MATAR MUTUM COMPLETE
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 1_
A hankali take tafiya d’auke da tiren talla a kanta cikin sanyin jiki da alama tunani take. Yanayinta kadai zai sa kagane nutsatsiyar yarinya ce bakin titi take tafiya wasu samari na zaune a bakin wani shagon kaya, d’aya daga cikinsu ne yace.
“Kai jama’a kudubi wata yarinya a chan tana tafiya,she is beautiful”
Dukkansu suka dubeta banda mutum d’aya..
wanda yayi maganar, shi ya sake magana
“Kai! kunsan matsalar yarinyar nan kuwa?”
Dukkansu suka amsa da a’a, banda dai mutum d’ayan saurayin nan.
“Matsalarta d’aya,she is sojan tire”
dukansu sukasa dariya a hankali naga ya dubi saurayin nan da baya magana yace masa
“Look my friend kowa na magana kayi shiru wannan wacce irin rayuwa ce?”
Sai yanzu ya d’ago kanshi.
Ya salam wani kyakkyawan saurayi ne nagani wanda bazai wuce shekara 30 bah, cikin isa ya fara magana ya furta
“So what ina ruwana da ita”
Mai surutun nan ya kuma fad’ar
“Haba HAMEED listen to me yarinya nan nada kyau fa sosai..”
Hameed cikin fushi yace
“Kamal pls just keep quite u will never understand me, nagaya maka banason maganar wata mace, meyasa bazaka fahimce ni ba?”
Hameed ya tashi yashiga motarsa cikin fushi koya kalli inda yarinyar nan take yaja motarsa yayi gaba..
kamal yace mata
“Yan mata zo mana”
A hankali ta karaso wajensu ta ajiye masu tiren tallar ,Kamal ya furta
“Nawa-nawa ‘yan mata?”
Cikin wata murya mai dadin gaske ta furta
“Goma-goma”
Kai ya girgiza yace
“Toh kafin aci miye sunanki?“
Dariya tayi ta washe baki tace
“Ni malam bani da suna”
“Da gaske?”
Ta murguda mai baki had’i da fad’in “Eh”
Murmushi yayi yace
“Kai amma kinyi kyau fa“
Shiru tayi abinta
“Please yan mata tell me ur name”
Ido ta ware tace
“Na’am me kace?”
“Oh bakiji abinda na fad’a bane?”
“Eh..“
Kamal ya dafa kanshi yace
“Oh am sorry I am familiar with English so na kan manta wajen da yadace nayi shi”
Kai ta girgiza tace
“An saba kuma”
“Koh”
“Eh mana”
“Toh naji mubar maganar dan Allah yaya sunanki? badan niba dan Allah”
Tayi shiru tana kallon sa ya kuma cewa
“Ko baki kaunar Allah ne”
Da sauri ta girgiza kai tace
“A’a ina kaunarsa mana”
“Toh gaya man”
“Sunana…..”
Ta sauke ajiyar zuciyar ta furta
”Sunana MUHABBAT…”
Tana ambatar sunanta sai da k’irjin Hameed ya buga yana cikin driving motarsa da sauri ya ambaci sunan Allah ..
Kamal yace
“Wow suna mai dad’i sai kace a kasar india”
Tayi murmushi wanda ya bayyana kyaunta Muhabbat kyakkyawa ce son kuwa kin wanda bai samuba yarinya da atattarata bazata wuce shekara 15 bah macece har mace ga idanuwa ga hanci ga dukiyar Fulani wallahi ko ke mace in kika ganta sai kin sota don kyanta she is damn beautiful..
Kamal yace
“Toh inaso nazo gidanku nakawo maki ziyara yaya za’ayi yanzu?”
“Hummm ai ni gidanmu ba abarina fira da kowa”
“Toh ko meyasa?”
“Wallahi bansani ba”
“Toh ko an maki miji ne?”
“A’a wallahi kai malam wallahi kacika tambaya kamar d’an jarida“
“Au baki sani ba ai d’an jarida kike tare dashi“
“Toh naji ni zan tafi talla yamma nayi“
“Kar ki damu zan saye dukka Ayar da gyadar yanzu duk kayan tire d’in nanawa ne?”
Muhabbat ta dubi tiran tallar tace
“Dukka na dari 300 ne”
“OK”
Kamal yazaro five hundred yabata tace
“Ai bani da change”
“Ba damuwa na bar maki“
Muhabbat bata tsaya wata ja in ja dashi ba tace
“Toh nagode, yauwa ina zan zuba maka ita?”
“A’a kada ki damu kije dashi kiba wa yara sadaka”
“To! dama badashi zakaba?”
“Eh”
“Toh nagode”
Kamal yace da ita
“To yanzu sai yaushe kenan zamu sake haduwa?”
“Sai gobe insha Allah”
“OK Allah yakaimu rai da lafiya”
“Toh amin ya Rabbi”
“Ki gaida gida”
“Toh amma kai ya sunanka?”
Dariya Kamal yayi yace
“A’a sai kinzo gobe zan fad’a maki ko ni waye”
“Toh Allah yakaimu”
“Amin…”
Ta juya ta tafi abinta, sauran matasan suka bishi da kallon tuhuma.
A hankali Muhabbat ke tafiya a nitse har takai wata kwana ta karya, wani gida tashiga tana zuwa ko sallama batayi ba, naji wata masifaffiyar mata ta tashi tsaye da bala’i tana fad’in.
“Toh shegiya har kin dawo daga tallar baki saida ba koh?”
A hankali Muhabbat ta karasa wajenta tace
“A’a baaba dama wani mutum yasaye dukka yace naba yara sadaka to kuma..”
“Hmmm munafukar banza idan ma yawon gantalinki kikaji ina ruwana nidai bani kud’in nan kuma anjima ki d’auketa sai kin saidota shegiya mai manyan idanuwa kamar na uwarta”
Ta fizgi kud’in da karfi, Muhabbat tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka tace
“Toh Inna amma lokacin islamiyya yayi kuma malam Umar yace idan banje ba fa yau sai ya dake ni”
“Rufe mun baki munafukar banza ai keda samun karatu har abada sai dai kiga wasu nayi amma badai ke bah”..
Suna cikin magana sai ga baaba Lami ta shigo wato kanwar Inna itama tana shigowa ko sallama batayi ba kawai sai cewa tayi
“Hmm kina nan kina fama da wannan shegiyar koh?”
“Ai ke dai bari ‘yar uwa ai wannan muguwar yarinyar bazata bar munaunci bah irin na uwarta shegiya tashi kiba ni waje kina kallona da manyan idanuwa kamar mujiya”
Lami ta kwashe da dariyar mugunta..
A hankali Muhabbat tanufi toilet don yin alwala dama batayi sallah la’asar bah bayan ta fito tana cikin alwala Inna tazo da sauri ta kwasheta da mari tace
“Dan ubanki tallar kenan?”
Cikin kuka Muhabbat tace
“A’a dama Inna inaso nayi sallah ne sai in tafi”
“Sallar ubanki munafuka”
Tashi tayi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka Muhabbat ta d’auki tallar nan tafita…
“Kai ‘yar uwa kuto-kuto mugun icce yaro bai bani ba balle ya raba,wane mutum yaja dake ya kwana kiyama ai ko aljani sai yashirya miki ke’ke sawa ayi dan uban mutum ko baya so sama_sama dai ‘yar uwa”
“Kai Lami ki daina zugani da yawa, ai kinsan wallahi yanda na raba uwarta da garin nan toh itama haka zan rabata dashi har abada amma kafin nan sai ta gama nema man duniya ai shiyasa idan zata talla bana barin ta fita da dati jikinta sai tayi wanka saboda tayi kasuwa da sauri…”
Lami ta kwashe da dariya tace
“Ai na sanki ba wasa, yaushe zamu koma wajan boka tsiga dan kinsan aikinsa naja”
“Hmmm ai ni zan gaya maki aikin boka tsiga naja saboda yanzu dukkan abinda nace wa malam a gidan nan toh ya zauna wallahi”
“Hahaha kai amma wallahi kinyi sa’a shiyasa nake sonki ‘yar uwa, kina wuta fa”
“Hmm ke dai bari kawai ai ni wallahi dukkan wanda yace bani bace nice an fada maki ni ta wasa ce?”
“Ina fa wane mutum sai dai buzunsa, toh yanzu dai ranar asabar zamuje wajen bokan koh?”
“Toh Allah yakaimu”
“Amin, bari nayi niyyar gida dare nayi nabar yara a gida”
“Toh shi kenan sai ranar asabar d’in kenan?”
“Eh toh gaskiya”
“To ki gaida gida”
Toh gida zaiji….”
Zaune suke saman (Dinning table) d’in cin abinci wanda su hudu kawai ke zama kansa mahaifinsu sai mahaifiyarsu sai Hameed da kuma kanwarsa Minal…._WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 2_
Dukkanninsu sun fito amma banda Hameed Dady ya dubi Mom yace
“Hajiya yau ina Hameed yake ne bai fitoba?”
“Wallahi alhaji nima ban sani ba”
Dady ya dubi Minal yace mata
“Minal go and call Hameed”
“OK Dady.”
Ta mike ta nufi dakin da Hameed yake tayi sallama irin ta addinin musulunci.
“Assalamu alaikum yaya”
“Ya salam wai menene Minal”
“Dama Yaya Dady ne ke kiranka”
“OK kice mai ina zuwa”
Murd’a kofar tayi tajita a rufe magana ta sake yi masa.
“Toh Yaya what are u doing? kabud’e mun kofar mana”
“Oh! Minal I am doing something please just go, because inaso naje wani waje..”
Bai karasa ba ta katseshi.
“Please yaya where are u going?”
“Wai ke wacce irin yarinya ce? mai tambayar tsiya, nace maki ina zuwa a’a see me see wahala oo”
“Toh Yaya am sorry”
“Ok naji kije zanzo yanzu..”
“Yaya Tad’i zakaje ne?”
“Bansani ba, Minal karfa kibari nafito wajan nan”
Hameed na kokarin bud’e kofar d’akin Minal ta gudu..
Sai da Hameed yagama shirinsa sannan yafito, yasamu su Daddy da Mom zaune suna breakfast shima ya zauna kan kujera da yasaba zama koda yaushe.
“Daddy good morning”
“Morning my son how are u?”
“Am fine daddy”
Sannan ya juya ya kalli Mom d’insa yace
“Mom ina kwana”
“Lafiya qlau, au nida hausa za’a gaishe ni kenan da yake ni bahausa ce?”
Daddy yayi dariya yace
“In banda abinki ai ke bahausace”
“Hahaha kukuma gaku turawa koh?”
“A’a Mom ba haka yake nufi bah,”
“Toh miyake nufi?”
“Yana nufin mu yanzu munsaba zaman cikin turawa,”
“koh jikokin Obama”
Dariya suka sa Hameed yace
“Eh toh Mom zai iya zama haka”
“Shi kenan mubar maganar haka”
Suna cikin cin abinci Daddy ya dubi Hameed yace.
“Wai hutun kwana nawa aka baka ne?”
“Wallahi Daddy two weeks ne kawai”
“Ai sunyi kokari ma but before you go you have to look for a lady and marry Dan bana son kana zama haka babu mata kusa da kai”
“Daddy am sorry you need to give me more time because har yanzu ban samu Matar aure bah”
“Ok zan baka amma gaskiya nake gaya maka”
“Nasani Daddy in shaa Allah zan samu”
“Toh Allah yayarda”
Dukkansu sukace
“Amin”
Bayan sun kammala Hameed ya tashi ya shiga d’akinsa Minal tabisa tana mai dariya.
“Yaya an kusan zama ango da gudu ya biyo ta……
*****
*YAU TAKAMA RANAR ASABAR*
Muhabbat tatashi da matsananci ciwon ciki, Inna tana fitowa tace
“Wannn kayan tallar da kika bari ubanwa kika barma su?”
Muhabbat tayi kamar zata fasa kuka tace.
“Wallahi Inna yau bani da lafiya..”
“Kut! me baki da lafiya? toh Allah yasa mutuwa kike wallahi sai kinje tallar nan yar bakin ciki ohh so kike ki barmin tallar nan toh wallahi sai kinjeta munafukar banza mai mugun hali…”
Muhabbat tatashi a haka ta d’auki tallar ta tafita daga gidan, ga ciwon cikin da takeji kamar zata mutu, ga jiri ga amai tana cikin tafiya a hankali tana tunanin halin da take cikin (horn) d’in da taji a nayi ne, yasata dawowa daga tunanin da takeyi.
Wanda ke cikin motar ya fito cikin fushi yana fad’in
“Ke wacce irin yarinya ce ana maki horn bakyaji”
Yana cikin magana Muhabbat kawai tayi wani luuu… zata fad’i yayi sauri ya rikota.
Hameed ya rikota ta fad’a jikinsa cewa yake
“SUBHANALLAHI please mike damunki”
Ina ai Muhabbat har ta suma, da gudu yasata a mota sai asibiti , kai tsaye ya nufi *ALLAH BAMU LAFIYA* yawuce da ita direct yana zuwa yayi sa’a akwai Dr, akayi sauri aka shiga da ita Hameed ya dad’e tsaye sannan sai ga Dr ya fito da sauri Hameed ya isa wajensa yace.
“Please Dr ya jikinta Meke damunta?”
Dr yayi ajiyar zuciya yace.
“Gaskiya nayi mamakin ace yarinya kamar wannan jininta ya hau har kusan 170”
“What! hawan jini kuma?
“Eh wallahi abinda report ya bada kenan”
“Toh Dan Allah Dr you should try ur best and treat her well”
“Yes i will try my best”
“Yauwa Dr nagode yanzu zan iya zuwa ganinta?”
“Eh muje kaganta”
Hameed ya bi Dr suna zuwa suka samu Muhabbat na k’okarin tashi da sauri Hameed ya riketa, a hankali ta kalleshi tace.
“Malam kai kuma waye?”
Murmushi yayi yace
“Hmm I am a human being yanzu dai meke damunki?”
Numfashi ta sauke tace.
“Bakomai”
“Ke kanwata ki fad’i gaskiya”
“Allah bakomi”
Barinta yayi ya maida hankalinsu ga Dr yana cewa.
“Dr yanzu zamu iya tafiya gida koh?”
“Eh zaku iya tafiya amma dan Allah a dinga bata magani akan lokaci saboda kula da lafiyarta she is very young da hawan jini”
“Insha Allah Dr za’a bata, amma Dr yanzu ba abinda ke damuta koh?“
“Eh gaskiya babu sai dai kawai ciwon mara amma wannan ba problem bane, kawai dai duk wata dole tayisa”
“Toh Dr thank u so much…”
Hameed yasa hannu ya riko hannunta suka fito harabar asibitin yasata mota, tunda suke tafiya ba wanda yace ma wani qala sai yanzu Hameed ya juyo ya kalleta yace.
“Ina ne gidanku?”
Tayi kamar zatayi kuka tace.
“Ai ni ba gida zanje ba”
“Toh,! ina zakije?”
“Talla”
“What talla da wannan jikin naki?”
“OK naji toh yanzu wacce unguwa kike?”
“Ina K’ofar kaura”
“Yanzu tun daga K’ofar kaura kike zuwa talla har nan?”
“Eh”
Tunda Hameed ya tambayeta unguwarsu bai sake mata magana bah.
Muhabbat taga yajuya kan motarsa ya nufa titin K’ofar kaura ta zaro ido tana fad’in .
“Nashiga uku ina zaka kaini ban sayar da tallar bah?”
Juyowa yayi ya sake kallonta fuska a d’aure yace.
“Gidanku..”
“Dan Allah karufa min asiri in tafi tallana”
Hameed ko kallanta bai sake yi ba.
Muhabbat ta fashe da kuka ko qala Hameed baice mata bah, sai da suka isa kofar kaura sannan yace…
“Please malama idan kin gama kukan Ina ne gidanku?”
“Ni nace maka ba gida zanje bah’”
“OK naji duka kayan tallar na nawa ne”
Da sauri ta furta
“Na dari hud’u ne, (400)”
“OK toh naji zan biyaki, yanzu ina ne gidan?”
“Gashi chan”
Hameed yana parking motarsa Muhabbat ta fito da sauri.
“Toh mu shiga ciki koh?”
Kai ta girgiza nasa tace
“A’a ni dai ban yarda bah zan shiga ni d’aya”
“A’a inaso muyi magana da babanki”
“Ayya ai babana baya nan yaje kasuwa”
“OK toh kiyi min magana da mamanki”
Muhabbat zata bud’e bak’i tayi magana kenan taji Inna na cewa
“Wai su waye anan?”
Hameed yayi magana yace
“Mune”
“Ku suwa?”
“Bako ne”
“Toh shigo maraba”
Hameed yayi sallama Inna ta amsa masa.
“Sannu da zuwa bako mukayi gidan namu?”
“Eh wallahi”
“Toh ga kujera”
Hameed ya zauna, sai da suka gaisa sannan, Hameed yace.
“To dama ina cikin tafiya ne da motana na had’u da wannan yarinyar, bata da lafiya toh nan dai ta fadi na d’auketa na kaita asibiti daga karshe dai Dr yace wai tana d’auke da hawan jini..”
“Hawan jini na shiga uku dama”
“Ebba baki da lafiya baki fad’a min bah, salan muta ne su zage ni, wallahi Ebba kisake hali Allah nagani ina zaune dake tsakani da Allah amma bakya gani”
Inna sai aka fashe da kuka, Hameed yace
“Toh yanzu dai ga maganin da suka ba ni nan a dinga bata dan Allah Mama a d’in ga bata su a kan lokaci”
“Haba ai bakomi za’a bata su”
“Toh shi kenan ni zan koma duk sanda nasamu lokaci zan dinga zuwa..”
“A’a wallahi bama sai kazo bah, haka ma mungode”
“Toh shi kenan ga wannan asai guro”
“A’a wannan kud’i haka…”
“Mama kenan ai ba yawa”
“Toh nagode yaro Allah yayi albarka”
“Amin toh sai anjima”
“Toh ka gaida gida, yauwa ‘yar albarka ki rakasa mana”
“Toh Inna”
Muhabbat tayi mamaki yanda Inna ta sauya halinta lokaci d’aya har jikin motarsa ta rakasa a hankali Muhabbat ta kalleshi tace.
“Nagode”
Hameed yace
“Bakomi but ya kamata idan baki da lafiya ki gayawa mamanki kinji koh”
Kai ta d’aga masa tace
“Eh naji”
“Yauwa ga kud’in tallar ki nan”
“A’a ai naga kaba Inna”
“Kada ki damu wa’anan kyauta nabata”
“Toh nagode”
“Amma ya sunanki?”
“Sunana MUHABBAT amma Inna na kirana da Ebba”
“OK yayi kyau”
“Toh amma kai ya sunanka?”
Murmushi Hameed yayi yace.
“Hmm ni sunana mai *TAIMAKO DAN ALLAH*._WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 3_
*BAYAN KWANA BIYU*
Yau da gobe sai Allah yau tunda Muhabbat ta d’auko talla babu wanda ya tsayar da ita, har ta iso wajan dasu Kamar ke zama, yana hangota ya taso yabar wajan abokan firar nasa ya iso wajanta ya fad’in
“A’a Hajiyata kenan kwana biyu kin manta damu”
Muhabbat ta washe baki tace
“Wallahi kwana biyu tun a hanya nake sayarwa to kasan yau da gobe zai Allah ”
“Haka ne wallahi”
Kamal ya tsaya yana kare mata kallo sama da kasa, kafin yace
“Kinga yadda kikayi kyau kuwa?”
Muhabbat ta d’an saci kallon jikinta, taga babu laifi jikinta dai babu dati”
Kamal ya d’an kara matsowa dab da ita, da sauri taja baya, hannu yasa zai kamata yayi dai-dai da lokacin da Hameed ya tsaya da motarsa, da sauri ya fito fuskarsa a d’aure dan ganin Muhabbat tsaye da Kamal, yana isowa ya dubeta yace
“ke mikeke a wajan nan, maza ki wuce ki tafi talla”
Jikin Muhabbat na rawa ta juya zata tafi Kamal yace
“To sarkin ustazanci ina ruwanka da ita”
“Look Kamal yanzu ba lokacin wasa bane, ke nace kibar wajan nan”
Da sauri Muhabbat tabar wajan, Kamal ji yake kamar ya shake Hameed, amma babu yanda zayayi ya juya ya tafi, dan yasan halin abokin nasa idan yayi fushi..
+
*******
*WAYE HAMEED DA KAMAL?*
Alhaji Abubakar mai chanji shine ainihin mahaifin Hameed hamshaqin mai kud’i ne a cikin garin Katsina wanda yayi fice, yaro da Babba yasansa alhaji Abubakar matar shi d’aya watau mahaifiyar Hameed mai suna Saratu alhaji Abubakar iyayensa sun rasu tun yana yaro sakamakon hatsarin mota, haka alhaji Abubakar ya taso komai nashi shi d’aya yake, har Allah yasa yagama karatunsa a A.B.U ZARIA yafara chanjin dollar’s har Allah ya had’ashi da Hajiya Saratu,alhaji Abubakar yasha wahala kafin ya samu auren Saratu saboda mahaifansa basa duniyar, haka har Allah yasa aka d’aura masu aure inda ya gina gidansa a G R A bayan sunyi aure da wata uku Allah ya albarkacesu da juna biyu haka Saratu tasha wahala kafin Allah ya sauketa lafiya inda ta haifi kyakkyawan saurayinta, ranar suna yaro yaci sunan ABDULHAMEED bayan shekara biyar Hameed yayi wayau aka sashi primary achan ne suka had’u da KAMAL suka shaku sosai, har takai iyayensu sunsan abotansu bayan shekara shida suka gama primary dukkansu sukace sai dai a had’asu a makaranta d’aya haka aka sasu a secondary bayan shekara 10 Saratu tasake haihuwa yarinya mai suna Minal, haka su Hameed suka gama secondary inda mahaifin Kamal da Hameed suka zauna sukayi magana inda zasu kaisu makaranta ta gaba da secondary wato Nigeria Defence Academic watau (N D A) Kaduna sai da sukayi shekara biyar sannan suka gama suka fito cikakkun Nigeria army inda suka fito a matsayin second leftanant, haka akayi posting d’insu Barrack d’aya a garin port Harcourt watau boni island barrack.
Sai dai kash halin Kamal da Hameed ya bambanta saboda shi Kamal ma’abaucin son mata ne shi kuma Hameed ba ruwansa da ko wacce mace aikinsa kawai yake.
Yanzu an basu hutu sunzo AREWA ………
*DAWOWA LABARI*
Hameed gida ya nufa yana zuwa yasamu su Daddy da mom zaune a parlour suna hira ya gaishesu ya wuce d’akinsa bedroom ya wuce ya fad’a kan gado yana tunani, wata zuciyar tace masa tunda yasan gidansu yarinyar yaje kawai haka yafito ya hau motarsa sai gidansu Muhabbat…..
Muhabbat yau tadawo Inna sai masifa take mata, wai yau ta dawo bata sayar da tallar bah, tace
“Wallahi Inna yau garin ba kasuwa nayi yawo har na gaji..”
“Ba kasuwar ubanki munafuka..”
Inna tabiyo Muhabbat da gudu ashe Hameed na tsaye a soro yana jinsu.
Muhabbat na gudu tayi tuntube zata fad’i sai ta fad’a jikin Hameed, jinta kawai tayi cikin k’irjin mutum a hankali Hameed ya d’ago kanta yana mata wani irin kallo…..
Toh jama’a wani kallo Hameed ke ma muhabbat kallo so ne ko na me?
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 4_
Hameed wani irin kallo na tausayi ya bita dashi, har cikin zuciyar shi yake tausaya mata, can a zuci yake cewa
‘Ashe matar nan karya take fad’a man dama tana cutar yarinyar mutane gaskiya wasu mutane basa tsoron Allah’
Yana cikin wannan tunani ne, yaji Inna na magana tana cewa
“Toh bakin munafuki yau ma ka biyo ta koh? toh wallahi baka isa bah, sai na shiga duk inda zan shiga dan ganin na rabaku ni zaka tonawa asiri?”
Hameed bai gane abinda take nufi bah.
A hankali ya kalleta yace
“Mama I did not understand what u are saying, please just tell me ta yanda zan fahimta”
Dariya Inna ta kwasa tace
“To bakin munafuki me kace turwa uwar turi-turi ta ture uwata, sannu bature, ni zaka gwadawa turanci muda lokacin mu, ake koya mana, dimi-dimi ikamin i don’t to wari dai-dai ”
Murmushi Hameed yayi a zuciyarsa yace
“Toh ni dai Mama wallahi bansan menayi bah amma ayi hakuri”
“Munafuki kace baka sani ba mana tunda kabiyota kusake shashancin ko”
Ido Hameed ya zaro yace
“ INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN.
Mama wallahi ni ba fasik’i bane na shiga uku”
Inna tayi murmushi takaici tace
“Hmm yaro yaro ne”
Zata jawo Muhabbat Hameed yasha gabanta cikin fushi yace
“Wai ke wacce irin macece ana baki hakuri bazakiyi bah dan Allah haba”
“Ba zanyi ba munafuki kawai, toh wallahi ina mai kara gaya maka karabu da ita idan ba haka ba duk abinda yabiyo baya kar kayi kuka da ni kayi kuka da kanka”
Hameed yayi murmushi yace
“Mama kenan ai ni da Allah na dogara ba da mutum ba, dan haka kada ki damu Allah na tare dani”
“Aikin banza”
Inna ta juya kawai ta shige gida tana fad’in
“Ai yarinya zakizo ki sameni, zaki gane kurenki”
Hameed ya juyo Muhabbat a hankali a gabansa ya d’ago kanta yafara Share mata hawayen idonta yace
“Its alright stop crying kiyi hakuri duk mai hakuri yana tare da Allah ni bansan abinda ke faruwa dake kenan ba, dama nazo in gaya maki duk ranar da Kamal yace ku had’u a wani waje please kar kije kinji koh?”
A hankali Muhabbat ta d’aga masa kai tace alamar to.
“Yauwa kanwata kiyi hakuri insha Allah zan dinga zuwa ina dubaki kije ciki kinji koh?”
“Eh naji nagode”
Hameed ya zaro kud’i masu yawa ya bata yace
“Ga wannan ki shiga gida”
Muhabbat tace
“A’a wallahi nagode”
Lallashinta ya fara yace
“Haba ai ni nabaki dan haka ki amsa”
Amsa tayi tana fad’in
“Toh shi kenan nagode”
“Haba ba komi, but idan kin shga duk abinda za ayi maki kiyi hakuri please”
Cikin muryar kuka tace toh nagode…+
Hameed ya nufi motarsa yashiga ita kuma gida tashiga.
Ashe Inna tana labe zaure duk tana jinsu Muhabbat na shiga Inna tace
“Munafuka bani kud’in da yabaki, kafin naci ubanki”
Da sauri ta bata Inna tadaka mata tsawa tana fad’in
“Daga yau kada na sake ganin wannan munafukin a gidan nan kinaji ko?”
“Eh Inna”
“Shegiya munafikar banza sai kije ki zauna”
Da sauri Muhabbat tashiga ta zauna….
*********
Hameed har ya isa gida yana tunanin halin da yabar Muhabbat d’akinsa ya nufa dama lokacin sallah yayi sai yanufi, toilet dan yin alwala bayan yagama yin alwala yazo yayi sallah sannan yayi adduar da yasaba a kullum …
Kan kujera yakoma ya kwanta yana tunani a cikin zuciyarsa yake magana.
‘A gaskiya ina mai tausayin wannan yarinyar abinda yabani tsoro game da ita ga Dr yace man tana da hawan jini toh wane taimako ya dace nabata, gashi kuma yarinyar bata cikin jerin matar da nake so na aura’
Hameed yana cikin tunani sai ga Minal ta shigo da sauri ya d’aga idonsa ya kalleta ta fad’a kan kujerar da yake, cikin wasa kamar yanda tasaba koda yaushe, Hameed yace
“Please Minal yau bana jin dad’i ki barni na huta”
“Yaya What is wrong with u?”
“I’m feeling sick and tired please just go”
Fuska ta 6ata ta kallesa tace
“Yes yaya I will go”
Tafita tana fushi saboda Minal tana son yayanta sosai.
Shi kuma ajiyar zuciya ya sauke yace
“Insha Allah sai na taimakeki Muhabbat Ko ta halin Yaya”
*WASHE GARI*
Inna tana zaune ita da baaba Lami tana gaya mata abinda yafaru jiya da daddare, lami tace
“To ai wannan magana Mairo ba ta bari bace ai wajan boka zamu koma saboda idan har muka bari wannan shegiyar yarinyar ta auri wannan yaron shi kenan kashinmu yabushe Mairo“
Kai Inna ta girgiza alamar gamsuwa da maganar kawarta tace
“Toh yanzu yaushe zamu koma wajensa?”
“Ai ni ko yanzu in kin shirya mutafi kawai”
“A’a mubari sai gobe da safe zaifi dad’in tafiya”
“Toh shi kenan”
Duk maganar nan Muhabbat najinsu hankalinta ya tashi sosai tace.
“Na shiga uku kada su Inna fa, su kashe yaron mutane saboda basu da imani a ransu”
Da sauri Muhabbat ta karaso wajensu tace
“Inna nagama ina kayan tallar?”
“hmm munafika yau tun yanzu zaki d’auki tallar? toh wallahi naganki ke da wannan yaron sai naci ubanki munafuka”
Muhabbat tace Toh Inna.
Muhabbat ta d’auki tallar sauri take kamar zata tashi sama ba inda ta tsaya sai inda su Hameed ke zama tana zuwa tasameshi zaune da sauri ta k’arasa wajensa jikinta har rawa yake tace
“Dan Allah malam mai taimako inaso nayi magana da kai”
Cikin mamaki ganin yanda jikinta ke rawa Hameed yace
“Lafiya dai koh?”
Take Muhabbat ta fashe da kuka, da sauri Kamal ya taso yana shirin kamata, Hameed ya sha gabansa, yana cewa
“What’s that,is it with u she said she wants to talk?
Kamal ya daure fuska yace
“Yes what is your own?”
Hameed yayi tsaki yaja hannunta yasa a motarsa shima ya shiga itako kuka take kamar rainta zai fita..
KAMAL yaji haushi kamar ya mutu…
Ba inda Hameed ya tsaya da Muhabbat sai wani katan waje inda mutane ke hutawa Hameed ya bud’e mata mota tafito sai yanzu Muhabbat ta bud’e idonta tunda tafara kuka bata bud’e su ba sai yanzu, Hameed yanuna mata inda zata zauna, dukkansu suka zauna a hankali Hameed ya kalleta yace
“Please kanwata meke damunki?”
Muhabbat takara fashewa da kuka mai cin rai a hankali Hameed ya matso kusa da ita ya kama hannunta yace
“Please ki daina kuka ki fad’a man me ke damunki?”
Muhabbat ta kifa kanta a kafarsa tana fad’in
“Nashiga uku wallahi akwai matsala
Hameed yace
“Muhabbat matsalar me yafaru?”
Ya d’ago kanta yana kallonta.
Majina taja tace
“Naji Inna tana fad’a ma baaba Lami wai zata kaika wajan boka, kuma wallahi Inna zata iya yin komai dan ta rabaka da duniya, dan Allah karka kara zuwa gidanmu”
Hameed yayi murmushi yace
“Muhabbat kenan ai ba abinda Inna ta isa tayi man bayan wanda Allah zai yi min, dan haka ki kwantar da hankalinki inaso yau ki bani labarin rayuwarki da ta Inna
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 5_
Numfashi Muhabbat ta sauke ta matso kwallan idonta tace.
*ASALIN LABARINA SHINE*
“Malam Amadu shine ainihin sunan mahaifina ba wani mai kud’i bane yana dai kasuwancinsa yana da mata mai suna Maryam wato Inna Mairo kenan, mahaifina yana hakuri da Inna Mairo sosai, gashi suna da matsalar haihuwa kusan shakararsu 5 da aure amma Allah bai basu haihuwa bah, mahaifina yadamu kwarai da gaske haka mahaifiyar babana ta damu sosai wata rana har tazo tasamu Inna kan matsalar, amma Inna tayi mata rashin kunya sosai.
Mahaifina da yaji maganar baiji dad’i ba, amma yayi hakuri saboda yasan halin Inna Mairo kenan bata ganin kowa da mutunci.
Wata rana mahaifina yaje kauyensu ranar tayi masa dad’i saboda ranar ce ya had’u da mahaifiyata mai suna Fatima, sunzo bikin wasu ‘yan uwansu daga Cameroon mahaifiyata ba ‘yar Nigeria bace su fulanin Cameroon ne, a nan ne mahaifina ya nemi auren mahaifiyata.
Mahaifina yasha wahala kafin yasamu auren mahaifiyata sai da ya bita har Cameroon ‘yan uwanta sukace bazasu ba kado auren yarsu bah, sai da suka ga ba sarki sai Allah domin kuwa mahaifiyata tace bata son kowa sai shi, sannan suka bashi aurenta.
Inna tunda taji labarin baba zai kara aure hankalinta yatashi sosai ba inda Inna bata shiga ba, dan ganin an fasa auren amma abin yaci tura, haka mahaifiyata tazo gidan Inna ta dameta da wahala da bala’i na yau daban na gobe daban, abin Allah bayan aurensu da wata uku Allah yabata ciki tunda Inna taga cikin nan take safa da marwa wajan malamai da bokaye har sai da Inna taga cikin nan yafita kafin hankalinta ya kwanta ba a jima ba, tasake samun ciki sai dai wannan salon ya chanza saboda ba yanda Inna batayi ba, dan ganin cikin yafita amma yak’i fita haka ta hakura har Allah ya sauki mamana lafiya aka haifeni…
Mahaifina tunda aka haifeni yake nuna mun so Inna abin na bata haushi kamar zata mutu amma ba yanda zatayi, idan mahaifina yatafi kasuwa mamana takoma kamar baiwa wajan Inna..
Inna duk wajrn bokan da taje dan akashe mamana sai bokan yace bazai iya ba, wata rana Lami tazo tace mata tasamo mata wani sabon boka suka shirya sukaje wajan bokan tunda suka dawo gida mamana bata kara gane kan babana ba, yabi ya tsanemu,ana haka wata rana aka wayi gari ba mamana ba dalilinta hankalina yatashi sosai naje nasamu babana amma sai naga ko a jikinsa tun daga ranar har yau bansa mamana a idona ba, kusan shekara 10 kenan saboda wannan lokacin bani da wayau sosai, bayan tafiyar mamana kakata tazo d’aukata wato maman babana amma Inna ta hana nayi kuka kamar ba gobe maganar da nake maka har yanzu ‘yan uwan mamana basuzo sun tambaya ina take bah, babbar matsalata yanzu itace rashin ilimin da nake fama dashi bansan komi ba bayan talla, toh kaji labarina”+
Hameed yayi ajiyar zuciya yace
“INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN dama har yanzu ana samun irin wadan nan matan marasa imani a duniya?”
A hankali ya kalleta dama tunda ta fara bashi labari kanta a kasa tana kuka yace
“Muhabbat please stop crying relex your mind I will help u”
Muhabbat ta d’ago kai tana fad’in
“Na’am me kace?”
“ Muhabbat am sorry I am so familiar with English sai kiyi hakuri dani, yauwa abinda nake so dake Muhabbat ki k’ara hakuri insha Allahu zan taimakeki kinji ko?”
Muhabbat ta zaro idanuwanta a waje cikin fargaba.
Hameed yayi murmushi wanda sai da ya baiyana kyakkyawar fuskarsa yace
“Ki kwantar da hankalinki nasan abinda kike tsoro kada Inna tayi min wani abu ko? toh in shaa Allahu ba abinda zai faru dani sai alkhairi kinji koh? ki d’auke ni a matsayin yayanki uwa d’aya uba d’aya daga yau hawayenki zasu tsaya in shaa Allahu, sai kema kin d’andani dad’in duniya kamar yanda sauran mutane keji”
Cikin jindad’in maganarsa Muhabba tace.
“Toh Yaya nagode amma ina tsoron Allah ina tsoron Inna saboda bata da imani a ranta ko alama”
“Hmm karki damu ai duk abinta batafi k’arfin Allah ba, yauwa yanzu kin rik’e sunan garin da mamanki take a Cameroon?”
“A’a wallahi dama kakata tasani kuma Allah yayi mata rasuwa”
Kawai sai ta sake fashewa da kuka, a hankali ya d’aga kanta yana share mata hawayen idonta
“Please Muhabbat stop crying I promise u zan taimakeki kota wane hali indai bai sa6awa shari’ar musulinci ba, kinji koh?”
Kai ta daga masa tace
“Toh”
“Yauwa kanwata, toh yanzu mutafi na kaiki gida ko?”
“A’a zan tafi talla yanzu, domin kuwa na mayarwa Inna tallar nan yau sai na lahira yafini jindad’i” “Hmm Muhabbat don’t worry zan saye kayan tallar kinji mutafi”
Yakama mata hannu , a hankali ta kallesa tace.
“ yayana mamana tace min a lokacin kafin ta tafi, ba kyau namiji ya ta6a matar da ba tasaba”
Murmushi Hameed yayi cikin jindad’in maganarta yace
“Hmm Muhabbat kenan kin manta yanzu ni yayanki ne ai yaya yakan kama hannun kanwarsa, so dan haka karki damu ba abinda zanyi maki my sweet sister”
Ya bud’e mata kofar mota tashiga shima ya shiga yasa mata key.
Sai da Hameed ya kusan zuwa unguwarsu sannan ya tsaya da motarsa yace.
“Toh Muhabbat zan barki a nan because banaso naja maki duka”
“Toh Yayana nagode”
Ta fad’a cikin jindad’i.
“Toh ga kud’inki sai ki juye man kayan a mota saboda nasan in kika koma dasu gida in anjima sai kin fito talla”
“Haka ne fa”
“Yauwa my sweet sister kin gano kenan”
Dariya sukayi kana sukayi ban kwana ta kama hanyar gida.
*******
Kamal ne zaune inda suka barsa yana magana a zuciyarsa yace
‘Hmmm Hameed kenan ai wallahi in kasan wata toh wallahi bakasan wata ba, idanma son Muhabbat kake toh wallahi kamakaro saboda na rigaka sai na biya bukatata kafin inma aurenta zakayi sai kayi i swear to my God no one can stop me from what I want to do..’
Yana cikin maganar a zuciyarsa sai ga Hameed ya dawo yace
“Ya abokina?”
Kamal wani irin kallo yayi masa na ko in kula, hmm dama in dai irin wannan kallo ne toh Kamal gidan yazo.
Hameed ya yatsina fuska yace
“Ai banza thats ur problem”
Kawai ya shige motarsa….
****
Muhabbat tana komawa gida tasamu har baaba Lami tatafi gida tayi murna a zuciyarta, saboda ta san in har Lami na gidan toh ta shiga uku, tana zuwa tayi sallama Inna kota kalleta ta aje kayan tallar tace
“Inna ga kud’in nan yau na sayar da wuri”
“Hmm munafuka yau ma har yayi maki juyen koh?”
“A’a Inna yau an samu kasuwa ne”
“Humm yarinya kenan ai na kusan kawo k’arshen wannan wasan naku nan bada jimawa ba, bani kud’ina munafuka”
Muhabbat jiki na rawa ta bata kud’in, a hankali tace dan Allah Inna intafi islamiyya?”
Inna ta yatsina fuska wanda sai da ya baiyana mumunnan fuskar nan tata, ta jawo kwalin sigari ta d’auki daya ta banka masa wuta, taja hayaki ta butar tace.
“Hmm ai sai kitafi na san yau zasuci ubanki munafuka, dama abinda nake so kenan”
Muhabbat ita dai juyawa tayi ta nufa d’akin da tsummokaranta ke ciki tayi shirin islamiyya dama bata da uniform d’in islamiyya haka take tafiya tana zuwa ta samu malam Umar a tsaye zata wuce ya kirata, yace
“Muhabbat zo nan meya hanaki zuwa islamiyya kwana biyu?”
Tayi shiru tana narai narai da ido.
Magana ya kara yi mata
“Ina tambayarki kinyi shiru kina jina”
Take kawai ta fashe da kuka a hankali ya karaso kusa da ita yace
“Muhabbat ya isa nasan matsalarki kawayenki sunyi min bayanin komai, akwai alkawarin da na d’aukarwa zuciya ta zan taimakeki kota halin Yaya insha Allah…..
Toh makaranta novel d’in MATAR MUTUM Hameed yace zai taimaki Muhabbat haka kuma malam Umar toh dukkansu ko wane taimako zasu bata…..
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 6_
*KORAFI*
_Masu korafi akan kada su fara karanta wannan buk nazo na tsaya sai na d’auki lokaci kafin nacigaba, to ku kwantar da hankalinku wannan littafi mai suna matar mutum ina da shi tun daga farko har karshensa yanzu haka, dan haka masoya kada kuji tsoro da yardar Allah bani tsayawa har sai na dire alkalamina har karshe, amma fa sai kon bani goyan baya_
*******
“Dan haka Muhabbat ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu komai yazo karshe, amma inaso na tambayeki kuma ki bani amsa yanzu”
“Toh malam Allah yasa na sani ina jinka”
Saida ya sauke numfashi kana yace
Muhabbat zaki iya aure na kuwa?” Muhabbat ta zaro ido waje tace
“Malam aure fah kace?”
“Eh ko bazaki aureni bah?”
Kai ta girgiza tace
“A’a malam ai kafi k’arfina, dan Allah karufa mun asiri wallahi malam..”
Sai kawai ta fashe da kuka, ta kasa karasa magana.
“Inajinki ki ida maganarki mana”
Ina ta kasa magana sai kuka..
“OK toh shikenan nasan abinda kike ma kuka bakya sona ne toh ba matsala tashi ki shiga class”
A hankali ta d’ago kai tace
“A’a wallahi malam ba haka bane..”
Katseta yayi da sauri yace
“ naji jeki ki zauna zan nemi ki”
Cikin sanyi jiki ta tashi tashiga ta zauna tunda ta zauna take tunani toh dama yau saboda maganar da malam umar zaiyi mata ne, Allah yasa Inna ta barta tazo islamiyya kenan..+
A cikin zuciyarta kuwa cewa take
‘Gaskiya ina son malam Umar saboda na tabbata idan na auri malam Umar nayi dacen miji sai dai kash in dai Inna na duniyar nan baza ta bar ni nayi aure bah’
Bata san lokaci da ta fashe da kuka bah.
Wata kyakkyawar yarinya ta dafata da alama Bakuwace a islamiyya tace
“Haba baiwar Allah me yafaru kike kuka?”
Sai yanzu ta gane kuka take ta sauri tace
“Bakomai”
“Haba ‘yar uwa dan Allah ki fad’a min mana”
“ Allah bakomai”
“ OK toh shi kenan ni sunana Minal Bakuwace ni a islamiyya nan Ke fah?”
“Humm sunana Muhabbat”
“Wow sweet name, so kinga dama a islamiyyar nan bani da k’awa yanzu inaso muzama abokai kin yarda?”
Muhabbat ta d’aga mata kai alamar eh..
Suna cikin maganar sai ga malam mai hadisi yashigo nan suka tsaya da maganarsu.
Bayan yagama masu aka tashesu, Minal tace
“Toh ni yanzu za’azo d’aukata kefa ina gidanku?”
hmm gidanmu ba nisa sosai yanzu zan karasa”
“A’a ki tsaya sai mu wuce dake”
“A’a wallahi nagode”
“Toh shi kenan tunda bakya so na hakura”
Muhabbat tayi murmushi tace
“A’a wallahi ba haka bane ina dai sauri ne”
Haka sukayi ban kwana ta dawo gida ..
*****
Inna ce keta ruwan bala’i wai dan sunje wajen boka yace masu gaskiya aikin nan yafi k’arfinsa saboda duk sanda ya aiki shedanu aljanu dan suyi ma Hameed mugun abu sai sutarar yana addua sai dai su dawo,
Inna tace dama a duniya akwai aikin da yagagari boka tsiga, Lami tace
“Haba ‘yar uwa kwantar da hankalinki kamar kinyi bako ya mutu ai na samo mana mafita akwai wani boka a Niger bokan aikinsa kamar yankan wuka ne sha yanzu magani yanzu nima wata kawata taje wajansa shine take bani labari”
“Haba Lami dama kin san da wannan boka baki gaya man bah”
“Toh kiyi hakuri yanzu zamu bari gobe da safe sai mutafi”
“Kai Lami ai jinake kamar mutafi yanzu”
“A’a mubari sai gobe dai”
“Toh shi kenan ….
*****
*Washe gari*
Su Inna suka kama hanyar Niger domin zuwa wajan boka.
babu inda suka yiwa tsinke sai a wani kauye can cikin Niger.
Sunyi tafiyar k’afa mai nisa kafin suje wani kauye saboda tafiyar kasa ake sosai kafin aje garin, suna zuwa Inna tayi sallama bokan yadaka mata tsawa yace
“Ke nan ba’ayi mana sallama”
Inna jiki na rawa Lami tace
“tuba take boka”
Ya kwashe da dariyar mugunta yace
“Hahaha toh nasan abinda ke tafe daku, akan yarinyar kishiyarta ne, saboda bata so tayi aure toh bah damuwa shedanu sun san da zuwanku kuma anyi an gama, amma aikinmu akwai sharade idan muna aiki saikin tsayar da duk wani aikin lada, bake bah sallah sannan idan azumi yazo baza kiyi bah kin yarda?”
Innah ta juya ta kalli Lami.
Lami ta d’aga mata kai alamar ta aminci, ta dubi boka tace
“Na yarda boka”
Yayi dariya wanda sai da duk wajen ya amsa yace
“Yauwa ‘yar gari, yanzu akwai wata matsala kwaya d’aya, akwai wani shegen yaro dake zuwa wajanta”
Ana fad’an yaro sai da k’irjin Inna ya harba, cikin ranta tace
‘Kar dai ace wannan boka ma ba zai iya aikin bah wahalar banza zamuyi’
Boka ya katseta da fad’in
“Ki kwantar da hankalinki, kina tunanin kamar bazan iya bah kamar wancan bokan ko”
Innah ta zaro ido tana mai mamakin yanda akai har boka yagane abinda ke ranta, lallai aikin boka nan zaiyi nasara.
Boka yace
“Mairo matsalarki ta warke tunda har kika zo nan, yaron nan idan yakoma wajen aikinsa toh shida garin Katsina har abada ita kuma bata ba aure.”
Inna tayi dariya mugunta ita da Lami kamar ansa uwarsu aljanna.
Boka yace
“Toh ga wannan laya ce kije ki sata a makabarta, wannan kuma a cikin gida zaki rufe kinji koh?”
“Eh boka”
“Yauwa na baku nan da sati biyu ku dawo ku bani labari”
“Toh boka mungode”
“Hahaha ai mu nan ba’ayi mana godiya saboda bama aikin Allah”
“Toh boka ga wannan”
“Ku aje anan”
Da sauri suuka aje nan fa suka fito suka kama hanyar gida Nigeria (Wannan wace irin rayuwace irin tasu Inna da Lami sun manta Allah shine mai komai,
ya Allah kashiryar da bayinka Allah yasa mudace..)
Yau ta kama ranar Saturday Hameed na d’akinsa kwance idanuwansa a rufe yana mai tunani.
A hankali Minal ta zauna dai-dai kafafunsa, tace
“,Yaya what is wrong with u this days?” A hankali ya bud’e idonsa yayi murmushi yace
“No problem Minal kawai ina tuna wani abu ne”
“Kai yaya please tell me what is the problem” wallahi nasan akwai abinda ke damunka.”
“Hmm Minal sarkin rigima kenan Allah bakomai”
“Toh shi kenan yaya dama I want to tell u something”
“Hmm ina jinki”
“Yaya wallahi jiya da naje islamiyya nayi kawa yarinyar baruwanta”
Hameed ya 6ata fuska yace
“But mai nagaya maki da zakije islamiyya, ba nace ba ruwanki da kawaye bah”
“Haka ne Yaya, toh yaya wallahi yarinyar naganta tanata kuka ne a class, shine taban tausayi har ta gaya man sunanta wai sunanta MUHABBAT”
A firgice ya mike daga kwancen dayake yace
“What muhabbat!!!!!”
Cike da alaman tambaya tace mai
“Eh yaya, kasanta ne?”
Matar soja ce taku har kullum ina tare daku
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 7_
“Yaya kasanta ne?”
Hameed murmushi yayi yace
“No! kawai naji kamar na ta6a jin mai irin sunan ne a wani waje”
“Kai!!! yaya ka fad’i gaskiya idan ma kasanta ne, toh ba matsala she is my friend I will make a way for u”
Tana dariya cikin tsokana ta fad’i haka, d’an dukan wasa Hameed ya kai mata yace
“Ke ina wasa dake i don’t even no the girl how can I marry her?”
“Hmm yaya kenan please calm down don’t worry nasan baka santa bah”
“OK kinsan da haka amma kike tsokanata, anyway to sai tace maki kukan me take?”
Minal ta kwashe da dariya tace
“A’a yaya ai kai kace baka son maganarta toh dan haka I will leave u”
Hameed ya yatsina fuska yace
“OK na barki tunda bazaki fad’a min ba, amma yau ni zan kaiki islamiyyar da kaina”
“Minal ta buga tsalle tana murna tace
“Yaya da gaske zaka kai ni Islamiyya?”
“Eh mana zan kaiki”
“Kai amma naji dad’i wallahi, idan mukaje zan nuna maka kawata Muhabbat”
Yayi murmushi Hameed yace
“Toh my sister yanzu inason in fita sai nadawo bada jimawa ba”
“Toh yaya nima bari naje wajen mom a kitchen na tayata aiki”
“Ok”+
Bayan fitar Minal daga d’akin Hameed,
tashi yayi ya d’auki makullin motarsa.
Ba inda ya nufa sai gidansu Muhabbat, yana zuwa yasamu, yaro a k’ofar gidansu ya turasa domin ya kira mai ita.
Allah sarki, Muhabbat da sauri ta fito kasancewar yau inna bata gida, tana fitowa ta ga Hameed tsaye a jikin motarsa, tayi murna da ganinsa sosai,
Muhabbat tace
“Yaya sannu da zuwa”
A hankali Hameed yace
“Yauwa my sister yakike?”
“Lafiya qlau”
Hameed ya d’aga kyakkyawar fuskasa ya kalleta sosai, yace
“Nazo ni inaso muyi magana dake I have an Important issue to discuss with u, amma yau ina Inna? naga kin fito da dauri”
Cikin sanyin murya ta furta.
“Wallahi sun fita ita da baaba Lami”
Hameed ya ta6e fuska yace
“Ok! Muhabbat ina da k’anwa mai suna Minal, tace min islamiyyarku d’aya”
Da sauri Muhabbat tayi murmushi tace
“Eh wallahi jiya muka fara had’uwa da ita”
“Ok Muhabbat inaso ki fad’a min gaskiya me yasaki kuka jiya?”
Muhabbat ta zaro ido waje cike da mamakin Minal tace
“Ita tagaya maka ina kuka jiya?”
Hameed ya yatsina fuska yace
“Bah wannan na tambayeki bah, ina tambayarki ne a kan kukanki na jiya”
“Cikin murya kasa-kasa Muhabbat tace
“Baakomai Allah ya’ya”
“Ok jin dad’i ne yasaki kuka? hmm Muhabbat kenan nifa ba yaro bane duk na fahimci damuwarki, shiyasa yau na yanke shawara daga yau kukanki ya tsaya zan share maki hawayenki, Muhabbat I want to marry u, zan aureki!!!”
Yana fad’in maganar dai-dai lokacin da su Innah suka, dawo daga wajen boka. mai mashin ya saukesu
Bayan mai mashin ya sauke su Innah ta hango Muhabbat tsaye ita da Hameed.
Da sauri ta k’araso wajen su tana fad’in
“Kutumar uban can au yau ma ka biyo ta? toh wallahi baka isa ba yau zanyi maganinka baqin shege”
Innah tacima Hameed kwalar riga ta fashe da kuka, tace
“Yanzu duk abinda kuke bai isheka bah macuci azallumi sai da ka biyota har gida”
Duk ‘yan unguwar da sukaji maganar Innah saida suka fito amma da sunga ita da Muhabbat ce sai su koma gida..
Hameed ransa ya6aci sosai saboda a rayuwarsa yana bak’in cikin cin fuska, ya d’ago idanunsa har sun chanza kala sun koma jajawur kamar gauta, morah tasa ta motsa soja yayi fushi, Hameed Yace
“Innah wallahi kin ban mamaki, ai ji nake yanzu ba mai irin halinki a duniya, toh bari kiji dan ma mutuwa zakiyi kiyi na d’auki alkawari zan auri Muhabbat, kuma auren bazai d’auki wani lokaci bah, zan rabaki da ita saboda rashin imaninki yayi yawa”
Innah ta kara fasa kara tace
“Na shiga uku yaro ni kake kira da banda imani?”
Sai kuma can tayi murmushin takaici wanda yafi kuka ciwo tace
“Hmm yaro baka san wuta ba sai ka taka, ai ni kabewar kan kabari ce bakin cikin mai daushe, yaro ana babbakar giwa wazai jiwo kamshin zomo, ni nazama kadangaren bakin tulu akasheni a kashe tulu a barni kuma na 6ata ruwa, kuma wallahi zanyi maganinka, zan 6atar dakai kamar yanda na kora uwarta a cikin garin nan haka kai ma zanyi maka”
Hameed ya gyara tsayuwarsa jikin mota yayi murmushi,
Yace
“To ai karki manta ni da Allah na dogara ba da boka bah, ai duk abinki sai na auri Muhabbat..”
Ya juya ya kalli Muhabbat tana ta kuka, Yace
“Haba matata kukan me kike kuma? share hawayenki i promise u. zan aure ki kuma no one can stop me from marying u”
Innah tace
“,Munafiki ai zan ga yarda za’ayi ka aureta indai ina numfashi a doron duniya, ba kai ba auren Ebba, shin barima na tambayeka wai kai d’an gidan uban waye a garin nan?”
Hameed yayi murmushi yace
“Ni d’an gidan mutunci ne wanda suka san darajar d’an adam”
Nan fa Innah ta kara jin haushi ta fara zagin Hameed ta uwa ta uba, Lami tace
“Haba Mairo ya kina 6ata yawon baki’nki”
Lami taja Innah cikin gida.
Innah cewa take
“Lami ki barni da d’an iskan yaro nan yau sai na nuna masa rashin kunyarsa ta karya ce”
“Haba Mairo ai karki manta komai yazo karshe, wallahi aikin bokan nan nayi kuma tunda munga abinsa iskanci ne toh ni zan koma wajen boka, kawai a rabasa da duniyar gaba daya”
Innah tayi murmushin jin dad’i tace
“Yauwa ‘yar uwa ai idan har Boka yayi mun haka toh ya gamamun komai a duniya, zanso naga wannan d’an iskan baya duniya”
Lami tayi dariya tace
“Ai karki damu Muhabbat ita da jin dad’in rayuwa har abada sai dai taga wasu nayi amma bah ita bah”
“Kai Lami shiyasa nake sonki”
Lami ta kara sakin dariya tace
“Yauwa tsaya kiga na k’ora maki shi da kaina”
Lami ta fito tasamu Hameed tsaye inda suka barshi yana ta kallon Muhabbat.
Ta k’araso wajensa baki washe tace
“Bawan Allah dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru”
Hameed ya juya ya kalleta saboda mamaki ma ta basa, saboda yasan ai duk abinda Innah ke k’ullawa a tare sukeyi abinsu, amma sai ya nuna mata kamar bai san ma tanayi bah, Lami ta kara cewa
“Malam magana nake ma”
Hameed ya yatsina fuska yace
“Au wai dani kike?”
Lami tace
“Eh”
“Toh naji malama zaki iya tafiya”
Ya gwasaleta Allah sarki Lami takoma da ‘yar kunyarta.
Muhabbat ta sulale kasa tana kuka, Hameed ya durk’usa kasan, yace
“Haba Muhabbat kukan me kike kuma? wallahi alkawarin da na d’aukar maki ba wanda ya isa ya hanani aurenki, kada ki damu iyayena basu da matsala yau zanje na samu Dady d’ina, zaizo yasamu abbanki ayi maganar aurenmu, saboda naga ba abin da zai kawo karshen abin nan illa na aureki..”
Muhabbat tana kuka tace
“Dan Allah ka rufa min asiri ka barni, ni dai wallahi bana sonka” Hameed ya mik’e tsaye yace mata
“Toh nidai na gama magana ko ki soni ko karki soni nidai na gama magana..”
Bai tsaya jin amsarta ba kawai ya shiga motarsa ya barta nan tana kuka…………
Taku ce mrs. Omaru ‘yar mutan katsinawa
*MATAR MUTUM*BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 8_
Muhabbat tana cikin kuka,sai ga mahaifinta ya dawo daga kasuwa. Tunda ya hangota, yasan akwai abinda ya faru,da sauri yak’araso wajenta,
Yace
“Toh sababba yau kuma me kikayi mata?”
Da sauri tamik’e tsaye saboda tasan da Inna da abbanta duk tafiyarsu d’aya ce, sai dai bambancinsu shine mahaifinta duk abinda yakeyi ba a cikin hayyacinsa yake ba.
“Toh munafuka mushiga cikin yaja hannunta suka shiga.
Tun daga zaure yake kiran sunan Innah.
Kamar tana jira ta amsa, yace mata
“Fito me yafaru yau kuma ke da wannan Yar duniyar ‘yar?”
Innah ta yatsina fuska, tace
”Wai daga tayi bak’o sai tace bazataje bah, shine nake mata fad’a shine fa tafita tana fushi,tafi son duk wanda yazo, ya zagemu ace munk’i yimata aure”
Muhabbat sakin baki tayi tana kallo Innah cikin ban mamaki, cikin zuciyarta tace
‘Toh yau kuma Innah ta chanza magana haka cikin kwanciyar hankali, hmm na tabbata Innah akwai abinda zata kulla”
Muhabbat duk acikin zuciyarta take wannan maganar, ta sauke numfashi.
Abba ya juya ya kalli Muhabbat, yace
“Au dama saboda wannan maganar kika zauna a waje kina kuka? saboda kija mata zagi wajen jama’a, Munafuka mai bak’in hali”
Lami tafito daga d’akin Innah, tace
“Haba malam ai zagin ya isa haka yarinya ce fa. abita a sannu”
Ko yanzu Muhabbat mamaki maganarsu ke bata.
Abba ya kad’a kanshi ya shiga d’aki, Innah tajuya ta kalli Muhabbat, tace
“Ai sai ki shga cikin koh, Muhabbat tace
“Toh”
Lami tace wa Innah
“Ni zan tafi gida”
Innah ta rako Lami har zauren gidan, sannan Lami tace
“Toh kinji abinda na gaya maki, idan wannan d’an iskan ya dawo yana neman auren wannan ballagazar toh ki nuna kinfi kowa murna, saboda ko mutuwa yayi bah wanda zai ce da sa hannunmu aciki”
Innah tace
“Amma Lami zan iya hakuri har ya kawu kud’in auren wannan shegiyar kuwa”
Lami tayi murmushi tace
“Ai hakuri zaki har mucinma burinmu, saboda bana so ya mutu a garin nan za’a iya zarginmu, ai ance ba nan yake aiki ba”
Innah tace
“Toh shkenan na hakura. kigaida gida”
Sukayi sallama Lami ta wuce gidanta
+
****************
Hameed gida ya nufa yana zuwa yayi sa’a su Dady na zaune a falo, gabansa sai dukan uku-uku yake, yana tunanin ko Dady bazai aminci bah, dan ya auri Muhabbat.
Saboda idan har yaji ita yar talla ce ba lalle ya amince ba.
A hankali Hameed ya zauna saman kujera ya gaishe da su sannan ya dubi Dady,
yace
“Dad I what to speak to u about something very important”
Dady ya gyara zama ya fuskanci d’an nasa yace
Ina jinka. Hameed ya sauke ajiyar zuciya mai karfi yace
“Dama Dady a kan wata yarinya ne da na samu zan aura”
Dady ya sake murmushi cike da jin dad’i yace
“Kai my son am very happy, yarinyar waye kuma waye mahaifinta a garin nan?”
Hameed yayi shiru yana tunani, dady yace
“Kai nake saurare Hameed”
Hameed yace
“Dad ita ba yar kowa bace mahaifinta talaka ne yarinyar zan aureta ne akan wani dalili mai k’arfi”
Dad yace
“To meye dalilin naka na aurenta?”
Hameed yayi ajiyar zuciya ya gyara zama yace
Allah abinda yasa zan aure Muhabbat yarinyar tana cikin wahala kuma mahaifiyarta bata gidan. Dady tsaya kuji dalilin da yasa zan aure Muhabbat”
Nan fa Hameed ya fad’a ma mahaifinsa ko wacece Muhabbat, kafin Dady ya fara magana mom ta fara, tace
“Ai wannan maganar banza ce karasa wadda zaka aura sai Yar talla? ina da sake wallahi”
Murmushi Dady yayi irin na manya yace
“Dakata Saratu ai MATAR MUTUM kabarinsa. idan Allah yace Muhabbat matar Hameed ce bah wanda ya isa ya hana duk duniyar nan”
Mom jikinta yayi sanyi tace
“Toh shi kenan Alhaji , Allah yasa haka shine mafi alkairi”
Dady yaji dad’in yace
“Yauwa ko kefa Allah ya basa sa’ar taimakon da yayi niyya, don haka yanzu in nafita office zanje nasamu mahaifin Kamal sai muje a ayi maganar aure, so when are u going back to port Harcourt?”
Hameed yayi ajiyar zuciya sannan yace
“Dad am going back in the next 4 day’s, insha Allah sannan hutunmu yakare”
“Toh Allah yakaimu kafin lokaci zamu tsayar da lokaci aurenku in shaa Allah”
Mom tace
“Toh yaushe zaka kawo min ita mugaisa?”
Hameed yayi murmushi yace
“Mom ai islamiyyarsu d’aya da Minal ai tasan Muhabbat”
Hameed yana fad’i sunan Muhabbat dai-dai lokaci da Minal zata shigo falo da gudu ta k’araso ta fad’a jikin Hameed, tana fad’in
“Laaa yaya ashe kasan Muhabbat shiyasa ina gaya maka sunanta sai da kazabura yaya kenan”
Hameed ya d’aure fuska yace
“Ke bansan shirmen banza go and get ready for islamiyya, zan kaiki yanzu”
“Hahaha yaya kace kanaso kaga Muhabbat dai”
Hameed ya wurga mata harara. Mom tace
“A’a dakata ai gaskiya ta fad’a. Hameed yace
“Ai mom ke kike sakatar da wannan yarinyar”
Dukkansu suka sa dariya har da Dady, Minal ta tashi da gudu ta haura sama dan sa kayan islamiyya.
Hameed ma d’akinsa ya nufa dan watsa ruwa, Dady kuwa zama sukayi shida Mom suna magana akan yanda Hameed har ya amince da Muhabbat gaskiya sun godema Allah da yabasu d’a irin Hameed.
Suna cikin hira sai ga Hameed sun fito shida Minal yana rik’e da hannunta,Dady yadube ta Yace
“Toh sarkin rigima har an fito? toh Hameed in kaje ka gaida Muhabbat”
Hameed yasosa k’eya yace
“Ai Dady bah wajenta zanje bah, zankai Minal ne kawai sai nadawo”
Dady yayi murmushi yace
“Ok toh sai kun dawo”
Dukkansu suka amsa da
“Toh Dady”
Sannan suka fito Hameed ya bud’e mota ya shiga Minal itama haka sannan yayi ma mai gadi horn yabud’e mai gate suka fita, suna tafiya a mota suna fira.
Sun kusan zuwa islamiyya kenan Hameed ya yanke wata hanya, Minal ta bud’e baki tace
“Yaya ina kuma zaka a nan?”
Hameed ya wurga mata harara yace
“Sa ido kiyi kallo”
Yana gama maganar dai-dai lokaci da Hameed yayi parking d’in motarsa k’ofar gidansu Muhabbat.
Minal tace
“Laaa yaya ina ne nan?”
“Fito kiga ko ina ne.”
Suna fitowa dai-dai lokacin da wani yaro zai wuce, Hameed yak’irasa. Yace
“Kai dan Allah shiga nan kace ana kiran Muhabbat”
Yaron ya juya ya shiga yasamu Innah zaune tana gyaran gyada, yayi sallama. Yace
“Wai wani mutumi yace” yana k’iran Muhabbat”
Innah tayi shiru sai can kuma ta tuna wani abu sai tace
“Kace ga tanan zuwa , Innah ta dube Muhabbat tace
“Muhabbat bakiji ana k’iranki a waje bah”
Muhabbat ai kasa magana tayi sai kawai ta sak’i baki tana kallon Innah, dan mamaki take yanda halin Innah ya sauya lokaci d’aya, cikin ranta kuwa cewa take ya Allah yasa halin Innah ya chanza, tana cikin tunani Innah ta sake yi mata magana a hankali ta tashi dan fita taga waye.
Minal ta kalli yayanta, tace
“Au dama yaya kace gidansu Muhabbat zakazo?”
Hameed ya wurga mata harara, yace
“Minal kin cika surutu”
“Toh yaya daga fad’ar gaskiya”
Tana rufe baki sai ga Muhabbat tafito, tana fitowa Minal ta bud’e kofar mota tafito da gudu. Tace
“Aunty Muhabbat kenan dama ashe kece matar da yaya zai aura baki gaya min bah?”
Muhabbat tayi murmushi tace
“Au shiya gaya maki ni zai aura?”
Kafin Minal ta bata amsa Hameed yabata amsa. Yace
“Eh nina gaya mata, dan haka yanzu jike shirin islamiyya zamu wuce da ke”
Muhabbat ta zaro idanuwa tace
“Ai ni bah yanzu zanje bah sai anjima”
Hameed ya d’aure fuska yace
”Ki shiga ki fito muna jiranki yanzu nan”
Muhabbat da taga Hameed ya d’aure fuska yasa ta wuce cikin gida dan zuwa ta gaya ma Innah tana zuwa ta zamu Innah zaune inda tabarta, tana zuwa Innah ta daga kai ta kalleta, Muhabbat tsayi tayi ta kasa magana dan gudun fad’an Innah,
Innah kamar ta sani tace
“Lafiya kika tsaya man a kai?”
Muhabbat ta fara inda-inda tace
“Innah dama….”
“Toh dama me?”
“Innah dama yaya Hameed ne yazo da kanwarsa yace wai in na shirya nazo su wuce dani islamiyya”
Innah tayi murmushi ta zuki karan sugari dake hannunta na haugu tace
“Toh miye Muhabbat ai kutafi kawai, sai kindawo”
Muhabbat jiki a sanyaye tace
“Toh Inna”
Tafito abinta, dama ba wasu kayan na isalamiyya gare ta ba balle ta tsaya sakawa ta juya ta fita.
Ba Muhabbat ba ni kaina sai da nace gaskiya Innah ta sake hali Allah yasa da gaske ne.
Bayan ta fito ta nufi motar Hameed dama suna tsaye shida Minal suna hira, Hameed yabud’e kofar mota ya shiga Minal zata shiga gaba, Hameed yace
“Mai zakiyi? haba dan Allah malama koma baya ai yanzu matata zata shiga gaban motata bake ba”
Minal tasake baki tana kallon yayanta, don taga lokaci d’aya yana shirin sake mata mazauni. Tace
“Ok to ba komi zamu koma gida”
Ta koma baya abinta Muhabbat kuwa tsayawa tayi ta kasa shiga sai da takai Hameed da yaga bata da niyyar shiga yasa yafito ya bud’e mata kofar motar ya kamata yasata a ciki, Minal ta kwashe da dariya tace
“Wayyo Allah yaya wannan irin Luv haka motarma bazata iya shiga ba sai kasata, wayyo ai idan nakoma gida sai naba mom labari.
Hameed bai mata magana bah ya zagaya ya shiga mota, itako Muhabbat kunya duk ta kamata, sai da ya shiga sannan ya fizgo Muhabbat jikinsa ya rungumeta Minal ta zaro ido, Muhabbat tasake k’ara tace
“Na shiga uku miye haka yaya..?”
A hankali ya dagota ya kalle Minal dake baya, itako jikinta rawa kawai yak e yace
“Minal yanzu sai ki gaya ma mom da kyau na rungumi matata koh…”
*MATAR MUTUM*
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 9_
Minal shiru tayi takasa magana a hankali Hameed yasake Muhabbat, ai kam yana sakinta kamar tana jira takai hannunta zata bud’e kofar, Hameed yayi saurin fizgota takara fad’awa jikinsa ya rufe kofar mota sannan ya tayar da motarsa Minal bata daddara bah .tace
“Wayyo duniya yau ina ganin abu, yaya ai wannan soyayyar ‘yan india kawai suke yinta”
Hameed ya juyo ya wurga mata harara yace
“Minal can u just keep quite or i shud deal with u”
Minal tayi shiru sai dariya take a zuciya da ta kalli Hameed ta cikin mirror suna had’a ido sai ta sunkuyar da kai kasa ta kece da dariya. Muhabbat ko duk kunya ta kamata tarasa inda zata sa kanta saboda kunyar Minal, kanta tasa cikin cinyoyinta ta kasa d’ago kai, Hameed ya kalleta yayi murmushi ya girgiza kansa ya cigaba da driving d’insa , Minal ta sake kallon yayanta. Tace
“When will they fix the date of ur marriage?”
Hameed ya wurga mata harara. yace
“I don’t know Minal wallahi kin cika surutu”
Yana rufe baki dai-dai lokaci da motarsu ta isa gate d’in islamiyyarsu, yana tsayawa Muhabbat ta kai hannunta zata bud’e kofar mota Hameed ya rik’e hannunta yace
“Ina zaki kike sauri? toh ki tsaya zamuyi magana dake yanzu”
Muhabbat na so ta kwace hannunta daga garesa amma takasa, taji rik’on maza ballantana na soja, Muhabbat bata san lokacin da hawaye ya dinga fita daga idonta bah. Minal tace
“Yaya please kabarta mutafi class.+
Hameed ya juyo ya wurga mata harara yace
“Ina ruwanki please just go, ki tafi yanzu zatazo, zamuyi magana da matata”
Minal ta yatsina fuska. Tace
“Yaya ai ba inda zani sai naji me zaka gaya mata”
Cikin fushi Hameed ya daka mata tsawa. Yace
“Minal ina wasa dake?”
ta turo baki ta bud’e motar tafita tana fushi, Muhabbat itama takai hannu zata bude kofar Hameed yasa key yarufe, tayi-tayi ta bud’e ta kasa haka ta hakura sai ta koma bashi hakuri idonta a kasa tana hawaye, a hankali Hameed ya juyo ya kalleta. Yace
“Please am sorry Muhabbat wallahi ba haka halina yake ba nayi haka ne dan Minal ta tabbatar ina sonki but am sorry my sweet sister wallahi har yanzu ke kanwata ce , kuma maganar da zamuyi dama inaso nagaya maki nayi ma iyayena maganar aurenki sunce ba matsala sun amince so d’an haka yanzu insha Allahu su Innah kawai suka rage kuma suma zamu tsaya da addu’a ba za’a samu matsala bah”
Muhabbat ta d’ago kai tana kallonsa har yanzu hawaye fita yake a idonta.
Hameed ya ciro Hanki ya d’ago fuskarta yafara share mata hawayen idonta, Muhabbat bata san lokaci da ta k’ara fashewa da kuka bah, ta fad’a jikin Hameed, tana fad’in.
“Wallahi yaya na tabbata in dai Innah na raye toh wallahi bazata barni nayi aure bah tayi wannan alkawarin tun ban fahimci mai duniya take ciki ba”
Maganar da Muhabbat keyi yak’ara sashi tausaya mata, a hankali ya d’ago hannunsa ya fara bubbuga bayanta tamkar jaririya yana fad’in.
“Ya kukan ya isa haka Muhabbat ai duk abin Innah batafi k’arfin Allah bah, inaso ki sani idan Allah yace ni mijinki ne toh bah wanda ya isa ya hana , shi yasa hausawa ke cewa *MATAR MUTUM KABARINSA* ,Muhabbat idan har Allah yace ni mijinki ne toh ba wanda ya isa ya hana duk duniyar nan..”
Sannan ya d’ago ta daga jikinsa yafara share mata hawaye yana bata baki har ta daina kuka sannan ya bud’e mata k’ofar mota, tafita abinta, tana zuwa ta samu Minal zaune Muhabbat tayi mamakin yanda ta ganta, saboda ba alamar fushi a fuskarta sai ma murmushi,haka ta karasa wajenta suna cikin hira har malam yashigo bayan sun gama karatu aka tashesu kowacce ta kama hanyar gida, Minal tana zuwa gida ta samu Hameed zaune a falo shida mom suna hira tayi sallama sannan ta karasa ta zauna kusa da mom, ta d’aga ido ta kalli Hameed ta kece da dariya Hameed ya d’aure fuska Minal tana ganin haka ta tashi ta haura sama….
**************************
Dady bayan ya tashi office ,bah inda ya wuce sai gidan mahaifin Kamal don ya sanar dashi Hameed ya samu mata, kuma su tsayar da magana ranar da zasuje gidansu Muhabbat, Dady yayi sa’a yasamu mahaifin Kamal yayi masa tarba sosai , bayan sun gaisa da Dady yace
“Dama Alhaji maganar d’anka ya kawoni saboda yasamu matar aure shiyasa nace bari nazo na gaya maka sai muje ayi magana”
“Kai amma naji dad’i yarinyar ina ce, kuma waye mahaifinta?”
Dady yayi ajiyar zuciya sannan yace
“Muhabbat ba Yar kowa bace asali ma ita Yar talla ce”
Nan fa Dady yayi ma mahaifin Kamal bayani ko wacece Muhabbat, tunda mahaifin Kamal yaji wacece Muhabbat ya tausaya mata sosai . yace
“Toh Allah ya sanya alkhairi, alhaji ai duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi”
tur k’ashi ashe duk maganar da su Dady keyi a kunnen Kamal yana tsaye yana jinsu, kawai sai yajuya ya fita, yana fad’in
“Ai wallahi Hameed baka isa ba, in kasan wata toh baka san wata bah sai nasaka *KAYI NADAMA* wallahi……”
Kamal juyawa yayi yafito daga falon har yafito basu san ya shigo ba yana fitowa motarsa ya d’auka yafita yana tafiya yana tunani yanzu ina zaiga Muhabbat gashi bai san gidansu bah, kan motarsa ya juya ya nufi inda suke zama ,kafin ya karasa wajen da suke zama yaga wata kamar Muhabbat,da sauri ya danna kan motarsa wajenta yana zuwa yaga itace kuwa ai kam yasha gabanta, Muhabbat tana murmushi ta d’aga kanta saboda tana tunanin ko Hameed ne, Kamal ya bud’e mota yafito Muhabbat tana ganin Kamal ne ta daure fuska, Kamal ya karaso gabanta yana cewa
“Malama Muhabbat dama kina duniyar nan?”
Muhabbat ta murgud’a mai baki, tace
“bansani ba ina ruwanka dani, malam bani hanya na wuce”
Kamal yayi murmushi yace
“Allah yabaki hakuri ni bada fad’a nazo bah dama I wanted to tell u something ne Hameed ne ya aikoni yace nagaya maki bashi da lafiya sosai so dama yanzu gidanku zanje sai gashi Allah yasa na ganki”
Muhabbat ta zaro ido tace
“Na shiga uku me yasameshi jiya fa muna tare dama kenan bashida lafiya?”
Muhabbat bata san lokaci da hawaye ya fara fita daga idonta bah”
Kamal yace
“So yanzu ba wata doguwar magana zamu tsaya yi ba, zaki biyo ni muje ki ganshi koh?”
Muhabbat ta share hawayen idonta. tace
“A’a kabari zanje saboda yanzu ina talla amma idan na sayar zanje.”
“Haba Muhabbat don’t worry indai kayan tallarki ne karki damu, yanzu idan nakoma ban kaiki bah Muhabbat ai bakiyi ma Hameed adalci ba”
Muhabbat tayi shiru tana tunani.
‘A gaskiya idan har banje naduba yaya Hameed ba ban kyauta ba saboda yaya Hameed *SHINE GATANA*’
Muhabbat duk cikin zuciyarta take magana , a hankali ta d’aga kai ta kalli Kamal tace
“Toh ba damuwa muje naganshi”
Kamal yayi murmushin mugunta yace
“Yauwa ko kefa”
Muhabbat bata sake yimashi magana ba ta nufi motarsa ta bud’e baya ta shiga, Kamal ma ya zagaya ya shiga yasa key yatada, yana cikin driving ya kalli Muhabbat ta cikin mirror yace
“This girl today am gonna teach u a lesson”
Muhabbat tayi saurin fad’in
“Na’am magana kake”
“No kawai ina tunani ne”
“Toh”
Kamal yayi murmushi yace
“Since u don’t know how to speak English I have sold u.”
Ba inda Kamal ya nufa da Muhabbat sai mai kud’i hotel,yana zuwa Muhabbat ta dinga zaro ido saboda bata ta6a zuwa irin wannan asibitin bah, bama asibitin bah ko unguwar bata sani ba duk yawon tallarta kuwa, Kamal yayi parking d’in motarsa yafito sannan Muhabbat ta fito. Yace
“Toh munzo Muhabbat mushiga ciki”
Suna zuwa Kamal yace
“Toh tsaya nan na amshi kati kinsan irin wannan asibitin ba’a bari mutane na shiga sai an basu kati saboda tsaro”
Muhabbat bata ce komai ba Kamal ya juya ya nufe wajan receptionist don biyan kud’in d’aki a hankali ya juyo ya kalleta yana tunani ko tana kallonsa kwata-kwata hankalinta baya wajansa da sauri ya biya kud’i aka bashi key din d’akin da yakama, sai da yaje ya bud’e d’akin kafin ya dawo yace mata
“Muje yana sama”
Muhabbat ta bishi a baya sai da sukaje dai-dai kofar sannan yace
“Shiga”
Tana shiga Kamal ya bita da sauri ya rufe kofa Muhabbat cak ta tsaya saboda yanda taga alamar d’akin bah asibiti bane da sauri ta juyo zata fita ina Kamal yarufe kofa ,Muhabbat sai ta d’aure.tace
“Ina yaya Hameed d’in yake?”
Kamal ya kece da dariya. Yace
“Au wai kina tunani Hameed na nan toh kinyi kuskuren biyo ni don wallahi yau sai kinyi da nasanin sani na a duniya Muhabbat.”
Muhabbat ta fashe da kuka. tace
“Dan Allah karufa min asiri wallahi ni ba yar iska bace”
Muhabbat takai hannunta zata bud’e kofa, Kamal ya rik’e mata hannunta ya fincikota ya jifata kan gadon d’akin, Muhabbat ta fasa wani irin ihu mai k’arfi……
Toh makaranta da alama kenan ko Allah zai ba Kamal sa’ar Muhabbat?
*MATAR MUTUM*
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 10
Kamal ya kama Muhabbat ya jefata kan gado ta fasa k’ara,tana bashi hakuri
“Dan Allah kayi hakuri karufa min asiri kada ka tozartani na dade ina tattalin mutuncina ba dan komai ba sai dan ya’yana, ka tausaya min wayyo Allah na shiga uku,wayyo yaya Hameed kazo kacece ni zai rabani da mutuncina”
Ai yanda kuka san tana kara zuga Kamal bai tsaya saurararta ba yakai hannunsa zai cafko dukiyar Fulaninta kenan aka buga kofa da k’arfi wanda shi kansa yatsorata, sai yayi shiru yana tunani ko za’a k’ara bugawa sai yaji shiru.
Shirun daya jine yasa shi yafizgi hijabinta, hohoho ai yana cire mata hijab sai wata sha’awa tak’ara ziyartasa sha’awarsa tatashi idanunsa har sun sauya kala sunyi jajawur ko iya bud’esu bayayi sosai, yakara kai hannunsa wajen dukiyar fulaninta, Muhabbat tafasa kuka mai k’arfi jikinta sai rawa yake tace
“Shi kenan yau mutuncina zai zub’e yaya alkawarin da ka d’aukan min shi kenan yanzu bazan iya aurenka bah wayyo yaya Hameed!”+
Wani irin bugo k’ofa akai yanda kukasan katafila, ai kam kofa ya bud’e don bala’i, ai kam Muhabbat tana ganin wanda ya shigo d’akin ta wani bangaje Kamal da dugu tanufa wajensa ta fad’a jikinsa. Tace
“Wayyo yaya Hameed na shiga uku zai rabani da mutuncina.”
Hmm ashe duk abin nan Hameed yaje wuce wa yaga Kamal tsaye da Muhabbat yayi mamakin hakan shiyasa yatsaya yaga mezai faru har saida yaga ta shiga motar Kamal sannan yabiyosu a baya.
Hameed yayi fushi sosai ya janye Muhabbat daga jikinsa yaje ya shak’e Kamal yana fad’in
“Why did u touch my wife”
Hameed yakai ma Kamal wani wawan duka,Kamal ya d’aga hannu zai rama ,ina Hameed yakara hadashi da bango yace
“Kamal u made mistake by touching my wife, wallahi Kamal kabani mamaki dama halinka har yakai haka, me yasa bazaka daina halin akuyanci ba? to wallahi yau bazaka fita a d’akin nan lafiya ba sai nayi maganinka”
Hameed fa yayi fushi zuciyar soja ta tashi Hmm kunsan soja bai had’a kowa da matarsa ba, soja akan matarsa zai iya yin komai wallahi.
Allah sarki Muhabbat da taga yanda Hameed ke ma Kamal ta tsorata sosai sai ta koma bashi hakuri, sannan Hameed yasake Kamal.
Yace masa
“Kamal we are no more friends bani ba kai kuma idan kana tunanin zan rabu da Muhabbat toh wallahi kayi kuskure Babba don Muhabbat belongs to me alone tsaya ma ka gani”
Hameed ya finciko Muhabbat jikinsa ya had’a bakinsa da nata yafara tsotsa, Muhabbat ta fasa k’ara cikin rawar jiki sai kawai ta sume jikin Hameed, yanda Hameed yaga Muhabbat ta sume jikinsa hankalinshi ya tashi sosai sulalewa kasa yayi da ita yana jijigata ,ina, ai Muhabbat ko numfashi batayi Kamal yataho da sauri zai kai hannunsa jikin Muhabbat Hameed ya bangaje shi yace
”Stop Kamal don’t u dear touch my wife in ur life ever”
Hameed da yaga Muhabbat bata da alaman farfadowa haka ya d’auki Muhabbat cak tamkar jaririya da sauri yabud’e k’ofar d’akin yana sauri ya nufi motarshi da ita, Kamal ya biyoshi a baya Hameed ya bud’e mota yasata a bayan mota sannan ya bud’e shima ya shiga yasa key, Kamal da sauri yazo zai bud’e ya shiga, Hameed yadaka mai wata tsawa yace
“Kamal na gaya maka kada kasake shiga rayuwata daga yau bani ba kai, kuma bari kaji wani abu wallahi Kamal yanzu saboda kai zan bar garin port Harcourt nadawo Kano da aiki because banaso wata alaka ta k’ara had’amu don wallahi Kamal, ban tab’a jin natsaneka a rayuwata ba sai yau, so don haka duk wata alaka tamu nayanke ta daga yau”
Hameed bai tsaya yaji me Kamal zaice ba kawai yaba wa motarsa wuta ya wuce, ai Kamal kasa binsa yayi sai kawai ya nufi motarshi ya zauna yana mai tunani, amma bansan tunanin me yake bah.
Hameed gudu yake har bai San yanda motarsa ta kaishi asibiti ba asibitin *ALLAH BAMU LAFIYA,* yana isa asibitin yayi parking d’in motarsa da sauri yafito ya bud’e ya d’auki Muhabbat yana shiga 0.P.D.aka amshi Muhabbat ba’a b’ata lokaci bah aka shiga da ita d’akin da aka basu gado sannan Dr ya shiga, Allah sarki Hameed duk yadamu fad’i yake.
“Ya Allah kaba Muhabbat lafiya har na cika alkawarin dana daukar mata”
Yana cikin sinturi a harabar asibitin sai ga Dr ya fito, a hankali Dr ya dafa Hameed ta baya da sauri Hameed ya juya yaga Dr ne Dr yayi murmushin yake yace
“Hameed kabiyoni office zamuyi magana da kai”
Dr yayi gaba Hameed ya biyoshi suka shiga office d’in Dr suka zauna, Dr ya dubi Hameed sannan, yace
“Am sorry Hameed”
Dr nacewa am sorry sai da k’irjin Hameed ya harba saboda shi a nasa tunani ko Muhabbat ta mutu, Dr yaci gaba da cewa.
“Hameed garin yaya haka ta faru ka manta na gaya maka ,yarinyar nan na d’auke da hawan jini, nace maka yarinyar nan nason a bata kulawa sosai, but u didn’t listen to me gashi yanzu jininta yayi high da yawa, gaskiya yarinyar nan nason kulawa sosai Hameed bazan 6oye maka ba kuna sakaki da lafiyar yarinyar nan, idan bazaku iya zama da ita ba ku mayar da ita wajaniyayenta mana”
Karshen maganar Dr ya buga hannunsa a table d’in office d’insa, da sauri Hameed ya d’ago kanshi ya kalli Dr idanuwanshi duk sun cika da kwalla, yace
“Dr wallahi bansan haka zata faru ba please kayi wani abu akai, domin Muhabbat ta samu lafiya wallahi ko nawa zan kashe wallahi zan kashe domin tasamu lafiya”
Dr yayi ajiyar zuciya, yadanyi shiru na d’an wani lokaci sannan yace
“OK no problem yanzu ba wata matsala nasan zuwa nan da dare zata farka because nayi mata allurar barci saboda ta samu ta huta, but yanzu ba wata matsala sai dai ba zamu sallameta bah ,sai ta kwana biyu a nan.”
Take Hameed yasake fuskarshi, yace
“Thank u Dr yanzu Kenan sai ankawo wadda zata zauna da ita kenan ko?”
“Eh gaskiya Hameed”
“Toh shi kenan bari naje nakawo wadda zata zauna da ita..”
“Hameed yafito daga wajen Dr yanufi motashi yabud’e ya zauna yana cikin yana tunani, toh wazaizo ya kula da Muhabbat, baya son yaje gidansu Innah tayi masa rashin mutunci, wata zuciyar tace
‘Ai dole kaje gidansu ka fad’a masu bata da lafiya, toh idan bakaje bah, inhar ta kwana biyu a waje ai akwai matsala ko’
Take ya sauke ajiyar zuciya ya furta
“Gaskiya ne fa dole naje gidansu Muhabbat na fad’a koda kuwa Innah zata kashe ni”
Hameed ya tada motarshi ya nufi gidansu Muhabbat, yana zuwa yayi sa’a Abbanta na gida sai ya gaya masa Muhabbat ba lafiya tana asibitin, Abba yace
“Garin yaya haka ta faru?”
Hameed yace
“Abba tana cikin tafiya kawai sai ta fad’i Allah yasa ina kusa nakaita asibitin”
Ai kam sai ga Innah tafito, nata cewa
“Yanzu Muhabbat d’ina ke asibiti, dama yau naga alama kamar bata da lafiya amma ta matsa sai ta d’auki talla kai wannan yarinya bata gudun ayi mani magana”
Hameed sakin baki yayi yana kallon Innah cikin mamaki yana tunani yaushe Innah ta sauya haka, Innah ta katse masa tunaninshi, da cewa
“Toh malam kabishi kaga asibitin da take ni kuma yanzu zanzo in na kimtsa”
Hameed da Abba suka nufi asibitin, ai kam suna fita Innah ta kwashe da dariya tace_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 11_
Inna na tsaye a zaure tana ta faman dariya, sai ga baba Lami tazo,da sauri ta karaso wajan ta cewa
“Toh Mairo yau da alama duniyar tayi maki dad’i irin wannan dariya haka , toh yau kuma me kika aikata?”
“Humm ke dai bari ‘yar uwa ai yau ina ciki’n farin ciki, wai yanzu wannan d’an iskan yaro yazo wai Ebba ba lafiya, ya kaita asibiti an bata gado shine yazo yafad’a wai naje, humm ‘yar uwa bama wannan ba ke bakya tunani kodai, ciki yadirka ma shegiyar shine yazo yana so ya aure ta kafin asirinsu yatonu, kinsan yaran masu kud’i”
Lami ta kece da dariya tace.
“Nima fa ‘yar uwa na dad’e ina zargin haka kai amma indai da gaske ne haka, toh gaskiya da duniya tayi mana dad’i, kinga daga nan da ya tuno shi kenan Muhabbat bata ba zaman Katsina don Wallahi nasan malam ba zai barta ta zauna mai gida bah shi kenan kinga gida ya zama naki”
“Haka ne fa Lami ke wallahi shiyasa nake sonki a duniya, Lami duk abinda zanyi tare mukeyi, toh wai ni Lami ya magana BOKA kuwa?”
“Humm kwantar da hankalinki ‘yar uwa kamar kinyi bak’o ya mutu ai na koma wajen boka yace
“Karkiji komai indai aljanu na duniyar nan toh Hameed ba zai tab’a auren Muhabbat ba, shi da auranta har abada”
Innah tayi dariya tayi ihu tace.
“Ihooo wayyo sai ni Mairo wallahi wazaija dani ya kwana k’iyama, ai wallahi Lami naji a jikina wannan shegen yaron ba zaikai labari bah saboda a duniya na tsani Muhabbat kamar yanda na tsani uwarta, au Lami mubar wannan magana tunda kinzo yanzu sai muje asibitin tare, muga ya shegiyar take”
Suka kece da dariya suka shiga cikin gida Innah tana zuwa zane kawai ta sake Lami ta kalleta tace
“A’a Mairo ai lokacin sallah yayi bazakiyi sallah ba kafin mutafi”
Innah ta wurga ma Lami harara tace.
“Au har kin manta abinda boka ya gaya mana kenan? yace na tsayar da sallah indai har inaso aiki nan yayi kyau, koh don haka ai ni na tsayar da sallah, dama can bata dameni ba, ba koda yaushe nake yinta bah yanzu kuma na samu sauki ai kawai mutafi”+
Kai jama’a wannan wace irin rayuwace Innah keyi kamar ba musulma ba, toh Allah dai yasa mudace Amin!!!
Bayan sun fito bakin titi suka nufa, suka hau mashin, suna zuwa suka samu Abba da Hameed zaune a d’akin, Innah taje masu a cikin fuskar tausayi, har yanzu Muhabbat bata farka ba, bayan zuwansu suka gaisa Abba ya dube Innah yace.
“Toh Mairo ni zan koma gida amma nan zaki kwana ko zaki koma gida sai da safe kindawo?”
Innah tayi saurin furta.
“A’a malam ai gara na koma gida saboda kar abar gidan ba kowa, kuma ai naga nan asibitin kud’i ce ana kula da ita ba abinda zai sameta”
“Gaskiya ne Mairo toh mutafi gida, bawan Allah kai ma ya kamata kakoma gidan haka tunda ana kula da ita”
Hameed yayi shiru yana kallon Abba dake magana saboda abin mamaki yake bashi yanda Abba ke magana kamar ba namiji ba, gaskiya Innah ta gama da Abba, a hankali Hameed ya sake kallon Abba cikin yar k’aramar murya yace.
“Toh Abba shi kenan kugaida gida nima yanzu zan tafi amma ina jiran Dr ne yazo muji ko suna da bukatar wani abu”
Toh sukace Dukkansu da Innah da Lami suka ce
“Toh shi kenan Allah yabata lafiya sai gobe zamu dawo ,basu tsaya sunji me zaice bah suka k’ara gaba,bayan fitarsu Hameed kujerar da yake zaune yajawota kusa da Muhabbat, Allah sarki ido ya k’ora mata yana kallonta, baisan lokacin da hawaye ya fara fita daga idonsa ba na tausayin Muhabbat yace
“Toh wai ni wannan hawayen da nake na tausayin Muhabbat ni koko na sone? kai ina na tausayine amma kuma ai Muhabbat takai macen da kowane namiji zai sota”
Yana cikin wannan tunani Muhabbat ta fara magana cikin ihu.
“Wayyo yaya Hameed Dan Allah kazo kacece ni zai rabani da mutumcina, wayyo na shiga uku shi kenan…”
Hameed da sauri ya tashi ya dagota jikinsa ya fad’in
“Muhabbat please calm down am here ba abinda zaiyi maki I promise u”
A hankali Muhabbat ta fara bud’e idanuwanta tana bud’ewa taga Hameed zaune kusa da ita, ta fara mai da numfashi sama_sama tamkar warda tayi gudu, Hameed ya d’auki hannunshi d’aya yana shafa bayanta yana cewa
“Is ok please stop crying am here, don’t worry everything is ok”
A hankali ya d’ago fuskarta ya tallabo kumatunta yana kallonta cikin ido, da sauri Muhabbat ta lumshi idanuwanta saboda bazata iya had’a idonta dana Hameed bah, cikin murya can kasa Hameed ke magana
“Please open ur eye ki bud’e idonki yau inaso naga cikin idonki Muhabbat”
Yana cikin kallonta sai kawai yaji wani abu ya sokeshi, da sauri ya saki Muhabbat yayi SALLATI saboda yanda yaji abin ba komai bani illa sha’awar Muhabbat da taziyarcishi saboda yasan idan har yaci gaba da kallonta toh maybe shed’an zai iya shiga tsakanunsu, sai kawai ya koma kan kujera ya zauna, ya d’ago kanshi ya dubeta yace
“Muhabbat yanzu abinda nake so dake ki kwanta a nan zan turo maki nurse yanzu ta dinga kula dake saboda naje na gayama su Innah sunzo amma tace bazata kwana ba sai gobe zata dawo.
Ai sai yanzu Muhabbat tatuna da zancen Innah da sauri Muhabbat ta buga k’irjinta tace
“Na shiga uku ina kayan tallata da tazo me kace mata?”
Hameed ya kalleta yayi murmushi, sannan yace
“Don’t worry ban gaya masu abinda ya faru bah ki kwanta kiyi barci ba matsala, because Muhabbat kinsan ba yarda za’ayi na kwana a nan kinsan shaidan saboda har yanzu niba mijinki bane but insha Allah gobe da safe zan dawo kinji koh?” Muhabbat ta share hawayenta tace
“Toh yaya nagode”
“OK my sweet sister”
Yana gama maganar dai-dai lokacin da yake shafa fuskarta, sannan ya juya yafita abinshi,yana fita yayi ma nurse magana ta kulla da ita kuma ta tabbatar taci abinci, sannan ya fito ya d’auki motarshi, ya nufi gida direct yana zuwa ya samu su Mom da Dady zaune a falo suna kallon India a tashar ZEE WORLD, Hameed ya k’araso wajansu ya zauna kan kujera sannan ya gaidasu cikin girmamawa, dukkansu suka amsa cikin fara’a, sannan Dady ya dube Hameed yace,
“Lafiya yau baka dawo gida cikin lokaci bah?”
Saida ya dauke ajiyar zuciya kana yace
“Humm wallahi Dad, naje ziyaran wani abokina ne, baya jin dad’i”
“Ok toh ai haka nada kyau yauwa yanzu abinda nakeso dakai kaje ka samu mahaifin yarinyar nan ka gaya masa gobe insha Allah za’a kawu kud’in niman aure, saboda naje na samu mahaifin Kamal munyi magana gobe zamuji mukai”
“Toh Dady nagode Allah yakaimu gobe lafiya amin”
Hameed tashi yayi ya nufa d’akinshi yana zuwa toilet ya nufa sai da yayi wanka kafin yayi alwala yafito yayi sallah sannan ya zauna kan sallaya , yana addu’a Allah ya kareshi daga sharrin Innah, bayan ya gama kan gadonshi ya nufa, ya kwanta ya numshi idonshi kamar mai barci kuma ba barci yake bah, da ya lumshe idonshi sai ya d’inga ganin Muhabbat yana tunu irin kallon d’a yake mata d’azu, a hankali ya bude idonshi yayi murmushi yace,
“Na yarda yanzu inason Muhabbat sosai gaskiya inason ki Muhabbat sosai”
Sai ya sake lumshe idonshi yana nan yana tunani har barci yayi gaba dashi…..
***********
*Washe gari*
Hameed tunda asuba da ya dawo daga sallah, ba inda ya wuce sai asibiti don ganin ya jikin Muhabbat yake, ai kam yana zuwa ya tura k’ofar d’akin dai-dai lokacin da tafito daga toilet daga ita sai d’aurin gaba, Hameed suna had’a ido yayi sauri yarufe idonshi yace
“YA _SALAM AMINCIN ALLAH YA TABBATA GA UBANGIJIN DA YA K’IRA WANNAN KYAKKYAWAR HALINTAR_”
Sai kawai ya juya sai da ya tura k’ofar sannan yace
“Idan kin gama abinda kike ina waje kisa a k’irani”
Muhabbat batayi magana bah, sai dai kawai ta girgiza kai tayi murmushi….
*****
Wai kai Kamal meke damunka? kake had’a kaya haka ina zaka?”
“Humm Mom kenan wallahi zan koma Port-Harcourt ne yanzu”
“Bangane zaka koma port yanzu bah toh ina Hameed d’in?”
“Eh wallahi Mom dama yanzu aka kira ne wai ana son nadawo yau d’in nan, shi kuma Hameed maybe sai ranar Monday zai koma,na kirashi na gaya masa”
“Kai Kamal bana son karya na sanka da k’arya bari na kira Hameed d’in naji”
“Kai Mom ai ba sai kin k’ira Hameed bah.*MATAR MUTUM*
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 12_
Mom wayarta ta d’auka ta danna number Hameed cikin sa’a kira d’aya ya d’aga, cikin girmamawa yayi sallama.
“Ina kwana Mom?”
“Lafiya Qlau Hameed ka tashi lafiya?”
“Lafiya Qlau Mom”
“Toh masha Allah, dama abinda yasa na kiraka ba komi bane wai yanzu Kamal ke gaya min zai koma wajen aikin shine na tambayeshi nace toh ina kake da zai tafi shi d’aya sai yace kai ba yanzu zaka tafi ba, dan Allah ka gaya min ko k’arya yake”
Hameed yayi shiru yana tunani wace amsa zai ba Mom sai can dabara tazo masa yace
“Eh Mom nasani zai tafi ni abinda yasa banbisa bah, saboda maganar auren nan but ba wata matsala Mom ki kwantar da hankalinki”
Mom tayi murmushi cike da jin dad’i had’i da gamsuwa da maganarsa tace
“Toh shi kenan Hameed Allah yayi maka albarka”
“Amin Mom toh sai anjima”+
Ai kam dama k’irjin Kamal sai dukan uku-uku yake yana tunani ko Hameed zai gaya ma Mom abinda ya faru, sai gashi bai gaya mata bah, haka ya gama had’a kayanshi sannan ya kama hanyar garin Port….
************
Hameed ne zaune shida Muhabbat suna fira d’an zaman da sukai da junansu ya k’ara sa masu soyayyar juna, Hameed ya kalli Muhabbat yace
“ ya kamata Dr ya sallameki saboda maybe yau su Dady zasuje gidanku zasu kai kud’in magana, so yanzu bari nayi ma Dr magana, koh Amaryarta?”
Muhabbat tayi murmushi ta rufe fuskarta da hannuwanta, shima haka yayi murmushi ya fita wajen Dr.
Bai jumabah sai gashi ya dawo, yana zuwa yace ta taso su wuce gidan, haka suka nufi gidan suna zuwa suka had’u da Abba dai-dai lokacin da zai d’auki kekenshi ya fita cikin sauri Hameed yayi parking tare suka fito shida Muhabbat, cikin girmamawa ya gaida Abba sai da suka gama gaisawa kafin Hameed ya fara yimasa maganar abinda ya kawoshi yace
“Dama Abba Dr ya sallamemu kuma dama mahaifina yace nagaya maka yau insha Allahu za’a kawu kud’in neman auren Muhabbat”
Abba yayi shiru na wani lokaci sannan ya dube Hameed yace
“Toh yaron ba zance maka eh ba kuma bazance a’a bah dan haka sai na shiga nayi ma mahaifiyarta magana idan ta aminci toh shi kenan idan bata aminci bah, toh sai dai kayi hakuri”
Hameed yayi shiru yana tunani maganar Abba, anya kuwa Abba Inna zata barshi ya aminci da maganar auren nan, toh Allah gamu garika duk cikin zuciyarsa yake wannan maganar, cikin murya kasa-kasa yace
“Toh Abba kashiga ka gaya mata ina nan ina jiranka kafito”
Abba baiyi magana bah yajuya ya shiga cikin gida, yana zuwa ya samu Inna zaune a tsakar gida Muhabbat na gefenta zaune, Abba ya tsuguna gaban Inna kamar mai neman ga fara yace
“Mairo dama yaron nan ne yazo man da wata magana wai yanaso ya aure Muhabbat shine nace mashi toh bari nazo na gaya maki idan kin aminci shi kenan idan kuma baki amince ba, sai a fasa”
“
Inna tayi shiru sai can ta tuna wani abu sai tayi murmushi tace
“Kai madalla abu yayi kyau toh yaushe zasuzo?”
“Yace min kamar yau zasuzo”
“Toh ai tafiya kasuwa ya faso, sai ka bari suzo”
Abba yace
“Toh shi kenan bari na gaya mashi suzo”
Ya tashi jiki na rawa ya fita, inda yabar Hameed nan ya sameshi tsaya yace mashi ba matsala suzo.
Hameed yayi murna sosai, sannan ya shiga motarshi ya tafi tun yana mota yakira Dady ya gaya mashi…..
*****
Haka su Dady sukaje gidansu Muhabbat gaskiya ba laifi Abba yayi masu tarba mai kyau nan suka yanke shawarar bikin nan da wata biyu masu zuwa insha Allah. Abinda yaba mahaifan Hameed mamaki bai wuce ganin Abban Muhabbat shi d’aya ya tare su.
Bayan barin su Dady gidansu Muhabbat, ai suna tafiya Inna ta d’auki mayafinta sai gidan baba Lami, ai kam tana zuwa ta bata labarin an kawo kud’in neman auren Muhabbat, Lami tace
“Wannan shegen yaro kice sai da yakawo kud’in neman auren wannan shgeyar yarinya”
“Humm kedai kawai ki bari ai indai akayi wannan auren shi kenan asirina ya gama tunuwa, gashi maganar wannan bokan ma shiru ba wata magana gaskiya ne zan sake wani boka wanda zai man aiki sha yanzu magani yanzu”
“Haba Mairo me kike tauna na baka na zuba, ai karkiji komai aikin bakon nan nayi, ai wannan alkawari danayi maki kenan wannan auren bazai taba zama gaskiya ba saida suyishi a mafarki dan ubansu”
“Toh shi kenan Lami gashi yanzu dai ansa biki nan da wata biyu masu zuwa”
“Humm ai kafin sannan ya manta da yana k’iyama”
Dukkasu sukasa dariya nan sukaci gaba da hiransu ta rashin tsoron Allah…….
*****************
*BAYAN KWANA BIYU*
Allah sarki yau ne Hameed zai koma garin port Harcourt Minal duk ta damu sai hawaye take, tace
“Yaya yanzu in katafi sai yaushe kuma zaka sake dawowa?”
A hankali Hameed ya zage zip d’in jakarshi sannan ya zauna kan gado dai-dai inda Minal ke zaune, yayi murmushi sannan yace
“Humm Minal dama haka kike sona da yawa? so dan haka ki kwanta da hankalinki ai bazan d’auki wani time bah, zan dawo kinsan ba’asa bikin nan da nisa bah, zan dawo biki na d’auki Amaryarta na kama gabana, yauwa karki manta ki dinga kulla min da matata kinji koh my sister?”
“Toh Yaya naji Allah ya saukeka lafiya but Yaya don Allah ka dawo da wuri, so yanzu zaka biya kayi ma Muhabbat bankwana koh?”
“Ah!! abinda yazama dole, ai dole naje naga fuskar matata kafin na tafi, bari ma kiga na tashi naje”
Hameed ya mike ya d’auki key d’in motarshi ya fito falo yana zuwa ya ci karo da Dady, yace masa
“Toh ina zuwa koma?”
“Humm wallahi Dady dama inaso nayi ma Muhabbat ban kwana kafin na wuce”
“Ok ai haka nada kyau sai kadawo….”
Hameed ya nufi gidansu Muhabbat yana zuwa ya tura yaro a kirata ba’a b’ata lokaciba sai gata tafito, tana zuwa Hameed ya bud’e mata k’ofar mota tayi tsaye tak’i shiga saida taga ya 6ata rai kafin ta bud’e ta shiga, ta zauna.
“Yaya ina wuni?”
“Lafiya, ya kike?”
Muhabbat tayi shiru bata amsa bah, Hameed ya juyo sosai yana kallonta sannan yace
“Dama Muhabbat abinda ya kawoni inaso na gaya maki yau zan koma Port Harcourt hutuna yak’are insha Allah da lokacin biki yayi zandawo”
Allah sarki, take Muhabbat hawaye ya fara fita daga idonta ta kasa magana, Hameed yace
“Ya salam Muhabbat me yakawo kuka kuma? wallahi Muhabbat I promise u zan dawo ki daina kuka matata”
Sai kawai ta kara fashewa da kuka sosai, kanta ya d’ago yana kallonta cikin murya kasa-kasa kamar mai jin barci yace
“Muhabbat bakya so na koma wajen aikina ne? toh shi kenan idan bakya so zan hakura na zauna”
Muhabbat ta girgiza kai hawaye yacigaba da fitowa a idunuwanta”
“Toh gaya min kukan me kike?”
Cikin shashekar kuka tace
“Yaya wallahi yanaji a jikina kamar in ka tafi bazaka dawo b…”
“Haba Muhabbat ya kike irin wannan magana kamar baki da tawalkali? ai Muhabbat insha Allah sai naga yayana dani dake koh matata”
Hameed ya katseta da sauri yayinda ya d’aura d’an yatsansa kan lip d’inta, Muhabbat taji kunya ta rufi idonta, Hameed ya kuma cewa
“yanzu me kike buk’ata?”
Da sauri ta furta
“Ba komai ina maka addu’a Allah ya maidoka lafiya”
Sai kawai ta sake fashewa da kuka ta rike hannunshi tace
“Dan Allah idan kaje karka manta dani in ka samu ‘yan matan fatakwal ” Hameed dariya ta bashi yanda ta kira sunnan garin yace
“Ina!! ai ba zan manta dake bah ai ke TAWA CE Muhabbat kiyi hakuri yanzu zan wuce kar nayi missing jirgina”
Da kyar ya shawo kanta ta hakura.
Ya ciro kud’i masu yawa ya bata sannan ya koma gida….
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 13_
Hameed yana zuwa gida bai sake 6ata lokaci ba, sukayi ban kwana da su Dady da Mom sannan yafito driver ya d’auke shi ya kaisa airport….
★★★
★★……°•°•°•°•°•°•°°•°°•
★
Muhabbat duk ta damu da tafiyarsa, saboda tana tunani kamar in yatafi bazai dawo bah, gida ta shiga amma da ka ganta kasan tasha kuka, tana shiga Inna tace,
“Toh!!! lafiya koh anyi mutuwa ne?”
Muhabbat ta girgiza mata kai tace
“A’a Inna dama wai yaya Hameed ne zai k’oma fatakwal wajen aikinshi shine yazo mukayi sallama”
“Au dan yakoma wajen aikinsa shiyasa kike kuka? toh ai sai ki bishi bama sai an d’aura auren bah, dama ai ba kanku farau ba ai duk soja dan iska ne”
Muhabbat tayi shiru tana kallon Inna saboda maganar da take ta fad’i mata, tana tsaye sai ga Lami ta shgo Inna tace wa Muhabbat maza ta d’auki talla ta tafi haka Muhabbat ta d’auki talla ga ba kwari a jikinta, bayan fitarta Inna ta kalli Lami tace
“ ‘Yar uwa sannu da zuwa dama yanzu nake so naje wajenki”
“Toh tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba, me yafaru?sha faman”
“Humm dama ai tatsuniyar gizo ai bata wuce ta k’ok’i, wannan d’an iskan yaron nan ne wai yau ya koma wajen aikinshi, Lami taso dan Allah kiyiwa boka magana kada yaron nan yasake dawowa cikin garin nan”
“Haba Mairo sau nawa zanyi maki magana wallahi aiki bokan nan nayi ai ina gaya maki yanda Hameed yabar cikin uwarshi toh haka yabar garin Katsina”
“Hahaha Lami wai zanga wannan lokacin dama likita yace tana da ciwon zuciya kinga da taji maganar mutuwarshi shi kenan itama zata bishi, amma fa bansan mutuwarta yanzu domin kuwa tana nema min kud’i”
“Ke dai kika sani aike shegiyar uwace da ya’yan kanya”
Sukayi shewa suka ta6a.
+
********
Jirgin su Hameed ya isa garin port Harcourt lafiya bayan sun sauka, wayarshi ya d’auka ya kira wani yaronshi, soja ne yace yazo yanzu ya d’aukeshi yana airport, ba’a 6ata lokaci ba yazo ya d’aukeshi barrack suka nufa direct yana zuwa ya aje shi k’ofar gidansu, yana kallon k’ofar yaga alamar takalmen Kamal, kawai sai ya d’aure fuska yana bud’e k’ofar d’akin Kamal na kwance saman kujera 3 seaters, Hameed ko ya kalli inda yake kawai ya wuce abinshi, a hankali Kamal ya d’aga kai ya kalli Hameed amma ya kasa yayi masa magana sai kawai yacigaba da d’anna wayarshi, Hameed bedroom ya nufa ya aje jikarshi sannan ya cire kayan jikinshi ya shiga toilet dan watsa ruwa yayi alwala ya tafi masallaci, yana fitowa yaga Kamal inda ya sameshi zaune, da sauri Kamal ya tashi yace
“Sannnu da zuwa yanzu ka iso kenan but baka kira ni bah”
Hameed ya d’aga kai ya wurga mashi harara yayi tsok’i yayi fitarsa abinshi , Kamal yaji haushi sosai.
Inda Hameed yabar Kamal nan ya sameshi da alama koh sallah bai yi bah, Hameed yace
“Humm mutum dai ya dai ji tsoron Allah saboda wallahi wannan duniyar bacikinta zamu dauwama bah, kar atashi ai sallah a zauna latsa waya”
Bai tsaya yaji amsarshi ba yayi gabah abinshi, lokacin kwanciya yayi Kamal ya shiga bedroom toilet yanufa yayi wanka sannan yafito kayan bacci yasa duk Hameed na kallonshi sai da yagama sannan yanufi gado zai kwanta yana hawa Hameed da sauri ya d’auki fillo d’in da ya tada kai ya nufi falo, Kamal abin dariya ma yabashi.
Bayan dawowar Hameed falo kenan sai ga kiran Dady ya shigo a wayarshi, da sauri ya d’aga cikin girmamawa.
“Hello Dady ina wuni?”
“Lafiya Qlau my son, ya kun isa lafiya?”
“Lafiya Qlau Dady ya Mom?”
“Gata a kusa dani”
Sai da Dady yaba Mom suka gaisa kafin ya kashe wayarshi,Hameed yayi addu’a ya kwanta barci…
Washe gari
Bayan dawowarshi daga masallaci sallar asuba, bai koma ya kwanta bah kitchen ya nufa direct yasa ruwan zafi tea, sannan ya shiga bedroom dan ya watsa ruwa saboda yau zai koma aiki, yana shiga ya samu Kamal ko juya kafad’a bai yi bah, Hameed ya girgiza kai yace
“Allah ya shiryika asuba tayi but mutum bazai iya tashi yayi sallah bah. Hameed yana rufe baki ya shiga toilet abinshi, sai da Hameed ya kusan gama shirinshi kafin Kamal ya tashi daga barci,
Hameed ruwan tea kawai yasha ya d’auki key d’in motarshi ya fita, Kamal fad’i yake
“A’a katsaya mana nima nagama mufita tare”
Ai Hameed baima san yana yiba, yashiga mota yayi tafiyarshi office.
Yana zuwa office yasamu har ancika saboda yau antashi garin MAIDUGURI ba lafiya , yanzu-yanzu za’a kwashi sojjoji zuwa maiduguri, yana zuwa commanda, yace masa
“Yauwa Major Hameed kai zaka wuce dasu zuwa maiduguri because no one can do this work like u, aikin nan dole sai kai Hameed, but yau d’in nan zaku wuce, dan haka ka koma gida ka shirya”
Allah sarki Hameed yana yinshi har ya sauya yace
“Am sorry sir duk ga manyana nan sir ai ya kamata asa wani wanda zai kula dasu”
“Hameed are u mad? ina magana kanace min, a’a so ba wanda zansa , sai kai because riqo da addininka yasa har na tabbata zaka kula dasu kuma yanzu maza ka koma gida ka had’a kayanka kuwuce yau d’in nan!.”
Ogansu yana gama magana yajuya yafita, sojjojin da aka za6a zuwa maiduguri sukasa ihu sukace.
“Yauwa munji dad’i da aka had’amu da major Hameed because zai bamu goyan baya d’ari bisa d’ari”
Hameed kasa magana yayi saboda haushe, gashi d’aga dawowarshi, jiya-jiyan nan yanzu har ansa sunanshi zuwa Maiduguri, ga maganar aurenshi da Muhabbat, hawaye da zasu zo6o mashi ne yayi sauri ya sharesu, wata Zuciyar tace
‘Haba mazan fama kada kaba maza kunya mana kaifa jarumi ne’
Fitowa yayi ya d’auki motarshi ya koma gida, har yanzu Kamal bai gama abinda yake bah, yana zuwa yasamu Kamal kan kujera yana sa boot d’inshi, Hameed naso ya gaya mashi amma ya kasa, bedroom ya nufa ya d’auki Biro da takarda yayi rubutu sannan ya fito, ya aje masa kan kujerar da yake zaune, sannan ya koma bedroom had’a kayanshi..
Kamal ya d’auki tardar ya bud’e, ga abinda ke cikinta…
*ASSALAMU ALAIKUM*
Da farko dai maganar da zan fara yimaka itace Kamal kaji tsoro Allah, a koda yaushe ka sani duniyar nan ba madauwama bace, Kamal ka natsu ka komama Allah tun kafin yayi fushi da kai, ni yanzu ansa sunana zuwa Maiduguri bansani bah koh Allah zai sake had’amu, sannan kuma wallahi yanzu duk laifin da kayi min nayafe maka sai dai kuma ka rok’i Allah ya yafimaka, dan Allah ko bayan ba raina kar kayi ma Muhabbat!!! d’ita komai indai bah taimakonta za kayi bah, kuma dan Allah ka kula da iyayena, sannan uwa uba Kamal ka kula da sallah …. na barka lafiya daga dan uwanka Hameed Abubakar mai Changi…….
Allah sarki sanda Kamal ke karanta takardan nan hawaye ya fara fita daga idonshi saboda maganan da yaji Hameed yayi mashi, zuciyarshi ta karaya, Mek’ewa yayi ya nufi bedroom, koh da shigarsa yasamu Hameed har ya d’auki jakarshi, Kamal ya fad’a jikin Hameed, ya fashe da kuka yace
“Hameed dan Allah kayi hakuri da abinda ya faru kuma I promise u from today, duk wani abu da nake na daina insha Allah kuma yanda katafi lafiya haka zaka dawo lafiya”
Hannu Hameed ya d’auka yana buga bayan Kamal yace
“Is ok Kamal ya isa haka, Kamal na yafe maka inaso yanzu ka taya ni da addu’a, sannan dan Allah kar kayi ma Muhabbat d’ina komai”
“Humm Hameed kenan wallahi bazanyi mata komai bah, yanda ka barta haka zaka dawo ka sameta Lafiya da yarda Allah ”
“Yauwa my friend thank u very much, mutafi ka sauki ni a office because nasan yanzu mutanen na jirana”
Allah sarki ni kaina sai da hawaye ya zubu min na tafiyar Hameed Maiduguri
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 14_
Suna cikin mota Hameed ya
d’auki wayarshi ya kira Dady ya gaya mashi koda Dady yaji haka, hankalinshi yatashi sosai amma Hameed sai yanuna mai ba wata matsala sudai tayashi da addu’a kawai, Dady yaba Mom haka itama tayi mashi addu’a sosai, sannan ya kira Minal yace maza ta kaima Muhabbat zaiyi magana da ita, Minal bata 6ata lokaci bah ta isa gidansu Muhabbat tayi sa’a bata fita talla bah, Minal tayi sallama Muhabbat ta amsa, tayi mamakin ganinta, sai da suka gaisa kafin ta danna wayarta ta kira Hameed, ringing d’aya ya d’aga Minal tayi sauri taba Muhabbat haka ta amshi wayar yau ce rana ta farko da Muhabbat ta fara rike waya a rayuwarta..
“Hello Muhabbat kina jina yakike?”
“Eh Yaya ina jinka lafiya Qlau ya aiki?”
“Lafiya Qlau matata da fatan baki tare da wani problem”
Kai ta d’aga masa tamkar yana kallonta, magana yacigaba da ita
“So idanma kina da Matsala kiyi ma Minal magana zata gaya min, sannan magana ta biyu yau zamu wuce Maiduguri, inaso ki tayani da addu’a Allah yamaidomu lafiya kinji my wife?”
Inda Muhabbat ke tsaye nan tayi mutuwar tsaye sai hawaye kawai ke fita d’aga idonta, Hameed shiru yaji tayi a hankali ya rage murya yace
“Muhabbat kuka kike kinaso natafi cikin 6acin rai, bakya so na tafi ina tunanin kyakkyawar fuskarki, haba Fulani matata kuma uwar ya’yana insha Allah sai munga yayanmu nidaki, dan Allah kiyi min magana ko zuciyata zatayi sanyi”
Wata irin ajiyar zuciya tayi saboda yanda tayi ajiyar zuciyar sai da tsigar jikin Hameed tatashi saboda har cikin kanshi tashiga saboda da a gabanshi tayita toh gaskiya da anyi abu..
“Toh Yaya Allah yatsare hanya yabada sa’a amma Yaya inajin wani abu a jikina Yaya kamar in katafi bazaka dawo bah…”
“Haba Muhabbat ya kike irin wannan magana, addu’a kawai nake buk’ata kinji koh?”
“Toh Yaya dan Allah idan kaji ka dinga tunawa dani, kasan kai ne gatana”
“Oh my wife abinda yazama dole, insha Allahu bikinmu saura sati biyu zandawo naga matata daga nan in anyi bikin zan maidake makaranta”
“Da Gaske yaya?”
“Allah, so yanzu zan barki mutane najirana dan naga alama kina so ki hana ni aikina, sai munyi waya zan kira Minal sai ta kawu maki”
“Toh Yaya nagode, amma ka sani zanyi kewarka”
Ido Hameed ya lumshe a hankali ya bud’e ya furta
“Muhabbat da gaske zakiyi kewata”
Fuska ta rufe cikin jin kunya ta kasa magana, dariya yayi ya kashe wayarshi yana mai tunani Muhabbat d’inshi.
Mutane duk sun taro, kusan sojjoji guda 100 aka kwasa zuwa Maiduguri kuma duk Hameed ne ogansu shi zai kula dasu, Kamal bai tafi ba saida yaga su Hameed suntashi, yayi kuka kamar ba gobe, saboda yaso ace shi akasa bah Hameed bah….+
Muhabbat sun danyi fira da Minal kafin ta rakata har bakin titi bayan fitarsu Inna tayi dariya sosai tace
“Ai yanda ka tafi Maiduguri toh, insha Allahu sai dai a kawo gawarka, garin nan”
*****
*GARIN MAIDUGURI*
su Hameed sun sauka garin Maiduguri lafiya inda aka d’aukesu aka kaisu wani kauye a *DAMBUWA* kauyan na kusa da bodar Cameron, nan fa suka yada zango..
*Washe gari*
Inna sai gidan Lami dan ta bata ruhoto, Inna na zuwa tace mata, yau sai sun koma wajen boka dan kar Hameed yakai labari, haka sukaje wajen boka, yayi masu albishir da shiyasa aka kai Hameed Maiduguri, kuma Hameed ya gama rayuwa a duniya….
Hummm boka kenan ai ka manta bakai bane Allah kuma MATAR MUTUM kabarinshi idan Allah yace Muhabbat matar Hameed ce ba wanda ya isa yahana.
Allah sarki Kamal duk ya damu kamar anyi mashi mutuwa, saboda rashin abokinshi kusa dashi, Kamal ya natsu, ya daina duk abinda yake, zaune yake kan sallaya, yana lazimi hawaye sai fita yake a idonsa, abin tambayar bansan kukan da yake bah,ko kukan me yake oho sanin gaibu sai Allah,
a filin kuwa abinda yake fad’i cewa yake
“Gaskiya dole naji na samu Muhabbat na bata hakuri kan abinda ya faru, gaskiya ban kyauta bah, ashe ada ina cutar rayuwata, duk abinda Hameed ke gayamin gaskiya ne, Allah sarki abokina naso ace kana kosa dani na gyara halina”
Sai kawai ya fashe da kuka,sai da yaci kukanshi ya gaji kafin yatashi yayi Shiri zuwa office….
Itama Muhabbat duk ta damu da rashin masoyinta, saboda duk ta rame dama abinku da fulani da k’aramin jiki, Inna tana jin dad’i ganinta haka gashi kwana biyu bataji islamiyya bah, ballatana taji d’aga bakin Minal ko suna waya da Hameed, haka ta d’auki talla ta tafi badan ranta nasobah, amma koda yaushe da tunanin Hameed take kwana take tashi…
*****
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah yau watan Hameed d’aya da sati biyu kenan, a Maiduguri sai dai kash!!! tunda Hameed ya tafi ba labari, hankalin Mom ya tashi sosai hakama Dady saboda rabunsu da suji muryar Hameed tun ranar da ya kirasu yace gashi ya isa garin Maiduguri Mom ce da Dady zaune a falo suna magana mom tace
“A gaskiya Alhaji ya kamata musan halin da yaron nan yake Alhaji hankalina ya tashi, gashi bikin nan yau saura sati biyu, Alhaji ya zamuyi yanzu”
“Haba Saratu ki daina kuka mana kinaso hankalina ya tashi, haba Saratu da wani zanji? Ki kwantar da hankalinki insha Allah ba abinda ya faru da Hameed, yanzu zan kira Kamal inji d’aga bakinshi”
“Yauwa Alhaji dan Allah ka kirashi muji abinda ya faru da Hameed d’ina…”
Dady wayarshi ya d’auka ya danna ya kira Kamal, cikin girmamawa Kamal ya d’auki waya ya gaishe da Dady, Dady ya amsa bayan Dady ya amsa sai yayi shiru jim kadan yayi ajiyar zuciya yace
“Kamal inaso ka gaya man me yafaru da abokinka? idan na kira numbershi baya zuwa”
“Allah sarki Dady maybe nan Katsina kuna da Matsala network amma ko yau manyi waya dashi yananan lafiya Qlau”
“Humm Kamal kenan nifa ba yaro bane dan Allah ka fito fili ka gaya man, gaskiya nifa musulmi ne na yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau wallahi duk abinda ya faru da Hameed na yarda da kaddara zanyi mashi addu’a”
Allah sarki Kamal kuka ya fashi dashi kamar karamin yaro yace
“Gaskiya ne dady bama waya da Hameed tun ranar da ya isa gari Maiduguri rabon mu da waya, naje office nayi binciki sai dai Dady yanda rahoto ya nuna man cewa, inda su Hameed suke ankai masu hari bomb ya tashi a wajen…”
“INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIRRAJI’UN shi kenan Hameed Allah yaji kanka”
Wata uwar k’ara Mom ta fasa tace
“Alhaji Hameed d’in ne yarasu wallahi karya ne Hameed d’ina bai mutu ba, saboda naji a jikina Hameed yana duniya, insha Allahu sai naga ya’yan Hameed a duniyar nan”
“Haba Saratu ya kike irin wannan maganar karki manta kefa musulmace ki yarda da kaddara mana”
“Toh Alhaji yanzu shi kenan alkawarin da ya daukarwa Muhabbat ba rabon ya cikashi, Allah sarki Muhabbat na tausaya maki Inama ace inada wani d’an da sai ya aureki, Hameed shi kenan ya tafi ya barmu…”
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 15_
Saratu karki damu indai wannan ne, ai ga Kamal nan na tabbata Kamal zai cikama abokinshi burinshi”
“Shi kenan Allah yajikanka Hameed”
Suna cikin kuka haka Kamal yasake kiran Dady da sauri Dady ya d’auka
“Ina jinka Kamal ya ake cikin?”
“Toh Dady yanzu dai gani a office din commander yace min missing in action, so ba’a ganshi ba”
“Oh my God yanzu kenan bama a ga gawarshi bah?”
“Eh dady addu’a kawai ya kamata muyi wa Hameed ”
“Toh shi kenan Kamal mungode”
“Toh Dady gobe insha Allah zan kama hanya nazo muyi magana”
“Toh Allah yakaimu”
„Amin”
Haka Kamal ya kashe wayarshi, Dady yace bari yaje yasamu mahaifin Muhabbat ya gaya mashi abinda ya faru, haka yafita ya tafi gidansu Muhabbat….
Dady gidansu Muhabbat ya isa yana zuwa yayi sa’a Abba zai tafi kasuwa, sai da suka gaisa kafin Dady yayi mashi bayanin abinda ya kawoshi, duk abin Abba saida yaji ba dad’i, gida ya shiga yana zuwa ya gayawa Inna abinda yafaru, Muhabbat inda take hawaye ya fara fita d’aga idonta, sai da Abba ya juya yafita, kafin Innah ta kece da dariya harda ihu tace
“Wanda baiji bariba yaji ohoho yau duniya tayi man dad’i abinda nad’e ina jira yasamu yau Hameed yazama gawa”
Da sauri Muhabbat ta d’ago kai tana kallon Innah, saboda abin mamaki yake bata”
‘Na shiga uku! kardai ace Innah ita ta kashe Ya Hameed na shiga uku shi kenan ya Hameed ya barni dama shi yayi niyyar taimakona’
Muhabbat duk acikin zuciyarta take magana, dadai taga kuka bazayi mata komai bah buta ta d’auka tayi alwala tayi sallah….+
*GARIN MAIDUGURI*
kwance yake bai san inda kanshi yake bah cikin dajine sosai ba mutane ko alama sai kukan tsuntsaye sai iskan sararin samaniya, ana cikin haka sai ga wani bafulatani zai wuce, ya ganshi kwance a kasa da sauri bafulatanin nan yadawo, abinku da Fulani da tausayi, da sauri ya d’aukeshi ya sashi cikin keken shanu, da alama shi ba Fulani Nigeria bane Fulani Cameroon ne, aikam hanyar boda ya nufa direct yak’etara bodar Cameroon wani kauye ya nufa dashi mai suna bonheri kauyen dukka fulani ne, yana zuwa wata kyakkyawar mata tazo ta tareshi matar atatarta bazata wuce shekara 40 bah, matar masha Allah, a cikin harshen fulatanci tayi mashi magana.
“Baffa ja6ma”
“Yauwa FADIMA”
“A’a baffa bak’omu kayi gidan?”
“Wallahi Fadima kingashi a dawa na d’auketa gata nan kamar ta mutu bah rai, amma bari yanzu zan mata magani zata tashi da yardar Allah…”
*GARIN KATSINA*
Yau Kamal ya iso garin KT lafiya, amma da kaganshi kasan yana cikin damuwa, bai nufi gidansu bah gidansu Hameed ya nufa direct, yana zuwa ya samesu zaune a falo, ai kam yana yin sallama Mom ta fashe da kuka, da sauri yakarasa wajen Mom ya duka shima kukan ya fasa, Mom tace
“Kamal kaga yanda Allah yayi damu ko? Kamal ashe ba rabon naga auren Hameed, alkawarin da ya d’auka ba rabon ya cikashi”
“Mom don Allah ki daina kuka insha Allah komai zaizo da sauki”
“Toh shi kenan Kamal amma inaso yanzu ka d’aukar min wani alkawarin”
“Toh Mom insha Allah kowane alkawarin ne zan maki”
“Toh Kamal dama ba komai bani illa inaso alkawarin da abokinka ya d’auka zai aure Muhabbat tunda yanzu baya duniyar inaso yanzu Kamal ka amshi aure Muhabbat!!!!!”
Da sauri Kamal ya zaro ido yace
“Mom ai wannan bazai…..”
“Dakata Kamal kaidai kayi min alkawarin, dan haka yanzu magana ta wuce insha Allahu lokacin bikin da akasa baza’a d’aga ba”
Sai yanzu Dady yayi magana yace
“Gaskiya ne Kamal nima na yanke wannan shawarar akan ka cika ma abokinka burinshi na auren Muhabbat dan Allah in bazaka damu bah”
Kamal shiru yayi yana tunani maganarsu Dady
‘Ya za’ayi na aure Muhabbat bayan na so na cutar da rayuwarta ai nasan Muhabbat! kanta bazata yarda bah, saboda nasan yanzu Muhabbat ta tsaneni sosai’
“Kamal ya kayi shiru muna magana?”
“Na’am Dady toh Dady zanyi tunani a kan maganar”
“Kamal listen to me! ya kamata kayi tunani mai kyau, wai ba dan komai bah mukace ka aure Muhabbat sai dan ceto, yarinyar d’aga cikin halin da take ciki”
“Toh shi kenan Dady ba damuwa na aminci Allah yamabu sa’a but ina tunani Muhabbat bazata aminci bah, dana zama mijinta!!?”
“Da sauri Mom tace
“Haba Kamal ai nasan Muhabbat zatayi murna da wannan maganar”
“Haka ne Saratu idan anjima zanje nasamu mahaifinka sai muje ayiwa mahaifin Muhabbat d’in magana, dan haka tashi kashiga d’akin d’an uwanka kaje ka huta, Allah yayi maka albarka”
“Amin Dady”
Kamal ya tashi yashiga bedroom d’in Hameed kan kujera ya zauna yana tunani yanzu tayaya zai aure Muhabbat alhalin babu soyayya a tsakaninsu yasan ko ya auren Muhabbat bazata tabba sonshi bah saboda abinda yayi mata.
‘A gaskiya ada na cuci rayuwata, gashi Muhabbat macece da kowani namiji zai sota, kai bama wannan bah yanzu su Dady da suke cewa na aure Muhabbat idan Hameed bai mutuba fa? in yazo da wani ido zan ganshi kai this is impossible’
Kamal ya buga hannunsa saman kujera dai-dai lokacin da yagama maganarsa a zuciyarsa, Minal ce ta turo k’ofar d’akin a hankali, da sauri ya d’aga kai ya kalli Minal, ta saba da tashigo ta fad’a jikin Hameed, toh yau ma haka ta shigo da gudu ta fad’a jikin Kamal.
Ji yayi tsakar jikinshi tatashi wani yar!!!! A hankali yace
“Minal miye haka?”
“Toh Yaya Kamal oyoyo nazo nayi maka”
“Humm Minal haka ake oyoyo sai an fad’a jikin mutum”
“Oh sorry ya Kamal wallahi nasaba da yi wa ya Hameed”
“Da sauri Minal ta 6ata fuska kamar zatayi kuka tace
“Ya Kamal wai da gaske ya Hameed ya rasu? ni fa har ga Allah ban yarda Yaya Hameed ya mutu ya barni ba”
Tanayin tambayar dai-dai lokacin da hawayen da ke idonta ya sauka, da sauri Kamal ya d’ago kanshi yana kallonta cikin murya kasa-kasa yace
“Waya gaya maki haka?”
“Humm ya Kamal kar kayi min karya ai Mom ta gaya min komai”
“Minal bamu da tabbas Hameed ya mutu saboda cikin wanda a kaga gawarsu bata Hameed aciki, dan haka ki daina kuka”
“Kamal yasa hannunsa yana goge ma Minal hawayen idonta har ya samu tayi shiru.
Haka suka dinga fira da ita tana bashi dariya
*BAYAN SATI DAYA*
Bafulatanin da ya d’auki Hameed yanayi mashi magani, hankalinshi ya tashi sosai saboda yau satin Hameed d’aya a kwanci tunda aka kawoshi koda d’an yatsanshi baiyi motsibah. Matar da ke gidan ya duba yace
“Fadima kina ganin wannan yaron tana da rai kuwa?”
“Baffa tana da rai da yardar Allah, yanzu me zamu bata tatashi?”
“Yauwa d’auko man magani nan a bata”
“Toh baffa”
Fadima tatashi ta shiga d’an d’akinsu ta d’auko magani ta kawowa Baffa, ya amsa ya d’aga kan Hameed yana bashi, Fadima tace
“Baffa kasan wani abu wallahi Baffa tunda yaron nan tazo gidan nan nake jinta a jikina kamar nasanta”
“Toh ai dama hakane Fadima akwai wanda zakaji kana sonshi a rayuwarka”
Yana gama maganar ya kwantar da Hameed, suka tashi zasu fita, ai kam hameed yafara nishi da sauri Fadima ta dawo, nan fa Baffa ya farayi mashi addu’a, can sai ya fara ajiyar zuciya yana bud’e idanuwanshi a hankali ai kam yana bud’ewa wanda ya fara had’a ido da ita sai Fadima da sauri ya bud’e baki yana nunata da d’an yatsanshi yace
”MA!!!!!!!!!!!!…”
Toh masu karatu wai dan Allah wacce mata ce wannan? tsaya muga suwa ke da Basira cikin masu karatu…
*MATAR MUTUM*
*
_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 16_
Hameed ya bud’e baki yace
“Muhabbat!!”
Da sauri Fadima ta d’aga kai ta kalleshi cikin firgita, tace
“Muhabbat kuma yaro kai d’an Nigeria ne dama? Muhabbat d’ina nada rai bata mutu bah? Yaro kiyi hakuri kiyi man bayani don Allah”
Hameed ajiyar zuciya yayi mai k’arfi sannan ya lumshi idanunshi, sai da ya d’auki wani lokaci kafin ya bud’e idonsa, sannan ya d’aga mata kanshi alamar eh.
“Yanzu dama Muhabbat na duniya Mairo bata kashe taba? shi kuma malam koya biyo sawona, toh amma ya akai ni ban sanka ba bayan ni duk zamana a garin Katsina bansan malam nada ‘yan uwa masu kud’i bah, kuma gaka da alama kai soja ne”
“Eh ni soja ne kuma ni ba d’an uwansu Muhabbat bane ni mijin da zan aure tane insha Allah, mama dama kece mahaifiyar Muhabbat?”
“Eh yaro nice”
“Amma Mama meyasa baki d’auki d’iyarki kun tafi tare bah, meyasa duk tsawon lokacin nan baki koma bah?”
“Humm yaro maganar mai tsawoce zanyi maka bayani in kasamu sauki, Allah yabaka lafiya”
“Ameen”
Duk wannan magana da suke Baffa na tsaye yana jinsu…+
***********
*Washe gari*
Dady ya shirya ya tafi gidan mahaifin Kamal, bayan sun gaisa Dady yayi mashi bayanin abinda ya kawoshi, mahaifin Kamal yayi murna da jin magana yace Allah yasa haka shine mafi alkairi ameen, Dady yace toh su wuce gidansu Muhabbat tare don suyi wa Abba bayani, gaba d’ayansu suka tashi suka fito mota suka shiga sai gidansu Muhabbat,
Yauma sunyi sa’a Abba bai tafi kasuwa bah, Abba yayi murna da ganinsu sosai nan fa suka gaisa kafin Dady ya gabatar da abinda yakawosu, Abba yace
“Toh ai ni Alhaji banida wata magana duk abinda kukace ai yayi bah Matsala”
Dady yace
“Toh shi kenan dama bikin yanzu yanda aka sashi saura sati d’aya, toh haka za’a barshi baza’a d’aga bah, dama Allah yayi Kamal shine mijin Muhabbat, dama hausawa sunce *MATAR MUTUM* kabarinsa.
“Haka ne Alhaji”
“Toh yanzu idan kashiga kayiwa ita Muhabbat d’in bayanin”
“Toh mungode”
“Haka su Dady sukayi masa sallama suka tafi gida abinsu, shi kuma gida ya shiga yasamu Inna yafara gaya mata abinda yafaru Muhabbat na gefensu zaune, Abba yana gayawa Inna zufa na sauka a jikinta, yayin da Muhabbat hankalinta ya tashi sosai sai hawaye ke bin idonta, Abba yana gama magana yajuya ya fita, ai kam Inna tamike tsaye tana fad’in.
“Kutt ni za’ayiwa iskanci au ba’a rabu da Bukar bah an yaye Garba an haihe Abu kenan ta nan zasu billo, toh wallahi banga ta zama bah”
Muhabbat itako a cikin zuciyarta take cewa.
‘Ta Yaya zan aure d’an iska nidai wallahi bana sonka bana sonka Allah sarki ya Hameed dina….”
Sai kawai ta fashe da kuka…
****************
A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, yau saura kwana uku Muhabbat ta zama Amaryar Kamal za’a d’aura masu aure ranar asabar da misalin 2:30PM, yayin da Inna hankalinta ya tashi sosai ta rasa zaune ta rasa tsaye, haka ma Muhabbat kwatata bata son auren, ango kuwa ai ba’a cewa komai wajen murna su Minal sune k’awayen Amarya……
*****
Jikin Hameed yayi sauki sosai saboda yanzu yana tafiya ko ina, hakan yasa sukayi magana da mahaifiyar Muhabbat tare zasu komo da ita Nigeria amma yasha wahala kafin yashawo kanta ta yarda zata bishi badan komai ta yarda bah sai saboda d’iyarta, sun aji rana zasu tashi ranar jama’at sai su isa ranar asabar tunda mota zasu hau ba jirgi bah, Hameed yace wa Fadima
“Toh Allah ya kaimu ranar amma inaji a zuciyata kamar wani abu zai faru kafin ranar”
Baffa yace
“Haba ka kwantar da hankalinka ba abinda zai faru insha Allah sai alheri”
“Toh shi kenan na yarda Allah ya kaimu ranar”
“Amin..”
*******
Yau ta kama ranar Friday Hameed da Fadima zasu kama hanyar dawowa Nigeria, inda Baffa ya rakosu har tasha suka shiga motar fita dasu Maiduguri, kafin in sunje suhau motar garin Katsina, Fadima ta danyi kukan rabuwa da Baffa, sannan Hameed yayiwa Baffa godiya sosai…
Innah ce zaune a gaban boka ita da Lami sai faman kuka take masa wai ya taimaketa kada yabari ayi auren nan, Boka bud’ar bakinshi yace
“Mairo abinda zan gaya maki kadaki yarda ayi auren nan saboda idan har kika bari akayi auren nan toh duk wani asiri da kikayi ya tashi aikin daga ranar duk wani farin cikinki zai kare”
“Haba Boka yanzu ba abinda zakayi akai?”
“Hahaha akwai Mairo, mu har ance bamuda abinda zamuyi ai muke da abinyi, ga wannan idan kinje gida ki binne shi k’ofar gida, ina gaya maki da kinyi wannan anyi angama, amma kada ki bari wani ya ganki, da wani yaganki toh aikin yakare sai tayi aure, dan akwai bani babban al’amari na shirin faruwa, wannan ne kawai zai hana faruwar lamarin”
“Toh shi kenan boka mungode”
Su Innah aka fito daga wajen boka ana murna..
★★★
Su Minal k’awayen Amarya sai kaiwa da kawowa ake, zaune take a gaban Muhabbat tanata fama da ita tazo suje a gyara mata jiki saboda gata Amarya ai bata zauna haka bah, bud’ar bakinta tace
“Ni ba idan zani kwalliyar me zanyi bayan wanda zai ganta baya duniyar yanzu”
“Haba Anty Muhabbat miyasa kike fad’in haka ai da ya Hameed da ya Kamal ai duk d’aya ne”
“Humm Minal kenan bazaki ta6a ganewa bah”
“Eh nidai naji muje koda salon ne ayi maki saboda wallahi Mom tace nazo mutafi tare dake, konaje nacewa Mom kince bazaki bah?”
“Haba dai wace ni, badamuwa bari Innah tadawo sai muje nasan yanzu takusan dawowa”
Muhabbat na rufe baki sai ga Innah ta danno kai, Minal ta gaida ita kafin Muhabbat tace masu zasu fita, Innah tace ai badamuwa, saboda taji dad’in rufe maganinta.
Waje suka fito suna fita Muhabbat taga ashe da mota ma Minal tazo, jikin motar suka nufa Minal ta bud’ewa Muhabbat tashiga gaba, tana shiga taga mutum zaune amma ya kifa kanshi a steering motar ita dai tashiga ta zauna sannan Minal ta zauna a baya saida suka rufe k’ofar motar kafin ya d’aga kanshi, kirjin Muhabbat ne yabuga saboda ganin fuskar Kamal a gabanta nan danan zufa yafara binta shikam key yasa ya tada motar, suka fara tafiya Muhabbat jitake kamar tayi tsale ta fita motar sai da sukayi nisa ba wanda yayi magana kafin yace
“Minal ina zakuje salon d’in?”
“A ZAINAB SALON zamuje tafi iyawa”
“OK is good, kefa madam baki iya gaisuwa bah kin shigo ba gaisuwa.”
Muhabbat tayi shiru bata tankashi bah, kai ya girgiza yayi murmushi
‘No problem tomorrow u will be my wife’
Yayi parking dai-dai lokacin sun isa Zainab salon, suka shiga ita da Minal da yake shagon maza basa shiga sai mata kawai, suna zuwa ba mutane kuwa aka fara masu…
*RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR D’IYA TAJI KUNYA*
yau takama ranar asabar wato ranar da za’a d’aura auren *KAMAL DA MUHABBAT* da misalin 2:30PM yanzu kuma wajen misalin 11:00.AM kenan Amarya sai faman kuka take Innah kuwa ai takoma kamar mahaukaciya…
Hameed tafiya tayi nisa yanzu haka suna cikin garin Zaria saidai kash!!!!! Motarsu tasamu Matsala a hanya suna ta fanan gyara…
*GARIN KATSINA*
jama’a ‘yan d’aurin aure ancika k’ofar gidan su Dady, da yake Abba yace ba Matsala kawai a d’aura gidansu Dady ba wata Matsala shiyasa duk wanda yataho gidansu Hameed suke nufa, wayaga ango sai faman bud’e baki ake, nidai cikin gida nashiga nasamu wajen na zauna ina kallon jama’a d’aya bayan d’aya, wata tsohowa tace
“Allah sarki ba rabon ayi auren nan da Hameed, Allah yace wannan yarinyar matar Kamal ce dama ance *MATAR MUTUM* kabarinsa”
“Eh wallahi baaba”
Mom ce ta amsata, yayinda idanuwanta suka cika da kwalla, daga waje muka jiyo muryar mutane suna cewa fatiha an d’aura, ana cewa an d’aura Mom ta fashi da kuka tace
“Shi kenan yau Muhabbat ta zama matar Kamal, Allah sarki Hameed…”
Maganarta ta tsaya ne a lokacin da akayi sallama gaba d’aya mutanen dakin suka juya….
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 17_
Da sauri Mom ta mik’e tsaye muryarta na rawa tana nunashi da d’an yatsa tace
“Jama’a waye nake gani a gabana? ko mafarki nake idanuwana nanuna man ga Hameed a gabana”
Jama’ar d’akin gaba d’aya suka had’a baki sukace
“Muma abinda muke gani kenan, yanzu dama Hameed bai mutu bah kenan”
A hankali Hameed yak’araso inda Mom take ya kama hannuta ya zaunar da ita yace,
“Mom inanan da raina *BAN MUTU BAH* Allah yasa da sauran kwanana a gaba”
“Yanzu dama Hameed kana duniyar nan duk tsayon kwanakin nan?”
Sai kawai Mom ta fashe da kuka tana fad’in
“Shi kenan Hameed kazo a makare kazo a lokacin da Muhabbat ta zama matar Kamal dama Allah yayi Muhabbat bah matarka bace”
Kai Hameed ya girgiza
“Oh my God Mom please stop crying, Mom kidaina kuka ko yanzu banzo a makare bah saboda Allah yariga ya rubuta *MUHABBAT MATATA CE*”
“What! ta yaya Muhabbat ta zama matarka bayan angama d’aurin aure?”
Hameed yayi ajiyar zuciya sannan ya gyara zama yace
“Mom muna cikin garin Zaria motarmu ta samu Marsala wajen 11AM tunda muka taso a Cameroon kirjina ke bugawa har lokacin da motarmu tasamu matsala da naga motar bata da niyar gyaruwa sai muka sake mota, misalin 2:PM muka shigo nan cikin garin Katsina,wata mota muka samu wanda zai kawomu har nan k’ofar gidan, abin mamaki ina zuwa sai naga taron jama’a da sauri na k’arasa wajensu, hummm jama’ar wajen sun tsorata da ganina, bayan sun gano da gaske nine ban mutu bah sai mahaifin Kamal yace tunda na dawo bai kamata a d’aura da Kamal bah, kawai a d’aura auren dani, shi kuma Dady hakan yasa yace toh bai kamata Kamal ya tashi haka bah kawai ya bashi auran MINAL, sai kawai aka had’a aka daura auren yanzu Minal itace matar Kamal ni kuma Muhabbat itace matata”
Mutane d’akin sukace Allah mai iko *MATAR MUTUM* kabarinsa Allah dai yace Muhabbat sai ta zama matarka”
Mom ta fara share hawaye idonta tace
“Yanzu Minal aka d’aura auenta da Kamal, toh ina Minal zata iya zama gidan miji”
“Haba Mom Muhabbat ma zata iya zama gidan miji ballanta Minal”
“Toh marar kunya au kadawo ko?”
Dukka d’akin a kasa dariya, Mom takai dubanta ga Fadima tace
“Au wai harda bakuwa kake tafe?”
Da sauri Hameed ya d’aga kai saboda ya manta ma suna tare yace
„I’m sorry, Mom wannan itace mahaifiyar Muhabbat tare muka tahu daga Cameroon”
Nan Hameed duk ya basu labari abinda yafaru,Mom tayi murna sosai da ganin Fadima nan fa aka fara karramata.+
Wayaga amare basu san abinda yake faruwa bah. Muhabbat sai faman kuka take tunda taga 3: tayi tasan an d’aura auren yau ta zama matar Kamal, Minal Keta aikin bata hakuri amma taki hakura, wata kawar Minal ce da ta gayyato mai suna *FIDDAUSI YAR FICIKA* tace
“Haba Muhabbat ya kamata kidaina kukan nan haka ki godewa Allah, shi Allah da yasa Kamal ya zama mijinki ai yasan abinda yakeyi, ki yarda da kaddara mana”
“Humm FICIKA bazaki gane bane, amma inaji a zuciyata Kamal bazai taba zama mijina bah”
Tana rufe baki phone d’in Minal nayi k’ara da sauri ta d’aga saboda ganin sunan dake kan screen din wayarta, Dady ne yace
“Minal kiyi sauri kidawo gida yanzu ina nemanki”
Minal tace
“Toh Dady ganinan zuwa”
Da sauri tatashi tace dasu tana zuwa, tana fitowa gidan ta nufa direct, falon Dady tayi tana zuwa ta sameshi zaune kan kujera, ta gaidashi sannan ya amsa yace
“Minal kin yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau?”
Ta d’aga kai tace
“Eh Dady na yarda da ita saboda a koda yaushe a islamiyya ana gaya mana mu yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau dan haka Dady na yarda da ita”
“Yauwa Minal ai nasani, toh inaso ki bud’e kun’nanki kiji abinda zan gaya maki Minal! daga yau kin zama matar aure”
“What?!!! Dady matar aure fa kace, ta yaya zan zama matar aure bayan ni bani da saurayi”
“Minal karki manta kefa kikace man kin yarda da kaddara”
“Eh Dady na yarda da ita”
“Toh Minal na d’aura maki aure da Kamal, saka makon Hameed yadawo bai mutu bah”
“Dady Yaya Hameed ya dawo bai mutu bah?”
“Eh Minal”
“Toh yana ina?”
“Gani nan Minal”
Da gudu Minal ta tashi ta fad’a jikinshi tana fad’in
“Dama yaya kana da rai baka mutu bah duk tsayo lokacin nan shine ka tafi ka barmu”
“Eh Minal ban mutu ba, Please Minal promise me zaki rike Kamal a matsayin mijinki”
Minal ta d’ago jikinta d’aga jikin Hameed tana share hawayenta tace
“Yes yaya I promise u zan zauna dashi a matsayin mijina, ai dawowarka ta fiye min komi a rayuwata”
“Yauwa my sweet sister nagode idan kikayi min haka kin gama min komi a duniya”
Dariya tayi ya kamata ya zaunar sukaci gaba da fira Dady yayi masu nasiha mai shiga jiki.
*****
Misalin karfe 8:PM Dady ya aika da mota yace a d’auki Muhabbat akaita gidan Hameed da ke kwado, har yanzu maganar da ake Muhabbat bata san da wanda aka d’aura masu aure bah, Allah sarki haka aka d’auki Muhabbat ba d’an rakiya ko d’aya, saboda tun safe Innah bata gida har yanzu bata dawo bah, d’aga ita sai driver, haka ya nuna mata inda zata shiga ya nuna mata d’akin ta, tana zuwa ta fad’a kan gado tana kuka mai cin rai, sallamar Hameed taji amma bata amsashi bah, saboda ta kifa kanta a kan gado, a hankali Hameed ya zauna dai-dai in da kanta yake cikin murya kasa-kasa yace
“Haba uwar ya’yana kukan me kike?”
Cikin zabura ta mike tsaye taga Kamal tsaye sai ga Hameed zaune kan gado sai kawai ta fashe da kuka tace
“Na shiga uku dan Allah Yaya Hameed kayi hakuri wallahi banida laifi wajen auren nan, ka koma ka kwanta wallahi nayi maka alkawarin bazan yarda dashi bah”
Hameed abin dariya ma ya bashi yace
“Oh my God Muhabbat please calm down, Muhabbat yau Hameed ne a gabanki ban mutu bah ina nan da raina”
“Yaya Hameed da gaske kaine baka mutu bah?”
“Eh nine da gaske zoki ta6a ni kiji”
Da gudu Muhabbat ta fad’a jikin Hameed tana kuka, hannunsa yasa ya d’ago kanta ya had’a kanshi da nata yana kallonta yana shafa kanta ai Kamal juya fuskasma yayi.
A hankali ta lumshe idonta saboda yanda yake shafa mata gashin kanta, cikin murya kasa-kasa yace
“Nasan kinyi missing dina koh?”
Kai ta d’aga alamar eh yace
“Good my wife ai nasan kina sona”
Kamal gani yayi idan ya tsaya jiransu toh zai kwana a haka, sai kawai ya dake yace
“Toh malam, ai Luv d’in ya isa haka, ko kunyata ma bakwaji, toh nima bari na tafi wajen Amaryarta”
“Au! Sorry fah na manta kana d’akin, toh zoka zauna muyi magana”
“A’a haba wani zama, ai sai kudasa min hawan jini”
Hameed yayi dariya warda sai da ta bayyana hak’oransa, a hankali Kamal yazo gaban Muhabbat ya fad’i kasa sai hawaye ya fara bin fuskarshi yace
“Muhabbat bansan da wani idon zan kalleki bah, Muhabbat dan Allah kiyi hakuri abinda yafaru a baya, *SON ZUCIYA* yaso yakaine ga halaka, Muhabbat wallahi yanzu *NAYI NADAMA* sosai, ki yafeni”
Muhabbat tayi shiru bata bashi amsa bah, a hankali Hameed ya juyo da fuskarta yana kallonta, yace
“Please matata kiyi hakuri ki yafe masa wallahi na tabbata Kamal yanatsu yanzu”
“Toh bah damuwa na yafe masa amma yaci albarkacinka”
“Yauwa my wife, yanzu dai Allah ya amsa addu’armu yau kin zama matata shikuma Kamal Minal ta zama matarshi.”
“Eh Yaya, ta
yaya Minal ta zama matar Kamal?”
Yanzu zakiji yanda akai Minal ta zama matar Kamal”
Nan fa Hameed duk yabata labarin yanda akai, sai dai bai gaya mata tare suka taho da mamanta bah, saboda yanaso da safe sai ya kaita, Muhabbat ta girgiza kai tace
“Allah mai iko”
Nan fa suka sha fira da Kamal, ya danyi mata nasiha, kafin Hameed ya rakosa har wajen motarsa, bayan ya tafi Hameed ya dawo cikin gida, ai kam inda yabar Muhabbat zaune nan ya sameta, toilet ya nufa yayi alwala sannan yafito, wardrobe ya bud’e ya d’auko mata wasu kayan barci ya bata, yace ta shiga toilet tayi wanka sannan tayi alwala tazo suyi sallah, kayan ta amsa ta nufa toilet, shikuma kayan jikinshi ya cire ya saka jallabiya, kan kujera yakoma ya zauna yana jiran ta fito, bayan ta gama wankan tasa kayan da yabata, Muhabbat bin jikinta tayi da kallo, saboda yanda kayan sukayi mata sunyi mata bala’in kyau duk wata surar jikinta kana kallonta, Hameed gani yayi bata da niyyar fitowa sai kawai yatashi ya nufa toilet d’in ya bud’e k’ofar, yana bud’ewa ya ganta tsaye a toilet d’in tana wasa da ‘yan yatsunta, murmushi yayi ya numshe idonsa ya nufa inda take, yakama hannunta ya fito da ita, hijabinta ya d’auka yasa mata, sannan ya kabbara sallah, bayan sun gama Hameed ya zauna yana masu addu’a, yadade yana addu’a har bacci yakwashe Muhabbat, juyowa yayi yaga har tayi bacci, yayi murmushi, ya d’auketa cak sai saman gado ya kwantar da ita, shikuma yacire jallabiyar jikinshi ya hau kan gado, yajanyota jikinshi yafara shafata cikin wani irin salo, da sauri ta bud’e idonta, nan fa jikinta ya fara rawa, shiko cigaba yayi da shafata, can yakai hannunsa a kan dukiyar Fulaninta, ya wani cafkosu kuka Muhabbat ta fasa jikinta narawa, can sai ga wayarsa tayi k’ara juyawa yayi ya d’auka amma, bai tsaya yaga waya kirasa bah, janyo Muhabbat yayi saman k’irjinsa yana wasa da gashin kanta, bayan ya d’auka yaji muryar Mom tace
“Hameed dama na manta ince maka dan Allah kabar yarinyar nan karkayi mata komai har nan zuwa kwana biyu kana jina ko?”
“Eh Mom”
Bayan mom ta kashe wayarta, Hameed a hankali ya rad’ama Muhabbat a kunne
“Don’t worry ki kwanta kiyi barci bah abinda zanyi maki kinji koh? Mom ta ruk’a maki alfarma na hakura amma fa an shiga hakkina…”
Su Kamal ango yana zuwa gidansa yasamu Minal har tayi bacci murmushi yayi yanufi d’akinsa saboda bayaso ya takura mata…_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 18_
*Washe gari*
Hameed tunda ya tashi ya tafi masallaci sallah asuba bai dawo bah, sai da gari ya fara haske, kafin ya dawo Muhabbat har ta tashi tayi sallar asuba, kitchen ta nufa danyi masu breakfast, tana zuwa kitchen d’in ta rasa yanda zatayi saboda gas ta gani gashi bata iya kunawa bah, tana nan tsaye tana tunanin yanda zatayi sai ga Hameed yashigo.
A hankali yasa hannunsa ya rungomota ta bayanta yace
“My wife kin tashi lafiya?”
Cikin sanyin murya ta furta
“Lafiya Qlau”
Hameed yajuyo da ita gabansa yana kallonta yace
“Me zakiyi haka?”
“Hmmm dama…..”
“Dama me? kinga je kiyi wanka yanzu ki shirya zamuje gidanmu yanzu kinji koh?”
Kai ta d’aga masa alamar eh tajuya ta fita yayin da ya bita da kallo, tana zuwa ta shiga toilet danyi wanka, shikuma ruwan tea yasa a wuta, bata dad’e bah, ta fito d’aga wankan, wajen mirror ta nufa ta zauna yin kwalliya duk da ba kwalliyar ta iya bah, amma tayi kyau masha Allah, bayan yagama yazo ya kirata suka zauna karyawa, kunya duk ta kamata, haka suka gama sannan shima ya tashi yashiga toilet dan yin wanka, ita kuma tana nan zaune kan kujera, yana gama wanka yafito dagashi sai towel, da sauri Muhabbat ta kauda kanta dan kunya, murmushi yayi ya nufa inda kayansa yake ya saka, saida yagama sannan yace
“Tashi mutafe sarauniyata”
Hannunta ya kama yasa mata hijabi, suka fito yace wa mai gadi ya rufe gidan, suka shiga mota Hameed yana driven amma hannunsa yana kan kafadar Muhabbat, ahaka har suka isa suna zuwa suka samu har Kamal sun iso shida Minal, Muhabbat suna yin sallama kasa shiga tayi saboda Fadima da tagani zaune, a zuciyarta take fad’a Allah mai iko kuji wata mata kamar mamana.
Ashe duk magana nan a waje take yinta, Fadima tace
“Muhabbat nice fah mamanki”
Allah sarki uwa mai dad’i, da gudu Muhabbat ta karasa wajanta ta fad’a jikin Fadima, tama manta akwai mutane a d’akin, nan fa ta fara kuka tana fad’in cewa
“Mama dama kina nan amma kika tafi kika barni har tsawan wannan lokacin, kinsan irin wahalar da nasha a rayuwata me yasa baki tafi dani ba”
“Muhabbat kiyi hakuri wallahi nima ba yanda na iya, saboda dana zauna a gidanku toh wallahi yanzu da babu ni a duniya, ni kaina nasan Allah ne ya kwace ni har na koma kasarmu”
“Toh Mama amma ya akayi kika san nan gidan?”
“Humm sanadiyar Hameed nasan nan gidan Muhabbat”
“Ban gane bah?”
Fadima taba Muhabbat labari duk abinda ya faru, sai yanzu Mom tayi magana tace
“Toh Muhabbat abarta haka azo mugaisa koh”
Kunya ce duk ta kamata..+
Nan fah Hameed yace
“Ya kamata kutaso muje gidansu Muhabbat”
Mom tace
“Gaskiya ne Hameed”
Dakyar suka samu Fadima ta yarda, saboda cewa tayi ita ba inda zata, dukka gidan suka fito har da Minal da Kamal, suka shiga motocinsu, gidan suka nufa direct, ai kam suna zuwa Muhabbat akace ta fara yin gaba tana shiga tasamu Innah da Lami, Innah tace
“Toh munafika ya koroki koh?”
Hameed ya amsa yana dai-dai shigowa yace
“Ai ni nafi karfin nakori Muhabbat, ai auranmu mutu ka raba takalmin kaza”
“Toh marar kunya dama baka mutu bah?”
Maganar Innah tatsaya ne a lokacin da Fadima ta shigo, ido tazaro tana nuna ta da d’an yatsa. Hameed yayi murmushi yace
“Ban mutu bah, dama kinaso namutu ne? toh Allah bai baki sa’a bah.”
Ashe Abba yana tsaye, ai kam yana gani Fadima kanshi ya dafe, saboda abinda yasokeshi, Innah tace
“Lami kinga ya dawo itama wannan shegiyar ta dawo hahaha ai dole nakuma wajen bako hahaha ai gidan nan nawa ne ni d’aya hahaha babu shegen daya isa ya shigo”
Ai dukka mutane wajen bin Innah sukayi da kallo, saboda da alama Innah ta haukace, ai kam ta haukace da gudu tafita tana dariya tana wayyo, Lami kuwa ai bah magana, sai yanzu suka lura da halin da Abba yake ciki, ai kam nan suka kamasa…
Ya d’an d’auki lokaci kafin yafara magana, yace
“Fadima yau kece a gabana me yafaru dani har na manta dake, dan Allah ki yafeman”
“Malam na yafi maka, nima ka yafe min”
“Fadima baki ta6a 6ata min ba, wallahi nayi dana sanin auran Mairo a duniya ta cutar da rayuwa ta”
Hakuri suka fara bashi dakyal ya saita zuciyarshi.
Nan fa suka tashi gaba d’ayansu suka koma gidansu Hameed, bayan sun koma Hameed yace
“Wa Muhabbat tatashi su tafi gida
Mom tace
“Ba inda zata inaso su danyi kwana biyu ita da Minal akwai abinda zamu dan nuna masu”
Hameed yace
“Mom wane abu koma bayan an riga da anyi aure, ni gaskiya kubani matata mu tafi gida”
Ido Mom ta zaro tace
“Toh marar kunya, Kamal ma bai magana bah sai kai”
Dady ne ya katseta da fad’in
“A’a Saratu ba’a haka ki basu matansu sutafi gidan”
“A’a Alhaji wallahi akwai abinda zan nuna masu, kasan bazanyi abinda zai cutar dasu ba”
“Haka ne toh shi kenan kuyi hakuri har ta gama, nasan dai irin abin nan nasu na mata zata basu”
Mom ta 6ata fuska tace
“Kajika koh Alhaji da wata magana gaban yara”
“Toh ai gaskiya na fad’a, yauwa Hameed ya kamata, Muhabbat kasata makaranta, dan ilimi shine gaba da komi a rayuwa”
“Eh dama Dady na yanke shawarar zan sata school d’insu Minal sai sudinga zuwa tare”
“Yauwa ai kayi shawara mai kyau”
Nan fah su Hameed sukace suma ba inda zasu, sai dai su zauna dakinshi, Mom tace bata yarda bah, Dad yace a’a su zauna ba damuwa…..
Nan fah Abba yayi magana yace
“Nima ya kamata na maida matata d’akin ta tunda bah sakinta nayi bah”
Dady yace
“Gaskiya ne dole Fadima ki koma d’akin ki saboda har yanzu malam mijinki ne”
Mom ma ta bada goyan baya dari bisa dari! nan fa Dady yasa driver yace yakaisu gida.
Minal tace wa Muhabbat tataso sutafi d’akin ta, suna tashi Hameed ya Mike zai bisu, Mom ta daka mai tsawa tace
“Toh marar kunya ina zaka bisu, maza kaja abokinka kuma kutafi d’akinku, mutumim banza kawai, ko kunyarmu bakaji”
Duk d’akin sukasa dariya Hameed ya fara sosar keya.
Bayan su Muhabbat sun shiga d’aki, Minal tace
“Anty Muhabbat sai kikaji an d’aura mana aure da yaya Kamal, wallahi har yanzu abin mamaki yake bani, zan iya zama da ya Kamal kuwa a matsayin mijina?”
“Humm Minal kenan zaki iya mana, ai bah abin mamaki bane, dama chan Allah yace Kamal shine mijinki, kinsan *MATAR MUTUM* kabarinsa.”
“Haka ne Anty Muhabbat, toh Allah yabamu hakurin zama dasu”
“Amin, a nan bah wata wayewa”
Dariya sukasa su dukka, sannan sukayi addu’a suka kwanta….
*Washe gari*
Tunda safe mom tatashi, dan zasu fita ita dasu Muhabbat, d’akinsu tashiga, Muhabbat ta duk’a har kasa tagaida Mom, Mom ta amsa cikin fara’arta, sannan tace masu maza kushriya zamu fita yanzu daku, sukace toh, Minal ta fara shiga wanka kafin, bayan ta fito Muhabbat tashiga, itama tashiga tayi wanka, bayan sun fito suka zauna kwalliya, kunga yanda sukayi kyau kuwa? yanda kukasan yan biyu wallahi haka sukayi kyau, kayan da sukasa sun amshe su kamar dansu akayisu, wani d’an mayafi Minal taba Muhabbat tace ta rufa, dakyal ta amsa saboda cewa tayi bazata iya fita dashibah, sai da tace mata
Ai a mota zamu fita kuma har inda zamu driver zai saukemu”
Sannan fah ta yarda, falo suka fito suna fitowa kamshin turarensu ya duke hancin Hameed da Kamal da sauri suka juyo daga inda suke zaune kan kujera, kowane bin matarsa yayi da kallo, saida suka iso sannan suka gaidasu, da sauri suka amsa, Mom tafito itama har ta shirya, tace
“Yauwa har kun shirya kenan toh mutafi”
Da Hameed da Kamal ai had’a baki sukayi sukace
“Mom ina zaku haka da wannan kwalliyar?”
Mom tace
“Gidan uwaku zamu”
Hameed ya 6ata fuska yace
“Toh wallahi Mom kafarku kafarmu, abokina taso mubisu?”
Mom ta d’aga dan yatsa tana nuna Hameed dashi tace
“Wallahi Hameed kafita daga idona”
“Toh yanzu Mom haka zaki fita dasu bah hijabi jikinsu?”
Mom tayi dariya tace
“Toh sarkin kishi kamar mace, ai a mota zamu kuma yanzu zamu dawo”
“Nidai gaskiya Mom matata taje tasa hijabi”
Kamal yayi saurin fad’in
“Au matarka kawai banda tawa, ai nima taje tasa hijabi”
Dady na dai-dai fitowa yace
“Kuna da gaskiya yara suje susa hijabinsu”
Minal ta turo baki tatafi ta d’auko hijabensu, suka fita driver ya d’aukesu Mom tace masa ya kaisu gidan kawarta HAJIYA BINTA mai turaren wuta, watau unguwar kwado, canko driver ya nufa dasu direct….
Sunyi sa’a sun samu Hajiya Binta tayi murna da ganinsu sosai, sannan suka gaisa, nan Mom ta gabatar da abinda ya kawosu, Hajiya Binta tace
“Don’t worry Kawata indai wannan ne zanyi masu gyaran jiki na gani na fad’a sannan akwai wasu maguguna da zan basu sannan uwa uba zan dafa masu kaza, gyaran jikin da duk inda suka gifta sai an sake kallonsu, zanyi masu na sati d’aya tunda lokaci ya kure”
“Toh nagode Kawata”
“Haba badamuwa, yanzu zan fara masu gyaran jiki daga yau”
Haka ta gama masu suka kama hanyar gida, da suka dawo sunyi sa’a su Hameed basa gida sun fita, d’akinsu suka nufa direct.
Bayan sun shiga sunyi wanka sunyi sallah, sannan suka zauna fira, Minal tace
“Hummm wallahi d’azu naji haushe fah da akace muje musa hijabi”
“Toh ya zakiyi aure kenan ai..”
Kafin ta rufe baki Hameed ya turo k’ofa yace
“Ina my wife d’ina har kun dawo”
Minal ta kwashe da dariya tace
“Lah Yaya a gabana?”
“Ke ni tsaranki ne ina magana kina saman baki, zan fasa maki baki yanzu nan”
“A’a kaga malam karka ta6a man mata”
Kamal ne yanzu yayi magana, da Muhabbat da Minal kansu, suka a kasa.
Saboda su duka kunyar mazajen nasu suke
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 19_
Mom ce ta turo k’ofa fuskarta babu alamar wasa ta d’aga hannunta tana zuwa
“To ku fita marasa kunya, ku ko kunyata ma bakwaji”
“To Mom dan munshigo wajan su ai ba laifi bane tunda matanmu ne…”
“Gaskiya ne marar kunya Hameed ni kake fad’awa su matanku ne gaskiya wuyarka ya isa yanka”
“A’a Mom abin duk bai kai haka ba kiyi hakuri zamu fita”
Kamal ya kama hannun Hameed ya jashi zuwa waje.
Mom ta juyawa ta watsa masu Minal wani irin kallo tace
“Saura ku ai kuke jawosu”
Tana rufe baki ta juya tafita a d’akin, su kam raba idanu suka cigaba dayi…
******
D’an zaman da Muhabbat tayi a gidan har ta fara zuwa school d’insu Minal, a gaskiya ba laifi Muhabbat nada kwakwalwa sosai duk abinda akayi masu tana d’auka da sauri, gashi yanzu ta iya abubuwa da dama Mom ta nuna masu hatta girki, dasu kunna gas duk ta iya, gashi suna ta zuwa gidan Hajiya Binta wajen gyaran jiki…
+
*BAYAN SATI DAYA*
Yau ne ranar da za’a gama masu gyaran jikin, a gaskiya Hajiya Binta tayi k’okari sosai, because idan ka gansu kai kanka kasan sun wanku, jikinsu har wani shik’e yake dan kyau, can kasa kuwa ba’a cewa komai sai ranar da suka shiga za suyi bayani, hakan yasa Hameed da Kamal duk suka tada hankalinsu wajen dole a basu matansu amma Mom tace ba inda zasu sai ta gama masu abinda take masu.
Hakan yasa suka d’aure suka hakura ba dan rai yaso bah.
Hameed ne da Kamal zaune a d’akinshi suna fira Hameed yace
“Abokina kasan wani abu kuwa?”
“A’a ban sani ba sai ka fad’a”
“Humm tsaya kaga yau zan kawo karshen wannan Game d’in Mom”
“Toh taya me zakayi?”
“Humm sa ido kayi kallo”
Hameed wayarsa ya d’auka ya danna number Minal, ai kam tana kusa da wayar ta d’aga take yace mata
“Yauwa Minal kuna tare da Muhabbat kuwa?”
“Eh yaya gata nan”
“Yauwa dan Allah ki turo man ita yanzu nan akwai abinda zan bata, ta kawo maku”
“Toh Yaya gata nan zuwa amma na biyota?”
“A’a ita d’aya nace”
Hameed ya kashe wayarshi yace
“Yauwa abokina yanzu ka tashi kafita ka boye waje tana fitowa kaima kashiga d’akin Minal ni kuma nan zan gama aiki”
“Haba Hameed ba kunya gidanku ne fa”
“Au toh idan bazakayi bah tashi kaje chan waje”
“Haba dai malam ai ni nafika buk’ata ma…”
Nan sukayi dariya, Kamal ya fita, Muhabbat ta d’auko hijabinta har kasa ta fito ta nufa d’akin Hameed, ai kam tana fita Kamal shikuma yashige d’akin Minal, ido ta zaro, saboda batayi tunani zai iya zuwa bah, karasowa yayi wajanta yace
“A’a haba my sweetheart what happen, naga daga na shigo kin zaro ido”
Murmushin karfin halin Minal tayi tace
“No problem”
“Are u sure?”
Kai ta d’aga masa alamar eh, kan gado ya zauna yana bin jikinta da kallo, ita kuma Muhabbat tana shiga dama Hameed na jikin k’ofa bata sani bah, kawai ya maida k’ofar yarufe, nan fa jikinta ya fara rawa, karasowa yayi ya d’auketa cak…..
Ashe duk bidirin nan Mom na zaune kan kujera ita da Dady suna kallonsu, Mom tace
“Alhaji kana kallon wani Sabon iskanci a gidan nan”
“Humm na gani, toh laifinwa? kiba yara matansu sutafi gida amma kince a’a, ai gwara sununa maki suma yaran zamani ne su”
“Hmm gaskiya naga yaran zamani toh ai kam yanzu nan zasu kwashe matansu sutafi gidan nasu su bamu waje”
“A’a haba ai kibarsu sukara kwana biyu”
“Wani kwana biyu? Alhaji ina, ai bari kaga”
Mom wayarta ta d’auka ta danna number Hameed, yana cikin shafa Muhabbat yaji karar wayarsa, ya d’auka Mom tace
“Maza kufito falo ina nemanku, kudukka yanzu yanzu nan”
Hameed yaji haushe sosai ya tashi d’aga abinda yake, hijabi yasa mata ya kama hannunta sannan ya kira Kamal suka sauko kasa.
Bayan sun sauko, Mom ta fara magana cikin fad’a-fad’a tana cewa
“Toh marasa kunya, maza ku d’auki matayenku kutafi gida lada ta isa haka”
Dady yace
“A’a Saratu! kibarsu sukara kwana biyu mana ai..”
“A’a wallahi yanzu-yanzu nan zasu tafi basai anjima bah”
A hankali Hameed yace
“Toh Mom yanzu zamu tafi”
“Eh ai na sani marar kunya banza”
Hameed yayi dariya suka tashi, sai da suka had’a kayansu gaba d’aya kafin suka fito, Mom tace
“Toh dukkanku kurike matanku kada nasake ganin kafarku gidana”
Ba suyi magana bah, saboda sun samu abinda sukeso, Minal kuwa da Muhabbat ji suke kamar su bud’a kasa su shiga d’an kunya, motocinsu suka shiga sai gidan…
Bayan sun koma gidansu dama dare yayi sosai,
Hameed suna shiga, toilet ya nufa direct yayi wanka, saida yafito sannan yaba Muhabbat kayan bacci, yace taje tasaka, yau ma kamar ranar taji kunya! amma tafito, tana fitowa Hameed ya taho wajanta ya kamata, cak ya d’auketa sai kan gado, hannunta tasa ta rufe fuskarta, Hameed yasa hannunsa yacire hannunta daga fuskarta, yana bin fuskarta da kallo kota Ina, can kuma ya d’agota ya zaunar da ita ya d’auki hannunsa na dama ya d’aura saman kanta ya fara yi mata addu’a saida ya gama kafin, ya fara shafata, cikin muryar kuka tace
“Dan Allah Yaya kayi hakuri”
Sai kawai ta fashe da kuka, Hameed harshensa yasa yana lashe hawayen, chan yakai hannunsa bisa abinda Jiddah ta ta hanani fad’a, ya fara shafasu yana wani lumshe ido kamar mai jin barci, bakinshi ya had’a da nata ya fara kiss d’inta, Muhabbat da taga da gaske yake sai ta fasa kuka mai k’arfi, a hankali Hameed cikin murya kasa-kasa dako idonsa baya iya bud’ewa, yace
“Please accept me as ur husband, koh kinaso na neme wata mace a waje ne?”
Muhabbat ta girgiza kai alamar a’a yace
“Kin amince yanzu nazama mijinki na gaskiya”
Kai ta sake d’aga masa alamar eh, nan fah Hameed yashiga kiss d’inta kota ina, ya k’ara kankameta, nan fah yashiga shafata kota ina, sai da yayi mata wasanni mai rai da lafiya kafin yayi addu’a ya tafi duniyar ma’aurata ai jiyayi bai san duniyar da yake ba, itakuwa tun tana kuka har tagaji ta hakura..
Toh a 6angaran Minal ma haka abin yake, sun fafata sosai, amma baiyi wahalar shayo kanta bah.
Wannan rana dukkansu sunsha wahala ba yar kad’an bah, basu kyalesu ba sai asuba, dan Hajiya Binta tayi gyara mai kyau, Hameed yayi ma Allah godiya da yasamu matansa a sabuwa kar a laida, shi ya fara bud’eta.
Kamal kuwa ai ba’a cewa komai dan kuwa sai da YAYI NADAMA abinda ya ai kata a baya saboda yanzu yasan mace…
Rayuwa tayi masu dad’i soyayya suke nunawa junansu ba gidan Hameed bah, ba gidan Kamal bah, gaskiya dukkansu babu laifi wajen kula da miji, gashi a haka suna ta zuwa school d’insu,
*BAYAN WATA DAYA*
Su Hameed har sun koma garin Port Harcourt watau wajen aikinsu, amma a koda yaushe suna kewar matansu, Hameed yanzu ne ya tabbata Kamal ya natsu dan kuwa baya kulla matan banza…
*MATAR MUTUM*_WRITTEN BY_
*FATIMA ISAH*
( _MRS. OMAR_)
_PAGE 20_
*KARSHE*
Fadima da Abba kuwa ai ba’a cewa komai dan kuwa yanzu suka San, rayuwar aure, gashi yanzu yana kasuwanci sosai ba inda baya zuwa, Innah mairo kuwa hauka sai abinda yayi gaba, Lami kuwa babu wadda yasan duniyar data shiga an nemeta sama da kasa an rasa.
Yau Muhabbat ta kawo masu ziyara, Fadima tana ta bata shawara yanda zata, zauna da mijinta lafiya, dama yanzu Muhabbat an waye sosai, dan har turanci tanaji yanzu,
******************
*BAYAN SHEKARA HUDU*
Rayuwa tayi dad’i duniya tana juya masu zaman da akai yanzu, Muhabbat da Minal Allah ya basu ya’yansu, Muhabbat namiji Minal kuma mace, gashi yanzu suna d’auke da wani cikin.
Yanzu su Hameed sun baro garin port da aiki, suna kusa da matayensu watau Katsina..
Hameed ne naga zaune shida Muhabbat, tana kwanci saman kafarsa shikuma yana shafa gashin kanta, Muhabbat tace
“My sweetheart today am very happy”
“Why My wife?”
“Because yanzu ne kaza ma uban ya’yana ina alfahari da kai mijina..”
Minal ce da Kamal suka shigo, Minal ta amsa da zuwa
“Nima *INA ALFAHARI DAKAI MIJINA*”
Sannan sukayi sallama suka shigo, Muhabbat tayi murmushi tatashi daga jikin Hameed tace
“Sanunku da zuwa Minal baki da dama watau kina jinmu, Takwara zo mana”
Da gudu ta fad’a jikin Muhabbat, Hameed yayi saurin cewa
“A’a Muhabbat karki karya min mata mana” Dariya sukayi Minal tace
“A’a yau ina mijina ban ganshi yana wasa bah?”
“Wallahi yana sama yana barci kinsan halin kayanki”
Cewar Muhabbat dariya sukayi sukaci gaba da fira, Muhabbat karama ta nufa dakin da Kamal karami ke kwance yana barci ta tashi shi yana ganinta ya fara murna, shida ita kusan sa’annine.
Nan fa suka sha fira sai dare suka tafi gida.
Bayan sun tafi Hameed ya d’auki Muhabbat cak sai kan gado nan ya fara shafata cikin murya kasa-kasa yace
“I LUV U MY WIFE”
Cikin sanyin murya itama ta rad’a masa
“I LUV TOO MY DEAR HUSBAND”
Nan fa ya had’a bakinsa da nata , aka fad’a duniyar masoya.
Hameed da Kamal ji suke duk duniya sunfi kowa dacen mata, sunyi murna sosai da samunsu..
*ALHAMDULILLAHI*
Laifin dad’i karewa inji hausawa
_Toh makaranta littafin MATAR MUTUM anan nakawo k’arshen wannan littafin, mai suna MATAR MUTUM kabarinsa, indan nayi kuskure a cikinsa ubangiji Allah kagafartamani, idan kuma na fad’a dai-dai toh Allah kabani lada!_
*Thank u so much my “FANS” I Luv all*
_JINJINA ga yan group d’ina WhatsApp MRS UMAR HAUSA NOVELS ina alfahari daku_
*Ina kike sweety na! HAUWA SHEHU ALIYU watau JIDDAH ALIYU a gaskiya ke kawace ta gaskiya ina alfahari dake a koda yaushe*
_Yan uwana masoyana Khadija Umar Aisha Ibrahim maman Lukman maman Ummi maman Jine Saratu Ali bukar SAMIRA UNCLE DEE_
*Sai kuma kun jini a sabon littafin na mai suna K’ASATA zaizo maku nan bada jimawa ba*
Masoyana dan Karin bayani
*NA MRS UMAR*