MARWAN CHAPTER A

 MARWAN CHAPTER A

Maryam mai kike yi ne wai tun ɗazu nace miki kije ki kwashe mun tuwo amma kina ɗaki banga wucewarki ba, idan bazaki kwashe ba inje inkwashe abina da kaina ” Umma ta ƙarasa maganar tana sauraren abinda Maryam zata faɗa, da sauri Maryam ta ajiye wayar hannunta tace, ” wallahi Umma kinga nazo tashi kenan kayan drower ta suka zubo shi ne na tsaya nake gyarawa ” ta ƙarasa maganar tana rufe murfin drower kamar wacce ta gama gyara kayan nata da gaske, Umma ce ta cigaba da mita tana faɗin, ” ay na ɗauka wayar ce ahannunki kike dannawa dan inkika rike waya kamar mai ibada ” fitowa tayi ta wuce cikin kitchen ɗinsu alokacin tuni anfara kiran sallar magriba, kwashe tuwon tayi sannan taje tayi alwala ta gabatar da sallah.+

          Gaba ɗaya suna zaune Maryam da ƙannenta uku, biyu maza ɗaya mace sai mahaifiyarsu Umma suna hira bayan sallah isha’i yaro ne yayi sallama  ya shigo cikin gidan bayan sun amsa yace, ” wai ana sallama da Maryam inji Marwan ” Umma ce tace, ” kaje kace tana zuwa ” kasancewar dama sun san da zuwansa duk ranar alhamis da juma’a yake zuwa hira, fitar yaron babu jimawa Maryam ta ɗauki mayafinta ta fita, kamar kullin yana zaune akan lifan ɗinsa da murmushi ta ƙarasa gurinsa suka gaisa, kamar yanda ya saba zolayarta cikin barkwancinsa yace, ” ina nawa tuwon da kika ci baki rage mun ba ” bata yi wani mamaki ba saboda dama ta saba da jin abubuwan almara daga bakinsa cikin hali ko inkula tace, ” yana cikina ay idan naci kamar kaci ne ” murmushi yayi yace, ” haka ne my Queen, rufe idanki zan miki wani suprise. “

        Ba musu Maryam ta rufe idanta tana murmushi, hannunsa ya ɗora adai-dai kanta wani haske ne ya fito daga hannunsa lokaci ɗaya suka ɓace daga gurun tafiya sukayi mai nisan gaske basu sauka a ko’ina ba sai awata babbar da’ira ta alƙarya, mai ɗauke da waɗansu irin hallitu marasa fasali abun tsoro ne ga duk wani bil’adama, da alama babbar masarauta ce ta aljanu wacce ta ƙunshi hallitun aljanu na duniyoyi daban-daban, duk abinda yake faruwa Maryam bata sani ba.

           kallanta Marwan yayi cikin murmushi yace, ” buɗe idanki My Queen ” Buɗe idanunta Maryam tayi ga mamakin ta ta fara kallan tsakiyar fadar da suke ganin munanan halittun gurin yasa ta cikin ruɗewa da tashin hankali ta rungume Marwan tana runtse idanunta haɗe da kwallah ƙara mai karfin gaske, Marwan ya manta sam ganin haka ne yasa ya kalle su cikin jin haushi ya buga musu tsawa cikin wani irin yare, ” kaskuwase kasmelasi kaskuwase papupasku hagabarsi mundadusi ”  ( Kun fara bijirewa umarnina ne bance muku bil adam zan aura ba ku rikiɗa yanxun nan )  jikinsu na rawa suka amsa masa da, ” faaaaaakusakun malasin yatma ” ( tuba muke Yarima mai jiran gado ) kafin ƙiftawa da bismillah lokaci ɗaya suka riƙiɗa zuwa bil adama hatta da alƙaryar gurun sun sauyata zuwa ta mutane.

       kallan ta yayi yace, ” haba my Queen mai yasa kin fiya tsoro ne kawo ki fa nayi ki gaida su mommy buɗe idanki ki gani ” a tsorace Maryam ta buɗe idanta wani irin kyakykyawan guri ta gani da alama gidan masarauta ne wasu kyawawan ƴan mata ne suka ƙaraso gurinta suna faɗin, ” barkanki da zuwa gimbiya muna miki fatan alheri ” da idanu Maryam ta bisu tana kallo bata amsa musu sai Marwan da ya gyaɗa musu kai, wuce wa sukayi haka aka dinga zuwa gaida Maryam tun tana jin tsoro har ta fara sakin jikinta, Marwan ne yace mata, ” mu ƙarasa ki gaida su Mai martaba ” ba musu tabi bayansa suka ƙarasa wani babban falo ma ɗauke da ƙayatattun kujeru an ƙawata falon da zallar kayan sarauta, wasu ƙyawawan dattijai ta hango mace da namiji suna zaune cikin kamala sanye suke da alkyabba masu kyawun gaske, har ƙasa ta tsugunna ta gaida su sannan suka taso suka fice daga falon, suna fitowa Maryam ta fashe da kuka tana cewa Marwan, ” ina ne nan kawo ni Marwan ko ka fara satar mutane ne bansani ba ” kallanta yayi yana murmushi ya shammace ta yana hura mata iska afuska ” lokaci ɗaya jikin Maryam ya saki Marwan dunƙule hannunsa yayi ya wulwula shi yana buɗewa wani irin haske ya mamaye ɗakin gaba ɗaya, atake suka ɓace daga gurin.

           Bayan sallar Asuba  Umma ce ta ƙara shiga ɗakin Maryam take mata magana, ” wai Maryam kamar mai baccin mutuwa tun ɗaxu nake tashin ki kinƙi ki fito kiyo sallah ” tashi zaune Maryam tayi tana cewa Umma, ” Na fa tashi Umma ” gaba Umma tayi bata ƙara mata magana ba, kallan ɗakin da take ta ƙarayi tana mamakin ganinta aɗakinta.Tuno wani abu take sanyi amma gani take kamar mafarki ne tayi, bacci ne ya ƙara sha mata kai aykuwa haka taja bargo tayi kwanciyarta ta cigaba da bacci, Abba dake ɗakinsu shida Umma kallanta yayi yace, ” har yanxu banga fitowar yarinyar nan ba ƴan uwanta tuni sukayi sallah kin kuwa tashe ta ” kallan sheƙeƙe tayi masa tace, ” haba malam tashi nawa nayi mata yarinyar nan fa ba ƴar goye bace da zan dinga yaƙi da ita akan tayi sallah, kanta zatayiwa ay ” kallan tsaf malam yayi mata yace, ” Yanxu Maryam har nawa take da zaki ce wai kanta zata yiwa inma batayi sallah ba, karki manta haryanxu tana ƙarƙashin tarbiyantarwar mu ce idan bamu bata tarbiyya mai kyau na tabbata sai Ubangiji ya tambayemu ” taɓe baki Umma tayi sannan tace, ” ay sai kuma kayi ni nayi iya yi na ” ta ƙarasa maganar tana jan bargo tana kwanciya, girgiza kai Malam yayi cikin takaici ya tashi yaje ƙofar ɗakin su Maryam yana ƙwala mata kira, firgigita ta taso ta fito tana murza idanu, Abba faɗa ya rufeta da shi jiki na rawa ta wuce ta ɗauki buta ta faɗa banɗaki tana gunguni acikin zuciyarta, kanta tsaye ta faɗa banɗaki babu ko Addu’a tana ƙarajin hauahin tasowar da mahaifinta yayi mata.+

       Washe gari da safe bayan ƙannen maryam sun tafi makaranta, abinda ya faru da ita adaren jiya ne yake ta damunta acikin zuciya, tasan akwai abubuwa da dama da Marwan yake mata na almara amma na jiya yafi damunta gani take kamar mafarki ne, tana zaune jugum tana nazari Umma ta shigo ta same ta a haka kamar kullin Umma cikin faɗa take ta fara faɗin, ” ƴar nema wannan tagumin da kika ja uwar ki ce ta mutu ko ubanki shegiya zaki janyo mana jafa’i ? ” jiki a sanyaye ta kalli Umma tace, ” wallahi Umma wani abu ne ya ɗauremun kai jiya lokacin da Marwan yaxo, daga cemun na rufe ido na sai ganina nayi acikin ƙatan gidan sarauta to nidai daga wannan lokacin bansan mai ya ƙara faruwa ba sai ji nayi fa kince na tashi sallar asuba ” Kallan sheƙeƙe Umma ta watsa mata sannan tace, ” Maryam shaye-shaye kika fara ko kanki ne ya buga? ” jiya kina fita ko minti biyar bakiyi ba ki shigomun harda babbar leda kice mun Marwan ya tafi sannan ki kawo mun zancen rainin hankali lallai Maryam fuskar da nake sakar miki ta fara yawa ” Umma ta ƙarasa maganar tana shigewa uwar ɗaki tana cigaba da mita.

        Da mamaki Maryam ta bi Umma da kallo tana tunanin wacce irin leda ce ta shigo da ita ahankali cikin jimami ta furta, ” to ko dai mafarki nayi jiya ” aykuwa Umma ta uwar ɗaki ta leƙo ta window tace, ” sai dai kam idan mafarkin kikayi kina cen kin yashe ƙaton baki kina bacci, ki tashi kije kitchen zakiga  babbar farar ledar da kika shigo da ita ki ɗauko mun ita, kazar da kikace asa miki acikin firji ki ɗauko ta ki dumamata ”  gaba ɗaya kan maryam ya kullewa yayi ganin abun take kamar labari ne Umma take bata, jiki asanyaye ta wuce ta ɗauko ledar da Umma ta umarce ta zama tayi ta dinga zaro kayan da suke ciki kala-kala biscuit ne da su alawa sai kifin gwangwani dasu chocolate, sai drinks kala-kala kayan ta zurawa idanu tana kallo sai kuma taji daɗi musamman yanda ta tuno irin ɗawainiyar da Marwan yake mata, kira ne ya shigo wayarta da sauri ta ajiye kayan ta ɗauko wayar tata, ganin number Marwan yasa ta fara murmushi, da sallama ta ɗauki wayar muryarta cikin annushuwa.

           Bayan sun gaisa yace mata, ” ƙara duba ledar sai na kiraki anjima” mamaki ne ya kamata tace, ” bangane ba wacce irin leda kuma?”  ta faɗa dan ta tabbatar da ledar da yake nufi, murmushi yayi yace, ” to shikenan na barmiki musun ” har lokacin mamaki ne fal axuciyarta  tanasan tambayarsa tana jin wani iri ƙarfin hali tayi tace masa, ” Marwan jiya da kaxo ba muje wani guri da kai ba? ” murmushi yayi yace, ” to ki tuno mana kinsan ɗan baiwa ne ni ayanxu ma kina iya gani na akusa dake ” dariya ya bata sosai ahakali tace, ” sai kace wani mai layar ɓata, ko ka fara hulɗa da makarai ne ” shi ɗinma murmushi yayi yace, ” ba ɗaya aciki idan kinasan ganina kawai kiyi bayani amma ina fatan bazakiji tsoro ba” cikin gatse tace, ” dan naganka yanxu shi ne zanji wani tsoro kana ina? ” tana rufe bakinta sai ji tayi Marwan yace, ” gani nan my Queen ” tana juyawa ta ganshi sarƙe da hannu ajikin bango yana murmushi.

       Idanu ta zaro waje tana kallon wayar dake hannunta tsoro ne ya kamata tana shirin guduwa sai ganinsa tayi kamar walƙiya ya ɓace, wani uban ihu ta kurma ta yanke jiki ta faɗi asume, bayyana Marwan ya ƙarayi yana murmushi ahankali yace, ” My Queen kin cika rigima sai da na gaya miki ay ” yana gama magana ya kalli ƙofar banɗakinsu sannan yace, ” kargasu-kargasu lamistagu kiginaru ” ( fito-fito ki maye gurbin Queen ) yana rufe baki sai ga wata mai kamar Maryam nan ta fito babu abinda ya banbanta su, tun kafin ta ƙaraso ya ɗora hannunsa adai-dai kan Maryam atake wani haske ya mamaye gurin lokaci ɗaya suka ɓace daga gurin.

        Umma fitowa tayi tana faɗin, ” Maryam idan kin gama wayar kixo na aike ki gidan Maman baby mai adashi ” ba musu kuwa kamar yanda Maryam kewa Umma itama haka ta ɗago tana amsawa Umma da, ” to Umma ay na gama wayar ma ” ta ƙarasa magara tana kallan Umma.Kallan ta Umma tayi tace, ” au wai kina nufin har kun gama waya da Marwan ɗin? ” jabun maryam gyaɗa mata kai tayi, hararara Umma ta watsa mata tace, ” ciwon baki kika fara ne da zaki mun shiru kina gyaɗa mun kai yana ƙadangare ” cikin sanyin hali tace, ” a’a Umma dan Allah kiyi hakuri, Umma bata bi ta kanta ba ta kunto kuɗin bakin zaninta ta miƙawa Jabun Mayam, karɓa tayi har tabi bakin ƙofa zata fita ba hijabi Umma ta saki baki tana kallon Maryam cikin Masifa tace, ” Au abin naki har ya kai haka yaushe kika falle haka da zaki fita babu mayafi kamar muna ƙasar arna ” juyowa tayi bata bawa Umma amsa ba saboda yanda ta balbaleta da faɗa ya ɓata mata rai, janyo hijabi tayi akan igiya ta fice daga gidan.+

            Marwan tunda suka ɓace daga gidansu Maryam basu sauka a ko’ina ba sai tsakiyar dajin Wargass daji ne mai ɗauke da duhun bishiyoyi da ƙoramu masu yawan gaske, hannunsa ɗaya na riƙe da Maryam direwa yayi akan tsakiyar babban wani tafkin teku, ɗayan ɗan yatsan hannunsa yasa ya nuna kan ruwan lokaci ɗaya ruwan ya da re yayi wani irin zurfi Faɗawa ciki Marwan yayi sai da suka lula da nisan gaske sannan suka isa wani daji mai ɗauke da ƙyawan bishiyoyi da waɗansu irin gine-gine, kwantar da ita yayi kan wani gadon ƙarfe wanda yasha ado da zinari yana shafa fuskarta da tayi fayau, wani tunani yayi lokaci ɗaya ya miƙe tsaye ya ɗaga hannunsa sama ya dunƙule shi na ɗan mintina yana buɗewa sai ga wata irin guguwa ta kaure agurin, sai bayan wani lokaci sannan ta lafa lokaci ɗaya sai ga irin gidansu Maryam ya bayyana agurin, wata mata ce ta fito daga ɗaki mai siffar Umma, tana fitowa ta russuna ta fara cewa, ” Yanzulak, kasgasuga walfasu tani mingasukagu tusfatusga minsatu kilgamu kijsahu kilamaau wasbatu kkishu  ” ( Barka da wannan lokacin yarima, zamuyi yanda kake buƙata gimbiya zata zauna damu cikin jindaɗi ) Marwan cikin jin daɗi ya bata amsa, ” labuska lakugasu minsa ki walfati kisasu zarraki minsaku lahanh ” ( hakan yayi mun dai-dai karku bari kuyi yanda zata fahimci wani abu ” kafin matar nan tayi magana sai ga wata matashiyar budurwa ta fito kallan sheƙeƙe tayiwa Maryam sannan tace masa, ” Yanzulak, muaatusaku wajkatu bakaku misatu garsaku gasmarjaka kalkasu ta walsa mimsatu masasi tafu ” ( Yarima wulakancin har ya kai ka kawo mun matarka har gida? wallahi ina gabda hallaka ta muddin bazaka rabu da ita ba ) mugun kallo ya watsa mata cikin ɓacin rai yace, ” musadahu kalfasaci caccasaku kamas kusatu mikasu gagaru ” ( wallahi ko taɓata kikayi zaki gane baki da wayo abinda baki sani ba ko iyayenta suka nemi rabani da Maryam ina iya hallakasu balle ke ) yana gama faɗa yasa hannu ya bigi sama lokaci ɗaya gurin ya buɗe atake ya ɓace daga gurin.2

          Jabun Maryam na fita daga gidan kai tsaye gidan Maman baby ta dira, Maman baby na ɗakinta tana aiki juyowar da zatayi sai ganin Maryam tayi abayanta ko kaɗan bataji motsinta ba,  gaishe ta tayi sannan ta bata kuɗin da Umma ta aiko ta dashi, abinne ya ɓatawa Maman baby rai aykuwa cikin ɓacin rai ta rufeta da faɗa, ” ke bakida hankali ne xaki shigo mun har tsakiyar ɗaki babu sallama, yara sai ku dinga abu kamar dabbobi….” Maman baby bata rufe baki taga idanun Maryam ya rine zuwa jawur saiga faratanta sunyi zaƙo-zaƙo cikin wata irin kausashiyar murya ta fara mata magana, ” ki iya bakinta saboda bakisan koni wacece ba gargaɗi nayi miki inba haka ba gaba zakiyi nadama ” tana gama maganar ta keta ta jikin bango ta wuce abinta, Maman baby dube-dube ta dingayi lokaci ɗaya tsoro ya kama ta ficewa tayi daga cikin gidan saboda yanda tsoro ya kamata gani take bata iya cigaba da zama ba.

          Maryam ta jima ayanda take bayan wani lokaci buɗe idanta tayi ta ganta kwance akan gadon Umma mamaki ne ya kamata saboda tasan tunda tayi wayo bata kuma hawa kan gadon Umma ba bare kuma har tayi bacci, tsakar gida ta fito ta samu Umma na shara Marwan ne ya faɗo mata da abinda ya faru cikin tsoro ta fara mata magana, ” Umma wallahi akwai abinda yake ɗaure mun kai game da Marwan ɗazu fa waya mukayi kawai sai……” kamar yanda Umma ta saba mata haka itama wannan Umman tayi mata cikin Faɗa tace, ” wannan tsakaninku ne keda shi karki kuma sako ni cikin sabgar ku ” shiru Maryam tayi tana nan zaune jugum tana nazari, Buta ta ɗauka zata shiga tayi fitasari tana faɗawa banɗaki bayan ta tsugunna sai ganin wani jariri tayi atsaye yana kallanta yana ɓaɓɓaka dariya, batayi aune ba sai gani tayi yayi taalle ya kama jikin ƙyauren kofar tana kallan gurin sai gani rayi ya ɓace, ihu Maryam ta kurma sosai azabure ta fito daga banɗaki, tashin hankalin wajen har yafi mata na cikin banɗakin,  abinda ya ƙara ɗaga mata hankali ganinta a tsakiyar daji mai ɗauke da mugayen hallitu, jarirai ta dinga gani masu fuskar tsofaffi suna ƙyalƙyale mata da dariya, sai ƙwarangwal masu ƙafafuwan shanu wata matashiyar budurwa ce ta faso ta cikin ƙasa, mai ɗauke da da ƙafafun dokuna harda jelar doki abayanta sai da ta jima tana dariya sannan ta murtuke fuska ta fara magana da murya mara daɗin sauraro.

       ” Ke Maryam ki gaggauta fita daga rayuwar Yanzulak wanda yace miki sunansa Marwan inba haka sai na halakaki, Yanzulak nawa ne ni kaɗai banda ma haukanki waya ce miki ana soyayya tsakanin mutum da aljan harta kaiku ga aure” gaba ɗaya tsoro ya kama dabaibaye Maryam da tsananin mamakin jin abinda wannan hallitar take gaya mata, banda hawaye ba abinda take yi, tana shirin yin magana daga bayanta taji anriƙe mata ƙafa, tana juyawa taga wani ɗan gajeren tsoho atsaye ko ƙwarinta bai kai ba idanunsa na zubda hawayen jini hannunsa na ƙwarangwal” wata uwar ƙara ta kwalla  mai ƙarfin gaske tana fisge ƙafarta, wata irin guguwa taji ta turniƙe gurun daga cikin guguwar Marwan ta gani ya bayyana fuskarsa murtuk ba annuri, da sauri ta ƙarasa gurinsa tana ƙara fashewa da kuka, riƙe ta yayi sosai yana huci atake yasa hannu ɗaya yana nuna jariren ɗake gurin, lokaci ɗaya duk suka daskare suka koma kamar gunkina wasunsu kuma suka fara narkewa, matashiyar budurwar nan na ganin haka ta daki ƙasa lokaci ɗaya ta ɓace daga gurin.

        Maryam fisge hannunta tayi cikin kuka ta fara magana, ” Marwan ina ne nan ka kawo ni dama kai ba mutum bane ka yaudare ni kabari nayi zurfi asoyayyarka bayan kasan babu soyayya tsakanin mutum da Aljan,  na tsaneka Marwan banasanka bana ƙaunarka tsakanina da kai Allah ya isa kuma ka maidani gaban iyaye na ” girgiza kai Marwan yayi cikin halin ko inkula yace, ” Karya kike maryam ni Marwan naki ne na har abada abinda baki sani ba tuni andaɗe da ɗaura mana aure dake amasarautar GADBASGAJI, yanxu haka kina ɗauke da cikin ɗana ajikinki na tsawon wata bakwai kina ganin zan iya rabuwa da Uwar gidana kuma uwar ƴaƴana? ” zaro idanu Maryam tayi cikin tashin hankali tana shafa cikinta tana kallan Marwan.Da mamaki ƙarara afuskarta ta ƙara kallanshi asanyaye tace, ” ciki wane iri Marwan kasan dai tunda muke da kai ba abinda ya taɓa shiga tsakanina da kai?wane irin Aure ne akayi bada sani na ba kuma bada yardar iyaye na ba? Marwan kayi gaggawar maidani gurin iyayena na tabbata ahalin yanxu suna cikin tashin hankali, wallahi nayi dana sanin haɗuwata da kai Marwan mugu azzalumi baƙin macuci Allah ya isa tsakanina da kai” Maryam ta ƙarasa magana tana fashewa da kuka, girgiza kai yayi cikin tausayawa ya fara magana, ” haba Queen meye zaki damu ranki duk kibi ki tada hankalinki bayan kinsan bake kaɗai bace kuma kinsan banasan ɓacin ranki, kuma maganar aurenmu ay mantawa kikayi kin tuna lokacin da kika taba mafarki anɗaura mana aure ana ta shagali washe gari muna waya kike sanar dani cikin farin ciki ? maganar bada sanin iyayenki ba kuwa wannan bai taso wannan labari ne mai yawan gaske, amma mai yasa kika tsaneni haka My Queen? ni banyi niyyar cutar dake ba kuma bazan bari wani ya cuceki ba daga mutum har zuwa jinsinmu ” bata bashi amsa ba sai ma duƙushewa da tayi agurin tana kuka mai tsuma zuciya” shima tsugunnawa yayi cikin kalaman soyayya ya fara lallashinta yana bata hakuri.+

      Jabun Maryam na ficewa daga gidan maman baby ta tsakiyar bangon kitchen ɗin Umma ta bulla lokacin Umma na tsakar gid tana gyaran kayan miya motsi taji a kitchen tana ɗan  leƙawa taga Maryam tsaye tana leƙa cikin shara tana waɗansu irin maganganu da Umma bata san mai take faɗa ba, ahassale ta fara mata magana kamar yanda ta saba, ” dan Ubanki dama kin dawo ɗazu nake ta kwala miki kira kika rabu dani, fuskar  ubanki kike leƙawa a shara kina surutai zaki bar gurin nan ko sai na jefo miki kujerar nan ta sheme ki ” kallan gefen ido tayi wa Umma cikin ɓacin rai hancinta ya fara ɗigar da jini lokaci ɗaya faratan ƙafarta suka fara kara tsayi ga waɗansu irin baƙaƙen gashi da suka fara tsirowa daga jikinta, jin shirun Maryam yayi yawa Umma ta kuma cewa, ” wato bazaki amsa mun ba kenan ko? ” tana cikin haka taji sallamar Abba ya shigo bayan ta amsa yace mata, ” hajja kullin ke kenan cikin yiwa yara masifa da andoshi soron gidan nan muryarki za’a fara ji kwata-kwata bazaki dinga jan yara ajikinki ba ” ita ɗinma cikin faɗa ta bashi amsa, ” yoo kai baka ganin iskancin da yaran suke yi ne wato so kake indinga zuba musu ido kenan ” guntun tsaki yayi yace,” yaran naki kike cewa suna miki iskanci? to Allah ya shiryeki naga ranar da zakiyi hankali, muje ki ɗauko mun ajiyar da na baki jiya dama ita na dawo ɗauka ” ya ƙarasa maganar yan shigewa ɗaki, itama Umma tashi tayi ta bishi tana tafe tana ta mitar maganar da yayi mata.

       Tun lokacin da Abba ya shiga gidan jabun Maryam ta zabura jikinta ya fara ɗaukan zafi atake ta ɓace daga cikin gidan gaba ɗaya, bata sauka a ko ina ba sai tsakiyar fadar su wato masarautar GADBASGAJI tana sauke ajiyar zuciya bayan ta huta tambayar yarima tayi suka ce mata baya nan, tana jin haka ta miƙe tsaye tana wata iriyar hajijiya lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wani kyakykyawan tsuntsu ya keta ta cikin ƙasa ya ɓace, tsuntsun nan bai sauka a ko’ina ba sai tsakiyar dajin da su Marwan suke, akan kafaɗar Marwan ya dira yana yi masa wani irin kuka irin na tsuntsaye, Marwan na gama saurarensa ya gyaɗa masa kai tsuntsun na ganin haka ya tashi sama ya lula cikin gajimare.

           Lokacin Maryam taci kukanta ta mo re gaba ɗaya abun duniya ya isheta, kallanta Marwan yayi yace, ” Queen zan maida ki gida hakan ba shi yake nuna na rabu da ke ba sai dai zanyi haka ne dan kar hankalin ki dana su Umma ya ƙi kwanciya, ki kular mun da kanki da babyna kinji ” Maryam ko kallan inda Marwan yake batayi ba gani tayi ya huro mata iskar bakinsa tana shirin tashi sai ganinta tayi acikin kitchen ɗin Umma, azabure ta miƙe tsaye tana duba inda take maganar Abba taji ya fito daga ɗaki yana kwala mata kira, ” asanyaye ta fito taso ta boye musu halin da take ciki amma ganin mahaifinta yasa ta tafi da gudu ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka.

        Umma riƙe baki tayi tana kallon Maryam cikin mamaki haɗe da masifa ta fara magana, ” yau me zan gani ni hajja makirci zaki mun saboda na miki faɗa wato ke mai uba ko, aykuwa zaki ci ubanki Maryam shegiya nidai da a asibiti na haifeku sai ince canja mun ku akayi, to uban naku ya miki abinda zai miki yanxu ” haushi ne ya kama Abba cikin jin haushin kuwa ya rufeta da faɗa, ” ke wai wacce irin uwa ce da bata damu da damuwar yaranta ba wallahi idan baki rufemun baki ba sai ranki ya ɓaci ” ganin ran Abba ya ɓaci yasa Umma tayi shiru tana gunguni ƙasa-ƙasa, yajima yana jin kukan Maryam har cikin zuciyarsa sai da tayi mai isarta sannan ya  kalleta yace, ” Me yake damunki Maryamu na gaya mun kinji? ” wani kukan ne yazo mata cikin tasashshiyar murya tace,” Abba wallahi bana sanshi macuci ne kuma… ” sai ji tayi bakinta yayi nauyi ta kasa ƙarasa abinda take shirin faɗa, kallan tsaf Abba yayi mata yace, ” waye kuma bakya so? ” kamar dama jiran tambayar take tace,  ” Marwan ” cikin mamaki Abba ya maimaita sunansa sannan yace, ” saboda bakyasan Marwan kike wannan kukan haka haba Maryamu na, wani abu ne ya haɗaku dashi ne? ” samun kanta tayi da  girgiza kai ” dafa kafaɗarta Abba yayi yace, ” kinga yanxu jirana akeyi amma idan na dawo zamuyi magana dake kinji ” gyaɗa masa kai tayi aykuwa Umma ta fara tafa hannuwa tana faɗin, ” makirmakir wato tanan kika ɓullo da makircinki yaro ɗan mutumci ga kyauta da alheri amma ki ce bakya sansa ubanme ya haɗa ku naga ɗazunan naji kun gama waya dashi kina ta tuntsira dariya ” Abba baibi takan ta ba yacewa Maryam, ” Maryamu  bari na wuce sai na dawo ” yana ƙarasa maganar yasa kai ya fice, Maryam jikin bango ta jingina ta durƙushe agun tana fashewa da kuka mai cin zuciya.

        Umma ta jima akan Maryam tana yi mata faɗa ta inda take shiga ba tanan take fita ba tanayi tana zaginta akan tace batasan marwan, Maryam kukanta takeyi duk zagin da Umma take mata bai dameta ba saboda abinda take ji azuciyarta yafi zagin Umma zafi, Ƙara hazuƙa Umma tayi ganin tana ta yiwa Maryam faɗa amma uffan bata ce mata ba, cikin huci ta tunkari Maryam zata doketa tana miƙa hannu wani tafkeken baƙin kare ta gani ya taso mata daga gefen Maryam ya wage mata baki banda turiri babu abinda yake fita daga bakinsa, cikin gurnani ya kalleta ya fara mata magana, ” idan kika sake kika ƙara zaginta zaki gane kurenki ko mugun kallo kika ƙara yi mata ranar zaki gane baki da wayo ” jikin Umma tsuma yake tana karkarwa ta maƙure cen ƙarshen kusurwar bango, atake taga karen yayi girgiza ya nitse ta cikin ƙasa, duk abinda yake faruwa Maryam bata sani ba taji dai Umma tayi shiru atunaninta ma ɗaki ta shiga, ihun Umma taji da sauri ta ɗago kai ganin Umma ta faɗa ɗaki  tana ihu ita ma tabi bayanta tan tambayarta.2

      _wohohoho team Marwan where are u? aikin ka na kyau Yanzulak jamuje wani budurin sai ma Maryam ta haihu musha suna a fadar GADBASAGAJI_💃🏼💃🏼Umma bata tsaya ko’ina ba sai cen ƙuryar uwar ɗaki lokacin da Maryam ta shiga ɗakin acen ƙarshen gado ta hango Umma na sauke ajiyar zuciya, ahankali ta ƙarasa gurin cikin sanyin jiki ta fara yiwa Umma magana, ” Umma me yake faruwa menene ya tsorata ki? ” cikin rawar murya Umma ta buɗe baki zata fara magana sai ganin wannan tafkeken karen tayi ya faso ta jikin bangon ɗakin bakinsa na fidda wuta, akausashe ya ƙara yi mata magana, ” idan kika sake kika sanar da ita wani abu abakin ranki sai na taune wuyanki na haɗiya ƙashinki ” yana gama magana taga ya tashi sama cikin iska ya bi ta saman siling ya ɓace, ganin Umma tana kallon guri ɗaya tana gyaɗa kai yasa abun ya bawa Maryam mamaki, Kiran sunanta Maryam take amma batasan ma tana yi ba sai da ta kirata sau uku sannan ta juya ta kalleta tana amsawa, cikin mamaki Maryam ta ƙara tambayar Umma, ” Umma ina tambayarki lafiya kuwa? wani kika gani ko tsorataki akeyi? ” jiki a sanyaye Umma tace, ” a’a ba komai kawai ƙadangare ne yaso faɗomun ajiki ” shiru Maryam tayi tana wasu-wasun abinda Umma ta faɗa saboda sam ta lura ba haka bane, amma sanin halin Umma na faɗa yasa ta haƙura bata tilsta mata da tambaya ba, asanyaye ta fice daga ɗakin ta koma ɗakinsu tan haɗa kai da gwiwa, gaba ɗaya abun duniya ya dame ta, Umma na ganin fitowar Maryam itama da sauri ta fito ta koma tsakar gida ta zauna har zuwa lokacin tsoro bai gama sakinta ba.+

             Maryam ta jima tana mamakin halin da take ciki afili take furta, ” Marwan dama ba mutum bane duk tsawon shekarun da muka shafe da shi, wai yau nice harda cikin aljani amma kuwa indai haka ne na shiga uku na shiga cikin tashin hankali, Allah ya isa tsakanina da kai Marwan ubangiji yayi mana sakayya da kai cikin gaggawa ” tana ƙarasa maganar ta fashe da kuka, haka Maryam ta wuni a ɗaki cikin ƙunci da ɓacin rai tun tana tunani tana hawaye har bacci yayi awon gaba da ita, cikin bacci tayi mafarki ta ganta acikin fadar su Marwan tana zaune akan wata tamfatsetsiyar kujerar alfarma wasu kyawawan ƴanmata su shida na zagaye da Ita Marwan ne ya shigo inda take, lokaci ɗaya suka russuna suna gaishe shi sannan suka fice daga fadar, yana ƙarasowa gabanta afusace Maryam ta ɗaga hannu ta wanke Marwan ta kyawawan Mari guda biyu, kafin yayi mata magana ƙarar dirar abu sukaji, Maryam na juyawa taga wannan matashiyar budurwar mai ƙafafum dokuna ce tsaye acen abayanta fuska ba walwala ta fara yiwa Marwan magana, ” labsajasakinsati masgufata kalbasu tayi fafutakisna walkadisani magrasafatu hutmasagu kalamasu minsata gasunkaji banjinma ” ( ka duba kaga ƙasƙantacciyar data ke marinka, wannan ba abin kunya bane agareka dama masarautar mu ba ) cikin jin haushin kalamanta ya maida mata da martani, ” mududukafi sakufadu kismaki fadukati mimjakijawulatin? mafardu  fagmasuhatu? kisadasuyasu minsagiratunkalima kinjidufat ” ( bance miki ki daina shiga hurumina da matata ba? kinmance hukuncin da na miki wancen karan ko? zaki gane kurenki tunda kike niyyar kaini bango ” yana rufe baki daga gurin da yake ya miƙa hannunsa har zuwa gurin da take tsaye, tazararsu kuwa zatayi wajen taku huɗu ko biyar, afisace ya fisge kanta daga jikinta sai ga kanta ahannun marwan ya rabu da gangar jikinta, cikin jin haushi itama ta fara masa magana, ” lukasu markahujihinkas minsaku warkajuka lokazugamu ninmaaugafdasu Yanzulak ” ( yanxu saboda wannan yarinyar kake dizgani agabanta yarima ” kanta dake hannun Marwan ne yake wannan maganar, baibi ta kanta ba ya wulwula kan nata yayi jifa dashi sama, atake kan ya ɓace, girgiza gangar jikin ta yake yi lokaci ɗaya ya fara riƙida yana daddarewa, Maryam ji tayi gangar jikin ta kece ta wata mahaukaciyar dariya kafin Maryam tayi wani yunƙuri tuni wannan dararren jikin ya fara sauya yanayi zuwa siffar mace mai kama da Maryam sak, rabuwa sukayo gida uku ajikin kowacce uku wata ukunce take fita daga jikinta, kafin wani lokaci tuni sun cika gurin farrr Maryam ta gansu sun buɗe mata ido, rufe idanta tayi tana kwarma uban ihu, azabure ta tashi tana kiran sunan Umma jikin duk ya jiƙe da gumi sai dube-dube take yi, tana cikin wannan halin Umma ta shigo ɗakin da sauri tana tambayar ta.

       ” lafiya Maryam kike wannan ihun haka ” ta ƙarasa maganar tana kallan jikin bango dan a tunanin Umma karen daya tsorata ta shi ne ya tsorata Maryam, hawaye ne ke zuba a idanun Maryam tace wa Umma, ” Wallahi Umma wani irin mugun mafarki nayi wallahi tsoro nake ji ” ta ƙarasa maganar tana shigewa jikin Umma tana tusa kanta ajikinta, jimm Umma tayi saboda tasan Maryam tun tana yarinya sam bata da tsoro, ahankali cikin sanyin murya tace mata, ” wanne irin mfarki kikayi? ” da sauri ta ɗago zata gayawa Umma sai ji tayi bakinta yayi mata nauyi ta kasa gaya mata jiki ba ƙwari tace, ” na manta Umma amma dai ma abun tsoro ne ” jinjina kai Umma tayi tace, ” kinsan ba’asan bacci atsakiyar rana saboda lokacin tafiya da dawowar makarai ne sai ki kiyaye gaba ” ta ƙarasa magana tana miƙewa saboda ƙaurin girkinta da taji yana konewa, Umma na fita komai ya dawowa Maryam sabo, ahanakali tace, ” Marwan bazaka kyaleni ba na shiga uku ni Maryam aykuwa duk yanda za’ayi Abba na dawo sai na gaya masa halin da nake ciki ” tana rufe baki taga Marwan ya faso ta jikin bango yana ce mata, ” Maryam karkiyi gangancin sanya iyayenki cikin matsala, banasan abunda zai kaimu ga ɓatacciya tsakanina dasu, banasan ta sanadinki ki rasa iyayenki gaba ɗaya ina fatan kin fahimci abinda nake nufi…” tun bai rufe baki ba ta shammaceshi ta ɗauki wani bokitin ƙarfensu dake gefe zata rafka masa aka, sai ji tayi ya wuce ta cikin iska ga kuma marwan tsaye agabanta, murmushi yayi ahankali yace, ” Maryam kenan kina wasa da lamarina haryanxu bakisan waye Yanzulak ba Marwan kika sani ” yana rufe baki yabi ta jikinta ya koma ta jikin bango ya wuce.  Maryam juye-juye takeyi amma babu Marwan ba alamarsa jikin bango ta jingina cikin baƙin ciki da jimami hawaye ya fara gangaro mata tana dana sanin haɗuwarta da Marwan, Kiran sallar la’asar taji sai lokacin ta tuna bata yi azahar ba jiki ba kwari ta fice daga ɗakin ta ɗauki buta ta faɗa banɗaki bayan ta fito taje ta gabatar da sallah, tana sallah tana hamma kamar wacce ta kwana batayi bacci ba, adaddafe ta idar da sallolinta tana idarwa taji sallamar su Mustafa sun shigo ɗakin, da murnar su suka fara mata magana ganin yanayinta ba walwala yasa suka wuce kowannensu ya fara ƙoƙarin fidda uniform ɗinsa, Umma ce ta leƙo ɗakin ta kalli Maryam tace, ” Maryam wai me ya sameki ne yau wuni guda baki ci abincin rana ba, yanxu idan ubanki ya dawo kila ki kuma sashi gaba kina wani kukan na munafurci ko? to ni na fita idan kin gaji da zaman ɗakin sai ki fito kije ki ɗebi abinci ki cinye……. ” maganar Umma ce ta maƙale lokacin da taji saukar wani irin duka agadon bayanta har sai da ta kusa durƙushewa, azabure ta juya tana ƙunduma uban ashar, mugun gamon da tayi da wannan baƙin karen shi yasa ta ja bakinta ta tsuke shi tana sauke ajiyar zuciya, wanna karan karen da tagani yasha banban da wancen, wannan ganinsa tayi yana ɗauke da ƙafafun mutane ga kunnuwansa irin na mutane, sannan harshensa wani irin tsayi gareshi har  ja yake da ƙasa, bai cewa Umma uffan ba sai nuna ta da yake da hannunsa yana gyaɗa mata kai, kafin ta buɗe baki  taga ya nitsa cikin ƙasa ya bace, gumi Umma ta goge daya tsatstsafo mata afili ta furta, ” na shiga uku ni hajja ” dago da kai Maryam tayi tace, ” magana kikeyi Umma? ” cikin sauri Umma tace, ” a’a cewa nai ki zuba abincinki ya huce tuntuni ” jiki ba ƙwari Maryam ta tashi ta wuce kitchen ta zuba abinci badan tana san ci ba sai dan gudun faɗan da umma zata yi mata.+

            Gaba ɗaya yanayin Maryam ya canja ko magana bata san yiwa kowa sai dai ta zauna ita kaɗai tayi shiru, da daddare bayan Abba ya dawo yaci abinci kiran Maryam yayi tunda taji Abba ya kirata gaban yake ta dukan uku-uku haka kawai taji tana tsoron gaya masa, aɓangare ɗaya kuma tana fargabar sanar dashi batasan mai Marwan zai aiwatar akansa ba.

       Jiki a sanyaye ta ƙarasa kan tabar da mahaifinta yake zaune ta zauna, kallan tsaf yayi mata ayanda ya fahimceta tana cikin matsananciyar damuwa saboda wuni guda fuskarta har ta faɗa, cikin tausayawa ya fara mata magana, ” Maryamu na ɗazu kin fara yimun wani zance, naji kince bakya san Marwan bayan ke da kanki kika bawa yaran nan dama har ya turo iyayensa suka kawo kuɗin aurenku dashi, amma bansan dalilinki na cewa bakya sanshi ba ko wani abune ya haɗaku? ” ƙirjinta ne ya cigaba ta bugawa ahankali tace, ” a’a ba komai ” Umma dake gefe baƙin ciki ya cikata ji take kamar ta janyo Maryam ta rufe da duka saboda ko kaɗan ita bata ga aibun Marwan ba, ita gani take ma kamar Maryam nasan yi musu baƙin cikin ɗan abun arxikin da yake yi musu ne.

        Abba tsam yayi yana nazari sannan ya ƙara cewa Maryam, ” Maryamu kin tabbatar da ba abinda ya shiga tsakaninku, karfa nayi bincike naje ba haka bane ” kallan mahaifin nata tayi a ɗan tsorace tace, ” bincike kuma Abba? ” shi ɗinma amsa ya bata, ” ƙwarai bincike ay bazan yanke hukunci ke kaɗai ba idan nayi haka kinga ay banyi adalci ba, bari inje insa kati inkira Marwan ɗin awaya shima inji daga bakinsa ” atsorace Maryam ta kafe mahaifinta ido lokaci ɗaya ta ji hawaye na zubo mata musamman data tuno da gargaɗin da Marwan yayi mata, dafa hannun Mahaifinta tayi tace, ” dan Allah Abba karka yi wani bincike ka ƙyaleshi kawai banasan wani abu ya sameka Abba ” Abba ya jima yana kallan Maryam musamman da waɗannan kalaman nata, cikin rashin fahimta ya tambayeta, ” bangane ba kina nufin mu zuba muku ido ahaka, to idan iyayensa suka xo da maganar sa rana sai Alokacin zamu ce musu kince bakya sansa? Ya kike ganin zasu ɗauke mu, kina ganin zasu ɗaukemu a dattijan kwarai kuwa? nafisan tunda zafi-zafi nasan matsalar da kuke ciki idan wacce xa’a dai-dai ta ku ce mu manya mu shiga maganar idan kuma bamai daidaituwa bace shikenan sai mu basu hakuri mu maida musu da kuɗinsu, Maryam ki nutsu ki yi tunani ni bazan aura miki wanda bakya so ba bazan miki auren dole ba, na baki nan da gobe kiyi tunani zan jinkirta bazan kira Marwan ba har sai naji hukuncin da kika yanke” hawaye ne yake ta wanke fuskar Maryam gaba ɗaya kanta ya kulle tama rasa abinda yake mata daɗi, shi kansa Abba yasan ba banza ba tabbas akwai abinda yake faruwa tsakanin Maryam da Marwan sai dai yanda ya fuskanta kamar tana san ɓoye masa wani abu ne, kallan tsaf ya ƙara yi mata sannan yace, ” Maryamu na idan kina jin kunyar sanar dani wani abu ki samu mahaifiyarki ki sanar mata ita sai tamun bayani, karki yanke hukuncin da kikasan zai cutar dake kiyi nazari kinji? ” ya ƙarasa magana yana kallanta, gyaɗa masa kai tayi sannan yace ta tashi ta fita, ba musu kuwa haka ta miƙe ta wuce Umma sai binta take da mugun kallo tanasan magana tana tsoron abinda zai biyo baya, Abba ne ya kalli Umma ya fara mata magana, ” Hajja ki tsaya ki nutsu na lura yarinyar nan tana cikin damuwa, ki jata ajikinki kiji matsalarta da abinda ke damunta, banda hantara dan Allah…..” katse shi tayi da, ” wallahi malam nima akwai maganar da nake san yi maka tsakani da Allah gidan nan anfara tsorata ni wallahi makarai ne acikin gidan nan ” kallanta yayi yaga fuskarta ba alamun wasa yace, ” azkar zaki dage dashi kina karatun alkur’ani Allah ya shiga tsakanimu dasu ” ahankali tace, ” Aameen ” ya jima yana jaddada mata maganar Maryam yana kuma yi mata nasiha, jikin Umma ne yayi sanyi musamman da ta lura da yanayin canjin da ta gani daga gurun ƴar tata.

       Maryam na shiga ɗaki kwanciya tayi akan katifar ta tana nutsawa cikin tunani, motsi taji daga gefenta atunaninta Hafsa ce bata ko kalli gurin ba tace, ” Au dama hafsa kina ɗakin nan akwance tun shigowa ta shine kikayi shiru ko bacci kikeyi? tsabar wulakanci zaki kwanta sai bacci yayi gaba dake bayan kinsan yau kece da ɗaura mana gidan sauro, wallahi idan na tashi da duka zan tashe ki ” Marwan murmushi yayi ayanda take faɗan nan ba ƙaramin birgeshi tayi ba magana ya fara yi mata, ” Queen wasa-wasa kema fa kin iya faɗa ” numfashinta ne ya kusa ɗaukewa cikin tashin hankali azabure ta tashi tana sauke ajiyar zuciya, murmushi ya ƙarayi sannan yace, ” naji duk abinda kuka tattauna da Abba, Maryam karkixo kiyi abinda bazakiji daɗinsa nan gaba wallahi muddin kika sa Abba ya fahimci lamarin jinnu a tattare da ke wallahi agoben nan sai dai gawarsa, ke idan ma kunga gawarsa ku gode Allah ina iya shafe shi daga duniyar nan ku nemeshi sama ko ƙasa ku rasa, kuma duk duniya nan ba wanda ya isa ya dawo dashi ” bai jira cewar ta ba ya tashi cikin iska yabi ta saman siling ya ɓace, Maryam dafe kanta tayi jiki a sanyaye ta silale ƙasa tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya.Hafsa ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke bargon shinfiɗarsu jin irin kukan da Maryam take yi yasa jikinta yayi sanyi saboda asaninta da Maryam bata taɓa ganin tana gursheƙen kuka irin wannan, cikin sanyin jiki ta dafa ƴar uwar tata aykuwa Maryam azabure ta tashi atunaninta Marwan ne ya ƙara zuwar mata, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, Hafsa ce ta jefa mata tambaya, ” Yaya Maryam lafiya kike kuka me Umma ta miki? ” ta ƙarasa maganar ƙasa-ƙasa dan kar Umma taji saboda atunaninta ko ita da Umma ne, Maryam goge hawayenta tayi sannan tace mata, ” ba abinda aka mun Hafsa kaina ne kawai yake ciwo ” ta ƙarasa maganar tana kwanciya akan katifa haɗe da dafe kanta, jin abinda Maryam ta faɗa yasa Hafsa tace mata, ” Sannu to kisha magani man ” ta ƙarasa maganar tana janyo net zata ɗaura musu.+

        Cikin tsakiyar dare Abba na bacci yayi mafarki da wani baƙin mutum mai mummunar hallita kawuna gareshi sunkai wajen guda goma sha biyu sai hannuwa babu adadi amma ƙafafunsa da gangar jikinsa daidai dana mutane ne, kowacce fuska ɗauke take da wani wagegen baki sai zubar da wani baƙin jini sukeyi, da gudun gaske ya biyo Abba ga harshinansu sai kaiwa Abba cafka sukeyi, gudu yakeyi har sai da ƙarfinsa ya kusa ƙarewa tsayawa yayi cikin ikon Allah, Allah ya bashi sa’ar furta ayatulkursiyyu tun iya ƙarfinsa yake yi lokaci ɗaya yaga wannan kawunan suna narkewa suna rozayewa, ganin haka yasa ya ƙara ƙaimi ya dinga karanto ayayin kariya ya tofawa wannan mutumin duk inda yawun Abba ya sameshi sai gurin ya kama da wuta, da ƙyar yaja jiki ya gudu, Abba bai fasa karantawa ba har sai da ya farka afili yana faɗin, A’uzibillahi minnashshaiɗanirrajim” cikin yanayin bacci yaso yaga giftawar abu amma da yake yana cikin firgici sai bai yarda da abinda ya gani ba, gaba ɗaya jikinsa gumi yake sharkaf, tashi yayi da a’uziya ya fita yaje ya ɗauro alwala, ɗakin ya koma ya shinfiɗa dadduma yana gabatar da sallar nafiloli bayan ya idar ya buɗe kur’ani ya fara karantawa.

        Waahegari ma haka Maryam tayi wannan wuni sukuf ba um ba umm umm sai dai tayi shiru tana nazari idan ta tuno da lamarin Marwan sai tayi kukanta ta share hawayenta, ita kanta Umma wannan sauyin halin na Maryam ba ƙaramin damunta yayi ba gashin wunin ranar Maryam ba abinda tasa acikinta, sai dai daɗin da taji da wunin ranar gaba ɗaya Marwan baizo mata ba.

       Bayan dawowar Abba kamar yanda ya mata alƙawarin  kiranta yayi ta zauna yau ɗinma jikinta gaba ɗaya ba kwari bare walwala, kallan tsab yayi mata gaba ɗaya ta bushe ta rame ta lalace kamar mai jinya, magana ya fara yi cikin tausayawa, ” Maryamu na wane hukuncin kika yanke? ” wannan karan taji faɗuwar ƙurjin da sauƙi shiyasa tayi ƙarfin hali tace, ” Abba ban yanke wata shawara ba nidai Abba banasan Marwan ” gingina kai yayi sannam yace, ” ikon Allah kenan, to ko kinada wani wanda kike so bayan shi? ” shiru tayi sai cen kuma tace, ” bani da kowa amma dan Allah Abba ka aura mun koma waye zan zauna amma banda Marwan ” ba Abba ba hatta Umma sai da ta girgiza da jin maganar da ta fito daga bakin Maryam, Abba ya jima yana girgiza kai sannan yace mata, ” Allah yayi miki albarka Maryamu tashi kije xan nemi iyayen yaron sai inyi musu magana cikin fahimta yanda bazasu ga anmusu wulaƙanci ba ” kamar bazata tashi ba haka ta kafe mahaifinta da idanu tana kallo, magana take sanyi masa amma bakinta yayi nauyi, gyaɗa mata kai yayi alamar ta tafi ya gama da ita, tashi tayi jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinsu.

          Maryam na shiga ɗakin su taga wata baƙar guguwa ta turniƙe gurin, daga cikin ƙurar Marwan ne yaso fuskarsa atsuke ba alamar wasa sai jikinsa duk raunika, da ƙarfin gaske ya fisgi hannun maryam daga ɗayan hannu sa kuma jabun Maryam ce ya ajiye, yana buga ƙasa ta dare ya fisgi Maryam suka nitsa ciki.Marwan shi da Maryam basu sauka a ko’ina ba sai cikin wani tafkeken kogon dutse, suna dira cikin dutsen haske yabi ya mamaye gurin, wannan karan Maryam kasa kukan tayi ta zubawa sarautar Allah ido lamarin Marwan ya fara bawa Maryam mamaki, suna nan tsaya taji ya fara waɗansu irin surutai cen sai ga wani ƙaton tsuntsu yaxo ya rissina agabansa, magana ya fara yi masa shikuma cikin girmamawa yake saurarensa, ” kagaadirati lamsafudatsuka bomsakaadi wakalsab tinsak ” ( kaje ka kawomun duk kayan buƙata a agiye mun anan ) yana gama saurarensa ya fice da gudun gaske, kafin wani lokaci tuni tsutsun nan ya ƙayata musu kogon dutsen nan da kayan alatu kamar ba kogon dutse ba, gefen gado Marwan ya ja hannun Maryam ya zaunar da ita sai alokacin Maryam ta samu bakin magana, ” Marwan yanxu mai kayi kenan? kana ganin kayiwa iyayena adalci wai me kake so dani ne Marwan nace maka banasanka ana soyayya dole ne ko ana soyayya tsakanin mutum da aljan ne, ka raboni da iyaye na kai azzalumi ne Marwan soyayyata da kai ba abinda ta jaza mun sai masifa, wallahi da ina da yanda zanyi inkashe ka wallahi da nayi atake na kashe ka na rabu da masifarka, na tsaneka Marwan Allah yayi gaggawar kasa mun akan wahalar dani da kake yi ” ta ƙarasa maganar tana tusa kanta cikon ƙafafunta tana fashewa da kuka, kallan tsaf Marwan yake mata har zuwa lokacin babu walwala afuskarsa sannan yace, ” Maryam tunda nake aduniya babu wanda yake mun abunda kike mun daga jinsin mu har zuwa na bil adam, kinsan meye dalili saboda ina sanki kuma ina ƙaunarki amma mahaifinki na neman ya sanya kansa cikin masifa, dubi jikina nayi tsammanin zaki tambayeni meya faru dani? Mahaifinki yaji mun raunin da tunda nazo duniya ba’a taɓa jimun irinshi ba ” azabure Maryam ta ɗago jin cewa Abba ne ya ji masa mugayen rauninka da ta gani ajikinsa, bai saurareta ba ya cigaba da magana, ” nasan dama zamu fafata dashi saboda mugayen ɗabi’unsa amma nasan ta inda zan ɓullo masa, nasan dik cikin yaransa yafi ƙaunarki kuma yafi ji dake dan haka nasan zai iyayin komai akanki,sai dai duk wannan ya zama na banza tunda gaki ke na kawo ki nan kuma keɗin irinmu ce, nasan babu mahalukin da ya isa ya fiddake daga gurin nan sai ni, ke ko acikin jinsinmu babu wanda yasan na kawo ki gurin nan sai wancen tsuntsun, shikuma ina me tabbatar miki da ayau ɗin nan zan nakasta shi yanda ma bazai san awace duniya yake ba, kinga sai muyi rayuwar mu cikin kwanciyar hankali ” Maryam da haushi haɗe da tsoro ya cikata uffan bata ce da Marwan ba sai ruwan hawaye da takeyi.4

         Washegari da asuba Abba da kansa y leƙa ɗakinsu Maryam ya tashe su suyi sallah yanajin sun tashi yayi alwala ya wuce masallaci, Jabun Maryam ce ta fara tashi ta fice buta ta ɗauka ta faɗa banɗaki bayan ta fito tayi abunda zatayi ta koma ɗaki kan katifa ta zauna harsai da Hafsa tayo alwala taje tayi sallah duk tana kallanta, bayan ta idar ta kalleta tace, ” Yaya Maryam kinsan dai in Abba ya dawo yaji bakiyi sallah ba faɗa zaiyi ” cikin birgewa jabun Maryam ta tashi ta ɗauki hijabi tasa ta fara dundungurawa kamar yanda taga Hafsa tayi, bayan ta idar komawa tayi gefen Hafsat kan katifa ta kwanta tana mamakin irin rayuwar da bil adam sukeyi.

             Tana ganin bacci ya kwashe Hafsa da sauri ta tashi ta keta bango ta fito tsakar gida cikin ƙanƙanin lokaci ta gyara musu gida tsaf hatta ruwan shayi sai da ta ɗora musu, motsin Maryam ne ya tashi Umma da ta makara batayi sallah asuba ba har gari yayi haske, Abba dake gefe yana ganin tashinta yace, ” yanxu ke hajja ba kyajin kunya ki tashi kiyo alwala ga yara na ganinki da farar safiyar nan? ba irin tashin da ban miki ba sai kice zaki tashi amma kiyi biris, nikam zanga ranar da zaki gyara halinki ” Umma sosa kai take yi bata ƙarasajin mai yake faɗa ba tayi ficewarta, mamaki ne ya kamata ganin komai a kammale tsaf dashi, Maryam ta hango a kitchen cikin jindaɗi tace, ” a’a maryamu na yau tun farar safiya kika hutarsheni haka ” murmushi Maryam tayi mata tace, ” eh Umma ” banɗaki ta faɗa tayo alwala ta wuce ɗaki itama jabun Maryam ta koma nasu ɗakin.

               Da ƙarfin gaske sukaji ana buga musu gida Umma dake falo ita ta fara zuwa take tambayar mai bugawa daga cen ɓangaren akace, ” Nasiru ne ” jin sunan mai bugun gidan Umma ta ɗan ja guntun tsaki tace, ” Nasiru dama kaine kake mana wannan bugun kamar munci bashinka ” ta ƙarasa maganar tana zage sakatar ƙofar, Abba na jin haka ya taso ya fito daga ɗaki, nasiru cikin tashin hankali ya fara magana, ” ina mai gida yake ga shagonmu cen ya kama da wuta sai ruwa ake ta zubawa wutar taƙi mutuwa sai ma gaba da takeyi ” cikin tashin hankali Abba ya rafka salati yana fitawa daga gidan, tare da nasiru suka tafi ilahirin jikin Abba karkarwa yake saboda tashin hankali, Umma kuka ta fashe dashi tana kiransu Maryam, da sauri suka fito musamman da sukaji irin kukan da Umma takeyi, cikin kuka ta sanar dasu abunda ya samesu dama tuni Maryam taji duk abinda ya faru, cikin subutar baki tace, ” Yanzulak Wargass ” kallanta Umma tayi tace, ” kinajin abunda ya samu mahaifinku amma naga ko ajikinki ” cikin wayencewa ta ƙirƙiro kuka ta fara yi, ta jima tanayi sanna ta nufi hanyar fita tana cewa Umma, ” Ina zuwa Umma ” da sauri Umma tace, ” haka xaki fita ba hijabi kai Mustafa ɗauko mata hijabi taje ta gano mun halin da ake ciki ” tun kan ta rufe baki ya ɗaukowa Maryam hijabi da saurin gaske ta fice daga gidan.

       Tana fita bata tsaya ko’ina ba sai a tsakiyar dajin Mundarfajan, ” da ƙarfinta take kwalawa Marwan kira yana daga cikin kogon dutse yajiyo kiran da take masa, atake ya lula ya ƙarasa gurinta ranta aɗan ɓace ta fara masa magana, ” yadarihaka bansaku Maryam minsakauji? bangajirka biskafu laminsu vangafa tinsaku wasdafugahu mhnsatu kilmash jahaku gasuhu baisamun? ” ( naga Mahaifin Maryam yayi gobara maiyasa zakayi masa haka? ka ɗauke masa ƴa kuma kana neman ka fara sanya shi cikin matsala mai yayi maka ne haka? ) sai da ya xagayeta sannan ya fara mata magana, ” kuksasi minsagu kalamalis ninaski gahfazu wargasuhu binsahu,  likamsuhuk gafgasgaisu harbasu kalamsi ” ( banasan shishshigi ki tsaya akan aikin da na ajiyeki, taɓoni yayi kuma dole na ɗau mataki akansa ” cikin ɓacin rai tace, ” minsahu kalnasdughu Yanzulak misafu kalmansati ” (  gaskiya kai azzalumi ne Yanzulak, kafiye san kanka da yawa ) tana ƙarasa maganar ta ɓace daga gurin.

        Lokacin da ta dira wajen shagon Abba tuni mutane sunyi carko-carko kowa ya zubawa sarautar Allah ido saboda sunyi iya yinsu akan wutar sun kasa kashe ta, gadan-gadan Maryam ta tunkari shagon da gudun gaske mutane suka riƙota kowa da abinda yake faɗa, Abba ne ya fara mata faɗa, ” Maryamu kina ganin wuta zaki faɗa ciki meye haka zakiyi? bakisan wannan yana daga cikin ƙaddararmu bane ” murmushi tayi masa tace, ” Abba ka ƙyaleni ba abinda zai same ni ” kafin su ankara tuni Maryam ta tunkari kofar shagon da ƙarfin gaske tasa ƙasa ƙaf ta bugi kofar shagon, atake kofar ta buɗe hannunta biyu tasa ta dafa ƙofar shagon, buɗe bakinta tayi ta fara huro iska sannu ahankali wutar ta fara mutuwa, kutsa kanta tayi cikin shagon sannan ta ja ƙofar ta kulle bayan wani lokaci tana buɗe shagon sai gani sukayi shagon ya koma yanda yake kamar wani abu bai taɓa faruwa ba agurin, bayan fitowarta jama’ar gurin kallon kallo suka farayi ajunansu tana tunkaro inda suke zata gun Abba, gaba ɗaya gurun suka dare suka fara yin takai-takai.Shi Kansa Abba tsoro haɗe da mamakin abinda Maryam ta aikata yake yi ahankali ya fara ja da baya cikin tsoro, ganin halin da Abba yake ciki yasa Maryam ta ƙarasa gurinsa da sauri tana faɗin, ” Abba lafiya me yake faruwa? ” har zuwa lokacin zuciyar Abba rawa take yi aɗaɗɗare yace mata, ” Maryamu abinda kika aikata dole ya bawa kowa mamaki, Maryam inafatan ba wani ƙulunboton kika fara ba, tunda indai ba ƙulunboto ba babu wanda zai ga abinda kika aikata yace cikakken mutum ne yayi shi, ina tsoron abinda zaije ya dawo tunda kina ganin yanda mutane suka bazama aguje ” sai alokacin ta san lallai abunda tayi kuskure ne saboda babu wani bil adam da zai aikata irin abunda tayi shi, cikin rashin sani ta furta, ” musdarbarsahu kisasugar ” ( dole na sake salo ) ido Abba ya ƙura mata jin kalmomin da ta furta cikin rashin kwanciyar hankali yace, ” mai kika faɗa haka Maryamu? Ina tsoro fa karki shiga cikin irin waɗannan miyagun ƙungiyoyin, ki dubi Allah da Annabi ki gaya mun gaskiya karki ha’inceni Maryam bansanki da boye-boye ba ” sosai tausayin Abba ya kamata saboda yanda ta lura mutum ne mai sauƙin kai da sanyin hali, ga ɗabi’un sa ba ƙaramin burgeta suke ba, aɗan zaman da tayi dasu har taji sha’awa addininsu ya shige da tausayin halin da Marwan yake shirin jefa su, asanyaye tace masa, ” da gaske Abba babu wata ƙungiya da na shiga ka yarda dani bazan cutar da kai ba ” Abba badan ya yarda da abinda Maryam ta faɗa ba sai dai kawai yayi haka ne dan ya nuna mata amincewarsa saboda so yake ya fara bibiyar lamuranta, kallanta yayi yace, ” muje gida Allah yayi miki Albarka ” ɗan jim tayi saboda  batasan amsar da zata bashi ba, tsallakawa tayi taja ƙofar shagon ta rufe da key ta kuma tsallakowa, gaba ta wuce Abba ya rufa mata baya, duk inda suka wuce sai dai mutane su fara leƙensu kowa da abinda yake faɗa.+

           Suna shiga gida Umma dake ta safa da marwa atsakar gida da sauri ta ƙaraso gurinsu cikin tashin hankali ta fara tambayar Abba, “oh Malam shikenan kayan shagon sun ƙone ƙurmus ko? wallahi nifa gani nake akwai lauje cikin naɗi anya ba sa hannun maƙotan shagonka kuwa? A ce shagonka shi kaɗai ne ya kama da wuta kuma ba nepa aka kawo ba bare ace matsala ce ta faru waya ta haɗu da waya wutar ta kama ba, gaskiya akwai maƙarƙashiya ” Abba shiru yayi har yanxu acikin ta’ajibi yake, wannan karan ma Umma magana ta ƙara yi, ” Malam naga kayi shiru ina magana ” jiki asanyaye yace, ” Hajja muje na zauna tukunna ” ba musu suka wuce cikin falon su Hafsa duk sunyi carko-carko da kaga yanayinsu kasan suna cikin tashin hankali.

        Bayan sun zauna Abba ya zayyanewa Umma duk abinda ya faru da abin al’ajabin da Maryam ta aikata, Umma na jin haka azabure taja baya cikin halin tsoro tace, ” Maryam kece da shiga shagon gobara gashi naga ko ƙwarzane babu ajikinki anya Maryam wallahi ban yarda dake ba ” ba ƙaramin dariya Umma ta bawa jabun Maryam ba musamman yanayin da Umma tayi maganar da tsananin tsoron da tagani a idanunta, amma gudun karta ƙara tunzurata yasa ta gimtse dariyarta tace, ” Umma baki yarda dani ba? ” jabun Maryam ta tambayeta, Umma tayi karaf ta amshe, ” eh wallahi tunda daga ni har ubanki babu wanda ya gaji sharifantaka amma ace shagon da yake ci da wuta kika shaga kuma kayan shago suka dawo yanda suke kamar ba abinda ya faru, anya ƙawaye basu saki cikin ƙungiyar asiri ba kuwa? ” dakatar da ita Abba yayi yace, ” koma dai meye mu barwa Allah lamuranmu banasan wani tone-tone Allah ya ƙare tsare mu aduk inda muke ” Umma da jikinta ya gama sanyi ta amsa da, ” Aameen ” Jabun Maryam na zaune jin Ƙarar saukar abu taji a saman kwano, wanda su Abba ma basu san anayi ba azabure ta tashi ganin irin tashin da tayi yasa Abba yace mata, ” lafiya ina zaki? ” bata juyo ba tace masa, ” Abba ina zuwa bari na leƙa waje ” bata jira cewar su ba ta fice, tana fita tsakar gida ta riƙiɗe ta ɓace daga gidan gaba ɗaya, Abba da ya biyo bayanta yana kira yana fita tsakar gida ya nemeta sama da ƙasa ya rasa, wannan karan ba ƙaramin tsoro ne ya kamashi ba cikin sanyin jiki ya dawo cikin gidan, Umma ce ta tare shi da tambayar Maryam jiki ba ƙwari yace, ” na dubata banganta ba har bayan gidan nan duk na duba ta bansan inda tayi ba ” cikin jimami Umma tace Malam yarinyar nan fa ta fara bani tsoro dama jiya bangaya maka bane wallahi ba damar nayiwa yarinyar nan faɗa sai inga wannan baƙin karen ya tasomun kamar zai cinye ni ” tsam Abba yayi yana naxari tunani yake sosai sannan yace, ” gaskiya indai haka ne akwai jinnu acikin lamarin nan dan bana ganin atarbiyyar da na bawa Maryam zata shiga wata ƙungiya amma zan ɗauki mataki ” ya ƙarasa maganar cikin damuwa.

         Jabun Maryam bata sauka ko ina ba sai asaman ƙwano inda taji saukar Marwan, yana ganinta afusace ya ɗaga hannu ya zabgeta da mari, agigice ta kalleshi tace, ” makasas kinsadu jikasuga bilkahi kalamusu? ” ( Mai nayi maka ka yanke mun wannan hukuncin? ) cikin ɓacin rai ya fara mata magana, ” kalbasu minraki ƙafasu gidigihkash minsaku wakalkalkinsa jakasuk minsaku kalbasu miaafus  minsatu kilasu bisakinsa fatusaku mansarutakaji ” dana turo ki gidan nan cewa nai ki take umarnina, cewa nai fa ki maye mun gurbinta, ke har kin isa inyi abu ki dakatar dashi ” ita ɗinma azafafe ta bashi amsa, ” kalmnau fisaku likasminsa bisaki hakzakis manaku tisabu katdartiska, lalamikasu hakafu kinsatu umaksi zaigatu ” ( naga kana shirin cutar dasu alhalin ba abinda sukayi maka sai ma kai da ka shiga rayuwarsu, ashirye nake na kare su daga duk wani kaidinka ” akausashe yace mata, ” guskahu jakigjamus? gahisdabu miskasgaafi wakis musbagu lafuskinabu warzikasu kinsatu kinbash hakazi Maryam misganbi kisaku ” ( haka kika ce? mu zuba nida ke ki zaune ki karesu zanga wanda zai kawo ɗauko musu ƴarsu Maryam ya dawo da ita ) cikin ƙarfin hali ta ce masa, ” misgakal wasgijik farsatu gisatu unbasgus harbaau ijakinfas dunkansbat burgat ” ( da taimakon Mahaifinta da kuma Addinsu da ƙarfin iko na zan dawo musu da ƴarsu har gida ) tana gama magana ta sauko ta dira acikin soron gidan  tana mamakin mugun hali irin na Yanzulak.

  Ba zato ko tsammani haka suka ga shigowar Maryam gaba ɗaya jikinsu asanyaye yake, lura da halin da suke ciki ne yasa ta wayance musu tana faɗin, ” Abba wallahi ɗazu abinda yasa kuka ga na fita da sauri Hauwa na bawa saƙonta dan kar ta tafi makaranta banbata ba ” da idanu duk suka bita har ta gama jawabinta sunjita ne badan sun yarda da abinda ta faɗa musu ba, Abba ne yayi ƙarfin hali yace, ” eh hakan da kikayi yayi dai-dai kam ” yana faɗar haka ya tashi ya wuce cen ɗaki Umma ma kamar wacce aka zabura da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, tana wayancewa da zatayi aiki bayan babu wani aiki da zatayi tunda Maryam duk ta gama mata komai, bayan fitarsu jabun Maryam nutsawa tayi kogin tunani tana neman mafitar da zata samowa kanta saboda tasan sarai waye Yanxulak da mugun halinsa, bayan wani lokaci Abba ne yayi wanka ya shirya ya fice daga gidan yayi gurin shagonsa.

          Maryam firgigit ta tashi daga ɓarawon baccin daya ɗauketa, ayanda ta lura gari har ya waye dube-dube ta hauyi tana neman inda zata samu ruwa tayi alwala, ganin Marwan baya cikin kogon dutsen yasa ta tai sauri da gudun gaske tana ƙoƙarin ficewa daga ciki, har ta fice sai ta hangi wani ɗan ƙaramin kogi acen gefenta alwala taje ta gabatar ta miƙe tsaye tana shirin guduwa sai gani tayi wasu tafka-tafkam zakuna sun ɓullo daga hanyar suna niyyar yowa kanta gadan-gadan, da gudun gaske ta juya cikin kogon dutsen tana maida numfashi, ta jima ahaka tana sauraron shigowarsu har bayan wani lokaci ba abinda taga ya shigo, aɗan tsoracen ta taka ta janyo zanim da aka rufe gadon dashi ta rufa tayi sallah asuba wacce tuni gari ya daɗe da wayewa, mafarkin da tayi dasu Abba ne ya ƙara faɗo mata, aykuwa lokaci ɗaya ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, duk wanda yaga halin da Maryam take awannan lokacim sai ya tausaya mata saboda yanda duk ta fige ta lalace ga rashin kwanciyar hankali.

     *BAYAN WASU KWANAKI*

        Duk yanda Abba yaso da komawa kan harkar kasuwancinsa abun yaci tura, tunda lamarin nan ya faru shikenan kowa ya ƙaurace masa babu mai zuwa shagon sa siyayya kai wasu ma ko magana yayi musu babu mai amsawa, idan masallaci yaje sallah babu wanda yake haɗa sahu dashi har sai da Abun yakai Abba bango yaje ya samu limamin unguwarsu ya sanar dashi halin da ake ciki, wata ranar juma’ar da tazo ne Mlm liman yayi wata zazzafar huɗuba akan hakan ta wannan hanyarce yasa aka daina ƙyamar Abba ake amsa gaisuwa ko sallamar sa amma har zuwa lokacin babu wanda ya koma shagon da sunan siyayya, nasiru na ganin sun fara faɗawa cikin wani yayi tuni yayiwa Abba sallama ya canja ubangida, Abba tashi tsaye yayi kullin gayawa Allah yakeyi ba dare ba rana ya miƙa lamuransa gurun ubangijin talikai, hakanan bai fasa sanya Maryam cikin addua’arsa ba yana kaiwa Allah kukansa akan ya zaɓa masa abinda yafi alheri tsakaninta da Marwan, da kuma baƙin halaye da ɗabi’un da ta sake, yake roƙon Allah da ya bayyana musu duk wani ƙullin ɓoye nata wanda basu sani ba.

        Bahaushe yace zara bata barin dami yau da gobe duk ƴan kuɗaden dake hannun Abba sun ƙare danma basu da matsalar kayan abinci tunda na shago yake debowa suna amfani dashi, sai dai ɗan kuɗin cefen abubuwan da baza’a rasa ba, yau ma tashi sukayi ba kudin kalanzir da ɗan kayan miyar da zasu siya ga kuɗin hannun Abba duk sun ƙare, Umma ce ta tuno da kuɗin adashinta na gidan Maman baby da sauri ta kira Hafsa tace mata, ” jeki gidan Maman baby kice mata dan Allah wata matsala ta ɗan taso mun, tayi hakuri ta bani kuɗin nan inyaso wadanda banyiwa zubi ba basai sunyi mun ba ” ba musu Hafsa ta tafi gidan Maman baby bayan wani lokaci sai ga Hafsa ta dawo tace wa Umma, ” wai tace bazata bayar ba, wai da kinsan da matsalar kika shiga adashin ” aykuwa lokaci ɗaya Umma taje wuya ta dinga faɗa ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Maryam dake gefe ce ta kalleta tace, ” Umma bari naje ni ko inta ganni zata bani ” Umma bata hana Maryam zuwa ba saboda tana maruƙar buƙatar kudin ahannunta, Maryam tafiya tayi gidan Maman baby atsakar gida ta sameta tana ninke kaya, ganin Maryam tayi ko sallama babu, tana shirin yin masifa ta tuno da abinda ya faru da ita abaya, ko uffan Maryam batace mata ba ta wuce har uwar ɗakin Maman baby taje ta buɗe drower ta, jakar kuɗin adashin ta ɗauko sai da taxo tsakar gida sannan ta ciro kuɗin jakar ta irgi iya na Umma sauran kuma ta ajiyewa Maman baby abinta ta sa kai ta fice, ilahirin jikin maman baby rawa yake atunaninta ma yanzu Maryam zata ƙara wucewa ta bango sai kuma taga saɓanin haka.

          Jabun Maryam duk yanda tayi ta gano gurin da Marwan ya ajiye Maryam ta gagara samu duk iya bincikenta da hangenta abun ya faskara, haka nan tun daga ranar da ta shiga shagon Abba take taka tsantsan yin abunda zasu kuma zarginta akan wani abun dukda dai yanda ta lura har wannan lokacin Abba da Umma basu gama sakin jiki da ita ba saɓanin su Hafsa da babu alamar ko ɗar atattare dasu, duk binciken da takeyi akan Maryam ta kanyi shi ne da daddare dan gudun kar suga tana yawan fita nan ma su zargeta, tana fita idan kowa yayi bacci wajen shabiyun dare sai ta dawo gabda asuba ta yanda babu wanda zai gane ta.

          Wata rana da daddare kamar kullin jabun Maryam taji gidan yayi tsit da alama sunyi bacci, sai dai abinda bata sani ba Abba na daga jikin window abun duniya ya isheshi na matsin rayuwa ya kasa bacci, shiyasa yaje bakin window ya tsaya yake tunani, tsakar gidan fes yake da hasken nepa motsi yaji na fitowar Maryam atunaninsa ko fitsari zatayi amma ga mamakinsa sai gani yayi tabi ta kusurwar bangon  banɗaki ta wuce, tsoro haɗe da mamaki ne ya kama Abba afili yake furta, ” innalillahiwa’inna’ilahirraji’un ” Abba kamar mutum mutumi haka ya daskare agurin, da har zai tashi Umma ya sanar mata sai kuma ya tuno da kwarorotanta ya hakura, da addu’a ɗauke abakinsa ya fito tsakar gidan a hankali ya leƙa ɗakinsu Maryam, wayam ya gani agun kwanciyar Maryam sai Hafsa da take ta sharar baccinta, fitowa yayi daga ɗakin sannan ya ɗaura alwala daddauma ya shimfiɗa ya gabatar da sallolin nafilarsa yana kaiwa Allah kukansa da godiyarsa ga ubangiji bisa bayyana masa wannan abun da ya gani game da Maryam, bacci nasan ɗaukan sa amma Abba yaƙi dan yaci alwashin sai yaga dawowarta, adaddafe Abba yakai ƙarfe huɗun asuba yana nan tsaye wajen window sai gani yayi Maryam ta kuma fasowa daga jikin bango wannan karan kanta ne kawai na mutum jikinta kuma irin na shaho ne, girziga tayi a tsakar gidan nan da nan ta rikiɗa ta koma sak Maryam bata lura da Abba ba hakan ne yasa tayi shigewarta ɗaki.

              Bayan sallah asuba kamar yanda Abba ya saba haka ya leƙa ya tashe su sallah atare kuwa suka fito alwala, da ido yake bin Maryam amma zuciyar wasi-wasi take akanta haɗe da tsoronta, da safe bayan su Hafsa sun tafi makaranta Umma na gefen kujera azaune sai Abba dake kan kujera, Maryam ya ƙwalawa kira cikin nutsuwa ta shigo ɗakin ta zauna a ƙasa tana sauraron Abba, kallan tsaf yayi mata fuskarsa ba alamun wasa ya fara magana, ” Maryamu ki dubi Allah da girman sa, ki dubi irin tarbiyyar da muka baki tun kina ƙarama, ki dubi ɗawainiyar da mahaifiyarki take miki tun kina ciki har haihuwa ki gayamana gaskiyar lamari, sannan ki sani idan kin ɓoye mana wani abu bazaki ɓoyewa Ubangijinmu ba, muda ke zamu mutu mu tadda Allah kuma tsakanin Akwai hisabi idan mumuka cutar dake sai Allah yabi miki haƙƙinki haka nan idan kece kika cutar damu ” jikin jabun Maryam ne ya gama sanyi kallan Abba tayi tace, ” nayi alƙawari zan sanar muku duk abinda zaku tambayeni ” jinjina kai Abba yayi yace, ” Maryam azahiri ke Maryamuna ce amma a baɗini ba ita bace, ina kika kai mun Maryamuna kuma maiyasa kika shigo cikin rayuwar mu, ina kika kaimun ƴata wacce duk cikin ƴaƴana nafiji da ƙaunarta azuciyata? ” Abba ya ƙarasa maganar idansa na zubda ƙwallah, gyara zama jabun Maryam tayi tace, ” Tabbas ni ba Maryam ɗinku bace hasalima ni ba jinsinku bace ni aljana ce sunana na ainihi Falzuƙa………………. “*ASALIN TARIHIN SU MARYAM*

        Umar Muhammad Sani PRP shi ne aynihin cikakken sunan Abba asalinsa ɗan garin Kano ne a unguwar Kwanar jaba dake ƙarƙashin Nasarawa local govnment, mahaifinsa mai suna Muhammad Sani yanada mata biyu da yara ƴaƴa goma, matarsa uwar gida sunanta Harira tana da yara shida Fatima, Zainab,Musa, Idirs,Ibrahim da Lawan, sai matar sa ta biyu Mai suna Zainabu tana da yara huɗu Umar wato Abba shi ne babba sai Yahaya,Maimuna da Jamilu, Mahaifnsu ɗan kasuwar kofar wanbai ne,  ya bawa yaransa tarbiyya ta dai-dai gwargwado, yaransa gaba ɗaya sai da suka sauke alƙur’ani mai girma daga maza har matansu, yaransa mata basa karatun boko mai zurfi iyakarsu primary, haka suma mazan basa wani karatu cen mai zurfi  suna kammala secondary yake dakatar dasu ya maidasu kan harkar kasuwancinsa, Mahaifinsu Abba yana da rufin asiri dai-dai misali shi ba mai kuɗi ba kuma bazaka kirashi talaka ba, yaransa gaba ɗaya shi yake zaɓa masu matan da zasu aura su kuma matan ya zaɓa musu mazan da zasu aura, yana dubawa acikin ƴaƴan abokansa ko yaransa da suke karƙashinsa ya nemarwa wanda yaga yakai munzalin aure ko takai minzalin aure, cikin biyayya suke amincewa suyi aurensu kuma su zauna cikin kwanciyar hankali, sai dai Abba shi kaɗai shi ya fita zakka acikinsu saboda shi ne kaɗai wanda ya nemo tashi matar ya kawowa mahaifinsa wanda shi kuma tuni yayi wa wani abokinsa magana zasu haɗa Abba da ƴar abokin nasa, Mahaifin su Abba yaji haushin abinda Abba yayi kuma da farko ƙin amincewa yayi sai da sa bakin Manyan abokansa sannan ya amince amma har akayi auran bada san ranshi akayi ba.+

         Mahaifiyar Abba ta rasu tun suna ƙanana yayinda ruƙonsu ya koma gurin matar ubansu kuma ta riƙesu da Amana kamar ƴaƴan da ta haifesu na cikinta, haka zalika gaba ɗaya sun taso kansu a haɗe gwanin sha’awa babu maijin kansu, Mahaifinsu ya rasu yana da shekara casa’in da biyu aduniya lokacin yana da ƴaƴa tara da jikoki hamsin da biyar alokacin Abba nada ƴaƴa biyu aduniya, bayan rasuwarsa da shekara guda sai harkar kasuwancin su ta fara durƙushewa ƙasa ganin haka yasa akayi musu rabon gado kowa aka bashi haƙƙinsa.

          *wannan kenan*🤓

            Salamatu ma’aruf mai Shanu shi ne ainihin cikakken sunan Umma, asalinta yar ƙauyen doguwa ce ɗaya daga cikin ƙauyikan kano, Mahaifinta Mlm Ma’aruf mai shanu bafulatanin ƙauyen doguwa ne matarsa ɗaya mai suna Luba tana da ƴaƴa biyar, Rahane, Audu, Mudansiru, Salamatu sai autarta safare, Mahaifin Umma mutum ne mai matuƙar san abin duniya gashi mafaɗacin gaske, hakan ne yasa tun su Umma na yara yake tasasu gaba da ƙwaryar nono su tafi tallah shi kuma ya wuce kiwon shanunsa, idan yamma tayi sun daidaici ya kusa komawa gida suma sai su tarkata su koma cen bakin kasuwa, cen ne mararrabar da suke rabuwa da shi haka idan gida zasu koma cen ne zasu haɗu yasasu gaba su koma gida, Mahaifiyar su Umma macece da ba sawa ba fitarwa sai dai Allah yayita da san yaran ta su sami ilimin addini dana boko koda kuwa iya primary ne, acewarta tunda su basu samu sunyi na addinin mai zurfi ba yaransu su samu  su suyi, idan da so samu ma su haɗa harda na bokon musamman da rayuwa ta zama ana damawa da boko cikin harkokin yau da kullin, duk cinikin nonon da su Umma zasu yi suna dawowa gida Baffansu zai sasu gaba ya amshe kuɗaɗen, idan yaga cinikin ma bamai yawa bane har cajesu yake yana lalubesu idan kuwa bai samu komai a jikinsu ba haka zai sasu gaba yayi ta faɗa kamar zai cinye su ɗanye, duk wannan uwar dukiyar da yake da ita bai cika wadata su ba hasalima goggonsu ita take faɗi tashin akan waɗansu abubuwan nasu take yi musu, saboda tana tambayarsa abu zai rufeta da faɗa ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, ko kaɗan baffansu bai damu da suyi ilimi ba shidai burinsa su fita talla su kawo masa kuɗi, babu yanda goggonsu batayi dashi ba ya sasu makarantar islamiya ba amma fir ya ƙeƙashe ƙasa ya ƙi, sai ita ce ma ta sasu makarantar dare to anan ne ma suka samu suka ɗan san wasu abubuwan game da addini.

         Su Umma tun suna tallan nono anan cikin ƴan ƙauyikansu har ta kai ga Baffa ya fara turasu cikin gari, lokacin da kuwa suka zama ƴan mata da samari sai yasa mazan suka fara zuwa kiwo shi kuma yana gida abinsa idan kuma lokacin damuna ne suna gona sai shi ya tafi kiwon, su kuma su Umma sai su fito cikin garin birnin Kano sune kai nono da man shanu har cikin kasuwannin Kano, sai yamma likis sai su tafi tasha ayarinsu guda ƴanmata kowacce da kwaryar ta suke cika bus su tafi garinsu.

            Yau da gobe su Umma na kai fura da nono kasuwar wambai suka fara sabo da Abba daga haka har soyayya mai ƙarfin gaske ta ƙullu a tsakani su, Umma kyakykyawar gaske ce fara ce sol doguwa ga gashi babu mutumin da zai ganta ya kushe halittarta sai dai babbar matsalarta sakaci da addini, sam bata damu da addini ba dan wani lokacinmu tun sallar asuba bazata kuma yin wata sallar ba sai sun koma daga tallar fura da nono zata fara jero su daga azahar zuwa isha’i saɓanin ƴan uwanta da inlokacin sallah yayi suke yin kayarsu, danma Goggo na tsawa kai da fata akan Umma shiyasa ma take shakkar yin wasu abubuwan, Umma itace ta ɗebo sak halin Mahaifinsu ganin haka ne yasa Goggo ta ƙara tashi tsaye akan umma saboda ita macece da bata damu da abin duniya ba.

        Abba yasha fama sosai kafin ya samu yardar mahaifinsa akan auren Umma amma da yake Allah yayi matarsa ce haka ya amince manya suka shiga cikin maganar har aka tsaida lokacin aure, lokacin na zuwa aka sha biki Amarya da Ango suka tare.      Lokacin da akayi auren Abba da umma da farko a unguwar PRP suka tare sai daga baya Abba ya fara tafiye-tafiye xuwa garuruwa daban-daban yana sarar kaya yana kaiwa idan xai dawo ya saro kaya ya dawo dasu anan gidan iyayensa yake barin Umma tayi zamanta ita da sauran facalolinta, da farko zamsu gwanin sha’awa sai daga baya kuma matsaloli suka fara  ɓullowa tsakanin su da Umma abun yakai su harda dasu dambe, ganin haka ne yasa Abba ya fara tafiya da Umma  saboda gudun abunda zaije yazo, tun farkon aurensu Abba ya fara cin karo waɗannan ɗabi’un nata na biris da harkokin addini da azkar, yayi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya musanya mata halayenta amma ina wanda yayi nisa baya jin kira.+

          Saida suka shafe shekara takwas da aure Umma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba tun abun baya damunsu har ya fara damunsu, nan fa facalolinfa suka samu na habaici saboda yanda take hura musu hanci ita adole mijinta yafi nasu samu, wannan abun da take musu yasa suka sa ta gaba ba damar su haɗu zasu fara zubar mata da ruwan habaici, danma Abba na kwantar mata da hankali yasa damuwar tata tayi sauƙi.

            Cikin ikon Allah ashekararsu ta tara da aure Allah ya bawa Umma ciki murna gurinta baya musaltuwa, bayan wata tara Allah ya sauketa lafiya ta haifo ɗiyarta mace mai kama da ita ranar suna aka sa mata suna Maryam, Maryam sai da ta shekara uku sannan Umma ta haifi Mustafa, mustafa nada shekara uku da rabi ta haifi Ibrahim shi kuma yana da shekara biyu shima ta haifi hafsa, ganin sun fara tara iyali yasa Abba yasai gidansa a unguwar zangon dakata Umma ta dawo kano da zama shi kuma Abba na ƴan tafiye-tafiyensa bayan wani lokaci yana zuwa ganinsu, wannan shi ne silar sakankancewar tarbiyyar su Maryam sam Umma bata damu da tata ibadar ba ma bare ta sanya nata yaran suyi, dama Abba ne yake matsa mata kuma basa kusa bare ya dinga tilasta mata, duk abinda ya zama haƙƙinsu ne akanshi ya na musu dai-dai iya ƙarfinsa, amma duk da haka Umma sai tayi yanda tayi ta ajiye wasu kuɗaɗen daga cikin kuɗin da yake turo musu, hatta makarantu Umma masu sauƙi-sauƙi ta sasu amma agurin Abba tana karɓar kuɗaɗe masu yawan gaske, wata dawowa da Abba zaiyi ya taho da kuɗaɗensa masu yawan gaske ahanya ɓarayi suka taresu sukayi musu fashi suka karɓe kuɗin gurinsa, wannan shi ne silar dawowar Abba kano da sana’arsa, da sauran ƴan kuɗaɗen sa ya buɗe shagon provision sannu ahankali har Allah yasa masa albarka, tun shagon na ɗan ƙarami har ya haɗe da wani na kusa dashi aka fashe masa ta ciki ya zama babban kanti dan masu ƙananan traders har sari suke agurinsa.

        Shekarar Maryam sha bakwai suka haɗu da Marwan tana da shekara goma sha Tara tayi Candy bayan Candy ɗinta da watanni Marwan ya turo Iyayensa suka kawo kuɗin aurensa gurin Yayyan Abba akayi gaisuwar Manya cikin mutumci da niyyar idan ankwana biyu zasu zo asa ranar aure.

     

       _*BACT TO LABARI*_💃🏼

           Azabure Umma ta tashi ta faɗa kan Abba tana ƙwaƙumeshi cikin firgici da tashin hankali ta fara faɗin, ” Malam yau mun shiga uku Aljanu har cikin gidanmu, wallahi ni dama tun sanda kace ta faɗa shagon gobara na fara ɗari-ɗari da ita ashe ba Maryam ɗina bace kuma…. ” cikin jarumta da ƙarfin halin Abba yace wa Umma, ” meye haka kike yi ki nutsu mana tayi mana bayani dallah-dallah so nake naji dalilin zuwanta da inda Maryamu na take? ” Umma luf tayi har lokacin jikinta rawa yake kuma taƙi sakin Abba ko kanta taƙi yarda ta ɗago dashi bare su haɗa ido da jabun Maryam, cikin tausayawa jabun Maryam ta cigaba da magana, ” Abba karku zargeni domin kuwa ni kaina aynxu bansan inda Maryam ɗinku take ba, sai dai nasan wanda ya ɗauke muku ita kuma shi ne ya turo ni gurinku saboda inmaye gurbinta, na tabbata zakuyi mamakin jin sunan wanda xan gaya muku amma inasan ku nutsu da kyau saboda yana da matuƙar hatsari, zancen nan da nake muku ni kaina rayuwata tana cikin hatsari saboda nasan wayeshi nasan halinsa sarai Yanzulak bashi da imani ” azabure Abba yace, ” waye kuma Yanzulak ni ko sunansa bantaɓa ji Maryamu ta gayamun ba kuma wallahi bata da abokin faɗa bawai dan tana ƴa ta ba ” girgiza kai tayi tace, ” ba kowa bane fa ce Marwan da yake neman auren ƴarka Maryam, Marwan ba mutum bane Aljani ne sai dai acikin jinsinmu yana da babban Matsayi, shi ɗan sarki ne kuma ɗa ɗaya tilo agurinsa yana gabda zama sarki dan mahaifinsa yace bada jimawa ba zaiyi murabus ya bashi gadon mulki ” ba Abba hatta Umma sakin Abba tayi azubure suka zuba mata idanu suna watso mata da tambaya, ” Marwan ne aljanin? ” murmushin takaici tayi sannan tace, ” ku kuka sanshi da Marwan amma mu da Yanzulak muka sanshi, tabbas ba bil adam bane kamar yanda yaxo muku naji ya sanar a fada ma wai Maryam na ɗauke da cikinsa kusan wata bakwai iya abinda na sani kenan kuma shi na sanar muku mafita itace mu taru nida ku mu nemi hanyar da zamu dawo da Maryam cikin ku, alƙawari na ɗaukarwa kaina zan taimakeku karkuji tsorona bazan cutar daku ba, ku yarda dani da zan cutar daku  da tuni nayi abinda zanyi na cutar daku, Marwan ya sanar dani cewar kaine zaka bashi matsala shiyasa yaxo ta mafarki dan ya halakaka amma ka ƙona shi da Addu’ar ka da kukeyi acikin addininku, dan haka inasan ka koya mun addu’arku ita kaɗai ce zata iya kuɓuto da Maryam daga inda take ” gumi haɗe da faɗuwar gaba ne ke sauka ta ko’ina daga jikin Abba jiki ba ƙwari yace, ” tabbas Annabi yayi gaskiya, amma fa ita wannan Addua tamu bata taɓa amfanuwa ga maiyinta sai ya ɗayanta Allah ɗaya ya yarda da Annabi Muhammad sallallahu alaihiwasallam, idan kina da burin musulunta zan musuluntar dake kuma abinda nake so dake karki musulunta saboda ceton Maryam ki musulunta saboda Allah da Manzansa ” cikin ƙwarin gwiwa jabun Maryam tace, ” ashirye nake  na karɓi addininku saboda Allanku” Cikin jindaɗi Abba ya fara karanto mata kalmar shahada tana maimaitawa har ya kai ƙarshe, daga ƙarshe ya tambayeta sunan da take so, murmushi tayi tace, ” Abba inasan sunan Maryam ku cigaba da kirana da sunan yana mun daɗi…. ” bata rufe baki ba sukaji gaba ɗaya gidan ya ɗauki wata irin girgiza anfara tambal-tambal dasu cikin firgici Sabuwar Maryam tace, ” Yanzukal yaxo wallahi shi ne “.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *