MATAR DOCTOR CHAPTER B KARSHE

 MATAR DOCTOR CHAPTER B KARSHE

_Monday_

Da wurwuri Janan ta shirya ta wuce asibiti sbd bata so Dr.Godwin ya riga ta ko ya fara tsareta da sleepy eyes din shi.. Cikin kankanin lokaci ta shigo asibitin ta ko ci sa’a ta riga duk yan officr din su zuwa  amma abun haushi a rufe kofar take ko da tai ma masu kula da wajen magana se cewa sukayi “ai yanzu da key din office Dr.G yake tafia”
Cike da jin haushi ta zauna akan kujeran da patients suke zama…..

Yau Dr.Godwin cikin mulki da miskilanci ya shigo asibitin as usual yana sanye da suit da bakin glasses tunda ya shigo be cewa kowa komai har Janan dake zaune be kalle ta ba ganin haka ya sa ita ma taki gaida shi tayi kamar bata ganshi ba.. Ta cikin glasses dinshi ya kalleta a ran shi yace “wow! She looks so cute! Yau ta riga kowa zuwa abun is surprising ko dai dama da gangan take zuwa latti? Anyways, ita ta san dalilin zuwa da wuri yau”
Ya bude office din yayi shigewan shi ciki… Itama ta bi bayan shi…

Can daga baya su Ruth suka shigo a tare yau kayan aikin nasu da gani sabo suka dinka ya matse su ga kirjin su a waje fuska tasha heavy make-up sunyi fixing nails da eyelashes se yanga suke kamar baza su taka kasa ba… Table din Dr.Godwin suka nufa harda dan rankwafawa suna gaida shi kamar ance ya dago idon shi ya ajiye a kansu cikin sauri ya cire glasses dinshi, Jessica harda wani kara jijjiga jiki duk a tunanin ta ganin daya musu ne ya sa shi cire glasses dan ya gansu da kyau…. Cikin tsawa yace “what d hell is this? R u girls insane? Wani irin dressing ne haka? Zaku zo asibiti nd u r dressing shabbily? Party zaku je ko club? Ku kalli kan ku! U r looking so disgusting! Daga yau in kuka kara dressing haka u will see d other side of me”  ya buga tsaki “mitchwwwww will u get out of my sight u bunch of idiots?

Jiki na rawa suka koma wajen zaman su duk sun razana da yanda yayi musu..

Janan na daga gefe se faman daria kasa kasa take yi a ranta tace “daidan ku kenan”

Cike da bacin rai Dr.Godwin ya mike idon shi sun kada sunyi jazir ya bar office din don yau su Ruth sun kai shi bango

Seda yayi kusan minti 30 sannan ya dawo cikin office din yana chewing gum yana zama wani cardiologist (likitan zucia)  Dr.Bichi ya shigo da sauri yace “Surgeon G pls muna neman taimakon ka an kawo mana patient yanzu tana emergency room kuma akwai bukatan yi mata operation… Cikin azama Dr.Godwin ya miqe tare da fadin bani secs 10 in canza kaya na… Inner room na office din ya shiga ciki seconds 15 se gashi sanye da kayan aiki yace “muje ko?

Dr.Bichi yace “we need a nurse wacce zata taimaka mana”.. Da sauri Ruth da Jessica suka tashi wani kallo Dr.Godwin ya watsa musu yace  “ko a mafarki kar kuyi zaton zaku bi ni theater room da wannan kayan, ku zauna kuyi gadin office dama shine daidai daku….
Ke!! Ki biyo ni in kin ga dama” yana gama fadan haka ya fita abin shi
Dr.Bichi yace ma Janan “muje time yana wuce wa”
Ba dan taso ba ta bisu dan ke! din da Dr.Godwin yace mata ya bata haushi…

Emergency room suka nufa nan taga baby Hanayya ce jini na fita ta baki da hanci Dr.Godwin na kanta yana yan gwaje gwaje suna shigo yace “mu wuce theater room yanzu yanzu”

Sallati kawai Janan keyi nan da nan idon ta ya ciko da kwalla tausayin yarinyar ya kamata…. Suna shiga dakin theatre suka fara aikin su Janan haka ta dinga yi kamar kwai ya fashe mata a ciki.. Duk abun da take yi idon Dr.Godwin na kanta se yaga sun kusa hada ido ze kawar da kai gefe…

Sun dau awa har 4 cikin dakin theatre kafin suka fito duk sun jike da zufa cikin sauri iyayen suka yo kan su suna tambayan jikin yarinyar su… Be ce musu komai ba ya wuce zuwa office din shi  Janan na binshi a baya suna jerowa tare da Maman Hanayya…
Suna shiga suka zazzauna ya fara musu bayani kamar haka “abunda ke damun ta shine dai ciwon zucian dana fada muku gwaje gwaje ya nuna cewa bugun zuciar ta is nt normal yana bugawa fiye da yanda ya kamata sakamakon haka se ya haifar mata da taruwan jini a cikin zuciar domin jinin baya circulating ya daskare waje daya har ya kumbura zuciar sannan jinin daya rasa hanyar wuce wa se ya tunkudo mata ta baki da hanci amma yanzu an gama operation lfya sedai mu jira ta farfado muga yanda jikin yake”

Ajiyan zucia suka sauke duk tausayin Hanayya ya kama su…

Bayan awa hudu ta farfado Alhamdulillah sedai bazata ci komai ba sbd ana mata karin ruwa da jini se sun kare tukunna……

*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [2/5, 8:51 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰 *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿�

_Dedicated this page to my one nd only Bro. Even though u will nt read this novel but u deserve a dedication from me. U r more than a Brother to me u r part of my life_
_I love u so much_   *_Abdurrasheed Zubairu Aliyu_*
_# MY STRAWBERRY_# a special name 4 u鉂も潱鉂�

*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒

            8鈨�8鈨�

_Bayan wata 1 da sati 3_

Haka asibitin Barau Dikko ya zama talk of d town domin aiki tukuru akeyi a cikin sa gashi likitoci da Nurses sun san aikin su yanzu Janan ta dena kuka in za ayi ma mutum operation sedai har yanzu in taga za ayi se tausayi ya kamata..
Dr.Godwin yayi kaurin suna domin kusan ko ina an san _’Surgeon G’ d youngest must chamming nd active Doctor_…

          
          *************

Shirye shirye ya kan kama sbd saukan su Janan ya matso saura sati daya.. Sun raba kati ma Nurses waenda suke mutunci har da Dr.Magaji basu mance da shi ba sun kai ma.. Amma Janan ta hana Dr.Godwin katin dan a ganin ta babu anfanin bashi…

Cikin lokacin nan aka sallami patients din da aka ma operation domin jikin su yayi kyau sosai.. Kuma Maman Hanayya tayi alkwarin zuwa wajen daukan Janan

Ana gobe sauka su Janan suka karbo kayan su gun tela ita da Eesher sun yi kitso se kuma jan lalle da aka masu se yamma likis suka dawo Eesher ta wuce gidan su..
Yan uwan Ummiey na Gombe har sun zazzo maza da mata se kuma dangin Abbiey na Makarfi suma haka zuka ciko  mota suka zo se aiki ake yi …

Washe gari tun asuba ta tashi ta fara shi ga wani nishadi da farin ciki daya ke ratsa duk jikin ta ko abinci ta kasa ci sbd doki kayan saukan su fari kal tasa tana sa socks wayar ta ta fara ringing ko bata duba ba tasan Imran ne bayan sun gaisa yake mata fatan alkhairi da kuma addua’a basu dade suna waya ba suka yi sallama sbd kar ta makara.. Tana ajiye wayar taji alaman sako ya shigo kamar kar ta duba se kuma ta dau wayar ta zauna bakin gado tare da bude msg din.. Ga abinda sakon ya kunsa
*_Congratulations on ur graduation.. I wish u all d best Baby girl_*
Ta karanta text din yafi so a kirga tana mamakin wanda ya turo mata wannan sakon harda ce mata Baby girl ko dai mistake ne ta fada a ranta ganin tunani ba zai mata anfani ba ya sa ta tashi ta karasa shirin ta…..

            ***********

Daya bayan daya aka kira su suka fara karatu wajen a cike yake da jama’a maza da mata Aisha na cikin yan farko da suka fara karatu can daga baya aka kira Janan Pharouk Makarfi kowa yayi shiru nan ta fara karatu da muryan ta me zaqin gaske cikin suratul Bakrah shafin karshe cikin qira’ar Sheikh Sudais.. Yanda take karatun ya sanyaya zukatan masu sauraro dayawa seda suka zubda hawaye domin dadin karatun ta ita kanta karfin hali take yi amma ji take kamar ta fashe da kuka.. Tana kaiwa karshe wajen ya kaure da kabbara…
Seda aka gama da yan sanawiyya sannan aka dawo kan mahaddata nan fa aka kowa ya fito yayi nashi karatu Janan aka sake kira ta fito tayi karatu cikin suratul Ahzab da sautin Sheikh Shureim nan fa ta nuna kwarewar ta domin tana son kira’ar kuma ta iya sosai…

An basu kyaututtuka da yawa domin Janan ta karbi kyauta kusan guda 5 ciki harda wacce tafi kowa ladabi da kuma tsafta… Sunyi hotuna sosai se faman kukan rabuwa suke da juna… Dr.Magaji da iyalin shi sun zo harda kyauta suka ma Eesher da Janan.. Mmn Hanayya ma tazo kuma ta fada ma Janan har gida zata biya se yamma Baban Hanayya ze zo ya dauke su

Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan…..

Shin ko waye wannan saurayi ko ince mutumin??

_Godia da jin jina gare ku masoya na ngd da adduo’in ku Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci_
_Allah ya biya muku bukatun ku na alkhairi_
_Sai kun sake jina_馃槈馃槈

*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [3/4, 4:10 PM] Rukky Bae馃槒馃槒馃槒鉂b潳鉂�: 鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も殰鉂b殰鉂も潱鈿溾潳 *_MATAR DOCTOR_*鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱鈿溾潳鈿溾潱

*_Few days to my birthday in shaa Allah_*馃拑馃懐鈥嶁檪馃懐鈥嶁檪馃懐馃拑馃懐馃懐馃拑馃拑

*_Rukky Bae_*馃槒馃槒馃槒

_Dedicated this page to My pretty nd Maman Abulkhyry_馃槝馃槝
_Thanks 4 ur support_

              8鈨�9鈨�

Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan….

A hankali ta fara takawa zuwa gaban motar gab da zata karasa taji daga baya ance “Angel ina zaki je?

Da sauri ta waigo don jin an kirata da Angel… Imran ta gani a tsaye sanye da sky blue caftan.. Murmushi tayi mashi tace “Nurul-qalbee ashe kazo.. Ban ganka ba se yanzu”

Yace “Haba ni na isa in zo yanzu? Saukan Angel guda! Tun kafin ayi nisa da karatu nazo sbd kar nai missing karatun ki”

Murmushi tayi seda fararen hakoranta suka bayyana..

Mai daukan hoto ne yazo wuce wa, da sauri Imran ya kira shi yace “zo ka dauke mu nida Angel dina”

Karasowa yayi ya dinga daukan su hotuna kala kala

Tari Janan ta fara yi sbd kuran da yake tashi wajen duk ya kaure da kura.. Hango motar nan suka yi tayi nisa wanda ke ciki se gudu yake kamar ze tashi sama duk ya tayar da kura.. Imran yayi saurin mika mata ruwan goran dake hannun shi na mata sannu..
Se da tarin ya lafa mata sannan yace tazo su wuce ya kai ta gida lokaci yana kurewa ga shi akwai walima a gidan.. Ba musu ta bishi suka fara tafiya duk an watse saura mutane yan kadan…

Mintuna 30 ya kai su gidan su Janan daga can nesa kadan da gidan yayi parking ji yake kamar kar ta sauka amma ba yanda ze yi.. Handle din kofan ta bude har ta fitar da kafa daya waje yace “oops! Naso in manta. Hannu ya miqa ya dakko wasu manyan ledoji guda 4 yace “Angel ga nawa gift din Allah ya sanya ma karatun ki albarka”

Tace “Ameen nagode Nurul-qalbee” ..

Ya cigaba “Allah ya mallaka min ke a matsayin mata uwa ga ‘ya’yana”

Shiru tayi kanta a kasa bata amsa ba..

Yace “Angel baki amsa ba”

Da sauri ta dauki ledojin ko sallama bata mishi ba sbd kunya..

Murmushi yayi yana girgiza kai shi gaba daya mamakin irin kunyarta yake.. Yana murmushi yayi reverse ya bar layin..

Tana shiga gida ta fara neman Ummiey bata ganta ba… Nan ta fara kiranta “Ummiey! Ummiey!!
Muryan ta daga baya tace “oh ni wannan kira kamar makauniya ko ance miki na bata ne kike min irin kiran nan”
Dariya Janan tayi tace “tor ba na shigo bane ban ganki ba se neman ki nake yi’

Ummiey tace “gani ai yanzu kin ganni”
Hannun ta Janan taja suka wuce dakin Ummiey.. Nan ta mika mata ledojin da Imran ya bata..
Kallon ta Ummiey tayi tace “wannan daga ina kuma?

Janan ta fara inda inda “Am.. am.. Yanzu ya bani wai gift din sauka..

Murmushi Ummiey tayi dan ta gano wanda ya ba Janan din.. “Tor Allah ya saka da alkhairi”

Kayan Ummiey ta fito dasu nan suka ga atamfofi leda daya se cosmetics leda daya takalma da Hijjab leda daya se ledan karshe tarkacen chocolates da sweets..

Albarka Ummiey ta sama Imran sannan tace ma Janan “tashi ga kayayya kin ki a cikin wardrobe an karbo daga dinki ki shirya mutane sun taru” tana gama fadan haka ta bar dakin ita kuma Janan ta shiga bayi ta watsa ruwa… A gurguje ta shirya bata wani bata lokaci ba wajen kwalliya dama batayi, kwalli, powder sai lip balm kawai tashafa se dauri me kyau da tayi… Ba karamin kyau tayi ba.. Tana fitowo mutane suka fara fadin “Tubarakallah Ma shaa Allah”……

An ci ansha sannan anyi rabon souvenirs sosai tamkar ana biki haka Janan tayi ta canza kaya ana ta hotuna…

Alhamdulillah taro ya tashi lfya gwanin ban sha’awa ga tarin gifts da mutane keta kawowa harda sisters din Imran sun zo da nasu kyaututtukan se yaba Janan suke farat daya ta shiga ran su…. Se yamma mutane suka fara watsewa harda Maman Hanayya..

Bayan Sallan Magrib Janan da Ummiey zaune a parlor wani yaro yayi sallama suka amsa.. Wata karamar jan jaka ya miqa ma Janan tare da fadin “gashi wai in kawo miki inji wani a waje”

“Wani a waje kuma?? Janan ta fada cike da mamaki..

Yaron yace  “eh a mota yazo yana bani kuma ya wuce”

Ummiey tace “ko dai Imran ne? Ki kira shi kiji”

Yaron bema tsaya jira a kira ba ya wuce abin shi

Tana kokarin kiran shi se ga kiran nashi ya shigo “bayan sun gaisa se take mishi godia da hidima..

Albarka ta sama Imran sannan tace ma Janan “tashi ga kayayya kin ki a cikin wardrobe an karbo daga dinki ki shirya mutane sun taru” tana gama fadan haka ta bar dakin ita kuma Janan ta shiga bayi ta watsa ruwa… A gurguje ta shirya bata wani bata lokaci ba wajen kwalliya dama batayi kwalli, powder sai lip balm kawai tashafa se dauri me kyau da datayi… Ba karamin kyau tayi ba.. Tana fitowo mutane suka fara fadin “Tubarakallah Ma shaa Allah”……

An ci ansha sannan anyi rabon souvenirs sosai tamkar ana biki haka Janan tayi ta canza kaya ana ta hotuna

Alhamdulillah taro ya tashi lfya gwanin ban sha’awa ga tarin gifts da mutane keta kawowa harda sisters din Imran sun zo da nasu kyaututtukan se yaba Janan suke farat daya ta shiga ran su….

Bayan Sallan Magrib Janan da Ummiey zaune a parlor wani yaro yayi sallama suka amsa.. Wata karamar jan jaka ya miqa ma Janan tare da fadin “gashi wai in kawo miki inji wani a waje”

“Wani a waje kuma?? Janan ta fada cike da mamaki..

Yaron yace  “eh a mota yazo yana bani kuma ya wuce”

Ummiey tace “ko dai Imran ne? Ki kira shi kiji”

Tana kokarin kiran shi se ga kiran nashi ya shigo “bayan sun gaisa se take mishi godia da hidima….

Yace “haba Angel ki dena gode min.. Naso in zo se kuma aiki ya rike ni tunda na bar wajen ki ina asibiti har yanzu ban dawo gida ba ma”

Shiru tayi hakan ya tabbatar mata ba shi bane ya kawo mata sako yanzu.. Katseta yayi daga shirun “Angel zan kiraki anjima I love u”.. Dinggg ya katse wayar…

“Ummiey bashi ya aiko da sakon ba”

Ummiey tace “Tor bude ki ga mene ne a ciki”

Envelop ta gani tana bude wa taga bandir din 500 ( dubu Hamsin) abun ya bata mamaki gashi bata san wanda ya aiko mata da shi ba.. Tashi tayi zata miqa ma Ummiey kudin wani farin soft tissue paper ya fado kasa.. Dauka tayi anyi rubutu da bakin biro yayi kyau sosai kamar anyi typing da computer..

Ga abun da aka rubuta kamar haka…..

*_Rukky Bae_*馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂b潱鉂b潱鉂b潱鉂p煍扁殰鉂b潳馃敱鈿滒煍扁潳鉂も潳鉂� *MATAR DOCTOR* 鉂も潱鉂b潳鉂も潱鉂b潱鉂b潳鉂も潳鉂も潱鉂ゐ煍�

_*RukkyBae*_馃槒馃槒

_Bismillahirrahmanirraheem_

_Yabo da godia sun tabbata ga Ubangijin halittu baki daya_!

Da farko dai karfin in cigaba da rubuta wannan littafi mai farin jini se na fara da baku hakuri Masoyana kuma mabiya wannan littafi! Dalilin Jina shiru ya faru ne sakamakon sace min wayar da aka yi a makaranta.. Nasan cewa kun jini shiru na lokaci mai tsawo wanda har wasu sun fara tunanin ko na daina rubuta *MATAR DOCTOR* ne wasu kuma suka dinga fadin wai basira ce ta kare min shiyasa na kasa cigaba da rubutun鈽衡樅… Wannan shine farkon novel din dana fara rubutawa kuma Bayan shi akwai wanda da izinin Allah zan rubuta wanda nake kyautata zaton se yafi nishadantar daku fiye da *MATAR DOCTOR*! In shaa Allah….

Ina so ku kara min hakuri akan yanda kuke min tun baya kuma ku cigaba da bani kwarin gwiwa tare da tayani da addu’a..
Ina godia a gare ku mai tarin yawa kuma ku sani RukkyBae na son ku fiye da yanda kuke sona鉂p煉� Naga Kiran ku da sakonnin ku masu tarin yawa. Allah ya bar zumunci ya bar mu tare….

Can daga gefe ta hango wani zaune kan motar shi yana share fuska da hanky daga baya kuma ya shiga cikin mota ya daura kai akan steering motan…..

Shin ko waye wannan saurayi ko ince mutumin??

_*CONTINUATION*_
(CIGABA)

     *** 8鈨�9鈨�****

   Wannan page din naku ne Masoyana 馃槃鉂b潳馃槝馃槏馃拫

A hankali ta karasa gaban motar sannan tayi sallama.. Cikin hanzari ya dago suka hada ido, Dr. Godwin ta gani da sauri taja baya tana runtse ido, bude motar yayi ya fito hade da sanya hannayen sa biyu cikin aljihun wandon shi yana kare mata kallo kafin yace

“Monster kika gani ne da kika wani tsorata? Ko kuma nayi kama da dodo ne? A tare ya jero mata waennan tambayoyin.

Maimakon ta bashi amsa se ta jefa mishi tata tambayar da fadin “Kai ka aika min da sako?

Harara ya watsa mata sannan yace “amma dai kin san na tsani inyi tambaya instead of a bani amsa se a sake min wata tambayar ko?
Yi tayi kamar bata ji shi ba, jin shirun yayi yawa ya sake fadin

“anyway congrats kuma ba don halinki nazo ba kawai naga dama ne”

Murmushin takaici tayi tana mamakin girman kai irin nashi kafin ta miqa mishi envelope din tace “gashi bana so ka barshi” ta ajiye a saman motan ta juya zata daga kafa kenan ya take bayan takalmin ta tayi gaba zata fadi yayi saurin riqe gefen hijjab dinta, da sauri ta qabe mishi hannu cike da masifa tace

“miye haka kuma?
Gira daya ya daga yace
“ban sani ba, ni bana kyauta a dawo min dashi in karba sbd haka zoki dauka in kinga dama ki sa a dustbin I don’t care amma baki isa in amsa ba kuma naji ana fada a addinin ku ba a maida hannun kyauta baya so yanzu the decision is urs in kinga zaki karba oho in ma bazaki amsa ba duk ke kika jiyo stubborn girl”

Komawa tayi ta dauka ta murguda mishi baki tace kasakasa “se iyayin tsiya ko ana kyauta dole ne ban sani ba kuma bani bace stubborn girl”

“me kike cewa? Ya tambayeta

Tace  “ban ce komai ba”,
ya jita sarai amma so yake ta sake maimatawa

“yaushe zaki dawo asibiti? Ya sake tambayanta

“Upper week” ta bashi amsa

“Baki isa ba goben nan zaki dawo aiki kuma it’s a command”

Wani kallon uku saura kwata tayi mishi,

“hope ba dani kike ba”

“‘Da kai nake yi kuma ba zan zo goben ba”

“Ni kike fada ma haka

Batayi zaton yaji mai tace ba
Ai da gudu tayi kofar gida seda taga tasa kafa daya a ciki hannu daya a kugu daya a jikin side na gate din sannan ta juyo ta murguda baki tace “Yes!

Cikin zafin nama ya biyota ta juya zata shige ciki warwaron ta mai chain ya maqale a jikin gate din ba shiri ta dawo    baya tana kokarin cirewa amma ta kasa gashi ya matse mata hannu kuma ga Dr. Godwin ya nufota ta san in ya kamata ta gama yawo, a hankali ya  cigaba da matsowa tun kafin ya karaso ta fara bashi hakuri, abun yaso bashi daria amma ya dake, hannun rigarshi ya fara nadewa kamar mai shirin dambe, tana ganin haka ta rufe ido tana jiran saukan mari, ji tayi kamar ana hura mata iska a hannu da sauri ta bude ido akan hannun nata, Dr. Godwin ta gani ya sa bakin shi yana kokarin cire mata ya kusa minti daya yana kokarin cire mata yana gama cirewa maimakon ya dago sai ya manna mata peck a hannu tare da cizon ta da sauri ta cire hannun tana yarfewa be gama dagowa ba tace
“ban gode ba”
ta shige gida da sauri ko waigowa bata sake yi ba, girgiza kai yayi yana daria ya koma ya tada mota amma be dena daria ba yana tuno yanayin ta da yanda take murguda baki komai tayi burge shi take yi a haka har ya kai gida cikin farin ciki da kewar Janan yana tuno hannun ta me laushi…..

Tana shiga gida seda ta dan tsaya ta kalli hannun ta ga shaidan hakoran san a jiki dan guntun tsaki taja tace mugu sannan ta shiga parlor ta fadama Ummiey Dr. Godwin ne ya bata a matsayin gift! Murmushi Ummiey tayi hade da godia tana fadin “ai kudin sunyi yawa”

Janan ta ce wallahi nima da kyar na karba gashi ki ajiye a wajen ki babu abunda zan yi da su”
Aa ki rike a wajen ki ko da abunda za kiyi dasu koda a asibiti ne ki taimakawa gajiyayyu

Toh Ummiey tace sannan tayi hanyar dakin ta har ta kusa shiga Ummiey tace yaushe yace ki koma bakin aiki?
“‘Wai gobe” ta ba ta amsa

“Haba dai gobe ai ya kamata ki dan huta gajia kafin ki koma”

A tou ai ba inda zani tayi shigawar daki….

*_RukkyBae_*馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂b潱鉂も潱鉂も潱鉂も潱鉂も潱鉂も潱鉂b潳鉂b潳鉂b潳 *MATAR DOCTOR*馃枻鈾b櫊鈾モ櫊鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾�

Rukkybae馃槒馃槒馃槒

This page is urs my CUPCAKE .. Ina sonki fiye da yanda nake son kaina cuz ke ce Best Frnd dina kuma abokiyar shawarata.. Muna fada amma ba wanda ya isa ya shiga tsakanin mu.. I can’t imagine life without u Safiyya Zubairu Aliyu (Sophie_Luv) I love you more than chocolate Big Sis鈾ヰ煉� my partner in Gulma 馃槀馃ぃ

***9鈨�0鈨�***

Tunda Janan ta shiga daki tayi sallah ta watsa ruwa zata kwanta kenan sega kiran Imran ya shigo sun dade suna waya daga bisani sukayi sallama ba don sun gaji ba se dan ya bar ta tayi bacci…

Washe Gari tunda ta koma bacci da asuba ba ita ta tashi ba se karfe 10 na safe shima ringing din wayar ta ta tashe ta, ta janyo cikin bacci ido rufe ta dauka sallama bisa tsarinta tayi tana da fadin waye pls a dan shagwabe
Jin muryar baccin ta da kuma yar shagwaban ta ya sa shi ajiyar zucia yana fadin ohh wato bacci ma kike yi kin ma manta nace yau ki dawo wajen aiki ko?
Nan take idon ta ya wartsake ta yaye bargon jikin ta tare da duro da duk kafafunta kasa tana sake murza idanuwa   cikin jin haushi yace “how dare u ina miki magana kinyi shiru kuma kina Jina!
Sorry tace irin na ko a jiki na din nan, mitchwww yaja tsaki “oya ki shirya yanzu ki taho,
kamar za tayi kuka tace “ka bar in dan huta Allah yau bazan iya zuwa ba cuz am extremely tired kuma jiki na is weak ko nazo nasan ba zan iya aikin komai ba help me plss! Yanda tayi maganan ta kashe mishi jiki amma se ya basar yace “point of correction Miss whatever u call ur self I don’t help kuma bazan taba taimako ba”
Kayi hakuri naji bazan sake neman taimakon ka ba amma ka bari ko da nan da 4 days ne se in dawo”
What! Are u insane? Ni kike ba ma command? Kuma da kike cewa in baki 4 days idan supervisors suka zo daga Ministry of Health me kike so in fada musu? Kin san dai bana taimako kuma bana karya sbd haka daga kanki bazan fara ba, na baki nan da 2hrs ki taho asibiti!
Be jira amsarta ba ya kashe wayan shi,
Cikin ranta tace masifaffen Likita kawai wallahi ba inda zani se gobe in Allah ya kaimu in kaga dama ka tsire ni karshen hukunci kenan….

Bayi ta shiga tayi wanka ta wanke bakin ta sannan ta fito ta sa fitted gown na atamfa tayi kyau kayan sun mata kyau. Palor ta fito taga duk kowa ya tashi har sunyi brkfst ita kadai ya rage, se da ta gaida kowa sannan ta wuce kitchen ta zubo pankasau da kunun gyada ta dawo ta fara ci seda ta koshi sannan ta maida kayan kitchen ta wanko hannu ta dawo ta zauna aka cigaba da hira inda yan Makarfi suka ce gobe da rana za su tafi su kuma yan Gombe suka ce suma gobe zasu tafi amma da bayan sallan asubahi sbd garin nasu da nisa…

Seda aka kara gyara gidan sannan kowa ya samu natsuwa..
Da yamma Imran ya kirata yace ze zo bayan sallan Isha’i ya gaida baki kafin su tafi,  toh kawai tace amma bata san yanda zata fada musu ba, dabara ce ta fado mata ta tura ma Ummiey text, Ummiey na gani tayi murmushi sannan ta fada musu surukin su zai zo gaishe su.

Kamar yanda yayi alkwari se gashi yazo Khaleel ne ya shigo dashi sbd Janan tace ba zata iya ba.
Cikin ladabi ya gaishe su nanfa daki ya kacame da gaishe gaishe aka cika gaban shi da kayan ciye ciye da shayeshaye ya dan ci ko ba laifi kuma ya saki jiki an dan taba hira da zai tafi ya ajiye musu kudi tare da yi musu Allah ya kiyaye hanya.. Haka ya tafi ba tare da yaga Angel din tashi se dai a waya suka yi magana.

Washe Gari ba da wuri ta tafi asibiti ba sbd Imran dinta yace ta jira shi yau shi da kanshi zai kai ta, se wajajen 8:30am yazo ta fada ma Ummiey kafin ta wuce ta same shi sanye da half jampa kalar coffee brown haka hula da takalmin shi duk kalar coffee brown din ce yayi kyau sosai.. Janan na ganin shi ta saki murmushi sbd Imran jarumin namiji ne ga nagarta da kamala seda ta gaishe shi ya amsa sannan ya bude mata gaban mota seda ta zauna ya rufe kafin shima ya koma mazaunin sa ya shiga suka fara tafiya tace   “My King kayi kyau sosai” Murmushi yayi yace Angel kin fini yin kyau kayan asibitin nan kamar dan ke ake yi su kuma banda abin ki namiji ai bashi da wani kyau mata ne aka sani masu kyau.
Haka dai ka fada amma akwaio kyawawa a maza kuma kaima kana cikin su domin kai cikakken Namiji ne kuma daya tamkar da dubu. Yaji dadi sosai kuma ya kara tabbatar daya samu mace ta gari, haka sukayi ta hira har ya kaita kofan asibiti yace Angel yau karki sai komai zan kawo miki lunch kinji,
“Haba Mijina kar… Shhhh ya katseta bana son jin komai kuma fa kin kira ni da Mijin ki karki manta hakkin miji ne ya ciyar da matar shi sbd haka bana son kice komai.. Shikenan Nurulqalb nagode, kallon ta yayi da wani irin salo sannan yace ni ba godia nake so ba
Toh me kake so? Ta tambaye shi
Kin fini sanin abunda nake so, hannun biyu ta rufe fuska dasu sannan tace Ina son ka
Daria yayi yace nima Ina son ki amma wannan kunyar ya kamata ace kin rage shi ko sai munyi aure tukunna zaki de ne? Da sauri ta wuce tana daria ba tare data bashi amsa ba se dai ta dago mishi hanni..
Ina sonki Angel ya fada a hankali tukunna yaja motar shi ya wuce

Tun tsayuwar su Dr. Godwin na kallon su ta saman window ji yake zuciyar shi na wani irin daci kamar ya sauka yaje ya janyo ta ganin yanda take ma wani murmushi be ga wucewar ta ba sbd ya lula duniyar tunani se ji yayi kamar mutum ya bude kofa yana juyowa daidai ta rufe kofar ta juyo suka hada wani kallo yayi mata wanda ita ma bata san nufin shi ba.. Kamar ba za tayi magana ba a hankali tace “Morning! Be kulata ba har ta gaji da tsayuwa taje tayi zaman ta..

Kallon ta kawai yake yi kan shi ya kwance yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata.. Can wata dabara ta fado mishi yace  “ke! Zo nan! Ba musu taje yayi rubuce rubucen shi sannan ya miqa mata hade da kudi yace kiyi sauri ki siyo min maganin nan dana rubuta kiyi sauri karki bata min lokaci.
Kin karba tayi, cikin hasala yace zaki amsa ko sai ranki ya baci?
Ka aiki masinja mana ai ni aiki na zo ba aike ba ta fada adan tsorace.. Wani mahaukacin tsawa ya daka mata wanda seda ta toshe kunnuwan ta cike da gigita.
Karba nace! kuma saura time din da na baki a cikin zuciyata ya cika baki dawo ba kiga yanda zanyi da ke! .. Jiki a sanyaye idanuwanta sun ciko da kwalla ta karba ta fita…
Jingina kanshi yayi a jikin kujera ya runtse ido hade da yamutsa gashin kanshi  “I’m sorry Baby girl I don’t mean to hurt u kece kika yi forcing dina na ji haushin ki har na baki aiken da zaki sha wahala cuz baa samun maganin a garin nan se a Egypt ko Lagos.. Kiyi hakuri dole ne inyi punishing din ki sbd in samu peace of mind”

Marasa lfya ne suka fara shigowa yana duba su tare da basu appointment time to time yana duba agogon dake maqale a hannun shi yanzu after 11 kuma tun tara da rabi ya aike ta har yanzu shiru, masinja ya kira yana tambayar shi patients nawa ne a waje sukayi saura?
6 ne ranka shi dade
Good! Kace musu am nt in the mood da zan iya cigaba da duba su kace musu gobe su dawo”
Masinja ze yi magana yace out! Ba shiri ya fita ya ba su hakuri ba yanda suka iya haka suka hakura..

鈾モ櫏鈾ヰ煐ゐ煐も櫍鈾犫櫊鈾︹櫏鈾︹櫏

Tunda ta fita take bi shago shago duk inda taje se a ce mata babu se dai ta tambayi wasu shagunan.. Gajiya tayi da tafiya gashi bata fito da kudi ba ko wayar ta balle ta kira ta fada mishi bata samu ba ko ta hau Napepe ta dubo wasu shagunan, agogon hannun ta ta duba taga har 12 tayi ba tada zabi se kara gaba data cigaba dayi da alkawarin 12:30 nayi in bata samu ba zata koma ta fada mishi.

Kamar yanda ta alkawarta time din na cika ta juya ta kama hanyan komawa kamar da bakin kwarya aka fara ruwa ba tada wani zabi daya wuce ta cigaba da tafia ba dan tsoron fakewa take yi sbd yanda taga maza a mafi yawan gurin sun fake haka ta dinga tafia seda taji kafafunta sun kasa daukarta sbd gajia gashi nunfashin ta na wani irin daukewa.. Wani mai adaidaita ta tsaida tace ya kaita Barau Dikko ganin yanayin ta yasa be musa ba ya dauke ta, sun dau lokaci suna tafiya daga bisani suka iso, kudin shi ta bashi dakyar take daga kafa har ta kai kofar office din shi ta tura jikin ta na bari sbd dukan ruwan data sha, tana dago ido tayi mummunar gani nan take jiri ya debeta ta saki salati hade da faduwa kasa sumammiya…..

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も潱鈾犫潱鉂も櫊鈾モ櫊鉂も潱鈾犫櫏鉂も潱鈾犫潳鈾犫櫏 *MATAR DOCTOR*  鈾犫潱鉂も櫊鈾モ櫊鉂b櫊鉂も櫊鈾モ櫊鉂b櫊鉂も櫊鈾モ櫊

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

Dedicated this page to one of my fan Saratuh Salisu Usman (Momy Jidderh) thanks for ur support.. Allah ya bar zumunci.

    ***9鈨�1鈨�***

  *Flashback*

Tun lokacin da Dr. Godwin yace ma masinja ya fada ma patients su dawo gobe ya tashi yake safa da marwa yana leqa window ko zai hango ta amma bata ba alamarta yana cikin haka ya juya baya ji yayi an rungume shi ta baya da sauri ya juyo da ita cikin ihu tace surprise!
Precious budurwar shi ya gani ba wani fara’a a fuskar shi yace “yaushe kika dawo daga UK din?
Shekaran jiya na dawo na sauka a Abuja jiya na biyo morning flight na kwana a Asaa pyramid hotel ban fada maka ba sbd Ina son baka surprise but naga kamar bakayi missing dina ba kuma kaman baka ji dadin gani ba..
No ba haka bane kawai am nt in a good mood kuma kema kin san hali na ai sbd haka ki zauna bana son yawan surutu, da yake tasan halin shi bata ce komai ba ta zauna shima ya zauna tace  “Baby zan sha ruwa,
Ga fridge can kije ki dakko akwai cups a cikin wancan show glass din ki dauka dan ba zan iya tashi ba,
ba yanda ta iya da kanta ta dakko holandia ta zuba a cup tana sha, saman table din dayake zaune ta hau tana kallon cikin idon shi seda ta kara sipping sannan ta ajiye tace “Baby anjima zaka zo hotel din dana sauka?
Me zan zo in miki a hotel?
Wani kallo tayi mishi irin na yan barikin nan tace “haba shekaran mu nawa muna tare amma bamu taba hada shinfida ba kuma kasan Ina son hakan tun yaushe nake boyewa na kasa fada maka se dai in nuna maka amma ka kasa ganewa na gaji! Na gaji! I want to hv u I want us to… Cup din data ajiye ya dauka yayi wurgi dash ji kake tasssss! Ya fashe a kasa.
Ke wace irin yarinya ce mara kamun kai? A haka kike kiran kanki Christian? Kina bata sunan idinin ki duk da bana zuwa church amma nasan cewa Zina is prohibited domin Mary wacce kuke koyi da ita bata taba Zina ba!
Shiru tayi tana kallon shi tana mamakin hali irin nashi kamar ba namiji ba amma ta dau alwashin yau seta kauda kwadayin ta a kanshi duk da tana muamula da maza harda manyan maza amma bata bari ya sani ba sbd a sirri takeyi kuma ita burinta be wuce ta hada shinfida dashi ba sbd tana ganin hakan ze sa ya kara sonta (Waiyazubillah), tashi tayi daga kan table din ta zauna akan cinyar shi tana shafa sajen shi a hankali ta fara mishi wani sallo tun yana ture ta har ya fara biye mata sunyi nisa sosai a abunda suke yi a wannan yanayin ne Janan ta shigo ta same su abun yazo mata a ba zata kuma sabon al’amari sbd bata taba ganin haka ba fargaba da tashin hankali ga ruwan daya mata duka su suka haddasa mata faduwa kasa cikin glass din da ya fashe!

鉂も櫊鉂も櫏鈾犫潳鈾犫櫏鈾犫櫏鈾犫潳

Faduwar ta ne ya dawo dasu daga duniyar da suka lula cikin sauri ya hankadeta gefe “oh no! Damn it! Ya fadi yayo kanta yana girgiza ta, ke! Ke! Ke! Ki tashi mana ki tashi nace! Ki tashi! Ya rude bema lura akan glass din da yake ba har jini na fita a hannun shi itama jini ya bata mata kaya se malala yake yi a kasa kamar an yanka rago.. Precious ce taja tsaki cike da jin haushin bata mata plan da Janan tayi bata damu da halin da suke ciki ba ta dau jakar ta ta fice tana laluban numb din chief dinta yazo dan yau in bata samu abun da take so ba zata iya mutuwa..(Allah ka kare mu daga Zina! Ameen)

Idon shi ya kada yayi jajur gaba daya ji ya ke kaman ze haukace da sauri ya dauke ta cak gaba daya duk jikin ta ya saki, kara tsorata yayi dan gani yake kamar ta mutu.. Da gudu ya nufi emergency room da ita akan gado ya ajiye ta ya fara danna kirjin ta se zufa yake yi duk da sanyin garin, Baby girl ki tashi mana pls open ur eyes daurewa yake yi amma kuka ne fal a cikin shi.. Ganin taki motsi yasa ya sa mata oxygen kwatakwata nunfashin ta yaki zuwa abun ma yaki motsi zama dirshan yayi a kasa yana fadin “pls karki mutu karki tafi ki barni in kika mutu I will definitely kill myself”
Bude kofan akayi Dr.Jalal ne da Dr.Magaji suka shigo dan suna ganin lokacin da Dr.Godwin ya wuce da Janan a hannun shi,  da sauri Dr.Jalal yayi kanta yana dubata yace “Ya Salaam! She is an Asthmatic patient sanyi ya shiga jikin ta sosai kuma zuciyar ta tayi sanyi kamar taga wani abun tsoro ko na tashin hankali nunfashin ta yayi nisa gashi kafanta da hannu suna bleeding ta zubar da jini haba Dr. Godwin me yasa baka tsaida jinin ba? Dr. Godwin kasa magana yayi..
Suna  cikin haka se ga Dr. Imran ya shigo a gigice sanye da lab coat be bi ta kan su ba ya nufeta yana danna kirjin ta jin nunfashin yaki kawowa ya hada bakin shi da nata yana hura mata iska yafi minti 10 yana haka se abun ya fara reading alamun nunfashin ta ya fara dawowa can ta saki ajiyar zuciya, Dr. Imran da Dr. Godwin suma suka saki ajiyar zuciya lokaci guda.. Dr. Imran yace  “I’m sorry banyi introducing kaina ba na shigo without ur permission sunana Imran a Doc. frm Sefa specialist hospital kuyi hakuri da shiga cikin muku aiki amma dole ne inyi haka sbd bana so inyi loosing dinta cuz she is my wife to be in shaa Allah………

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も櫍鈾犫櫏鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾犫潳 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鉂も櫏鈾b櫊鉂も櫏鈾犫潳

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

Ina godia a gare ku masoya na kun nuna kulawar ku a gare ni tare da bani kwarin gwiwa.. Allah saka muku da alkhairi ngd da shawarwarin ku kuma in shaa Allah zan yi anfani da shawar ku!! ILYSM馃槏

Wannan shafin naku NE _YAN MUTAN JOS NOVELS GROUP_! U guys deserve a dedication frm me! Thanks for the love nd the support u always make me happy馃馃槂馃槃 Allah bar soyayya!

     ***9鈨�2鈨�***

Wani irin razanannan kallo Dr. Godwin ya ke ma Dr. Imran a ranshi yace “His wife to be? Ta yaya? Wannan shi ake kira Impossible! Gaba daya wani irin haushin Dr. Imran yake ji ko don yanda ya hada bakin shi da na Janan.. Ji yake kamar ya tashi ya shaqe shi

Fatan alkhairi su Dr. Jalal suka mishi tare da taya shi murnan samun yarinya mai tarbiyya irin Janan! Murmushin jin dadi yayi hade da yi musu godia… Wajen ta suka koma Dr. Jalal ya cire mata glass din da suka ji mata ciwo ya goggoge jinin yana mamakin irin yanda glass din ya ji mata ciwo dan harda dinki yayi mata , maganar shi ta dawo da Dr. Godwin daga dogon tunanin da yake yi, hankalin su duk ya koma kan Dr. Jalal din yana cewa gaskiya ta zubar da jini sosai yanzu dole za a kara mata jini..

Eesher ce tayi knocking sannan ta shigo cike da tashin hankali ganin halin da kawarta take ciki! Gaishe su tayi Dr. Jalal yace yawwa kije lab ki ce ta su bani jini leda daya.
Dr. Godwin ne yace haba dai taya za a amso jinin wanda ba a sani ba a sa mata bari in je a diba nawa, be jira abun da za su ce ba ya fice daga dakin, Dr. Imran cikin ranshi yace “ikon Allah! Taya za ayi Ina nan a sa mata jinin wani? Wanin ma Christian?
Bayan Dr. Godwin ya bi ita ma Eesher ta bi Bayan su!
Dr. Godwin na shiga Imran da Eesher suka shigo, sun tarar da Dr. Godwin har ya bada order a diba jinin shi, Nurse din tace  “Sir jini na zuba daga hannun ka kuma se an duba jinin ka in zaka iya donating!
Wani tsawa ya daka mata yana fadin ba kida hankali ne? Ni zaki fada ma abun da ya kamata? Kin fini sanin kaina ne ko kin fini sanin blood grp dina ne ko kuma aiki na? In  baki sani ba toh ki sani ni A+ ne sannan ni donor ne zan iya donating jini ga kowa!
Sorry Sir! Ta fada dan ta san shi tun zuwan shi asibitin.
Ki riqe sorry din ki dan ba zai mun anfani ba…
Cike da jin tsoro tace
Sir pls ka bari a cire glass din dake hannun ka kuma a tsayar da jinin dake zuba daga hannun ka kafin a diba jinin, kallon hannun yayi dan shi gaba daya ma be lura da ciwon da yaji ba kuma kwalban ya shiga sosai, ba musu yace ma Eesher ke zo kiyi dressing min hannun na kuma make it fast cuz bana son a bata mun time.. Se a lokacin Imran yayi magana da fadin ni yafi dacewa da in bata jini na sbd already jinin ta yana yawo a jiki na nima kuma nawa yana yawo a nata karka damu kanka ni zan bada na hutashshe ka..
Hey! Mr what so ever u call ur self nan asibiti ne kuma baka da iko a kanta sbd she is under my custody inji Dr. Godwin.
Kizo kiyi aikin ki yace ma Eesher, kamar tace ba za tayi ba amma hakan be dace ba ta bude first aid box din dake wajen ta fara cire mishi kwalban.. Kallon shi kawai Imran yayi ba tare da yace komai ba abun ka da mara son hayaniya! Wajen wata Nurse musulma yaje dan ya ga dayar kamar tana tsoron Dr. Godwin yace mata ki diba jini na ki gwada in yayi ki zo ki diba Dan girman Allah kiyi sauri akwai patient da za a sama jinin kuma shi is unconscious!
Ba musu ta diba tare da fadin bani 5 min in duba in gani.. Dr. Godwin be ma san abun da ake ciki ba sbd se yanzu yake jin zafin ciwon ashe kwalban ya shiga sosai zufa kawai yake yi yana jin zafin sosai tausayin Janan ya darsu a zuciar shi yana tuno yanda ta fada akan kwalban dai dai minti 5 din da Nurse ta dawo dai dai lokacin Eesher itama ta gama gama dinke mishi hannun tare da nadewa da bandeji, Nurse din ta dawo wajen Imran tana fadi i’m so sorry Sir ba zaka iya donating jinin ka ba cuz kai ba donor bane, karap a kunnan Dr. Godwin wani irin sanyi yaji ya sauka har cikin kashin shi,
shi kuma Imran gefe ya koma ya durkusa tare da dafe kai dan har wani irin jiri jiri yake ji Innalillahi wainnailaihirrajiun kawai yake nanatawa a zucian shi yana wajen Dr. Godwin ya zo ya wuce shi ya kwanta saman Gado  tare da miqa ma Nurse din hannu bata tsaya bata lokaci ba ta fara diba..
Ana gama diba ya dan tsaya minti 2 kafin ya tashi sbd kar jiri ya kwashe shi ya karba ledan jinin yayi ficewar sa.

Jiki a sanyaye Imran ya tashi gaba daya se yaji kamar kafafun shi ba zasu dauke shi ba sbd halin da yake ciki, Eesher ce ta ba shi baki sannan ya dan daure suka koma emergency room din suna zuwa suka tarar har an sa mata karin jinin har lokacin idon ta a rufe suke se nunfashin ta da yake sauka a hankali!
Special room aka maida ta wanda se special mutane ake ajiyewa a nan, se a sannan suka samu natsuwa Imran ya kira Khaleel ya fada mishi abun da ke faruwa..

Ba suyi kyakkyawan mintuna 40 se gasu a asibitin suna zuwa kafin su shiga suka hadu da Imran a hanya shima an kirashi da gaggawa a asibitin su dama lunch din Janan yazo kawo mata ya dinga kira amma wayar bata shiga ba dalilin da hankalin shi ya daga kenan ya zo asibitin yana zuwa ya kira Eesher yana tambayar ta Angel din sa nan take fada masa bata lfya sbd taga an shigar da ita Emergency room..

Har kasa ya durkusa yana gaida Ummiey da Abbiey sukayi musabaha da Khaleel da Saleem sannan yayi musu jagora zuwa dakin, har yanzu bata tashi ba Imran ya koma mota ya kawo abincin da ya taho mata da shi su Ummiey suna ta fadi baka gajia da dawainiya?
Yana sosa keya yace Aa babu komai Ummiey sannan ya fada musu ze je ya dawo an kirashi a asibiti
Fatan alkhairi suka mishi sannan ya wuce..

Suna nan zaune na tsawon lokaci Saleem yana gefen gadon ya zaune se ga Dr. Godwin ya shigo ko ba a fada mishi ba yasan Family’n Janan sbd duk sun yi kama wani irin kwarjini suka mishi be san lokacin daya duqa har kasa yana gaida su Ummiey ba shi kan shi yayi mamakin kan shi sbd be taba duqawa ya gaida kowa ba har iyayen shi tun da yake se yau! Suka amsa mishi sannan ya ba su Saleem hannu suka gaisa Abbiey yana mishi kallon sanni haka ma Khaleel yana mishi kallon sanni amma sun kasa tuno inda suka san shi..

Dai dai nan ta farka hade da yin salati da sauri suka yo kanta in da a tare suke tambayar me ke mata ciwo, da kyar take iya magana tace babu ko Ina ku kwantar da hankalin ku in shaa Allah zan samu lfya….
Kina jin wani pain a jikin ki? Akwai inda yake miki zafi? Dr. Godwin ne ke mata waennan tambayoyin yana kokarin hada ido da ita, ita kuma taki bari su hada idon kuma taki bashi amsa…

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾犫櫏鈾b櫏鉂も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鉂も櫏鈾b櫊鈾モ潳鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫏鈾犫櫍

I specially dedicated this page to u Little Eesher u r no more Little Eesher but Bigger Eesher and also a Mrs to Engineer. Idrees Kabo! Ngd miki sosai sbd kin min abunda bazan taba mantawa ba Allah ya biya miki bukatunki na alkhairi! Allah ya baki lfya! Kece ta farko da kika dawo min da novel din lively kika turo min daga page one nayi murna sosai! ILYSM馃槏馃槝

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒

Idan kuka duba MATAR DOCTOR za kuga page 89 wanda na rubuta _few days to my birthday_ se kuma wani page 89 din wanda na rubuta _continuation_ karku zama confused duk cigaba ne kuma dai dai ne se kun karanta zaku gane me nake nufi! Ngd sosai da sosai鉂も櫏

   ***9鈨�3鈨�***

Ganin da yayi bata da niyyar kallon shi yasa duk jikin shi yayi sanyi, ya fara kokarin cire mata karin jinin da sauri matsar da hannun ta a hankali tace don’t touch me with this ur dirty hands”
Stop all this drama and lemme do my work” yace mata
Suna cikin haka Zee da Eesher suka shigo suna gaida su.
Gefen Janan suka koma suna tambayar ta jikin ta ta amsa musu da Alhamdulillah.
Ummiey ce tace Wai ya akayi haka ta faru?
Eesher tace wallahi Ummiey ni dai ban san ya akayi ba kawai dai naga an wuce da ita emergency room jikin ta duk jini Ina shiga se naji Dr. Jalal yana fadin wai Asthma din ta ne ya tashi se kuma ciwon da glass ya ji mata”
Ya Salaam! Rabon da Asthma din ki ya tashi an dade Hulwaty ya akayi har Asthma din ya tashi dan Ina kyautata zaton ruwa kika shiga!
Da kyar ta ce eh Ummiey ruwa na shiga naje siyo magani ne se ruwa ya tare ni a hanya rashin samun abun hawa yasa ruwan ya mun duka sanda na dawo asibiti kuma nazo shigowa office se jiri ya debe ni na fadi kan glass din da ban san yana wajen ba”
Yaya Khaleel yace babu masinja ne a asibitin da ke da kanki zaki je?
Bro in aka ake su shirme suke yi shiyasa naje da kai na!
Sannu Muhibbaty Allah baki lfya kin ji” Abbiey ne ya fada haka.
Saleem yace “our chef is sick wa zai dinga mana girkin?
Daria sukayi duka Abbiey yace ga Ummieyn ku nima yanzu Ummiey ta zata huta ai kai dama haka kake da son abinci gashi baka iya dafawa ba Allah dai yasa ka auri wacce ta iya girkin sbd karka dinga zuwa gidan Muhibbaty kana dan murya a san maka abinci”
Daria suka kuma yi..

Cike da mamakin Dr. Godwin ke kallon ta ganin yanda bata fada komai game da abun da ya faru ba duk ta boye fault din shi duk da ya san shine silla ji yayi wani abu na kara shiga cikin zuciyar shi har ya saukar mishi da kasala, kuma da gani ita yar gata ce a gidan su dan yaga kowa naji da ita

Ka matsa gefe Eesher zata cire min” Janan ta ce mishi
Ba musu ya matsa sbd duk ya tsargu gani yake kamar za a gane shine sillan shigan ta wannan halin..

Eesher na gama cire mata tace Ummiey kun zo mun da kaya? Ina so in yi wanka”
Bamu zo da komai ba se dai yanzu Saleem ya koma ya dakko mana duk abunda ake bukata dan ba cikin kwanciyar hankali muka fito dan duk mun damu bayan Imran ya fada mana condition din da kike ciki, ki fara cin abincin da Imran ya kawo kafin Saleem din ya dawo..
Ummiey se na yi wanka zan iya samu relief da natsuwa”

Abbiey ya miqa ma Saleem key din gida sannan ya bashi kudi yace ya siyo duk abun da ya dace
Toh kawai yace sannan ya fita..

Dr. Godwin yace kuyi hakuri da abun da ya faru da ita sannan yayi excusing kan shi ya bar dakin cike da dana sanin abunda ya aikata!

Yana fita daga dakin ya wuce inda ya ajiye motar shi ya tafi boutique ya zabo mata dogayen riguna guda 6 da towel daga nan ya wuce supermarket ya siya kayan tea se exotic carton daya da bottle water shima kwali daya ya tsaya ya siya gasassun kaji, cikin sauri yake komai sbd yana so ya kai musu kayan kafin Saleem ya dawo

Yana tafe yana tuna duk abunda ya faru tare da dukkan reactions din sa yana mamakin kan shi yanda yake ba iyayen ta respect tare da jin wani irin kunyan su!
Kwana yasha yana tuno yanda Janan ta rufa mishi asiri ko da ya tuno yanda ta fada kan glass din se yaji wani irin haushin kan shi daya biye ma Precious har hakan yaja Janan taji ciwo, gudu yake yi sosai har ya iso asibitin, dakin direct ya wuce ya ce ga shi pls kuyi managy kafin ya dawo sbd ba komai da kuke so ba na siyo da sauri ya bar dakin sbd baya so suyi mishi godia kuma yayi ma kan shi alkawarin ba zai kara hurting din ta ba koda da kallon banza ne!

Abu kadan ne babu a kayan da Dr. Godwin ya kawo, Saleem na dawowa ta shiga tayi wanka a bayin ta shirya, kwata kwata taki anfani da kayan da Dr. Godwin ya siyo abincin da Imran ya kawo tun dazu shi taci se ruwan gora da Dr. Godwin ya kawo shima dan Yaya Saleem ya manta be siyo ruwa ba shiyasa tasha..

Se can yamma Imran ya dawo kuma dai dai da lokacin da Dr. Jalal yayi discharging din ta shi kuma Dr. Godwin ya bata hutun 1 week ko hakan ze kara sata farin ciki kuma yasa ta huce daga fushin daya ga tana yi dashi duk da yasan zeyi missing din ta sosai..
Tunda ya shigo be kalla Imran ba har ya fita sbd yama tsani ganin shi balle har su tsaya a inuwa daya dashi…
Godia su Abbiey suka yi musu sannan suka kwashe kayan su suka tafi gida…

Get Well Soon Janan馃槏馃拫馃槝

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾犫櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾b潳鈾モ櫍鈾モ櫊鈾b櫏鉂も櫊鈾b櫏

Alhamdulillah! Alhamdulillah! Kamar wasa yanzu ya zama gaske babu abunda zan ce se dai Godia ga Allah daya daukaka wannan littafi!

Wannan shafin naku gaba dayan ku yan grp din *MATAR DOCTOR’S NOVEL ONLY*! Ngd da yanda kuke bani hadin kai kuma kuke son wannan littafin! Allah ya bar zumunci Ameen!

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

    ***9鈨�4鈨�***

Tun lokacin da Precious ta bar asibitin hotel din data sauka ta koma tayi wanka ta fito daure da towel se ga chief din ya kirata ta fada mishi room numb din ko knocking be yi ba ya shigo ganin ta haka yasa ya fara mata wani kallo kasakasa tana ganin haka tasan me yake nufi nan suka fara aikata masha’ar su(Allah ya kare mu daga saba maka)

Haka kwanaki yayi ta tafiya kullum Dr. Godwin na hanyar gidan su Janan siyayya kala kala yake ma ta se dai ya aika yara su shiga dashi amma ya kasa shiga ciki sbd kunya su da yake ji yana son ya ganta a rana na 4 daya je be aika yara ba shida kanshi ya shiga ciki a tsakar gidan ya tsaya ya rasa ta ya zai yi su san ya shigo se ga Saleem nan ya shigo da mamaki ya miqa mishi hannu suka gaisa sannan ya ce yana zuwa
Yana shiga parlor ya tarar dasu zaune suna kallon TV Janan na shan fruits yace “Black Sis ga wannan Doc. din wanda kike taya shi aiki yazo, a tsakar gidannan na ganshi a tsaye”
Ummiey tace Ikon Allah ka bude mishi dakin baki ya shiga mana ka barshi a tsaye kamar wani soja”

Kai! matsala ta da waenda ba musulmai ba kenan basu san su nemi izini ba kafin su shigo gidan mutane ko an ce mishi nan a garin Jahilai ne da ze wani shigo mana gida ba izini oho”

cike da mamaki Ummiey ke kallon ta tace ke kuma lfyar ki ke fadin haka yanzu idan ya ji ki fa? Yaushe kika zama haka?
Ta turo baki to ai gaskiya ne Ummiey..
Allahu yahadeeki (Allah ya shirye ki) tashi ki kai mishi ruwa da danbun nama da drinks ai bakon annabin ka Ina laifi ma yazo duba ki ga dawainiyar da yake yi dake sbd a karkashin sa kike amma kike fada haka maza ki tashi ki kai mishi..

A zuciyar tace Ummiey baki san waye shi ba ne shi yasa kike fadan haka ba karamin dan wulakanci bane ga rainin wayau da dan banzan mugunta”

Dogon hijjab tasa sannan ta jera kayan a kan tray ta fice ba dan ranta yaso ba.. Tana shiga ta ganshi zaune suna hira da Saleem ta fada a hankali “ji be shi kamar na kirki se iskanci fal ciki me qaton kai kawai”
Sallama tayi sannan ta shiga idon shi qyar a kanta gani yayi tayi mishi wani irin kyau amma ta dan rame har wani lumshe idanu yake yi, a gaban shi ta ajiye tray din sannan ta juya zata tafi Saleem yace ke haka ake yi ma baqo  a garin ku? Ko gaishe shi ba kiyi ba kin wani dungura mishi abu zaki tafi kin dai san shinfidar fuska tafi ta tabarma ko? .
Bata so haka ba dan ita haushi yake bata sbd bata son wani alaka ya dinga hada ta da dan iska, dawowa tayi ta zauna gefen Saleem, “Ina wuni” ta fada a daqile kamar ba magana take yi ba,
Shiru yayi yana wani shan kamshi irin shi a dole be ji ba din nan Yaya Saleem yace ko ni da nake kusa dake ban jiba balle shi da yake nesa.

Cikin qosawa ta sake gaida shi amma wannan karan da karfi tayi
Ze yi magana kenan aka kira wayar Saleem yace bari ya amsa waya yana zuwa, kamar jira Dr. Godwin ke yi Saleem na fita ya dawo kusa da ita yana mata kallon nayi kewar ki ta kawar da kai gefe tana jin haushin irin wannan kallon tace a hankali ni dai ba yar… Bata karasa ba yace ba yar me ba?
Ba komai tace a takaice
Yasan cewa yayi mata ba dai dai ba amma shi a ganin shi ba komai bane dan ta gansu a wannan halin shida Precious sbd haka be ma sa wannan a matsayin laifi ba shi dai laifin daya da ya aike ta har aka samu matsala

*JANAN* ya kira sunan ta!
Ya Salaammm! Ta fadi a ranta tana lumshe ido cike da mamakin yanda ya iya kiran sunan kamar shi ya rada mata kuma in zata tuna yau ne first time daya fara kiran sunan ta tunda suke! Ya katse mata tunani da fadin “kina gani kamar nayi miki laifi ne bayan kuma kece da laifi sbd ke kika ja komai ya faru ya kamata kizo office da wuri amma kika ki shine ni kuma nayi punishing din ki  sbd nxt time karki sake haka”
Wani kallo tayi mishi irin na ka raina min wayau bata ce komai ba ya cigaba “ki manta da komai kuma ya kamata ki bani hakuri a matsayina na Boss din ki”

Tabb! Ka dade kana min laifi ban taba cewa komai ba ka ja Asthma na ya tashi wanda ni kaina na manta Ina da shi sannan na shigo naga kuna iskanci da wata ka fasa glass a kasa na fada a akai naji ciwo harda dinki aka min amma kace wai ni ya kamata in baka hakuri” niyyar tashi tayi amma yasa hannun shi ya danne kafar ta

Miye haka kuma ni ka dena taba ni sbd ni ba yar iska bace”

Killer smile din shi ya mata yace to waye dan iska?
Shiru tayi sbd yanda ya tsareta da mayun idon shi ba zata iya cewa komai ba

Anyway! Tunda ba zaki bani hakuri ba shikenan ya tashi ya koma mazaunin shi yace zo ki zuba min ruwa in sha”

Ta so tace ai kana da hannu kuma ni ba yar aikin ka bace se dai kawai ta fasa sbd ta gaji da magana da shi..
Cup ta dauka ta zuba mishi ya fara sha se ga Saleem ya dawo yana cewa “baka ci komai ba se ruwa? Pls Kaci danbun naman nan I knw u will like it”
Kadan ya diba yasa a baki wani irin dadi da gardi ya ji ya mamaye ilahirin bakin shi ji yake kamar ya dau bowl din ya tura a baki ganin kar ya bada kanshi ya zubda class din shi yasa ya miqe yana fadin “zan tafi ngd sosai”
Hanyar waje yayi Saleem yace ma Janan ta dakko bowl din ta bashi sbd ya lura Dr. Godwin naso yaci sosai amma yana jan aji!

Foil paper ta koma ciki ta dakko sannan ta rufe ta bishi dashi, a bakin kofar gate ta same su sukayi sallama da Saleem ya koma cikin gida ita kuma Janan taje wajen motar shi dan ta bashi danbun.. Jikin motar ya tsaya ya harde hannayen shi a kirji yana kallon ta tana tahowa a hankali har ta karaso, miqa mishi tayi yaki amsa ta zagaya dayan bangaren ta ajiye mishi akan kujeran motan ta juya tayi tafiyar ta..
Girgiza kai yayi yace       “ke kadai ce kike min abunda kika ga dama ba wanda naga dama ba,”
ya shiga motar shi ya wuce yana jin dadin ganin ta da kuma abunda ta bashi…

Dakin bakin ta koma dan tayi clearing komai kawai se taga ledoji guda 2, daya chocolates da sweets dayan kuma turarruka ne masu kyau baki ta tabe sannan ta kwashe ta kaima Ummiey, zuciyar Ummiey ta fara raya mata wasu abubuwa amma se ta share tana fadin it’s impossible! A fili kuma tace gaskiya Yaron nan akwai kokari ga kirki”
Saleem yace wallahi kuwa baki ga yanda muka sha hira da shi ba”
Hmm! Dan baku san halin shi bane shiyasa kuke fadin haka” Janan tace
Ummiey tace mu dai abun da muka gani shi zamu fada”
Shiru Janan tayi bata sake cewa komai ba sema ta canza hiran…

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ櫍鉂も櫊鉂も櫍鉂も櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫊鈾モ潳 *MATAR DOCTOR*
鈾b潳鈾犫櫏鈾b櫊鈾b潳鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鉂も櫍

Rukkybae 馃槒馃槒馃槒

A piece of advice! Duk sanda period din ki yazo ki karanta wannan adduaar  *Alhamdulillahi Ala kulli halin wa ana astagfirullah wa atubi ilaihi*
Sannan ki yawaita istigfari domin neman gafaran Allah kuma ki kasance kullum cikin alwala sbd neman tsari daga Aljanu da kuma Sihiri domin lokacin da mace bata cikin tsarki toh Asiri da aljanu za suyi saurin tasiri a jikin ta! Wallahu Aalam!

  ****9鈨�5鈨�****

Yau sati dayan da Dr. Godwin ya daukar wa Janan har ya cika ba da son ranta ta koma asibitin ba se dan taimakon jamaa..

Tana shiga ta gaishe shi ta zauna tana hada rai sau daya ya kalleta ya kauda kai sbd yaga alaman yau fada take ji.. Marasa lfya suka fara shigowa yana duba su can wajen 12 se ga kira nan ya shigo da zumudi ya dauka cikin shagwaba yace “Momma nayi fushi dake yaushe rabon ki kira ni? Kallon shi Janan ta tsaya yi ganin yanda yake shagwaba kamar wani yaron goye!
Momma daga daya bangaren tace Baby muna missing dinka sosai ka kunna laptop din ka muyi video call inga yanda ka zama.

No! No! Not now yanzu Ina cikin aiki ne when i’m free I will call se muyi video call din”
Momma tace yanzu nake so in ganka kuma Ina jiranka na baka 2 mints” tayi hanging call din.. Yasan tayi fushi ne ba yanda ya iya haka ya jawo laptop din yana kunnawa se ga call din ya shigo da sauri yayi connecting daga  bangaren ta tace “wow baby naga ka kara girma ne kayi fresh wato ka barmu kana can kana jin dadin ka menene sirrin! Janan ya kalla da gefen ido yaga shi take kallo murmushi yayi yace “Momma ba wani fresh ni da nake missing din ku wani jin dadi kuma”

Fada min me kaci yau da safe? Rolling idon shi sama yayi kamar me tunani yace “no bazan fada ba kiyi guessing!
Tayi daria tace ” Garri ba sugar”
Daria ya kwashe da shi harda kyakyatawa yace haba Momma yaushe kika dena sona ban sani ba how on earth za ace in rasa abun breakfast se garri kuma wai ba sugar” ya sake kwashewa da daria, tunda kin kasa guessing kuma kin manta favorite dina toh I ate sandwich nd oat”
Tace wow! Dole ka dinga qiba.

Haka sukayi ta hiran su yana zuba mata shagwaba Annabell da Dad shigowar su kenan suma sukayi joining hiran..

Duk sun yi farin cikin ganin junan su..
Mamaki ne ya cika Janan ganin yanda Family’n nashi suke son shi kamar zasu hadiye shi..

Dad yace hope dai kana zuwa church”
No Dad bana zuwa kasan aiki na bazai barni ba”

Stop dodging nasan halin ka I knw ba zaka dinga zuwa ba since u aren’t interested!
Kai kawai ya ke sosawa alaman rashin gaskiya
Momma tace Precious ta zo tace min kayi mata wulakanci”
Yamutsa fuska yayi yace forget abt her Momma I don’t wanna talk abt her”
Annabell sister’n shi tace “Babyn Momma yaushe zaka zo?
Soon Princess don’t worry kin ji?

Wayar office din sa ce ta fara ringing yasan emergency ne sbd dalilin haka aka ajiye wayar a office din, da sauri yace Momma urgent call ne ana nema na a emergency inna samu time I will call u I love u all yayi musu kiss suma suka ce we love u more sukayi kissing din shi da sauri ya kashe yace ma Janan let’s go! Ya zari lab coat din shi.. Ba musu tabi bayan shi..

_Labour Room_

Tun safe aka kawo matar amma ta kasa haihuwa da kanta sbd BP din ta yayi high kusan awa 3 da rabi kenan duk ta jigata har ta gaji da nunfashi da karfi ta koma a hankali..

Takardan yarjejeniya akan za’a mata operation aka ba mijin ta ya cika..

Kan gado aka daurata cikin gaggawa aka shigar da ita dakin theatre..

Kwararrun Likitoci ne har 5 a kanta amma sun kasa komai duk iya kokarin su sun kasa se kai kawo suke yi amma abu yaci tura!   Dr. Godwin yace ohhh my God! This is serious!
Duk suka hada baki suka ce very serious!
BP din yaki sauka balle a mata operation kuma akwai tabbacin da zaran sun mata theatre jinin be sauka ba zata iya rasa ranta so dole ne ita da kanta ta haihu but how?
kwata kwata dabara ta dauke musu..

Da sauri Janan ta fita ta koma office ta dakko ruwan gora ta zuba a cup jikin ta se rawa yake yi ta tofa adduaa a ciki sannan ta karanta _thummassabila yassara_ ba adadi sannan ta koma dakin yanda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta same su, inda matar take kwance ta wuce seda ta ajiye cup din akan wani table tace “pls ku bani dama in bata ruwan nan by the Grace of Allah zata haihu da kanta” Wani irin kallo suke mata Dr. John yace “ya za ayi mu barki ki bata ruwa bayan kin san ba zai yiwu ba kina abu kamar ba kida kwakwalwa! Gaskiya be kamata ki bata ba Dr. Salma da Dr. Abraham suka ce.
Dr. Magaji dai be ce komai ba Dr. Godwin yace allow her!
Kallon shi suka juyo suna yi yace “yes allow her dama options din biyu ne either ta mutu ko Babyn ya mutu ko kuma dukkan su su mutu sbd haka let her try tunda mu mun kasa!
Dr. John yace duk abunda ya faru we will hold u responsible nt her tunda kai kace tayi ka yarda?
Yeah na yarda!  Ke dauka ki bata yace mata.. Cike da tsoro ta dauka tana adduaan neman saa a wajen Allah… Dago kan matar tayi ta bata seda tasha kusan rabin cup sannan Janan ta cire daga bakin ta.. Fiye da minti 5 mata ba wani change se ma abu ya kara worst ta fara wanni irin jijjiga Dr. John yace u see! Ka ga abun da nake fada maka ko! Duk sukayi kanta da gudu

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [9/28, 7:51 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鉂も櫏鈾b潳鈾b櫏鉂も櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒

_Aduaa itace makamin mumini kuma adduaa bata fadi kasa banza_
_Mu yawaita yin adduaa tare da neman zabin Allah a dukkan lamarin mu! za muga daidai da yardar sa_

_Tunatar wa ce_馃憣馃徎

      ***9鈨�6鈨�****

Duk sun tsorata ganin yanda take jijjiga da sauri Janan ta je ta daura kan matar a cinyar ta tana goge mata zufa tare da tofa mata duk adduaar
da ta zo bakin ta..

Wani irin nishi mai karfi tayi se ga baby ta fito cikin ikon Allah da sauri Dr. Salma ta cabe babyn sbd kar ta fadi tana fadin Allah Mai iko…
Wani irin ajiyar zuciya Janan ta saki tare da hamdala ga Allah shi kuma Dr. Godwin murmushi ya sakar mata tare da jinjina mata馃憤 yace masu “I know she can do it! I told u she can make it!
Jiki a sanyaye Dr. John ya cire hand gloves din shi ya fita daga theatre room din Dr. Abraham ya saki baki yana mamaki shi kuma Dr. Magaji yace a ranshi Alhamdulillah Ala Niimatil Islam”

Gyara matar akayi amma unfortunately babyn ta mutu sbd ta jigata sannan jinin Maman da yayi mugun tashi yayi affecting din ta..
Dakin hutu aka maidata se baccin wahala take yi abun gwanin ban tausayi..
Dr. Magaji ya kira mijinta office din shi yayi mishi nasiha
Mutumin yace Matata ta mutu ko? Shiyasa kake min nasiha ko? Ya kifa kai a table yana gunjin kuka Dr. Magaji yace cool down bata mutu ba sedai ta wahala amma babyn ta mutu gata can ana goge mata jiki kayi signing se ka amsheta a kaita makwancin ta Allah ne ya baku ita kuma ya amshi abun sa Allah ya baku wasu masu albarka Allah yasa me ceton ku ce”
Ya amsa da Ameen yaji dadin maganar Dr. din ko ba komai ya samu natsuwa da wannan nasihar.. Signing yayi sannan ya fita…

Dr. Godwin yaji dadi sosai Janan na shigowa ya ji kamar ya daga ta sama sbd murna, gaban ta yaje ya tsaya yana kallon ta kafin yace  “u really impressed me today ki fada duk abunda kike so I will definitely do it 4 u nayi miki alkawari”
Nothing tace mishi..

Be ce mata komai ba ya wuce ya bude locker ya dakko check da biro yayi signing yace ki rubuta amount din da kike s”

Bata rai tayi tace I don’t need it nayi ne sbd Allah kuma sbd ni musulmace addinin mu ya hore mu da taimako a duk inda muke kuma she ze bani lada so ka ga no need in amsa kudin ka ka ajiye su kaima ka taimaki wasu dashi “
Tace excuse me ta wuce waje sbd ta gyara kanta toilet din Nurses ta nufa tayi duk abunda take son yi..

Bangaren Dr. Godwin kuwa ta soso mishi inda yake mishi kaikayi nan da nan idon shi ya kada yayi ja a rayuwar shi in akwai abunda ya tsana to a kira mishi taimako gani yake duk Dunia ba kalmar daya tsana kamar ta. Kanshi  ne ya fara juyawa ya fara wani tunanin, wajen zaman shi ya koma ya zauna dafe da kai yana fadin No! No! No! Ya watsar da takardun kan table din sannan ya janyo drawer ya dakko maganin bacci ya zuba a baki yana tauna su ko daci bayaji sbd da dacin yake ji a zuciyar shi ya ninka dacin maganin ninkin ba ninkin..
Cikin mintunan da basu fi 2 ba bacci ya kwashe shi.. Tana shigowa taga yana bacci kallo ta karshe mishi taga baccin shi yayi nisa ga takaddu nan yashe a kasa seda ta kwashe su ta ajiye akan wani table sannan ta tattara kayanta dama karfe 5 saura ta wuce gida abun ta…

鉂も潳鈾b櫍鉂も櫍鉂も櫍鈾b潳鉂も櫍鉂も櫊鈾犫櫏鈾モ櫏

Haka lokaci yayi ta tafiya Janan da Dr. Godwin suyi fada wata Rana kuma ya mata kirki in yaga dama se dai ta lura baya so a ambaci kalmar taimako ko
menene dalili oho!!

Yanzu bikin su da Imran saura watanni uku se faman shirye shirye ake yi daga dukkan bangare… Imran duk ya kosa se dai kullum ya kwanta se yayi wani mugun mafarki amma ya rasa dalili kuma baya gane kan mafarkin…

Wani dare bayan ya gama mafarkin daya zama kamar dole a gare shi ya tashi da ciwo mai zafin gaske tun yana daurewa har ya kasa jure, sakkowa yayi daga gadon ya kwanta flat a kasa nan da nan ya fara rawan sanyi da kyar ya jawo bargo ya rufe jikin shi amma be ji saukin ciwon ba haka yayi ta murkususu har aka kira sallan asuba ya kasa tashi balle yayi sallah nunfashi ma ya fara gagaran shi..
Yau shiru Imran be zo yayi knocking kofar kannan shi ba alaman su tashi sallah Daddy ma be ganshi a masallaci ba dan kusan kullum shine a gaba gaba baya wasa da bautan Allah.. Ana idar da sallah Daddy ya shigo ya tarar da Maman su Imran din tana sallah ya jirata ta idar yace lafiya banga Imran a masallaci ba?
Tace inaga ba lfya ba kasan baya fashin sallah toh ko dai ya makara ne?
Muje dai mu duba mu gani inji Daddy, a tare suka fita dan zuwa dakin Imran din suna shiga suka ganshi kwance a kasa da bargo a lullube, Subhanallahi Imran lfyar ka? Inji Mommy tana yaye bargon, sallati suka saki ganin Imran kwance ba nunfashi babu alamar nunfashi…….

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [9/30, 6:29 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫍   *MATAR DOCTOR*
鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾犫櫏鈾b櫏鈾犫櫏鈾b櫏鈾犫櫏鈾b櫊

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

_Mutuwa bata sanar da lokacin zuwanta se dai kawai ta dauke mutum idan lokacin shi yayi.. Mu aikata aikin kwarai domin mu samu tsira gobe Qiyamah_!

_Tunatarwa ce_馃憣馃徎

    ****9鈨�7鈨�****

Cikin sauri Daddy ya fito dauke dashi a hannu yana cema Mommy ta dakko key akan drawer, bada bata lokaci ba suka sashi a mota suka nufi family hospital din su *Garkuwa*
Da shigar su Likitoci suka yo kan su da sauri aka dakko gadon tura mara lfya aka daura shi ana tura shi likita yana shafa mishi ruwa a fuska nan da nan nunfashin shi ya dawo suka shiga dashi wani daki aka bar Daddy da Mommy a waje suna ta safa da marwa suna adduuan Allah bashi lfya
bayan kusan minti 40 se ga likitan ya fito da sauri Daddy yaje gurin shi yana tambayar jikin yaron shi, likitan yace  “ku kwantar da hankalin ku in shaa Allah ze samu sauki yanzu ma ya dawo normal se dai za a diba jinin shi a tabbatar da abunda ke damun shi..
Godia ya mishi sannan yace za su iya shiga su ganshi, da sauri suka shiga,  a kwance suka ganshi idon shi a bude se karin ruwan dake hannun shi, a tare suke tambayar jikin shi ya amsa da Alhamdulillah!

Yau tun da Janan ta tashi gaban ta ke faduwa gashi Imran be kirata ba nan zuciyar ta ta fara raya mata babu lfya tunda be saba mata haka ba.. Wayar ta ta dakko tayi dialing numb din shi amma no answer bata hakura ba ta dinga kira seda ta kira sau 7 ana 8 ne aka dauka gab da zata tsinke, muryar Hammeda taji kanwar Imran wacce za su kusa saa da ita suka gaisa a mutunce sannan take fada mata ai ankai Imran asibiti suma yanzu zasu shirya su tafi a rikice Janan tace wani asibitin? Ta fada mata sannan sukayi sallama
Dakin Ummiey taje ta fada mata Imran ba shida lfya yana asibiti,
Subhanallah maza tashi ki daura abinci a kai asibitin Yayan ki ya kaimu tunda yau weekend
jiki babu kwari ta wuce kitchen parpesun kayan ciki tayi da paten dankali se kunun tamba bata sa sugar da madara ba sbd kar ya tsinke..
Tana kammalawa taje tayi wanka ta sa riga da skirt ta dau dogon hijjab me hannu ta saka babu komai a fuskar ta, tana fitowa ta tarar da Ummiey har ta shirya,  Janan ta koma kitchen ta kwaso kayan dama ta hada komai a basket tare suka fita sbd khaleel ya fara musu horn..

Suna zuwa asibitin suka tarar da har kannen shi sun zo, har kasa Janan ta duqa ta gaida Mommy da Daddy cike da jin kunya, Ummiey da Yaya Khalee suka gaida su tare da tambayan jikin Imran din, idon Imran a kan Janan ji yayi wasu hawaye sun ciko mishi ido ya rasa na menene, da kyar ta karasa kusa dashi ta gaida shi da jiki ta fita waje sbd gaba daya ta kasa sakewa a dakin tana fita su Hameeda suma suka fito suka zauna tare da ita suna mata hira nan Ameerah karamar su dake kusa da ita tace wallahi Anty Janan kina da kyau Ina sonki sosai, murmushi Janan tayi tare da ja mata kumatu tace kema kina da kyau sosai
Wow! Yawwa ngd miki dama su Yaya Hameeda na cewa nice mummunar gidan mu yau kin wanke ni tayi musu gwalo duk suka kwashe da daria….

Se yamma suka shirya tafiya Mommy nata jin dadi sbd Imran yaci abincin da su Janan suka kawo dama tuntuni take fama dashi yaci yaqi se yanzu..
Har gaban mota Mommy ta rako su sannan tace  “Angel yaushe zaki zo gidan mu?
Cike da jin kunya ta sunkuyar da kanta qasa sbd sunan data kirata dashi bata taba zaton har yan gidan su Imran sun san sunan da yake kiranta dashi ba… Mommy ta kara cewa shikenan tunda kunyata kike ji ni dai ba yar kunya tsakanin mu sbd na dauke ki tamkar su Hammeda, Ummiey dai tana gefe bata ce komai ba..
Janan cikin jin kunya tace zan zo in shaa Allah
Mommy tace “Toh Allah ya kaimu sannan tace ma Ummiey “Hajia mungode Allah huta gajiya…
A ba komai ai Allah ya bashi lfya, suka amsa da Ameen sannan Khaleel yaja mota suka tafi

Likita ne ya shigo ya kara duba shi sannan yace ma Daddy yana son ganin shi a office, tare suka tafi bayan ya bashi wajen zama se yake ce mishi “anyi gwaji malaria da typhoid ke da mun shi se kuma baya samun isheshen bacci yanzu ga takardan maganin da za a siya mishi gobe da safe in Allah ya kaimu za a sallame shi sedai wani hanzari ba gudu ba a kwajin da mukayi akwai abun da nake so mu tattauna a kanshi da fatan zaka bani hadin kai…

_Kuyi hakuri da wannan_
_Ku sani a adduoin ku Dan Allah_

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [10/2, 7:35 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鉂も櫍鉂も櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾犫潳鈾b櫏鈾犫潳鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾b潳鈾犫櫏鈾b櫏鉂も櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾モ櫍

Rukkybae 馃槒馃槒馃槒

*Ya Rabbi ka bawa Baba na lfya da tsawon kwana.. Allah ka sa kaffara ce a gare shi we love u Baba*馃槶馃槶馃槩
*Ya Allah duk waenda ba su da lfya gida da asibiti Allah ka basu lfya mai anfani.. Ameen*

     ****9鈨�8鈨�****

Daddy yace in shaa Allah ba matsala ai duk mun zama daya”
Likita yace ka san abunda ake nufi da sickle cell?
Daddy yace eh”
Likita ya cigaba da fadin bayan gwajin da muka yi mun tabbatar da Imran idan ya auri mace wacce genotype din su ya zo daya toh akwai high probability za su haifi sickler

Daddy yace ban gane ba menene genotype din nasa kuma mene ne risk din dake ciki in ya auri me genotype irin nashi?

Likita yace AS ne genotype din shi kuma idan AS da AS suka auri juna toh za su sami yara masu dauke da cutar sickler wacce a yanzu ta zama ruwan dare shi yasa asibitoci da wajajen bauta, gidan radio da telebijin suke fadakarwa akan ayi gwajin jini sbd cututtukan zamani da kuma sanin kwayoyin hallitan juna sbd ana samun yawan macece a cikin alumma sbd wannan cutar
da yanzu zan kai ka inda ake basu magani za kayi mamakin yawan su shiyasa nake so ku tabbatar in zai yi aure a kawo matar domin duba jinin ta sbd lfyar su da kuma kwanciyar hankalin su..

Daddy ya gyada kai tare da jinjina abun a ran shi kuma shima ya sha ganin yanda mutane ke fama da wannan cutar a lokacin ya tuno da yarinyar abokin shi yanda suke fama kullum asibiti gata ta girma amma har yanzu ta rasa wanda zai aure ta sbd wannan ciwon nata, seda ya nunfasa sannan yace ma Likita in shaa Allah ni da kaina zan kawo su dama yanzu bikin su kwata kwata be fi wata 3 ba zan je in samu Baban ta sbd mu fahimce juna sbd mu gudu tare mu tsira tare..

Dr. Yace shikenan Allah yasa a dace.. Suka sake musabaha sannan Daddy ya fito daga office din..

Washe Gari aka sallame su Likita yace kar ka manta da maganan da mukayi!

Daddy yace in shaa
Allah…

Bayan sun koma gida Imran yayi wanka sannan ya ci abinci ya sha magani ya kwanta amma ba bacci yake ba Hammeda ta turo kofar ta shigo tare da gaishe shi da jiki sannan ta miqa mishi wayan shi tace Yaya gashi na ajiye maka ne sbd kar a dinga kiran ka a asibiti..

Ya karba tare da fadin good girl ngd sosai..

Ta fita tare da rufe mishi kofan.
Tana fita ya kira Janan sbd yaga text mssgs din ta da missed calls din ta..
Sun ji dadin jin muryar juna seda suka rama hiran kwanakin da basu yi sannan suka yi sallama…

Mommy da Daddy na zaune a parlour ya kwashe duk yanda sukayi da Likita ya fada mata tare da neman shawaran ta akan yanda zasu tunkari Iyayen Janan da wannan zance..
Ajiyar zuciya ta sake tana fadin gaskiya nima na rasa yanda za muyi sbd nima naji abun banbarakwai ballatana su…
Daddy yace wallahi kuwa amma da yardar Allah zan je in same shi kin san yanada ilimi ba zai kasa fahimtar magana ta ba dadin muaamula da mai ilimi kenan..
Mommy tace gaskiya ne Allah dai yasa mu dace..
Ya amsa da Ameen..

Wayar shi ce ta fara ringing ya dauka, yana gamawa yace kinji wai zamu tafi Istanbul wani seminar se bayan wata daya zamu dawo..
Mommy tace Toh fa! Allah ya bada saa yasa kuje a saa ku dawo a saa Allah kuma ya kare min kai yaushe za ku tafin?
Gobe wai morning flight za mu bi so yanzu dole zan je office in ji yanda ake ciki ki hada min kaya na Bari in je in dawo..

Da asuba Daddy ya gama shirin shi sbd Mommy ta kasa taya shi duk tayi wani iri idonta ya ciko da kwalla..
Daddy ya dawo gefen gadon ya zauna yana fadin “ohhh Darling bana son inga kwallan ki ya zubo ko kadan ne.
Kuka ta fashe dashi tare da fadawa jikin shi tace bana so ka tafi sbd zanyi missing dinka sosai..
Nima zanyi missing din ki babu yanda zanyi ne da tare dake zamu tafi amma kinga su Ameerah na zuwa sch babu yanda za ayi mu barsu su kadai ki dena kuka kin ji My Wifey yasa hannu yana goge mata hawayen tare da fadin ki dena mun asaran hawayennan sbd yanzu kin girma..

Tace in dai a wajen ka ne bazan taba girma ba am still a Baby..
Daria yayi yace toh shikenan zan kawo miki pampas da feeder tunda u r still a Baby… Duka suka kwashe da daria ta ce tashi muje kar kayi latti tayi mishi goodbye kiss shi kuma ya ce hau in goya ki ba musu ta hau seda ya kaita parlor sannan tace Toh ya isa haka sauke ni
daria yayi sannan ya sauke ta… Yaran ne suka fito daga dakin su suka gaida su
Mommy tace ku kwaso sauran kayan Daddy mu raka shi da sauri suka kwaso kayan Imran ne ze kaishi office sannan motan office din su ya kaisu airport.
har bakin mota suka raka shi yana daga musu hannu ya bar gidan su kuma suka koma ciki…

Yau ta kama Friday Dr. Godwin ya shigo sanye da fararen kaftan ya sa wani black slippers irin na maza se black agogo se bakin glasses ya gyara gashin kanshi se faman kanshi yake yi ga wani annuri dake fita a fuskar shi alamun yana cikin farin ciki tun daga kan masu gadi ya fara rabon kudi harda nurses duk ya basu rabon su..

Kowa se mamakin shi yake yi dan tunda yake be taba shigowa cikin farin ciki ba kullum cikin shan kamshi da jijji da kai…

Yana shiga office yace ma masinja yau Ina off babu patient din dazan duba ka tura su office din Dr. Magaji jiya nayi mishi bayani..
Masinja yace an gama ranka ya dade sannan ya fita…

Janan ta shigo ganin Dr. Godwin cikin kaftan abun ya bata mamaki a ranta tace  “wow gaskiya yayi kyau kamar ba Christian ba”
Kallon ta yayi yace ya dai kike kallo na ko nayi miki kyau ne?

Gefe ta kauda kanta kafin tace no baka yi kyau ba

A hankali ya taho yazo dab da ita ya hura mata iska a fuska har seda eye lashes din ta suka motsa kamshin turaren shi da sweet din ya yake sha suka hadu suka bada wani kanshi me dadi a dolen ta ta lumshe ido…
Kallon ta yake yi can yace zaki raka ni wani waje?

Ido ta zaro tace Ni?

Yes ke!

Gaskiya ba… Hannun shi ya daura a kan lips din ta yace karki ce ba zaki ba plssss! Yanda yace plss din ya bata daria sbd yayi kamar karamin yaro kuma bata taba zaton ze iya roqonta ba…
Shiru tayi bata ce komai ba

Yace I promise to do whatever u want ba zan miki abun da ba kya so ba I just want to spend a little time with u… Just do this for me yau kadai!

Be kamata ace ta bishi ba sbd ba muharramin ta bane amma a zuciyar bata jin wani tsoro dan tasan shi in yace ba zai yi abu ba bayayi… Ajiyar zuciya ta saki sannan tace na yarda…

Yess! Thank u Baby se wani irin dadi yake ji..
Ita dai Janan gani take kamar a film wai yau ita Dr. Godwin the mighty yake ce ma thanks…

Key din  motar shi ya dakko yace let’s go!
Waje ya fita ta bishi yace can I hold ur hand?
Wani harara ta watsa mishi tare da fadin No!
Daria yayi yace “am just kidding kin san dai ba zan miki abun da ba kya so ba…

Sabuwar motar shi BMW fara sol tasha tinted ya nufa tare da danna mabudin suna karasowa ya bude mata gaban mota seda ta zauna sannan ya koma ya shiga shima..
Da mugun gudu ya figi motar har Janan na buge kai
seda suka hau kan titi sannan yace ki daura belt din ki.. Babu musu ta daura sbd tasan in dai ya cigaba da kalan tukin nan nashi ta dinga bugewa kenan..
Wakan *Despacito* ya saka ya kure volume da sauri Janan ta toshe kunnen ta da karfi tace wayyo ear drum dina zai toshe
A hankali ya rage volume din..
Tace gwara haka dai

Hotel 17 taga ya sa hancin motar shi da sauri ta kalle shi tana neman karin bayani, ya gane me take nufi yace mata “chill babu abunda ze faru kin san am nt a bad person just watch nd see!

Parking space yaje ya ajiye motar shi sannan ya kira wani numb yace “hey! Mun karaso fa.
Bata ji me aka ce ba yace OK but anything that happens to her ke zan kama nd also do whatever she want bana so a bata mata rai! Hope u understand! Ya sake cewa better..

Fitowa yayi sannan ya bude mata itama ta fito suka fara tafiya suna zuwa daidai wani lungu yace ki bi nan za ki ga wata me qiba ki bita.

Kamar ya in bi wacce ban sani ba?
Be kulata ba ya juya abin shi bata da wani zabi face tayi abunda yace dan taga alaman miskilancin nashi ya motso..

Cike da tsoro ta bi lungun bata ga kowa ba ji tayi an dafa mata kafada sallati ta fara yi amma ta kasa juyo wa sbd tsaban tsoro……

Miyau ta hadiye da kyar sannan ta juyo, wata mata ta gani kafin tayi magana matar tace  “sunana Suhailat nice wacce Doc yace kizo waje na”
Kai Janan ta daga tare da fadin OK
Suhailat tace  “in bazaki damu ba muje ko!
Ba musu Janan ta bita….

Cikin wani daki me kyau suka shiga Suhailat ta nuna mata kujera tace pls sit ina zuwa… Bayan mintuna 3 ta fito,
wani guri kebabbe tace ma Janan ta shigo
kallon ta kawai take yi, wata dogon riga fara da baka me kyan gaske ta miqa ma Janan din tace ki saka Ina zuwa..

Tsayawa tayi tana mamakin me hakan yake nufi seda tayi kusan secs 30 kafin ta tashi ta saka kayan full length mirror din dake wajen ta juya tana kallon kanta, mamaki take yi yanda kayan suka zauna a jikin ta cass kamar an gwada ta daga sama ya kamata daga kasa kuma ya bude yana dan jan kasa kadan yanada dogon hannu se belt daga baya
tana cikin kallon kanta matar ta dawo tana fadin “wow! So perfect.. U look super cute! Murmushi Janan tayi tace thanks

Inda Janan din ta zauna da farko nan suka koma…

Suhailat ta fito dauke da wani purple & pink jaka ta ajiye a kusa da Janan sannan ta bude fridge ta dakko mata drink..

Jakar ta bude se ga kayan makeup ashe makeup kit ne..
Seda Janan din tasha juice din sannan Suhailat tace kiyi hakuri zan kara miki artificial beauty akan natural beauty din ki! Janan dai bata ce komai ba illa shirun da tayi dan ita gaba daya kanta ya kwance bata san plan din Dr. Godwin ba..

Cikin minti 40 ta gama mata makeup din..
Ya Salaammm! Fadin irin kyan da tayi bata lokaci ne a takaice dai shi looks extra ordinary beautiful…
Gashin kanta Suhailat ta gyara tayi mishi style ta yi parking din shi a tsakiya, bakin veil ta dakko tayi mata rolling irin na Larabawa

Takalmi hill ta dakko ta miqa mata,  Janan na cikin sawa sega kira ya shigo wayan Suhailat da sauri ta dauka tana fadin sorry Doc. Yanzu zan kawo maka ita ka bani 3 minutes”
be ce komai ba ya kashe wayan.
Janan ta kalle ta tace Miss Suhailat pls why all this? What r u guys planning?

Suhailat tace  “ki bari Dr da kanshi ze miki bayani ni dai ga iya abunda ya sani kenan kiyi sauri kisa takalmin yana jiran ki…
Janan ji tayi kamar tayi kuka amma haka ta daure ta gama sa takalmin… Suhailat tace Tubarakallah Ma shaa Allah! Ki gode ma Allah gaskiya u r a real definition of beauty, Bari in dauke ki hoto…
Haka ta dinga mata hotuna sannan tayi musu selfie sunyi kyau sosai!
Wajen mirror din ta sake kai Janan tace just take a look at ur self”
ita kanta gani take kamar ba ita ba sbd gaba daya ta canza ta zama kamar wata Amarya a ranta ta gode ma Allah da wannan baiwar da yayi mata…

Hannun ta Suhailat ta riqe suka fito tare,  wani guri ta nuna mata tace can zaki shiga ni ga iya inda aka bani izini tsayawa”
Janan tace gaskiya am scared ba zan iya zuwa ni kadai ba

No karki ji tsoro zan tsaya a nan har se kin shiga zan wuce”

Babu yanda ta iya haka ta fara tafiya tana yi tana waigen Suhailat seda ta kai kofan shiga sannan Suhailat ta daga mata hannu ta juya…

Rufe ido ta yi gam sannan ta tura kofan ta shiga.. Duhu ta gani a ciki kamar ta koma se kuma ta daure ta cigaba da tafiya seda ta kai tsakiya sannan taga haske ya mamaye gurin daga baya ta jiyo muryar Dr. Godwin yana wakan happy birthday…
Da sauri ta waiga tana kallon shi cike da mamaki, a hankali ya tako yazo daidai gaban ta yace
“kinyi mamaki ko? Today is 14th Feb ur birthday nd also my birthday”

Se a lokacin ta tuno yau birthday dinta kwata kwata ta manta da wani abu wai shi birthday

Hannu tasa ta rufe bakin ta Cikin jin dadi tace “ya akayi kasan birth date dina?

Sbd nima birthday dina ne shiyasa yau kika ganni so excited duk da bana celebrating se dai su Momma suyi dan ni bana son hayaniya amma yau tunda na samu birthday mate shiyasa na hada mana at least yau am happy kuma zai zama history cewa I celebrated my birthday once in my life with u kuma na saki farin ciki…

Kallon shi kawai take yi amma she is totally speechless. A ranta tace shiyasa yake ta faraa harda sa kaftan ashe yau birthday din shi …
Ganin bata da niyyan magana yasa ya raba ta gefen ta seda yazo gefen kunnen ta yace “kinyi kyau sosai u look like a princess ya wuce sannan yace muje ko!
ba musu tabi bayan shi steps kamar guda 3 suka hau sannan suka iso wani waje rufe da curtain hannu yasa yaja curtain din gafe!
Ohhh My God!! 馃槏 gurin zagaye yake da decoration black nd white se table aka daura katon cake akai da wasu manyan drinks da flowers red se kujeru guda 2 a gefe akwai haske sosai a wajen ga wani sanyi me ratsa jiki se dan karami swimming pool daga gefe, wajen ya hadu iya haduwa..
Kallon ta yayi yace kina son wajen ko be yi miki ba?

Tace “I love it yayi min kyau sosai”

Duk kyan wajen be kai kyan ki ba..
Ita dai shiru tayi, gaban cake din yaje ya yanko yace  “ahh” alaman ta bude baki
Ido ta zaro waje kamar ya I should open my mouth!?

Yace “Yes ki bude nace”
kafada ta maqe kamar karamar yarinya..

“Ki bude ko in matse miki bakin”

Ka manta kayi alkawari ba zaka yi min komai ba kuma kace duk abunda nake so za kayi min ?

Naji bazan miki ba ai wannan ba komai bane..
Ita dai taki yarda haka ya hakura ya kyale ta….

Sunci sun sha ya dauke ta hotuna sun kusa 50 duk wani motsi a idon shi take yi kuma se ya dauka haka suka gama komai duk da hankalin ta yana gida amma yau ta daure har sun ta taba hira..
A cikin hiran su take ce mishi can I ask u a question?

Yace yea go ahead u are free to ask me anything..

Tace “anything fa kace koda baka son magana akan abun kayi alkawari zaka fada min?

Yace eh zan fada miki

Ajiyar zuciya tayi kafin tace “me yasa baka taimako kuma baka so a ambaci taimako?

Lebe ya cije tare da runtse idon shi zuciyar shi ta fara tafarfasa kwata kwata ya kasa magana sbd be taba tunanin zata mishi wannan tambayar ba…

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [10/6, 9:43 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫏鈾b櫏鈾b潳鈾モ櫍鈾モ潳鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾b櫏

*Innalillahi wainnailaihirrajiun! Allah ka sa mu cika da kyau da Imani. Mutawar Samari, Yammata da Yara kanana yana daga min hankali gaba daya yanzu a ko Ina mutuwa ake yi Allah kaji tausayin mu ka ji qan mu* 馃槶馃槶馃槶

  

         1鈨�0鈨�0鈨�

Ajiyar zuciya ya sake kafin yace  “nayi miki alkawari zan fada miki in ba dan haka ba babu wanda ze san lbrn nan wannan lbrn daga family na babu wanda ya san shi se ke yanzu da zan fada miki kuma inna gama kema akwai tambayoyin da zan miki kin yarda?

Ta amsa da in shaa Allah in dai na san amsa tambayan zan fada maka”

Wannan al’amarin ya faru ne tun Ina shekara 10….

Kwance muku ni, Momma da Dad a wani kongo bayan na dawo daga dako na samu naira 100 da kudin na siyo mana Gari da ruwa ko sugar babu balle gyada ko kuli kuli…

Ruwa ake sosai kayan jikin mu kwata kwata basa kare mu daga jin sanyi dan duk a yace suke, Momma ce ta fara wani irin nishi nan da nan muka tashi dama ba wani baccin arziki muke ba, Dad ya riqo ta yana fadin abunne? Shiru kawai tayi tana yarfe yarfen hannu amma ta kasa magana da sauri nima na matsa kusa Ina yi mata sannu!  Dad yace in je wajen wani mutum wanda gidan shi ke kallon kongo yazo ya taimaka mana mu kai Momma asibiti

Da gudu na fita duk da ana ruwa naje kofar gidan mutumin Ina ta kwankwasawa amma ba a bude ba seda na juya zan tafi sannan naji ana budewa, gaishe shi nayi sannan na fada mishi abunda ake ciki se ya ce gaskiya bazai iya ba sbd bacci yake ji sannan yanzu be shirya fitowa da mota ba se dai in je wani wajen, rokon shi na dinga yi amma be kula ni ba ja kofar shi ya rufe,
jiki a sanyaye na koma dan in fadawa Dad naje na tarar da Momma ta suma a wajen da gudu na karasa Ina jijjiga ta amma bata motsa ba ban tsaya jiran komai ba na koma gidan wannan mutumin seda na dade sannan ya Kuma zuwa ya bude yana ganina ya fara min fada harda zagi ban damu ba na duka kasa Ina mishi magiya kawai naji ya wanke mun fuska da mari yana fadin kai wani irin yaro ne? Wannan wani irin naci ne?  Idan ka kara zuwa kofar gida na sena sa an kulle ku kaida iyayen ka”
ya hankada ni gefe cikin cabalbali..

Haka na dinga zuwa gida gida Ina rokon mutane amma babu wanda ya taimaka mana har safiya Ina ta yawo ruwa yayi min duka sosai se diga nake yi dama ga kayan ba suda kauri faduwar da nayi suka kara yagewa

Ba wani kwarin gwiwa a tare da ni na koma wajen su Ina zuwa naga Momma nata wani irin jijjjga Dad yana goge mata zufa kuka na fara yi Ina kara fada mishi na rasa yanda zanyi ban samu me kaimu ba shiru yayi shima kukan yake yi yama kasa magana… Ganin be ce komai ba yasa wata dabara ta fado mun na sake fita da gudu,
bakin titi naje na nemo me a daidai ta sahu ban tsaya tayi dashi ba, muka je muka dakko ta se wani asibiti na gwamnati jmuna zuwa ko ta kan me adaidaita bamu bi ba da gudu Dad ya dauke ta aka muka shiga asibitin.. Likita ne ya fito yana fadin kun bude mata file a asibitin nan?

Dad yace aa

Likita yace toh kuyi maza ku bude mata file sannan ku je ku biya kudin aikin da zaa yi mata za ku biya dubu hamsin”

Dad ya fara roqon Likita akan ya rage mana kudin sannan ayi mata aikin kafin ya nemo kudin”

Likita yace mu bama haka a asibiti

Dad yace ka taimake mu karta mutu”

In baka da shi ka dauke ta ku tafi amma mu ba a taimako a asibiti sbd ba wajen taimako bane, nan da minti 30 in baka kawo kudin ba ku bar asibitin nan babu dole se ku wani zo kuna a taimaka muku
yana gama fadin haka yayi tafiyar shi..

Zama Dad yayi tare da dafe kai ya rasa ta inda ze fara..

Nima haka na zauna Ina ta kuka..

Kamar an mintsili Dad ya tashi ya fita ba tare da yace komai ba,
be dade da fita ba se ga me adaidaita ya shigo yana cewa mun barshi a waje bamu bashi kudi shiru nayi sbd ban san me zan ce mishi ba rashin mutunci ya fara mun mutane se kallon mu suke yi yace in baka bani kudina ba zan je in dakko wanda zasu amsan min kudin

rokon shi na fara yi Ina ce mishi ba muda komai ya yi hakuri ya taimaka mana ko kallo na be yi ba ya fita…..

Bayan kamar minti 10 se gashi ya dawo tare da dan Sanda nan aka ce nayi karami ba zaa iya kulle ni ba Ina Baba na?
Nace baya nan ya fita nemo kudin da zaa biya a ma Mama na operation”

Mai adaidaita yace Oga kawai a tafi dashi in Baban ya dawo be ganshi ba dole ya kawo kanshi sbd a sake mishi Yaron shi”

Babu musu Dan sandan nan ya iza keyata ya tafi dani Ina kuka amma babu wanda ya kalle ni balle ya taimaka min”

Bayan awa 2 se ga Dad ya zo waje na ban san Ina ya samu kudi ba yaba yan Sanda sannan aka abude ni duk na sha wahala sbd wari da zarnin cell ga wani dan shaye shaye da yake ciki ya dinga duka na babu wanda ya hana shi…

Lallashi na Dad ya fara yi ni dai hankali na yana kan Momma nan na tambaye shi Ina take?

Yace min kar in damu tana nan lfya kuma ta haifi baby girl”
doki da murna yasa na manta halin da nake ciki…

Wani gida me kyan gaske muka shiga se dai ba wani babba bane gidan amma ya yi kyau ko Ina an kwata shi…. Wani daki muka shiga nan naga Momma kwance tana bacci akan Gado ga Baby a gefe ita ma cikin gadon ta… Mamaki na dinga yi nace Dad gidan waye wannan?
Yace namu ne Son muje in nuna maka Dakin ka…

Tun daga lokacin rayuwar mu ta canza muka koma rayuwar jin dadi sakamakon wani babban alamari daya faru wanda bazan iya fada miki ba watakila se nan gaba….. Kuma yau kinji dalilin da yasa bana taimako kuma bana so a furta min kalmar taimakotaimako!

Janan wacce tunda ya fara bata lbrn take kuka tare da tausayawa rayuwar shi ta baya.. Wani irin ajiyar zuciya tayi sannan tace “gaskiya kunyi facing hardship a rayuwar ku amma…..

Dakatar da ita yayi yana fadin mu bar maganan.. Kamar yanda nace miki akwai tambayoyin da zan miki kin shirya in tambaye ke?

Kai ta daga alamar eh”

Yace……

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [10/7, 2:40 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫍

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

_Mata mune iyayen giji tarbiyyar Yara na hannun mu! Mene ne anfanin exposing jikin mu? Me yake kara mana? Wace riba muke samu akan haka? Mutuncin mu yafi komai! Dame muka fi matan da suka gabata kafin mu? Shin se mun bayyana baiwar da Allah yayi mana kafin mu samu masu son mu? Mace ta gari itace me kare darajar da Ubangiji yayi mata…. ALLAH ka yafe mana ka bamu ikon kare mutuncin kan mu Ameen!_

_Tunatarwa ce_馃憣馃徎

         1鈨�0鈨�1鈨�

Yace Ina so ki fada min mene ne musulunci? Da duk abunda kika sani game da musulunci sannan Ina so ki fada min abunda ke sa mutum ya zama cikakken Musulmi kuma Ina so ki fada min akwai tursasawa a addinin ku! ma’ana ana tilasatawa mutum shiga addinin kuma dole ne yayi alkawari akan bazai bar addinin ba?

Zama Janan ta gyara sannan ta fara da fadin “zan baka amsar tambayoyin ka daidai abun da na sani sbd shi ilimin addinin musulunci yanada zurfi….. Kamar yanda yazo a cikin littafin tauheedi _Mulunci shine miqa wuya ga Allah da kadaita shi which means yarda da Allah shi kadai ba tare da hada shi da komai ba_..

Yace ban gane ba ki kara min haske”

Zan maka misali da Christian yanda zaka fi fahimta kun yarda da Allah amma baku kaida ta shi ba u believe in trinity ( Father, Son and d Holy spirit) kun yarda kuma kuna fadin Annabi Isah ‘Dan Allah ne (Wa’iyazubillah) mu kuma munce Annabi Isah Manzon Allah ne, kuma ita maihaifiyar Annabi Isah ayace ga mutane baki daya domin mutane su tabbatar da Allah can do d possible frm impossible nd d impossible frm d possible kuma ze iya tashin rayayye daga matacce sannan matacce daga rayayye…
Sannan dole ne Imani da Allah,
da Manzonin shi,
da Mala’ikun sa,
da littafan sa (Attaurah, Injila wato Bible,  Zaburah da kuma Al’qur’ani mai girma)
Imani da ranar tashin alqiyama sannan Imani da Kaddara me kyau da mara kyau..
Sannan kalmar da yake tabbatar da mutum ya zama cikakken musulumi shine _Laiha illallah Muhammadurrasulullah (SAW)… (wato Shaidawa babu abun bautawa da gaskiya se Allah kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne)_..

Kamar yanda yazo a cikin Hadisin Annabi Muhammad (SAW) an gina Musulunci akan abubuwa guda 5

1. Shahadatain (shaidawa babu abun bautawa da gaskiya se Allah kuma Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne

2. Ikamatussalah (tsaida sallah maana kiyaye sallah akan lokacin ta)

3. Saumu Ramadan (azumin watan Ramadan)

4. Eeta’uzzakah (Bada zakkah)

5. Hajj (aikin Hajji ga wanda Allah ya bawa ikon zuwa)

Ajiyar zuciya Dr. Godwin yayi sannan yace kuma kun yarda da Bible kenan?

Tace eh mun yarda da Bible domin kafin zuwan Annabi Muhammad (SAW) lokacin Annabi Isah da Bible ake amfani amma bayan zuwan Annabi Muhammad (SAW) se aka umurce mu da anfani da Al’qur’ani me girma domin  duk wani abu dake cikin dukkan littattafan da suka gabata a kwai shi a cikin Al’qur’ani me girma shiyasa duk wani Musulumi ya dena anfani da Bible sbd a halin yanzu babu old testament wanda yake na ainihi se new testament wanda a ko wani lokaci ake cikin caccanza abubuwan dake ciki waenda suka sabawa koyarwar Annabi Isah..

Shiru yayi ko me yake tunani oho! Ya sake cewa shin Christian ze iya auren Musulumi?

Tace eh akwai aure tsakanin Ahlul kitab da Musulmi amma ba a cika yin haka ba sbd yawan matsaloli da ake samu sannan hakan yana jan rabuwar kan yara sbd kowa ze so subi addinin sa,  sannan Musulumi baya cin gadon Christian…

Ya Kuma cewa toh idan addinin ku daya amma ba yaren ku daya ba fa?

Za su yi auren su mana sbd babu tribalism a Islam domin Allah Madaukakin Sarki ya fada a cikin Al’qur’ani : _ya ku mutane lallai Allah ya hallice ku Maza da Mata, kuma ya hallice ku qabilu daban daban domin kuyi tarayya da juna, babu wanda yafi wani se wanda ya fiku tsoron Allah_

Mene ne tsoron Allah?

Shine gujewa duk wani abunda yayi hani dashi,  kaji tsoron shi kamar kana ganin shi, idan kai baka ganin shi to shi yana ganin ka.. Sbd duk wanda ya aikata aikin kwarai ze sa shi a cikin Aljannah wanda kuma ya saba mishi ze shiga wuta”

Yace “na yarda Shi ya hallice mu with different structure akwai wani anfani da surorin mu za suyi wajen shiga Aljanna ko wuta?

Tace “tace aa babu wani anfani da za suyi domin bayan mun mutu duk tsutsotsi ne zasu cinye jikin kuma Hadisin Manzon Allah yana fadin ” “! _”lallai Allah baya dubi zuwa ga jikkunan ku, ko zuwa ga surorin ku, se dai shi yana dubi zuwa ga zuciyoyin ku da kuma ayyukan ku_

Kallon ta kawai yake yi yana kara jin wani irin sonta na shigar shi…

Yace sannan se tambayar da na miki akan cewa akwai tilastawa a cikin addin ku?

Janan tace babu tilastawa a cikin addinin Musulunci domin fadar Allah (SWT) a cikin Al’qur’ani me girma cikin Suratul Baqarah Aya ta 256: _Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata, duk wanda ya kafurcewa gumaka kuma yayi Imani da Allah toh lallai yayi riqo da igiya me karfi wacce bata tsinkewa, kuma Allah Mai ji ne,  Masani_:

Hawaye ne ya fara kwaranyowa daga idon Dr. Godwin….

Cike da tsoro Janan take kallon shi dan tunda take bata taba ganin hawayen shi ba se yau wani irin tausayin shi taji a ranta tana mishi kwadayin musulunta sbd ya samu rabo gobe Qiyamah…
Maganar shi ta dawo da ita daga tunanin da take yi inda yake ce mata shin wani abu ne mafi girman sabo a wajen Allah?

Kamar yanda yazo a cikin littafin Kaba’eer (wato manya manyan zunubai)  akwai abubuwa masu yawa waenda suke a matsayin manyan zunubai a wajen Ubangiji but zan fada maka kadan daga cikin su..
Akwai shirka! Wato hada Allah da wani  a wajen bauta kamar mutum, dabba, rana, wata, taurari, wuta da duk wani abu da mutum yayi Imani da shi wanda ba Allah ba!
Sannan saba ma iyaye
Sannan Zina, Luwadi, Madigo duk suna cikin manyan zunubai… Duk wannan abubuwan dana lissafo babu wanda ba a aikatawa a bayan kasa kuma duk da haka idan muka roki Allah gafara yana yafe mana domin shi Mai Gafara ne kuma Mai Tausayi….
Hmm lallai Ilimin addinin Musulunci akwai shi da zurfi se dai ni a ganina Islam is so complicated komai kayi se ace ba daidai ba kuma akwai hukunci akai…

Tace No no no u r mistaken! Islam is nt complicated and it will nvr be cuz it is d total way of life sbd babu abunda Musulunci be koyar da mu ba, ya koyar damu yanda za muci abinci,  kamar yanda yazo a hadisin Annabi Muhammad (SAW)  inda yake cema wani Yaro lokacin da zai ci abinci : _ya kai Yaro! Ka anbaci sunan Allah, kuma Kaci da daman ka, kuma Kaci abunda ke gaban ka_…
Musulunci ya koya mana zamantakewa da mutane, kula da iyalin mu, da abubuwa masu yawa wanda idan nace zan fada maka ba zan taba iya gamawa ba, kuma shi hukuncin da ake yankewa mutum se yayi laifi idan beyi laifi ba babu yanda za a zalince shi domin Allah Madaukakin Sarki yana fadin _Lallai na haramtawa kaina zalunci kuma na sanya shi haramun ne a tsakanin ku, kada kuyi zalunci_

Hmmmm! Yau na gane abubuwa masu yawa thanks a lot, ki tashi in maida ki gida… Ya dau glasses din shi ya maida ido sbd baya so taga yanda suka kada suka yi ja cake din kawai ya dakko suka fito, mota suka shiga yazo fita ya cewa masu gadi suje su kwashe sauran drinks da abincin!! Godia suka fara mishi be bi ta kansu ba yaja motar shi suka tafi…. Babu me cewa kowa komai sbd kowa da kalan tunanin shi wannan karan a hankali yake tukin ko waka ma be kunna ba…

Daidai kofar gidan su Janan ya tsaya ya bude kofa ya fito itama ta fito tana fadin “Nagode sosai Doc. Seda safe” ta juya ta fara tafiya… Da sauri ya kirata ta juyo yace ki zo mana”
Ba musu ta dawo booth ya bude ya dakko wasu ledoji guda 2 se wani karami akwati wanda be fi girman hannu ba ya bata yana fadin ga birthday gift din ki kuma bana so ki furta ko kalma dayace” shiru tayi..

ya ce bari in taya ki shiga da kayan ke kuma ki dakko cake din”
Babu yanda ta iya haka ta bude motan ta dakko cake din da kyar sbd nauyi duk tsoro ya cika ta sbd bata san me zata ce a gida ba…. Ji tayi yace take care of ur self inna kai gida I will call u” ya daga mata hannu yayi shigewar shi mota ya wuce…

Tafi minti 15 tana tarabbabin shiga gida can dai tayi adduaa ta shige…. A parlor ta tarar dasu duka tana sallama suka amsa nan parlor ya kaure da wakan happy birthday! Dadi ne ya kamata ta shiga ta ajiye cake din akan table tace Ina zuwa ta koma ta kwaso ledojin.. Mamaki suke wa ya bata kayan, nan dai ta basu lbr amma ta kasa fada musu sun je Hotel 17 sbd abun ma ba zai yi dadi ji ba… Ba su kawo komai a ransu ba suka cigaba da nasu celebration din…
Daki ta shiga ta bude karamar akwatin nan dan duk ta kosa taga miye a ciki sbd se daukan ido yake, wani zobe ta gani karami na gold me kyan gaske, ido ta zaro tana mamaki, ta bude drawer ta ajiye…..

Seda tayi wanka sannan ta tuno da wayar ta dake cikin jaka ta dakko nan taga missed calls kusan 28 duk Imran ne kafin ta kira ya ya kara kira tana mishi sallama tace “ayi min hakuri kaina bisa wuya” Duk wani  bacin ranshi yaji ya kau sukayi hira sosai yayi mata adduaa na shiga wani shekaran tare da fatan samun lfya da tsawon kwana a gare ta…..

Tunda Dr. Godwin ya sauke Janan a gida yake ta wasu irin tunane tunane ya rasa me ke mishi dadi a haka har ya kai gida… Dakin baccin shi ya wuce ya haye gado sbd yana bukatar bacci, be dade da kwantawa ba bacci ya kwashe shi cikin baccin ya fara wasu mafarkai wanda suka haddasa mishi tashi a firgice…..

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [10/9, 8:22 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ潳鈾b櫏鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ潳鈾b潳鈾b櫏鈾モ潳鈾モ潳鈾モ潳鈾モ潳鈾b潳鈾b潳鈾b潳鈾b櫏鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鉂も櫍鈾モ潳鈾b櫍鈾モ潳鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b櫍鈾モ潳鈾b櫏鈾b櫍

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

_Alhamdulillah 馃槝馃槏Baba yaji sauki sosai.. Ngd da adduo’in ku Allah ya bar zumunci…. Allah ya biya mana bukatun mu na alkhairi baki daya_

          1鈨�0鈨�2鈨�

Ji yayi kanshi na juyawa sosai a take ya fara tuno mafarkin yana so ya gane me mafarkin yake nufi….

Cikin mafarkin yaga Janan sanye da fararen kaya shi kuma gashi can da Momma, Dad, Annabelle a kulle da wasu igiyoyi ko motsin arziki basa yi a hankali take takowa har tazo gaban su ta durkusa a kasa tare da fadin  “kuce ashhadu an La ilaha illallah”

Godwin da Annabelle na kokarin fadan haka Dad yace aa! karku fada! kar ku fada! kar ku karya alkawari karku karya!

Janan ta tashi tare da miko hannuwan ta biyu Annabelle da Godwin suka mika mata amma sun kasa riqe mata hannun.. Duk Iya kokarin su sun kasa se gani sukayi tana ja da baya su kuma suka fada wani rami me zurfi da tsananin duhu… . Mafarkin daya farkar dashi kenan a firgice… Jikin shi duk yayi weak gashi yana jin kan shi na wani irin yi mishi ciwo… Bayi ya wuce yayi wanka ya sauya kaya zuwa riga baka da wando 3quarter… Wayar shi ya jawo ya fara kallon hotunan da yayi ma Janan dazu a take yaji wani irin natsuwa na saukar mishi duk wani tsoron da yake ji ya fita daga ranshi…. Be kirata ba sbd be san me ze ce mata ba duk da yana missing dinta sosai, da kyar ya iya cin abinci ya zauna yana dube dube a laptop din shi…

    _Bayan Sati 2_

Biki se matsowa yake yi duk wani abu daya dace su Ummiey da Abbiey sun yi jira kawai suke yi lokaci yayi…

Kamar koda yaushe yau ma Imran din ne ya kaita asibiti seda ta zo sauka sannan ya mika mata wasu envelope guda biyu yace daya naki da frnds din ki dayan kuma na Ummiey, anjima in shaa Allah zan kaima Abbiey nashi da kaina,
Murmushi tayi tare da fadin na gode sosai Nurul_Qalb Allah ya kare mun kai..
Ya ce Ameen Angel se munyi waya… Suka daga ma juna hannu ya wuce ita kuma ta shiga cikin asibitin….

Tana shiga bata ga Dr. Godwin ba cike da mamaki take tambayar kanta toh Ina ya shiga!

Bata fi minti 5 da zama ba se gashi ya shigo sanye da Navy Blue riga da Navy Blue jeans se bakin cover shoes, yayi kyau sosai
Kallon ta yake yi gani yayi ta kara kyau…
Be mata magana ba ya zauna sbd yau duk ji yake wani abu ya tokare mishi maqogoro ya rasa mene ne haka..

Kiran shi aka yi a waya da sauri ya fita..

Wajen su Eesher taje ta basu kati suna ta mata tsiya ita dai bata kula su ba nan suka yanke weekend za su raka ta rabon kati, tayi musu godia ta koma office din kafin ya dawo….

Lokacin data shigo ta tarar har ya dawo cikin office din se faman hada abubuwan bukatan shi yake yi yana juyowa ya ganta, key din shi ya dauka yace “ni nayi tafiya se bayan 3weeks zan dawo so ga office nan ki kula da shi watakila za a kaiki office din Dr. Magaji ki dinga taya shi aiki kafin in dawo”
Yana gama fadin haka ya fita da sauri sbd wayar shi se ringing take yi..
Yana fita tace “Alhamdulillah gwara ka tafi zan samu ayi biki na cikin kwanciyar hankali, in dai aka maida ni office din Dr. Magaji na huta kuma na san ze dunga daga min kafa ba kamar wannan Dr. Godwin din ba…

Duk wata old frnd din su sun kai mata kati ba suyi anko ba ance kowa tasa kayan da take so… M.Sabo tace “haka za ayi biki ba wani motsi!

Zee tace ke ma ai kin san halin mutuniyar taki bata da son bidi’a..

Eesher da take gefe tace “ai an hadu ne da an dace shima Dr. Imran din baya so”
Duk suka kwashe da daria se yamma likis sannan suka koma gida…

Yau Daddy ya dawo kowa a cikin su yana farin ciki, an hada mishi abinci masu kayatarwa na gargajiya sbd shi dai be bar al’adar shi ba,  seda yayi wanka ya huta can da dare bayan sun gama cin abinci Imran ya kwaso katunan biki ya ba Daddy, cike firgici yace har ka bugo kati? Ka kai musu ne?

Imran ya fara sosai keya yace eh na kai musu Daddy….

Sallati Daddy ya fara yana fadin kayi gaggawa Imrana, na so ace ka bari na dawo se a yi a tsanake, akwai abunda nake so mu tattauna da Baban ta, gobe in Allah ya kaimu da yamma in ka dawo daga office ka kaini gidan nasu sbd maganar nada muhimmanci..
Imran dai be gane inda Daddy ya daso ba babu yanda ya iya yace in shaa Allah goben se muje..

Daddy yace tashi kaje Allah ya kaimu

Yana shiga daki ya kira Janan ya fada mata gobe Daddy ze zo wajen Abbiey,

tace Allah ya kaimu da safe in Allah ya yarda zan sanar da Ummiey..
Yau dai hirar su ba wani walwala a cikin ta gaba daya Imran ya rasa me ke mishi dadi, da Janan din ta tambaye shi sai yace  “Angel ban san abunda ke damu na ba kawai ji nayi gaba na yanata faduwa ban san dalili ba”

Ayya Nurul_Qalb ka yawaita fadin “innalillahi wainnailaihirrajiun.. ni ma kwata kwata bana jin dadin jiki na ji nake yi kamar zazzabi na son kamani..
Haka dai suka gama wayan suka kwanta..

Washe Gari da safe ta fada ma Ummiey ita kuma ta fadawa Abbiey, can da yamma se gasu sun zo kamar yanda sukayi alkawari, an sauke su a parlorn baki aka kayata gaban su da kayan ciyeciye da shayeshaye kala kala.. Sun dan ci sannan aka sake gaishe gaishe Imran ya tashi ya koma mota sbd ya basu dama suyi maganan su…
Daddy yayi ma Abbiey bayanin komai,
Abbiey yayi shiru yana sauraren shi bayan Daddy ya gama se Abbiey yace  “gaskiya nayi farin ciki da wannan hangen nesan da kuka yi kuma haka shi yafi dacewa da ma’aurata kafin auren su sbd gudun abunda ze je ya dawo, kuma duk wani abun da zai faru toh lallai dukkan mu zai shafa ba su kadai ba, in Allah ya kaimu cikin satin nan se suje ayi gwajin Allah yasa mu ji alkhairi…

Daddy ya amsa da Ameen cike da jin dadi kuma ya yaba da dattakun Abbiey… sallama suka yi sannan suka tafi..

Da dare suna daki shida Ummiey ya bata lbrn komai, itama ta goyi bayan haka kuma taji dadin hukuncin da suka yanke…..

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/8/2017, 10:15 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/8, 7:28 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫊鈾モ櫍鈾モ櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏

馃寪HAJOW馃寪
*Hakuri Da Juriya Online Writers*鉁嶐煆烩湇馃徎

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒

_Alhamdulillah! Na gama exams dina lfya se fatan samun result me kyau Ina matukar godia da adduo’in ku a gare ni Allah ya saka muku da alkhairi ngd, ngd kwarai dagaske_

_Wannan page din naki ne ke kadai Khadeeja Adam (Mrs Haydar) I love u so much Babe_馃槝

       1鈨�0鈨�3鈨�

Kamar yanda manya su ka yanke hukunci haka aka yi Imran yazo ya dauki Janan suka tafi asibiti suna tafe suna hira amma dukkan su cikin zullumi suke dan basu san me ze je ya dawo ba. A wajen ajiye motoci yayi parking sannan suka fito suna jerawa abun gwanin ban sha’awa.
Office din Family Dr din su suka nufa Imran yayi knocking aka basu izinin shigowa. Cikin girmamawa suka gaida shi shima a mutunce ya amsa musu..

Wayan dake kan table din shi ya daga ya kira Nurse nan da nan se gata dama an san da zuwan su Janan din cikin dan lokaci kadan aka gama diban jinin nasu. Bayan fitan Nurse din ne Dr yace “zaku iya tafiya in result din ya fito zan kira Daddy in fada mishi”
Jiki a salube suka ce toh tare da yin godia suka fita..

Har kofar gida ya ajiye ta sannan ya juya ya tafi. Ji take kamar kafafunta ba zasu iya motsawa ba sbd yanda take jin nauyin su da kyar dai ta lallaba ta shiga gida..

Da Sallama ta shiga parlor nan ta tarar da Ummiey a zaune tana kallon Sunna TV seda ta zauna sannan Ummiey tace “ya akayi? Anyi gwajin? Me Likitan yace?
Nunfashi Janan taja sannan tace “an deba jinin mu amma Likita yace ze kira Daddy ya fada mishi yanda ake ciki”

“Toh Allah yasa muji alkhairi” inji Ummiey.

Janan ta ansan da Ameen tace Ummiey bari in shiga ciki…

Da yamma Abbiey ya dawo bayan sun mishi sannun da zuwa Janan tace Abbiey naga yau duk ka gaji bari in kawo maka abu me sanyi kadan sha sbd naga yau Garin anyi rana”

Yace ”yawwa Yar Albarka”

Zobo ta kawo mishi me sanyi ta ajiye akan center table sannan ta zuba mishi a cup ta mika mishi, tas ya shanye tare da fadin Alhamdulillah sannan ya kara da fadin dazu Mahaifin Imran ya kira ni yace zuwa bayan Isha’i zasu zo harda Likitan sbd ayi komai cikin yarda da aminci, toh da dai nace musu ai duk daya muke babu wani matsala se naga sun fi son ayi komai dalla dalla sbd aba kowa hakkin shi se nima na amince da shawarar su yanzu dai ku shirya zuwan su”

Ummiey tace Toh ba matsala Allah ya kawo su lfya”

Ummiey , Abbiey, Daddy, Imran, Janan da Likita duk zaune suke a cikin Parlorn baki suna jiran bayanin Likitan duk sun kagara sbd ko Daddy be san komai akan result din ba ..

Murya Likita ya gyara sannan ya fara bayanin shi “kamar yanda kuka sani wannan gwaji anyi shi sbd sanin kwayoyin hallitan Janan da Imran kuma anyi haka ne sbd gudun fadawa hatsari tare da gujewa cutar sickle cell, sakamako ya nuna za su iya aure kuma su samu iri amma fa kaso mafi yawa daga cikin yaran zasu kasance masu dauke da sickle cell domin kwayoyin hallitar su dayane maana genotype din duk su biyun AS ne wanda a kimiyance akwai Babban hatsari idan AS da AS suka auri juna,
Amma wasu sukan dauki risk din yin haka wanda kuma daga karshe suke regretting abun da suka aikata.. Yanzu dai ku a matsayin iyayen su ku zaku yanke hukunci..
Ya koma ya zauna.
Shiru parlon ya dauka kamar babu masu rai a ciki domin gaba dayan su hankalin su ya kai kololuwan tashi… Zufa ne ya fara ketowa Imran frm no where ita ko Janan wani irin kyarma jikin ta yake yi kamar me fama da fever….

Har yanzu dai babu wanda yayi magana can dai Abbiey yayi karfin hali cikin dashashshiyar murya ya ce “Likita munji bayanin ka kuma mu bamu isa muja da hukuncin Ubangiji ba muna adduaar Allah yasa haka ne mafi alkhairi kuma mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau sbd dukkan mu nan Musulmai ne suma Yaran Allah ya basu hakuri da Juriyan rashin da suka yi”

Daddy yace  “nayi bakin ciki kuma nasan munyi babban rashi domin samun irin Janan se an tona kuma samun iyaye irin ku masu mutunci da dattako se a tona amma haka Allah ya tsaro mana kuma ya fimu sanin dalilin haka”

Abbiey yace babu komai hakan kuma ba yana nufin ba zamu dinga zumunci ba da yardar Allah yanzu ma muka fara fatan mu dai Allah ya musanya musu da mafificin alkhairi..

Janan da Imran kuwa ji suke kamar rayuwar su ta kare, dan a wajen suka zauna suna kuka kamar ransu ze fita dukkan su sun kasa controlling hawayen su babu wanda be tausaya musu ba, Ummiey ta janyo Janan jikin ta tana shafa mata baya alaman rarrashi da kyar Daddy ya lallaba Imran ya tashi amma ya kasa tsayawa balle ya yi tafiya haka Daddy da Dr suka sa shi a tsakayi suka bashi support dan da alama ba zai iya tafiya shi daya ba…
A haka suka bar gidan ranan dai sunga tashin hankali dan Janan seda Ummiey da Abbiey suka dinga bata baki suna mata nasiha ita dai binsu kawai take yi da ido,
har daki Ummiey ta rakata tayi mata adduaa sannan ta rufa mata bargo ta fita..

Gefen Imran kuwa sambatu ya dingayi tun suna ganin ze dena har suka fara tsorata, Mummy ce ta debo ruwa a cup tayi mishi adduaa ta bashi yasha sannan ya dan yi shiru cikin yan mintuna kadan bacci ya dauke shi..

Can cikin dare kamar hadin baki suka farka lokaci daya se a lokacin abun ya kara dawo musu sabo daidai lokacin da Janan ta dauka wayarta kiran Imran ya shigo da kyar ta iya hada wayan da kunne ta dan kwatakwata bata jin karfi a jikin ta.. murya can ciki tayi mishi sallama shima cikin mutawar jiki ya amsa seda suka dau kusan minti 2 suna sauke nunfashi kowa yana tausayin dan uwan shi can dai Imran yayi karfin hali yace “Angel shikenan yanzu Ina ji ina gani zan rabu dake? Duk tsawon lokacin da muka dauka muna gina soyayyar mu me tsafta yanzu duk ya tashi for nothing? Ban san wani hali zan shiga ba na rashin ki bazan taba jin dadin rayuwa ba tare da ke ba pls kice min mafarki ne ya fashe da wani irin kuka itama dai Janan din kuka take yi sbd bata taba zaton wani abu ze rabata da Nurul Qalb din ta ba amma yau gashi sun rabu rana tsaka…. Ita kuka shi kuka babu me lallashin wani a haka har bacci ya sake awon gaba dasu ba tare da sanin su ba…..

Tsayawa fadin irin tashin hankalin da Masoyan suke ciki abu ne me matukar wahala… Daka gansu kallo daya zaka musu kasan zuciyoyin su na azabtuwa da rashin juna kwata kwata Imran ya dena fita ya dena zuwa aiki kullum yana daki daga massalaci se daki abinci kuwa ba a magana Dan ko kallo be ishe shi ba tun su Daddy da Mummy suna fada har suka koma lallashi da ban baki tare da adduaa…

Ita ko Janan ta zama kamar mutum mutumi daga ido se ido be fi tayi magana sau 4 zuwa 5 ba a rana… Saleem da Khaleel kullum suna janta a jiki sbd su rage mata damuwa amma abun yaci tura..

_Hmmm! Ciwon so ba shida magani_

RukkyBae 馃槒馃槒馃槒
[11/10/2017, 10:33 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/10, 8:21 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b櫏鉂も櫏鈾b櫏鉂も櫍鈾モ潳鈾b櫏鉂も櫍鈾モ潳鈾b櫏鉂も櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ潳鈾b潳鈾b潳鉂も櫍鉂も櫍鈾モ潳

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*馃寪
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Mutuwa, Aure, Arziki, Haihuwa, Daukaka.. Duk na Allah ne kuma lokaci ne.. Ya Rabbi ka cire mana son Duniya da abunda ke cikin ta_

        1鈨�0鈨�4鈨�

Yau tun 12 na rana su Eesher ke gidan su Janan suna ta jan ta da hira suna da ban baki. Sosai taji dadin zuwan su ko ba komai sun rage mata wani radadi da take ji a zuciyar ta dan in tana tare dasu dole su sata farin ciki..  Zee ta kwashe da daria harda hawaye Eesheer da Janan suka kalli juna hade da daga gira suna juya yatsansu a setin kansu alamar ‘notin kan Zee ya kwance’ can ta dakata tana ce musu ku dena mun kallon nan kamar kun ga wata mahau ..”
Suka hada baki da fadin “kaciya cuz we see za example” (kalan turancin da suke yi in suna tare wanda su kadai suke ganewa)
Tare suka yi daria wannan karan sannan Zee tace “kun tuno lokacin da muka sama Mr. Jolly mayen mata bawon ayaba ya zame? Daria suke kaman sun sha laughing gas da sun tsagaita se su cigaba.. Janan tace secondary school memories Allah dai ya yafe mana amma mun tsula tsiya.. Nan fa suka dinga tuna rashin jin da suka yi.. Se yamma likis suka tafi gida..

         ****

Ummiey da Abbiey na zaune Janan ta fito daga daki duk ta rame a yan kwanakin nan sbd tun randa suka yi waya da Imran ta cire SIM card din ta dan ba zata iya cigaba da jin muryar shi ba tunda kaddara ta riga fata sbd jin muryar shi na kara dagula mata lissafi tare da fama mata ciwukan da warkewar su ba nan kusa ba..

Zama tayi tana fadin “Ummiey, Abbiey barkan ku da hutawa”
Tare suka amsa mata cike da kulawa.. Ganin tayi shiru tana wasa da yatsun ta suka gane akwai maganar da take son fada., Abbiey ne yayi saurin cewa  “Muhibbatie bakin ki kamar akwai magana, ki fadi abun da ke ranki idan muna da iko zamu miki maganin shi da yardar Allah”
Har yanzu dai wasan take yi da yatsun ta sannan tace “dama Ina so ne in ajiye aikina” ta karasa maganar muryan ta na rawa..

Haba Hulwaty kina so ki dinga zama kina tunani ne? Ni a nawa ganin kamar zaki fi sakewa in kina wajen aiki tunda ga su Aisha suma sa debe miki kewa ga kuma aiki zaki dinga yi ba kida lokacin tunanin wani abu” Ummiey tayi    maganar..

Abbiey yace haka ne amma bari mu gani zuwa nan da 2 weeks din da aka bata a wajen aiki ya cika tukunna kin san na fada miki suna so suyi min canjen wajen aiki daga nan zuwa Abuja”

Ummiey ta jin jina kai tana fadin “Toh Allah ya zaba mafi alkhairi mu fara shiri kenan..

An tabbatar ma dasu Abbiey maganar komawan su can din bayan ya dawo gida ya fadi ma su Ummiey Janan kuma ya tayata ta rubuta takardar barin aikin amma can kasan zuciyar ta tana jin ba dadi dan ko ba komai za tayi kewar fadan su ita da Dr. Godwin the mighty kamar yanda take ce mishi…

Su Zee sun sha kuka sbd za suyi kewar ta shi kuma Dr. Magaji yayi mata fatan alkhairi amma shima ya san za suyi rashin Nurse me tausayi da sanin makamar aiki..

Cikin kankanin lokaci aka gama komai aka kai takardan ta Ministry of Health suka buga stamp me tabbatar da ajiye aikin nata..

   ********

Wuse zone II nan sabon gidan su Janan yake gidan me kyau ba wani babba bane amma komai daidai su har BQ inda Ya Khaleel da Ya Saleem zasu zauna tunda sunki aure… Allah yasa sun yo takeaway suna zuwa suka baje suka ci abinci dama tun a hanya sukayi sallah hutawa kadan suka yi sannan suka dan yi gyare gyaren su…

          鈾�

Yau ta kama Lahadi su Dr. Godwin suka dawo daga Garin Makarfi in da aka tura su dalilin bude wata Babbar asibiti cike da Nasara da jin dadi suka dawo Garin Kaduna babu ma kamar Dr. Godwin wanda yake jin shi kamar wani sabon halitta yanzu ya fara sanin dadin rayuwa da kuma abubuwa da dama daya rasa a shekarun baya masu yawa.. Allah Allah yake Gobe tayi ya koma office ya ga Janan din shi wacce yake matukar missing ga kuma labaran da yake son bata, kwanakin baya ya sha trying numb din ta amma baya shiga ya dan damu amma kuma se ya basar yace ko ma dai mene ne ai ze dawo… A gajiye ya koma gida seda yayi wanka yaci abinci sannan ya kwanta bacci duk ya kosa gobe tayi.. Ya farka yafi sau 3 duk a tunanin shi safiya tayi amma gani yayi Daren ya mishi tsawo….

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[11/18/2017, 5:14 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/14, 7:15 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫏鈾モ櫊鈾モ櫏鈾b櫏鈾犫櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾犫潳鈾b櫏鈾犫潳鈾� *MATAR DOCTOR* 鉂も櫏鈾b櫊鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫏

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 _*HAJOW*_馃寪
*_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_*鉁嶐煆烩湇馃徎

_Wannan shafin na sadaukar da shi ga duk wata UWA da ta rasa Ya’ ko Da’ ubangiji Allah ya baku juriya da hakuri, Allah yasa ma su ceton ku ne鈾モ潳_….

_FROM ALLAH WE ARE AND TO HIM WE SHALL ALL RETURN_馃槶馃槶

     1鈨�0鈨�5鈨�

             鈾�

Kiran sallan farko Dr. Godwin ya tashi yayi wanka yasa wani yadi sky blue mai laushi wandon pencil ne ita kuma rigar bata karasa gwiwar sa ba da sauri da sauri yake saka links din rigan agogon shi baki dake kan mirror ya dauka ya fito parlor yana zuwa yaga har Agnes ta gama jera breakfast akan dining table.
Ba ya jin ze iya tsayawa ya karya sbd tsabar zumudi.. Tea ya hada da sauri ya sha sbd be son ya bar cikin shi empty dan ma ya san anfanin breakfast a jikin Dan Adam if nt ba zai ci komai ba..

Bakwai saura kwata ya karaso asibitin, da izzan shi yake tafiya da ganin shi zaka san yana ji da samartaka yana tafiya ma su aikin wajen na gaida shi ga mamakin su yau da fara’a ya dinga amsa su a haka har ya shiga office din shi, tas ya ganshi komai a gyare se kamshin air freshener ke tashi a hankali ya lumshe idon shi yana shakan kamshin kafin ya bude ido, kujeran shi ya zauna ga takardu himm a kan table din yace ”huh akwai aiki” daya bayan daya yake duba takardun can wani takadda ya fado cikin envelop cike da gajiya ya duk’a ya dakko har ya ajiye a gefe. se can zuciyar shi tace ya bude, hannu  yasa ya jawo ya bude, abun da ya gani ya bashi mamaki kwata kwata ya kasa yarda da abun da yake karantawa,
jingina yayi da kujeran a hankali yake ma kanshi magana “calm down, take a breath, ba gaskiya ba ne”

Ido ya budewa ya kara karantawa kusan sau 5 sannan ya fara fadin “why Janan? Why? Me yasa za kiyi min haka? Me yasa zaki ajiye aiki ba tare da dalili ba ba tare da kin tambayi shawara ta ba, ba tare da sani na ba? Ya kike so in yi? Me yasa? Me yasa zaki tafi ki barni bayan yanzu nake bukatar ki d most? Oh My God!
Wani daci yaji bakin shi nayi mishi, kamar an tsikare shi ya tashi da takardar ya bar office din..

Office din Dr. Magaji ya nufa sbd ya mishi karin bayani dan shi ya bar ma amanan Janan kuma yaga sa hannun shi a cikin takardar wato harda amincewar shi akan barin aikin ta…

Ko knocking be yi ba ya tura kofan, a rufe ya ji ta se yanzu ya tuno irin sammakon da yayi, da karfi ya buga kofan yana fadin “shit!

Kai komo ya dinga yi lokaci zuwa lokaci yana duba agogon hannun shi gani yake kamar time baya gudu..

Se karfe takwas saura sannan Dr. Magaji ya shigo asibitin sbd hold up da ya rutsa dashi a hanya.. Cike da sakin fuska suka gaisa da ma’aikatan wajen sannan ya bude kofar office din..
Dr. Godwin dake jingine da bango ya dafe kan shi be lura da zuwa shi ba,
Karan rufe kofa kawai yaji da sauri shima ya tura kofan ba tare da yayi knocking ba.. Yana shiga Dr. Magaji ya juyo da sauri dan ko kaiwa da zama be yi ba yaji an hankado kofar ba tare da anyi knocking ba,
Cike da mamaki yace  “a a Surgeon G yaushe a gari?
Ba tare da fara’a ba ya dan yamutsa fuska yace a takaice “jiya”

“have  a seat” yace mishi lokacin yana kokarin zama a nashi kujerar..

“No, thanks ba zan zauna ba ina so na koma office akwai aiki sosai dama ina so muyi wata magana ce”

“Uhum am all ears”

Takardan ya mika mishi ba tare da yace komai ba..

Hannu Dr. Magaji yasa ya amsa ya bude se a lokacin ya tuna ba su yi maganar da shi ba yace  “Ya Salaam! Ka ga na manta koh! thou dai na tura maka through email din ka naga kuma baka yi replying dina back ba”

Ba karamin kimar Dr. Magaji yake gani ba shiyasa yake kokarin controlling temper din shi,
a hankali yace “ni ban gane komai ba kaina ya kulle I need more explanation yanda zan fahimta”

Nan ya bashi lbrn yanda tazo ta fadi mishi zata bar aiki duk da yayi kokarin ya fahimtar da ita kan aure baya hana but tayi insisting akan tana son ta bar aikin maybe mijin ta ne baya so shiyasa kawai na sa hannu Ministry of Health suma suka amince suka buga stamp!

Gaban table din ya karasa tare da dafawa yace  “excuse me! Kamar aure naji kace!

Dr. Magaji yace “yea aure za tayi gama IV din bikin” ya jawo drawer din shi ya ciro katin yana mika ma Dr. Godwin

Jikin shi na kyarma ya karba da baya da baya ya fara tafiya seda ya kai kan wani kujera dake can nesa yayi zaman yan bori yana jin iskar wajen na ko karin dena kaiwa inda ya kamata duk da AC dake kunne…
Zazzare ido yake yi yana kokarin karantawa dan gani yake size din idon shi sunyi kanana wajen karatun yafi minti 2 kafin kwakwalwar shi ta fara aiki sannan ya fara gane abun da yake karantawa, yi yake yana karawa ya gane komai amma ya kasa hana kan shi karantawa, wani irin zufa me zafi ya fara karyo mishi, hannu yasa yana balle botiran rigan shi ko zai ji iska amma ina! Kamar ma yana karama kan shi zafi ne…

Dr. Magaji dake gefe ya zuba mishi ido cike da mamaki, duk da shi ba malamin soyayya bane yana ganin kamar Dr. Godwin yana son Janan din…

Ji yayi Dr. Godwin ya ruko hannun shi duka biyu yana fadin   “Ba da gaske bane ko? Kace min wasa ne, ka ce min idona ba su gani da kyau, kace min ba au… Ya kasa karasa maganar dan ba zai iya fadin wai Janan din shi zata auri wani ba, idon shi yayi jajawur zuciyar shi na zafi so yake yayi kuka ko zai samu relief amma ya kasa…!

A hankali Dr. Magaji ya fara bubbuga bayan shi har zuwa lokacin be yi magana ba sbd be san abun da ze ce mishi ba kuma ba zai iya yi mishi karya ba… Ganin da yayi ba shida niyyar magana yasa shi wani irin murmushi wanda gara kuka a kan shi sannan yasa kai ya fice daga office din ba tare daya kara magana ba…

Dr. Magaji na kiran shi amma be juyo ba ya fice da saurin gaske,
tafiya yake yi amma be san inda yake sa kafar shi ba da uku_uku, bibbiyu yake tsallake steps din a haka ya kai wajen da ya ajiye motar shi ya zura hannu a aljihu be ji key din shi ba, se lokacin ya tuno ya baro shi a kan table din office din shi dazu daya shiga da dan karfi ya naushi hannun shi yana fadin “damn it”

Hanyan gate ya nufa dan ba zai iya komawa ya dakko mukullin ba yana fitowa ya tsaida me adaidaita……..

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[11/19/2017, 11:00 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/18, 5:27 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾b櫐鈾b櫏鈾︹櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫍鈾モ櫍鈾b櫏鈾モ櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪HAJOW馃寪
*HAKURI DA JURIYA ONLINE*鉁嶐煆烩湇馃徎

          1鈨�0鈨�6鈨�

Yana tsaida me adaidaitan ya shiga ba tare da tanbayan kudi ba balle ya fada mishi inda za su..

Mai adaidata yace  “ina muka dosa ne?

Mitchwwwww yaja tsaki yace muje mana dole se na fadi in da zaka kai ni? In ba zaka je ba In sauka na hau wani”

Ah me ze hana in kaika? Kawai da kar muje ne ka kasa biya na kudin dana fada maka”

A dan hasale yace “kai kudi ya dama dilla ka wuce muje bana son raini, kai da gani na na maka kalan wanda ze kasa biyan kudi?

Me adaidaita yace  “oho! Wannan kai ka jiwo”  Ya ja suka fara tafiya.. Can ya danna radio aiko dai dai an sa wakan *JIRGIN SO* yana yi yana bin wakan harda kara volume..

Haushi kaman ya kashe Dr. Godwin dan shi wakan ma ji yake tana kara dagula mishi lissafi..
Masifa ya fara ma dan adaidaita “ka cire wakan ko ka rage kuma ka kara sauri kana tuki kamar dan koyo”

Kai ni fa wallahi zan sauke ka ka cika korafi ni da abu na zaka zo kana bani ka’ida kamar wani ubana? Toh baka isa ka fada min yanda zan yi ba ka san shekarata nawa ina wannan sana’ar zaka zo kana wani surutu? Yasin da yanzu zan baka ba zaka iya tukawa ba se dai ku kife kai da adaidaitan”

Banza Dr. Godwin yayi da shi dan abun da ke damun shi yafi wannan shirmen! Da hannu ya dinga nuna mishi har suka kai, a dai dai kofar gidan suka tsaya ya sakko yace “ka jira ni yanzu zan dawo”

Alqur’an ka bani kudi na dan ba zan yarda ka tafi ka ki dawowa ba” Ya kashe adaidaitan tare da zare key din ya fito…

Abun ma yaso ya ba Dr. Godwin din daria amma se ya basar yayi wucewar shi,

Mai adaidaita ya kalle shi yaga kayan dake jikin shi se ya shafa gemu yace “da alama yana dan da kudi amma dai mutum ba abun yarda bane bari dai in ga iya gudun ruwan shi…….

Shiko Dr. Godwin a hankali yake tafiya yana dosar kofan gidan amma ji yake kamar yana tafiya akan kaya, a haka har ya karasa yana zuwa yaga kofar a kulle da katon padlock, buga kofan ya fara yi da duk iya karfin shi yi yake yana karawa.. Da sauri mai adaidaitan ya karaso tare da fadin “Ba ka ganin kofan a rufe take da kwado? Da alama babu kowa ka gane mana”

Wani yaro ne ya fito daga gidan dake kusa da na su Janan din, har ya wuce se kuma ya dawo, gaishe su yayi sannan yace lafiya dai ko?

Eh lafiya ba lau ba, na kawo wannan mutumin ne se naga yana ta buga kofan gidan nan kuma da alama babu kowa dan na ganshi a rufe da kwado..

Ayya! Ai basa nan sun tashi daga gidan”

Dr. Godwin yace “sun tashi? Yaushe? Ina suka koma? Zaka iya raka ni inda suka koma?

Gaskiya ban san inda suka koma ba dan lokacin da suka zo yima yan gidan mu sallama bana nan ina makaranta,

Toh yanzu kai baka san komai ba akan labarin su? Ya kara tanbayan yaron

Gaskiya ba ni da labari amma na san ba zaka rasa lambar su ba ka kira se suyi maka kwatancen in da suka koma ina ga haka ze fi..

Se a lokacin ya dan ji sanyi daya tuno yana da lambar ta koma mene ne zai zo da sauki, yasa hannu a aljihu ya ciro kudi hannun shi a dunqule ya mika ma yaron, kin karba yayi yace “ni Dan Allah nayi maka ba dan komai ba”

Eh na sani kuma sbd Allah ka karba ba dan ni ba, da kyar yasa hannu ya karba tare da godia ya wuce..

Komawa su kayi me adaidaita ya shiga suka fara tafiya, tun da suka shiga Dr. Godwin ya jingina kan shi a jikin kujera ya lumshe ido,wayar shi ya ciro ya fara dialing numb din Janan amma taki zuwa ya kira yafi so a kirga amma taki shiga, ji yayi kamar ya cillar da wayan se kuma ya ajiye ta a gefe zuciyar shi na tafasa sosai komai ya birkice mishi ya rasa me ke mishi dadi a duniya…

“Kayi hakuri ka bar ma Allah komai naga ka damu da yawa amma ina so ka sani duk abunda ke damun ka ka yi Addu’a Allah ze amsa maka kuma ze tausaya makamaka, sannan shi da ya saka ka a wannan halin shi ze cire ka!

Kai kawai yake gyadawa yana mamakin mai adaidaitan dan be yi zaton yana da tunani ba kuma yaji dadi a ranshi dan ko ba komai ya dan ji radadin dake zuciyar shi ta fara dan ragewa, be ce mishi komai ba se dai yana bin shi da kallo

Dai dai kofar asibitin ya tsaya Dr. Godwin ya fito tare da ciro dubu 5 ya mika mishi, ido ya zaro waje yace “ai kudin ka basu kai haka ba dari biyar ce itama dan sbd drop ka dauka amma da na dau pasinja ba zai kai haka ba!

Eh na sani kuma ni na baka sbd naji dadin shawaran daka bani sannan ni Dan Allah na baka, ko ba komai yanda naji dadi kaima zaka ji dadi!

Cikin sanyin jiki yasa hannu ya karba tare da mishi godia, hadi da fadin kayi hakuri da duk abun da nayi maka, nayi maka haka ne sbd yanda tsoron Allah yayi karanci a zuciyar mutane wasu ma sun fi so suci hakkin mutun ya bar su da Allah..

No ba komai karka damu ai hakkin ka ne dole ne kabi duk wata hanya da zaka kare abun ka, se anjima… Ya zuya ya shiga asibitin, me adaidaita ya tafi yana me farin ciki tare da jinjina ma wannan mutumi…

Yana shiga office ya rufe ta ciki dan kwata kwata yau baya jin ze iya duba kowa hannu yasa a aljihu dan ya ciro waya ya kara trying ko zai samu wayar ta shiga se yaji wayam!

Oh My God! Na manta da shi a Napep! Yasa hannu ya bugi goshin shi, I loose It! Shikenan I loose her number and pics! Shi ba ma wayar ta dame shi ba lambar ta ce ya dame shi dan yana ji ze iya siyan irin wayar guda goma ba tare da yaji komai ba amma shi ba wannan bane matsalar shi ba..

Mintuna 30 bayan haka kawai me adaidaita yaji waya na kara a bayan sit,
Laaa! Mutumin nan ya manta wayar shi!
Juyawa yayi ya koma hanyar Asibitin! Yana zuwa ya shiga nan ya samu me gadi yayi mishi kwatancen Dr. Godwin

Kwatancen office din shi yayi ma mai adaidaitan, yana zuwa ya sake tambaya aka kara nuna mishi, har kofan ya karasa yayi knocking, tsaki Dr. Godwin yaja, baya jin ze iya bari azo a dame shi.. Kara knocking aka yi

cike da jin haushi ya mike ya bude kofan, yana fadin “What the… Sauran kalman ya makale a wuyan shi ganin me adaidaitan a tsaye yana washe mishi hakora!

Ya dai? Ya tambaye shi

Wayar ka ce na ji tana kara shine nace bari na kowa maka kada hankalin ka ya tashi dan na san kana ta nema!

Murmushi yayi ya mika hannu ya karba yana fadin Na.. Go.. De! Abun da be saba ba kenan amma yau ya fada sbd hallacin da yayi mishi… gaskiya da za a dinga samun matasa irin ka da an huta da sace sace ka burge ni kwarai! Ina zuwa” Ya shiga ciki, drawer ya bude ya rubuta mishi cheque na dubu 100, yana fitowa ya mika mishi  yace  “kada kayi min godia kaje kai ma in ka samu hali ka taimaki wani”  yana gama fadin haka ya rufe office din shi… Me adaidaita ya wuce jiki a sanyaye harda dan hawayen shi na farin ciki ……

Bayan Sati daya!

Dr. Magaji tsaye a kan shi yana magiya  “Haba Surgeon G! Ya  zaka mana haka? Kazo muje dakin theater ka gama ba wani dadewa za kayi ba appendix ne plsss!! Ya hade hannayen shi biyu waje daya!

Nifa bana cikin walwalan da zan iya yin komai ba kawai ku bari nxt time”

Eh duk da haka muje abun yayi chronic dan any moment frm now ze iya fashewa..

Ohhhh no! Kana so a kara samun matsala kenan? Sau 3 ina yin operation amma daga in manta almakashi se in mata sirinji, kaima a gaban ka aka dawo dasu kuka cire ni kam bazan iya ba!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[11/19/2017, 11:17 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/18, 9:25 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鈾b櫏鈾犫潳鈾モ櫍鈾犫潳鈾モ櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾犫潳鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾b櫊鈾犫潳鈾犫櫏鈾b潳鈾犫櫍鈾モ櫊鉂も櫏鈾b潳鈾犫櫏鈾b潳鈾犫櫏鈾b櫊

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

*HAJOW*馃寪
_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_鉁嶐煆烩湇馃徎

        1鈨�0鈨�7鈨�

Zaka iya! Na sani zaka yi, ni nafi yarda da aikin ka, hankali na yafi kwanciya da aikin ka, ban taba rokon ka wani abu ba amma yau na roke! Yau kadai…

Huh! Sabo da kai kadai zan yi!

Yesss! Thank u!

Tare suka tafi dakin theater, cikin kwarewa yake aikin har ya gama, kafin ya dinke se da yasa Dr. Magaji ya duba mishi kada yayi mantuwa

Murmushi yayi yace “job well-done Surgeon G”

Yau kusan kwana 4 kenan kullum ya kwanta se yayi mafarkin Janan tana kuka, ya rasa wannan wani irin mafarki ne! Haka ya kasa komawa bacci ya zauna! Hotunan ta dake wayan shi ya fara kallo yana shafa fuskan ta a haka har bacci ya kwashe shi!

Tun bayan da yayi last theater din nan be kara zuwa asibitin ba dan shi yanzu baya iya komai, komai yake yi se yaga fuskan Janan, be taba zaton son ta ya kai har haka ba,  dai dai setin zuciyar shi ya dafa yana fadin “ke kadai nake so, ke kadai zuciya ta ta aminta da ita, ba zan kara son ko wace ‘ya mace ba a duniyanan, ko wani bugu na zuciya ta da ke take yi, na so ki jiya, ina son ki yau kuma zan so ki har abada! Hawaye yaji suna kwaranya daga idon shi, a hankali ya shafo hawayen yana fadin “nayi kuka a kan son ki,
Na so ace na baki labari na wanda ze faranta miki rai! A ina zan ganki? Yaushe zan sake ganin ki? Ya rushe da wani irin kuka me ban tausayi! Na yarda soyayya halittace sannan bata da magani!

Wayan shi dake gefe ta fara ringing Dr. Magaji ne ke kiran shi tun jiya amma ya kasa dauka dan be san me zai ce ba har kiran ya katse, wani kiran ya kara shigowa seda ya seta muryan shi sannan ya dauka!

“Surgeon G lafiya dai ko? Yau kwanan ka nawa rabon ka da zuwa asibiti? Ga patients se zuwa suke yi ta ko ina”

“Bana jin dadi ne, but gobe zan yi kokari in zo”

Ya Allah! Meke damun ka? Bari inna tashi daga office zan biyo in duba ka”

No karka damu na warke ai, gobe dai kuyi expecting zuwa na!

Suka ajiye waya!

  
    Washe gari

Yau patients 5 yayi ma operation duk ya gaji!

Ba tare da shawaran kowa ba ya rubutu takardan barin aiki! Da kanshi ya kai Ministry,, suka ce nan da kwana biyu ze ji daga gare su…

Cikin shirin shi ya tafi Ministry dan yau kwana biyu ya cika kuma sun kira shi!
Wani conference hall aka gyayyace shi da ya shiga! Yana shiga yaga mutane da yawa a zazzaune be damu ba kuma be tsorata ba dan tsoro ba ya da muhalli a zuciyar shi! Wata kujera aka nuna mishi ya zauna!
Wani mutumi ya mike yana fadin “Sunana Kabeer Sulaiman ina daya daga cikin members na wannan Ministry din, mun ga takardan daka kawo,  kuma munyi bincike a kanka sosai mun gano kana da matukar anfani a wannan asibitin domin kana daya daga cikin wanda muke alfahiri da shi kuma Garin nan ke alfahiri da shi, but unfortunately ka turo mana da abunda ban zaton za mu iya barin ka subuce mana, se dai ba muda ikon hanaka abunda kake so amma muna so muji dalilan ka”

sannan ya zauna..

Dr. Godwin yana zaune yayi gyaran murya kafin ya fara magana  “Sunana Godwin Williams Albert, General Surgery DOCTOR a Barau Dikko Special Hospital, dalilai na ba masu karfi bane amma na zabi ajiye aiki na sbd bani da natsuwar aiwatar da aikin, sannan kusan ko da yaushe ina shiga theater cikin tunani wanda ya ke haddasa min mantuwa da abubuwa masu kaifi a cikin patients, bana so wani ko wata su rasa ransu ta dalili na shiyasa kawai na zabi barin aikin!

Me yasa ba zaka dauki hutu ba ka zabi ka bar aikin? Wani daga cikin su ya tambaye shi..

Saboda matsalar babbace kuma bana tunanin zan fita daga ita nan kusa!

Shin ko za mu iya sanin mece ce matsalar?

Gaskiya aa sbd wannan personal problem dina ne!

Munji bayanin ka kuma zamu sa maka hannu dan ka bar aiki amma se ka yi mana wani aiki wanda daga shi in dai baka kuskure ba zamu barka ka tafi kuma ba zamu taba mantawa da kai ba amma in ka kuskure ba zaka ajiye aiki ba kuma zamu kai maganar zuwa kotu dan lokacin da zamu dauke ka aiki se da ka yi rantsuwa za kayi aiki a ko wani yanayi kuma a ko wani hali!

Ku fadi abunda kuke so ina jin ku!

Projector a kunna a jikin bango, nan kowa ya kai duban shi jikin bangon,  wata matashiyar yarinya ce kwance fuskarta kacakaca abun ba kyan gani, nan waje ya kaceme da hayaniya kowa da abunda yake fada!

Nan Kabeer ya jiyo da duban shi wajen Dr. Godwin yace “Hanan sunan ta yarinyar Mataimakin Gwamnan garin nan, sun sami plane crash ne wanda haka yayi sanadiyar kwashewar fatan fuskar ta, yanzu haka tana Egypt nan da 3days zasu dawo sbd sun ki karban ta a duk kasar da suka je, mu kuma mun san muna da kai kuma u can do It shine mu kayi convincing Baban ta a kawo ta nan garin kai zaka yi aikin!

Sosai hankalin Dr. Godwin ya tashi dan shi be taba irin wannan aikin ba duk da ya san ze iya amma abun yayi worse, ga kuma halin da yake ciki!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[11/24/2017, 4:07 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

*_HAJOW_*馃寪馃寪
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

        1鈨�0鈨�8鈨�

Kabeer yace “kai muke jira muji ta bakin ka Dr. Godwin!
Se a lokacin hankalin shi ya dawo jikin shi! Ajiyar zuciya yayi sannan yace “na ji bayanin ku kuma na gani dan haka plastic surgery za ayi mata amma ta ya ze yiwu ba muda kayan aiki ingantattu? In fact  ba muda kayan da za muyi anfani da su wajen yin aikin!

“wannan ba matsala bace kar ka damu za a samo su in dai zaka iya!

Nan dai taro ya watse da alkawarin za a bashi kwangilar siyo kayan online tunda babu lokacin da zai iya zuwa siyowa da kan shi..

Yau kwanakin ukun suka cika komai a ake bukata sun iso tun jiya nan da awa daya za su karaso a fara aikin… Dr. Godwin yau yayi kokarin seta kanshi ko dan ya ba su mamaki..

Saukowan su kenan daga jirgi ko gida ba su wuce ba suka kamo hanyar asibitin.. Tun kafin su karaso har an sakko da wani sabon gadon mara lfya wanda duk yana cikin kayan…

Sabuwar motar ambulance  ce ta shigo cikin asibitin, tana tsayawa Dr. Godwin ya taka a hankali har ya karasa bakin motar
Hannu yasa ya bude kofar, a lullube take tun daga kanta har kafa, a hankali ya dan bude fuskarta wani irin zabura yayi yana fadin “Ohhhh My God! Tare da zare ido, ganin yanda fuskarta take har tafi munin gani akan na hoton da aka nuna mishi, cikin sanyin jiki yayi ma Nurses alama su matso da gadon, cikin hanzari suka karaso, Maman ta da Baban ta suka fito daga wata jeep suka tsaya dai dai bakin kofar motan da take, hawaye ne ke fita daga idon Maman tace “kuyi a hankali jikin ta babu kaya kuma akwai raunuka idan kuka yi mata da karfi fatan da ze iya sabulewa!

Ajiyar zuciya Dr. Godwin ya sauke,

kamar kwai haka suka dakko ta suka daura akan gadon sannan suka tura ta, Dr. Godwin da iyayen ta suna bin su a baya har suka kai kofar wani daki inda aka tanada sbd yi mata operation din!

Daki na musamman aka kai Iyayen nata don jira!

Dr. Godwin ya kira Dr. Magaji sbd yafi so yayi aikin da wani a kusa da shi duk da ba fannin Dr. Magaji din bane, Nurses 4 ne suke ciki dan taya su… Seda ya tuno Janan din shi a ran shi yace “da yanzu kina gefe na kina tayani, koda baki taya ni ba inna kalle ki zan samu courage duk da na san da kina nan kuka zaki dinga yi dan na san water melon eyes gare ki! Ya yi murmushi…

Motsi ya dinga yi da bakin shi kaman yana addua’a sannan ya matsa kusa da ita

Cikin dauri ya fara aikin duk da zuciyar shi tana dokawa shi kan shi Dr. Magaji jikin shi rawa yake yi…

Awananni goma sha biyar suka dauka suna abu daya cikin ikon Allah suka gama duk jikin ta nade da bandeji tana kwance kamar ba ta da rai…

Suna fitowa suka tarar da Iyayen ta da sauri suka karaso suna fadin “Dr. Ya akayi? Ya jikin nata? An dace?

Ku biyo ni office” abunda yace dasu kenan..

Jiki na rawa suka bi bayan shi, waje ya nuna musu suka zauna sannan ya fara musu bayani “mun gama mata aikin kuma muna fatan samun out come me kyau,

Dr. Zamu iya zuwa mu ganta?

Aa ba zaku iya ba sbd yanayin jiki ta se nan da sati daya zaku iya ganin ta.

Godia suka mishi sannan suka tafi..

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[11/24/2017, 9:20 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ櫍鈾モ潳鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍鉂も櫏鈾b潳鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鈾b潳鈾b櫏鉂も櫍

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 _*HAJOW*_ 馃寪
*Hakuri Da Juriya Online Writers*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Duk wanda baya tausayin mutane Allah ba zai ji tausayin shi ba_

         1鈨�0鈨�9鈨�

             鈾�

Abbiey ya shigo gida da sallama, a parlor ya sami Ummiey da Janan zaune yace “me ake tattauna babu ni”

Ummiey tace “Sirri ne tsakanin ‘Ya da Uwa”

“Nima ai ‘Ya tace kuma Mama ta kin ga ko na fiki matsayi”

Duk suka sa daria

Ummiey tace “dama magana muke yi akan ko za ta samu wani aiki ne ko kuma zata koma makaranta shine ka shigo ka ji mu muna magana”

Aiko faduwa tazo dai dai da zama dama jiya na ji an fara saida form yanzu dai bari in duba naga ina da yafi dacewa ta tafi tunda Direct Entery ne”

Ummiey tace Allah yasa a dace Allah ya zaba mafi alkhairi..

Abbiey na ngd sosai Allah ya sa a dace Allah kuma yasa albarka” inji Janan..

Ya amsa da Ameen

           *****

Bayan kwana 3 se gashi da forms guda  2, daya na Base University Abuja dayan kuma na UNILAG wato University of Lagos! Ummiey tace “Nursing zaki dai saka koh?

Tace “a’a ni yanzu so nake na zama kwararriyar Likitan Mata wato Gynae Doctor sbd mata sunyi karanci a wannan fannin daga maza se waenda ba Muslmai ba, se kiga mace ta je ganin Likita kuma namiji tana fada mishi sirrin ta wanda ko gaban mace yar uwarta se ta jin kunyan fadar haka, sannan idan ma ya kai da yaga tsiraicin ta haka nan zata bude mishi ya gani in dai tana so ta samu maganin ciwon ta ni kuma wannan dalilin yasa nake jin kishin matan mu kuma shi ya sa zan karanta wannan fannin sbd muma mu samu cigaba kuma in kare mutuncin mata yan uwana”

Dadi sosai Ummiey taji tace “gaskiya wannan shawarar taki abun dubawa ce kuma da za a samu mata kaman ki dayawa za a samu ci gaba me anfani Allah yayi miki albarka ya baki ilimi me yawa”

Abbiey yace ina alfahiri dake Allah yayi miki albarka!

Ameen ya Rabbi Jazakumullahu khairan!

Ameen wa iyyaki!

        
        *****

Yau sati daya kenan da yi ma Hanan yar gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna aiki, bakin kofan dakin cike yake da jama’a yan zuwa dubiya, Dr. Godwin ne ya karaso bayan sun gaisa yace “zaku shiga one after d other kuma pls banda hayaniya”

Maman ta da Baban ta ne suka fara shiga, a kwance suka ganta nade da bandeji babu inda ake gani hatta idanun ta an sa mata wani karafuna, a jiki ga kuma wasu na’urori jone a jikin ta.. Kallon ta suke yi duk jikin su a sanyaye dan sun fara cire rai da ita gata ita kadai ce kwal a wajen su

Hankali tashe suka fito, wajen Dr. Godwin suka nufa Maman se kuka take yi shima dai Baban karfin hali yake yi amma hankalin shi ya kai kololuwa wajen tashi, suna karasawa yace “Dr. Zata samu sauki kuwa? Kana ganin zata tashi? Dr. Kar ka bari ta mutu ita kadai kawai muke da Dr. Ka taimake mu!

Cike da tausayi yake kallon su yana mamaki wai shine yau Mataimakin Gwamna ke ronkon shi? Yau ina mulkin? Ina karfin ikon? Ina wani girma da jijji da kan yake? Hmmm lallai mu mutane ba a bakin komai muke ba, kuma mu bamu isa muyi ma kan mu komai ba dole ne se wani ya taimake mu ta wata hanya!

Dr kayi shiru baka ce komai ba kai muke sauraro, ni nayi maka alkwarin kudi masu yawan gaske da duk wani abu da kake so zan baka!

Dr. Godwin yace “kuyi hakuri kuje ku cigaba da addua’a ni ban isa in bata lfya ba, Allah ne ze bata lfya ni dai nayi iya kokari na ban isa in sa ta rayu ba ko Da zaka bani duk duniya da abunda ke cikin ta dan ranta baya hannu na se dai in zama sila wajen cigaba da rayuwar ta sannan ban san gaibu balle in san koh zata warke ko bazataba zata warke ba!

Jikin su yayi sanyi da maganganun da ya fada musu, godia suka yi sannan suka wuce!

An saki list kuma a duka Universities din sunan Janan ya fito Base Uni sun bata Biochem, UNILAG ne suka bata Gynaecology!
Nan fa ta dinga murna tayi ma Allah godia se dai ita bata so tayi nisa da gida kuma taji Ummiey da Abbiey suna tunanin barin ta tafiya can Lagos din!  Ita dai ta bar ma Allah zabi! Sannan tana jiran su yanke hukunci a matsayin su na iyayen ta…

Cikin kwana 2 suka yanke hukunci kawai su barta ta tafi dan sun yarda da tarbiyan da suka bata amma za su cigaba da taya ta da addua’ar Allah ya tsare ta a duk in da take dan yanzu duk tarbiyyan Yaro seka hada da addua’a.

Da Ummiey ta fada mata abunda suka yanke a take a wajen ta fadi tayi sujjadar godia sannan ta rungume Ummiey tana farin ciki.. Itama Ummiey tayi farin ciki da ganin yarta na cikin farin ciki dan tun bayan rabuwar su da Imran ta rage walwala da farin ciki…

Kwanakin da Dr. Godwin ya diba dan bude fuskarta yau ya cika mutane sun cika ta ko ina a asibitin, yan jirida, yan gidan T.V da Radio duk suna wajen dan daukan rahoto, Dr. Godwin kawai ake jira ya karaso..

Cikin Izza da Jarumta ya shigo asibitin sanye da Bakar suit da mint blue shirt ya rufe idon shi da bakin glasses, yana zuwa yan jirada suka yo caaa a kanshi suna mishi tambayoyi!

Ku bari muga yanayin aikin kafin ku fara min tambayoyi! Abunda kawai yace dasu kenan ya wuce.. !

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[11/28/2017, 7:55 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [11/27, 7:44 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂ゐ煐も潳馃枻鈾モ潳鈾モ潳馃枻鉂ゐ煐も潳馃枻鉂ゐ煐も潳馃枻鉂ゐ煐も潳鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫍鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫏鈾b櫏

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 _*HAJOW*_ 馃寪
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_* 鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Wannan Shafin na sadaukar da shi ga dukkan cousins dina! Ina son ku fiye da yanda kuke zato_!! 馃馃馃憚馃拫馃槝鉂�

        1鈨�1鈨�0鈨�

Zuciyar shi na dokawa da karfi ya bude dakin! Kamar kullum tana kwance, gaban gadon ya karasa ya tsaya yana kallon ta kamar yana tunanin wani abu, bude kofan da akayi ne ya sa shi waigawa, Dr. Magaji, Dr. John da wasu Likitoci mata guda 2 suka shigo, suma gefen gadon suka je suka tsaya, bayan sun dan gaisa ya mika musu hand gloves, cikin kwarewa suka fara warware mata bandejin da almakashi suna yi suna yankewa sbd rage mishi tsawi! Jikin ta yayi fari tas sbd dadewan da tayi da bandeji da kuma maganin da aka shafa mata a jiki! Wani lotion da riga armless dai dai gwiwa Dr. Godwin ya dakko ya miqa ma Likita mace yace  “ki shafa mata a ko ina in kin gama ki sa mata wannan rigan kafin a bude fuskan”

Abun da ya umurce ta tayi har ta gama ta sa mata rigar!

Baya duk suka koma suka bar Dr. Godwin ya bude mata fuskar da kanshi sbd aikin shi ne su dai yan kallo ne se kuma in ya ba su umurni su yi wani abun!

Sabbin hand gloves ya sanya sannan ya fara warware mata fuskan su kan su da suke tsaye sun kosa ya gama suga fuskarta, ya kai kusan mintuna 30 yana yi yana shafa mata wani abu a haka har ya kusa gamawa!

Cak ya tsaya dan ji yake kamar karya bude, zuciyar shi tana mishi waswasi, ji yayi an dafa shi yana juyowa yaga Dr. Magaji yana daga mishi kai alamar ya bude!

Motsi ya fara yi da bakin shi wanda shi kadai ya san me yake fada sannan ya ji wani karfin gwiwa ya zo mishi! Janan ta fado mishi rai ya tuno duk lokacin da suke aiki ko me za tayi se ta ambaci sunan Allah, murmushi yayi  yana me tsintar kanshi da fadin “BISMILLAH! Sannan ya bude fuskan!

Ya Salaammmmmmmm! What a transformation! unbelievable! Dr. Magaji ne ke wannan maganan  ya rungume Dr. Godwin cike da farin ciki!

Dr. John ya sake baki yana kallon wannan abun mamaki

Su kuma Likitoci matan nan suka ce “congratulations Sir!

Wani irin farin ciki ne mara misaltuwa ya lullube Dr. Godwin dan gaba daya be yi zaton aikin nan ze yi kyau ba!  Ohhhh My God!! Thank u Lord! Ngd maka da wannan ikon naka!

Duk kallon ta suke yi cike da mamakin ganin fuskarta tas! Babu ciwo balle tabo! Tayi fari dan gaba daya fuskarta ta canza domin wancan fatan nata daya lalace ya daye gaba daya wani sabo ya fito!

Waje ya fita fuskar shi dauke da murmushi! Iyayen ta na ganin shi suka dinga kutsawa cikin tarin jama’a suka karaso gaban shi!  Suna fadin “Dr. an dace? Ta tashi?

Be iya ce musu komai ba se juyawa yayi alaman su biyo shi, har rige rige suke yi wajen shiga dakin! Dai dai bakin gadon ya tsaya suma da sauri suka karaso suka tsaya! Kallon ta suke yi suna karawa, amma sun rasa bakin magana! Da kyar Baban ya bude baki yana fadin ”Dr. Yarinya ta ce wannan? Ka tabbata ita ce? Ya kalli matar shi  “kin ga abun da na gani? Sweetheart din mu ce ko idona ne ke min gizo?

Nima dai ban tantance ba gani nake kamar mafarki! Ta bashi amsa

Yanda suke yi yasa Dr. Godwin murmushi yace “ita ce ba wata ba! Mu gode ma Allah daya dawo mata da abun da ta rasa, sannan kuma ya barta da ranta!

Dr. Yaushe zata bude ido toh? Suka tambaye shi

Nan da awa daya sbd alluran da aka mata!

Murnar da suke yi fadan shi ma bata lokaci ne..

Hayaniyar mutane yasa shi da kan shi Baban ta ya fita yace “ku dan rage murya! Nan da awa daya za a fito da ita ku ganta ku ga yanda ta koma! Be jira amsan su ba ya koma ciki!

               馃枻

Awa daya dai dai ta fara bude ido a hankali, dishi dishi take ganin komai, har ta fara dan gani ba sosai ba “innalilllahi wainnailaihirrajiun” abunda ya fara fitowa daga bakin ta kenan! Da azama suka karaso inda take! Hanan! Hanan! Kina ganin mu? Ina ne yake miki ciwo Darling? Maman ta ke wannan maganan!

Hannu ta daga a hankali ta mika ma Maman tace “Mum! Ta juya kalli Baban ta tayi mishi murmushi tace “Dad! Hawaye suka zubo mata!

Dr. Godwin ya karaso da sauri yana kallon ta “akwai inda yake miki ciwo ne?

Ta girgiza kai

Kina gani na?

Ta share hawayen ta tace “eh ina ganin ka amma ba sosai ba Ido na is not clear!

OK bari muga zuwa anjima maybe idanun su dawo normal!

A tare Maman ta da Baban ta suka rungume ta! Hannun ta ta daura a bayan su se hawaye ke fita daga idon ta dana Maman ta! Se sun dago sun kalle ta se su kara rungume ta!

Mum!

Dagowa tayi tace ”naam Darling!

Hannu tasa tana goge ma Maman hawayen ta tace “ki dena kuka, godiya zamu mika ma Allah daya bani lafiya!

Gaskiyar ki ne, Allah mun gode maka da wannan ni’imar..

Tace “Ya Allah na gode maka! Mum, Dad kuma nagode muku kuma ina alfahari daku a koda yaushe!

Muma muna alfahari dake! Suka manna mata peck a kumatu!

Gefen Dr. Godwin ta kalla tace “thank u very much DOC thanks 4 everything, May Allah bless u!

Ya amsa da Ameen
Tare da fadin ”ya kamata a kaita dakin hutawa sbd tana bukatar hakan!

Ba dan sun so ba suka tashi! Wata riga kamar ta shan iska me dogon hannu da hula ya miqa ma Mama ta yace “ki sa mata don za a fitar da ita kuma naga mutane dayawa a waje sannan ba a so iska ya dinga taba ta da yawa sbd skin din ta beyi kwari sosai ba,

A hankali take sa mata rigar dan gani take in tayi da karfi zata gwalje mata fatan!

A tare suka fito dukkan su ana turo ta akan gado!

Suna fitowa yan jarida suka fara turereniya wajen daukan rahoto! Kowa da abunda yake fada a haka da kyar suka ratsa su suka wuce! Special daki aka kai ta… Nan ma yan jirada seda suka biyo su! Masinja Dr. Godwin ya kira wanda Mataimakin Gwamna ne ya bukaci haka! Yana shigowa ya zube a kasa yace “gani Sir”

Dr. Godwin yace “bani nake neman ka ba”

“ni nake neman ka! Kaje ka ce ma yan jiradan nan su tafi se ranan Juma’a su zo gida na zan hada gagarumar walima tare da kyauta na musanman da zan ba Dr. Godwin, za su iya zuwa su dauki duk rahoton da suke so zan bar su dauki duk abunda suke so!
An gama ya mai girma! Ya fita da dan gudun shi!

Sakon ya fada musu, ba haka suka so ba amma duk da haka sun ji dadi dan ko ba komai ranan Juma’a za su samu daman daukan rahoto! Daya bayan daya suka fara watsewa!

Ta ko ina labarin ake watsa tare da gayyatan mutane zuwa wannan taro! Duk jaridan daka siya labarin ne a farkon shafi tare da hoton Dr. Godwin, se kuma hoton ta lokacin da baayi mata surgery din ba da hoton da aka mata! Haka gidan radio kullum se an sanar! Duk channel din TV daka sa shine a headline din su!

*Ranar Juma’a*

Tun da safe aka fara ta ruwa dan mutane ta ko ina se zuwa suke dan su ganewa idon su, duk wanda yazo mai kudi, dan kasuwa, talaka da duk wani mutum an barshi ya shiga gidan dan Mataimakin Gwamna yace a bar kowa ya shigo kar a hana kowa shigowa!

Karfe 1 dai dai Hanan da Maman ta suka fito cikin shiga ta alfarma! An ma Hanan kwalliya me kyau da kayatarwa, ta yi kyau sosai tamkar ba ita bace mara lfya wacce tasha jinya, fuskar nan kamar ba wacce ta baci ba kyan gani kwanakin baya! Wajen zaman da aka ware musu suka zauna!

Baban ma ya zo

Dr. Godwin kawai ake jira ya karaso! Se kusan 1:30 ya zo wajen cikin shigar data amshe shi, idan ka ganshi zaka dauka tamkar ba dan Nigeria ba yayi kyau sosai! Wajen zama aka bashi kusa da Mai Girma Gwamna! Seda ya zauna sannan aka fara gabatar da abunda aka zo yi!

Live gidan T.V suke  nuna komai a lokacin su Janan dukkan su suna parlor Abbiey ya sa BBC.. Nan suka ga headline din! Zama suka gyara, Dr. Godwin aka nuno zaune yayi crossing kafar shi, cikin zare ido Janan take kara kallon shi dan ko daga bacci ta tashi ba zata manta fuskar shi ba!

Ya Khaleel yace  “kamar wannan Dr. Din na asibitin da Little Princess tayi aiki koh”

Ya Saleem yace “ai kuwa shine!

Abbiey yace “Ikon Allah gaskiya ya burge ni gashi very young, kuma shine na farko daya fara wannan surgery din a duk fadin Nigeria!

Hoton Hanan aka nuna a alon talbijin din an hada wanda fuskan ta ya lalace da kuma wanda aka gyara!

Ummiey tace “lallai Allah ya bashi fiqrah da basira, ga kuma sa’a se dai yana da nakasu ta wajen addini, dama ya musulunta da mutane sun ji dadi!

Abbiey yace “Wallahi kuwa ni yana min yanayi da musulmai kuma ina mishi kallon sani!

Duk abunda suke fada ita dai Janan kallon su take yi ta kasa cewa komai!

Mai girma Gwamna ne ya tashi bayan ya yi jawabi tare da janjinar ban girma ga Dr. Godwin se yace  “a matsayi na na Gwamnan garin nan na baka kyautar motoci guda 10 tare da kudi miliyan 20! Nan fa waje ya kaure da ihu!

Mataimakin Gwamna shima ya tashi yace “a matsayi na na maihaifin yarinya na baka kyautan filaye guda 5 da gidaje 4 sannan a madadi na da iyalai na baki daya na baka miliyan 30! Sannan kofa a bude take ka fadi duk abunda kake so zaa baka shi yanzu!

Dr. Godwin ya tashi ya fara magana cikin turanci me daukar hankali yana fadin  “ina godia da duk kyautar da kuka bani duk da ban cancanci wannan kyauta me yawa ba amma ina farin ciki da matukar nuna godia a gare ku, ina son abu 2, daya ba zaku iya bani ba se dai in fadi dayan!

Ka fadi duk abunda kake so zaka same shi!

Ina so daga yau in ajiye aiki a bisa yarjejeniyar da muka yi da yan Ministry Of Health da fatan zan samu haka!

Kowa dake gurin be ji dadi ba dan in har ya bar aiki sun yi babban rashi!

Mai Girma Gwamna yace  “munji bukatar ka amma ba haka muka so ba tunda mun maka alkawari zamu maka duk abun kake so toh ba zamu saba alkawari ba, mun yarda ka ajiye sannan a duk lokacin da kake bukatar dawowa toh kofa a bude take”

Wani murmushin dadi ya kubce a fuskan shi sannan yace “Nagode sosai da sosai!

Duk wanda yazo wajen yaci ya sha wasu ma harda guzuri suka yi ga kuma kyautan shadda, karamin buhun shinkafa da dubu 10 aka ba ko wani namiji mata kuma atamfa, shinkafa da dubu 10!
Haka taro ya watse kowa yana cikin farin ciki da annashuwa!

Dr. Godwin yana fitowa yan jirada suka tsare shi suna mishi tambayoyi!

Wani yace shin zaka iya fada mana ya akayi ka iya yin wannan aiki me hatsari wanda baka taba yi ba?

“Ba yin kaina ba ne ikon Allah ne kawai domin da yardar shi ne na samu daman yin wannan aiki!

Zaka iya fada mana dalilin ajiye aikin ka a lokacin da mutane ke tsananin bukatar ka?

“Bana yin aiki cikin walwala kuma a cikin damuwa nake yin komai shiyasa na zabi barin aikin domin aiki na yana bukatar natsuwa da kwanciyar hankali!

Toh meke saka damuwa?

Wannan kuma personal issue na nane wanda ba zan iya fada ba!

Haka dai suka yi ta mishi tambayoyi wani ya ba su amsa wani kuma ya share su!

A can Lagos ma Momma, Dad da Annabelle suma suna kallon komai! Farin ciki mara misaltuwa suka dinga yi Momma har da kukan farin ciki, nan fa suka zube gwiwowin su kasa suna wakan godia irin na addinin su!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/4/2017, 10:45 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/3, 2:45 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂ゐ煐も櫏鈾b櫏馃枻鈾b潳馃枻鈾ヰ煐も櫍鈾モ潳馃枻鉂も櫍鈾モ櫍鉂も櫍鈾モ櫍鉂ゐ煐も潳馃枻鈾b潳鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏馃枻鉂も櫍鈾ヰ煐も櫍鉂も櫏鈾p煐も櫏鉂も櫍馃枻鈾モ櫍鉂ゐ煐ゐ煐も潳鈾モ櫍馃枻鈾モ潳馃枻鈾b櫏

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_* 鉁嶐煆烩湇馃徎

_Duk abunda hakuri be baka ba toh rashin hakuri ba zai baka ba!!!_
_Mu kasan ce masu hakuri a koda yaushe!!_

      1鈨�1鈨�1鈨�

Washe gari da wuri ya fara shiri dan komawa Lagos ko su Momma basu san ze zo ba dan surprise yake son basu!

Yana zuwa airport ya gama komai nan da mintuna 30 zasu tashi!

             馃枻

Yana fitowa daga jirgi ya tsare taxi, daya ke drop ya dauka har kofan gida ya ajiye shi!

Kallon gidan ya dinga yi a ran shi yace  “nayi missing gidan nan da mutanen gidan! Sannan ya fara knocking kofan!

Mai gadi dake zaune yana gyangyadi yaja tsaki yana fadin “waye ne ze zo ya dame ni ina hutawa ta! Ya tashi riqe da sanda yana fadin  ”waye ne a wajen?
Shiru Dr. Godwin yayi!
Mai gadin ya kara tambaya nan ma shiru! Wani dan karamin space dake jikin kofan wanda zaka iya hango mutum daga waje ya dan leqa!
Budewa yayi yana fadin  “ka zo kana ta faman knocking ana tambayan ka waye kayi shiru kuma kana ji! Wa kake nema?

Cike da mamaki Dr. Godwin ke kallon shi a ran shi yace “gaskiya wannan bako ne be san da wanda yake magana ba!

”Mr. Man in ba zaka yi magana ba ka fita tun kafin raina ya baci in maka rashin mutuncin”

Kallon sama da kasa Dr. Godwin yayi mishi sannan ya raba shi ya fara tafiya!

Da gudu ya biyo shi yana fadin  “kai wani irin mutum ne? Kazo ana maka magana kayi banza da mutum sannan ka wani shige ba tare da izini ba”

Shi dai be tanka shi ba ya cigaba da tafiya cikin bacin rai!
Se fama masifa Mai gadin yake mishi tare da fada mishi duk maganar day yaga dama a haka har suka kai kofan parlor’n gidan!

Hayaniyar mai gadin ne ya fito da su Momma cikin sauri! Cak suka tsaya suna kallon Dr. Godwin tsaye ya yamutsa fuska da ganin shi yana cikin bacin rai! Har rige rige suke wajen karasowa in da yake, a tare suka karaso suka rungume shi, shima ya ajiye akwatin hannun shi ya rungume su yana jin wani irin natsuwa tare da jin duk wata bacin rai ya kau suka ce “we really missed u Baby!

yace “I missed u more ! There is no place like home!

Mai gadi dai kallon su kawai yake yi yana mamakin waye wannan! Yana cikin tunani ya tsinkayo muryan Dr. Godwin yana fadin  “Momma I want this trash outta this house! Ya nuna mai gadi!

Kallon shi Momma tayi tace ” haba Baby daga dawowan ka yau ka fara daga murya mu je ciki kada kanka yayi ciwo”

“No Momma ba zan shiga ba se naga an kore wannan abun daga cikin gidan nan kuma ba se anjima ba yanzu nake so ya bar gidan nan”

Gwiwowi biyu mai gadi yasa a kasa yana fadin  ”Oga abeg, abeg u in d name of God forgive me, ban san kai dan gidan nan bane, nayi haka ne sbd kare aiki na amma ba dan komai ba ka taimake ni kayi hakuri!

Wani kallon raini ya watsa mishi kafin yace  “kar ka bari in fito in sake ganin ka a gidan nan! Ya wuce su Momma ya shige ciki!

A tsakar wajen Mai Gadin ya fadin yana ta kuka kamar karamin yaro! Annabelle ta kalle su tace “Momma haka zamu bar shi ya tafi? Ji yanda yake kuka, kuma kun san wahalan da yake ciki kafin ya samu wannan aikin kuma Dad ne fa ya kawo shi!

Momma tace “toh ya kike so muyi? Kema fa kin san halin Baby in yace yana son abu in ba a mishi ba akwai matsala, ni dai bazan bata mishi rai ba daga dawowan shi!

Annabelle ta kalli Dad tace “Dad zaka iya mishi magana ya yi hakuri?

“Princess kin san halin Brother din ki I don’t think ze janye daga abun da ya fadi!

A ranta tace “ohh! Gaskiya sun shagwaba Babyn Momma da yawa su basa tunanin halin da wasu zasu shiga  se gudun bacin ran dan su!

A fili kuma tace “OK! OK!! Naji I will handle it my self” ta wuce su!

A bakin kofan dakin shi ta tarar da shi a tsaye ya dafa kanshi , a hankali ta karaso tare da dafa bayan shi  ”Babyn Momma me ya faru?

“Lil Sis ki kalli Dakin nan duk kura! Na kasa shiga ciki sbd na san ba zan iya takawa ba kuma ina so in yi wanka amma ba zan iya ganin dattin nan ba gaskiya”

Huh! Babyn Momma ba zaka taba canzawa ba, ni ban ga wani datti ba dan ko shekaran jiya seda Momma tasa aka gyara maka amma yanzu kazo har ka fara rigiman ka!

Dariya kadan yayi duk da baya jin yin haka amma ba zai iya bata rai ba In yana tare da ita sbd yana tsananin son ta!
“Toh naji ba zan iya yi a nan ba can I use ur toilet pls! Ya hade hannayen shi waje daya alaman ro’ko!

Dariya tayi tace  “Anything 4 u Babyn Momma, amma zan ro’ke ka wani abu in ba zaka damu ba!

Yace ” Uhum ina jin ki Lil Sis!

Hannu ta miko mishi alaman su kulla alkawari, shima ya mi’ka mata suka kulla!

Tace “Daman akan mai gadi ne pls kar ka kore shi, cuz in ya bar nan bazai dunga samun abinci ba pls ka taimake shi!

Ajiyar zuciya ya sauke dan dai kawai sun yi alkawari ne da ba zai janye kudurin shi akan koran mai gadin ba! Gira kawai ya daga mata ya wuce hanyar da zai kaishi dakin ta!

Dadi taji daya hakura kuma ya yarda , da sauri ta fita tace ma Mai gadi “yace ya hakura but kaima ka kiyaye ko dan nan gaba ka dena daukan mutane for granted! Godia ya dinga mata kamar ze kifa dan murna!

A takaice dai se da aka sake share dakin aka wanke mishi bayi tare da sa room freshener kafin ya iya shiga dakin!

Abinci aka shirya mishi yaci ya dan kwanta dan hutawa se bayan ya tashi  suka sha hira sosai harda irin nasarorin daya samu ta fannin aikin shi amma be fada musu komai akan Janan ba dan ya barma kan shi sani! Dad ya fada mishi nan da 1 week zasu koma gidan daya gina musu a Abuja a nan se ya nema aiki kafin a gina mishi nashi asibitin!

Yaji dadi sosai!

Se can dare suka wuce dakunan su don su kwanta…!!!

              馃枻
              鈾�

*Kuyi hakuri zaku dan dinga jina shiru ba zan samu daman turo muku MATAR DOCTOR a kan kari ba sbd waya ta tana da matsala..!! Da fatan zaku fahimce ni kuma za ku yi min uzuri!! Nagode sosai!! I LOVE YOU ALL!!!*

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/9/2017, 11:14 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/9, 7:25 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ櫊鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫏鉂も櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鉂も櫊鈾モ櫍鈾犫潳鈾犫櫏鈾b櫏鈾犫潳鈾犫櫏鈾b櫏鈾犫潳鈾犫櫍鈾モ潳鈾犫櫏鈾b潳鈾b櫏

馃寪 *HAJOW*馃寪
*Hakuri Da Juriya Online Writers*

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

_Wannan shafin naku ne Masoya na!_
_Wasu sun sanni ni ban san su ba!_
_Wasu na san su amma su basu sanni ba!_
_Wasu na san su sun sanni_!!
_A duk inda kuke ina son ku kuma ina gaida ku!! Allah ya bar soyayya_!! 馃槝馃槝

          1鈨�1鈨�2鈨�

Sati na zagayowa su Momma suka koma sabon gidan su dake Maitama Abuja! Gida ne mai kyawun gaske komai ya ji! Self contain aka ware ma Dr. Godwin!

  Cikin satin suka fara shirye shiryen komawan Annabelle sch, Momma tayi tayi ta bari a aiki driver ya siyo mata duk abunda take bukata amma Annabelle ta k’i yarda tace  “Momma ni kam nafi so in je da kai na ba lallai bane ya siyo min duk abunda ya kamata ba”  suna cikin haka se ga Dr. Godwin ya shigo yana danna wayar shi, kujeran da suke zaune ya zauna shima amma a tsakiyar su

Yace “maganar me kuke yi baku kira ni ba?

Momma tace  “wai dole Ita da kanta zata je kasuwa siyo kayan komawan ta sch, ni kuma nace ta bari Driver yaje”

Yace “toh Momma ki barta mana in dai zata iya good and fine” ya daga kafadu!

Toh shikenan tunda haka kace, but ba za tayi driving ba se dai driver ya kaita in ta gama su dawo”

Tace ”na yarda! Thank u Momma!

Gefen Dr. Godwin ta juya tana mishi wani kallo me nuna alaman roko!

Ya gane me take nufi amma yace “ki je ki shirya mana ki tafi kin zauna kuma time yana wucewa”

Kasa tayi da ido tana lankwasa yatsun ta kafin ta d’ago tana fadin “Babyn Momma pls ka taimake ni ka raka ni”

“I can’t! Ki je ke kadan ki se kin dawo! Ya cigaba da danna wayar shi! Jiki a sanyaye ta tashi, be ankara ba ta fizge wayan tana mishi gwalo, ganin ya tashi ne yasa ta fara gudu, aiko shima ya bita, haka suka dinga zagaye dakin se faman ihu suke yi kamar kananan yara

Momma na daria tace  ”baku san kun girma bane?

Da kyar ya iya kamo ta rike da kunnen ta suka karaso inda Momma take suka zube suna maida nunfashi, da sun kalla juna se su tuntsire da daria, haka Momma ta biye musu suka dinga kwasar daria mara dalili! Seda suka gaji dan kansu sannan suka yi shiru!

Tace ”Babyn Momma bari in shiriyo mu tafi” bata tsaya jin amsar shi ba ta wuce da sauri..
Inda ta barshi ta dawo ta same shi, ta fito dauke da hand bag,  tace  ”are we good to go?
Ya mike ya na fadin  “ni dai gaskiya kin takura ni, oya muje”
A tare suka je suka yi kissing kumatun Momma suka ce ”se mun dawo!

Tace ”a dawo lfya, ku kula da kan ku banda rough driving kuma kada kuyi dare ku dawo da wuri”

Yes MUM! Suka amsa sannan suka fice!

Murmushi tayi ita kadai tana fadin “ina matukar son ku, bani da tamkar ku, ina alfahari daku ‘ya’ ya na! Ta jingina a kujera tana murmushin jin dadi!

Se yamma likis suka dawo, basu samu Momma a parlor’n ba, suna shigowa suka baje a kan kujera dan ba karamin gajiya suka yi ba! A haka Momma tazo ta same su  tace  ”kun sha kasuwa!

Annabelle taja dan gutun tsaki tana fadin ”I’m damn tired Momma ji nake kaman ba zan iya daga yatsa na ba sbd gajiya”

Dr. Godwin yace  “ke kenan da kayan ki ne ni da naje rakiya in ce me? Duk kin bani wahala yau din nan yanzu ma kaina ciwo yake min” ya yamutsa fuska!

Momma ta tako da sauri tana taba goshin shi tare da mishi sannu!

Annabelle tace ‘”O! Momma abun ma yar son kai ne? Ni ba ki da mu da gajiyan da nayi ba se Babyn ki koh?

”eh mana! Ai shi rakiya yayi ke kuma fa kika ce da kanki zaki je toh yanzu miye kike korafi?

Sum_sum ta wuce dakin ta dan bata da bakin magana tunda ita tace taji kuma ta gani!

     *******
Su Janan ma se shirin tafiya makaranta ake yi, duk abunda take bukata Abbiey ya siyo mata dai dai gwargwado! Gobe za a tafi kai ta!
Ummiey da Abbiey zaune a parlor suka kirata suka mata nasiha me tsuma zuciya tare da mata Addu’ar samun nasara!

              鈾�

Washe gari!!! Cikin shiri suka fito dukkan su harda Ya Khaleel da Ya Saleem, a motar da Abbiey ya siya musu na gida zasu tafi wacce ta sha tinted glass, Abbiey yaso suje da nashi amma da safe suna dubawa suka ga tayoyin sun yi kasa, babu yanda za su haka suka hakura!

  
             鈾�
   
Momma suma sun shirya an saka komai a bayan boot, sun so subi jirgi amma basu yi booking da wuri ba Dr. Godwin ne ze tuka su, shima dai motar tashi rufe take da tinted! Hanya suka dauka suna tafe suna jin waka Dr. Godwin yana ta sharara gudu don sun makara wajen fitowa, seda suka biya banki suka biya kudin komai harda wajen kwana inda Momma taso a kama mata off k’ amma ita Annabelle din tak’i tace tafi son cikin sch yanda komai za ayi tana nan ba zata dinga makara ba.. .

Cikin lokaci kadan aka gamawa Janan komai, harda dakin kwanan ta, sun gamsu da dakin Ummiey ta tayata jera kayayyakin ta sannan suka shirya tafiya, tayi kuka kamar idon ta ze fita, suma dai duk jikin su yayi sanyi da ba karamar kewanta za suyi ba, da kyar suka lallashe ta tayi shiru sannan suka dau hanyar tafiya tana daga musu hannu har suka bace sannan ta koma ciki!

A dai dai bakin gate suna zuwa fitowa su kuma Motar su Dr. Godwin na kokarin shigowa, da yake tinted ne glasses din nasu babu me ganin wani a haka kowa ya kama gaban shi!

Suma haka suka gama komai aka ba Annabelle dakin da Janan din take, har bakin dakin suka rakata ta Momma da Dad suka shiga shi kuma Dr. Godwin yace ba zai shiga ba yana jiran su a mota, babu irin rokon da Annabelle bata mishi ba ya shigo amma ya k’i, dan dolen ta ta kyaleshi ta shiga,..

Sallah suka tarar da Janan tana yi, su kuma suka dinga jide kayan su har ta idar,  ganin su yasa gaban ta ya fadi, ga shi harda namiji ya shigo ita bata so aka hada ta da Christian ba amma babu yanda ta iya, cikin mutuntawa da girmamawa ta gaida su! Da fara’a tare da sakin fuska suka amsa mata!

Momma tace  ”kina da kyau ya sunan ki?
Murmushi tayi cike da jin nauyi tace “Janan Pharouk Makarfi!

Wow nice name suka ce da ita!

Ita kuma sunan ta Annabelle, hope zaku zauna lfya!

”In shaa Allah” tace da su!

Horn din da Dr. Godwin ke zabga musu ne yasa su fitowa da sauri tare da yima Janan sallama, har bakin mota Annabelle ta rakasu sannan ta dawo cikin dakin!!

Se da suka kara introducing kan su ma junan su, a yanda Janan ta lura da Annabelle tana da sakin fuska! Hira jefi jefi suke dan yi tunda ba wani sabawa suka yi balle su saki jiki sosai, Janan tace  “Wani course zaki karanta?
Annabelle tace  ”ai ni returning student ce ina karanta Pharmacy” ke fa?

Janan tace  ”ni sabuwar daliba ce amma through Direct Entry yanzu haka zan karanta Gynecology ne!

”Wow kice ke babba ce, gaskiya nayi sa’an roommate, congratulations Dear!

Murmushi me sanyi Janan tayi mata tana fadin thanks!

               ******

Haka zaman su ya kasance gwanin ban sha’awa inda Annabelle ta dinga nunawa Janan koina na makarantan! Tare suke fita lectures dan kusan komai iri daya ake musu se dan abunda ba za a rasa ba!

Kusan kullum se sun yi waya da su Ummiey, dan ba karamin kewan ta suke yi ba, ga kuma kudi da dukkan su suke turo mata harda su Yaya Khaleel wai na handouts da Assignment, kwata kwata Annabelle bata bari tayi komai da kudin ta ita take musu wani lokacin ma Janan bata san an bada abu ba tunda bata shige-shige se dai taga Annabelle tayi mata,  har girki basa yi se dai Annabelle tayi musu takeaway!

Yau ma kamar kullum Janan sanye da dogon Hijjab har kasa da socks sun fito daga lectures a gajiye suna tafe suna maganan lectures din da aka musu yau, Annabelle tace   ”mitchwwwww ni ban san me ya sa ba ban son mutumin nan, lectures din shi is boring ni bana ma gane komai idan na shiga class din!

Janan tace ”ni kuma gaskiya ina ganewa duk da baya da method of teaching amma yana kokari!

Annabelle zata kara magana wayan ta ya fara ringing! Babyn Momma ne ke kiran ta, murmushi tayi sannan ta dauka tana fadin “Babyn Momma nayi fushi da kai, tunda na zo sch din nan sau 2 kawai ka kira ni kaman baka missing dina!

Daga daya bangaren yace  ”No Lil Sis ba haka bane ke ma kin san dole in yi missing din ki kwana biyu ban san meke damuna ba ne kawai ina jin kamar wani abu da na rasa yana kokarin dawo min kuma ban se mene ne wannan ba!

Babyn Momma ka dena sa damuwa a cikin ranka kar ka ja ma kanka ciwo pls!

”Thanks Lil Sys shiyasa nake kara son ki!

Hira suka dinga yi harda shirme ma!

Can tace Babyn Momma ga Bestie na da nake baka lbr ku gaisa!

Ki bari wani lokacin yanzu zan dan yi wani abu ne!

Jin tayi shiru alaman ta ji haushi yasa shi fadin  “ki ce ina gaida ta kafin in kira mu gaisa da ita!
Yawwa Babyn Momma I love u! Bye! Tayi dropping call din!

Sorry Bestie, na barki ina ta waya, Babyn Momma ne yace in gaishe ki!

Bata san dalili ba taji gaban ta ya fadi, daurewa tayi tace ina amsawa!

Wajen siyan abinci suka je nan sukayo takeaway Janan na mamakin tsadan abincin , ita bata ma yi zaton kudin da Annabelle take kashe musu wajen siyan abinci ya kai har haka ba!

Tafiya suke za su koma hostel se ga wani course mate din Annabelle ya zo wucewa shida yan grp din su yace  ” Hi Anny!

Tace hello Sam!

Janan dake gefe taga alaman yana son tsayawa yasa ta matsa can nesa dasu tana jiran Annabelle!

Suma yan group din Sam suka koma gefe!

Sam yace  ”wassap Babe, ykk ne?

Tace ”am fyn!

Wai waccan kawar taki me take nufi ne?
Wani harara ta balla mishi tace kamar ya? Ta san halin Sam akwai san matan tsiya irin marasa jin ‘ya’ yan masu kudin nan ne!

Yace haba ki gane mana ita kullum fuska a daure ga wani abu da take sawa tana yawo a ciki ko irin dan gayun nan ba tayi balle agane ko tana da figure 8 ko…. Be karasa maganan shi ba Annabelle ta dakatar da shi da fadin

”excuse me! Kada ma ka kuskura ka zage ta ko ka fadi wani mugun magana a kanta! Ina ruwan ka da dressing din ta? Ina ruwan ka da shape din ta? Ka ga ka kama kanka ka natsu ita ba irin wawayen emmatan da suke biye maka bane!

Ganin ta dau zafi yasa shi fadin  “calm down Babe ba wai na fadi haka bane dan in bata miki rai ba, kawai dai tana burge ni ne” ya karasa maganan yana shafa kai!

Mitchwwwww taja tsaki sannan tace “whatever! Ni kaga tafiya ta! Har tayi taku biyu se ta juyo tana fadin ” Ehen! Mind u! Daga yau se yau kar ka kara tsayar da ni kana fadin min shirme cuz lokaci na yana da anfani a waje na in kai ba shida anfani a wajen ka! Tayi wucewar ta

Yaji haushin abunda tayi mishi amma Dan dai kawai yana shakkatar ta ne da se ya koya mata hankali!

Wajen abokan tafiyar sa ya koma suka wuce, suna ta tambayan shi abunda ya faru amma ya share dan ba zai iya fada musu wannan abun kunyan ba!

Tana komawa wajen Janan tace  “muje!

Duk da taga yanayi Annabelle din ya nuna tana cikin bacin rai bata tambaye ta dalili ba dan ita ba ta san shiga abunda ba a sata ba! Suna shiga daki suka ajiye kayan su da books din su, Janan ta wuce bayi dan yin alwala sbd lokacin sallah yana wucewa sakamakon rike su da Lecturer din su yayi ita kuma Annabelle plate ta dakko ta juye musu abincin tun daga tsaye ta fara ci dai dai lokacin da Janan ta fito daga bayi tana goge ruwan dake fuskan ta! Da sauri Annabelle ta ajiye cokalin tana rufe baki, daria Janan tayi tace  ”na riga na kamaki kina cin abinci a tsaye, ai na san ba zaki dena ba kuma na fada miki ba kyau!

Sorry Bestie na dena, na kasa jurewa ne cuz yunwan nan kamar zata kashe ni!

“Aiko se dai ta kashe ki cuz se na idar da Sallah za mu ci punishment din ki kenan!

“Pls kiyi hakuri ba zan kara ba, idan kika ce se kin idar ai se dai ki ganni a sume dan kin iya dogon Sallah kuma in kika idar se kin dade kina Addu’a ni kam ba zan jure jiran ki ba!

“Toh ki fara ci kafin in idar kin ga time ya wuce sosai! Ta janyo Hijjab din ta ta shimfida darduma ta tada sallah!

Babu yanda Annabelle ta iya dole se ta jira Janan din cuz ta saba cin abinci tare da ita yanzu ba zata iya ci ita kadai ba!

Bata ja dogayen surori ba sbd bata so ta shiga hakkin Annabelle!

              **
Seda suka koshi sannan Janan tace  ”Sis! Gaskiya lokaci yayi da zamu dena siyan abinci a waje muna da komai fa, tunda muka zo sch din nan bamu taba girki ba se dai mu siya haka zamu bar food stuffs din mu su lalace? Kinga almubazzaranci ba kyau sbd wasu na neman ko da kwatan abincin da muke da shi su dinga dafawa!

“Naji kuma na yarda da shawaran ki amma ai akwai kudi sosai kuma duk Friday Babyn Momma ke turo min kudi banda wanda Momma da Dad suke turo min ai ze ishe mu har muyi hutu dan ni gaskiya ban iya girki ba kuma bana yi ko a gida”!

“Ni zan dinga yi kuma zaki iya In Shaa Allah in muna tare!

Thanks Bestie!

Suka yi murmushi a tare!

          ***
Tun daga ranan suka rage siyan abinci se dai snacks ko abun marmari sbd Janan tana kokarin dafa musu abinci masu dadi!
        
          **
Kowa ya san Janan da Annabelle da kuma yanda suke tafiyar da rayuwar su a sch, yan gulma da sun gansu se su tsaya suna kallon su suna mamakin su! Wasu ma har wajen Annabelle suke zuwa su ta sukan Janan amma da tsiya suke rabuwa dan ita bata yarda a zagi Janan a gaban ta ba!
              

                鈾�

Karatu suke yi sosai dan Jarabawa ta karato, duk abunda Annabelle bata gane ba Janan ke kara mata haske a kai haka duk abunda Janan bata gane ba Annabelle din ne ke kara mata haske akai!

Haka suka yi Jarabawa suka gama cike da jin dadi!

Dad da Momma suka zo daukan Annabelle dan Dr.Godwin baya jin dadi shiyasa be biyo su ba suma din jirgi za su bi! Exchanging address suka yi da alkawarin ziyara, sun so Janan ta bisu su tafi tunda garin su daya amma taki tace ita ma za a zo daukan ta! Babu yanda suka iya haka suka tafi suka barta!
Can ba da jimawa ba se ga Yaya Khaleel da Yaya Saleem sun zo daukan ta! Taji dadi sosai,, suma sun ji dadin ganin ta su suka taya ta kwasan kayanta suka sa a bayan boot suka tafi….

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/17/2017, 11:11 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/17, 7:05 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂も潱: 鉂ゐ煐も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫍鈾b櫏鈾モ櫍鈾犫櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾犫櫏鈾モ潳鈾p煐も潳鈾モ櫊馃枻鉂も櫍馃枻鈾モ櫊鈾b潳馃枻 *MATAR DOCTOR* 鈾モ櫍馃枻鉂も潳馃枻鈾b櫊鈾モ櫍馃枻馃枻鉂も櫍馃枻鉂も櫏鈾犫櫏馃枻鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾p煐も櫏鈾狆煐�

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW* 馃寪
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_* 鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Your birthday was on the 14th and page 114 is urs Safiyya Zubairu Aliyu (Sophie Luv) WOW! What a coincidence….. Happy Birthday to u, wish u Allah’s Noor and Khair Always! Em sorry 4 d late birthday wishes but is better than none! I love u so much Habibty! Allah ya kawo miji na gari! AMEEN!_馃槝馃槝馃槝

   
         1鈨�1鈨�4鈨�

Sun ji dadin hutun da aka basu kuma hakan yana su daman waya a kai a kai!

Wata ranan Laraba suna waya Annabelle tace  ”Bestie gobe ina nan zuwa gidan ku zan tambayi Momma anjima na san ba zata hana ni zuwa but idan na zo kema se kin zo idan mu!

Janan dake tsaye ta dan yi tsalle tare da ihun murna tana fadin ”naji dadi sosai dama ina ta missing din ki nima muna gama waya zan fada ma Ummiey zaki zo kuma nima In Shaa Allah zan zo! Sun taba hira sannan suka ajiye wayan!

Annabelle na fitowa daga dakin ta ta wuce dakin Momma,  a gado ta same ta kwance tana duba wani magazine, jin an shigo ya sata dagowa, Annabelle ta gani ta shigo tare da fadin  ”Hi Momma!

Tace “Hello Princess!

Gefen kafafun ta ta zauna tana dan danna mata su kafin ta fara fadin “Momma gobe ina so in je gidan su Bestie dazu mu kayi waya da ita na fadi mata zan zo shine nace bari in sanar dake”

“naga alama kina ji da wannan kawar taki!

“Momma, nima kaina na san ina son ta, tana da kirki, tsafta, kamun kai, kyauta ga kokari, bata da yawan surutu kuma it’s hardly tayi fushi shiyasa take burge ni kuma nake kara jin ta har raina!

Tunda ta fara magana Momma ta tsaya tana kallon ta se da ta gama sannan tace  “lallai Princess wannan irin zuzuta ta haka! Kinyi saan kawa dama ni tunda nake dake ban taba ji yau kin ce ga frnd dinki ba balle har ki zauna kina yabon ta har haka!

“Momma Janan is different, duk yanda zan miki bayani ba zaki gane ba se kin zauna da ita zaki gane haka!

Murmushi Momma tayi sannan tace  “goben se ki shirya driver ya kaiki!

Cike da jin dadi ta rungume ta tana fadin ”Thank u Momma, U r d bst! Ta fice daga dakin!

      
        ****

Da Yamma Dr. Godwin ya dawo gida yana shaida musu ze tafi Makarfi sannan ga letter nan daga Teaching Hospital Abuja sun turo mishi akan suna so ya fara aiki da su! Sun yi murna sosai tare da mishi Addu’a!

Annabelle tace “Babyn Momma me zaka je yi a Makarfi?

“Kiyi min fatan alkhairi kawai ba se kin sani ba”  Ya tashi ya bar parlon!

Kallon juna suka yi ita da Momma tare suka hada baki wajen fadin miskilancin ya motsa!

         ***
Janan ta sanar da Ummiey zuwan Annabelle, murmushi tayi tace  ”Allah ya kawo ta lfya, ashe gobe muna da babbar bakuwa!

Tace ”aikam dai Ummiey, bari in duba abinci karya kone!

       馃枻

Washe gari Annabelle sanye da riga da skirt na lashi orange nd black, simple makeup tayi ta taje kanta, dan gutun tsaki tayi tace  “Ba abun in je haka ba yanzu Bestie zata fara min korafi bana son rufe kai” dankwalin ta ta jawo tare da zama tayi dauri me kyan gaske sannan ta sa flat shoes baki ta dauka bakin jakarta ta fito!  A parlor ta tarar da Momma zaune, kamshin turaren ta ne yasa Momma kallon ta tana fadin  “wow! Kin yi kyau sosai Princess”

Annabelle tace “like seriously Mum!

Gira Momma ta daga mata!

That’s My Momma” ta fada tare da daga mata hannu ta fita!

Har ta dan yi nisa Momma ta daga murya tana fadin  “Ki gaida min ita, kuma ki dawo da wuri, hope kin tafi mata da tsaraba!

“zan fadi mata, zan tsaya a hanya mu siya mata chocolates!

A hanya ta tsaya ta siyo mata packs na chocolate me yawa sannan suka wuce! Suna hanya Janan ta dinga kiranta tana dauka tace  “huh! Gani nan zuwa ko in fasa zuwan ne?

“Aa karki fasa pls! Se kin karaso! Ta kashe wayan..

Basu wani sha wahalan gane gidan ba sbd driver din dan gari ne kuma gidan yana da saukin ganewa! Har kofan gidan ya kaita yace “Maam zan jira ki fito se mu tafi bari in yi parking a inuwa!

Cike da tausayi ta kalle shi tace “no karka jira ni, naji dazu kana waya akwai ina da zaka je watakila abun is important kaje kar in tsayar da kai cuz I don’t think zan fito nan kusa idan na gama zan kira ka”

Godiya sosai yayi mata yana jinjina kirkin ta, seda yaga shiganta gidan sannan ya juya ya tafi!

A harabar gidan ta tarar da Janan tsaye tana jiran ta, da gudu suka karaso tare da rungume juna cike da farin ciki sannan suka rabu, ta kalli Janan tace  “Bestie me kike ci haka ne kika yi wani fresh da ‘kiba?

Janan tayi daria tace “Ba wani nan ke baki ga kanki ba se ni? Suka kwashe da daria sannan suka shiga parlorn!

Har kasa ta duka tana gaida Ummiey!

Ummiey tace yau dai at long last kinzo kullum Hulwaty bata da hira se naki, sannu da zuwa, ga wuri ki zauna, ya mutan gidan naku?

Cike da jin kunya ta zauna sannan ta amsa mata!

Ganin ta kasa sakewa yasa Ummiey ce ma Janan “Ki kaita dakin ki, anan se ta huta taci abinci koh!

Annabelle taji dadin haka kuwa, suna shiga Janan ta wuce kitchen ta kawo mata abinci a cikin cooler tare da Kunun aya me sanyi cikin jug, ba wani abinci iyayi tayi ba dambun couscous tayi wanda ta sa nikakken nama, zogale, se karas, albasa da green pepper se kamshin abincin yake yi,  Annabelle taci sosai tana ta santi suna hira tana shan kunun aya can se wayan Janan ta fara ringing da sauri ta dauka tana fadin  ”Ayi min hakuri kawar amana, Eeesher ce ta kira take mata tsiya wai ta share su, bata da bakin magana se dai hakurin da ta bata, sun dan dade suna waya sannan suka ajiye! Annabelle cikin damuwa tace wacece haka?

Kafin ta kai ga bata amsa Wani kiran ya shigo tace ina zuwa pls, ta daga wayan tana fadin “kawar rai da rai hada baki kuka yi ne? Zee ce! ita ma dai tsiyan tayi mata daga karshe suka ‘bige da hira! Se can suka ajiye wayan!

Annabelle ta cika fam! Idon ta sun ciko da kwalla, Janan tace lfya?

Cikin murya me rauni tace su waye?

Janan tace Aisha da Zainab kawaye na da na baki labarin su”

“Kin fi son su ko? Sbd ni ba Musulma bace shiyasa kika fi son su a a kaina ko?
Janan tayi shiru jiki a sanyaye dan maganan Annabelle ya taba ta, can ta daure tace “Ba haka bane!

Hmmm! Cikin mu wa kika fi so toh?

“Dukkan ku ina son ku sosai, but ke matsayin ki ya wuce frndship kin koma yar uwata baki ji Sis nake kiran ki ba ma?
Haka yadan sa taji sanyi a ranta tana fadin in dai kika fi son wata a kaina gaskiya ba zan ji dadi ba sbd ni bani da wacce nake so kamar ki!
Ina son komai naki Bestie, ta ruko hannun ta duka biyu tana fadin “ina jin matsayin ki na daban a zuciya ta, pls ki rike ni da amana kar ki juya min baya sbd ni christian ce!

Zuciyar Janan ta yi rauni ita kanta ta san Annabelle na son ta sosai dan haka ta dinga mata kalamai masu dadi har ta samu ta saki jiki!

Bata bari Yamma tayi sosai ba ta kira Driver, dama yana kan hanya dan haka bada dadewa ba ya karaso!

Ledan chocolate din ta mika Janan tace gashi nan a sha lfya in an gama asha maganin ciwon ciki da bisir” suka yi daria Janan tayi mata godia!

Wani agogo da zoben azurfa me kyau ta bata Ummiey kuma ta bata Arabian perfumes guda biyu masu tsada,  har bakin mota Janan ta raka ta tare da alkawarin ita ma tana nan zuwa! Haka suka rabu cike da kewan juna…..!!!!

Cikin ranta tana jinjina tsafta da karamcin su Janan!!!!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/22/2017, 9:56 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/21, 6:17 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂も櫏鈾b櫊鈾b潳鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b潳鈾犫櫍鈾モ櫍鉂も櫊鈾b櫏鉂も櫍鈾犫櫏鈾b櫏鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ潳鈾b櫊鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鈾b潳鈾モ潳鈾モ櫊鈾b櫏鈾b潳鈾モ櫊鈾モ潳鈾モ櫍鈾犫潳鈾犫櫏鈾犫櫍

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW* 馃寪
*_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_This page is 4 u Bilkisu Muh’d Hassan, Alhaji Khaleefa and CO. Thank y’all for the support, Allah ya saka da alkhairi_鉂b潱鉂�

           1鈨�1鈨�5鈨�

            ******

Sati na zagayowa Janan ta shirya ta tafi gidan su Annabelle, sosai Momma taji dadin zuwanta dan haka kawai taji tana kaunar Janan, tarba na musamman aka mata ga abinci da drinks din kwali kala kala aka ajiye mata Ta dan ci abinci dai dai dama ita ba wani ci gare ta ba! Nan suka fara hira Momma na kallon su cike da sha’awa, tun tana iya biye musu ayi da ita har ta gaji dan da alama hiran su ba me karewa bace daga karshe dai tashi tayi ta koma dakin ta suma tashi suka yi suka shige dakin Annabelle suka cigaba da hiran su.. Annabelle tace  “Nifa kin san duk yawan lecturers din mu babu wanda ke burge ni kuma nake gane lectures din shi kaman me mana Biochem akwai daukan wanka ga sakin fuska gaskiya bashi da matsala”

Tsaki Janan taja tana fadin “wallahi ni baya burge ni, ke dan kina son course din ne shiyasa kike fadan haka”

“No ba sbd haka bane ke ma dai kin san abunda na fada gaskiya ne”

“Ba wani gaskiya, in banda iyayi da kallon matan tsiya daya sa a gaba”

“Kai Bestie wannan mutumin kike ce ma haka? Ba ruwan shi very silent abun shi”

“Nifa ban gane irin wannan yabon da kike mishi ba”

“Ba abunda zaki gane tunda abun haka ne”

Musu suka dinga yi!

Dr. Godwin dake kwance a dakin shi yana bacci hayaniyar su ya tashe shi, tsaki yaja tare da janyo pillow ya cusa kan shi a ciki ko ze dena jin hayaniyar amma kamar kara zuga su ake yi, yama fi jin muryan Annabelle duk da baya fahimtan abun da suke fada, ignoring din shirmen su yayi ya juya dan ya cigaba da baccin amma wani ihu da suka yi seda ya tashe zaune nan take kanshi ya sara!

“Ohhhh My God! Na dawo daga tafi ina son in samu bacci amma wannan shirmen ya hanani ya kara jan tsaki!

Cike da jin haushi ya tashi ya canza kaya, makulli da wayar shi ya dauka dan baya jin ze iya zaman gidan nan sbd hayaniyar su tayi yawa!

Parlor’n ya shiga bega kowa ba In banda muryan Annabelle dake tashi daga dakin ta,  “wato Momma itama hayaniyar ta hanata zaman parlor! kalan ta kalar kawarta shiyasa suke ta zuba shirme,   har yanzu basu girma ba, yarinta yana damun su”

Dakin Momma ya nufa yana daga labule ya ganta tana bacci, dakin ya shiga har gaban gado ya durkusa yana kallon fuskan ta, peck ya mata a kumatu sannan ya bar dakin!
hanyar dakin Annabelle ya nufa, dai dai an fara kiraye kirayen sallah,  Janan tayi wuf! Ta mike tana fadin  “Anny! Musun ya isa haka ana kiran sallah”

Sannin halin Janan yasa tayi shiru dan ta san ko wani magana ake yi ba zata amsa ba  In dai ana kiran sallah!

Bayi ta shiga dan tayi alwala tana rufe kofan bayin Dr. Godwin ya daga labulen dakin, wani kallo yake ma Annabelle sannan yace  ”sannu da aiki, duk kun bi kun ishe mu da ihu da surutu kaman parrots, bakin ku ko ciwo ba ya muku, toh hankalin ku ya kwanta kun tashe ni daga bacci”

Kallon mamaki take mishi dan bata san ya dawo ba, tasowa tayi ta karaso har bakin kofan tana fadin  “Babyn Momma yaushe ka dawo?

“Ba wannan nake son ji ba, ai kin ji na fada miki kin tashe ni bacci gashi nan kaina yana ciwo”

Kunnuwan ta duka biyu ta kama sannan tace  “sorry Dr. Babyn Momma”

Abun yaso bashi daria se kawai ya dan yi murmushi, ya juya yana son barin dakin da sauri tace  “Babyn Momma ka dan tsaya ku gaisa da Bestie na tana alwala a toilet”

A ranshi yace  “bana son haduwa da kawar Lil Sis din nan kafin ma taga kaman ni na damu mu hadu haka nan ta raina ni!  A fili kuma yace “OK bari in bata mintuna 2 in bata fito ba zan tafi cuz ina sauri ne akwai inda zanje”

“toh lemme tell her tayi sauri kana jiran ta ku gaisa”

“No ki barta mana, kin san wasu basa son rushing in suna abu balle kuma kin ce alwala take yi”

Kwata kwata be son haduwa da kawar Annabelle din nan Dan ba karamin faduwa gaban shi ke yi ba In tana maganan ta toh ina ga sun hadu? Maybe zuciyar ta fito daga kirjin shi sbd faduwa!

Hira ta dinga jan shi da shi dan ta dauke mishi hankali!

Mintuna 2 na cika kamar hadin baki wayar shi ta fara ringing yaji dadin haka, da sauri yace  “Lil Sis ki gaida ta an fara kira na kuma gashi bata fito ba In ta fito ina gaida ta”  ya juya da sauri ya bar dakin!

Yana wuce wa sega Janan ta fito tana gyara hannun rigar ta!

Annabelle tace “yanzu Babyn Momma ya wuce se jiran ki yake yi ku gaisa kin wani yi zaman ki a bayi! Bari in ga in beyi nisa ba In ce kin fito”
Kafin Janan tayi magana har ta fita kiran shi!

Mai gadi har ya bude mishi gate yana shirin fita ta karaso tana fadin Babyn Momma pls ta fito!

“Kin cika rigima Princess, Dad ne kadai ke iyawa dake,  kinga yanzu bazan iya fitowa ba bt zan dawo da wuri se mu gaisa haka yayi miki?

Ba dan taso ba tace  “Eh! Ta juya ciki abunta!

Sallah ta tarar Janan nayi ta zauna tana jiran ta ta idar!

Tana idarwa taga bata gan shi ba, taji dadin haka Annabelle tace “Ana jiran shi ne bt na san ba zai dade ba ze dawo in ya so se mu maida ki gida ni da shi!

Kai kawai ta daga amma a ranta tana ta Addu’a kar ya dawo ya same ta a gidan nan!

Har La’asar be dawo ba Janan kam abun ya mata dadi dan haka tace ita yanzu zata wuce kar tayi dare bari ta kira Yaya Khaleel in ya gama yazo ya dauke ta!

“Kar ki kira shi bari mu kai ki nida driver”, jiki a sanyaye ta tashi taje dakin Momma ta tarar ta tashi daga baccin, ta fada mata Janan zata wuce! Takalma flats guda biyu da loafers  guda daya ta sa a leda suka fito tare, Annabelle kuma kayan kwalliya ta hada mata godia ta dinga ma Momma kamar zata ari baki! driver’n gidan su tare da Annabelle din suka kaita har kofan gida amma bata shiga ba se dai tace a gaida Ummiey!

Se can dare Dr. Godwin ya dawo,, ko inda yake Annabelle bata kalla ba sbd tana fushi, ya san dama haka ze faru amma shi yaji dadi daya dawo bata nan!

Har inda take yaje ya dinga janta da magana da tsokana har seda ta hakura!
Suka dan taba hira!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/24/2017, 8:27 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/23, 11:15 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ潱鉂も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫏鈾犫櫍鈾モ櫍鈾b櫏鈾犫櫊鈾モ櫍鉂b櫊鈾モ潱鈾b櫏鉂も潱鈾b櫊鈾モ櫊鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾b櫏鉂b櫍鉂も櫊鈾モ櫊鉂も櫊鉂も櫊鈾モ櫊鉂も櫍鈾モ潱鉂も櫊鈾モ櫊鉂も潱

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*馃寪
_*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*_鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Wannan shafin naki ne *Lubnerh Sufyan!* Baki sanni ba nima ban sanki bt posts dinki da novels dinki su suka sa nake son ki kuma kike burge ni, kina kokari wajen kare mutuncin mata tare da fadakar da alummah!! Allah ya kara miki Ilimi, hazaka da basira!_鉂b櫏 _Rukkybae_馃槒 loves u so much!!! 馃槝馃槝

           1鈨�1鈨�6鈨�

Hutun su Janan ya kare suka koma makaranta! Dawowa nan yasa Janan ta canza salo, ta kan shiga cikin mutane a dan yi hira, sakin fuskan ta da farin jinin ta yasa kowa ke son suyi mutunci da ita, ta lura Musulman sch din addini be dame su ba kwata kwata, se taga wata wai Muslma amma ko gyale babu a jikin ta!

Dan zaman da suke yi kafin a shiga lectures yasa ta fara jan hankalin su cikin taushin harshe akan irin dressing din da suke yi!

Da alama nasihan ta ya fara tasiri a cikin zukatan su, dan haka a yan kwanakin nan da yawa sun fara sa gyale duk da kanana ne amma ta ji dadi dan da alama akwai nasara! Ganin irin raunin addinin Musulunci a makarantan yasa ta rubuta Letter ta kai Department din su a kan a kirkiro Kungiyar MSS (Muslim Students Society) a sch din dan a kara daukaka Darajan Addinin Musulunci! Yafi kusan sati biyu tana bi amma anki approving mata, wani Letter ta kara rubutawa ta kai ma Dean na Faculty of Sciences shima shiru….. Dabara ce ta fado mata dan haka ta sake rubuta wani Letter din ta nufi office din V.C  (Vice Chancellor)! Kwanaki Uku ta jera tana zuwa amma bata samu daman ganin shi ba se a rana na hudu, da kyar ta samu securities din wajen suka barta ta shiga wajen shi! Cikin faduwar gaba tayi knocking ya bata izinin shiga, Babban Mutum ne me kwarjini, wurin zama ya nuna mata ta zauna kafin yace
“ina so in san me ya kawo ki kuma me kike bukata!

Addu’a ta jero a zuciyar ta sannan tayi mishi bayanin komai da duk hanyoyin data bi dan isar da sakon amma be zo wajen shi ba!

Mamaki ne ya cika shi yanda karamar yarinya kamarta tayi wannan tunanin duk da shi ba Musulmi bane amma ta burge shi kuma ya yaba da jajircewan ta tare da yanda ta nuna kishin Addinin ta a fili!

“kar ki damu nan bada dadewa zaki ji feedback daga gare ni” yace mata

Numban wayan ta ta rubuta a wani takadda cike da murna ta dinga mishi godia!

Sauri sauri ta koma dakin su harda sallama tana shiga ta tarar da Annabelle kwance a gado tana karanta Kitabbuttauhid me fassaran turanci! Kallon ta kawai Janan take yi dan da alama Annabelle din ma bata san ta shigo ba!

Tace “Sis Anny Em Back!

Wani irin firgita Annabelle tayi tare da tura takardan a karkashin pillow din ta!
Inda inda ta fara yi tana fadin “Bestie yaushe kika shigo ban sani ba?

“tun dazu na shigo har Sallama seda nayi amma naji ki shiru”

“Am.. am..am I was so carried away ne shiyasa ban ji ki ba”

Gefen ta Janan ta zauna tare da dafa mata kafada tana fadin “tell me! Ina so in sani, ya akayi kika samu book din nan kuma yaushe kika fara karantawa?

Shiru tayi kanta a kasa ta kasa magana

Janan ta kara cewa “kin san bama boye ma juna komai koh? And kece kika kawo wannan shawarar akan mu dena boye ma juna komai, so tell me”

“it’s been long Bestie, na dade ina so in gane mene ne a ciki amma se naga naki na larabci ne shine na dauka naje kasuwa na siyo me fassara!

“Sis! Kina so ki shiga Addinin Musulunci ne?

“Bestie ina so, na dade ina kallon duk wani dabi’un ki da komai naki, yanda kike tafiyar da Addinin ki shi yafi komai daukan hankali na, nasha mafarke mafarke akan ki da kuma hasken dake tattare dake, duk wani littafin addini da kike da shi nima ina da shi kuma ina karantawa, tsam ta tashi ta dakko wani jakarta ta dinga fito ma da Janan Islamic Books su Seerah, Fiqhu, Hadeeth harda littafin Kaba’ir!

Wani irin runguma Janan ta mata tana zubda hawayen farin ciki, ita ma Annabelle hawayen ke zuba daga idon ta, janye jikin ta tayi daga rungumar da Janan tayi mata ta fara share mata hawaye tana fadin  “Bestie ki dena zubda hawayen ki, na sani haduwar mu alkhairi ne”

Janan tace  “hawayen farin ciki ne ke zuba daga ido na ba na komai ba! Ta kara fashewa da kuka!

Da kyar suka tsagaita da kukan sannan Janan tace zan fada miki kalmar shiga Addinin Musulunci kema se ki maimaita amma ki tsarkake zuciyar ki akan zaki shiga addinin Musulunci ba tare da tursasawa ba ko dan wani abu se Don Allah!

Kai Annabelle ta daga sannan Janan ta fara fadin
“Ashhadu Alla ilaha illallah, Annabelle ta fada kamar yanda Janan din ta fada kafin Janan ta kai ga karasawa Annabelle tace “wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu!
“ya akayi kike iya? Janan ta tambaya

Murmushi tayi tace “na gani a cikin littafin tauhid kuma na dade da haddacewa!

Janan ta rasa inda zata sa kanta sbd farin ciki! Ta ce “duk wani zunubi da kika aikata lokacin kina cikin addinin ki na baya yanzu Allah ya yafe miki kin koma tamkar jaririyar da aka haifa yau, baki da zunubi ko daya, zan koya miki wankan tsarki wanda shine mataki na biyu da zaki dauka bayan amsan kalmar shahada, wannan wankan ana yin shi sbd tsarkaka sannan ana yin shi a bisa dalilai daban daban kuma duk iri daya ne se dai banbancin niyya! Kuma ya wajabta akan Baligi namiji da baliga Ta mace!
Ana yin shi idan janaba ya samu mutum,
ana yin shi bayan daukewar jinin al’ada ga mace,
Mace na yin shi lokacin daukewar jinin Biki wato Jinin haihuwa
Ana yin shi lokacin shiga addinin Musulunci bayan karban kalman shahada
Sannan ana yi ma duk mutumin daya mutu cikin Musulunci
Sannan yana da kyau duk wani Musulmi yayi wannan wankan duk Juma’a domin Allah Mai tsarki ne, ya wajabta tsarki akan mu kuma yana son masu tsarki!

Dalla dalla tayi mata bayanin wankan tsarki!

Bayi ta shiga tayi kamar yanda Janan din ta koya mata! Tana fitowa ta gyara jikin ta ta sa wani dogon riga, ita kanta yau taji wani iska me ni’ima yana shiga jikin ta sannan ga wani Kwanciyar hankali na daban, har zuciyar ta kara tabbatar da Addinin Musulunci addini ne na gaskiya!

Janan dake zaune gefen gado ta kalle ta dauke da murmushi a fuskan ta sannan tace  “wlcm to the world of Islam! (Barka da zuwa duniyar Musulunci) Annabelle ta zauna cike da jin dadi sannan tace “Bestie na zaba sunan Fadimatuzzarah! Sbd na dade ina son sunan!

“Alhamdulillah kin zabi suna me kyau kuma me daraja domin sunan ‘Yar Annabi Muhammad SAW ce kuma duk yafi son ta a cikin ‘ya’yan domin ita kadai ce tayi rayuwa me tsawo da shi dan duk sauran suna kanana suka rasu!

Tace “Dan Allah kada ki fada ma kowa cewa na Musulunta sbd iyaye ne manyan mutane ne kuma an san su sosai domin Dad din shine Babban Pastor a Church din mu, ina tsoro a fada musu nafi so in fada musu da kaina amma ba yanzu ba se na samu enough Ilimi da Hujjan da zanyi challenging din su!

Janan ta jinjina kai! Sannan ta bata lbrn yanda suka yi da V.C !

Tun daga ranan Janan ta zama Malamar Zarah (Annabelle) ta dauki alwashin koya mata karatu tun daga *Alif*!! Sannan ta koya mata karatun Alqurani daga *Quhuwallahu zuwa Ammah* sannan ta fara koya mata sallah! Alhamdulillah ta fara daukan abunda ake koya mata dama tana da saurin fahimtan abu!

           鉂�

A yau sako ya iso zuwa ga Janan kan an yarje mata ta yada addinin Musulunci amma akwai sharrudan da aka gindaya mata kuma ta dauka! Ciki harda kare mutuncin waenda ba addini  su daya ba!

Mutane kadan suka fara aiki tare da ita a haka suka dinga jurewa suna Da’awah cikin Hikima da Mutuntawa!

An samu bunkasar mutane a cikin Kungiyar wanda ya hada da Malaman su da basu cika nuna addinin su a fili ba, an hada Seminar inda mutane dayawa suka zo harda daliban wasu makarantu, abun ya kayatar inda Janan ta tashi tayi bayani akan *Mutuwa DA KWANCIYAR KABARI* cike da kwarewa cikin harshen turanci!
Sosai Jawabin ta ya taba Zukatan masu sauraro!! Bayan kammala taron aka nadata a matsayin *Ameerah* ta Kungiyar!!

Abubuwa sun ma Janan yawa sbd Jarabarwar su ta matso ga kuma Da’awah da suke yi!! Cikin Hukunci Ubangiji suka kammala Jarabawan su, wannan karon Dad din Zarah (Annabelle) ya turo musu da kudi suka biyo jirgi suka dawo Abuja, driver’n su Zarah ne ya dauko su daga Airport, seda aka kai Janan sannan suka wuce!!!!

_Rukkybae_馃槒馃槒馃槒
[12/28/2017, 8:52 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: RukkyBae馃槒 馃槒馃槒鉂b潱: 鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾モ櫊鈾モ櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鉂も櫊鈾b潳鈾モ櫊馃枻鈾b櫏鉂も櫍鉂も櫏鈾p煐も潳鈾p煐も櫊馃枻鉂も櫍鈾ヰ煐も櫊鈾ヰ煐も櫍鈾狆煐も櫍鈾モ櫏鈾b櫊鈾�

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_*鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Sallah na da haske me girma, tana haskaka zukatan masu yinta, idan ka tashi dan yin sallah, seka kakkabe zuciyar ka daga duniya da abunda ke cikinta kuma ka shagaltu da ganawa da Ubangijin ka! Kada ka bari shedan yayi wasa da zuciyar ka…!!_

        1鈨�1鈨�7鈨�

Gaba daya yanzu Dr. Godwin ba shida lokaci sbd ayyuka sun mishi yawa har baya samun time din kanshi sbd duba marasa lafiya, kullum se dare yake dawowa gida…. Tun Momma na damuwa har ta dena dan ta fara sabawa da hakan!

      Da zaran lokacin sallah yayi Annabelle (Zarah) zata sulale jiki ta faki idon su Dad ta shige dakin ta ta rufe da makulli sannan tayi sallan ta!

Yau kusan kwanaki 3 kenan bata samun lamban Janan, ta damu sosai dama Janan din ce ke yawan tashin ta sallan asuba sbd karta makara.. Parlor ta fita tana zuwa ta tarar da Momma da Dad sunyi ankon kaya ta kalle su tace  “Morning Momma, morning Dad bata jira sun amsa mata ba tace ina zaku je?

Kallon ta kawai suke yi tunda ta fito cike da mamaki ganin ta da kayan bacci sannan kuma tana tambayan su inda zasu je!
Dad yace  “Princess kar dai kice min kin manta yau Sunday, dan naga ko alaman shirin zuwa Church ba kiyi ba”

Kai ta dafe tana fadin  ”na manta yau Sunday fa!

Momma tace “toh kije ki shirya da sauri se mu tafi ko kuma driver ya kawo ki dan zaki iya bata mana lokaci”

Gaban ta ne ya fadi tace  “Momma yau ba zan iya bin ku ba cuz bana jin zuwa Church yau, em nt in a good mood, sbd yau kusan 3 days kenan ba muyi waya da Bestie ba kuma ina ji a jiki na ba lafiya so se kun dawo ni se driver ya kaini gidan su inna gama”

Tunda Annabelle ta dawo hutun nan suka kasa gane kanta kwata kwata bata san zuwa Church duk sanda za a je tana da excuse din da zata bada!

Ki bari in mun dawo se muje gidan su Bestie din taki, mu ga iyayen ta kuma mu san ko tana lfya cuz yanda kika damu da wannan frnd din taki abun yanada daure kai!

Duka su biyun ta hada ta rungume tana jin wani irin son su na ratsa ta, tace  “I love u Both,  se kun dawo”
Ta ruga dakin ta da gudu su kuma suka wuce abun su, ko ta kan Godwin basu bi ba dan sun san halin shi baya zuwa Church!!

Bacci ta koma, se can da aka idar da sallan Azahar ta iya tashi, agogon dake manne a dakin ta kalla cikin hanzari ta mike tana fadin “Subhannallah”
Bayi ta shiga tayi wanka sannan ta dauro alwala, wardrobe din ta ta bude ta fito da kayan ta masu kyau ta saka tare da fesa turaren ta me kamshi, Darduma ta shimfida ta dakko dogon Hijjab da socks ta saka sannan ta tayar da sallah tana me farin ciki, zuciyar ta cike da nishadi!
Tana raka’an karshe taji alaman an shigo dakin dan yau bata kulle ba tunda su Momma basa gida, gaban ta ne ya dinga faduwa amma haka ta kara maida hankali kan sallan ta, tana idarwa ta waiga dan taga waye! Dr. Godwin ta gani tsaye ya harde hannuwan shi a kirji yana kallon ta, ido ta zaro waje tare da dafe kirjin ta, bakin ta na rawa tana shirin mishi magana suka jiyo muryan su Momma alaman sun dawo, da sauri ta cire Hijjab din tare da tura shi cikin drawer tana waigowa taga Momma a tsaye a kofan dakin tana musu kallo me nuna alaman lafiya?
Da kafa Annabelle (Zarah) ta dinga jan darduman har seda ta tura karkashin gado! Wayancewa tayi da fadin  “Momma sannun ku da zuwa ina Dad?
A haka ta samu ta janye ta zuwa parlor Dr. Godwin na biye da su!

Abincin rana suke ci amma duk ta tsargu dan data dago za su hada ido da Dr. Godwin, gani take yi kamar ze fadawa su Momma! Ya gane abun da take nufi dan haka suna sake hada ido yayi mata murmushi tare da girgiza kai! Se a sannan hankalin ta yadan kwanta!
Suna gamawa suka dan taba hira, nan ta kara musu tuni akan zuwa gidan su Janan!! Dr. Godwin yaji yau yana son ganin kawar Lil Sis din shi dan haka ya dau aniyar bin su!

Se da aka yi sallan Isha’i sannan suka shiraya tafiya, Godwin wasu carton brown half kaftan ya saka, yayi kyau sosai, Zarah tayi mamakin jin Yayan ta ze bisu!

A tare suka fito, motar shi yace suyi anfanin da ita, Momma da Zarah suka shiga baya, Dad ya zauna a gaba, Dr. Godwin ya ja motan suka tafi!!!

Kwatance Zarah ta dinga yi mishi har suka kai bakin kofan gidan, parking suka yi tare da gaisawa da Mai gadi, yana ganin Annabelle (Zarah) ya gane ta da sauri yace su shigo, kin shiga suka yi Dad yace  “Princess je ki fadawa mutanen gidan tare muke dan kar mu shigan musu gida ba tare da izinin su ba”

Tace ”OK Dad” sannan tayi shigewar ta!

A parlor ta tarar dasu Ummiey da wasu dattijai 2 amma Janan bata parlor’n, har kasa ta duka ta gaida su tare da fada musu dasu Dad suke, Nan Abbiey yace  “aa, ya suka tsaya a waje? Je ki shigo da su! Da sauri ta fita tace musu su shigo!
Gaban Dr. Godwin se faduwa yake amma ya rasa dalilin hakan!

A tare suka shiga parlor’n, dai dai Janan ta fito daga dakin ta!

Wani irin abune ya gilma musu kamar walkiya, Dr. Godwin yace *JANAN!!* tare da nuna ta, Be gama Mamaki ba yaji ance  *SHRUIEM!!* yana juyawa yaga daya daga cikin dattijan ke mishi magana, Dr. Godwin yace *BABA LIMAN!!*

Abbiey ya kalli Dad tare da fadin *MR. AHMAD!!*

Dad yace  *BARRISTER PHAROUK MAKARFI!!*

Ummiey ta kalli MOMMA tace *HAJIA HALEEMAH!!!*

Momma kuma tace  *HAJIA NANA!!*

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[12/31/2017, 12:17 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [12/28, 8:54 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱:  鉂ゐ煐も櫍鈾モ櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾モ櫊鈾モ櫏鈾b櫏 *MATAR DOCTOR* 鉂も櫊鈾b潳鈾モ櫊馃枻鈾b櫏鉂も櫍鉂も櫏鈾p煐も潳鈾p煐も櫊馃枻鉂も櫍鈾ヰ煐も櫊鈾ヰ煐も櫍鈾狆煐も櫍鈾モ櫏鈾b櫊鈾�

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_*鉁嶐煆烩湇馃徎

_Wannan Shafin naku ne gabaki dayan ku Makaranta kuma Masoya littafin MATAR DOCTOR!! Ina godia da kulawar ku da soyayyar ku a gare ni!! Ina gaishe ku tare da muku fatan alkhairi a duk in da kuke!! Allah ya kara mana son juna!!…._

       

            1鈨�1鈨�8鈨�

Gaba dayan su sun zama confused se kallon kallo suke yi a tsakanin su! Abbiey ne yayi karfin halin samun kujera ya zauna, su Momma suma suka zauna, Dr. Godwin da Janan kuma suna tsaye kamar an dasa su!!

Shiru ya ratsa dakin se T.V kadai ke aiki, fuskan Dad aka nuno a alon TV yana preaching a Church! Tambaya da mamaki ne a fuskan Abbiey, Ummiey da Baba Liman! Se yanzu suka lura Momma ko Dankwali babu akan ta!

Abbiey yace “Mr&Mrs Ahmad??

Dad ya gane Abbiey na neman karin bayani ne!

Shiru ya dan yi se ga hawaye suna fita daga idon shi, ganin haka yasa su Janan suka zauna dan abun da mamaki Babban Mutum kamar Dad yana zubda hawaye!

Dai dai lokacin Yaya Khaleel da Yaya Saleem suka shigo!
Abbiey ya musu nuni da su zauna!

Godwin, Annabelle yau zaku san abunda baku sani ba, gara kai Godwin zaka iya tuno wasu abubuwan!! Dad yace

  
       *TUSHEN LABARI!!*

Asalin su Dad yan garin Sokoto ne, sunan Mahaifin su Malam Shureim, su biyu kadai iyayen su suka haifa Dad (Ahmad) da Yayan shi Hamza! Sun yi karatun primary da secondary duk a nan Sokoto, mahaifin su ya rasu da shekara daya da rabi Mahaifiyar su itama ta rasu, sun yi kuka har suka dangana, lokacin Dad yana Ss2, shi kuma Yayan shi ya fara zuwa Jami’ar Dan Fodio, yau dadi gobe ba dadi a haka Dad ya fara aikin kanikanci, da haka ya samu ya biya kudin WAEC da NECO harda Jamb, cikin sa’a ya samu ya ci komai inda ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria ya karanta Geography, kwata kwata Yayan shi be cika damuwa da shi ba, da kyar da wahala ya samu yake karatun nan, ana haka kudin Baban su na Pension ya fito
Da yake lokacin kudi na da daraja se suka dan samu da tsoka, ya kira Dad ya fada mishi kudin Baban su ya fito, yaji dadi dan ya san ko ba komai ze huta da wahala, ba abunda ya sauya daga rashin kulan da Yayan shi ke mishi, haka ya samu ya kammala karatun shi cike da nasara, a lokacin Yayan shi ya yi aure suka zauna a gidan su da Baban ya bar musu, tun lokacin Dad yace a raba gado aba kowa nashi sbd yana so ya fara kasuwan ci amma Yayan shi ya ki yarda, babu yanda Dad ya iya haka ya kyale shi, wani dan mokocin su dake zuwa Lagos saro kaya ya fara bi suna siyo kayan tare ana bashi lada…

Kudin ya dinga tarawa har shima ya fara saida takalma, cikin hukuncin Allah ya hadu da Haleema (Momma) lokacin yaje Kano saro takalma, sun shaku da juna har suka yi aure, bayan da kyar Yayan shi ya yarda!

Tun bayan auren su da Momma yake samun budi amma basu samu haihuwa ba, cinikin takalma ya habbaka da haka ya koma Lagos, ganin yana ciniki kuma Alhamdulillah yana da rufin asiri yasa shi be nema aiki ba, lokacin daya zo Sokoto dan duba Yayan shi se yake ce mishi  “Ahmad yanzu baka son zuwa garin nan kuma ka san bani da kowa se kai amma ka kyale ni a nan, me yasa nima ba zaka samamin wuri a can ba in dawo kusa da kai!

Ba haka Dad yaso ba amma daya fadawa Momma ta dinga murna tace ai ba komai gara su zauna kusa da shi!

Bayan ya dawo ya neman mishi wani gida ba nisa tsakanin su, tunda ya dawo Dad ke dawainiya dashi!

Wani abokin kasuwancin shi yace  “Malam Ahmad me yasa ba zaka sa kudin a hannun jari ba? Ana samun riba sosai da sosai fa!

Maganan abokin kasuwan cin shi ya tsaya mishi a rai dan haka ya fada wa Momma komai ita kuma ta bashi shawara ya fada wa Yayan shi Hamza!

Bayan ya fada mishi komai da irin riban da zasu samu se yace  “toh ai wannan cigaba ne a gare mu baki daya ka bari kudin gadon mu se in sa mana a ciki ko ya ka gani?

Ba tare da wani tunani ba ya yarda da shawaran Yayan nashi!

Duk wani shige da ficen kudin ta hannun Yaya Hamza yake fita, a haka har abun ya bunkasa ya gina haddaden gida!

Duk Dad be ce komai sbd hakuri da kawaici, a haka kasuwancin shi ya fara kasa ga Momma da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, duk ya fita hayyacin shi tun yana daurewa har ya fara sarewa, wajen Yayan shi yaje akan ya bashi rance a kudin su amma ya rufe ido yayi mishi kacakaca! Jiki a sanyaye ya dawo gida, Momma ta lura mijin ta baya cikin kwanciyar hankali ga nakuda ta fara, a haka ta dinga kokarin kwantar mishi da hankali! Washe gari yana shirin tafiya kasuwa yaga tana cije cije, tambayan ta yayi ko lfya amma tace ba komai, haka ya shirya ya fita ko nisa be yiba faya ta fashe, mantuwa yayi dan haka da sauri ya dawo gida, yana shigowa ya ganta a wannan halin ga wani ruwa dake bin kafafun ta, cikin hanzari ya fita ya nemo me taxi ya kwashe ta se asibiti! Labor room aka wuce da ita, bada dadewa Nurse ta fito tana tambayan kayan haihuwa dan ta kusa sauka, shi gaba daya ma ya rude ya manta da wani abu wai kayan haihuwa dan haka da sauri ya koma ya kwaso dan tun cikin be yi kwari ba yake siyo kayan haihuwa!

Bayan mintuna 30 aka mishi albishir da ta haifi dan ta namiji! Yayi farin ciki sosai, da Baby da Maman duk suna cikin koshin lfya! Kwanaki 2 bayan haka aka sallame su, nan ya sa ma yaro sunan Baban shi marigayi (Shureim) suna kiran shi da Baba!

    Haihuwan Baba ya sa sun samu alkhairi dayawa daga wajen mutane ta fanni daban daban! A haka suka cigaba da manajin rayuwa har Baba ya fara zuwa makaranta, kuma Momma bata kara haihuwa ba!!
    Ganin alamura sun kara kasa yasa Dad komawa wajen Yayan shi kan kudin gadon shi, wannan karan ma rashin mutunci ya sake mishi dan haka Dad yace  “ba zan yarda ka danne min hakki na ba shekara da shekaru dan haka kotu ce zata raba mu! Fuu ya fita daga gidan, abunka da wanda be iya fushi ba, da barin gidan Yayan shi kotu ya tafi ya kai kara nan aka hada shi da Barrister Pharouk Makarfi (Abbiey)! Be boye mishi komai ba tun daga tasowan su har zuwa yanzu!

Daya koma gida ya ba Momma lbr bata ji dadin haka amma ta mishi fatan alkhairi!

   Sammaci aka aikawa Yaya Hamza, abun yazo mishi a ba zata dan haka ya dinga bala’i daga karshe shima ya nemo lawyer!

     Bayan zama da hujjoji masu yawa su Abbiey suka cinye shari’a kuma a take a kotu Alkali yasa aka raba kudin kowa aka bashi!

  Dad yayi farin ciki tare da godia ga Allah, bayan barin su kotu ya ciro kudi masu yawa ya ba Abbiey amma yace shi ba zai karba, Dan Allah ya taimake shi!

Tun daga lokacin suka kulla alaka suka zama tamkar yan uwa!
    Haka Momma (Haleema) da Ummiey (Nana Khadeeja) suka zama kawaye! Har hutu Shrueim na zuwa yi a gidan da yake sa’anni suke da Saleem!

   Tamfatsetsen gida Dad ya gina suka koma ciki, ya hada walima dan godema Allah! Har gidan Yayan shi ya zo yace  “kada ka kuskura ka nuna ni a matsayin dan uwanka kuma duk abunda ya same ka kada ka sake kazo inda nake, bani ba kai! Ya fice daga gidan!

Abun ya dade yana damun Dad tare da mamakin hali irin na Yayan shi!!

Hannun jari ya cigaba da zubawa kafin ya samu sana’an yi!

  Ya dade yana tunanin abunda ze yi ya saka ma Abbiey amma ya rasa dan haka ya biya ma dukkan su kudin aikin Hajji, Ummiey da Abbiey sun yi farin ciki dan haka aka kai su Shrueim, Khaleel da Saleem Makarfi kafin su dawo!!

    
          
           鈾�

Bayan dawowan su da wata 3 aka ma Abbiey canjin wajen aiki! Harda su Dad suka je suka ga sabon gidan da su Abbiey suka koma! Lokaci zuwa Lokaci suna ziyartan junan su!

Bayan Shekaru 9 Momma ta samu ciki, sun yi murna sosai!
     Dad ganin yayi karfi a cikin hannun jari yasa shi janyewa, gaba daya kudaden shi ya kwaso dan yana so ya fara business a Dubai, a daren ranan yan fashi suka duro gidan tare da kwashe duka kudin sannan suka cinnawa gidan wuta, Allah yayi da sauran rayuwa a tare da su Dad suka fito a guje, Shureim yana hannun Dad!

Wani kongo suka samu suka rakube dan basu san inda suka dosa ba! A haka suka kwana su tashi a cikin kongon nan, ba suda abinci se gari, haka Dad ze fita nemo musu abunda za su ci amma baya samu, Haka Shureim shima ze fita yana dako duk da kankancin shekarun shi!

Wani dare hadari ya hadu a take aka fara ruwa! A nan nakuda ya turnuke Momma duk inda suka je a taimaka musu babu wanda ke kallon su, a haka ya samu ya nemo me mota suka kaita asibiti (labarin baya da Dr. Godwin ya ba Janan a ranan birthday din su kan dalilin da yasa ya tsani kalman taimako)

       Tana labour Dad ya fito haraban asibitin nan aka bashi lbrn an tafi da dan shi police station! Ya shiga rudu ya ma rasa ta ina ze fara, kongon da suke kwana ya koma ya hada kai da gwiwa yana kuka! Horn din mota ya dinga ji amma be damu daya dago ba, ji yayi an dafa shi da sauri ya dago fuska yana kallon su, wasu mutane ne guda 2 sanye da coat, daya yace  “da gani kana cikin matsala, toh kada ka damu mu zamu taimake ke amma idan muka taimake ka zaka mana duk abunda muke so”

Cikin muryan kuka yace  ” wani abu kuke so in muku?

“zamu fada maka amma yanzu kai ka fara fada mana damuwar ka mu nan masu taimako ne!

“gida na ya kone, matata tana asibiti tana nakuda, ba nida kudin da zan biya asibiti, ‘Dana yana police station wajen en sanda, ta ina zaku fara taimaka min?

Kallon juna suka yi tare da murmushi, motar suka koma suka ce ya biyo su! Babu musu ya bi su! Wani gida me kyau suka kai shi tare da fadin   “ga sabon gida nan mun baka, wani brief case suka miko mishi, wannan kudi ne ka je ka yi settling bills dinka na asibiti kuma ka yi bailing yaron ka, nan da sati daya zamu dawo kuma lokacin zamu fada maka abunda muke so”

Dad ya dinga godia yana kuka! A haka suka wuce suka barshi!

Se da yayi bailing Shureim sannan suka biya komai na asibiti tare da dawowa sabon gidan su! Momma tayi mamaki kan sauyin da suka samu dan haka ta dinga tambayan shi yanda aka yi, be boye mata komai ba ya fada mata! Ita dai jikin ta be yarda da mutanen ba amma haka tayi shiru!

Kamar yanda suka fada sati na zagayowa suka zo gidan! A parlor suka zauna bayan sun huta suka ce  “Mr. Ahmad kamar yanda muka yi da kai yau zaka cika mana alkawarin mu!
Dad da Momma suka kalli juna! Dad yace “ina jin ku, ku fadi abunda kuke so!

” So muke ka bar addinin ka ka koma addinin mu na Christian!!

Wani irin mikewa Dad da Momma suka yi lokaci guda suna fadin ”What!!

Suka ce “Calm down, ai deal muka hada dan haka babu ja da baya!

Zuciyar Dad na tafarfasa ya ce “ba zan taba barin addini na ba, duk abunda kuka bani zan dawo muku dashi nan da sati daya nima!

Murmushi suka yi sannan suka tashi tsaye ” OK nan da sati daya idan muka dawo baka biya mu komai namu ba baka da wani option illa ka dawo addinin mu! Da haka suka bar gidan!

Momma tayi kuka kamar ranta ze fita, haka ma Dad ya shiga tashin hankalin da be taba shiga ba!

Duk inda ya san ze samu kudi yabi amma be samu ba gashi saura kwana 2 sati daya ta cika dan haka ya yanke shawara ya tafi garin da aka maida Abbiey dan tun kafin suyi gobara yaje shida su Momma! Yana zuwa yaji labarin an canza ma Abbiey wajen aiki kuma suma basu san inda ya koma ba!
Tun a hanya yake kuka da dana sani har ya iso gida!
Tunda ya fadawa Momma be samu su Abbiey take ta faman kuka! Kullum ba suda aiki se kuka! A haka har satin ya zagayo, mutanen suka dawo, su Dad ba suda mafita face suka koma addinin kiristanci! Inda Momma daga *Haleema* ta koma *Lidia*
Dad daga *Ahmad* ya koma *Williams*
*Shuruiem* ya koma *Godwin*
Ita kuma jaririya aka sa mata *Annabelle*!!

Sosai suke daukan dawainiyar mu ga kudi da ake sake mana, a haka har muka fara zuwa Church nan aka yanke shawaran a bani Babban Pastor a Cocin sbd kar ma in samu hanyar barin addinin!!!!…..

Dad ya karasa labarin yana gunjin kuka!!!

Kowa a dakin kuka yake sbd labarin akwai tausayi da daga hankali! Abbiey cikin kuka yace “nima nazo Lagos yafi so a kirga ina neman ka amma na kasa samun ka ashe abunda ya faru kenan” ya karasa maganan yana kuka!

Nan Dr.Godwin yace nima ina da labarin da zan bada!!!

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[1/2, 10:06 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/2, 5:57 PM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鉂ゐ煐も櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫏鈾犫櫍鈾モ櫍 *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫏馃枻鈾b櫏鈾ヰ煐も櫍鈾犫櫏鈾モ櫍鈾犫櫏馃枻鈾モ櫏鈾モ櫏鈾p煐ゐ煐も櫏鈾�

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW*
鉁嶐煆烩湇馃徎 _Hakuri Da Juriya Online Writers_鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Musulunci shine mika wuya ga Allah da kadai tashi tare da yi Mishi biyayya da bauta Mishi!_

          1鈨�1鈨�9鈨�

Dr.Godwin ya fara magana “tun lokacin da naji Dad ya canza min suna na tsani sunan, lokacin shekaru na ba suda yawa amma ina da wayau sosai, tun lokacin na lura mun dena zuwa masallaci se Church, kafin a cire ni a islamiya Malamin mu yana mana waazi tare nuna mana addinin Musulunci shine addinin gaskiya sannan babu inda yafi dacewa ayi ibada se masallaci, wannan dalilin yasa bana bin su Momma Church!

A haka har na gama karatuna na samu aiki a Kaduna, anan na hadu da Janan, ita ta fara nuna min tare da koya min sannin darajan Mutum, dabi’un ta da yanayin rayuwar ta yasa na fara kwadayin nima in kama addini guda daya, lokacin da muka je Seminar da aka bude Babban asibiti a Makarfi, a nan na hadu da Baba Liman, muna da wajen kwana amma yace me ze hana in sauka a gidan shi!
Tunda na zauna a gidan suke girmama ni da darajta ni, so da dama idan yana ma mutane karatu tare da fada musu hukunce hukunce a Musulunci na kan saurara, na lura akwai rikon addini a gidan Baba Liman kuma ba sa nuna kyama ga wanda ba Musulmi ba!

A haka na fara tuno maganganun Janan, ji nayi ina son nima in koma Musulunci!
   Ana saura kwanaki 2 mu gama Seminar din mu naje na samu Baba Liman na fada mishi ina so in koma Musulunci, yayi farin ciki da jin haka! Ni nace a maida min sunan na farko wato SHUREIM!!

Tunda na shiga Musulunci nake karo da abubuwan alkhairi tare da cin nasara a duk abunda nasa agaba, kuma a lokacin ne nayiwa Yar Mataimakin Gwamna Plastic Surgery!

Ko san da na bar aiki na dawo gida naga su Momma still suna cikin addinin dana barsu ciki, nayi bakin ciki na so in fada musu na canza addini amma na san hankalin su ze tashi shiyasa ban sanar da su ba se dai na cigaba da musu addua’a Allah ya ganar dasu gaskiya !!!

Maganar shi ta kashe musu jiki sosai! Janan murna da farin ciki take yi sosai tare da godia ga Allah!

Zarah ita ma ta basu labarin komai da yanda ta Musulunta!

     Dad yace  “a yau zamu bar wannan addinin ‘bata, kuma duk abunda na samu a cikin addinin zan barsu domin in yi kyakyawan tuba! Kuma ina rokon Allah ya yafe min duk zunubai na, Lallai munyi babban asara! Ya karasa maganan cikin kuka!

Dad da Momma kuka suke yi kamar za su shide, kowa na wajen jikin shi ya mutu ga tausayin su Dad na halin da suka shiga!

Baba Liman yayi gyran murya sannan ya fara da fadin  “Yabo da godiya sun tabbata ga Allah, abubuwa sun faru wanda dama kaddara ce kuma yana nan a rubuce a cikin littafin kowannen mu, bamu isa mu canza abunda Allah ya tsara ba!  Saboda haka mu gode mishi da har yasa baku mutu a cikin wannan addinin ba!

Nan suka karbi kalman shahada!
Kabbara kawai ke tashi a parlor’n! Se da suka ci abinci suka koshi sannan suka tafi cike da farin ciki mara misaltuwa!

Suna komawa gida suka yi wankan shiga addinin Musulunci! Se a lokacin suka samu natsuwa da kwaniyar hankalin da suka rasa na shekaru masu yawa!

             鈾�

Dr. Shureim sun kara fahimtan juna shi da Janan din shi, ga wani zumunci me karfi daya kara shiga tsakanin gidaje biyun!

Ya tambaye ta dalilin da yasa aka fasa auren ta da Imran! Bata boye ba ta fada mishi komai!

Wani irin soyayya ta ban mamaki ya kara shiga tsakanin su, magana tayi karfi dan har iyayen su sun san komai!

A haka hutun su ya kare suka koma sch inda a yanzu suke 300 lvl! Sosai Dr. Na kula da ita dan duk karshen sati se ya je sch din su ziyara!

         *******

Tunda suke hanya za su dawo daki daga lectures Zarah take waya har se da suka shiga daki sannan ta ajiye wayan, Janan tace  “Sis wai ke dawa kike waya tun dazu ne?

Zarah tace “Ni da Bro Saleem ne mana!

Janan tace “uhum! Ni fa ban gane tsakanin ku da Yaya Saleem ba, naga kuna wani mannewa ne kaman chewing gum!

“Bestie sa ido fa ba kyau! Me kike tunani toh!

“A! Ni ba ruwa na, nawa ido ne! In tayi wari ma ji!
Suka yi daria!

Duk wani abu da Dad yasan ta hanyan haram ya same su ya fitar ya maida musu Church harda takardun gidajen daya siya tare da tabbatar mu su ya bar addinin su ya koma Musulunci!

Sun yi bakin ciki tare da cewa za su bashi ninkin kudin da ya dawo da shi!

Dad yace  “ni yanzu ba wannan bane a Gaba na, ina so in gyara kurakuran da nayi kuma in ma addini na hidima! Ya fice daga cocin!
    
Gidan su Ummiey ya je ya samu Momma, nan yake fada musu yanda suka yi, bayan Ummiey ta tashi yace ma Momma “Yanzu ina kike ganin zamu koma? Ba ni da komai daga mu se rigunan jikin mu!

Kusa dashi ta koma tare da kamo hannun shi tace  “kada ka damu, Allah zai ba mu yanda za muyi!

Can yamma Dr. Shureim ya shigo gidan su Ummiey, bayan sun gaisa yace “Ummiey, Momma, Abbiey da Dad, ina so in roki alfarma a wajen ku, zamu je wani waje ne Gaba dayan mu!

Basu musa ba suka shiraya, a motan shi suka fita!

Kofan wani hadadden gida suka tsaya, gaba dayan suka fito yace su shiga! Komai yaji a gidan dan an tsara shi seda suka gama duba ko ina suka dawo parlor suka zauna!

Gaban su Momma da Dad yaje ya durkusa tare da ruko hannun su! Makulli ya sa musu a cikin hannun tare da fadin “wannan shine gidan ku, ina fatan zaku so shi kuma yayi muku!
A tare suka rungume shi suna sa mishi albarka!
Dadi ya dinga ji saboda ya faranta musu rai! Nan su Ummiey suka mishi godia!

            鈾�

       Haduwa akayi bayan dogon nazari da lura aka sa auren Janan da Shureim, Saleem da Zarah, Khaleel da Hameeda sister’n Imran! Shi kuma Imran aka hada zumunci da Zee inda se da akayi da gaske ta yarda wai kar Janan tayi tunani zata ci amanarta!

   

        Anyi hidima sosai tare da komai cikin tsari, duk da suna da kudi hakan be sa sun yi almubazzaranci ba!

Daurin auren su ya tara jama’a masu yawa inda aka daura auren Janan da Shureim, Saleem da Zarah akan sadaki mafi karanci dan auren yayi albarka! Angwaye sun sha akon cikin manyan fararen kaya!

Ana gama daurawa aka tafi Kaduna aka daura na Khaleel da Hameeda! Shi kuma Imran da Zainab!

Walima, Kamu da Dinner kadai akayi! Amare suka tare a gidajen su!!!

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒
[1/11, 10:50 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: [1/8, 10:29 AM] RukkyBae馃槒馃槒馃槒鉂b潱: 鈾モ潳鉂ゐ煐も櫍鈾犫櫏鈾b櫍鈾モ櫏鈾犫櫍鈾モ櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾b櫊鈾b櫏鈾モ櫍鈾b櫊鈾モ櫏鈾モ櫍鈾b櫊鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫏鈾� *MATAR DOCTOR* 鈾犫櫍鈾b櫊鈾b櫍鈾b櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫏鈾b櫊鈾モ櫍鈾犫櫍鈾モ櫏鈾b櫊

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

馃寪 *HAJOW* 馃寪
鉁嶐煆烩湇馃徎 *_Hakuri Da Juriya Online Writers_* 鉁嶐煆烩湇馃徎鉁嶐煆�

_Alhamdulillah!_
           鈾�
_Alhamdulillah!!_
            馃枻
_Alhamdulillah!!!_
           鈾�

鈾� *_LAST PAGE_* 馃枻

            1鈨�2鈨�0鈨�

Da sallama Dr. Shureim ya shigo dakin Amaryar sa, zaune ya tadda ita a kan gado an nade jikin ta da Lapaya, a hankali ya karasa tare da ajiye ledojin hannun shi!
Gadon ya hau tare da bude mata fuska!  Ido ta runtse sbd kunyar da take ji! Murmushi yayi yana fadin  “Alhamdulillah! Nagode da Allah ya nuna min wannan rana wacce ba zan taba mantawa da ita ba, yau babban buri na ya cika, ina rokon Allah ya bani ikon kula dake tare da kare miki dukkan hakkin ki dake kaina, sannan ina neman alfarmar ki da kiyi  hakuri da duk wani laifi da zan miki cikin sani ko akasin haka domin shi Dan Adam ajizi ne! Allah ya bamu hakurin zama da juna cikin so, kauna, rikon amana, gaskiya da kuma juriya!

Tun da ya fara maganan bata ce komai ba kuma bata dago ta kalle shi, ji tayi wani irin son mijin ta na ratsa dukkan sassan jikin ta ga kuma girman shi da a yau taji ya kara nunkuwa a zuciyar ta!

Ganin bata yi magana ba yasa shi tashi tare da cire malum_malum din shi sannan ya mika mata hannu alaman tazo! Cike da jin kunya ta rarrafo a hankali sannan ta mika mishi hannu, mikar da ita tsaye yayi sannan ya riko ta ta gefe suka wuce toilet! Alwala suka yi sannan suka fito! Da sauri Janan ta nufi akwatunan ta dake gefe ta ciro darduma guda 2 se dagon Hijjab da socks! Daya ta shimfida mishi sannan itama ta shimfida nata a baya, seda ya jira ta saka socks din sannan ya tada sallan!

A nutse tare da kaskantar da kai yake jan su sallan! Rakao’i biyu suka yi sannan ya sallame! Juyowa yayi yana kallon ta dai dai ta dago ido ya sakar mata murmushi, itama murmushin tayi, har gaban ta ya matsa sannan ya mika hannu ya daura a saman kanta, adduo’i ya dinga jerowa sannan yayi mata tambayoyi akan addinin ta, duk da ya san tana da ilimin amma yana so ya kara tunatar da ita, bayan ta amsa mishi ya umurce ta itama ta tambaye shi!

Tayi mamakin yanda ya dinga bata amsa ba tare da kuskure ba! Shi da kanshi ya dakko plate da cups ya zuba musu Holandia da gasasshiyar kaza! Da kyar ta iya ci sbd kunya danma shi ya dinga bata har suka koshi, tare suka nufa kitchen ta wanke kayan shi kuma ya dauraye ya maida su in da suka sannan suka koma daki, toilet suka shiga suka yi brush!. Gado suka hau tare da yin addua’a! Sun bautawa Allah tare da raya sunan Manzo Allah SAW a daren!

Haka zaman su ya dinga tafiya cike da so da kaunan juna gashi dama Dr. An bashi hutun, babu inda yake zuwa suna tare kullum se dai in ya tafi masallaci sallah!     
   Tare suke wanka, gyaran daki, shara, wanke_wanke da girki, komai tare suke yi hatta wanki da guga su suke yi da kan su!

         Yau ta kama Weekend, bayan Dr. Shureim ya dawo daga sallan azahar suka shiraya suka nufi gidan su Momma, a nan suka tadda Abbiey da Ummiey, Janan taji dadi sosai dan tun bayan bikin su bata kara ganin su ba se dai suyi waya! Dr. Shureim ya duka har kasa ya gaida su sannan ya gaida su Momma!

Momma da kanta ta tashi ta debo musu dambun nama da juice, su na ta hiran su, Janan da Dr. Shureim kuwa suna ta faman kallon juna suna murmushi, ana haka Zarah da Yaya Saleem suka shigo!
Wani irin ihu Zarah tayi tare da fadowa kan Janan se gasu sun zube a kasa Dr. Shureim yace “ke miye haka? Kada ki karya ta mana! Ya tashi daga inda yake ya dago Janan yana fadin sorry Darling” gaba daya ya manta da su Ummiey a wajen ita ko Janan tayi kasa kasa da murya tace “ga fa su Momma a zauna kar suce ba muda kunya”
Kai ya dan sosa sannan ya mika hannu suka gaisa da Yaya Saleem!

Gefe Zarah taja Janan suka dinga hiran su, Mai Gadi yayi sallama daga waje, suka amsa Dr. Shureim ya tashi yaje yace “Ya dai?

Ina wuni Likita bokan turai? Be jira ya amsa ba ya cigaba da fadin, wasu Mutane ne su biyu suka zo wai suna neman Alhaji, dayan ma a keken guragu aka turo shi, shine suka ce in musu iso”

Kace su shigo! Watakila suna neman taimako ne!

(Tun bayan abunda ya faru da Dad yayi alkawarin taimaka wa duk wanda ba shida karfi! Gaba daya Dr. Shureim ya dauke nauyi su kuma duk wata yana turo musu kudi)

Dr. Shureim ya koma ciki ya fadawa Dad, sannan ya zauna!

Sallama aka yi tare da daga labulen! Zunbur Dad ya mike yana kallon su haka ma Momma, a hankali aka dinga turo wheel chair din har gaban Dad sannan suka tsaya!
Kallon su kawai Dad yake yi amma ya kasa magana dan ya rasa abunda ze ce be gane na tsayen ba amma ya gane na kan kujeran guragun!
Momma tayi karfin halin fadin  “Yaya Hamza? Kaine? Kaine a haka? Kuka ya subuce mata ta koma ta zauna a kujera!
  Dad da idon shi suka yi ja yace “me yasa ka neme ni? Me yasa ka tuno kana da wani dan Uwa a duniyar nan?

     Yaya Hamza yace “Kayi hakuri Kanina, ka yafe min na san ban kyauta maka kuma ban yi maka adalci ba, na cutar da rayuwar ka, ni ne na turo yan fashi suka kwashe kudin ka sannan suka kona maka gida sbd ina so ka shiga wani hali.. Bayan na biya su an kwana biyu nima suka zo suka kwashe komai harda takardun gidaje na sannan suka min duka tare da karya min kafafu sanadin haka na zama gurgu! Kuka yaci karfin shi!
  Salati kawai Dad yake yi sbd yanda jikin shi ke rawa… Duk wanda ke parlor’n se da ya dauke wuta sbd jin abunda Yaya Hamza ya fada! Momma, Ummiey, Janan da Zarah kuka kawai suke yi!
Dr. Shureim dake zaune ya tako har inda yake, da ganin shi yana cikin bacin rai da bakin ciki.. Dai dai setin kafafun shi ya durkusa yace  “mun gode da abunda kayi mana kuma mun ji bayanin ka saboda haka ku tafi! Ya mike tsaye dan ya san in ya cigaba da magana ze iya fadan abunda be dace ba!
   Kwata kwata Dad ya kasa magana se kallo kawai yake bin Yayan nashi da shi yana jin wani irin daci a zuciyar shi wai yau ace Dan Uwanka Uwa daya Uba daya ke maka wannan hassadar tare da son ganin bayan ka? Me ya tsare mishi? Daga ya karbi hakkin shi shikenan! Oh Duniya ina zaki damu ne?

     Cikin dauriya da karfin hali ya bude baki yana fadin  ”Lallai kaci amanan iyayen mu, ka ci amanar zumunci, ka cuce ni ka cuci kan ka, ka zama silan fadawa ta halaka ni da iyali na, saboda haka ni bani da dan Uwa illa wannan bawan Allahn da ka gani zaune ya nuna Abbiey, kuma ba zan taba yafe maka ba sannan daga karshe ina baka shawaran ka fice min daga gida kafin in sa a maka koran wulakanci kuma in kira yan sanda! Sannan baka ga komai ba ma in dai alhaki ne yanzu ya fara binka! Tari ya sarke shi a nan ya fadi kasa, gabaki daya suka yo kanshi, jijjiga shi Momma ta dinga yi amma kamar ba shida rai!
Da gudu Dr. Shureim ya nufi motan shi ya dakko kayan aiki, yana zuwa ya fara dudduba shi nan ya gano jinin shi ne ya hau sosai! Ruwan sanyi ya sa Zarah ta dakko a fridge ya dinga shafa mishi, can Dad yayi ajiyar zuciya alamar ya farfado kenan! Waigawa yayi ya ga Yayan shi yana nan be tafi ba, sake runtse ido yayi yana son yin magana! Ganin haka yasa Abbiey tashi yaje har gaban Yayan yace  “kayi hakuri muje waje”
    Jiki a sanyaye Yaron shi ya ja keken suka fita Abbiey na bin su a baya! A tsakar gidan suka tsaya Abbiey ya karaso yace  “kayi hakuri da duk abunda ka gani, ka san dole abun ze mishi ciwo kuma ba zai iya furta ya yafe maka ba a cikin halin da yake ciki ba! Tas Abbiey ya kwashe duk abunda ya faru dasu Dad ya fadawa Yaya Hamza!
  Hankalin Yaya Hamza ya tashi sosai da sosai, wani irin nadama da dana sani suka saukar mishi! Wasu hawaye masu zafin gaske suke ta zubo mishi, Lallai ya san cewa yayi babban kuskuren da baya fatan sake maimaitawa! Jiki a sanyaye suka bar gidan!
    Gaba daya abunda ya faru ya dagula wa Dad lissafi, ya kasa mantawa, a haka Abbiey ya dinga mishi Nasiha yana fada mishi ladan da zai samu idan ya yafe ma Dan Uwan shi!
     Se da akayi sati sannan Dad ya hakura, tare da Abbiey suka je gidan da Yaya Hamza ke haya wanda gidan kamar na almajirai saboda lalacewa!
    Nan Dad ya tabbatar mishi da ya  yafe mishi, suka rungume juna! Suna kukan farin ciki! Washe gari ya sama mishi gida yace su dawo shida yaran shi, ya jibge musu kayan abinci, harda masu aiki guda biyu!

     In an samu hutu dukkan su suke tafiya Kano wajen Dangin Momma haka ma suna zuwa Sokoto wajen abokan arziki! Sosai Dad yake musu alkhairi!

     Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, duk bayan sati 2 sukan je gidan su Momma ko gidan su Ummiey! Hakanan suna zuwa gidan su Zarah ko kuma su su zo! Har gidan su Yaya Khaleel suna zuwa!
   Akwai randa suka shirya suka je gidan su Imran, sun ko ci saa yana gida, sosai yayi farin ciki da zuwan su! dr. Shureim da Dr. Imran suna ta hira ita kuma Zee da Janan suka shige daki suna nasu hiran! Se da yamma suka tafi cike da jin dadi!

    Tunda Da Dr. Shureim ya koma wajen aiki Janan ta zama tamkar marainiya, duk da idan ya samu sararin aiki suna waya sosai!
  Cikin haka har hutun su ya kare suka fara shirin komawa sch, dauriya kawai Doctor ke yi amma gaba daya ya rasa me ke mishi dadi!

Tare suka tafi da Yaya Saleem da Zarah! Ya Saleem ke tukin Zarah na zaune a gefen shi! Dr. Shureim su kuma suna zaune a baya shida Janan! Tana kwance a cinyan shi yana ta fama shafa kanta! Seda suka tsaya suka siya abinci, snacks da drinks sannan suka cigaba da tafiya! Suna zuwa sch din suka ce su jira su a mota, su suka musu duka reg din su! Dama Dr. Shureim yasa an kama musu wani 2 bedroom flat dan yace ba za su koma hostel ba, can suka nufa seda suka yi sallah sannan suka cinye sauran abincin! Dare nayi su Zarah suka dau daki daya su Janan ma suka dau Daya! Washe gari da safe suka shiga kasuwa suka siyo abubuwan da za su bukata! Se da yamma sannan su Dr. Suka shirya tafiya! Janan ta sha kuka kamar ranta ze fita haka ya dinga jin kukan har zuciyar shi ji yake kamar ya bude kirjin shi ya sata a ciki, da kyar ya samu tayi shiru da alkawarin duk sanda ya samu time ze dinga zuwa dubata! Zarah ma ta sha kuka amma ba kamar Janan ba! Har bakin mota suka raka su, wannan karon Dr. Shureim ne ze tuka! Sun tafi cike da kewan Matan su! Suma haka suka dinga kewan mazajen su!

               鈾�

          Shekaru sun ja sosai dan a yau ake yaye su Janan daga makaranta a matsayin Cikakkun Likitoci! Farin ciki kawai suke yi tare da godia ga Allah! An bata kyauta a matsayin wacce ta kafa tarihi a makarantan dan har kawo lokacin ba a dena MSS ba!

  

           Zarah na nan da Babyn ta haka ma Zee da Hameeda Matar Yaya Khaleel! Janan kam har yanzu Allah be bata ba! Cikin yan tsakanin nan aka yi Bikin Eeesher da saurayin ta Pharouk, Fatima da saurayin ta Dawud! Janan ta je musu duk da bata kwana ba amma an kai amare da ita!

    Babban asibiti Dr. Shureim ya gina inda ya dauki kwararrun Likitoci da Nurses har da Pharmacists! A cikin asibitin ya ginawa Zarah Pharmacy (dakin shan magani) dan be manta alkawarin daya mata tun tana karama! Karshen shekara yake so su fara aiki, an samu tsaiko ne wajen isowar kayan da yayi ordering daga India! Se kuma Dan gyare gyare da baya a rasa ba!

   A lokacin Janan ta samu ciki, laulayi take yi sosai gashi bata iya cin komai, gaba daya hankalin Dr. Shureim na kanta! Seda cikin ya shiga wata uku sannan ta rage laulayin se dai bata cin komai se Buredi da yaji se kuma tasha Bobo!

 
  Dawowan shi kenan daga duba asibitin shi ya ganta zaune akan kujera tana cin Buredi da yaji, har inda take ya karaso ya jingina da fuskan ta yace  ” kina nan kina cin abincin ki kenan! ya Baby na? Baki ta turo tace “tun kafin a haifi Baby har ka fara nuna son kai ko?
Kunnuwan shi biyu ya kama yana fadin “a yi Hakuri, ai se da na fara sanin Maman Baby kafin in san Babyn afterall ma Babyn is still unborn sbd haka ki kwantar da hankalin ki babu batun son kai!
Har dining ta kaishi yaci abinci seda ya gama sannan suka fara hira yana bata labarin yanda aikin asibitin ke tafiya! Sosai taji dadi tare da fatan alkhairi!!

    Cikin ikon Allah asibitin ya samu karbuwa dan ba sa cika kudi kuma suna iya bakin kokarin su wajen taimakon marasa karfi! A kusa da office din shi ya ginawa Janan nata office din dan har akwai ma kofa ta ciki da zai iya sada su da juna!
Yau ta samu marasa lfya sosai amma haka be sa ta gaji ba, wata ce ta shigo ta zauna! Dr. Janan na duba result din ta! Ji tayi an rufe mata ido da tafin hannu ta baya, murmushi tayi tare da fadin wanene?

   Yace  “chewing gum din ki ne! Haka take ce mishi idan tana son tsokanan shi!
   Hannu ya zura ya shafo cikin ta da ya fara girma yace “I missed u Both!
  Kafin Janan tayi magana suka ji an ce “Godwin? Cike da mamaki suka dago suna kallon me magana! Precious ce tsohuwar budurwar shi , kallon ta kawai Janan ke yi dan ba zata taba manta fuskarta ba se dai yanzu tayi baki ta rame!

Se da ya kalli fuska  Janan yaga ba bacin rai a tare da ita sannan ya kalli Precious yace “yanzu ba sunana Godwin ba sunan Shureim nd here is my Wifey! Ya ruko hannun Janan yana murzawa!
   Kuka kawai take yi se yanzu take da na sanin abunda ta dinga aikatawa ga shi yanzu tana dauke da chronic infection wanda watakila se an mata aiki ga kuma cancer’n mahaifa!
  Tace  “kayi hakuri, naso in cutar da kai amma ban yi nasara ba sbd kai baka zina, garin biyebiye na yanzu gashi ina dauke da cuta! Ta cigaba da kukan ta!
Wani irin sanyi Janan taji a ranta da yau Precious ta kara wanke mijin ta kuma a yau ta kara tabbatar da shi kamilin Namiji ne! Shiru yayi se can yace  “kin ga illan abunda nake fada miki ko? Yanzu wa gari ya waya? Mece ce ribar ki in banda zubar da mutuncin ki da kika yi daga karshe kuma kika kwaso cuta? Kina da sauran lokacin barin wannan shirmen tun kafin ki hadu da cutar Kanjamau!
Ita dai ta kasa magana se kuka, a haka Dr. Janan ta duba ta tare da rubuta mata magunguna! Jiki a sanyaye ta bar asibitin tana dana sani mara anfani!
   Janan ta rungume shi tace  “I love u so much my chewing gum! Kara rungume ta yayi se ko Baby ya fara motsi, a tare suka kai hannu kan cikin tare da tuntsurewa da dariya suna fadin “we love u our unborn!

   Wata tara cif Janan ta haifi Babyn ta namiji me kama da Dr. Shureim! An yi shagalin suna inda Yaro yaci sunan Dad wato Ahmad amma suna kiran shi da Imam!

        Bayan Shekaru masu yawa! Janan ce kwance gefen ta Dr. Shureim ne suna ta bacci, kiran sallan farko tare da bugawan alarm ya tada su, tare suka yo alwala suka fito! Nafilfili suka gabatar  sannan suka yi raka’atanil Fijir! Dakin su Imam ya nufa ya tada su dan su wuce sallah shida kanin shi me sunan Abbiey wato Pharouk amma suna kiran shi Mahbub! Masallaci suka wuce dan tun basu kai haka ba yake zuwa dasu masallaci dan ya sa musu son ibadan! ita kuma Janan ta nufi dakin yammatan ta ta tada su, Khadeeja me sunan Ummiey suna kiran ta Iman, Haleema me sunan Momma suna kiran ta Baby se Little Janan suna kiranta Little!  Suma suka yi alwala suka yi sallah! Bayan dawowan su daga masallaci kowa ya biya karatun shi na Qur’ani Baban su ya musu kari haka suma Matan suka biya nasu Maman su tayi musu kari! Da yake ranar ta Jumma’a ce gashi ana public holiday dan haka basu koma bacci ba seda gari yayi haske Sannan suka koma! 10 dai dai Janan ta farka ta shiga kitchen dan hada musu abun kari tun kafin ta fara aikin dukkan su suka shigo suna gaida ta, sannan suka ce “Mum! Mun tashi ki bamu namu aikin da zamu taya ki da shi! Nan ta kasa musu kowa da abunda yake yi! Tana cikin fere dankali Baban su ya shigo suka gaida shi ya amsa yana kallon Janan yace “Mum em late kuma baki tashe ni ba, ki bani nawa aikin! Dariya suka yi sannan tace “saboda kayi latti kai zaka soya dankali, plantain harda kwai!
Fuska ya bata yace shikenan duk ni kadai zan yi wannan aikin?
  Tace “of course yes! 
  Cikin lokaci kankani suka gama kammala abun break din sannan suka ci!
    Daya bayan daya suka yi wanka, dukka yan mazan suka shirya cikin farin shadda me malum-malum harda Baban su, su kuma matan suka sa jallabiya iri daya da Maman su!
     Bayan su Dr. Sun dawo daga sallan Jumma’a dukkan suka tafi kaima su Momma Ziyara daga nan suka je gidan su Ummiey, Yaya Khaleel, da Yaya Saleem ! Se can dare suka dawo bayan sun biya ta Mr. Bigs sun yo takeaway!
   Tunanin zaman su take yi ita da Dr. Shureim duk da akwai soyayya a tsakanin su amma yau da gobe se Allah wata rana ayi fada wata rana a shirya! Ta lura cewa ba kasafai ake fadin kalman ayi *HAKURI* ba se dan rayuwar aure dole se da hakuri dan ba zaka samu komai dari bisa dari ba!
  Jin alaman motan ya tsaya yasa ta dawo daga Tunanin da take yi!
   Bayan sun ci abinci kowa yayi brush tare da yin alwala suka yi shafa’i da Wutri sannan suka wuce dakin su! Kayan bacci suka sa suka hau gado sannan suka yi addua’an bacci, Maman su da Baban suka shigo suma suka sake musu addua’a tare da manna ma kowannen su peck a goshi suka rufe su da bargo tare da kashe musu wuta!!!!!

*_Tammat Bi hamdulillah! Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka bani iko na kammala wannan littafin lafiya! Kuskuren da nayi Allah ya yafe min abunda na fada masu kyau Allah ya bamu ikon anfani da su!!__*

_RukkyBae_馃槒馃槒馃槒

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *