MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 23

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 23
ga Zahra da babu ruwanta. ‘ 
Duk da ba cikin wata shahararriyar daula Falmaba take ciki ba, lallai tana cikin rufin asirin Allah, da kulawar mijinta. Komai na sunan gwanin ban sha’awa ga shi dangin mijinta sai nan-nan suke da ita, sam ba ta cikin wata matsala, k0 damuwa. Hakan ya tunzura su Hajja Yakolo matuka, domin ranar suna kulewa suka yi cikin daki suna sakawa . da kwancewa ganin yadda Falmata ke shiga tana fita cikin manyan suturu da gwala-gwalai, takanas Malam ya bai wa Hajja Kaltum dankareren gwal har da abin hannu a Boye ta taho mata da shi. Sam basu san tsarabar Abba bace suka cika fam. Labarin da yafi komai yi ‘musu muni, bai wuce fitar kishiyar Falmata da suka ji ba. Ranar da suka ji wannan labarin ba Falmata ba hatta mahaifiyarta Hajja Iyami sai da ta sha tsinuwa da-zagi, domin sunce ita ke tura mata’ duk wani asiri. 
Ita kam Falmata k0 a jikinta duk da ta kula da irin habaici da kallon da suke mata na ‘yan ubanci da tafi su komai. Haka aka yi taron sunan aka kammala. 
Kwana biyu da yin suna suka tattara kayansu suka nufi garinsu, Falmata ta cika su da kYauta kala .-kala da kayan suna, sunbar Kano rai a bace matuKa, sai dai sun tafi da mugayen kudure kudure a cikin ransu na ganin bayan wannan aurE mai cike da kwanciyar hankali. 
Su ma gidan su Hajiya Kumatu wannan lokacin sun yi shi ne cikin bakin ciki da takaici, domin fatila ta rame ta Kare ba ta da aiki sai kuka, taqi ci taqi sha. Sai mahaifiyarta ke matsa mata dole ta ke cin abinci, haka neya daga hankalin Hajiya Kumatu, ga knma kwanakin iddarta suna ta karewa shiru ba maganar biko, daga Karshe dai sun yanke shawarar komawa gurin bokansu, domin sun ‘ tabbatar tsafinsa yafi na kowa Karfi, don haka dole sukaje biko da ban hakuri’.‘ , . . 
Sanda sukaje ya dinga yi musu dariya har da ihu yana fadin; “Duk duniyar nan k0 da zaku dangana da Kasar Hindu ne kuwa ba zaku samu biyan bukatarku ba sai kun dangano da mu”. 
Su dai sun lallaba shi da lallashi ya hada musu mugayen magunguna sun koma gida sun fara aiwatar da su. _ 
Da yake an ce tsafi gaskiyar mai shi, sannan Falmata tana cikin jini ne, .ga shi kuma yawan jama,’ar gidan su Hajiya kan dauke mata hankali da hira da wasa da dariya ya sanya ta rage yawan addu’o’in da také yi matuqa, sai dai idan zata 
kwanta bacci. Hakan ya sanya tsafin su Hajiya Kumatu ya fara tasiri a gare ta, sai ta fara jin haushi da tsanar Mukhtar shi kam har yafi ta jin hakan, domin ba don da mahaifiyarsa a gidan ba da k0 zuwa ba zai dinga yi a gidan ba. 
Sai dai sam hajiya Mariya ba ta kula da abin dake gudana ba, domin lokuta da dama idan ya shigo da daddare takan fice ta bar musu dakin ne, daga gaisuwa basa kara cewa juna komai, sai dai ‘ kowa ya maida hankalinsa ga kallo, shi kam k0 
. kallon yaron nasa Muhammad ma bai yi balle yace ‘ ya ya yini, k0 ya kwana? 
‘ Wannan ke Kara qular da Falmata, amma ta kasa gayawa kowa halin da suke ciki da mijin nata, domin shi bai fasa yin duk abin da yake yi din ba. 
. Ranar da suka ‘cika wata guda yana zaune a ofis dinsa abin duniya ya ishe shi, tunanin Fatila ’gaba daya ya cika shi, ya tabbatar idan bai dawo da ita ba ba shi da sauran samun. nutsuwa da kwanciyar hankali, domin k0 tuqi yake ita yake gani a gabansa. Kawai sai wayarshi ta kama kara. 
Da sauri ya kalli wayar ya daga da sallama, Fatila daga can Bangaren ta doka tsalle cike da tsananin murna ya daga kiranta; don a kwanaki daidai lokacin da Falmata ta haihu kusan kullum 
sai ta kira shi a wayar harda sako take rubutawa ta aika masa, na ban hakuri akan abin daya faru, amma bai taBa daga kiran nata k0 kuma ya dawo mata da amsar sakon da ta tura ma‘Sa ba. 
Cikin rawar murya tace“Mukhtar”. 
Ya lumshe ido, wani abu mai sanyi da ya jima baiji shi ba ya bugi zuciyarsa, tabbas Fatila ce farin cikin rayuwarsa. Sai da ya jingina da kujeran yace
“fatila manyan mata, dama kina duniyar nan kin share ni k0?” 
‘ Ta yi wata dariya mai shiga zuciya, tace“Ni na isa na share_mai zuciyata? Ni ai ya dace nayi wannan Korafin ma, domin na sha kiran wayarka kaki dagawa balle sako da har na gaji da rubuta wa, sai dai na ga laifina domin na aikata , maka abin da ya dace Ka yi min fiye da hakan ma”.
Ya yi*dariya yace“Na wannan dai ni ake gayawa magana, amma ai nima mai laifi ne sai dai mu tattara duk mu ajiye wannan batun a gefe guda, mu shiga abu na gaba. Kina ina yanzu domin ina son ganinki a yanzun nan”. 
Ta sake yin dariyarta, tace
“Wacce irin magana ce wannan, k0 ka
m‘anta ka sake ni ne?” Ya yi dan jum cike da takaici ya ce, “Tabbas haka ne amma ai na san ba ki kammala idda ba, don haka na maida ke dakinki, fatana kada ki kuma . tuna mini da na taBa sakinki ma kin ji k0?” . Ta kuma doka tsalle cike da farin ciki marar misaltuwa, wacce irin rana ce wannan yau a gareta mai cike da girma da daraja? Hakiqa ta yarda aikin ‘ boka yana kyau. Cikin kWantar da murya tace “K0 yanzu zaka iya zuwa ai ina gida’Nan da nan ya kama hada kayansa, duk da ‘ 
lokacin tashi bai yi ba. Ya kulle ofis jikinsa har. rawa yake fatansa da’ burinsa bai wuce yaga Fatila ‘ ba k0 ya’sami’jin dadi da nutsuwa. 
‘ Ita kam Fatila tana kammala amsa-wayar ta wani buga uban ihu cike da murna, mahaifiyarta ta iSo da sauri tana tambayarta abin da -ya faru ranta ya yi wasai, domin rabon da ta ga diyar tata cikin  farin ciki irin wannan har ta manta. 
, Ta dare mahaifiyar tata tana fadin, “Momy Mukhtar ya daga wayata har ya tabbatar mini da ya ‘ maida ni dakina, kuma ga shi nan zuwa na‘n gidan ma yanzu”, ‘ Hajja kumatu ta waro ido cikE da doki da zumudi tana fadin. 
“L‘allai dole mu godewa boka, da mun barshi da mun yi sake kenan. To yanzu maza je ki , ki shiryar kafin ya iso gidan, ki yi amfam’ da wadannan mayukan da turarukan da boka ya baki . Ta wuce da sauri cike da zumudi. Bai tsaya a ko’ina ba sai a kofar gidan su Fatila, farin’ ciki ya cika ransa matuka, ya bude motarsa ya fito ya nufi gidan, saboda tsabar doki kasa kiran wayarta ya yi ya sanar da ita ya ‘iso, su kuwa dama sun ji Karar motar suka yo kan wundo ‘ da sauri’ suna lekensa, suna ganin ya iso kofar falon suka koma da baya. Fatlla ta shige dakin bacci da gudu. ‘ ‘ Ya tsaya a kofar falon yana sallama, Hajiya ‘ Kutnatu ta amsa gami da ba shi lzinin ya shigo, Ya shiga yana Kara yin sallama, falon ya sha ‘bambam ‘dana baya, domin Fatila ta sauya kujerun da kayan kallon falon ’ Hajiya Kumatu ta dube shi da mamaki tana riqe da baki wai irin’bata san abin da ya faru ba, tace“Mukhtar yau kai ne a’gidan namu kuma?” Ya sami guri ya zauna yana dariya cike da kunya yace
“A yi hakuri ‘Hajiya, ayyuka ne suka yi min yawa. shi ya sanya ban sami lokacin zuwa ba”. 
‘ Hajiya tace lallai kam ayyukan nan sun kus‘a jaza maka, domin ina jin gobe za muje _ kwasar kayanta ai, domin a jibi ta ke kammala 
iddarta”. . ‘ 
Ya daga kai da sauri yace Lallai kam nak‘usa yin sakaCi, amma ai ni daman tuni na maida matata, don dai ban sanar daku bane shi be  laifin nawa”
Wani irin farin ciki da jin dadi ya kama. . Hajiya Kumatu, ta ce.
“Lallai kam to Allah ya shige mana gaba, .’ amma irin wannan dan laifin bai dace har a yi saki ba tunda» ita aka yiwa laifi komai ta yi sai a yi tunanin. zafin kishi ne ya sanyata aikata komai, amma sai aka yanke mata irin wannan hukuncin na _ rashin adalci”. ‘ 
Shi dai hakuri yake badawa, do‘min ya yarda shine ya cutar da Fatila, don gaba daya an mantar dashi laifin data aikata, sai da ta kammala cin kashinta sannan ta mike tace “Bari na kira maka ita” 
Fatila aka fito ana yanga, shi kuwa jikinsa 
har rawa yake sai da ta wana shi matuka sannan ta 
saki jiki suka koma hira, Wannan ne ya tabbatar musu da komai ya dawo yadda sukeso. A gidan ya ci abincin dare, ya yi sallar magriba da isha’i, da kyar ya iya barin gidan ma. 
K0 da ya isa gidan su Hajiyarsa ta kawo masa abincin da ta girka cewa ya yi ya koshi. Mamaki ya kamata don tasan ba shi da gurin da yake cin abincin dare tunda matarsa ta haihu sai nan, amma kuma yanzu yace ya koshi, ga shi kuma mutuminsa aka yi, tuwon shinkafa miyar zogale, amma sai ta yi zaton k0 yaje gidan wani . abokin nasa ne ya Ci abinci. 
Sai dai ta kula gaba daya kamar ba ya cikin nutsuwarsa, ta kalle shi da kulawa, tace
“Kamar wani abu yana damunka k0?” 
Ya yi yake yace, “Kaina ke mini ciwo, tashi zan yi na wuce gida ma”. 
‘ Ta girgiza kai, “Ai na ga alama, amma ai ya kamata ka shiga ku gaisa da falmata ka ga yaronka yadda ya kwana k0?” ” 
tana ambaton sunan Falmata yaji wani kunci da takaici a ransa hakan bai hana shi tashi ba, don ba ya son ta balbale shi da fad’a. 
Ta bi shi da kallo cike da zargi ta kula bayan ciwon kan akwai wani abu dake damunsa. amma 
k0 kusa ba ta kawo tunanin Fatila a ranta ba, domin a ganinta abin da ta aikata masa ba zai ba shi damar k0 Kara kallon inda takeba, balle har ya yi tunanin maidata. 
Falmata tana tsakiyar gado tana bai wa Muhammad nono, tana masa wasa domin yaron ya kura mata ido, ta jiyo sallamarsa. Gabanta ya yanke ya fadi, amma haka ta daure ta amsa sallamar tana kokarin kakaro murmushi gami da fadin. 
“Sannu da zuwa”. Bai amsa ba ya hade rai matuka, gami da sarke hannaye a kirji yace “Ya ya yaron naki?” 
Ta kalli Muhd idonta yai narai narai , wato yaron nata ba zai iya fadab sunansa ba, yaushe rabon da ya dauki Muhammad din ma don, ko kallonsa bai yi yanzu kamar ba shine mai tayata rainonsa a can baya ba. 
Da kyar tace Lafiyarshi kalau, sai dai‘ yar mura da yake yi, amma Hajiya ta had‘a masa maganin Hausa,da tafarnuwa ma yaji sauki, amma jiya da daddare ko kama mama kasawa yayi” . 
Bai nuna yaji abin da tace ba. don bai nuna wata damuwa akai ba, sai ma kwave fuska da ya yi. 
ya ce‘, “Ni zan koma sai da safe ke nan k0?” ‘ 
Kafin ta kai ga furta wani abu ya juya ya fice, mamaki mai tsanani ya kuma kamata, anya kuwa Mutarin da ta sani ne mai son dansa da tausayinsa? Tana ba shi labarin dansa ba shi da lafiya, amma bai ko kula ba? 
Tabi shi da kallo har lokacin da ya fice daga dakin, idonta daya cika da kwallah ya fara zubda hawaye mai zafi wannan irin laifi mai girma ta yiwa Mukhtar data cancanci wannan wulakancin? Idan ita tai masa laifi yake mata wannan hukuncin shi kuma Muhammad dan karamin da bai iya aikata laifi ga kowa ba me yayi masa? Tabbas tana cikin matsala, wa zata iya gayawa halin da ta ke ciki? Shin zata sanar da mahaifiyarsa ne ta yi masa fada ya Kara tsanarta da Kulla mata takaici, ko zata ci gaba da rike abin a cikin ranta ne har ya kashe ta? 
Sai kuka ya kwace mata mai ciwo da taba zuciya, yaron kam kamar yasan abin dake faruwa sai ya Kurawa mahaifiyar tasa ido kyar. 
Hajiya Mariya tana can Bangaren abokiyar zamanta suna ‘attauna wata magana da yake ba jimawa tayi ba, ta fito ta nufi sashinta. sai dai hango motar mukhtar da tayi ya fice neya bata 
matukar mamaki, bai taba zuwa gidan ya fita bai yi mata sallama ba, k0 da kuwa yana tsananin ciwo ne, daga yadda ya fice daga gidan a guje ya kara tsoratata, don haka ta yi tsammanin k0 wani abu ya hada shi da matar tasa, da sauri ta nufi dakin da Falmata kcme ciki. 
Falmata kam Allah Ya sanya ta jiyo takun tafiya, don haka da sauri ta hadiye kukanta ta ci gaba da baiwa yaron nono tana goge idonta. 
Hajiya Mariya ta shigo da sauri tana kiran sunanta Ta dago kai tana amsawa da kokarin Boye tsananin damuwar da ta k ciki. . 
Hajiya Mariya tai mata Wani’ kallo na tuhuma tace, Meya hada ki da Muhammad ne?” 
Gaban Falmata ya yanke ya fadi, shi ke nan ya tona mata asiri, maimakon ya sanar da ita abin da tayi masa sai ya je ya gayawa Hajiyar da taje bala’in. sonta da kaunarta, amma sai ta dan daure ta ce. 
“Hajiya wallahi ban san abin da nayi masa ba, tabbas ina sane ba zan aikata masa wani abu ba ‘ mummuna da zai bata masa rai ba, na kula nai ‘ masa laifine tun da naga yana ta shan kamshi, amma 
ina tsoron tambayarsa kada ya kara Bata masa ransa”. 
Tausayin falmata mai tsanani ya kama hajiya, daga jin yadda lafazin dake fita a bakinta, tasan kuka ta sha, wato kunu yake sha mata da hade rai amma tana tsoron tambayarsa don kada ta kuma Bata masa ransa, tabbas samun mace irin Falmata mai biyayya ga miji da aure a wannan zamanin zai yi wuya, son Falmata ya Kara shiga ranta, ta matso ta zauna kusa da ita tace
“K0 daya bai ce kin yi masa laifi ba, ganinsa _ na yi dai ya fice a fusace, na yi zaton ko fada kuka yi, kin tabbatar ba ki yi masa komai ba?” 
Da sauri tace, “Wallahi hajiya ban masa komai ba, sai dai ban sani ba k0 ba da sanina ba”. 
“To shi ne yayi miki na ga har kin yi kuka idonki ya sauya launi zuwa ja; alamar kin yi kuka?” . 
Nan da nan ta kuma shiga damuwa, ta ce, “Wallahi bai mini komai ba, babu abin da yace mini illa ni da nake tunanin na Bata masa ransa”. 
Hajiya ta girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin Falmata a matsayinta na babbar mace da ta jima da sanin halayyar maza har ta gama gano abin dake faruwa. Mulkin mallaka da shariya irin na maza. yake ta mata, ita kuma da yake mai ladabi ce sai take tsoron tambayarsa abin da tayi 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *