MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 20
mahaifinki ne, duk abin da Allah Ya Raddara zai same ki ni da ilimina ba mu isa mu sauya shi ba. Ki sani Ma,’aikin Allah ma an jarrabace shi da sammu da kuma wasu abubuwa na Bacin rai, to kw wace ce da Allah ba zai jarabce ki ba‘? Mumini na kwarai shi ake yiwa jarabawa duk wanda kika ga yana jin dadin duniya yana kuma juyata yadda yake so, to lallai ma’abocin sharholiya ne, sai kadan daga cikin mutane da Allah kan tsare, ki yawaita ambaton Allah a kowane hali kike, ki kuma rage sanar da kowa halin da kike ciki, musamman ita uwar mijinki, tunda kinga ta damu da al’amarinki matuka, idan kika yawaita yi mata korafi tabbas zata kosa dake, Allah ya yi miki albarka Ya sanya ki cinye duk wata jarabawa da aka yi miki, amin”.
Tabbas nasihar mahaifinta ta shigeta sosai, har idonta yana zubda hawaye tace Na gode Abba, na gode, zan kuma yi duk abin da ka cc, Allah Ya ja mini da ranku”.
‘Yaji dadi har cikin ransa, shi ya sanya kullum ya ke alfahari da ita, duk matsalarta ta shige yana ba ta shawara zata amsa saBanin ,diyoyin Hajja Yakolo da suke ganin bai damu da damuwarsu ba, sabaoda bai iya daukar wani mataki sai dai yace, wai su yi ta hakuei kawai.
Hajja Basm‘a dake gcfensa tana kallo. da yake ita ce da girki ta ji duk abin da suke tattaunawa da ita hakan tasa, ta kuma fuskanci diyar tana cikin babbar matsala, don haka ta kwantar da kai da kissa tana fadin.
“Abba wani abu me ya sami Falmatan? Tsiyar auren nesa ke nan wallahi, ba kasafai ‘ya’ya kejin dadi ba, don shi mijin sai ya aikata komai a gare ta tunda yasan babu iyayenta a kusa, ba ta da wanda zata sanarwa”.
Yadda ta bade rai tana maganar zaka yi tsammanin tsakani da Allah har cikin zuciyarta ta ke maganar, hakan ne ma ya sanya Malam din fara ba ta labarin halin da ake ciki.
“Wallahi Falmata ba ta da matsala da ‘mijinta k0 ‘yan uwansa, domin kusan wadanda ke auran a gabanmu ba su kai ta dacen mijin ba, sai dai matsala daga abokiyar zaman nata, yadda suke fada hatsabibiya ce matuka, sai dai a yi ta addu’a kawai, Allah‘ Ya tsare ta daga dukkan Wani sharrinta”. .
A fili ta amsa da, “Ameen”. Amma a ranta
cewa take “Insha Allah sai ta korota, sai ta zama Karamar bazawara sai mu gata karshen so kuma”.
Tana jin an yi sallama da shi ya fice ta mike da azama ita ma jikinta har rawa yake ta nufi dakin Hajiya_Yakolo da hanzarinta.
Ta tadda Hajiya Yakura suna waya da babbar diyar tata Yakura tana sanar da ita yadda zata yi amfani da magungunan da ta aikata mata. Wani tace wanka akeyi, wani turare, shirka dai tsagwaronsa ake dorata akai. Sai da ta jira suka kammala wayar sannan ta kalle ta tana fadin.
‘ “Hajja albishirinki, muna nan ana ta takaici, yaran gurinki kadai ke fuskantar matsalar aure, wancan diyar suna zaune qalau, ashe ba haka ba ne. Yanzu ina dakin Abba na ji suna waya da uban, yana ta mata wannan nasihar harda ba ta lakani da ya saba badawa. Bayan sun gama wayar na marairaicc ina tambayarsa abin dake damunta, yace mini, ai kishiya ce ta hanata sakat, ni wallahi da zan ga kishiyar da na ba ta lada ta ci gaba da azabtar da ita”.
Hajja Yakolo ta sheqc da dariya cike da farin ciki tacé, “Haba har na ji dadi wallahi,
kullum baza kunne ‘nake domin na ji halin da take ciki, amma da yake uwar tata munafuka ce baka jin komai, kullum sai dai a yi ta yiwa ‘ya’yana gorin sun cika yaji. To an hada su aure da wanda basu so ba dole su yi ta yaji ba? Ai Allah ba azzalumin Sarki bane yadda aka hada baki aka cutar dani da ‘ya’yana su ma tasu diyar insha Allahu ba zata zauna lafiya ba. Allah ya sanya ta dora mata ciwon hauka ma kowa ya huta”;
Hajja Basma ta ce, “Ameen, kin san murna suke yi ai ta sami ciki, zata ci gado tunda ita waccan din ai ba haihuwa ta ke yi ba. Ni nasan kwadayi ya sanya Iyami shiga malamai har Abba ya yarda aka baiwa diyarta Muhammadu, amma a ci gaba, kere na yawo zabo na yawo wallahi dole watarana a hadu
Haka nan suka dinga kitsa masifarsu da sharrinsu ga baiwar Allah wacce ba ta ji ba, ba ta gani ba a gare su. Saboda kyashi da hassada kawai Allah dai shi ne abin dogaro.
*** ***
Kwanakin Falmata uku a gidan su Hajiya
Mariya, ta__warke garau akwai Jidda diyar kanwar
Hajiyar wacce ta rasu, daman‘ makarantar kwana ta keyi. To tumda ta dawo hutu zama yaki dadi da matar uban da ta ke azabtar da ita ta gudo gurin Hajiyar ta zauna abinta, ta ci gaba da karatu.
Hajiyar ta yanke shawarar Falmata ta tafi da ita can gidan, sannan shi kansa Hashim Hajiya tace tunda dai a B.U.K yake karatu ya koma can da zama yafi masa saurin zuwa ma. Mukhtar kam yaji dadin wannan shirin, domin yana jin takaicin yadda ‘yan uwa suka ware shi daman, babu mai zuwa gidansa da yayi korafi sai ace wai matarsa ce ba ta son mutane.
To yanzu dai Allah Ya taimaké shi har gidan nasa ma za a je a tare, me yafi wannan dadi a tattare da shi?
Can ‘dakin yara Hashim ya tare, babu abin daya hada k0 Kofama da cikin gida, sai ya ga dama komai akwai a bangaren nasa, kasancewarsa mai karatun Pharmacy sai hakan ya fiye masa dadi don babu hayaniya yana .karatunsa cikin kwanciyar hankali, makaranta ‘ kuwa ko ihu ya Kwala za a jiyo shi, komai ya fiye masa sauki Falmata tana kula da cinsa, ba
ta bari ya fita da safe bai karya ba, kullum kuma sai ta amsar masa kudin kashewa gurin malam din, hakan ya sanya yake girmama Falmata matuka
Ita kuma Jidda daki guda aka ware mata har da kayan kallonta da komai, idan ta tuna wannan dakinta ne wani farin ciki ke rufe ta, domin gidan mahaifinta daman ba wani mai wadata babe, dakin nasu na hadaka ne da ‘ya’yan kishiyar uwar tata, amma kullum kayanta wulakance suke, a yi ta mata cilli daau amma yau, ga shi ta sami daki tamkar tana gidan mijinta. Sai kuma abin da ta ga dama zata ci.
Falmata tana da matukar kirki, ba ta matsa mata, ga shi su zauna su yi ta wasa da dariya, ita ce ta koyawa Falmata karatun littattafan Hausa, domin ita ba ta iya ba can baya kwata-kwata, domin tunda ta tashi ta ke fama da karatun haddar kur’ani wanda yafi kowane karatu wuya da dadi hakan ya sanya ta ‘tashi ba ta iya kallo k0 karance-karance irin na ‘yan matan zamani ba kwata-kwata, don idan ta ga Jidda na yin wani iya yin har mamaki take ta dinga tambayarta inda ta koyi wani girkin.
Ta yi dariya tace, a littafii. wannan ya sanya dai ta koyi karatun nan ita ma karfi da yaji.
Sati guda Hajiya Kumatu suna ta aiwatar da mugun nufinsu, sun binne na binnewa, sun shanye na shanyewa, sun turare na turarawa, sannan sun yi amfani da na wanka. Sati guda daman boka ya ba su aikin zai fara yi.
Falmata tana kwance cikin dare tana bacci, malam yana gefenta shi ma yana bacci, kawai ta ga kamar gilmawar wani abin tsoro a kanta yana nufota, da yake ta jiKu da addu’a sam ba ta firgita ba, sai ta kama kiran sunan Allah, daman A yatulkursiyyu ta zama kamar numfashi a gare ta, don haka ta kama yinta tana tofawa, wannan abin da yake nufarta mai ban tsoro wanda aka umarta da ya musanya abin da ke cikinta zuwa wata mummunar halitta ya kashe na cikin ya dauke shi.
Aljanin da aka turo ya fara ja da baya saboda ruwan addu’ar da ake masa, sam ya kasa dosar Falmata sai ji da yake ma kamar ana yarfa masa ruwan dalma. Ya fara ihu yana wani irin sambatu wanda falmata keji har cikin kanta bata daina ambaton Allah da karanto ayatulkursiyyu ba, har aljanin nan ya bace Bat! Saboda azaba idonta yana rufe ‘cikin baccin taci’gaba da addu’ar tana tofawa a gabanta.
Malam mai darasu dake ta bacci ya ji kamar sautin karatu ya cika dakin. Ya tashi da hanzari sai ya ga Falmata cek karatu tana tofawa kusurwar yamma, ga shi dai idonta a rufe yake alamar tana bacci, amma sautin karatunta yana fita.
Mamaki da tu’ajjibi ya kama shi, tabbas matar tasa ‘yar baiwa ce, ya janyota jikinsa ya rungume yana tofa mata addu’o’i shi ma, sai ta bude idonta kyar a kansa. Ya kura mata ido da alamun tambaya, yace
“Falmata lafiya, k0 mafarkin karatu kike yi ne?”
Ta kalle shi idonta yana zubda hawaye, duk jikinta ya mutu saboda gwabzawar da suka yi da aljanin nan, tace“Wani mugun mafarki na yi, amma Allah ya tserar dani daga sharrin abin da yazo min cikin mafarkin, sai dai…”
Ya toshe mata baki yana girgiza kai, yana fadin, “Kada ki bani labari, babu kyau a bada
labarun mummunan mafarki. Kici gaba da addu’a da neman tsari, nayi farin ciki da kika ‘kasance mai ilimi, masha Allah da samun mace saliha irinki”.
Dadi ya cikata, babu abin da take so a duniya illa mijinta ya yarda da ita, don haka sai taji gaba daya ranta ya yi sanyi, komai ya wuce a zuciyarta.
Ya rungumeta a jikinsa duk da cikin da ke tsikarinsa suka koma baccinsu, sai dai ita ba ta samu damar komawa baccin ba, don tana runtse idonta za ta ga aljanin nan yana kuma tunkarota
yana ihu da fadin.
“Ba zan yarda ba tunda kika kona ni sai na rama”.
Don haka da ta tabbatar bacci ya dauki malam din ta janye jikinta a hankali ta nufl bandaki ta dauro alwala ta fara yin sallah, tana sallama zata kuma tada wata sai da ta yi raka’a goma, sannan ta dauko kur’ani ta fara karantawa musamman guraren da mahaifinta ya sanar da ita ta yawaita karantawa, haka ta wanzu har aka kira sallar asuba ta farko ta tashi malam din ya yi alwala ya tafi masallaci, domin shi ne limamin masallacin unguwar tasu‘.
‘ Sai da ta idar da sallar asuba ta yi lazimi, saunan ta kwanta. A wannan lokacin kam babu abin da ta ke gani sai dai jikinta ya mutu murus, bacci ne kawa’i’: a idonta, tuni bacci ya dauketa, har malam ya shigo ya taddata a haka. Ya zauna yana zikirinsa da hailala har rana ta fito, ya kwanta shima domin ranar asabar ce ba shi da makaranta.
Jidda kam tunda ta farka karfe bakwai ta ga maigidan bata tashi ba ta shiga kicin ta fara aiwatar musu da abin da zasu karya.
Wajen tara falmata ta sami damar farkawa, da sauri ta mike tana salati. Sanda ta ga agogo ya nuna karfe tara‘ na safe, can ta hango malamin nata yana ta danne-danne bisa computer da alama aikin ofls yake yi, don ta ga tulin takardu a gabansa yana ta shigar wa ciki.
Da hanzari ta mike ta nufe shi ta dan durkusa tana fadin.
“Barka da safiya malam”.
Ya juya ya kalle ta yana dariya, yace, “Barka ka dai sleeping beauty, sai yanzu kika tashi kenan?”
Tayi dan murmushi, tace, “Ai duk laifinka ne da baka tashe ni ba, kaga yau sai rana zamu karya”
Ya yi dariya yana fadin, “Waye ya gaya miki ana tashin uwar biyu? Ai barinku ake yi ku yi baccinku ku more”.
Ta yi dariya tana nufar hanyar bandaki tana ci gaba da magana, “Wallahi ba zan biye maka ba bari na watsa ruwa naje na samar mana abin da zamu ci”.
. Ya bi ta da kallo yana dariya yana girgiza kai, tafiyarta kadai abar duba ce don duk ta wani gantsare cikin ya tsufa.
Tana fitowa daga wanka ta shirya a gaggauce cikin doguwar rigar atamfa mara nauyi, ba wata shahararriyar kwalliya ta yi ba, kwalli kawai ta sanya ta murza hoda sai man labba da ta sanya. Ta shafe jikinta da turare ta fice, Kamshinta duk ya cika shi, ya daga kansa da zummar tsokanarta amma sai ya ga har ta fice, yarinyar tana burge shi matuka komai nata a sassauke babu matsawa kai k0 takurawa rayuwa.
Hashim ya shigo gidan yana mika alamar bai dade da tashi daga bacci ba, kai tsaye kicin
ya nufa yana fadin.
“Kai antina yau ba a gama girki da wuri ba, yunwa duk ta ishe ni yasin”
Ganin Jidda gaban gaskuka din ya sanya ya tsaya turus cike da zolaya yana fadin
“Kada dai kice yau kece koke mana girki Tabdi jam lallai yau za muci jagwalgwalo kenan .
Jidda ta juya tana galla masa harara tana fadin, “Idan mutum ya isa kada yaci mana”.
Ya yi dariya yace, “kin san Allah ban da ina jin matukar yunwa da ba zanci ba… Hahaha”. Ya fashe da dariya, “Kalli fa yadda kike ta wani’ jagwalgwalo kawai”. . _
Falmata ta shigo kicin din cike da farin ciki, domin Tunda ta jiyo Kamshi ta san Jidda ce ta dora mata sanwar, ta isa ta kalli Hashim ta ce.
“A’a Hashim kada fa kazo ka ci abinci kana santi, ni bana son kuri da cika baki ‘ wallahi”. Ya yi dariya yana fadin, “Anti Falmata yarinyar ce sai a hankali wallahi, ki duba fa
Yadda ta keyi?” , Falmata ta yi dariya, tace “To so kake ta
barshi ya kone ne, kai ni na gaji da wannan tsamar taku, koda yake ba a san inda rana zata fadi ba”.
Da’ sauri Jidda ta waiga tana fadin, “Tabdijan, Allah ya sauwake, rana ai yamma zata fadi Anti, me zanci da wannan…” Tana kallonsa sama da kasa.
‘Ya yi dariya yana fadin, “Yarinya kin san dai nafi karfinki ne kawai”. Ya maida dubansa ga Falmata yace, “Don Allah And a zubo mini na tafi surutun yarinyar nan yunwa yake kara mini yasin”. ‘
Falmata ta yi dariya ta zuba masa kasonshi na shayinsa a fulas dinsa ta miqa masa cikin babban faranti. Ya amsa yana fadin, “Amma fa idan babu dadi zan dawo da shi…”
Da karfi Jidda tace “Idan ka isa ka ajiye tun ba ka dandana ba ma sai in tabbatar da ba kaci, na rantse Anti ko Kwara ba zai bari ba wannan ”. Ya wuce shi dai yana dariya, Falmata tana taya shi, in dai suka hadu tamkar kishiyoyi sai an yi sa’in’sa. Ta harhada na maigidanta da nata ta wuce tana fadin. ‘
‘ “Kedai Jidda Allah Ya yi miki alb‘uarka, kin taimake ni matuKa wallahi”.
Dadi ya cika Jiddan, domin Falmata kan burge ta k0 ya ya ka yi mata abu ta dinga godiya ke nan, shi sanya take samun karsashin yi mata komai.
Gaba daya haka falmata ta yi wunin ranaxmr jikinta duk babu kwari har zuwa dare da ta kwanta, sai da ta yi addu’o’inta ta kwanta.
Tana tsaka da bacci kamar jiya ta hango wannan aljanin wannan karon yana daga can nesa ya kasa ko karasowa inda yazo jiya, jikinsa kuma duk a kone, sai dai kuka yake yana fadin.
“Don Allah ki daina min wannan addu’ar da kike kona ni, Ubangijina ne ya aiko ni gurinki, idan banzo ba tabbas zai wahalar dani… Wayyo na tuba”.
Ita kam ba ta fasa karanto ayatulkursiyyu da sauran addu’o’i tana tofa masa ba, har ya Bace wa ganinta. sai ta tashi a firgice jikinta duk ya mutu, malam yana gefenta yana baccinsa sosai. Ta jima a zaura“ tana tunanin wannan mafarkin nata na jiya da. yau, abin da ke bata mamaki bazai’ wuce jin Aljani na fadin an turo shi ya dauke
abin dake cikinta ne ya musanya da mushen dan jaki, k0 biri ko mage k0 kadangare ba.
Yanayin yadda ta ganshi ya dinga fado mata tabbas a wannan lokacin bai kamata ta dinga bacci ba, dagewa ya dace tayi da rokon Allah, don haka ta mike ta daura alwala kamar jiya ta fara gayawa Allah halin da ta kc ciki.
Tsawon lokacin da Fatila ta kwashe a gida tana cikin’tsananin bakin ciki da takaici, wani lokacin ta dinga mamaki, wai ita Malam zai yiwa haka? Ta sadaukar da dukkan rayuwarta a kansa, amma ya saka mata da cin amana, tabbas dole ta daura sabuwar damarar yakar Hajiya Mariya domin ta yarda har abada ba zata so ta ba.
Saboda tsananin kishi k0 baccin kirki ba ta iya yi, kullum tana cikin kuka da damuwa, duk ta rame ta fige, wannan ne ma yake kara dagawa Hajiya Kumatu hankali, ta san tana da kishi amma ta kula kishin diyar tata yafi nata nesa ba kusa ba, don haka sun koma gurin boka don jin makomar aikinsu, sai dai ya tabbatar musu da ‘ aljanin da suka tura ma yana can yana jinya. domin ta konashi gaba daya, da ace bokan na Allah ne‘kamata ya yi ya gaya musu gaskiya,‘ aljaninsu duk shaidancinsu ba zasu iya tasiri a kan Falmata ba, domin ta jiqu da addu’o’i k0 bacci taje Iebenta yana ambaton ayatulkursiyyu, amma ba zai iya gaya musu ba sai wasu karairayin da ya kuma yi musu, yace za su tura mata rundunar aljannu su kara kudi.
Babu gardama suka Kara damin kudin kuwa, Ya Kara tabbatar musu da aikin zai tabbata da izinin aljaninsa, da wannan suka sake komawa gida, suka kara zaman jiran tsammani
*** *** *****************
Ta kusa wata ba ta ga komai ba, don haka tana baccinta cike da dadin rai, sai dai cikin kwanakin tana ganin sauyi daga malam Mai darasu domin yakan zauna shiru ba ya hira da sakin fuska irin na da, idan tayi masa magana ma a dakile zai amsa mata, ga kyara da hantara da yake yawan yi mata. Hakan ya sanya ta dan janye kanta daga wasu al,’amuransa, sai dai abin dake bata mamaki bai wuce yawan tunanin da yake ba.
Ta sha lekawa ta windo ta hango shi akan
Hmmm kodai an karkato da hankalinsa wajen tsohuwar zuwa fatila ne