MALIKA MALIK CHAPTER 19 BY JANAFTY

MALIKA MALIK CHAPTER 19 BY JANAFTY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

……………”Su Maman Abba da Saleema su kadai aka bari suka cigaba da soye soye basu Tafi ba sai da komai ya kammallah,Suka taimaka aka gyara gidan kana,maman Abba ta Wuce zamfara ita kuma Saleema tatafi Abuja ta kwana Washegari zata bi jirgi Zuwa Abia.

Ita kuma Hajiya, Ummi ta roketa Kan ta Zauna ta dan kara ko Sati daya ne kafin goggo Hadiza tazo wacce tatafi minna An mata rasuwa,sai ta dawo kana zata zo ta zauna Da Malika uwar mazaje.

Hajiya ta Zauna da Malika har Na tsawon Sati biyu tana kara kula da ita da Kuma su Ayyan Duk da gasu Merry suna kokarin Taimakamata,sai Ranar ta cika kwana ashirin da Hudu kana goggo Hadiza tazo,sai Hajiya Ta koma gida ta barta tana Kula da Malika wacce ta warke kamar ba ita ba.

******************

Tun Malika na kwana 36 Da haihuwa jini ya Dauke mata tayi wanka Tafara Sallah Ammh Bata bari Uban gayyah ya sani ba,domin taga take takenshi so yake ya barta da Abun kunya agaban Goggo Hadiza,Don Tun Satin daya wuce yake damunta da ya kosa ta Fara sallah wlh a daddafe yake yayi kokari ta taimakeshi,Bata nuna mai komai ba,Sai Ta nuna mai Data Fara zata mai mgana,sai dai wani lokacin ta Saci jiki taje dakinsa ta Dan mai Dubaran,su na mata ammh Duk da haka bai wani gamsuwa shi burinshi yajishi Cikin babban Fada😂.

  Ga wannan karon su Ayyan da Bala”in kuka suke da Tsotse,bata da lokacin kanta,data samu sararin zuwa dakinsa ko Dadewa baza tayi zata ji kukansu da kuma kiran goggo Hadiza,Da kuma ta Fahimci Dakinsa  Taje Sai goggo Hadiza ta kama mata Fadan zatayi kazantattacen jego matukar ta biye ma Namiji kaita zai yi ya Rabo wlh,wato yaga jiki yayi Taushi ,shine ita zata biyemai Shiyasa wani lokacin ko ya kirata bata Zuwa,sai tace mai su Aryan na Rigima.

    Yau da Wuri ya dawo yana Shigowa Direct dakin Malikan ya Shiga,yana Shiga ya ganta tana sallar mangariba,,galala ya tsaya yana kallonta,yana mamakinta domin Jiyan nan ya Tambayeta yaushe zata Fara Sallah ,tace bata sani ba,akofar dakin ya coge yana binta da kallo itako ta jikin madubi ta hangeshi sai da gabanta ya Fadi,Sai ta Daburce ta idar da sallar ammh sai ta sake kabartawa Yana kallonta bai mata mgana ba, illah takowa dayayi ya zauna agefen gado batare da yayi mata mgana ba.

Tun tana mai karyar Sallah harta hakura ta Sallame tana Raba ido,bata yarda sun Hada ido ba,tayi zaune tayi Zuru gabanta na bugawa,Ta gefen gado ya kalleta kafin ya saki Siririn mirmishi kafin yace”Kin idar da sallar..? Na zata sai gobe zaki idar..?

Shuru Malika tayi tana wasa da Gefen Hijabinta,ganin batayi mgana bane yasa ya mike yana Fadin”Ina ayda ko tana wajen goggo ita Da su Aryan..? Da kai Malika ta bashi amsa,Dariya ta kamashi yayi yana Fadin”Kin zama kurma ne..? Ko Azumin mgana kikeyi..? Bata dago ba balle ta bashi amsa,kofar ya isa ya sama key kafin yazo ya Tube karamin Towel ya daura iya kugunsa ya Fada Wanka tana binshi da kallon mamaki,tana zaune awajen har ya Fito yana kallonta Shima ita yake kallo kai Tsaye yace mata”Kinsan Hukuncin macen data kema mijinta karya..? Ya fada yana goge Sumar kanshi da wani karamin Towel,Kanta na kasa tace”Karya kuma…? Dan mirmishi yayi kafin yace”Eh kin min karya kince baki Fara sallah ba,saboda kada Nameni hakkina ki bani ko Malika..? ya Fada cikin wani yanayi,Mikewa tayi jikinta yayi sanyi kafin tace”Wlh ba…”Shiii…Is ok,ai bazan Nema ba Tunda na Fahimci Guduna kike,bakomai Zan zauna ahaka ammh ki sani in na kasa control din kaina har na Fada wani Hali kome ya Faru kece Sila..”Yafada cikin son Tabbatarwa,kafin ya isa gaban Merro ya jawo lotion ya Fara shafawa.

Jikin Malika yayi Sanyi da azama tataka zuwa gareshi kawai sai ji yayi ta Fadaomai jiki ta kamkameshi ta haya,Hannu yasa yana so ya bambareta daga Rumgumar da tayi mai,ammh ta ki sakinshi suka Fara kokawa,ranshi bace yake Fadin”plz Ki sakeni kafin Raina ya baci,badai jikinki ki keman Rowa ba,ki jika kisha,ni bazan yi zina ba,ammh kisani zan karo wacce ko acikin wani hali na nemeta zata bani kanta..”

Jin haka yasa ta fashe da kuka tana kara Rikeshi Kamkameshi tayi ta Zuro da hannunta ta cikinshi tana mai Shesshekan kuka cike da Shagwaba,Shuru yayi mata yana bin Fuskokinsu ta jikin madubi da kallo,Kara Hade rai yayi yana Fadin”Wai ina wasa dake ne Malika,i said leave my body ko..?Narkemai takarayi kafin tace”Wlh bazan tashi ba,ni da jikina,kuma Shikenan daga kuskure kadan sai ka yankemin Hukunci baka iya tsayawa kaji Uzurina..”karamin Tsaki yaja kafin ya waigo da karfi ya kuma sa hannu ya Ture malika baya sai ta Fada gefen gado yaraf,Arazane ta dago kanta tana kallonshi kafin ta samu Zarafin mgana yace”Bana son Jin komai daga bakin plz leave me olone,indai kan ki bani hakki na ne,Malika kiyi ta Rike kayanki bazan kara ce miki komai  ba Do wht ever u want i dont care..”Yafada kafin ya isa jikin Wardrope ya dauko Wasu Riga da wando na kamfanin Armani,ya saka yayi cumbing din kansa ya Fice bai kara kallon Inda Malika take ba,ta kallon ta bishi kafin ta kwanta bisa gadon Tana Fashewa da kukan takaichi da cin rai,Shiko Ficewa Yayi daga gidan gabadaya,har wajen 10 da Malika taje dakin Goggo Hadiza ta basu Aryan Nono Saleem bai Shigo sai hankalinta ya tashi Zuciyarta ta Fara mata wasu Tunanen ko dai wajen Wata yar iskan karuwan yaje..? Tuni Taji Hankalinta ya tashi,ammh sai tayi saurin Kauda wannan Tunanin Saboda tasan Halin mijinta baya shaye Shaye baya Neman mata,ammh ganin har pass 12 Saleem bai Shigo gida ba,yasa kuma hankalinta yakara tashi tayi Safa da marwan Tsakanin upstair da kuma kasa,haka tazauna afalo tayi Zuru ta Tsurama kofar falo ido,lokacin da 12:30 tabuga ne Goggo Hadiza ta sauko daga sama tana bin Malika da kallon mamaki,itako hankalinta yayi gaba bata ma san goggon ta sauko sai da taji tana Fadin”Malika…”Cike da mamaki…

Afirgice Malika ta Waigo ganin Goggo Hadiza yasa ta sauke ajiyar Zuciya tana Sosa kanta tace”Bakomai Goggo Zan kalli wani Shiri ne a Mbc yanzu…”Kallon mamaki goggo Hadiza ta Bita dashi tana karantarta kafin tace”Kuma shine kallon atsakar dare malika ..?Kina da danyen jiki,maza ki Wuce daki ki kwanta,dama na Shiga dakinki na kai miki su Aryan ne,sun yi barci kada Su tashi cikin dare suna kuka kinsansu da tsotso..”Kai ta sunkuyar Kafin ta Wuce tana Fadin”Toh Goggo sai da Safe..”Tafada jikinta asanyaye kafin ta haura sama da kallon Tsausayi goggo Hadiza ta bita kafin ta jinjina kai tabi bayanta,ammh tasan Dalilin wannan damuwar ta Malika,ita batajin Shigowar megidan ba Allah yasa lafiya.

Koda ta koma daki kasa barci tayi wayarta ta Dauka ta latso mai kiran Daidai lokacin dayake zuba hon akofar makeken gidan, nashi megadi yataso ya budemai yana mai Barka da Zuwa shima cike da mamakin yau yallabai yayi dare,duk mai irin aiki irin nashi kowani lokaci zasu iya Fita.

Sai da ya Daidaita motar a parking space kana ya daga kiran Malika wanda na Uku kenan ya Shigo wayarsa,Tana jin ya daga ta Fashemai da kuka Dan ware ido yayi yana Fitowa daga motar yake Fadin”Meya Ab
un kuka kuma..? Hmm mata sai abarku ku bata mutum rai kuma ku Fishi nuna ku aka cuta ko..?”Tana Share hanci tace”Don Allah Mallam ka ya Femin,ka dawo gida hakanan Hankalina yaki kwanciya Zuciyata tana Ta Tunanin kila ko kana tare da Wata ne..”Mirmishin gefen baki ya saki kafin yace”Na shigo gida yanzu..”Daga haka kawai ya yanke kiran,jin yace ya Shigo gida yasa ta Fito daga daki da sauri tana kallonshi ya Shigo yana Takunsa cikin isa,har ya hauro saman yana kallonta bai mata mgana ya Bude dakinsa ya Shiga ya maida kofa ya Rufe Ajiyar Zuciya Malika ta sauke kafin ta koma daki tana Share kwallar Daya Tarun mata.

*******************

Har washegari Saleem bai saki ba,,sboda yana Fushi da ita ko karyawa baiyi ba,da goggo Hadiza ta matsamai ya tsaya ya karya sai yace zai karya a office in yaje,kuma Malika na zaune adakin goggon Hadizan daya  shigo gaisheta da Safe,Ayda kadai ya daga Data rugo tana gaisheshi ko su Aryan dake hannunta bai karba ba Daga hannunta ya lakace musu hanci yana musu wasa koda Malikar ta gaisheshi dakyar ya amsa kamar yana Ciwon baki ganin haka yasa Malika taja bakinta ta Tsuke ya har Fice,goggo Hadiza ba macece bace mai Shiga Sha”anin yara,kuma Abu na ma’aurata Shiyasa tayi musu bakam kamar bata Fahimci basu jituwa ba.

Tafi tafi  Fushin Saleem yama Malika tsauri wajen Sati daya Abu yaki Wucewa awajensa,gashi yanzu baya zaman gida kwata kwata,baya Shigowa sai around 10 kuma yana Shigowa zai Shige dakinsa ya Kulle,malika tanemi hanyar Sulhu ammh yaki bata dama,shiyasa itama ta Kama kanta,iyakarta dashi gaisuwa sai ko in ya Shigo dubasu Aryan,wani lokacin ma Dakin goggo Hadiza yake tarar dasu,ganin yadda yaki Fahimtarta shiyasa Itama Ranta ya baci da wannan Fushin mara Dalilin da Saleem ya Dauka da ita gabadayansu suka Share juna kowa na ganin Shi ba’a mai Daidai ba.

  ******************

Ranar da Malika tayi Arba”in Ranar Ya marwan ya kawo joda gida domin cikinta ya Shiga wata na tara,kuma bashi da wani Hutu,shiyasa ya dawo da ita gida ta Haihu tunda chan kudu ne,koda hajiya ta kira Malika ta sanar da ita cewa kawai tayi zata kira jodan don yanzu bazata ce zata zo ba,kada ta kara wani laifin,Kuma shi Saleem din Ya dauko su daga Airport, Daganan Motar haya Ya marwan ya Shiga ya tafi Abuja achan ya kwana sai Washegari ya hau jirgi ya koma birin ikko don Ba”a bashi Hutu ba wannan ma Excuse ya dauka da zai kawo Joda gida.

Har Joda tayi Sati da Zuwa ammh kuma Malika bata jeba,Bai cemata ci kanki ba,itama bata tayaba ta rabu dashi,Aranar kuma Yasa ka Direba ya maida goggo Hadiza gida,domin ta matsa zata tafi,saleem ya hadamata Sha tara na arziki hakama Malika tayi ta godiya tana saka musu albarka,Malika ko sai tayi kwallar harta Fadin in goggo Hadiza tatafi zata kara zama marainiya bata da mai kula da ita,itako goggon Hadiza tace Kina dashi mana Malika ga mijinki nan,Cewar datayi haka sai da Malika ta kalli saleem Shiko ya Hade rai kamar bai taba Dariya ba,sai da suka raka goggo Hadiza bakin mota dama Direban gidan Hajiya ne zai kaita,har suka Fice Daga gidan suna daga musu hannu,Shi Saleem yana dauke da Ayda ne,ita kuma Malika Ayyan ne ke Hannunta Aryan ya gama Rigima ya kwanta,Gaba yayi ya barta ita kuma tana Shigowa ta haura sama,Bai Shigo ba sai da Ayda ta tafi wajen su Merry shikuma ya hauro sama dakin Malika ya tarar da ita tana bama Ayyan Nono,Tunda taga ya Shigo Fuskarshi ba Fara”a tace topha,aiko illai gabanta ya tsaya yana Fadin”Miye Dalinlinki na cema goggo Hadiza in tatafi Zaki kara zama marainiya,wannan wata irin mgana ce,sai kisa tayi tunanin ko ina cutar dake ne fa..”Yafada yana mata wani kallo,kanta ta dago tana kallonshi idanuwanta sun ciko da kwallah,,ido cikin ido suke kallon Juna kafin ita tafara Janye idonta Hawaye Datake kokarin Rikewa suka zubomata tasa hannu ta Share Abunda ta iya cewa kawai Shine”Kayi Hakuri..”

Yadda tayi ne jikinsa sai yayi Sanyi,duk Fushinsa sai ya sauka sausauta murya yayi yana Fadin”Kidaina irin haka ba dadi sai ta dauka wani abu ne..”Kanta na kasa ta dago tana kallonshi tace”Ba karya nayi ba,yanzu kadaina kula dani,Haba mallam takan laifin da nayi bisa kuskure kadan sai ka dauki Fushi dani mai tsawo haka,Sai yanzu nakeji ni Marainiya ce ada,ina ganin ka lullubemin maraicina amhhh..”TaKasa karisawa tayi Kuka taci karfinta da hanzari ya isa gareta ya zauna kusa da ita Ayyan ya karba ya Fita dashi sai gashi ya dawo Shikadai,Hannu ya mikata mata ta karba ya mikar da ita tsaye Habarta ya tallafa yana kallon kwanya idanuwanta kafin yace”waya gaya miki ke Marainiyace,Haba Amanata indai ina raye har abada baki ba kukan maraici..”Yafada Cike da kulawa,Runtse ido tayi hawaye suka kwaranyo mata kafin tace”Ka chanza mallam,ka barni inata wahala da Fushinka..”Harshensa ya sa yana lashe hawayenta,sai da ya lashe kaf,kafin ya Rumgumeta kam yana sakin ajiyar zuciya yake Fadin”Am srry Nayi kuskure insha Allahu baran kara ba..”Yafada yana kamkameta,ajiyar zuciya ta sauke tana zagaye kugunshi da hannuwanta,cikin muryan Sanyi tace”Nayi kewarka Abbu Ayda..”Ta fada tana sakarmai kiss Awuya kamkameta yayi yana Shinshinar Wuyanta kafin lokaci kadan sungama Rikita juna da salon wasanninsu,Cikin Fitan hayyaci suka raba junansu da kayan jikinsu,Kafin su Dangana da kan makeken gadonsu suna Tsotsan juna cike da kwarewa da muradi mai girma.

Ranar dai ma”auratan komai ya Daidaita tsakaninsu Haka suka kwana manne da juna,don ma Rigimar su Ayyan ta hanasu sakat,ammh duk da haka Sun mori juna ba laifi Saleem ya Famshe kwanakinsa,dama gashi goggo Hadiza ta gyare yarta Sosai Acp ya yaba kuma yayi ta sambatu😂

***********.

Washegari kuma suka tashi da Lbrin Haihuwar Joda wacce ta haihu lafiya kalau agida,sai da safe Hajiya ta kaita Federal medical Center Katsina,aka duba ita Bby lafiyanta Kalau,Ta haifi da Namiji masha Allah,Dama Malika Ranar take Shirin zuwa sai aka tafi da murna gabadaya,Saleem ya ijiyeta agidan bayan ya Shiga yayi barka Shima ya Wuce office yabar Malika nan sai dare yazo ya dauketa,suna hanyar komawa gida yake sanar da malika zata fara hawa daya daga cikin motocinta da kanta,ammh sai dai su bari Weeked ya dinga koyamata mota,Malika tayi ta murna harda kwallar Farinciki,Abun yayi ma Saleem dadi ganin Walwalar Malikarsa zata dawo,domin shi yanzu babban Farincikinsa yaga Malika na cikin Farinciki akoda yaushe..

………….””Har Zuwa Ranar Suna Kullum Malika sai taje gida,in Saleem zai Fita office Tare suke Fita ya sauketa shikuma ya Wuce,Daga Hajiyar har joda sunji dadin Haka sosai,Yan Malumfashi sunzo mota biyu,mota daya daga barayin Dangin Baban Joda,daya kuma Daga Family dinsu Hajiya,wato Baffanin Malika kenan,hakama yan kumo sunzo duba bby,Sun kuma zo da Abun arzikisu sukayi barka suka koma.

Ummi ma tazo,Da kayan suna Niki niki da nata dana Abbi dana ya marwan Wanda dama joda tazo da duka kayan Suna na bukatan da suka siya na haihuwa,sai kuma ya Turama Ummi kudi ta kara mata,Abun fa masha Allah sai wanda ya gani Ya marwan yazo kwana daya yayi ya koma inda yayi ma yaro Huduba da *SALEEM* wato yama Acp takwara kenan jin wannan Suna yasa daga Saleem din har Malika sukayi bajinta ban girma Malika makullin mota sur tabama Joda Shiko Saleem Kudi ya bata 100k ita kuma Malika ta dora mata Nata darin akai making 200k,Joda Saboda murna sai da ta Rumgume Malika kamar ta mata kwallar saboda godiya,Hakama Hajiya tayi ta godiya,itako Malika tace don Allah su bari,miye amfanin uban Dukiyan datake dashi in har batayi ma nata ba.

Saleema ma tazo Ranar suna ta kwana ita da malika sai washegari ta koma Abuja ta kwana kafin ta Wuce,Taro ya tashi lafiya sai Fatan Allah yara young Acp,wanda suke kira da Junior.

Hajiya ce ke Kula da Maijego da danta cikin kwanciyar Hankali,Hakama Malika itama tana cigaba da kula da kanta da kuma Mijinta da kuma ya”yanta,hakama Shima Saleem yana iya Bakin kokarinshi na ganin ya Sauke dukkan Hakkin Malika da na ya”yanshi daya Rataya awuyanshi,game da Harkan kasuwancinta Shi Malika ta dora Amatsayin manajojin kamfafon
inta,duk wani kudi da zai Shiga ko Ya fita,ko in wani Abu ya taso,sai dai in Abu ya gagareshi sai ya Fadama Malika ita kuma amtsayinta na wacce tasan kasuwanci sosai sai ta Fitar da mafita cikin Lokaci,Shiyasa Kasuwancinta da Kudinta suke kara hauhauwa.

Mganar koyamata Mota kuwa ya cika alqawari Duk Ranar Asabar da lahadi suke Fita da la”asar yana koyamata mota dayake Malika akwai kwalkwalwa basuyi wata ba ta koyi mota sosai,har tana tuka kanta taje gidan Hajiya ko asibiti,ammh bata taba Tafiya mai Nisa ba,sai dai ko cikin gari in zata Fita.

Joda kuma ta cigaba da jegonta cikin kwanciyar Hankali ayayinda Da hajiya ke kula da ita,bata koma ba sai tayi wajen wata biyu,taje Abuja ta kwana biyu taje malumfashi ta kwana biyu Shima,har wajen Malika tazo ta kwana,Washegari mijinta yazo ya dauketa suka je Abuja suka kara kwana daya suka daga zuwa birinin na ikko da su da Little Acp dinsu wanda yayi kiba sosai yasamu Nonon uwa mai kyau da kuma kulawa in ka ganshi gwanin ban” sha’awa.

Saleem ya saka Ayda awata private,sch Bby clss,saboda bakinta ya bude sosai ga Shigen wayau shiyasa Saleem ya sata amkaranta bakinta yakara bude achan,Malika ke kaita watarana taje ta ta Dauko Watarana kuma Saleem ya kaita kafin ya Wuce office in ko ya makara sai ya barta Malika ta kaita,Abun nasu cikin kwanciyar Hankali gefe daya kuma tana cigaba da Renon yan biyun ta suma da suka habake sukayi kiba sosai sai da wannan karon goyon Rigimammu take,don su Aryan akwai Rigima da daya ya Fara kuka,toh Daya zai dauka,Haka take Fama,don ma su merry suna kokarin Taimakamata da Renonsu wani lokacin.

*******************

Zahra ta yi sanyi Fiye da yadda kuke Tunani ta chanza daga zahra ada ta koma Fatimatulzahra’u Wacce take da Tarin natsuwa da hankali yanzu ba wannam rawan kan,da kuma shigen iyayi bashi,Game da zafin kishinta kuwa ta Fahimci Halittanta ne,sai ta koma tana Rokon Allah ya rage mata wannan Zafin kishin,kuma Alhamdullah,Yamzu Abun ya fara ragewa ba kamar da ba.

  Auren Nadira shiya kara maidata wani so silent,ada ta saba komai tare suke koda suka rabu da Saleem,kewar batamata yawa saboda Tana ganin Nadira ko banza zasu kwana tare su tashi tare,toh yanzu Nadira tayi Aure tana gidan Mijinta tana zaune lafiyanta,Ta kwantar da Hankalinta Da Zahra Taje gidan tayi mamakin ganin kibar da Nadira ta narka ya”yan Mijinta kuma shashenta suke Wuni Suna Anty kaza zanci ita kuma tana ta Ina kasa dasu,shiyasa ta Shiga ran iyayen kunsan me da wawa,Kwata kwata suna tafiyar da kishinsu Cikin tsafta Domin kunsan ba inda ba”a kishi sai dai akwai masu na ilimi dana Jahilci,Zahra bata fahimci Nadira nada ciki ba sai da ta sanar da ita da kanta tace mata tana ciki na tsawon wata Hudu,Abun ya daki zahra haka ta koma gida ta kulle kanta adaki tana kuka,Tana kara Nadamar Abunda ta aikata da”ace ta kwantar da Hankalinta da yanzu kila ta haihu Bama daya ba,ammh gashi har Nadira tayi aure jiya jiya har ta samu ciki,haka dai ta kwana kuka ta kuma yi alqawarin maida al”amarinta ga Allah ko zai kawo mata mafita.

Momi tana iya bakin kokarinta wajen ganin Zahra ta saki ranta ammh sai ahankali Shiyasa ta Shirya musu Tafiya lagos wajen Hajiya baraka mahaifiyar Su Nadira,Zahra taji dadi sosai Balle ma hajiya baraka macece mai Fara”a da barkwanci Shiyasa Zahra ke jin dadin zama da ita,sati daya Momi tayi ta baro Zahra chan ta dawo kuma ba laifi zahra ta saki ranta dayake ta sake aure bayan Rasuwar Mahaifinsu Nadira,har ta haihu,Zaman lagos yayima Zahra dadi sai tayi wata biyu kana ta Biyo ya Nadir suka dawo tare wanda Suka isketa achan Shida matarshi Sati daya sukayi da zasu dawo da taboyosu.

Bayan dawowarsu ne Ya Nadir yazo har gida ya samu momi ta complain Din zaman da Zahra take haka babu Abunda takeyi,gashi yaga Duk ta rame ta koma kamar Zahra bukar Mada,momi tayi bayanai ta yi iya bakin kokarinta ammh Zahra sai ahankali ganin haka yasa yasamu Abba ya mai mgana zai Nema ma Zahra aiki saboda zaman kadaichin yayi yawa,Bai yi mai musa ba,shiyasa ya karbi Takardunta bata da masaniyar komai sai da gidan Redion Freedom kano suka kirata interview Shi da kanshi yazo ya dauketa ya kaita tayi interview,cikin Nasara ko sati batayi da zuwa suka Turo mata sakon Sun Dauketa aiki ashashen labru,murna wajen Zahra ba”a mgana Haka ta Rumgume ya Nadir tana murna momi da Abba suna dariyan Farinciki Domin rabonsu da ganin murnan Zahra haka Har sun Manta Arana.

Ranar data Fara Zuwa aiki Ranar Ya Nadir ya bata key din sabuwar motar daya Siya mata 4matic,mai kyau,Zahra kamar bakinta zai Tsage saboda godiya,hakama su Abba da momi suna mai godiya ya bata rai yace Haba Zahra fa yar”uwanshi ce saboda haka zai iya komai domin ganin Rayuwarta ta dawo kamar da,Haka ko akayi acikin Sabuwar motarta tafara Zuwa aiki Ranar,Data tashi kuma ta biya gidan Nadira ta nuna mata Sabuwar motarta itama Nadira tayi murna haka suka Rinka Dane motan suna Santi,ita kanta Nadira murna ya kamata ganin Zahra Ta chanza kamar ba ita komai yanzu tana yinshi cikin aji ne,ganin Zahra ta Shirya zata tafi tace mata zata biya gidan Ya Nadir,aiko Nadira tace sai taje Dr ta kira awaya tace mai zata gidan Ya Nadir ita da Zahra yace adawo lafiya,saboda kwakwa Nadira ita tayi Driving dinsu zuwa gidan ya Nadir suka kuma yi sa”a suka iskeshi agida nan Nadira ta sakamai kukan wlh itama sai ya Siyamata mota,Yako yace bazai siya mata ba taje mijinta ya Siya mata nan ta bare baki tana kukan Shagwaba Zahra da matarshi wacce suke kira Madam suna mata Dariya sai yammah Zahra ta maidota gida suna tafe suna Hira Nadira na kara Yima Zahra Nasiha da kuma hakuri da Rayuwa Zahra ta mata alqawarin insha Allahu ta chanza ita yanzu ko me mata Uku ce itace ta Hudu yazo ciki zatayi dashi ta gaji da zaman gida,Don ma dan aikin nan da Ya Nadir ya samo mata shike Debemata kewa ammh Kadaichin yayi mata yawa Sosai,Dama haka Rayuwa take Duk wanda baiyi Sharar masallaci ba to ai zai yi na kasuwa kodon Dolensa don Ubanshi..”

******************

Dalilin wannan Abun yasa Shakuwa tare da Tsantsan Damuwa da juna ta Shiga tsakanin Nadir da Zahra,shi duk a kokarinsa na ganin ta dawo Normal zahran ta kuma Alhamdulillah yabada Gudumuwaa domin ko Zahra bata dawo duka ba,tafara dawowa sai dai yanzu wannan Zahra ta gama Daukan Darasin Rayuwa sosai kuma ta kara gogewa da wayewa ba kamar da da bata wayau sosai ba,yanzu Saboda Cudanya da jama”a yasa idonta ya bude Sosai ta kuma gane Rayuwa.

Wannan Shakuwarsu nasu ita iyayensu ke kallo da makusantansu suke zaton suna soyayye ne,kuma ba Haka bane,Kawai kulawa ne da kuma Shakuwa,hatta Matarshi ta Fara Shaka da Zahra shiko ko ajikinsa bai maida kai ba,hatta Nadira tana ta addu”an Allah sa Ya Nadir ya auri Zahra da tafi kowa murna Har Ummah su ta kita ta tsegumta mata itama Tayi murna Sosai bata kuma jira komai ta kira Abban Zahra ta sanar dashi wanda yaji mganar abazata Duk da dai Shima yana ganin Shakuwarsu ammh ko da ya tambayi momi sai tace batajin akwai wani Abu atsakaninsu,Ammh jin Batun Umman lagos yasa yace zai Nemi Shi Nadir yaji..

Koda ya kira Nadir ya zaunar dashi yana Tambayanshi shi ya kira Umman lagos yace yana Son Zahra,mamaki ya kama ya Nadir yayi Shuru yana hasaahen Daga ina wannan mgnar ta Fito ganin yadda yayi ne sai Abba yace kada ya damu in ba haka mganar take ya sanar dashi,girman Abba a idonshi da kuma Kimarsa da Yadda yake arayuwarsa yasa yakasa masa musu ya amsa da eh shi ya kirata ya sanar da ita,jin haka yasa Momi da Abba sukaji dadi sosai har suka kasa boye murnansu Afili,Shiko Ya Nadir zahra ya kira ya Fara tambayanta itama taji mganar tayi mata bazata Tace itama bata sani ba,sai da ya kira Umman lagos yake tambayanta ta kyalkyacemai da Dariya tana gayamai yadda sukayi da Nadira tace taga ya tsaya kunya Shiyasa ita ta kira baban nashi ta sanar dashi kada wani yamai Shigar Sauri,ganin yadda gabadaya lamarin ya Daure Nadir shiyasa ya share bai nuna ma kowa bai ta ma Zahra kallon Wacce zai ya Aura ba yana kallonta ne da Sigar dayake kallon Nadira,ammh kuma Abba ya Wuce haka agurinsa bazai taba wa
tsamai akasa a ido ba,Zai auri Zahra koda baya sonta ai kanwa take awajensa..

Tunda Abun na gida ne Umman lagos ne kadai tazo aka sanya Rana wata biyu masu Zuwa sai lokacin Ya Nadir ya sanar da matarshi,Taji wani iri sosai kuma bata iya boye kishinta ba,harta koken ko don bata taba Haihuwa ba yasa zai kara aure,lallashinta ya shiga yi da bata bKi har ta sauko ta karbi mganar hannu bibbiyu ta kuma yi mai Fatan alheri Duk da kishin Mijinta na cinta ammh ta danne Tunda dai mijinta bai Chanza mata Daga Son daya ke mata,Sai dai Wani dan Abunda ba”,a raasa ba Tunda Dan adama ajizi ne Tara yake bai cika goma ba.

Zahra ma haka taji Abun kawai Daga sama,Ammh kuma akasan Ranta tayi murna Domin Shima ya Nadir Namiji ne,Kodai baikai Saleem ba to zata jerasu a Aji da Takama da isa,lokacin daya Fara zuwa wajenta da Sigar Mijin da zata aura yayi mata mganganu sosai ya kuma sanar da ita sai tayi Hakuri don yana mata kuma ta sani,so suyi Hakuri da juna duka sai su zauna lafiya,Zahra bata daukan ma kanta Tun Farko ba,tuni ta watsar da wani kishin Banza ta rike Sabon Mijinta kuma yayanta dakyau gefe daya kuma suna ta Shiryen Shiryen bikinsu,da farko ita fara wasan buya da Madam,sai da bita har wajen aikinta bayan ta dawo daga asibiti tana mata tsiyan haka zasu kwashe In ta Shigo ai an zama daya,Zahra tayi murna sosai nan da nan suka koma kamar da,wani lokacin in Zahra tatashi Daga wajen aiki ta kan biya,Nadira kuma ta fikowa murna kamar me,tana ta addu”a Allah yasa kada ta Haihu sai bayan biki cos tana son ta baza kara”i ne part 2 awannan karon.

Biki ya karato Duk da ba gayyah Zahra tayi sai yan wajen aikinsu kawai sai wasu daga cikin kawayensu da sukayi mkranta Zahra ce ta matsamata ta kira Saleema ta Sanar da ita zatayi aure,bata yi musu ta karbi lambarta ta kirata sai da ta sanar da ita Sunanta kana ta ganeta Saleema tayi mamaki sosai kuma tayi murna da jin Zahra zatayi aure,nan take Sanar da ita Tayi Nauyi ammh zata Roke Ya Sadiq in ya yarda zata zo Katsina ta kwana sai su taho tare da Malika,jin haka yasa Zahra tace ta Rubuto mata Full address din gidan Saleem da lambar wayar Malika nan ko take Saleema ta tura musu suka rabu cike da Farinciki kowa na Mamakin yadda dan”uwansa ya chanza wai Saleema keda ciki wai Chanchadi😂

Nadira tabama Zahra Shawaran taje Har katsina ta kaima Malika Katin biki da cimgam,da kuma nemam ya Fiyan juna Tunda yanzu komai ya Wuce,Zahra ta yarda da mganar Nadira hakama momi ta amince mata taje,domin itama tace zata kira Ummi ta sanar da ita Ranar bikin,Nadira ta so ta raka Zahra ammh sai Dr ya hana Don cikinta ya tsufa,Shiyasa Ana saura kwana goma biki Zahra ta Tafi katsina da kanta ta tuka kanta cikin Sabuwar motarta ammh sai da ta tambayi ya Nadir ya kuma bata dama.³⁹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *