last zuwan da mukayi dan haka komawa wajenshi ba shi bane ba solution.”
“To yanzu ya zamuyi?”
Tsoki Mufeedah tayi tace
“Kibar komai a hannuna zanyi maganin komai da kaina.”
Murmushi Haneefa tayi cikin ranta tana fad’in.
“Asirinki ya gama tonuwa duk wani shiri da kikayi ni zan b’ata maki shiri daga yanzu zan fara bibiyarki dan nasan bazaki zauna haka ba.”
Duk a zuciya take magana, b’angare d’aya kuma kuka take da yau taji wacece dalilin mutuwar mutumin da tafi k’auna bayan iyayenta dan haka tama kanta alk’awari sai taga bayan Mufeedah kamar yanda taga bayan Ahmad.”
Hawaye ta share ta nufi cikin lambu.
STORY CONTINUES BELOW
Wuri ta samu ta zauna tayi ta gumi, babu abinda ka keji sai kukan tsuntsaye, hawaye suka dinga gangaro mata sakamakon tuna kalaman Mufeedah da taji tana ba k’awarta labari. Hannu ta d’aga sama tana rok’on Allah
“Allah kaban ikon tona duk wani asiri da wannan baiwar taka tayi.”
Shafawa tayi, tare da d’aukar wani d’an icce tana wasa dashi wani tudu ta gani ji tayi bata yarda dashi ba, tashi tayi ta matsa wajenshi iccen hannunta ta fara tona wurin amma yak’i tono abinda ke wurin. Tashi tayi ta fara waige waige, wani k’arfe ta hango dasauri ta d’aukoshi, duk’awa tayi da bismillah ta fara tona ramin, a hankali take tonashi har tazo k’arshe cigaba da tonawa tayi tauri taji bismillah tayi ta saka hannunta da zumar ta zaro koma miye. Iska ne ya taso mai k’arfi d’aukar ta yayi ya wurgi da ita, adu’a ta farayi cikin ikon Allah iskan nan yayi sauki. Tashi tayi ta koma wajen ramin adu’a tayi sosai kana ta saka hannunta cikin ramin, wani bak’ar leda ta d’auko tashi tayi da sauri ta matsa gefe warware ledan tayi wani hayaki ya dinga tashi adu’a tayi sosai kana hayak’in ya daina fita, layu ta gani cikin ledar warware tayi sunan Ramlah da Imran ta gani sai Allura 99. Hamdala tayi ma Allah ta maida k’asa ta rufe kamar yanda taga wurin dan kar a gane, kwashe layun tayi ta nufi hanyar cikin gidansu. Ganin ba kowa parlour yasa ta nufi kitchen, ashana ta d’auka ta kunna ma layun, ci suka dingayi tare da wani irin kuka da akeyi wanda bai tsoratata ba sai ma k’arfin guiwa da ta samu tare da adu’o’i, sai da wutar nan ta cinye layun nan tas kana ta daina jin kukan da akeyi.
Hamdala ta yima Allah ta juya zata koma cikin d’aki, juyawar da zatayi sukaci karo da Ramlah da gudu ta k’arasa gurinta ta rungume
“Ammi….”
Rufe mata baki tayi tare da murmushi tace
“Naga komai Allah ya maki albarka ya k’ara baki nasara abinda nakesan ki dashi yanzu ki k’ara kula kiyi a hankali kibi komai a sannu..”
“In shaa Allah Ammi ke dai ki cigaba da yimana adu’a.”
Tafe yake cikin mota, kanshi yaji ya sara mashi dafe kanshi yayi yana fad’in wash kaina, ganin idanuwanshi sun fara rufewa ya samu da kyar yayi parking gefen titi. Kanshi ya d’ora kan sitiyari da kyar ya fara adu’an neman d’auki a hankali yaji sarawan kan tana ragewa. K’ok’ari yake ya tuna wani abu da yafaru dashi amma ya kasa tunawa, haka ya tada mota yayi hanyar gida jiki a mace.
Yana shiga bai ko yi parking dai dai ba ya fito ya nufi cikin gida ba tare da sallama ba.
Dasauri ta tareshi
“Imran lafiya ka shigo cikin gida ba tare da kayi sallama ba?”
“Hannun ya d’aga mata alamar bai san magana, k’arasowa tayi inda yake tace
“Magana nake da kai”
D’ago idonshi yayi da suka canja kala yace
“Dan Allah Mufeedah ki rabu dani bansan surutu kuma ban ce ki shigo inda nake ba dan bana buk’atar kowa kusa dani a yanzu.”
Yana gama fad’in haka ya juya yayi d’akinshi, tsaye tayi sake da baki ga wani bak’in ciki da ya hanata magana. D’aki ta nufa da gudu tana kuka.
Yana shiga d’aki ya bud’e fridge buttle water ya d’auko ya bud’e ya kafa kai, bai aje roban ba sai da ya shanye kana yaji natsuwa ta sameshi. Bisa gado ya fad’a yayi rub da ciki yana tunani a haka bacci yayi gaba dashi.
BAYAN KWANA UKU
A gurguce, abubuwa sun faru da yawa cikin kwana uku ciki harda sauyawar Imran, kwata kwata bai shiga harkan mufeedah kuma idan ta ishe shi da surutu tashi yake ya bata wuri, ko ya bar mata gidan. Ba k’aramin d’aga hankali Mufeedah tayi ba duk hanyar da zata bi tabi dan ta juyo da hankalin Imran ya dawo kanta amma kwata kwata bata gabanshi, babu yanda ta iya illah ta koma wajen boka nakan Tudu ta bashi hak’uri ya sake mata sabon shiri akan Imran. Da wannan shawaran Mufeedah ta natsu akan idan gobe tayi zata shirya ta tafi wajen boka. Haka take a b’angare Imran duk abubuwa sun mashi yawa yana san ya tuna wani abu da ya manta amma ya kasa tuna komai. Duk halin da Mufeedah ke ciki Haneefa na sane dashi dan tana bibiyarta sosai ba tare da ta sani ba, harta zuwan ta wajen boka ta sani, Sai dai tayi alk’awari sai ta b’ata mata duk wani shiri da takeyi da wanda zatayi nan gaba.
2:30am
Sanye yake da fararen kaya sunyi mashi kyau sosai, ta kowa yakeyi wajenta murmushi yake mata itama murmushin ta mashi k’arasowa yayi kusa da ita ya zauna yana mai k’ara sakar mata murmushi, Itama murmushin take mashi. sun kusa minti goma ba wanda yayi ma d’an uwanshi magana sai dai murmushi, ganin shirun yayi yawa yasa ta yanke shirun tare da fad’in
“Papa ka k’ara kyau”
Dariya yayi wanda ya bayyana fararen hak’oranshi tare da fad’in
“Kema kinyi kin k’ara girma ga kyau da kikeyi.”
Murmushi tayi ta kauda kanta gefe guda. Hannunta ya rik’o juyowa tayi ta kalleshi, shima ita yake kallo.
“Nagode kwarai da yanda kika cikaman burina naji dad’i sosai da kikeso ki maido da martaban iyayenki tabbas haneefa kin cika d’iya, d’iyar da kowa zaiyi alfahari da ita bayan ya sameki, kinyi k’ok’ari sosai Sai dai har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu.”
Dasauri ta juyo tana fad’in
“Aiki?”
“Eh aiki”
“Wane irin aiki? Wallahi nagaji papa bazan iya ba”
“Zaki iya dan nasan zaki iya shiyasa na sakaki aikin da zakiyi yanzu yafi ko wane muhimmanci amma yafi kowane had’ari idan kikayi shi to ina tabbatar maki mahaifinki zai dawo cikin hayyacinshi ki daure ki k’arasa Haneefa.”
Ajiyan zuciya tayi tana fad’in
“Taya zan fara?”
Murmushi yayi tare da shafa kanta
“Allah ya maki albarka”
“Ameen”
“Akwai wani asiri da Mufeedah ta saka a d’akin Imran wanda idan kika cireshi kin gama da komai nata sai dai bansan inda yake ba amma nasana cikin d’akin yake shiyasa nace maki yafi sauran wahala amma nasan zaki iya.”
“Bazan iya ba”
“Zaki iya ni nasan zaki iya, ki taimaka ki dawo da farin cikin iyayenki ke kad’ai yanzu zaki iya basu farin ciki sanadiyar tona duk wani asiri da aka masu, idan har kika kasa to yana nufin iyayenki zasu cigaba da zama basu k’aunar junasu, kuma ni nasan zaki fisan farin cikin iyayenki akan naki nasan zaki iya dawowa da farin cikinsu koda hakan na nufin rasa naki farin ciki.”
Yana gama fad’in haka ya tashi ya tafi, kira ta dinga kwala mashi amma bai juyo ba.
A firgice ta farka ta fara juye juye, tabbas mafarki ne tayi kuma da Ahmad. Maganganun su suka dawo mata a kwakwalwa, hannu ta d’aga sama tana mai neman Allah ya taimaka mata. Tagumi tayi tana tunanin ta ina zata fara, ganin shirun ba abinda zai mata ta tashi ta d’auro alwalla tazo ta kabbara sallah tana mai neman Allah ya bata sa’a akan abinda ta saka gaba. Bata tashi akan sallaya ba sai k’arfe bakwai na Safiya kana ta koma kan gado, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita..
STORY CONTINUES BELOW
Bata farka ba sai k’arfe sha d’aya, dasauri ta diro daga kan gado tayi hanyar toilet, tana fitowa wanka ko mai bata shafa ba ta saka turare ta zura doguwan riga ta fita, a parlour suka had’u da Ammi. Gaida Ammi tayi, cikin sakin fuska ta amsa.
“Ina last born?”
“Ya tafi makaranta”
“Allah sarki Auta kwana biyu bamu had’uwa”
“Shi kanshi rigiman da ya dingayi kenan yau wai bazai tafi school ba sai ya tadaki ko ya jira sai kin tashi dan yana mssn d’inki dakyar na lallabashi ya tafi ga exams sun fara.”
Langwab’e fuska tayi tana fad’in
“Wayyo Auta nima nayi mssn d’inshi amma yau in shaa Allah zamu had’u d’akin mu ma zai kwanta ba wurinki ba yau.”
Tab’e baki tayi tace
“Kyaji dashi.”
Mik’ewa tayi tace
“Ammi bari naje lambu”
“Kalacin fa?”
“Kin manta yau Thursday ina azumi “
“Hakane fa na tuna”
Waje tayi dan tanasan yau ta fara aikinta akan cikin gidan Imran.
“Amma Taya?”
Tambayar da tama kanta kenan, kafin ta samo amsa taji hannunshi cikin nata, d’agota tayi ta kalleshi murmushi ya sakar mata.
“Tunanin mi kike princess ?”
“Bakomai Daddy Ina kwana?”
“Lafiya lau ya bata amsa”
“Ina zakije ne?”
“Zanje lambu”
“Dan zan fita da na rakaki.”
Murmushi tayi tana fad’in
“Ina Anty? Banga motar taba”
Tab’e baki yayi yace
“Ohon mata inaga tafita dan tun safe nima ban ganta ba.”
Wani murmushi ta saki tace
“Bari na shiga d’akin ka na gyara nasan yayi k’ura.”
“Kamar kin sani ki wanke harda toilet”
Amsa mashi tayi da
“To”
Tayi gaba cikin farin ciki. Shima wajen da ake fakin d’in mota ya nufa. Motarshi yama wuta yabar haraban gidan….
Da murnanta ta fad’a cikin gidan, kai tsaye d’akin Imran ta nufa, tana shiga taji gabanta ya fad’i adu’o’in neman tsari ta karanto kana ta nufi cikin d’akin, kai tsaye toilet ta nufa duk abind ke toilet sai da ta fito dashi duk wani sak’o da lungu sai da ta duba amma bata ga komai ba, wanke toilet d’in tayi ta maida komai wajen shi ta kunna turaren wuta, tsaf toilet d’in yayi kamar ba’a tab’a amfani dashi ba. Fitowa tayi bed room ta zauna bisa gado tayi tagumi.
Hawaye suka gangaro mata, duk iya tuninta ya k’re kan toilet zata ga komai sai gashi ta duba ko ina amma babu alamun wani abu da yayi kama da asiri, kuma Papa ya tabbatar mata koma miye yana cikin d’akin Daddy.
“Allah ka taimakeni”
Abinda ta fad’a kenan, tashi tayi ta fara tattara d’akin dan gadon a gyare yake shara tayi da goge goge harta mopping sai da tayi sai da ta ga komai yayi daidai kana ta nufi hanyar fita, juyawa tayi ta kalli d’akin, ji tayi tanasan ta juya katifan saboda taga kamar tayi k’asa kuma zata iya saka mutum ciwon baya, dasauri ta koma ta yaye zanin gadon, da kyar ta cire katifan tana neman juyawa datti tagani k’ark’ashin gadon, ajiye katifan tayi gefe guda ta d’auko tsintsiya, katakan gadon ta cire. Abinda tagani ne ya d’aga mata hankali kwarya ce da wani ruwa tsutsotsi na sha, adu’a tayi ta rufe ido ta ciro kwaryan ta aje gefe da sauri ta maida komai ta shimfid’a zanin gado ta d’auki kwaryan tayi hanyar fita dashi, can baya wajen lambu ta nufa, daidai fitowar Ramlah daga BQ ganin Haneefa da kwarya tayi hanyar lambu yasa tabi bayanta…
Tana aje kwaryan ta fara adu’o’i ta dad’e tana adu’a kana ta d’aga kwaryan sama ta saki wuta tafara ci wajen sai wani kuka da akeyi. Daidai Mufeedah na k’arasowa wajen da gudu dan tana shigowa gidan zata shiga cikin gida kenan ta juyo muryan Haneefa na karatu, zuwan da tayi dan ta ja mata kunne karta k’ara mata karatu kusa da d’aki kwaryan da ta gani hannun Haneefa ne ya d’aga mata hamkali amma kafin ta k’araso Haneefa ta fasa kwaryan. ta nufi Haneefa zata shak’e Ina k’afarta ta rik’e wasu k’urajene suka fara fito mata. Ja da baya Haneefa tayi ta nufi wajen Ammi dake tsaye ta kasa tab’uka komai
Hawaye Mufeedah ta farayi tana fad’in
“Kinyi nasara akaina dama boka ya gayaman na d’auka zan iya gamawa dake sai gashi kafin In an kara kin gama dani Haneefa lallai d’an hakkin da ka raina shike tsone maka ido ban tab’a d’aukan ke zaki gama dani ba.”
Dariya Haneefa ta tuntsire da ita tace
“Sai kuma gashi na gama dake ko? Dama na maki alk’awarin sai na kawo k’arshen ki to yau gashi kuma na cika maki alk’awari, sauran hukunci kuma sai Daddy yazo..”
Tana gama fad’in haka taja hannun Ammi sukayi cikin gida, sai a lokacin Hawaye suka zubo ma Ramlah, hannu Mufeedah ta d’ora akai tace
“na cuci kaina Allah ka kawo man d’auki.”
Nikam nace sai a yanzu kika san Allah?
STORY CONTINUES BELOW
Jiri ne yaji yana d’iban shi ga kanshi yana sarawa dafe kanshi yayi amma jiri bai daina d’ibanshi ba gaba d’aya kamaninshi ya canja.
“Kaina”
Abinda yake fad’a kenan, k’ara ya saki ya fad’i sumamme daidai Haneefa da Ramlah na k’arasowa da gudu sukayi kanshi, da taimakon mai gadi suka kaishi cikin gida. Ruwa Ramlah ta dinga yayyafa mashi ko motsi baiyi ba, kuka ta fashe dashi hannunta Haneefa taja ta zaunar da ita, komawa tayi kusa dashi ta fara mashi karatun alqur’ani an d’auki lokaci ya fara motsi da hannun shi a hankali ya dinga bud’e idonshi har ya gama bud’e su bai sauke idonshi ba sai kan ramlah, wadda tayi bak’i ta rame kamar ba Ramlah ba. Dasauri ya tashi sai dai jikinshi ba k’arfi komawa yayi ya kwanta yana mata nuni da hannu da tazo gareshi, kuka ne yaci k’arfinta ta tashi ta nufi d’aki da gudu tana kuka. Kallon Haneefa yayi da alamomin tambaya, murmushi tayi ta kamashi ya zauna, ruwa ta d’auko a cup ta mashi adu’a kana ta bashi ba musu ya karb’a, duk abin an da akeyi maigadi na tsaye shi kanshi kuka yakeyi dan duk abinda yake faruwa gidan babu abinda bai sani ba..
“Mike faruwa da nine princess?”
Tambayar Haneefa yayi yana mai dubanta, itama shi take duba da idanuwanta suka rine sukayi ja dan da wuya kaga kukanta.
“Daddy…….. nan ta kwashe komai ta gaya mashi har yanda taji mutuwar Ahmad sai da ta gaya mashi.”
Kuka ya fashe dashi mai tsuma rai yace
“Na cuci kaina na auro wadda ta rabani da farin cikina a dalilin auren da nayi ta rabani da d’an uwana da duk duniya banda kamar shi ta rabashi da numfashinshi ta kumayi sanadiyar rasa d’ana danayi Allah kayafeman.”
Kuka yakeyi sosai yana sabbatu, tashi yayi ya nufi d’akin Ramlah, Haneefa ba tayi yunk’urin binshi ba dan tasan suna buk’atar privacy.
Yana shiga d’akin ya zube kan k’afafuwanshi yana mai fuskantanta k’afarta ya kama yana kuka.
“Gani gabanki ni mai laifine ta sanadiyar auren da nayi kika rasa d’anki da d’an uwanki bazan iya baki hak’uri ba, ki yanke man hukuncin da kika san ya dace dani wallahi zan karb’i ko wane irin hukunci ne amma banda na rabuwa dake..”
Itama kuka takeyi sosai, d’agoshi tayi tace
“Duk abinda ya faru baka da laifi duk abinda kayi kayishi cikin rashin sani ne saboda an kauda maka hankalinka dan haka na yafe maka komai dama can ban rik’e ka ba.”
Kafin ta ida magana ya rungumota, suduka kuka sukeyi mai tsuma rai sun dad’e a haka kana yaja hannunta suka fita. Ganin su da Haneefa tayi haka ba k’aramin dad’i taji ba sai a sannan Hawaye suka gangaro mata, ko a yanzu tasan ta cikama Papa burinshi wanda ya dad’e yanaso yaga ya cika.
“Ina Mufeedah?”
Muryan Imran taji ya fad’a rai b’ace.
“Tana lambu”
Tabashi amsa, jan Ramlah yayi suka fita, binsu a baya Haneefa da maigadi sukayi. Inda suka barta tana nan zaune, Amma duk wanda yasan Mufeedah idan ya ganta yanzu bazai gane ta ba, saboda gaba d’aya halirtanta ta canja, gaba d’aya k’uraje sun fito mata masu k’ak’ayi duk inda ta sosa sai su fashe ga kuma wari da sukeyi. Suna isowa suka toshe hanci dan gaba d’aya wari takeyi ga k’uraje har a fuskanta.
Kallon takaici Imran ya mata yace
“Ko a haka aka barki kinga darasi ai da nayi niyar kasheki kamar yanda kika kasheman d’an uwa na da d’ana amma na fasa saboda nafisan kisha a zaba ki d’and’ani a zaba a duniya kafin kije lahira ki iske wadda Allah ya tanadarma irinku. Kiga yanda kika koma wannan ya isheki ishara dake da duk wani mai hali irin naki, Mufeedah na sakeki saki uku.”
Hannu ta d’ora bisa kai ta fasa uban ihu
“Nashiga uku Imran dan Allah kuyafeman Ramlah ke na cuta dan Allah ki yafeman ko nasamu sassauci daga wajen Allah wallahi jikina zafi yakeyi kamar ana huraman wuta, kuyafeman dan Allah yanzu haka daga wajen boka nake yabani magani in saka maka a abinci da kaci kaga ganin kowa sai ni sai dai kafin na saka Allah yayi ikonshi a kaina. Imran na cuceka kai da Ramlah duk abinda ya shiga tsakanin ku nice sila….” komai ta kwashe ta gaya mashi tun daga randa ta fara ganinsu da irin asirin da ta masu sai da ta tona.
Kallonta Imran yayi yana huci
“Allah ya isa tsakaninmu dake wallahi bazan iya yafe maki ba..”
Dubanta ta kai kan Ramlah tace
“Ramlah ki yafeman nasan ke mai hak’uri ce dan Allah ki yafeman ko nasamu sauk’in azabae da nakeji..”
Allah sarki Ramlah mai zuciyar imani kuka ta fashe dashi, ta bud’e baki zatayi magana, Imran ya rufe bakin tare da janta. Dan yasan da tayi magana to zata yafe mata ne shikuma abinda baiso kenan gara duniya ta mata hankali..
Hannun Ramlah da Haneefa ya kama suka nufi cikin gida suna kuka, dan bak’aramin tausanta Ramlah keji ba har dai yanda taga lokaci guda Allah ya canjata lallai mutum ba a bakin komai yake ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Dan Allah maigadi bani wayarka in kira Lash”
Ba gardama ya mik’a mata, number Lash ta kira sai da ta kusa tsinkewa kana aka d’auka
“Hello Lash”
“Ba ita baceba Allah yama Lash rasuwa d’azu sakamakon had’arin mota da suka samu yanzu ma aka dawo daga rufeta.”
Ihu ta saki tana fad’in
“Nashiga uku na lalace Ina zan saka kaina Lash ta rasu.”
Wayarshi maigadi ya karb’a yace
“Hajiya ki tashi ki tafi kar maigida ya zagayo yazo ya tardaki dan raina sai yafi naki b’aci.”
Bata da zab’i dole ta lallab’a ta tashi da kyar take taka k’afarta dan idan ta takata ji take kamar ranta zai fita saboda zafi da suke mata, haka ta fita daga cikin gidan, juyowa tayi ta kalli gidan hawayen da suka mak’ale mata suka gangaro, tafiya takeyi ita kanta batasan ina ta nufa ba…
Tunda suka shiga cikin gida ya had’a kan iyalanshi, dan a lokacin Mukhtar ya dawo daga school, kuka yakeyi sosai yana neman yafiyarsu da kyar suka samu yayi shiru, had’asu yayi gaba d’aya ya rungume kamar wani zai kwacesu.
Haneefa ce tayi gyaran muryan tace
“Nasan duk kunasan kusan ya akayi nasan komai, har dai kai Daddy dan Ammi tasan wasu abubuwa saidai itama ba komai ta sani ba to………..nan ta kwashe duk yanda sukayi da Ahmad a asibiti ta gaya masu har mafarkin da tayi da ya gaya mata akwai asiri d’aki Imran babu abin da ta rage.”
Kuka Imran da Ramlah keyi sosai. Imran yace
“Allah sarki Ahmad ta sanadiyar farin cikin mu ya rasa nashi farin cikin Allah ya jik’anka da rahma.”
“Ameen”
Gaba d’aya suka amsa. Kallon Haneefa yayi yace
“Tabbas samunki a rayuwa ba k’aramin alkairi ba ne nagode ma Allah da ya mallakaman ke a matsayin d’iya Ina alfahari dake kuma zan cigaba da alfahari dake har k’arshen rayuwata Allah ya maki albark.”
Fad’awa tayi kanshi tana fad’in
“Ameen Daddy, Zanyi komai dan inga kun dawwama cikin farin ciki, ganinku cikin farin ciki yafi man komai a rayuwa ko a yanzu nasan Papa yana cikin farin ciki saboda burinshi ya cika Allah ya jik’anshi da rahma.”
Gaba d’aya suka amsa da
“Ameen”
Gaba d’aya ya k’ara had’asu ya rungume yana k’ara godema Allah da yafarkar, dashi akan had’arin da ya fad’a…
A GURGUJE
Bayan kwana biyu, cikin kwana biyu komai ya koma daidai gidan Imran, duk idan ka gansu zakayi tunanin basu tab’a shiga halin k’unci ba, kullum k’ok’arinshi yaga ya kyautatama iyalanshi, a kullum sai yayi kuka ya rok’i Allah gafara akan ya yafe mashi abinda ya aikata, kuma kullum sai yama Ahmad da Haneef adu’a samun Aljanna. Ita kanta Ramlah kullum k’ok’ari take ta mantar dashi Abinda ya wuce saboda ba yin kanshi bane be..
Kwance take cikin bola gaba d’aya jikinta tsutsa yake fitarwa, tayi bak’i ta rame ga gabanta wasu ruwa masu wari da yake fitarwa babu wanda zai iya gane mufeedah ce cikin wannan halin.
Tafe yake da gudu bisa mashin sakamakon hanyar babu abun hawa sosai, gaba d’aya mashin d’in ya kwace mashi neman birki yake ya taka amma ya kasa, bai an kara ba sai dai yaji k’ara, dubawar da zaiyi yaga ya takata gaba d’aya k’afafuwanta suka kare, ga jini dake fita, ganin ba kowa yaja mashin d’inshi yayi gaba ya barta nan cikin azaba.. kuka take tana neman d’auki amma babu wanda yazo bare ya taimaka mata, fizge fizge ta fara tana cire gashin gabanta, a haka har Allah ya karb’i ran Mufeedah cikin wannan halin…
Gaba d’ayansu suna parlour zaune, shigowa yayi da sallama, tashi tayi taje wajenshi, tana k’arasawa ya kamata ya rungume yana mata peck a goshi, sunne kanta tayi cikin k’irjin shi tana mashi magana
“Baka ganin haneefa da Mukhtar?”
Dariya yayi yace
“Nagansu, dan suna wajen sai na fasa rungumar matata, beside Haneefa ma kwana nawa ya rage nayi suruki tunda gashi ta gama SSCE d’inta yau.”
Dariya tayi ta d’ago daga k’irjinshi taja hannunshi suka k’arasa cikin parlour.
“Daddy sannu da zuwa”
Gaba d’aya suka fad’a. Amsawa yayi da murmushi ya zauna cikinsu, kallon Haneefa yayi ya mik’a mata hannu sukayi shaking yace
“Congratz Allah amfana abinda kika karanta, my baby is grow up now.”
Dariya tayi tace
“Thnx Daddy”
Waya ya mik’o mata IPhone X yace
“Ga gift d’ina”
Ihu ta saki tare da fad’awa kan Imran tana murna
“Karki karyaman miji”
Cewar Ramlah dake tsaye
Dariya tayi tace
“Bazan karya maki tsohon mijinki ba”
Duka ta kai mata ta goce tana Dariya, suma Dariyan sukeyi.
“Daddy na gode Allah ya k’ara rufa asiri”
“Ameen princess”
“Daddy ni Ina nawa wayan?”
Mukhtar ne ke magana kamar zaiyi kuka, Dariya Ramlah tayi tace
“Kyalesu soja na ni zan sai maka wanda tafi na Adda kyau kaji.”
Murna ya dingayi za’a sai mashi wayan da yafi na Adda.
“Miji za’a fito dashi ko kuwa karatu za’a cigaba?”
Cewar Imran da ya zuba mata ido yana kallonta.
“Zumb’uro baki tayi tace
“Daddy karatu dai kasanfa jamb d’iya 209 naci beside Ina san na cikama Papa burinshi na In zama doctor, kasan dama yace ni medicine zanyi.”
Dariya Imran yayi yace
“Hakane nima wasa nake maki ay babu gatan da zan baku yanzu da ya wuce ilimi, amma kisani karatu bai hana aure idan miji ya zo maki wanda hankali na ya kwanta dashi zai rik’eman ke da amana to zan aurar dake.”
Sai a sannan Ramlah ta zauna kusa da Mukhtar tace
“Dama ko kasan yaron Alhaji Najeeb ya ganta yanaso nine na dakatar dashi nace ya bari sai ta k’are secondary school, to d’azu sai gashi ya turo Mamansu wai ya maganar tunda yanzu ta gama school.”
Da murmushi yace
“Wane Alhaji Najeeb ba dai makwabcinmu ba?”
“Shifa”
“Wane yaron nashi daga ciki?”
“Naufal, kasan germany yake aiki, to sun hana ya koma sai yayi aure kaga idan sun daidaita kansu bayan biki basai tayi karatunta can ba?”
Dariya Imran yayi sosai yace
“Wannan shawara tayi, amma sai naji daga gareta kinsan bazan yimata dole ba, in tana sanshi shikenan.”
Kallonta yayi yace
“Princess kina sanshi? Karkiji komai ki gayaman abinda ke ranki duk abinda kikeso shi nakeso bazan maki dole ba.”
K’asa tayi da kanta tana murmushi, dan gaskia ta dad’e tanasan Naufal dan guy ne wanda mata ke kwakwar samun irinshi kullum inta ganshi sai taji wani abu ya ratsata bata tab’a tunanin ya santa ba bare har yace yana santa dan ko kallon mutane bayayi dan Naufal miskili ne.
“Kinyi shiru ana tambayarki”
Cewar Ammi da taga bata da alaman yin magana.
D’agowa tayi ta kallesu tace
“Daddy Ammi idan kun yarda da natsuwarshi da tarbiyanshi na amince.”
“Allah ya maki albarka Haneefa, tabbas kinyi miji dan kowa yasan yaran gidan Alhaji Najeeb daidai gwargwado suna da tarbiya.”
D’agowar da zatayi suka had’a ido dashi wani murmushi ya sakar mata, wanda yasa jikinta yayi sanyi. Ya dad’e tsaye yana jinsu dama shigowar Imran ya gani shine yaje ya sami babanshi akan zaizo ya mashi magana, yanasan Haneefa, shine babanshi yace mashi yazo.
Sallama yayi ya k’arasa cikin parlourn, gaba d’aya suka amsa mashi suna mashi murmushi, Banda Haneefa da ta duk’ar da kanta tana jin kunya. Wuri ya samu k’asa ya zauna gaidasu yayi cikin Ladabi, amsawa sukayi cikin sakin fuska, nan ya gaya masu buk’atarshi, Imran kuma ya amsa mashi ya kuma k’ara bashi tabbacin cewa gobe ya turo mashi magabatanshi dan su tsaida maganar aure.
Magabatan Naufal sunzo akan neman ma d’an su auren Haneefa an kuma basu, an saka ranan aure sati d’aya saboda hutun Naufal zai k’are kuma yanasan ya tafi da matarshi, sun biya sadaki dubu d’ari, Sai dai jiran ranan d’aura aure.
Soyayya tsaftatacciya akeyi tsakanin Naufal da Hanefa kowa Yana burin kyautatama d’an uwanshi, dan dukansu Wannan ne soyayyarsu ta farko dan haka duk abu na kyautatawa shi sukeyi. Kallonta yayi yace
“Princess Visa d’inki tafito yau zanje na karb’o.”
“Inzo In rakaka?”
“Ah ah ki zaman ki randa mukaje kiga yanda maza ke kallonki sai da nace masu matata ce nidai bazanje dake ba.”
Dariya tayi tace
“Sai kadawo.”
Peck ya mata ya juya ya tafi.
A yau aka d’aura auren Naufal Najeeb da Haneefa Imran inda dubban mutane suka shaida, kuma a yau jirginsu zai d’aga Zuwa germany, bayan d’aurin aure aka kai amarya wajen iyayenta suyi mata fad’a dan za’a wuce da ita Abuja ta nan zasu tashi, gaba d’aya kuka sukeyi sosai, da kyar Imran yace
“Kiyi biyayya ga mijinki hak’urinki da juriyar da nasanki da ita ki cigaba Allah ya maki albarka.”
Yana gama fad’an haka yayi cikin d’aki, fad’awa tayi kan Ramlah tana kuka ita kanta Ramlah kuka takeyi sun dad’e a haka kana Ramlah ta janye ta daga jikinta ta mata adu’o’i ta tashi da kanta ta mik’a ma Naufal ita tana murmushi tace
“Ga amanar yar uwarka nan Allah ya maku albarka.”
Amsawa yayi da
“Ameen”
D’akinta ta nufa tana kuka, hannun Haneefa yaja suka shiga mota inda mota uku ce zata rakasu Abuja daga can kuma su wuce Germany. Sai muyi masu fatan alkairi, Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a d’ayyaba.
Zaune take parlour ita kad’ai yan biki kowa ya tafi, Mukhtar kuma yayi bacci. Shigowa yayi da sallama, amsa mashi tayi jiki ba kwari, k’arasowa yayi wajenta yace
“Angel lafiya?”
Fad’awa tayi jikinshi tana kuka, bubbuga mata baya ya farayi yace
“Kina mssn princess ryt?”
D’aga mashi kai tayi alamar
“Eh”
Dariya yayi yace
“Princess tama manta dake tana can ta kama mijinta Ke kuma zaki saki naki mijin kodai In k’aro maki abokiyar zama?”
Fad’awa tayi jikinshi tana mashi dukan wasa, shikuma yana janta, sai da yaga ta sake tana dariya kana ya kyaleta, rungumota yayi ya mata rad’a
“Ya kamata na baki ajiyar Lil Ahmad cikin Daren nan dan gidan nan yana buk’atar yara tunda princess tayi aure.”
Dariya ta fara tana neman kwace kanta, rik’e ta yayi sosai yanda bazata iya kwacewa ba a haka ya dinga aikamata da sak’onni kala kala, tun tana zillewa har tafara maida mashi, tashi yayi ya kamata suka nufi d’aki….
Nikuma zan dasa aya daga nan…
Alhamdulillah anan na kawo k’arshen makirci ko Asiri, kuskuren da nayi Allah ya yafeman,