MATACCIYAR RAYUWA CHAPTER 7

MATACCIYAR RAYUWA
CHAPTER 7
irin wannan kalaman daga bakin wani ba, don bata taba tsayawa da wani saurayi ba balle har ya dinga gaya mata irin wadannan kalaman. 
Tana jiyo hayaniyar ‘yan kai amarya sun dawo, amma shi ba shi da niyyar tafiya, ya tsareta da surutu, duk sai ta ke jin kamar ba wannan dan uztaz din malam mai darasun ba, sai daya kula dare yaja sannan ya mike tsaye yana fadin
“Toni Falmata zan wuce sai yaushe kenan?” , 
Ta kara qasa da kanta cikin sanyin murya, tace, “Sai ranar da ka dawo ke nan, yaushe zaka dawo?” 
Ya yi dariya, “Au kina son na dawo kusa kenan To kwantar da hankalinki, ina zuwa zan fara shirye-shiryen inda zaki zauna, don haka idan na _ dawo daje zan wuce, zoki amshi wayarki”. 
Ta daga kai tana kallonsa yana tsaye, kirjinta ya tsananta bugawa, suffarsa da Alabura ta taBa suf‘fantawa ta fara dawo mata, ashe ita Alabura ba ta fassara shi dai-dai ba ma. Ta mike ta nufe shi ta mika hannuwanta biyu ya Kara matsowa kusa da ita, duk tsawonta ya shallaketa a tsawo, ta yi kamar ta ja da baya saboda yadda take jinsa kamar zai shige mata, amma ta gaza. Ta mika hannun kuma Yaqi bata wayar sai kallon‘ta kawai yakeyi. 
Bata tabajin kunya irin ta yai ba tayi shirin komawa ta zauna taji ya riqe hannunta. 
“Wai ba zamu yi sallama bane miji da mata nefa mu?” Cikin wata irin rikitacciyar murya yake maganar. 
Sai ta kuma rudewa tayi qasa da kanta, sai kawai taji ya jata jikinsa tayi wata irin ajiyar zuciya sanda ta isa qirjinsa, sai dai kunya ta kuma rufe ta. 
Yayi dan murmushi ya janyeta jin yadda jikinta ke rawa, ya sumbaci kuncinta sannan ya kamo hannunta ya sanya mata wayar tata cikin sanyin murya kamar ba daga bakinsa maganar take . fitowa ba, yace“i love ❤️ you Falmata, ki kula da ‘kanki kafin na dawo, kinji k0?” 
Da kyarta iya daga kai alamar, “toh. Tana kallonsa ta Kasan idonta ya fice daga falon, ta koma ta zauna jabar a kujera ta dafe kai tana maida numfashi dai-dai, ta lumshe idanuwa cike da tsananin farin ciki, ita kuwa wace mace ce ta kai ta sa’a a duniyar nan a yanzu? 
Ta jima a nan sannan ta tashi ta nufi sashinsu kai tsaye dakinta ta wuce ta dauro alwala ta yi sallar isha’i da shafa’i da wutiri, sannan ta yi tilawar da ta saba duk dare da karatun alma,’asum  dinta, sannan ta sanya kayan bacci ta haye gadonta. 
Sai data kasa barci sbd dadi da farin ciki ta kamo filo ta rungume tanajin kamar muntari ne shin ashe daman haka soyayyah take
Kamshin turarebsa ya dinga mata yawo akai tabbas ta yarda da tayi sa,ar miji 
A haka kamar bazai iya soyayyah ba sai maganar ya gana ta fado mata data tabayi wata rana
Ke falmata ki rabu da uztazan nan sunfi kowa iya soyayyah suda suke koyi da sunna soyayyah mai tsafta sukeyi ai inason auren irinsu tunda naga haka wani kawuna yakema antynmu soyayyah yake nuna mata kamar ya lasheta in gaya mikj yayansu biyar amman tare suke wanka Allah, saida na gano hakan 
Ta lumshe idanu tamkar a sannan take kwance a qirjin nasa ranar kam tayi barci mai dadi sa nutsuwa
Shima abangarensa wani irin abu yakeji game da falmata wanda tunda yake bai tabajin hakan akan wata diya mace b a sai ita 
Gaba daya yan kwanakinnan ya manta da wata fatila son falmata ya cika masa zuciya 
Da safe kafin su wuce kanoma saida ya kirata a waya suka gaisa tare dayin hira sama sama sannan suka rabu akan idan ya isa kano zai sake kiranta 
                    KANO TA DABO CI GARI
Tunda ya dira a biRNin Kano ya ji Qirjinsa ya . cika da Qunci, kai tsaye gidansa ya wuce, bayan ya dauko motarsa a gidansu inda suka fara yada zango, wanda ke unguwar Rijiyar Zaki, babban gida ne da ya. sha gini irin na zamani. Maigadi ya wangale masa babbar qofar ya shiga da motar tasa ya sami guri ya ajiye motar, sannan ya kashe ya nufi cikin gida. ‘ ‘ . 
Hajiya Fatila manyan mata masu duniya, . tana zaune a kayataccen falonsu tana kallon tashoshin Turawa, tana sanye da wani dogon wando da riga mai fadi, tana son irin wannan shigar duk da bata fiye yi mata kyau ba, domin irin . gajerun matan nan ne masu kiba, fara tas kamar ka tsagata jini ya fito, amma kuma ba ta da shap balle hips”; bayanta kuma a shafe yake had‘e da mazaunanta, wannan ya sanya Kananan kaya ba sa mata kyau,-domin suna fito mata da ainihin surarta. 
‘Yar gayu ceta karshen zamani, don haka kullum zaka tarar da ita fes-fes ko da daga bacci kuma ta tashi. Tsananin kissa da son da take yiwa mijinta ke sanya ba ya ganin laifinta, don idan ta ganshi kamar zata yi masa sujjada don biyayya, komai yace bata qetarewa, amma kuma yana 
bala’in shakkarta, bai isa ya yi maganar wata mace a gabanta ba koda kuwa mahaitiyarsa ce saboda yadda take kishinsa ta neme shi ta kuma samu. 
Tana Jin shigowarsa ta mike da sauri-sauri, gudu-gudu ta nufe shi, ya ajiye jakarsa ta matafiya (brief case) ya bude hannayensa ta shige da sauri har da ajiyar zuciya, ta ce
‘ “Hubby i miss  you, kamar na yi tsuntsuwa na Bika don dai nasan taro ne na ustazai irinku”. ‘ Ya yi dariya cike da farin ciki domin idan yana gabanta mantawa yake da komai. Ya ce, “Nima sai da naji kamar na dawo na dauke ki, musamman da aka zubo mini abinci na ji ba irin naki ba neba Wani irin sanyin dadi ya cikata, ta yi wata irin wawuyar dariya, tana fadin
“Bari muje ka watsa ruwa ko kaji dadin jikinka ai kun sha hanya”. 
Ta dauki jakar  suka wucé sashinsa tana rungume a kirjinsa, ta raka shi har bandakin sannan ta kullo shi ta dawo. 
Kai tsaye gurin jakarsa ta wuce ta zugéta ta fara binciken da ta saba, amma ba ta ga wani abu ba, don haka tamaida kowane kaya mazauninsa. Ta yi kamar ta dauko wayarsa ta fara bincika amma 
sai taga gwara ta fara zuwa ta kammala zuzzuba
abin da zata zuba cikin abincinsa da ruwan lemonsa. 
Tana fita kuwa wayar ta kama kara yana daga bandakin gabansa ya dinga faduwa, don yasan kiran Falmata ne don ya sanya mata kiranta na daban, don haka ya hanzarta ya fito lokacin sau uku ta kira. Ya dauki wayar da sauri tare da sauke ajiyar zuciya, ya duba ga sako ya shigo kamar uku. 
malam ina fatan kun isa gida lafiya don yanzu inna tayi kirana taje kunje gida ina kirar wayar taka inajin baka kusa 
MATARKA FALMATA 
Da ‘sauri’ ya . fara gage saqon gabansa yana fad‘uwa, sam ya manta baiyi hiding din lambarta ba sai sanda yaso zai kirata da kansa. Yana yin hidding din kuwa Fatila ta shigo babu k0 sallama. 
Jikinsa yana rawa ya wayance, “Ina kika shiga wayata tana ta qara?” Da mamaki akan ’fuskarta tace, “Haba nifa nace saurin naka ya yi yawa, wayeya kiraka ne?” . Yana qokarin nemo dauriya yace, “Wani abokin kasuwanci nane Mr. Josep”. Ta zauna a gefen gado tana kallonsa bata kawo komai a ranta ba. “A binci yana jiranka, k0 sai kA dawo daga masallaci don naji kamar kiran. sallar magriba 
Ko  Da sauri yace, “Bari dai na dawo din”. 
Ya kama sanya kayansa da sauri ya fice yana  riqe da wayoyinsa a hannu. 
Bayan ya dawo daga masallaci shaf ya manta bai kira Falmata kamar yadda ya qudirta ba, sai da yaga sabuwar lamba ta shigo sanda suna tsaka da cin abinci, sannan ya tuna. Gaba d‘aya ya nude, yana son ya datse kiran yana kuma tsoron kada ta gano shi, don haka ya kara wayar a kunnensa, gami da yin sallama. Abinda ya yi niyyar yi shi ne da zarar ya fara jiyo muryarta zai’ fara cewa, “Hello… hello bana jinka, waye ne?” Amma sai ya ji ba muryar mace bace muryar namiji ce sai daga baya ya gano Gwani Muhammad ne, sai ya saki jiki suka kama hira sosai. Sai dai sanda ya soko masa maganar yaushe Falmata zata tare, sai ya yi duru duru yam fadin
“Zan sanar da kai idan ‘lokaci ya yi, wasu abubuwa ne suka sha min kai”. 
Bata fahimci abin da yake nufi ba don haka ko a jikinta, har suka kammala hirar ya kashe wayar. 
Ta tsare shi da ido bayan ya gama, tana fadin“Naji kana kiran Gwani Muhammad, waye shi kuma?” 
Yayi dariya yana qoqarin kai loma bakinsa yace shugaban wata makarantane a maiduguri ta islamiyyah wadanda sukazo kano musabaqa kwanaki 
Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta haushi da hira saidai shi hankalinsa gaba daya yana wajen falmata da akwai yaddah zaiyi da yayi kiranta 
A bangaren falmata kuw taji haushi matuqa somin ta tabbata daga lokacin data kirashi zuwa yanzu yaga kiranta da kuma saqonta amman ya kasa ko biyota ko yana gaban matar tasa ne da akace ta mallake shi!? 
Sai yanzu ta tuna da labarin matar tashi 
Wannan page din half yayi damage kuyi haquri
Gaba daya wunin ranar ta kasa sakewa, ranta a jagule yake kowa ya kalleta yasan tana cikin Bacin rai matuka, don haka kusan a daki ma ta wuni. 
Ta yi shirin kwanciya da wuri yau don k0 abinci ta gaza ci, ta ji wayarta tana kara Daga sautin kid‘an ta gane mai kimn, wani irin farin ciki ya mamayeta amma saita dake taki dauka tayi alkawarin saita raman itama don haka haryakira wayar kusan sau biyar bata d‘auka ba
Shi kam daga Bangarensa duk sai ya damu, tabbas yasan fushi tayi,toshi ya zaiyidaransa ne Dole ya hakura ya tura mata sakon ban hakuri, aransa yana mamakin miskilanci irin nata. Haka ya shiga gidan duk ransa a jagule kamar ya fasakuka. 
Yana shiga Fatila ta zuba masa idanu cike da kulawa take fadin, “Hubby na kamar kana da matsalafa tundaka iso nakula dabakacikin kazar kazar dinka kamar can baya”. 
Ya yi yake, yana fadin, “Kin fara halin naki k0? Sai kace ‘yar jarida, kawai ina ga gajiyar hanya ce, amma ni babu abin dake damuna”. 
Ita ma tayi yaken, amma cikin ranta ba ta yarda ba, yadda yake kaffa-kaffa da wayarsa tunda ya dawo ma ya sanyata shakku, balIe da suka zauna 
hira sai ta dinga kulawa lokuta da dama yakan yi shiru yana tunani, sai tayi magana sannan zai wayance. 
A Bangaren Falmata kuwa, tana jin kiranshi har ya yi ya gama, tana son ta nuna masa irin ciwon da taji ita ma, domin sai‘da ta zubda hawaye don tana matuqar girmama kanta da datajarta ta ya mace, batason duk wani abu dazaiyi kamada wulakanci k0 cin fuska Jin shigowar sakonsa ya sanya ta dauko da sauri ta fara karantawa, ga abin da ya ce
Haba amaryata fushi haka da sauri kin kira bana kusa amman ayi  haquri ki sani dukkan wani motsi kina raina a gobe zan fara nemar mana inda ya dace mu zauna domin muji sadin soyayyarmu babu sanya ido saida safe MMMD
Sai taji ranta ya yi dan sanyi, sannan ta lalubo ma,’anar kalmar da ya qare da ita, wato MMMD, ‘ta yi tsam tana tunani, karshe ta yi hasashen yana nufin Mijinki Muhammad Mukhtar mai Darasu, ba shakka abin da yake nufi kenan. sai ta tsinci kanta da jin haushin kanta da taqi daga wayarsa k0 sautin muryarsa taji. 
Yacc, “Sai da safe”. Wato ba zai iya kiranta ba kada matarshi ta kama shi? Tabbas ta yarda yana 
matukar tsoron matarsa, kamar yadda ake cewa. 
************************
Washcgari tunda sassafe ya nufi daya daga, cikin gidajensa, wadanda yake gini na nan Janbulo, anyi sa’a daman an kusakammala gininsa, don haka tunda asuba dama yaturawa ma’,aikatan sakon sufito,acanma yataddasu,sukadinga gaishe shi da girmamawa. 
Ya amsa kamar yadda ya saba, sannan ya basu umarnin yana son a kammala ginin nan cikin sati biyu, duk abin da ake bukata sun sanar da shi a ‘ shigo da shi yau. 
Shugabansu ya’ lissafa komai yana rubutawa a takarda, sai da ya kammala rubuta komai, sannan ya wuce kamfanoni komai za su shigo musu da shi. 
Daga nan ofis dinsa ya wuce na School of arabic studies wato Legal, domin shi ne mataimakin shugaban makarantar. Sai da ya nutsu ‘sannan ya fara neman layin Falmata. Daman taba zaune ta kurawa wayar ido tana ta kallon agogo har wajen sha biyu bai kirata ba, tana tunanin k0 har lokacin yana gida ne. 
Can kuwa sai ga kiransa, ta dauki wayar da sauri gami da ajiyar zuciya. Cikin sanyin muryarta ta yi masa sallama, ya lumshe ido tare da kwanciya 
Cikin kujera sabodn yadda zakin muryar ta ya ratsashi, cikin kwantar da murya yace. 
“Na yi zaton k0 har yanzu baki huce ba, Fatimatul Zahra, ashe haka kike da miskilanci, kin sake yin damarar rigima?” 
Ta yi dariya kasa-kasa cike da jin dadi, tacw  Kayi haquri, ban ji…” 
Yace “A‘a, kada ki mini karya, ke malama cefa ke dai kawai kinramako? Ina fatan hakanya sanya zuciyarki ta huce” . 
Ta yi ‘yar dariya, “Mutumin nan yana burgeta, akwai shi da iya kalamai da saurin karantar mutum. Ya katse mata tunaninta. 
“To meye labari? Jiya kin yi mafarkina kuwa?” 
Dariya kawai ta keyi, kunya ta hanata cewa komai. Shi kuma dariyar tata ke qara kashe masa dukkan ilahirin sassan jikinsa, domin ji yake kamar tana busa masa sarewa. 
Sun jima suna hira a cikin hirar tasu ne yake
fada mata  abin da ke ransa. “Fatimatul Zahra ina sonki fahimci wani abu, Fatila matata tanada tsananin kishi da rigima, don haka na yanke shawarar bin komai a sannu domin kin san yadda aka yi auran nan. to har zuwa 
Yanzu ban sanar da ita ba, nafison sai komai ya 
dai-daita tukunna, don haka idan ina gida ba zan dinga kiranki ba, kema ina fatan zaki kiyaye lokuttan da kika kula ina gida, k0 wani abu ne ya .taso gwara ki mini message zan gani, kinji k0?” 
Ta yi shiru cike da takaici, gaba daya farin cikin da take ciki ya gushe wacce irin mace ce da shi haka da yake shakkarta? 
Jin ta yi shiru ya sanya yace “Yaya na ji kinyishiru?Komaganar batayimikidadibane? Bana son nayi miki Karya ne, nafison ki gane k0 waye ni Fatimatul Zahra”. 
Cikin kwantar da murya tace, ‘“Lah babu komai fa, duk sanda ka kirawo dai shi kenan, ‘ amma Abba yace na tambaye ka k0 wai ka sanya ranar tariyar, domin ya sanar da masu rakoni din. ” 
Gabansa ya dan buga, amma ya dake, yace, “Kada ki damn, idan na kammala shiri zan sanar da shi, amma fa kafin lokacin dole zan shigo na ganki, don kina ta mini fatalwa a raina” 
Ta yi dariya, a ranta tana fadin, kamar da gaske. Haka nan ya dinga janta da hira har ta saki 
jikinta dai. 
Hajiya Fatila kam duk ta tsargu da yadda yake wani dari-dari da wayarshi, duk da ta bincike wayar gaba daya ba ta ga wani abu da ya yi kama da na mace ba, domin a number falmata Malam Jafar 2 ya sanya, sunan wani amininsa, duk da yayi 
Hidden din lambar sai sanda zai buga mata yake
cirewa, don kada ta yi gangancin kiransa ma suna
Tare, wannan ya sanya bata dago ba, da ace wani 
sabon sunan ya sanya ko na namiji ne sai ta kira taji wanda zai dauka, sannan hankalinta yake kwanciya. 
Rashin kwanciyar hankalin nata ya sanya ta kira wata kawarta Karima, wacce suke cewa iyana
Diyana irin tsinannun kawayen nan ne wadanda babu Allah a gabansu, ba za a ce itace ta koyawa Fatila bin bokaye ba, domin ita ma kusan a nono tasha, sai dai ta taka muhimmiyar rawa 
wajen kara dulmiyar da ita. 
Hamshakiya Hajiya Diyana tana zaune akan kujera tana kallon tasoshin Turawa, kiran qawarta 
ya shigo a wayarta da hamzari ta dauka tana dariya, Babu ko sallama ta hau zance
“Hajiyata ya ya aka yibe? Na manta shaf ban kiraki ba, tun bayan dawowar oga, wai na dan 
barki ne ku sha kola, kin more ne?” 
Fatila taja tsaki tana fadin, “Ki kyale ni da 
shan kola din nan, ki shirya gobe zamu je gurin Burbushe domin na kula akwai wani abu a zuciyar Mukhtar da yake boyc mini. Ina tsoron kada 
maganar mahaifiyarsa’ ta tabbata, kin san , maganarmu ta karshe ta rantse mini, wai ko ina tsafi da kan jaki sai d‘anta ya yi aure. To ban sani ba ko aiki ta farayi akansaba. Jikina yana bani wani abu yana’ shirin faruwa, gwara muje gurin Burbushe mai gani har hanji ya sanar dabi abin dake shirin faruwa”. 
Diyana tace “Kin yi gaskiya tawan, ai ba na son abu da sanya, ba irin wannan sanyar ce ta 
Kwari Helin ba? tana kallo yanzu Wata ta aure mata miji, wai kuma har da haihuwa, mtssss!” Taja tsaki, “Idan ni ce da tuni na shaketa ai ta tafi barzahu.. ” 
“Ki daina tunanin idan kece ma, domin ni ba zan yarda ta shigo ba balle har lissafina ya qaeu bama, shi da mace sai dai a kabari, don ko na mutu ya yi karya ya kalli wata da sunan so, ni kad‘ai ce abar son Mukhtar”. 
Diyana ta fashe da dariya; “Ina son irin haka, shi yasa kullum nake sonki wallahi qawalli, qarfe nawa za mu shiga gurin nasa goben?” 
“Ai da safe dole zamu shiga, don kada mu tadda layi k0?” 
Da wannan suka yi sallama. 
Shi kam gogan aikin gida yake bilhakki‘ don haka ko da ya tashi yau ma da sassafe ya fice
hakan kuwa ya yi mata dai-dai, don haka ta zari mota sai gidan Diyana suka nufi gurin Boka Burbushe. 
Da wani ne wanda bai saba irin Batansu ba da zaiji tsoron shiga surkukin dajin da suka shiga, amma su ko a jikinsu, sun saba. Haka nan suka dage zannuwansu suka dinga tsallake bishiyoyin Kaya da ciyayi suka kutsa surkukin dajin. Can cikin daji cikin wata bukka mai kama da ta aljanu yake zaune, ruwa da iska ba sa sauya masa gurin zama. 
Suka shiga da ihu kamar yadda ka’ idar gurin nasa ta ke suka sami guri suka tsugunna, jikinsu yana kyarma kamar sun ga wani mayunwacin zaki. Diyana ce ta so yin magana, amma ya dakatar da ita yana dariya mai ban tsoro, muninsa ya sake fitowa domin Katone mai Kira irin ta Samudawa da qaton kai da ciki, ga shi bakikkirin amma komai nasa kato ne. ‘ 
Kana ga hancinsa da ya kusa mamaye fuskar tasa, zuwa idanunsa da kamar za su zazzago bare bakinsa mai kama da kofar gari. Bai taba wanka ba, domin yana cikin alkawarinsa da aljanun da suke taimakonsa akan karyar tasa, don haka kullum idan ka shiga bukkar tasa zaka ji kamar an kashe mushe don wari, balle gashinsa baya aski, yawan zama a daji ya sanya gaba daya kamanninsa suka 
Bari mu dakata anan labari fa na tafiya yaddah ya kamata sai naji daga gareku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *