MALLAKIN WAYE? COMPLETE
*America* _California(Los Angeles)_ 2011. “Gidan yayi shiru banda sautin kukan mutanen dake ciki baka jin komai, wata Dattijiwan matace wacce bazata gaza shekaru 64 ba a duniya ta fito daga wani ‘daki hannunta ‘dauke da jaririya wacce a’kalla bazata wuce watanni 4 ba. “Zama tayi tsakiyan yaran dake ta shar’ban kuka cikinsu an rasa me ba ma wani baki, itama wnn Dattijiwa
kuka ne sosai ya kufce mata. “Wasu maza guda biyu ne suka shigo ‘daya saurayi ne wanda bazai wuce shekaru 22 ba a duniya, farine sol kyakyyawa yanayinsa zai tabbatar maka shima cikin tashin hankalin yake, mutumin da suka shigo tare dashi yana dafe da kafa’dunsa wanda ko ba’a fa’da maka zaka gane mahaifinsa ne, dan kuwa kammaninsu ya ‘baci saidai kawai matashin ya ‘dan nun masa ‘kuruciya, mutumin bazai gaza shekaru 48 ba, a tare suka shigo cikin parlorn ai kiwa gaba ‘daya yaran suka mi’ke suka rungumesu suna kuka. “Daddy is it true, mummy has gone…… “‘Yar budurwan ciki wacce bazata wuce shekaru 12 ba ta fa’di cikin tsananin kuka da tashin hankali, sosai mutumin da ta kira da daddy ya rungumeta kafin yace” Nadiya dukkaninmu ‘yan adam ne dukannninmu watarana zamu bar duniya, addu’a shi zamuyi wa mummyn ku Allah yasa ta huta Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita. “Sosai suke kuka, wasu ‘yan yara maza guda biyu wanda da gani kasan tagwaye ne baza wuce shekaru biyar ba a duniya suka rungume ‘dan matashin cikin suna kuka, ‘kan’kamesu yayi yana kuka shima sosai, sun jima a haka ko wanni na kuka kafin daga bisani ” Daddy ya ‘karasa ya kar’bi ‘yar jaririyan dake hannun dattijiwan nan yace” Amma kawota, Amma ta mi’ka masa ita tana gohe hawaye. Kallonta *Engr. Nazif Mumtaz* yake babu ko ‘ka’k’kautawa, tausayinta da sonta a lokaci guda yana ratsa ‘bargo da tsokansa, sosai ya rungumeta yana sharan hawaye. “Haka ranan gidan Engr Mumtaz ya wuni cikin tsananin tashin hankali da alhini na mutuwar matarsa kuma uwar ‘ya’yansa.