MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 17

MATACCIYAR RAYUWA

CHAPTER 17

da ba ya so, domin idab har tana yawaita bata masa ransa asirin ba zai yi tasiri ba. ‘
Bakinsa yaqi rufuwa sai kallonta yake yana murmushi, a ransa wani irin sonta ke. masa yawo, tunda yake bai taBa jin son wata mace kamar haka ba, da yake shi ba ma’abocin .kallekallen mata bane ba, ta karasa ta zauna tana wani yauki.
Har lokacin. bakinsa ya gaza rufuwa saida ta ce masa, “Ina wuni”. Sannan ya dan dawo hayyacinsa ya dan dake yana fadin. ‘ ‘
“Fatila manyan gari, lafiyalau, yaya jin dadi?
Tana dariya ta ce, “Yana gurinku, ashe kana magana haka?” ..
“Au kin yi zaton ni kurma ne ke nan?
Ta yi wata shagalalliyar dariya, “Ni kam bance ba, amma ai ko kallona baka yi ballé har
Kayimin ya gyara zama yana fadin magana  “Wannan ai maganar baya kika yi, amma a yanzu ai kece
Abokiyar maganata domin kece uwar yayana
Wani irin farin ciki ya shige ta ta dube shi a lalace, “Da sauri haka malam?”
“To me zan jira na kammala karatuna, kuma tun kafin na iso garin na sami aiki, daman kuma Hajiyata ta dage na yi aure tun tuni, to kinga me zan jira Fatila idan dai kina sona ai magana ta kare kawai”.
Haka nan suka dinga hira kamar wadanda suka shekara suna soyayya, Hajiya Kumatu dake labe har rawa ta taka don dadi, lallai dole gobe ta je ta sanarwa da boka yanda aka yi aiki kam ya yi kyau.
‘Bai yi shirin barin gidan ba sai da aka .fara kiraye-kirayen sallar magriba ya yi musu sallama akan sai an jima zai kuma shigowa.
Kai tsaye masallacin dake Kofar gidansu wanda mahaifinsu ya gina, wanda kusan duk jama’ar da ke unguwar a nan suke sallah ya nufa, ya shiga bandakin masallacin ya dauro alwala ya shiga da sauri aka tada sallaha da shi.
Bayan an yi sallama kannensa suka ganshi suka yi gida da gudu kai labari kai tsaye gidansu ya shiga bayan ya gama addu’a, gida ya rude da ihu da murnar dawowamhi, ya shiga
ya gaida Hajiya Babba, sannan ya wuce gurin mahaifiyarsa bakinta har kunne ta ce.
“Baba ashe dai zaka iso garin yau, yayanka ya je airpor tun hudu saura ya karaci yawonsa bai ganka ba”.
Ya yi dariya yana zaune a kujera ya ce, “Lallai sabani muka yi, ni kuma da na yi ta dubansa ban ganshi ba na biyo motar wani yaro dan nan unguwar. Mun same ku lafiya dai k0?”
“Lafiya lau, ya ya hanya? Da fatan dai an samu duk abin da ake so dai?”
Ya ce, “Masha Allah tafiya kam ta yi kyau, Yaya Hamza bai sanar dake har ya samar min aiki a makarantar gaba da sakandire ta Legal da na aiko da takarduna tuntuni  ba?”
“Yaushe? Bai gaya min ba, kai amma na ji dadi, Allah Yabar zumunci ya saka da alheri, ya kuma jikan mahaifinku da ya d‘ora ku akan wannan nagartaccen zumunci. Bari na kawo maka abinci, ai da har mun fidda rai da zuwanka”. Tana kokarin mikewa take maganar.
Da saurinsa yace, “Na koshi wallahi Hajiya, sai dai ko zuwa anjima k0 gobe naCi”.
tajuyo da mamaki tana kallonsa, domin tasan duk sanda ya iso garin ya dinga d’okin a‘ kawo masa abincin gida ya ci, domin ya ce sam ba ya jin dadin abincin cin can kamar na nan, amma yau kuma ya cc ya Roshi, ta daure dai ta _ ce.
“Kai sarkin dokin cin abincin gida kace ka koshi, kamar kaci a wani gurin, ko kuma dai ba ka jin dadi ne don daman na ganka
kamar a firgice kake”. ‘ Ya sosa keya yana fadin, “Lafiya ta kalau wallahi, na dai biya gidan Hajiya Kumatu na ci ne….”
A rude ta ce, “Hajiya Kumatu kuma‘.’ Wacecc me wannan sunan ma?” Duk ta rude don ba ta son zarginta ya tabbata.
Cikin sanyin jiki ya ce, “Aida yaron gidan muka hadu a airpor ta suka rage min hanya, sai na ga ya dacc na shiga na gaida mahaifiyarsu nayi godiya, sai ta yi min tayin abinci, to babu dadi naqi ci don ba zata ji dadi ba shine na
“La’ilaha illallahu na shiga uku, yanzu ka
ci abincin gidan kenan Baba?” A rude ta ke maganar. , Mamaki ya cika shi ganin yanda duk ta, rude, yace “Lafiya dai hajiya? K0 suna da kazantane? Ganin abincin na yi fes-fes ga kamshi yana tashi, nasan kuma kuna aikawa da kwangilar girki gidan idan kina sabga shi ya sanya naci don….”
“Ka ga tashi kaje ka bani guri don Allah”. Ta fada a zuciye.
Ya mike jikinsa sanyi Ralau domin idan akwai abin da ya tsana a duniya bai wuce Bacin ran mahaifiyarsa ba, ya nufi Kofa har ya kai
kofa ta ce. . . _. “Ka tabbatar yau ka yi tsayuwar dare ka
kuma nemi tsari da dukkan sharrin mutum da aljan kaji k0?” Yace “Insha Allahu Hajiya, ki yi hakuri ban san cin abincin nawa zai bata miki rai ba”. “Shi kenan jeka Allah Ya yi maka albarka, Ya shige mana gaba”. . Yana fita dakin Hajiya Babba ta shigo a rude, ta fashe da kuka, hankalin Hajiya Babba ya tashi matuka, domin suna yin zama na amana tun maigidansu yana raye har zuwa yanzu da kasa ta rufe masa ido, don haka zaka ga gidan sam babu wani ‘yan ubanci.
Cikin kuka ta sanar da ita duk abin da ya faru, hankalinta ita ma ya tashi amma dai ta dake ta dinga lallashinta, da nuna mata muhimmancin yin addu’a domin ita ce maganin komai
Shigo daga ciki domin karanta littafan hausa ba kakkautawa
https://web.facebook.com/groups/398700057206552/672674679809087/
Tun daga wannan lokaci soyayya mai zafi ta kullu tsakanin Fatila da Mukhtar duk wata muguwar shiga da kule-kulen samari ta daina sai shi kadai, ga shi Allah Ya doro mata kissa da iya zama da mutum, don haka ta shiga .zuciyarsa matuka ya zamana yana mata so na gaskiya ma don haka yawaita add’a da ba shi ruwan tofi da mahaifiyarsa ke yi ya sanya duk asirin da suka yi masa ya karye ya zama sai son Fatila na gaskiya wanda su suke ganin kawai aikin boka ne, shi kuma halinta da yanda take masa biyayya ya sanya ta shiga ransa matuka, domin a can baya yana mata kallon fitsararriya ne
Sannu a hankali maganar soyayyar Fatila da Mukhtar ta watsu a unguwa har ta kai kunnen ‘yan uwansa samari, su kuwa ba su yi kasa a gwiwa ba suka sanar da iyayensu da abin ya dagulawa Hajiya Mariya rai domin da farko ta yi zaton duk aikin da Hajiya Kumatu ta yi akan Mukhtar ya lalace, sai ga wannan muhimmiyar maganar ta flto, ta dinga zuci-zucin ya iso gidan ta ji tabbas. .
Nan fa ta nuna sam ba ta yarda ba duk matan da suke garin masu tarbiyya da mutumci ya rasa waccc zai ce yana so sai Fatila, me tafi sauran? Nan ya marairaice ya fara ba ta hakuri, amma ko a jikinta abu kamar zai yi sauki doniin ganin yanda hankalin mahaifiyarsa ya tashi ya ga gwara ya hakura da Fatila tunda ba zai iya kin bin umamin mahaifiyarsa ba, sanda Hajiya Mariya ta ji hukuncin da ya yanke ta ji dadi ta dinga sanya masa albarka tana godiya ga Allah da Ya sanya danta mai biyayya ne a gare ta.
Sai dai me? Sanda ‘ya tadda Fatila da bayanin shawarar da ya yanke sai ta kama yi masa kuka, hankalinta ya yi matukar tashi ta fashe masa da kuka sosai, ya dinga lallashinta haka ya rabu da ita tausayinta ya cika masa zuciya wanda hakan ya kuma sanyawa yaji sonta ya shige shi, sai dai sanda labarin ya isa kunnen Hajiya Kumatu ta ji shigar abin da zafu k0 da yake yanda ta ga hankalin diyar tata ya tashi har dasu jinya don haka babu shiri ta nufi gurin boka a rude tana kuka domin a wannan karon tana ganin kamar zata iya rasa diyar tata ne.
Boka kam ya ba ta abubuwan da za a haukata tunanin Mukhtar, ita kuma ta zube kudi don duk wata kadararsu sai da suka saidata a wannan lokacin, aiki kam ya yi kyau domin lokaci daya malam Mukhtar ya gigice ya hauka ce bai san sanda ya koma gurin Fatila ba, suka ci gaba da soyayyarsu a wannan karon ma labari ya koma kunnen Hajiya Mariya, ta kirawo danta da haushi da fad’a, sai ya fashe mata da kuka abin da ya tsoratata, amma ta ‘tabbatar masa ko kukan jini zai yi Karya yake ya auri Fatila tunda tasan ba auren Allah bane.
Da rikici ya kacame tsakanin dan da mahaifiyar abin da ke kara ba ta tsoro bai wuce
ganin yanda danta dake matukar yi mata biyayya yau da shi ta ke sa’insa ba, wato tun bai auri Fatilar ba ma kenan, to idan ya aureta ya ya za a yi kenan?
Shi kam Mukhtar ya shiga tsaka mai wuya, ga shi ya Ki yarda da wai asiri Fatila ke ‘yi masa ya sota balle har ya nemi tsari da shan’insu kamar yanda mahaifiyarsa ke so. Sai ya ce, wai shi yasan soyayya ce daga Allah, duk wani dadin baki ya yi a banza har rantsuwa ta yi’ muddin nononta ya sha ba zai auri Fatila ba, su kuma can basu daina aikinsu ba, daga karshe dai ya yanke shawarar taflya gurin Abbagana ,tunda yasan ‘iya’yen nasa da yayyensa suna jin maganarsa kamar ta mahaifinsu domin ya bada goyon b‘aya ta kowane Bangare, sanda Abba ya iso ya dinga yi masa nasiha da nuna masa duk abin da Allah ya Kaddara babu makawa sai ya faru.
Ya nuna Hajiya, “Idan Allah Ya kaddara da’rabon aure k0 haihuwa a tsakaninsu sai ya kasheta,’ da’ wannan ya sanya suka amince amma ransu basa kauna, bai bar garin‘ba sai da aka kai dukiyar aure.
Su Hajiya Kumatu kam murna suka ..’ Dingayi, domin sun tabbatar fatsarsu ta kama qaton kifi, da fara shirye-shiryen bikin Karya.
Tunda aka yi auren Fatila ba ta mu’amala. da kowa da ya shafi Mukhtar din a cewarta basa kaunarta ba ta ga amfanin hulda da su ba, duk yanda yake son ya kulla alaka tsakaninsu da mahaiflyarsa abin ya ci tura, domin ita kanta Hajiyar ba ta kaunar ganin Fatilar, dole haka ya hakura k0 sabga ake yi a danginsa sai ta ga
dama ta ke zuwa. Burinta ya ta’allaka akan ta haihu, domin
tasan tana haihuwa ta gama da shi, sai dai Allah ya Ki amincewar zata iya zame musu gibin da komai zai iya faruwa, hakan kuwa aka yi mahaifiyarsa ta fara fadan ya kara aure tunda an kwashi shekaru hudu matarsa k0 batan wata bata yi ba, saboda son da yake yine ya dawo da alakarsa kamar da mahaifiyarsa ya sanya ya amince ya fara neman auren wata yarinya Binta, wacce shi kam yake ganin zai aureta ne kawai don babu yanda zai yi, an sanya rana an gama komai kwatsam! Labari ‘yaje kunnen Fatila Allah Ya yi ta mace mai kishi wanda ya wuce irin na ka’idar addinin musulunci, don haka a rude suka yi gurin boka akan duk yanda za a yi a fasa wannan aure.
Sai aka turawa Binta aljanu yarinyar ta dinga fama da wahala ta fara kamar haukahauka hankalin iyayenta kam ya tashi suka dinga nemar mata magani, daga karshe suka ji matar Mukhtar ce ta yi mata shunen aljanu, don haka suka ce sun fasa ba shi, tun ba a yi auren ba ma ana turowa diyarsu iskokai balle an yi auren? Wannan ce ta watsa maganar auren, Mukhtar kam bai wani damu ba yace ya bar musu duk abin da ya kai.
Hajiya Mariya kam kamar zata hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki, amma da ta yi masa magana sai yace ai ba laifinsa bane  daga nan ta ce ya Kara neman wata.
An dan jima kafib su hadu da Shamsiyya, ita kam tana cikin’ dalibansa a nan Legal, kamun kan yarinyar ya sanya ya fara sonta, sanda ya tadda mahaifiyarsa da maganarsa taji dadi aka fara neman auren a Boye har kayan lefe aka kai. Ya rage saura kwana goma aure labarin ya isa kunnen Fatila ta sanar da mahaiflyarta, ba su yi kasa a gwiwa gurin tafiya  gurin bokansu ba. Ita kam Shamsiyya jini aka sakar mata, abu kamar da wasa sai ta yi ta sako pad sai ga abu ya haikake ko taflya take jini zai ta zubowa kawai, an kaita asibiti an tabbatar ba daga mahaifarta yake zubowa ba, dole suka koma na Hausa.
Shamsiyya duk ta rame ta kare saboda bakin ciki, domin bata iya flta k0 kofar gida kullum tana daki, wuni ake wanke zannuwanta da jini ya Bata. Hankalin Mukhtar kam ya tashi tunda yana son Shamsiyya ya dinga taimaka mata da addu’o’i idan abin ya yi sauqi sai ya dawo, su ma daga karshe aka sanar da su wadanda suka aikata abin dole hankalin iyayenta ya tashi matuka, tunda shekara guda ana ta abu daya duk diyarsu ta kare ta rame
‘ kamar mai fama da ciwon kanjamau, su da
kansu suka fara tattara kayan Mukhtar da kudinsa suka kai gidansu suna ba su hakurin cewa sun fasa.
Hankalin Hajiya Mariya ya tashi ta fara yi musu nasiha, amma sun tsorata suka ce sam ba su yarda ba., dole haka ta hakura shi kansa
da ya ji an dawo masa da kayansa, saida hankalinsa ya yi mugun tashi, da ya je gidan su Shamsiya ba su barshi ya ganta ba, suka kama ba shi hakuri, haka dole ya haKura ya tafi
Amma shi ya Ki yarda wai Fatila ce ke hana shi aure kamar yanda iyayensa da ‘yan uwansa ke fada, domin duk sanda ta ji labarin auren ba ta nuna damuwarta har kaya take siya ta bada gudunmawa, yasan tana‘da matukar kishi, don k0 kallon mace ta ga ya yi ranar sai ‘ sun KWana tashin hankali, amma idan taji labarin auran da kanta ta ke sanar da shi ta ji, har ta yi ta masa tsiya tana cewa, “Ai ni ban isa na hanaka aure ba, ni wannan soyayyar ce bana so ta titi”.
Da haka dai aka rufe babin Shamsiyya, bai kuma yunkurin kara neman aure ba.
Sai da aka yi shekara daya sannan mahaifiyarsa ta tura shi ya ga diyar kawarta, bai musa ba yaje ya ganta babu laifi shi dai bai ji wani sonta ba, amma kuma bai nuna ba ya sonta ba, ita kam sati guda kacal aka sanya auren don kada taji daren da za, a daura auren ya shigo da kayan da zai sanya na daurin aure nan fa hankalinta ya tashi da ya sanar da ita auransa za a daura gobe da safe.
Nan fa ta tuBure ta kama kuka tana nuna mai yasa yaqi sanar da ita tun da farko? A daren ta sanarwa da Hajiyarta ta a waya, ai kuwa a wannan daren Hajiya Kumaru ta nufi gurin boka a rude, ko tsoron duhuwar dajin ba ta ji ba.
Tsakar dare ana tsaka da bacci aka jiyo ihun Samira tana buge-buge tana surutai, da gudu iyayenta suka nufi dakin nata aka dinga’yi mata tofi da kyar ta kwanta, sai dai k0 minti daya ba a yi ba ta kuma farkawa a gigice, haka suka kwana a gigice domin idan dai zata runtsa to kuwa lallai zata ga bakin aljanin da ake . turowa ya ba ta tsoro, gari yana wayewa ana shirye-shiryen daurin aure amarya ta kama aman jini, aka kwasheta aka yi asibiti a gigice likitoci suka taru a kanta.
Daurin aure dai bai yiwu ba domin sai da aka sanya mata jini laida biyu, aka daga bikin sai wani satin. Kwananta uku a asibiti ta warke, sai dai ana dawowa gida ta kuma ci gaba da aman sai da aka yi haka kusan sau hudu, idan

Hmmm 🤔  lallai kumatu da fatila anyi shaidanu😲

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *