MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 14
amma ya ya ta iya da ranta? Ko domin ta ga ta haihu a dakin mijinta cikin rufIn Asiri ta yadda ta amince.
Washegari waJEN karfe biyar na yamma jirginsu ya daga, Falmata na ta zabga kuka a ranta tana jin kamar kurkuku za a kai ta, domin a yanzu ta gano Mukhtar bai sonta, ‘yan‘ . uwansa ne suka zo daukarta. Hajiya Mariya kam tana can tana shirin saukar surukarta. .
Jirginsu bai yi awa guda da tashi ba na Mukhtar ya sauka a garin, domin tunda garin Allah ya waye yau ya ji kamar an cire masa wani kulli daga zuciyarsa, Falmata kawai yake son gani, kai tsaye gidansu ya yi masauki.
Ya yi sa’a kuwa malam Abba-gana yana gida, don haka kai tsaye falonsa aka yi masa masauki, ya tadda shi a zaune akan kujera yana duba wani littafin addini, ya shiga da sallama kansa yana Kasa. Ya karasa kuSa da shi ya zauna akan kafet.
Fuskar Malam din ta fadada da fara’a, ya ajiye littafin yana fadin, “Lale marhabin da angon Falmata”.
Kunya ta kuma kama shi, ji yake kamar kaga ta tsage ya shige don kunya. A haka ya gaida malam din, ya amsa yana tsokanarshi .daga nan ya yi shiru yana raba ido ta ina ya . dace ya fara, yana son tambayar Falmata da abin dake cikinta, amma ta yaya? Kula da hakan da Malam din ya yi ya sanya yace. “Garin yaya ka bari jirgin nasu ya tashi baku tafi tare ba, ko makara ka yi ne?” Ya kalli malam din da rashin fahimta, da kyar yace, “Tafiya suka yi ke nan Malam?” Abinda malam yake son ji kenan don haka yace “Ai na yi zaton kasan da maganar tariyar Falmatan, da Hajiyarka ta turo aka d‘auke ta? Ai ina jin yanzu ma sun isa Kano ‘ ma . Ya Hayyu Ya Kayyum. ya ambata kafin
ya iy‘a cewa, “Hajiya ba ta sanar dani ba, daman ni ma zuwa na yi na tafi da su, hakan yayi kyau, sai dai ina kara neman‘ afuwark‘ malam. A yi hakuri don Allah akasi ne aka samu”.
Malam ya yi dariya yana fadin, “Kada ka damn Mukhtari, kai dai ka dinga yawaita yin
addu’a da neman tsari a duk wasu lamuranka na
rayuwa, amma mu ba ka yi mana wani laifi ba,
Allah Ya yi muku albarka, Ya ba ku zuri’a ta gari. Zaka koma yau din ne k0 sai gobe?
“Ai yau ya dace na koma, don kada a kaita ita daya, kuma komawar tawa ce zata zama ban hakuri ga Hajiyar tawa. Zan je na duba k0 zan sami jirgi idan bazan samu ba zan bi mota”. . ‘
Da haka suka yi sallama, malam Abba gana yana ta yi masa addu’a da nasiha. Shi kam wani irin dadi yake ji a ransa na son ganin Falmata da bebinsa a cikinta k0 yaya, ta koma yanzu? Yanayin yanda yake ta doki ya bai wa malam din mamaki, koda yake ba a ja da ikon Allah, kuma Shi ne Ya cc a rake Shi zai amsa, don’haka malam ya roke Shi da kyakkyawar niyya-, ga shi kuma Ya amsa masa, ya kawar da duk wani’ surkulle’ da binne-binnen su Fatila da su Yakolo
Su Hajja Yakolo kam kamar za su mutu d‘omin abin biyu ya hade musu, ga karyewar aikin d‘a suka yi, sannan ga hana su ‘zuwa ganin kwaf da aka yi, domin malam din yace babu
inda za a je dasu. Wannan abu ya yi musu ciwo, sai kuma ga wani karin abin takaicin domin a daren Yakura ta dako yaji don ‘ya’yan gidan sun mata duka ga laulayi da take fama da~ shi, wannan shi ne takaici goma da ashirin.
FALMATA A KANO
Falmata ta dawo Kano karo na biyu da cikar burin auren masoyinta Mukhtar, sai dai ba ta sani ba k0 zata sami cikar burinta ko a’a. Wannan kam shi keba ta tsoro, sai dai ta tadda soyayya a gurin uwar mijinta da sauran ‘yan uwansa, wannan ya dan wanke mata zuciya, haka nan aka shiga ina aka saka da su. Hajiya Mariya bakinta kamar gonar auduga, sai da aka dinga tambayar Falmata abin da ta ke son,ta.ci ma, hakan ya dinga bata kunya, domin alama ce da sun sami labarin tana da juna biyu.
Washegari tunda safe ‘yan rakiyarta suka je suka gano gidan nata, daga nan aka yi musu jagora gun da ake sayar da kaya na garari, Chedi suka nufa suka dandatsawa Falmata kayan daki, tabbas an kawata gidan kamar diyar Wani Sarki.
Da sassafe Dr. Mukhtar ya iso gidan cikin hadaddiyar kuma dakakkiyar Ghalila sai wani kyalli yake yi.
‘ Hajiyarsa tana falo suna kallo da sauran ‘ya’yan gidan ya shiga da sallama, duk da ta ji dadin zuwan nasa sai ta basar ta kawar da kanta ‘ gefe da kyar ta iya amSa sallamar ma. Ya isa ya zauna kusa da ita yana gaisheta. Da jyar ta iya . amsawa tana wani share shi, hakan ya qara fadar masa da gaba da kyar ya daure ya fara magana. ‘ ‘
“Ki yi hakuri mun sami saBani ne, domin sanda na isa mu taho da Falmata na tadda sun taho… , “Kada ka raina min hankali, kana nufin karya Zaka yi min? To tsaya ka ji na gaya maka, ban dauko Falmata don ta tare a gidanka , ba nan zata yi’zamanta har sanda Allah zai sauke ta lafiya ka sauwake mata aurenka ta auri mai sonta, kuma a cikin gidan nan”.
‘ Hankalinsa ya tashi da sauri yace, “Subhanallahi, don Allah ki yi hakuri, wallahi ki tambayi malam Abba ki ji, a hanya na kwana ma, nasan nayi laifi amma don Allah a yi mini afuwa”.
‘ Ya marairaice murya yana ta bata hakuri, .abin da yake kwararta kenan, dashi da zarar yaga ta yi fushi zai kwantar da kai ya yi ta bada hakuri kamar zai mata sujjada. Da kyar ta ce, “Komai ya wuce”.
Ya yi zaune burinsa tace ya shiga ya ga
Falmatan, amma kememe ta qiya, domin tasan abin da yake so kenan. Ya dinga satar kallon kofar dakin baccinta k0 zai yi katari ta leko amma shiru, har Hajiya Mariya ta gaji da zaman nasa ta ce. “Kazo ka wani sanya ni a gaba,. ka tashi ka bani guri, domin yanzu bakina zasu dawo. daga kasuwa, kuma bana son binbini idan lokacin da ya dace na neme ka ya yi zankira wayarka”.
Kamar ya fasa ihu jin abin da tace tabbas an yi niyyar gasa shi kenan, ga shi daga jiya zuwa yau wata irin kaunar Falmata ke yawo a ransa kamar zai fasa zuciyarrsa ta
Sullo. Ya miqe salo-salo ya nufi kofa gwiwarsa duk tayi sanyi ‘ yaji mahaifiyar tashi ba fadin
“Saura kuma ka je ka gayawa ‘yar mulkin naka an kawo Falmata, ka bari sai ta tare tukunna”.
Da sauri ya juyo yace “Insha Allahu ba zan sanar da ita ba Hajiya”.
Ya fice jiki sanyi kalau, yana waige.
‘ Falmata kenabn duk abin da ya faru akan . idonta,akai domin tunda ta jiyo sallamarsa ta gane muryarsa ta taso da sauri ta laBe jikin labule.. Tabbas ta so ace Hajiyar ta Kyale shi k0 ‘gaisaWa ne su yi, haka nan ta koma cikin dakin sumi-sumi ta zauna, maganar Hajiyar na mata . yawo a kunne, wai dole anan zata zauna, idan ta . haihu a raba auren a aura mata wani. Shin sun , san’ irin n son da take yiwa Mukhtar kuwa? Ita kam ta amince a kyale ta da mijinta ko yaya ne tunda yana sonta, zata yi ta masa addu’a Allah ,Yajuyo mata da hankalinsa kanta. Washegari tunda safe ‘suka yi haramar ‘ komawa, sun so tun a daren su kai Falmata dakinta, sai dai Hajiya tace su kyale ta akwai , wani gyara da zata yi mata, inyaso daga baya ‘ ‘yan uwa na nan sa kai ta.
Sanda suke shirinsu gaba daya hankalin Falmata ya tashi, gani’ ta ke kamar idan suka tafi ba zata kara ganinsu ba. Rarrashin da Hajiya Mariya ke mata ne ya sanya ta yi kokarin Boye damuwarta, amma zuciyarta cike ta ke da tashin hankali matuka, tana ji tana gani suka tafi, sai a sannan kuka yazo mata.
** ** **
Kwanakinta uku a gidan nan duk wani jin dadi da kulawa tana samunsa daga gurin . Hajiya, kullum sai an tsare ta an bata ruwan rubutu ta sha da wasu turaruka da aka yi mata addu’o’i na karya sammu. Ita da kanta tana jin dadin jikinta matuka, don ma dai sunkayi ya sanyata a gaba kullum sai an yi mata wani abu na kwadai. Hajiyar takan tsare‘ta da tambayar abin da ta keso a dafa mata, kunya ‘ba ta barinta ta iya fada.
Shi kam Dr. Mukhtar ya gamu da sintiri, kafin ya wuce ofls sai ya biyo, bayan ya dawo ma sai ya biyo. Mahaiflyarshi kam ranta yana yin sanyi da hakan, domin dai rabon da ta more ganin danta irin wannan akai-akai tun kafin ya
auri Fatila, amma taKi nuna masa yanda ta keji din. Sai dai ma ta dinga share shi tana dauke kai, ga shi taKi yadda ya ga Falmata, shi rashin ganin nata ne yafi daga masa hankali, ga. shi kullum sonta karuwa yake yi a cikin ransa, domin kullum ana kuma karya wasu sammukan ne na jikinsa. Idan yazi sai ya shantake ya yi ta hira yana kame-kame, duk wanda ke gidan kam abin ya zame masa bako.
Sai dai a Bangaren Fatila duk hankalinta ya tashi ganin mijin nata yana yin dare a waje, tun tana binshi da kissa har abin ya kai ta bango, domin yau dai ya kai kusan goma da rabi‘ na dare sannan ya shi’go gidan. Ta yi kwalliya har ta gaji ta tuge domin sai tsaki ta ke ja, tana jiyo horn dinshi ta Kara hade rai kamar ta ji sakon mutuwa. Ya shigo‘ da sallama maimakon ta amsa sai wata uwar harara data wurga masa kamar idonta zai fadi. Sarai ya kula da abin da ta yi din amma sai ya share ta ya wuce yana fadin.
“Madam har yanzu ba ki yi bacci ba kenan?”
Bai jira ta ba shi amsa ba ya wuce sashinsa. Ta mike da sauri’ ta bi bayansa ta tadda shi yana Balle botiran hannun riga. Ta tsaya a kansa kerere kamar zata rufe shi da duka tace
“Wai Mukhtar me kake nufi ne dani, iye?”
Ya daga kai ya kalleta sarai yasan abin da take nufi, amma sai ya basar yace, “Yanzu na dawo babu wani sannu da zuwa balle ki dan kawo min ruwa na sha, kin tsare ni da masifa kamar wani danki. Shin haka ya dace ki tarbe ni?”
Ta kuma hasala cike da mamakin maganarsa tace Ka ga bana son rainin wayo, wai daga ina kake ne ma a wannan daren?”
Ya kalle ta kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya dake ya ce, “Kin damu kanki bayan na gaya miki aiki ke tsare ni a OfiS, idan na tashi kuma nake wucewa can babban gida, shin kina tunanin zan iya zuwa wani guri na jima haka ne Fatila?” ‘
Maimakon ta sauko sai ta kuma hawa. domin idan akwai abin da ta tsana bai wuce yace ya je gidansu ba, don yawan kulafucin gidan nashi shike karya mata duk wani shirinta, domin mahaiflyarsa ta dinga ba shi ruwan “addu’o’i na karya sammu kenan har ta lalata mata aikinta. ,
. A hasale tace, “Wannan bai dace ba, ta yaya zaka ajiye ni a gida ka dinga wani tafiya -‘ gidanku, idan haka ne ni ma ai muna da gidan ko? Gaskiya ba zan dinga yadda da wannan , rashin adalcin ba, ace ka fita tun safe sai dare zaka shigo mini, wannan cuta ce karara”.
_ Mitar tata ta ishe shi, domin babu abin da ‘ yake‘so illa ya watsa ruwa ya kwanta ya yi ‘ tunanin Falmata da bebinsa don haka cikin tsawa yace mata.~ _ .
“‘Don Allah ki kyale ni na huta Fatila, -idan ba haka ba wallahi zan fice na bar miki gidan‘ na tafi can gidanmu na kwana. Haba mace sai shegiyar mita kamar. makauniya?”
Jin’ haka ya sanya ta yin shiry, domin tasan -zai iya tafiya din, don idan ya birkice mata irin haka tabbas aikinta ya fara girgidi kenan, don haka dole taja bakinta ta yi shiru, amma zuciyana tana tukuki, tsoronta d‘aya ma
kada yarinyar nan da suka aura masa ta dwo ransa tunda har yau bai sanar da ita ya saketa ba, ita kuma ba ta son ta yi masa maganarta, don kada ta tsokanowa kanta abin ‘dazai hanata bacci, haka nan ta hakura ta Kyale shi da zummar gobe ta nemi Diyana su san yaya zasu Bullowa abin.
Kwanaki bakwai cur ya gama iyakacin kaguwa, son Falmata ya cika ransa ya tunbatsa rashin ganinta ya zame masa wani miki da ke cin ransa ga rigima kullum shi da Fatila, har C.I.D ta sanya a gano mata inda yake yin dare aka tabbatar mata da gidansu yake tafiya, ga shi kullum aikin ake yi ‘mata amma a banza kamar an shuka dusa abin duk ya cakare mata.
Yau kam hakurinshi ya kai karshe, matarshi yake bukatar gani, ya kuma tabbatar dole yau ya roqi a bashi ikon koda ganinta ne, daga ofls sai da ya koma gida ya yi wanka sanda zai fita rikici suk yi sosai da Fatila tana tabbatar masa da yana fita zata fita ita ma don ta gaji. _ Ya watsa mata wata harara yace, “Ida‘n kin fita ba da izinina ba ai kin san mala’iku tsine miki zasu yi k0? Ki yi duk abin da kike so, amma hakan ba zai hanani zuwa gurin mahaiflyata ba”.
Ta kulu matuqa, sai dai kafln ta kai ga cewa wani abu ya wuce da sauri ya barta a nan. Ta yi shiru cike da takaici kamar ta bishi sai ta fasa, ba wai don tsoron tsinuwar Mala’iku ba, a’a sai don tana son jin abin da Diyana zata ba ta shawara akai. Ta janyo wayarta ta fara neman layin Diyana din.
Ta daga tana dariya tana fadin”‘Mukhtar din ne k0? Kai Fatila kina tare da wahala, namiji daya tal yayi ta kodaki haka ba ki yin sati cikin kwanciyar hankali fa, to wai ki yada kwallon mangwaro mana k0 Kudaje sa daina binki.
Kamar ta kurmawa Diyana ashar, amma
ta dake dai a fusace tace “Ai kin fi kowa sanin yanda nake son Mukhtar k0? Kuma kin san shi din ya bambanta da sauran maza, ko ke kanki kina yaba shi da komai nasa, shin kina tunanin zan iya rabuwa da shi na zauna lafiya ne? Son Mukhtar ya zame min bala’i da shi na rayu a zuciyata shi ne ma ya sanya ni kasa kallon koWane‘ namiji da gashin arziki, don haka neman mafita kawai zaki taya ni, tunda wancan Bataccen bokan ya debar mini wasu kwanaki da nake ganin kamar numfashina ba . zai iya riskarsu ba saboda nisa”. ‘ ’°’ Diyana ‘ta fashe da dariya, tana fadin, “‘Sheg‘en kishinki ne ya yi Yawa Fatila, amma ai kin san dai duk sintirin da Mukhtar yake yi . ‘ gidansu bai isa ya auri uwar tasa ba ko kuma ita ‘ duk wani asiri da aka ce tana yi nata janye hankalinsa kanki ba ta isa su kwanta gado guda ba k0? Ki kwantar da hankalinki kiga iyakacin ‘ gudun ruwansa mana, ‘tunda dai boka ya tabbatar miki da har abada bai isa ya kalli wata mace da sunan so ba balle har ta kai su ga aure ‘ ko ya kwanta da ita ba. Ya sha gaya miki ‘mijinki yana da wahalar sha,’ani yana yawaita karya aikin da aka yi masa ba irin mazajenmu ba ne ba wadanda ibadar ma bata wadace su ba,balle har su yi wata addu’ar kirki da zata lalata mana aiki ba”. Ta kwantar da kai ta feso huci mai ciwo tana fadin, “To wai me kike nufi nayi kenan yanzu? Shin Zuba masa ido zan yi, wata katuwa da ta gama cin moriyar mijinta ta raba ni da nawa mijin ke nan?”
“Ina baki kina Kin amsa, duk jidalin Hajiya Mariya ‘iyakacinta hirar baki da Mukhtari, idan kika kwantar da hankalinki kika ja shi a jiki sai kin ji duk‘wani abu da ta ke kullawa, kinga lalata shirin nata zaizo da sauKi k0?” ‘
Ta girgiza kai, “Haka, ne, sai dai lna ganin kafin sanda buqatar zata biya zuciyata ba zata buga ba, kin san fa yanda nakeson Mukhtar k0?”
“To ai saiki yi, ana kai ki kina dawowa, duk wani abu da zaki yi na asiri kinyi a banza ba kuma sai ki gwada baiwar kissa da kisisina ba, kishi ai kowa ma yana da shi, idan baki yi da gaskcme ba zaki rasa mijinki a wannan karon”.
Jikin Fatila ya yi sanyi, ita kam ba ta san ta inda zata fara ba, yaushe zata yadda mijinta ace wata tsohuwa ke juya mata shi, amma yaya
ta iya, dole ta bi shawarar Diyana din.
*************************
Ya yi sa’a sanda ya isa gidansu sai ‘yan samarin gidan kawai ya gani a falo suna kallo, suka gaishe shi ya amsa, sannan ya tambaye su Hajiya. Nan suka sanar da shi ta tafl gidan Inna Zulaihatun da ‘yan uwa (yayanta)
Wani irin farin ciki ya kama shi, kamar ya tashi ya taka rawa~ amma ganin kannen nasa a gurin ya sanya ya dan dake ya shige da saurinsa, kannen nasa suka bishi da kallo. Sanda ya shiga suka fashe da dariya.
Rabi’u me yace, “Ka ga man din nan kamar Fatila ba ta duniyar har yana rawar kafar son wata”.
Hamisu ya ce, “A toh, ai daman nasan komai dadewa sai Allah Ya tona mata asiri, ka manta sharrin da ta taBa kulla min kawai daga naje irin gidan yayana’ tace wai ina shigar mata har dakin bacci yazi nan ya dinga min bala’i ban da Hajiya na gurin ma ina jin dukana zai yi, shi bai san ba ta son kowa yaje gidansa. babe, amma yanzu tunda an auri yar uwarmu ai ka ga babu shegen da ya isa ya yi mana iyaka da gidan dan uwanmu”.
Hmmm bari na dakata anan mu tara domin ci gaba da sauraron wannan kayataccen book din