MALIKA MALIK CHAPTER 17 BY JANAFTY
……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata Soyayyah mai tsayawa azuciyar masoya Shi Saleem da Malika Suke gudanarwa gwanin ban Sha’awa ga Wanda ya gani,Yadda take mai ladabi da biyayyah yafi komai burgeshi da ita,uwa uba kuma komai zata gudanar sai da Shawaranshi da kuma izininshi.
Malika tana da tarin Dukiya wanda batasan iyakarta ba, akallah bankunanta sunfi guda 5 kuma kowanne banki Duk wata riban kudi na miliyoyi suna Shigo mata harma ta rasa wani Tunani zatayi domin Taimakon al’ummah Dashi Domin dai ita bata da muradin kudi ayanzu haka Kudinta shine mijinta da Yarta,yana mata komai na bukatan Rayuwa da cigaba baya duba tana Dashi komai dayasan hakkinshine yana kokarin kare mata shi Har gobe Kudin da malika ta mallaka bai taba Tsole mishi ido ba,Yana kokarin Dorata ahanyar mai kyau tare da kyakyawan Shawara Domin Rabauta daga Duniya har Zuwa gobe kiyama..
Mganar Filayen datace a bincikamata a malumfashi an samu har Saleem yaje ya gani an kuma yi ciniki da dillallai an biya kudin manyan Filayen Guda biyu wanda aka bashi Duka takardun Filayen mai dauke da Sunanye malika,batayi wasa ba tabama Saleem Duka dama,shi kuma sai ya Umarceta data bama kawun nan Daddy dake nan Malumfashi kwangila kula da ginin makrantan da masallacin Saboda sune ke gari,shi kuma yana Nesa,ammh yamata alqawari lokaci bayan lokaci zai Dunga Zuwa yana Duba aikin.
Haka ko akayi ta Tura musu Kudin da zasu isa Duka aikin nan da anan aka bama ma’aikatan gini kwangila,suka Fara gininsu cikin Nasara Abunka da Kudi kafin kace kwabo gini yayi Nisa kuma Alhamdulillah Da Saleem zai je Duba aikin Tare da Malika Sukaje,taga komai da idonta ta kuma yaba,awajen ma Sai da tayi kwallah Saboda Tunawa da Daddyta datayi ammh tana mai addu’an Allah jikansa da Rahma.
Tabiya Family house dinsu sun gaisa Duk da bata zauna ba,tama iske Hajiya ta koma katsina Satin daya gabata so basu hadu ba,Haka Dangin Daddy suka taru suna sakama malika albarka,itakuma sai tace su godema mijinta Domin Shine Silan zamowarta Duk Abunda ta zama ayanzu,Domin da babu Shi acikin Rayuwarta da yanzu batasan awani Hali rayuwarta Zata Shiga Ba.
**********
Joda da marwan Sati biyu sukayi gidansu Ummi suka tatattara su ka koma lagos wajen aikin mijinta,wanda kafin su tafi sai da ya kaita malumfashi tayi sallama da yan’uwa da abokan arzuka kafin yakaita Zamfara tayi musu kwana daya ya kaita katsina wajen Hajiya nan ta kwana daya,tana Dawowa suka tattara suka tafi suka bar su Ummi Cike da kewa.
************
*INA LABARIN ZAHRA*
Zahra dai tana cikin gararin Rayuwa Domin daga Abba har momi sun Fita batunta bamai Kulata balle ya Shiga Sha’aninta har gwarama Nadira takan xauna ta lallasheta in taga tana kuka,ko ita din ma ba kamar da ba,kowa laifinta yake gani.
Zahra kishinta yakaita ga aikata Abunda yazo yana damunta,gashi tana Bala’in son Saleem ammh lokaci daya Zuciyarta da Sharrin Shedan suka Taimaka wajen Nesanta ta da Abunda tafi kauna Duk Duniya,bata Fitowa kullum cikin daki tana kwance tana kuka,shiyasa kafin tagama idda duk ta lalace ta kwarzane kamar ba Zahra ba mai iyayi da Rawan kai yanzu Duk bashi,sai ki ganta ta zauna tayi Shuru tana Sharan Hawaye kamar ba ita ba.
Ganin haka yasa sai momi ta Fara jawota ajiki ganin tana neman kashe kanta da Tunani,ammh Duk da haka zahra bata dawo da karkashinta na baya ba,Duk da ko Daga momin har Abba yanzu Sun Yafeta sun koma mata addu”an Allah ya Cire mata wannan mugun kishin kuma ya bata Wani mijin na gari.
Satin daya wuce suka Sha Bikin ya Nadir inda ya Auri Wata Scientics Aisha bala,Itama anan Asibitin Aminu kano,anan Suka Hadu suka Fara Soyayyah har ta kaisu ga Aure.Auren da akasha Shagali sosai Duk da Zahra ta dan Warware ammh ba kamar da chan ba,suna zaune awajen Asibtin Aminu kanon nan ya Nadir ke da gidanshi mai kyau da tsari.
Awajen bikin ne Nadira ta Hadu da Wani DR HAMBALI, wanda ya kasance Shima likita ne Anan Mallam Aminun kanon,kuma Senior Ya Nadir ne don ba yaro bane zai kai Shekara 45 aduniya yana mtsayin Constlant ne yanzu,matansa Biyu, ya’yansa Biyar,Bakano ne gaba da baya,yazoma Nadir Daurin Aure Anan yaga Nadira kuma yaji ta Shiga Ranshi har kuma ya gabatar da kanshi kuma nan da nan Nadira tayi accepting dinshi,bayan ya Sanarma Nadir din shima yayi Na’am da mganar,har kuma ya Sanar ma da Abba kuma ga duk alamu Nadira tana son Dr Hambali.
**************
Nadira tana kwance Suna waya Da Dr Hambali,Zahra na gefenta tana buga game awayarta taji Nadira na gaisawa da Ya”yan Dr Hambali Abun yabama Zahra mamaki har sai da ta dago tana binta da kallo,ganin yadda take Wani Lallaba yaran kamar Wasu ya’yanta na cikinta tana ji baban ya karbi wayar Nadira ta chanza murya tana mai Shagwaba,Galala Zahra tayi tana bin Nadira da kallon mamaki,wacce Tun lokacin da Zahra ta Fara mata kallon Tuhuma bata bi ta kanta ba sai da Sukayi irin Rabuwar da suka sabayi Cike da kaunar juna,kana ta dago tana kallon Zahra bayan tatashi Zaune tana kallonta kai tsaye tace”Best lafiya..? irin wannan kallon ai sai kisa na kware..”
Zahra ta Tabe baki tana Fadin”Wai keda waye kike wannan uwar Kashe muryan..? Ba dai da Tsohon Likitan ba,.? Wani Mirmishin Takaichi Nadira tayi kafin tace”Eh dashi ne,kuma ke kika ga tsoho nidai bangani ba kuma,kinsan Allah best ina Son Dr Hambali sosai kuma da izinin Allah Shi zan Aura..”
Kwalalo ido Zahra tayi tana Fadin”Kutumar ubanchan,best kina da hankali kuwa..?tsohon zaki Aura mai mata har biyu da ya”ya..”.?.”Wani Dirty look Nadira ta sakarma Zahra kafin tace”Eh Shi fa,ko yana da wani Aibu ne,ok sai yanzu nagane ina kika dosa,Saboda yana da mata harda ya’ya ko? Toh ni ba Ruwana da matansa balle ya”yansa Ni da Zuciya daya nakeson Dr Hambali,kuma da Zuciya daya zan Shiga gidanshi matanshi kuma zan basu girmansu a matsayinsu na wadanda ke gaba dani ba Ruwana da kishin Hauka,kishina kenan shine na koyi yadda zan tsaya azuciyar mijina ta hanyar mishi biyayyah da yin Duk Abunda yake so,ya’yansa kuma Suma ya”ya ne Tunda Shine Ubansu kuma soyayyar gaskiya Shine kaso Uba kaso ya”yanshi Shine maganar Gaskiya…”
Tafada tana mikewa Zahra data daskare tana bin Nadira da kallon Mamaki,kafin Ta Hadiye miyau mai daci tace”Yanzu ke Nadira sai ki Shiga cikin kishiyoyi har biyu..? Tabe baki Nadira tayi kafin tace”Toh Shine me..? Naga dai kowa ya iya allonshi ya wanke,balle ma dukkansu matan nasu muna waya dasu Anty Umaima da Anty Bilkisu basu da Wata mtsala,kinga Zahra keda zaman gida ke Burgeki gaki gashi ammh nikam kinganni nan nakusa tashi,kuma mganar Auren mai mata da kike mgana in ka tsarkake zuciyarka ka Shiga da Zuciya daya wlh ko mutum nada Mugun Nufi akanka sai ya koma mai..”Daga Haka ta kada kai Ta Fice daga dakin tana wake wakenta ko ajikinta..
Da kallon mamaki da al’ajabi tare Da Nadama Zahra ta Bita,domin ta Fahimci mgana ne Nadira ta sakamata Awasa wandada suka Zafeta sosai,Tagumi ta lafta tana Nazarin Rayuwart
a ta baya Sai kawai taji Hawaye suna zubomata,Tasani cewa malika bata taba kulla tanta ba kuma ta sani macece mai kirki sosai ammh son Zuciyarta da mugun kishinta ya Rufemata ido,harta kaita ga Aikata Abunda yazo ya Rabata da mijinta mai sonta da kaunarta,Kuka yazoma Zahra ta Fada kan gado,tana kuka abayyane mai cin Rai Tana juya mganganun Nadira acikin aranta,duk da Nadira bata taba bata Shawaran banza game da zamanta da Malika ba,aamh bata tsammaci zata iya murje ido ta Fadamata wadanan bakake mganuganun ba,Abun ya mata ciwo sosai Wuni tayi kuka tana karajin Nadamar Abunda ta aikata ta kuma dama ace Ana Dawo da hannun agogo baya data Ruga da Gudu ta gyara kuskuran datayi abaya,da yanzu tana gidan Mijinta cikin kwanciyar Hankali Nadira bama zata ganta ba balle harta gayamata wadanan Bakaken mganungun.
_Anan zan dan yi jan hankali garemu mu yan mata Wadanda muke Waje bamu Shiga daga ciki, ba babban burinmu Shine in mai mata yazo yace yana sonmu,Abu na Farko Shine bazamu Tsarkake Zuciyarmu ba,balle mu barta ta sakama na alheri A”a sai mu bari Shedan ya Shiga Zuciyarmu yana zugamu kan in mun shiga gidan kokarin mu,Mu Fitar da wacce muka samu aciki,bama Tunanin ita ya taji lokacin da mijinta ya auro ki ya kawoki cikin gidan..? Bata kishin Mijinta..? wlh yan mata muna Kuskure Shiyasa Auren zamanin nan kwata kwata baya karko saboda Zuciyarmu ba alheri muke Shiga gidan Aure,shi kuma Allah sai ya barmu da Dubaranmu,daga karshe inta ciki ta tsarkake Zuciyarta Daga karshe ke baki Nasarar Fita da ba, ke ki kori kanki da kanki,wlh mata mu Farka mu chanja munanan Hallayyarmu na zafin kishi wanda bazai kaimu ko”ina ba sai ga Halaka,mune fa da munji wata kawarmu zata auri mai mata ko za”a kara mata Kishiya jikinmu na raawa mu wanke kafa muje mu sameta,in munga ta kwantar da Hankalita Zunciyarta mai kyau ne,sai mu hau cewa koke kina Zaune haka kishiyafa za”a miki ko kuma ke ko yanzu wance me ya’aike ki Shiga Gidan Kishiya kuma kike Zaune baki mike Tsaye ba..? Kuji fa wani zence ..? Toh Ta mike tsaye da me? Wlh da kin yarda da Shawaranta kingama wayo don Maza yanzu Sunfara tsada kuma na garin yanzu Sunyi karanci iskanci kadan zakiyi ya taraki gida wlh da anyi mgana yace Ga mata nan Sunyi Arha kamar ledan pure water,zai maida gomanki wlh,Toh ki natsu keda kika samu Shiga ki sadda kai Ki kuma tsarkake Zuciyarki da Tsoron Allah,ladabi ,da biyayyah ga mijinki kada ki daina,ko aure yace zai kara kada ki zama ballagaza yi kishin musulunci Kina nuna kinfi Shi so ma ya Raya Sunar ma’aiki sai kiga ya Saki jiki,in kina da Rabo ma sai ki tashi da makullin motan Uwargida ta bada Halin kai😂ke kuma ta Waje ko Kinshgo wlh bazai bari ki Raina matarshi Saboda Abunda tayi Darajanta ya karu ko kin Shigo da mugun Nufi sai kiga daga karshe yakoma kanki,Toh Shawarata gareku Shine keda kike Ciki kada kiyi Wasa Damke Abunki don duk yadda kika kai ga Raina mijinki in Wata zata sameshi Sarki zata maidashi saboda gata da so😂 So Tun Wuri ku sauya taku,Domin nima ina kafa kafa danawa kada wata tazo Wuf tamin pdp ta Ture gwannatina na Shiga uku😂,ammh bayan fa na Tsarkake Zuciyata,ALLAH YAYI MANA JAGORA YA KUMA TSARKAKEMANA ZUKATANMU AMEEN SUMMA AMEEN_
Haka Zahra ta Wuni kukanta bamai lallashinta don ko Nadira ta dawo dakin Ta ganta tana kuka,ammh sai ta bata tanka ba kuma harga Allah ta gayamata hakane ta kara ankarar da ita kuskurenta bawai don gori ko Cin Zarafi ba.
**************
Karamar mgana Fa ta zama babba Domin Mganar Auren Nadira da Dr Hambali ta Tabbata domin har iyaye sun Shiga ciki Dr Hambali ya Turo magabatansa wajen Abba sun Nemi Auren Nadira kuma yabasu kama daga yadda yayi binciken Shi Dr Hambalin Mutumin kirki ne,An sanya Rana Wata biyar masu Zuwa murna wajen Nadira ba’a mgana Zumudi take Abunda tare da kara Fito da Salo Salo na Soyayya ga Angon nata Dr Hambali.
An saka ranar da Sati daya sai ga Jerin matan na Dr Hambali da ya”yansu sunzo gaida momi su kuma ga amaryar tasu Nadira,ku kanku Abun sai ya burgeku yadda suka zo suna wasa da Dariya momi haka suke cemata momi sama momi kasa,Dama Nadira tunkan suzo ta yi musu kayatattacen Tarba,bayan ta tsala wankanta,haka ya”yansu suka zagayeta suna Kiran Anty Nadira kaza,Anty Nadira kaza,haka suma iyayen nasu Duk dukkansu sun Girmema Nadira Nesa ba kusa ba,ammh suna Darajata,musamman ma yaddaa Nadira take basu girmansu Daidai gwargwado Tunkan ta Shigo kuma hakan ya samo Asali ne da adalcin miji da suka samu kuma Dukkansu Zuciyarsu mai kyau ce…
Nan suka Wuninma Nadira sai yammah kana Dr Hambali yazo ya Daukesu harda momi da Zahra amasu rakiya, wacce Abun ya tabata,taji dama itama Tun Farko ta kwantar da Hankalinta ta tabbata Malika sai ta mata Abunda Matan Dr Hambali basu ma Nadira ba,momi Dubi biyar tabama yaran suka ki karba sai da iyayansu suka saka baki,itakuma Nadira tabama matan nashi kyautan Turaruka,suma dai dakyar suka amsa sai da Dr Hambali ya saka baki,haka suka rabu cikin farinciki kowani bangare Sun Tafi cike da Kewa da Farinciki,suna Tafiya momi na ganin Zahra da zata shiga daki tana Dauke Hawayenta itako Nadira Kichen ta Nufa domin ta Zubo abinci hayaniya yahana ta ci,Da kallon Tsausayi ta bita kafin ta kada kai Aranta tana Fadin Dama Allah ya kadarra baki da dogon Zama achan Zahra Allah ya baki wani mijin,yakuma sa wannan Abun daya Faru ya zama darasi agarki,agaremu,agareni ni mai Rubutun,da kuma agareku masu karatu Ameen ya Allah.
*************
*ZAMFARA*
Cikin Wannan Halin kara’in Soyewar Da Saleem da malika ke tsakar kwasa laulayin ciki yayi ma Malika salamu alaikum,wanda Ranar data Fahimci tana da shigar ciki Wuni tayi amai da zazzabi mai zafi,koda Saleem ya Dawo daga office yaga Halin datake ciki bai jira cewar datakeyi ya kyaleta basai sunje asibiti ba,ya Tada ita Zaune ya saka mata hijabi,ya kama hannunta Zuwa mota.
Private hopital ya kaita nan da nan aka Dibi jinita aka gwada sai ga sakamakon ya Fito Malika na Dauke da 2 month preganant,Murna wajen Saleem ba’a mgana bakin nan har kunne,ko kafin su koma gida sai da ya biya yayi musu takeaway Tunda bata da lafiya bata yi girki ba.
Malika dai wannan karon Cikin yafi Wahalar da ita Fiye da Cikin Ayda Wacce keda Shekara daya kenan,tafara Tatatan Tafiya Tuni,har mikewa tanayi ita kadai,Kullum cikin laulayi take,ga amai komai taci baya zama,ga Zazzabi dashi take Wuni ta kwana,har asibiti ta kwanta har sau biyu Ammh Abunda sai Addu”a,Duk sai ta rame kamar ba Malika ba,yadda cikin ke Wahalar da ita yasa Ummi tasata Ta yaye Ayda ita kuma tatafi da ita Abuja saboda Wahalan na Malika ya ragu Tunda yanzu Ayda Tunda tayi yawo kuma sai Shigen Rigima ba.
Cikin yasa Malika tayi muni duk tayi baki,ga Wasu manyan Pimples da suka Fitomata bula bula afuska,gashi yasata kazanta don in ba Saleem bane ya matsamata ya Shiga da ita tiolet yamata wanka ba,sai Malika tayi kwana Uku batayi wanka ba😂gashi kuma ya saka mata wata irin Masifa Abu kadan sai tataso tana jijiyar Wuya gashi yanzu Duk yadda take Bashi kulawa abangaren Shimfida yanzu ko kusa da ita ya matso,yanzu zata bata rai,balle yace zai Shiga majalisar dinkin Duniya,yanzu zata hau kuka,,Saleem yanzu lallaba malika yake,Saboda ta zama alallaba Auren zamani,saboda yadda take Wahala harta da Abbi yazo Dubata Saleema tazo daga kano tamusu kwana biyu takoma Tunda sun kusa gamawa ana ma mganar Aurenta da Ya Sadiq ne,Su joda dai sai dai suka kira ta waya suka mata sannu,ko fa awayar ne Malika in Masifarta tatashi yi take,merry kam na Hakuri don da ita da Saleem sun Fi kowa ganin Masifar Hajiya malika,mai Cikin yan gayu,shi Acp dayayi mgana tafara Zumbura baki tana kunkuni Duk shi yajamata wahala,😂Toh ya zaiyi Tunda Shi ya kumsa Abunda ke saka bala’in ai ya lallabata arabu lafiya,ko abinci bata ci daga Shasshaka sai awara take iyaci,sai daga baya kuma tafara cin kwaden garin kwaki ,ai Dole Acp Saleem ya jingine buhun gari,😂Shasshaka kuwa maman Abba keyowa tana kawomata,domin ita ke kula da Malika jamgwanm,,in kuma batanan Tasaka merry ta mata wa
ta Rana ma sai an gama ta kawo mata Tature tace bataci😂Shiyasa ACP saleem fa ya ijiye kiyuwa ya zage yana Taimakon Malika don in ya Zauna harta Wajen kwanansu sai yazama bolan Juji saboda Rashin gyara,gashi ta hana Merry Shiga dakinnsu guda biyu,iyakar gyaran nata daga dakinta sai Falo,da kichen…..
………….Malika bata samu Saukin Laulayi ba sai da cikinta yayi kwari yakai kimanin Wata Hudu kafin Tafara dawowa daidai tana kuma kokarin Maida jikinta,Ammh lokacin yana Farkon Shiganshi Malika tayi Rama Sosai kamar Wacce take ciwon Tari,ammh yanzu Alhamdulillah Tafara Maida jikinta ba kamar Da ba.
**************
Yau ma takama Weekend ne,ACP SALEEM yana gida bai Fita ko”ina ba,Yana daki ya kwanta bayan yagama latse latsensa ajikin laptop dinsa,malika kuma Tun Safe ta Fita Zuwa kichen Don Jiya dakyar tayi barci sakamakon kwadayin Cin Garin kwaki daya matsa mata Shiyasa tatashi da Safe zata karya dashi.
Kwadashi tayi da Kolokuli da kuma Manja kafin ta zo Falo ta zauna kan Kujera taja Filon kujera ta Daura Bisa kafafunta bayan ta Dora Filet din kwadan garin Saman Filo,cikin Zumudi da Murna take Tura garin Daga ganin yadda takeci kasan Abun ya kaimata,don ganin yadda Fuskarta yake Sakin Annurin Farinciki,Rabin Hankalinta naga Talabijin tana kallon Gidan Badamasi atashar Arewa 24 da,Haka kurum take son Shirin Don yana Sata Nishadi.
Merry ce ta Fito bayan ta Duka ta Gaisheta,Amsawa tayi kafin tace ta Shiga kichen ta gyara mata Shi ta gogeshi tsab,don yanzu tana kokarin sakawa a tsaftace waje ammh fa ba da kanta zatayi ba,don Malika ko Acp ya Fita Attaka yanzu😂😂.
Yadade tsaye daga kofar dakinsu yana Kallonta,Hannuwanshi cikin aljihun Wandonsa,na barci baki mai wani Roba ta kasa,jikinsa kuma babu Riga gabadaya yalwar gashin kirjinsa wanda ya kwanta yayi luf duk ya bayyana,batason da tsayuwar mutum ba balle taji karisowarshi sai dai kawai taji ya Dauke Filet din garin yana kallonta gefe daya kuma yana yamutsa Fuska kamar yaga kashi .
Dagowa tayi tana kallonshi kafin ta kwabe Fuska tana Fadin”Kai Mallam don Allah Ka bani bafa kyau mutum na cin abnci ana katseshi kafini sani,kune malamai magada Annabawa..”Tafada tana mai yar Dariya tana kuma gyara Zaman Shegiyar Shimin datake jikinta wanda Cibiyartama awaje,kwata kwata cikin nan ya chanzamai mata fa,Yanzu malika bata iya Wuni da kayan kirki Sai tace Zafi takeji,daga ita sai Karamar Riga da Wando.
Da kallo ya Bita kafin ya kara bin garin da kallo yana Fadin”Wai ke baki gajiya da Dura ma cikinki wannan Abun .? Baki tsoron ki haifomin bby,da Tabon garin kwaki..”Yafada yana Tamke Fuska Dariya ya bata Har Sai da ta Dara Tana Fadin”Au dama ana Haifan yara da tabon Abunda Uwa taci lokacin suna ciki ne..? Lalle ko da har dakai ka Fito da Tsiron Danwake don Ummi ta gayamin da cikinka Shine abincinta Shida Wainar Fulawa..”Ta karishe Fada tana Dariya.
Zaro ido yayi yana Fadin”Wai da gaske…?,Dariya Malika ta Kece dashi harda Dukawa,ganin haka yasa ya Bata dankwashi akai yana Fadin”Kazamar mai ciki kawai,wato nine yau na zama cartoon dinki ko..?”Tana Sosa kanta ta kwaremai baki tana Fadin”Wayyo tsakiyar kaina ya Burma wayyo Ummi da Abbi Mallam ya Burmamin tsakiyar kai..”Ta Fada harda matse ido,kamar gaske,dariya Abun ya Bashi har sai da Duka hakoransa suka bayyana Waje…
Kusa da ita ya Zauna yana Fadin”Yarinyarnan yar Sharri ce,dan wannan yafa danayi miki ne zaki sakamin kuka kice kanki ya burma,salon kijamin Sharri,in mazaki kukan Jini ne yarinya bamai Cetonki yau..”Jin haka yasa ta bata Fuska ta mika hannu tana Fadin”Ni dai bani Abuna..”Tafada tana kokarin amsa,shi kuma ya maida shi bayanshi yana Fadin”Anki abaki,in kina da karfi ki kwace…”Jin haka yasa ta mike zata tsallaka dayan gefe,shi kuma yayi Saurin mikewa ya daga Filet din sama yana Fadin”In mutum ya isa ya kwata din..”Tsalle ta Fara tana Fadin”Don Allah ka bani,wayyo…!”Dariya ta kamashi ya danne yana Daga mata gira yake Fadin”Au bazaki iya karba ba.? Amshi mana..”Yafada yana sauke hannunshi tayi Caraf zata kama ya dage sama yana Dariya,ganin haka yasa ta Fara Diddira kafa tana kukan Shagwaba,Tanayi yana kallonta yana jin Nishadi sosai yadda take Diran Kafafun ne,Ko’ina na jikinta na motsi yasa wata Sha’awarta takamashi Lumshe ido yayi yana Fadin”Tsaya tsaya..Gashi..”Ya fada yana mikamata Da Sauri ta dakata tana Washe Baki ta mikamai hannu,miko mata yayi ta saka Hannu kenan zaka karba ya Maida bayanshi yana fadin”Da Sharadi ammh..”Jin haka yasa ta Mele baki tana Fadin”Kayi ka Fada,don daga yanzu nadaina Biye maka,sai wahalar dani kake da wayau..”…
Yana Dariya ya kai bakinshi Saitin Kunnanta yana Fadin”Don Allah nayi….”Da Sauri ta dago ta kalleshi kafin tace’Kayi me…? Ido ya lumshe kafin ya Shafa saman Nonuwanta har Zuwa saman karamin matashin Cikinta kafin ya gangaro Zuwa kasar maranta yana Shafawa ahankali,kafin yace”Wannan…”yafada yana Kokarin Turamata hannu cikin wandon jiknta,duk da ya kashe mata jiki,Tureshi tayi tana Fadin”lalle naki wayon,na kwada wani yanzu..”Tafada Tana Nufar hanyar kichen din,Ganin Haka yasa ya Ijiye Filet din a bisa kujera ya isa gareta da Sauri sai dai taji ya Dagata sama cak yana Fadin”Ni da Hakkina adnga min yanga,lallema yarinya..”Yafada yana Dariya,itama Dariyan take tana bugunshi akirji tana ihun ya sauketa,shiko bai Direta ko”ina sai kan gadonsu,tana kokarin Tashi ya bita ya Danne,bayan ya sakarmata Nauyinshi,Baknta take kokarin Budewa sai yayi Caraf ya Hade bakinsu waje Daya.
***************
*BAYAN SATI DAYA*
Aikin ginin Masallacin da makarantan Da malika ta gina Tuni ya kammallah har sun kirata sun Sanar da ita,itakuma sai ta Sanar da Saleem,shine ya bata Shawaran Asanar da jama”a Saboda su samu hallartan Taron Bude Wajen,da kuma Addu”a Ga Daddy,Malika ta yarda da Shawaran Saleem nan aka Fara Sanar da gaddamar da makranta da kuma Masallacin da Malika malik ta gina y’a marigayi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa domin Sadakatul Jariya Zuwa gareshi wanda zai Gudana agarin Malumfashi RANAR ASABAR Da misalin Karfe 9 na Safe.
Kafin kace kwabo wannan Budaddiyar Sanarwan Hade da Gayyatan ta iske kowa yaji sai ya sakama Malika albarka domin akwai ya”yan masu dashi da yawa wadanda iyayensu ke Mutuwa su bar musu Tarin Dukiya,ammh bazasu taba Tunanin Yi musu Sadakatul jariya ba sai dai Suyi ta Facaka da kudi suna Abunda suga dama,ammh sai Gashi Malikan da ba”a taba Zato ba tama kowa mamaki,kuma wannan ba komai bane,Sila illah Saleem wanda Shine keda kaso 90% wajen Daidaita Rayuwar Malika hartazama Abun yabo da koyi awannan zamanin.
Ranar taron Tun wajen Karfe 8 Suka isa Malumfashi ita da ACP SALEEM dinta,cngam dinta kenan,suna Sanye ne da Shadda mai Ruwan kasa,wacce akallah zatabama Dubu 50 baya Saboda Yadda take Fitar da maiko da yarari,Shi Saleem yayi dinkin Tarzace ne Dinkin Muhammed na Samarin zamani masu ji da kyau da Mukami,Da hulansa Zannah bukar wacce take Kalan,Ruwan kasa ajikinta haka takalmin kafanshi ma Rufaffe ne Mai Kalan Ruwan kasa,hadadde na Fatan Damisa,hakama agogon Fatan Dake Hannunsa,shima Kalansa kenan wanda na kamfanin Rado ne…
Itama Malika Dinkin Jikinta Riga da zani ne,Stone work ne,Rigar harpjmp ce,domin ta sauko mata har Gwiwa,sai Babban mayafinta mai kalan Ruwan kasa,da Takalminta mai Dudu Shima mai kalan Ruwan kasa,hakama yar karamar Jakar dake Hannunta,agogon Hannunta kala daya ne,dana Saleem ammh Shi nashi is For men,ita kuma nata For women ne😂in ka gansu sai sun Burgeka kaji kana ta kallonsu baka sani ba,saboda yadda suka zama Abun Burgewa.
Taro yayi taro wanda ya Gudana a haraban sabuwar mkranta Wacce dama masallacin ke kusa da mkrantar,Abbi da Ummi sunzo,hakama Hajiya binta tazo,hakama manyan malamai hadda Dan majalisar Dake Wakiltar Malumfashin yazo,Yan jaridu harda gidan Talabijin duk sunzo daukan gani da ido Bayan Bude taro da Addu”a inda Wasu karin bayanai suka gudana,sai kabama Malika damar
mgana,wanda Tunkan aFara gabatar da Taron ta Fara Hawaye, Saleem ne yake Damke da hannunta alamun lallashi,ta Fita ta karbi Abun mgana ammh kuma ta kasa mgana,saboda Tunawa Da Daddyta datayi Abu daya ta iya Fada Bayan ta mika godiya Allah (SWA) sai ta koma mika sakon Jinjinarta Zuwa ga gwarzonta kuma bango gareta,wanda Shine Silan Faruwa komai,shi zata mikama sakon Godiyarta,kuma ta Wakiltashi amatsayin wanda Zai yi bayani Amadadinta,Awajen babu wanda baiji kwallah ba,lokacin da Malika ke Fadin ta Gina wannan mkrantan ne Fisabilla da kuma Sadakatul Jariya ga,Mahaifinta Allah yaji kansa Da Rahma,Kuka ne yaci karfinta,sai da Saleem yazo ya kamata ya Rumgumeta ya maidata wajen zamanta,,taron bai wani jima ba akayi Abunda ya kamata,Malika ta dauki Nauyin malaman mkratan da duk Abunda za”a bukata karatu takeso akoyar kyauta batare da an anshi Sisin kwabon wani ba,Anyi Addu’o’i Da fatan Allah yajikan Daddy,ita kanta Malikar tasha addu”a da Fatan gamawa Da Duniya lafiya kafin Taron ya Tashi bayan an gaddamar da Sunan masallacin *MARKAZUR UMAR BIN KHAD’DAB* Sai Shikuma Mkrantan *MADARASATUL UBAIYU BIN KA’AB*.
Basu kwana ba Aranar suka Jiyo zuwa zamfara,Ranar dai Malika Mutuwar Daddy ta dawo mata Sabuwa don da suka Dawo haka ta kwanta akan gado tana kuka mai Cinrai,Sai da Saleem yayi ta lallashi da jikinsa da hannunsa kana ta bar kuka ta koma tana Sakin ajiyar Zuciya,koda Dare yayi zazzabi ya Rufeta Ruf ta kwana tana Nishi sai da Saleem ya tasheta ya bata mgani,kuma yasa Ruwan sanyi bayan ya Rika jiko Towel yana matsa mata jiki dashi,shine taji sauki har kuma ta Samu barci.
___________________
Sannu bata Hana Zuwa sai dai Adade ba”a je ba,an kuma ce Duk Abunda aka Sanyama lokaci Toh zai zo,gashi har bikin Nadira da Dr Hambali yazo,sauran Sati daya inda Shirye Shirye ya Kamkama Aduka bangarorin,Nadira tayi gayyah sosai kawayensu na mkranta da kuma yan uwa da abokan Arzuka,Har Saleema sai dai ta kaima kati da Minti gayyata bayan kuma ta Tura mata ta waya,.
Saleema tayi mamakin ganin Nadira tazo har cikin Asibiti ta kawo mata kati gayyatanta Zuwa wajen Bikinta,nan nema Saleem ke Fadama Nadira itama asanya lokacin Bikinsu ita da Ya Sadiq,wanda nan da Wata uku ne lokacin take gama Housemanship dinta,Tayi Mata Fatan alheri tare da mata alqawarin indai tazo bikinta itama zata Sanar da Dr tasan bazai hanata ba,sun Rabu cikin Aminci inda Saleema ta mata alqawarin zata zo insha Allah.
Abun mamaki Nadira bata Sanar da Zahra ta gayyaci Saleema ba,shiko Saleem, Bukar Mada da kanshi ya Kirashi ta waya ya Sanar dashi,bayan kuma ya Turamai sakon gayyata ta waya,anyi haka da kwana biyu Sai ga kiran Nadira,bai da nombarta lokacin don ya Dade da Shareta da nata dana Zahra na Abba kadai ya bari,shima saboda yana kiranshi suna gaisawa ne, kada ya goge Watarana ya kirashi yace waye😂yace baida mutumci,yana dagawa bayan sun gaisa tace itace Nadira,yaji mamaki sosai nan take Sanar dashi mganar bikinta tare da cemai tana gayyatanshi Daurin aure,kuma tana son Don Allah ya Turamata Nombar Malika zata kirata,mirmishi kawai yayi mata yace kada ta damu in ya samu lokaci zai zo,mganar malika kuma ba sai ta kirata ba,Zai sanar ita ammh da Wuya ta samu Zuwa don bata jin dadi cikint jikinta yayi Nauyi..”Cike da Mamaki Nadira kema Malika Fatan Sauka lafiya kafin suyi sallama bayan tace agaisheta,shikuma yace ta gaida Momi,.
Ya dade Shuru bayan sungama waya,yana Tunanin wani abu,Abunda yasa bai bata Nombar Malika ba,saboda shi atunaninshi Zahra na wajen,kuma zata iya daukan Nombar Malikan ta kirata,saboda shima kwanaki tayi ta kiranshi baya dauka,daga karshe sai ta koma tana kiranshi Da Rufaffiyar Nomba,Sai da ya kulleta kana ta daina Damunshi..
Sai da yakoma gida yake sanar da Malika sakon Nadira,tayi ta mamaki harta Fadin in Saleem zai barta data jema Momi da Nadira biki suna da kirki sosai,wani kallon lalle ne ma Saleem yayima Malika dole taja bakinta tayi gum,itama din ma jnta baki ne,ammh tasan yadda Cikin jikinta yayi kato kuma Wata 6 kenan ammh kamar wanda zai Fito yau ko gobe,duk ta kumbura musamman kafafunta,Barin ma tayi dogon Zama kafin tatashi duk sai su haye,Sai Saleem ya dawo daga aikin kafin su kwanta yayi mata massges dinsu.
****************
Saleema ta cika alqawari tazo bikin Nadira,wanda Sai dai Zahra ta ganta kwatsam suka kama aikama juna kallon mamaki,Zahra ita tafarama Saleema mgana inda ta bata hannu suka gaisa tana tambayanta su Ummi,itako Saleema Karema Zahra kallo take yadda Rayuwa ta Horata Duk ta yi sanyi kamar ba ita ba,Ace yau Ana bikin Nadira ammh Zahra na Zaune waje daya cikin Natsuwa ba iyayi ba hayaniya ba Rawan kai,lalle Ruwa ya Daki babban Zakara kuma Gani ga wane ya ishi wane Tsoron Allah.
Saleem bai samu Zuwa Daurin Aure ba,ammh Abbi yazo Har suka Hadu ta Saleema ta biyoshi suka koma Katsina tare,dama tana son Zuwa weeked,amota take ta bama Abbi lbrin yadda taga Canzawar Zahra,Abbi sai yayi amfani da wannan Damar ya dingama Saleema Nasiha wanda suka kashemata jiki sosai takuma yi alqawarin yin amfani dashi…
Anyi taro lafiya an kai Amarya Lafiya,ta tare agidan Mijinta dake kusa da Asibitin murtala,,Tsakaninsu da Gidan ya Nadir Babu Nisa,Flat hudu ne Uku na matanshi daya kuma nashi ne,to cikin dayan ne aka Saka Nadira komai dai achan achan sai wanda ya gani,Sai inda ma kayi Ra”ayi ne zaka So ganin wata kishiya,ammh sai ka Wuni a Shashenka bakaga Gilmawar kowa ba,kowa na barayinshi sai ko in An hadu agaisa,kowacce cikinsu ta iya kama girmanta da kuma Salon kishinta yayinda itama Nadira ta iya jan kankanta da kuma Salon Jawo Hankalin Mijinta gareta,ammh batare data Cutar da abokan zamanta ba ³⁵