MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 12 Na Samira Harouna

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 12

Na Samira Harouna


👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *45*

Yana shiga d’akin ya samu Mimi bacci ya d’auketa, saidai da alama baiyi nisa ba dan hannunta har yanzu rik’e da robar ice cream d’inta, karb’a yayi ya aje gefe ya tattare kayan ya aje sannan ya gyara mata rufarta dan tayi wanka ta saka kayan bacci.

                     *07:30*

A sanyaye take amsa wayar Hajia tana fad’a mata auren Aisha kamar yanda sheikh ya fad’a, cikin son kwantar mata da hankali na iya abinda zata iya kawai Hajia tace “Hafsat karki damu kinji, dama ai sheikh ya sha fad’a idan har ya tashi aurar da ita babu abinda zaiyi na bidi’a, kar ki bari shed’an ya raya miki cewa ya yanke hukuncin nan ne saboda auren da yayi, ki mata addu’a matsayinki na Uwa Allah yasa haka shi yafi alkairi kinji.”

A hankali tace “Shikenan Hajia insha’Allah, yanzu ya maganar shirye shirye ko wani gyara?”

Murmushi Hajia tayi tace “Hafsat ai ke ce uwarta kuma kinfi sanin me ya dace da ita, kawai kiyi tunani sai ki tuntub’i Karima kuyi magana, na tabbata dai sheikh ba zai mata kayan d’aki ba dan shi baya cikin wannan tsarin.”

A sanyaye tace “Haka yake fad’a Hajia, ba zaiyi kayan d’aki ba kuma ya baka ‘ya sannan ya baka abincin da zaka ci, saidai yace a matsayin Anas naa d’alibin da yake ji da shi zai iya mishi kyauta tsakaninshi ne da shi wannan.”

Hajia ce tace “To kin gani, kawai ki mata addu’a tunda yaran ke kanki kin tabbatar da yaron kirki ne.”

A ladabce tace “Gaskiya ne Hajia, Allah ya tabbatar mana da alkairi.”

“Ameen.” Hajia ta fad’a kafin suyi sallama ta aje wayar ta fito dan shiga madafa ta taimakawa mai aikin da ke tayata aiki idan ta haihu.

Tun asuba daya tasheta ya tafi masallaci bata sake ganinshi ba, tana idar da sallah ta shiga gyaran d’akinta a nutse, duk da ba wani datti ko wani abun gyaran ke akwai ba, amma saida ta kimtsa komai tayi turaren ruwa dana wuta da kaskon na’ura, tana gamawa ta shiga wanka dan Alhamdulillah yanzu jikinta da sauk’i sosai, tana fitowa a wanka ta zauna ta d’auki ado kamar zata je gasar sarauniyar kyau, cikin wani leshi ta shige ta kashe d’aurin d’an kwali mai hawa-hawa.

Yanda tayi wani masifaffen kyau yasa ta kallon kanta a madubi har ta d’auki selfie, saida ta gama ta aje wayar ta tunkari k’ofar fita, yanda falonta ke ta tashin k’amshin turaren wutar data saka yasa ta fita a falon ta rufo k’ofar.

Falon Hafsat ta shiga da sallama a bakinta, Munzeer da Aswan ne suka amsa a tare suna kallonta, murmushi ta sakar musu tana k’arasawa da fad’in “Sannanku?”

Da ladabi da girmamawa Aswan yace “Ina kwana aunty.”

Da fara’a tace “Lafiya lau Aswan, har an shirya tafiya makaranta?”

Da ladabi yace “E aunty.”

Munzeer ta tarawa hannu tace “D’an Abbansa yaya? An shirya ne?”

Tasowa yayi da dariyarshi ya mik’a mata hannun, sunkuyawa tayi tana shafa kanshi tana murmushi tace “Ina mamanka?”

Madafa ya nuna mata yace “Tana ciki.”

Murmushi tayi tace “Kunyi karin kumallo ne?”

Girgiza kai yayi yace “Shi muke jira.”

Mik’ewa tayi daga sunkuyawar tace “Bari na shiga ciki to na kawo maka naka na musamman ko?”

Jinjina kai yayi yana dariya yace “To aunty.”

Hanyar madafar ta nufa sai kuma Aisha ta fito tana gyara jakar makarantarta a bayanta da alama sauri take, ba tare da tunanin komai ba Mimi ta sauko da kanta tana fara’a tace “Ina kwana Humaira.”

Kallonta tayi tana gimtse fuska, wani wawan tsaki taja ta ci gaba da takawa, ta gabanta ta wuce ta shiga madafar tana fad’in “Amie mun kusa makara fa, har yanzu baku gama ba?”

Girgiza kai Mimi tayi ta shiga madafar ita ma tana tab’e baki a ranta tana fad’in “Kinyi da yar halak yarinya, akan tsohon ubanki zaki min tsaki?”

Tana shigowa suka had’a ido da Hafsat dake aiki tuburan, dukansu murmushi suka ma juna inda Mimi tayi saurin fad’in “Ina kwana aunty?”

Da fara’a sosai ta amsa da “Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?”

Jinjina kai tayi tace “Lafiya lau, aiki ake?”

Cikin sakin fuska tace “Wallahi, kinga yau kamar an d’auremu na rasa me ya tsayar damu.”

Murmushi tayi tace “Allah sarki, yau da gobe kenan, bari na taimaka muku.”

Kamar daga sama Aisha tace “Amie indai wannan matar zata saka hannu a abincin da zamu ci yanzu wallahi saidai na hak’ura da shi.”

Da sauri Hafsat ta kalleta hankali tashe tace “Aisha kina lafiya? Me yake damunii ne? Wannan wane irin iskanci ne?”

Turo baki tayi haar da bubbuga k’afafu tace “Lafiya ta k’alau Amie, akan ta ne fa Abie ya daina son mû har zai min auren wuri.”

Zaburowa Hafsat tayi zata kwad’a mata mari sai kuwa tayi hanyar fita, Mimi dake k’ofar tsaye tana kallon Aisha da mamaki bata ankara ba ta bangajeta tana fad’in “Dallah malama matsa min ni.”

Yanda ta had’a kanta da bango yasa Mimi sakin siriryar k’ara tana dafe k’eyarta dan ta ji zafi sosai, da sauri Hafsat tayi kan Mimi tana tambayar “Subahanallah! Mimi kinji ciwo ne?”

Daurewa tayi ta mayar da hawayenta ta k’ak’aro murmushi ta girgiza kai tace “Ba komai aunty, ki k’yaleta dan Allah.”

A tsawace tace “Na k’yaleta fa kika ce? Aisha yarinya ce da har zata min d’anyan kai a gidan nan?”

Fita tayi a madafar a hassale, a sanyaye Mimi ta k’arasa kusa da mai aikin da take gaisheta ta amsa sannan suka ci gaba da aikin.

Hafsat na fitowa a fusace Aisha na daf da k’ofar fita tana ta kumburo baki, nunata tayi da yatsa tana fad’in “Abinda zaki min kenan Aisha? Wannan ita ce koyarwar dana miki? So kike ki nunawa duniya ni malalaciya ce kenan? Kina so ki fad’a da babban murya cewa ban isa dake ba?”

Cikin turo baki tace “Kiyi hak’uri Amie, amma faa ke ma kinsan gaskiya na fad’a, duk saboda ita ne komai yake faruwa.”

A zafafe tayi kanta sai kuma Heezam ya fito daga d’akinshi shi ma a shirye, da sauri Hafsat ta kalleshi tace “Heezam kamo min hannun yarinyar can?”

Aisha na jin haka ta fita a guje hakan yasa Heezam kallonta sai kuma ya kalli Hafsat yace “Amie lafiya? Me ta miki yanzu da safe? Ban tab’a ganin b’acin ranki irin haka ba?”

Kamar zatayi kuka tace “Dole ne Heezam, yanzu duk abinda mahaifinku ya fad’a muku jiya ace bai shiga kan Aiaha ba, har ta tsaya tana wa Mimi rashin kunya kuma a gabana.”

Girgiza kai yayi cike da rashin jin dad’i yace “Kiyi hak’uri, ina ga fa dalilin da yasa Abie yace zai mata aure kenan, kinsan matsalar Aisha kafuwa.”

D’aga kafad’a yayi yana feso iska yace “Ni dama a shirye nake da tafiyata Madina, dan gari ne da nake mafarkinshi kullum tun ranar da Abie ya labarta min zai turani can karatu, dan haka ban d’auki hukuncin nan da zafi ba, ya min dad’i ni kam.”

Wata yar k’wallar tausayinshi Hafsat ta matso tace “Allah ya maka albarka, Allah ya taimakeka ya haskaka maka neman iliminka.”

Murmushi yayi yace “Nagode Amie.”

Takawa ya shiga yi yana kallonsu Aswan yace “Ku tashi mu wuce kunsan Abie baya so mu tsayar da dreba yayi ta jiranmu ko.”

Mik’ewa sukayi inda Hafsat ke fad’in “To abun karin fa?”

Kallonta yayi yace “Amie lokaci ya k’ure, kawai idan munje zamu samu abinda zamu sa a cikinmu.”

Jinjina kai tayi tace “To shikenan, Allah ya tsare.”

Shafa kan Munzeer tayi tana masa murmushi tace “A dawo lafiya ko yarona.”

Bye bye ya mata suna daf da fita Mimi ta fito da sauri tana fad’in “Ku tsaya ku tsaya.”

Tsayawa duk sukayi suna kallonta, bred ne ta saka musu soyayyen dankalin turawa a ciki da k’wai da tomate fresh, ninkeshi duka tayi a tissus tana mik’awa kowannensu tana fad’in “Ai ba zaku tafi da yunwa ba, taya za’a fahimci karatu?”

A kunya ce Heezam ya kalleta dan gaskiya kwalliyar data cab’a sai ya gan ta wani wal-wal-wal, d’auke kanshi yayi yana fad’in “Ina kwana aunty.”

“Lafiya lau.” Ta fad’a sanda take mik’a mishi ta d’ora da “Antashi lafiya?”

“Lafiya lau.” Ya fad’a yana karb’a da fad’in “Nagode.”

Dukansu godiya suka mata kafin ta mik’awa Aswan tace “Ka mik’awa Aisha wannan.”

Hafsat dake murmushi tana kallonsu ne tace “Ai da kin barta ja’ira ta je da yunwar.”

Murmushi tayi tace “A’a aunty ayi hak’uri.”

Ganin sun fita suna fad’in “Sai mun dawo Amie, sai mun dawo Aunty.” Yasa su dukansu suka bisu da “A dawo lafiya, Allah ya tsare.”

Suna ficewa Hafsat ta kalli Mimi tace “To me kika girkawa mai gidan? Iya fa yaran kawai muka d’orawa su da zasu tafi.”

Murmushi tayi cike da kunya tace “Aunty ai duk abinda kika fad’a shi za ayi.”

Girgiza kai tayi tace “A’a fa uwata, karki manta girkinki ne yau da gobe da jibi ke har nan da kwana biyar, dan haka wannan alhakin yana wuyanki, muje dai na taimaka miki da wani abun.”

Cike da kunya ta sinne kai ta bi bayan Hafsat d’in, suna shiga ta tsare da tambayar me zata dafa mishi, dan haka kawai tace bari tayi sauce na k’wai da doya.

*Duk* abinda ya faru daga sanda Hafsat ke fad’awa Heezam abonda ya faru har k’arshe duk a idon sheikh daya shigo falon ta k’ofar dake fitowa daga falonshi, jin abinda ya faru yasa shi jin ba dad’i sosai, sai kawai ya share ya koma falonshi ya zauna.

Saida ta kamalla aikin nan tsaf Hafsat ta kalleta tace “Ki je b’angarensa ki ga ko ya dawo daga masallaci, ya kan jima dama bai shigo ba wani lokacin.”

Jinjina kai tayi da ladabi ta nufi hanyar, a tsoro tsoro ta k’arasa ta k’wank’wasa tare da bud’ewa a hankali ta tura tana kuma fad’in “Salam.”

Dake babu hasken fitila sai ta shiga waige waige, yana zaune kan kujera mai zaman mutum d’aya yana kallonta, saida ta saké furta “Salam.”

Mik’ewa yayi a hankali yalallab’a yayi ramda k’ugunta, hakan ya haddasa mata sakin k’ara a tsorace, da sauri ya rufe mata baki da hannunshi yana fad’in “Shiiii! Ni ne.”

Ajiyar zuciya ta saukea hankali ta kalleshi, had’a goshinsu yayi wuri d’aya ba tare daya d’auke hannunshi a bakinta ba yace “Banda abun *Marya* a duk duniyar nan waye yake da lasisin tab’a jikinki bayan ni?”

Lumshe ido tayi a hankali ta bud’e ta kalleshi, hannunta tasa ta d’auke hannunshi a bakinta tace “Ni ma kuma waye yake da hurumin tsoratani a garin nan idan bâ tsohona ba.”

Dariya yayi ya shiga neman bakinta saida ya kamoshi ya had’a da nashi ya shiga tsutsa, shiru tayi tana saurarenshi ita dai saida tana yana neman zage mata zip d’in riga tayi saurin ja baya tana fad’in “Abdallah abinci na zo yi maka tayi fa.”

Rik’o hannunta yayi yana sumbatar kuncinta yace “To ai sai na yi wanka ko?”

Jinjina kai tayi tace “To kayi wanka saika fito.”

K’ugunta ya sake rik’ewa yace “To muje a tayani wankan ko?”

Zaro ido tayi baki bud’e tace “Lahhh! Ni d’in? Gaskiya kunya nake ji.”

Murmushi yayi y’a lak’aci hancinta yana fad’in “Kunyar me? Shin ni ba naki bane? Ko kin manta mun zama d’aya ne.”

Mak’ale kafad’a tayi tace “Gaskiya ni dai kunya nake ji.”

Cak ya d’auketa ya nufi uwar d’akin da ita yana fad’in “Ba wani nan, idan baki taimaka min ba to zan fasa wankan ma.”

Wutsil wutsil ta shiga yi da k’afafu tana fad’in “Abdul ka saukeni k’asa dan Allah kar na fad’o fa.”

Murmushi ya saki yana fad’in “Ryam zan iya zagaye garin nan dake a haka babu abinda zai sameki.”

Kallon fuskarshi tayi ta sagala hannayenta a wuyanshi tace “Da gaske?”

Girgiza kai yayi yana murmushi, dan sosai take bashi mamaki idan yayi magana tace wai da gaske? Sai yaji wani daban a zuciyarshi yana jin wani nishad’i, tunda har shi ma zai iya yin magana ayi tamtama gaskiya ya fad’a ko akasin haka. Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi tace “Shikenan, ni kuma yau sai ka goyani ma nayi bacci a bayanka.”

Suna shiga d’akin ya sauketa yana fad’in “Ko zamu jaraba ne ki gani.”

Tattare siket d’inta tayi ta taka gadon sannan tace “To juyo bayanka.”

Da dariya ya tsaya kusanta ita kuma ta haye bayanshi, takawa ya fara yi da ita a tsakar d’akin yana fad’in “Kinga a haka sai na zaagaye k’asa d’ari ba d’aya dake.”

Dariya tayi ta d’ora hab’arta a kafad’arshi tace “Kenan gari na d’ari d’in ba zaka iya ba?”

Dariya yayi ya duk’a da ita kamar zata fad’a ta gaba yana fad’in “Ke ko? To me zai gagareni indai a kan ki ne?”

D’an bubbuga bayanshi tayi tace “Wai baka jin ciwo a bayanka?”

D’an d’ago kanshi yayi ya kalleta yace “Me yasa kika tambaya?”

Sunkuyar da kai tayi tace “To ai naga irinku…” Dariya tayi ta kwanta a bayanshi sosai kamar zatayi bacci tace “Shikenan dai.”

Girgiza kai yayi yana dariya yace “Tsofaffi iri na kike nufi ko? Ryam ban tsufa ba yanda kike tunani, amma sannu kad’an zan tabbatar miki da haka.”

Duk’o kanta tayi ta kafad’arshi tace “Ta ya ya akaramakallah?”

Kamar daga sama ta ji ya juyo da ita gabanshi da k’arfi kuma ya rik’eta gam tare da yin k’asa da ita kamar zata fad’i k’asa, rintse ido tayi ta k’amk’ameshi sosaai, cikin kunne ya rad’a “Kin amince na nuna miki?”

Girgiza kai tayi ta bud’e ido tace “Na yafe, na tuba Abdul.”

D’agata yayi ya direta k’asa ya jata zuwa ban d’akin yace “To muje a min wanka Innar Issa.”

Binshi tayi suka shiga ban d’akin, yanda ya tilasta mata yasa ta b’alle mishi botiran jallabiyarsa shi kuma ya cire, rintse ido tayi sosai tace “Abdallah fita zanyi waje kafin na suma a nan.”

Rik’eta yayi yace “Babu inda zaki je, ki suma a nan na gani.”

Da k’yar ta samu ta kubto ta baro ban d’akin, a haka ma cewa yayi ta fito mishi da kayanshi da zai saka, wurin kayan ta bud’a saai ta rikice ta rasa wanda zata d’aukar masa, da k’yar ta ciro wata shadda bleu ta d’auko hula da hiramin da takalma duk sa suka dace da kayan ta aje, feshesu tayi da turare ta zauna bakin gadon jiranshi.

*Watak’ila mun shiga hutun sallah insha’Allah*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *46*

Fitowarshi tasa ta yin zunbur ta mik’e tsaye tana kawar da kanta daga kallonshi dan d’aure yake da towel, kallonta yayi ya kalli kayan data fito mishi da su yana goge ruwan jikinshi yace “Inna Issa ya akayi kika san kayan da zan saka?”

Kallon kayan tayi tana murmushi amma ba tace komai ba, matsowa yayi kusanta yace “Na gane, wato ke ma kina so na ko? Hakan na nufin zuciya da tunaninmu d’aya ne.”

Da sauri ta girgiza kai tace “A’a ba haka bane.”

Wani kallo ya bita da shi yace “To ya ya ne?”

Sunkuyar da kai tayi a sanyaye tace “Ba komai.”

Daf da ita ya tsaya kamar zai had’eta yace “Baki so na Ryam?”

Cikin turo baki da rashin bawa abun mahimmanci tace “To ai ni ban ma san ya so d’in yake ba.”

Kallon tuhuma ya mata yace “Amma kuma a baya kika fad’a min kina son Asas?”

Da saurita kalleshi saikuma ta sunkuyar da kai, jawo k’ugunta yayi ya had’a da nashi yace “Hakan na nufin k’arya kika min?

Da sauri ta girgiza kai cikin sanyin murya tace ” Ba k’arya bace sheikh, kayi hak’uri kaji, muje ka ci abinci.”

K’arasawa yayi gaban kujera ya zauna ya d’auki mai ya fara murzawa a nutse, tana kallonshi har ya gama ya d’auki kayan ya saka, duk da turaren data fesa musu tana kallo ya d’auki wata k’aramar kwalba ya kuma shafawa a bayan kunnenshi sannan ya d’an murza a tafukan hannayenshi ya murza sosai sannan ya d’auki hula ya mik’a mata yace “Oya Hajia d’ora min.”

Karb’a tayi tana dariya tace “Ai naga yanda Abba yake d’orawa na yi.”

Murmushi yayi tare da sunkuyowa sosai tsayinsu ya daidaita sannan ta d’ora mishi hular, kallonshi tayi ta saki murmushi tace “Umm! Kayi kyau.”

D’aga mata gira yayi yace “Da gaske?”

Jinjina kai tayi alamar eh, nuna mata k’ofa yayi yace “Muje to.”

Wucewa tayi gaba ya bi bayanta yana fad’in “Ryam wannan kwalliyar wa ya miki?”

Dariya tayi ta juyo ta kalleshi tace “Ni na yi.”

Rik’e hannunta yayi yace “In kuwa hakane zan bayar da kud’in siyan wasu kayan kwalliyar dan a ci gaba da canccara min ita ina kallo.”

Dariya tayi cike da jin kunya har suka fita falon, Hafsat na zaune tare da mai aikin, gaisheshi sukayi a ladabce ya amsa a mutumce shi ma, k’arasa yayi wajen cin abincin ya zauna, Hafsat da Mimi ma k’arasawa sukayi sai mai aikin data koma madafa ta zauna, Mimi ce ta zuba musu abincin ta aje ma kowa sannan ta zauna ita ma da na ta a gabanta.

Cikin raha da farin ciki suka gama cin abincin, Mimi na kallonsu suna buga mata soyayyar manya, duk da Hafsat d’in na nuna kunya amma sheikh k’arara yake fad’a mata maganar soyayya ko ya rik’e hannunta, kallonsu ita dai take tana mamakin sheikh d’in. Ya rigasu gamawa ya mik’e, saida ya tsaya gaban kowace ya sumbaci goshinsu ya d’ora da fad’in “Allah ya muku albarka, Allah k’ara mana fahimtar junanmu da zama lafiya.”

Gyara rigarshi yayi yace “Zan fita.” Kallon Hafsat yayi yace “Nasan kinsan yau juma’a bana dawowa gida da rana.”

Jinjina kai tayi tana murmushi tace “Hakane, Allah ya tsare.”

Lumshe ido yayi yace “Ameen.”

Mimi ma a d’arare tace “A dawo lafiya.”

“Allah yasa.” Ya fad’a yana kallonta, mik’ewa Hafsat ma tayi ta juya ta nufi d’akinta tana fad’in “Bari na barku kuyi sallama.”

A kunyace Mimi ta mik’e tana fad’in “A’a…amma…”

Shiru tayi ganin har ta bud’e k’ofar d’akinta ta shige, kallonta yayi yana murmushi yace “Duk abinda kika ga *yar aljanna* tayi to da dalili, tafi kowa sanin bana yarda mace ta rakani bakin k’ofa fita saboda mazan dake gidan nan,iya falon nan ne kawai zamuyi sallama dake, kuma tasan waye mijinta shiyasa.”

Jiki a sanyaye ta d’aga kai alamar gamsuwa, kamo hannunta yayi yana kallon fuskarta yace “Kinyi kyau Ryam, kamar na zauna tare dake ina kallonki.”

K’asa tayi da kanta alamar kunya, tallabo hab’arta yayi yace “Fad’a min ciwonki ya warke ne?”

Cike da kunya ta sake sunkuyar da kai ta jinjina alamar eh, sumbatar goshinta ya k’ara yi yace “Jiya ai ina shiga na sameki kinyi bacci, sam ban ji dad’i ba da baccin nan ya hanani jin dad’ina.”

D’ora hannunta tayi a k’irjinshi ta d’ora goshinta ta rufe fuskarta tsabar kunya tana murmushi, shi ma murmushin ya shiga yi yana rad’a mata a kunne “Da gaske nake fad’a miki, kin kuwa san irin duniyar da kika kaini daren can Ryam?”

Tallabo kanta yayi ya kalli fuskarta yace “Wani irin dad’i ne daya fi zuma gigita tunani, d’and’ano ne marar misaltuwa Innar Issa, yau d’in nan zan…”

Duka ta kai mishi a k’irji tana sake nutsa kanta cikin rigarshi tana fad’in “Dan Allah ka daina fad’a, baka jin kunya ne wai?”

Shi ma dariya yayi yana sake rumgumeta a jikinshi, cikin muryar nishad’i yace “Kyautar da zan iya baki ita ce ki ci gaba da rik’e katina na banki kina aiki dashi duk sanda kike so, kyauta ta biyu kuma da zan iya yi miki ita ce…”

Nuna kanshi yayi yace “Ni ma yanzu na zama na ki, na zama mallakinki Ryam, dan Allah ke ma ki bani kanki da zuciyarki, kinji?”

Sinne kai ta sake yi tace “Ni dai kayi sauri ka tafi dan Allah, wallahi kunya kake bani.”

Dariya yayi yana sakinta ya gyara kayanshi da kyau yace “Shikenan tunda korata kike, zan tafi kuma sai dare zan dawo, dan yau ina da abubuwa da dama a gabana.”

Da mamaki ta kalleshi tace “To a ina zaka ci abinci?”

D’aga kafad’a yayi yace “Duk inda na yada zago.”

Girgiza kai tayi tace “A’a gaskiya ban yarda ba, a duk inda ka yada zago ka sanar dani zan tura a kai maka.”

Wani k’ayataccen murmushi ya saki yace “Da kamar wuya Ryam, Hafsat ma ta jaraba yin hakan amma ban amince saboda abun dayawa.”

Bubbuga k’afafu ta fara yi tana kukan shagwab’a da fad’in “Ni dai wallahi idan baka amince ba nima ba zan ci abinci yau ba sai ka dawo gidan nan.”

Tallaba kumatunta yayi da hannu biyu yace “To wai ni da aka ce ba’a so na me, me ye kuma na damuwa dani haka?”

Kallonshi tayi da fuskar yarinta tace “Lahhh! Ni fa ban fad’a ba.”

Lak’ace hancinta yayi yace “Zaki fad’a nan kusa *mai tsada*, ki shirya ma hakan.”

Kallonshi tayi sanda ya nufi hanyar fita yana fad’in “Saina dawo.”

Bye bye ta masa tace “A dawo lafiya.”

“Allah yasa.” Ya fad’a yana fita, saida ta matsa daf da k’ofar tana kallon yanda jami’an da mai gadi da mai bawa shukoki ruwa suke ta gaisheshi yana amsawa da fara’a, zagayeshi sukayi yana magana yana ta nunawa da hannu, saidai yanda yake maganar a nutse da kuma sakin fuska su kuma suna jinjina kai suna fara’a zai tabbatar maka da nasiha ko kuma dai gajeran wa’azi yake musu, bud’e mishi motar akayi ya shiga suka rufe kafin jerin gwanon motocin ukun suka fita a gidan.

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa tace “Allah ya tsare mana kai.”

Rarraba ido ta shiga yi kamar wacce ta tuna wani abu, sai kuma ta d’aga kafad’a tace “Ai hakan ba yana nufin so bane.”

D’akinta ta nufa ita ma tana fad’in “Nayi yaya ma na so shi ni kam?”

*10:20* ta fito kai tsaye madafa ta nufa inda ta samu mai aikin nan, da taimakonta suka shiga had’a girkin rana, sunyi nisa sosai Hafsat ta samesu madafar, da mamaki ta k’arasa shiga tana fad’in “Kai! Mimi wai ba dai aiki ne kuke ba?”

Dariya tayi cike da ladabi tace “E aunty, har mun kusa kammalawa ma.”

Murmushi tayi tace “Kai amma sannunki da k’ok’ari.”

Murmushi tayi ta amsa da “Yawwa aunty.”

Ci gaba sukayi da aikinsu, hakan yasa 12:00 na bugawa suka kammala komai suka jere a table, d’akinta ta shiga dan yin wanka ta shirya, tana shiga wayarta na kururuwa da sauri ta d’auka ta d’ora a kunne ganin sheikh ne.

Daga b’angarenshi ya fara fad’in _”Amincin Allah ya tabbata a gareki Innar Issa.”_

Murmushi ta saki tana jin wani farin ciki na daban ta amsa da _”Allah yasa muyi tarayya a cikin amincin daka rok’a min *old man*.”_

Dariya yayi yace _”Ni ko Ryam? Ni ne old man?”_

Turo baki tayi tana zafe zip d’in rigarta tace _”To yi hak’uri.”_

Numfashi ya sauke yace _”Na yi to tunda ai mun zama d’aya ni dake dama.”_

Murmushi tayi tace _”Ya aiki?”_

Saida ya sauke numfashin da har ta ji sautinshi sannan yace _”Ba dad’i Ryam, so nake na zo gida cikin iyalina na zauna amma ba hali. “_

D’an murmushi tayi kawai mai sauti dan gaskiya har zuciyarta ita kanta zata so ya zauna kusa da ita, dan zaman gidan idan da shi a kusa zata fi jin dad’i, a sanyaye ya d’ora da _” Ryam kina lafiya?”_

Jinjina kai tayi kamar yana gabanta sannan tace _”Lafiya k’alau.”_

D’orawa yayi da _”Babu abinda ke miki ciwo yanzu?”_

A sanyaye ta furta _”Babu Abdul, dan Allah ka daina tambaya ka ji, kunya nake ji.”_

Murmushi ya mata mai sauti yace _”Dole na tambayeki Ryam, ina tsananin buk’atarki ne kuma bana so na sake ji miki ciwo.”_

Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai tana murmushi tace _”Ni dai bana so ka k’ara.”_

Dariya yayi yace _”Ke ma kinsan ai baki isa ba, tunda kika barni na fara lasa zumar nan dole na ci gaba da lasawa ko na mutu.”_

Hira suka sha sosai har saida shi da kan shi yace _”Ryam hutuna ya k’are, zan kashe waya, watak’ila sai dare idan na dawo gida.”_

Marairaicewa tayi tace _”Kenan baka so na aika maka abinci?”_

Ajiyar zuciya ya sauke yace _”Na yau na yafe miki, amma daga gobe zaki fara insha’Allah.”_

Jinjina kai tayi tace _”Shikenan Allah kaimu.”_

_”Ameen.”_ Ya fad’a yana d’orawa da _”Ki kula da kanki kinji, ina sonki sosai.”_

A sanyaye tace _”Insha’Allah.”_ Da haka sukayi sallama ta shiga ban d’aki tayi wanka tare da d’auro alwala ta fito ta canza kaya tayi sallah. 

Saida ta gama komai a tsanake ta sake fita ta samu Hafsat, tare da duka yaran suka ci abinci saidai babu wani armashi dan ba hira suke ba. Suna gamawa kamar a kan k’aya take ta koma d’akinta ta kwanta abin ta.

Tasha baccinta saida kiran sallah la’asar ya tasheta, a gaggauce tayi alwala tayi sallah ta fito dan d’ora girki.

Falo ta samu Hafsat zaune da littafi a hannu tana karatu, zaune tayi kan kujera tace “Aunty barka da hutawa.”

Da fara’a ta amsa da “Barka Mimi, an fito?”

Da fara’a ita ma tace “E aunty, zan shiga madafa ne dama d’ora girki, me za’a dafa ne?”

Kallonta tayi cike da k’auna da jin dad’in tambayar da ta mata tace “Mimi ni kike tambaya? Kije ki d’ora abinda ranki yake so ko kuma mijinki.”

Yar dariya tayi tace “A’a aunty ku dai ku fad’a min.”

Jim tayi tana murmushi alamar tunani, can ta numfasa tace “To kinga ki d’ora nama, dan sheikh yana son romo sosai, sai kisan dubarar da zaki masa.”

Mik’ewa tayi tana murmushi tace “Shikenan aunty.”

Tana shiga madafar ta samu mai aiki tayi shara tana guga, a nutse ta d’auki nama a fridge ta fara aikinta, mai aikin na gama guga ta kama mata da yankan albasa da tumatir da b’are tafarnuwa da saurensu, suna aikin suna yar hira sama sama har Mimi taji hayaniyar yaran sun dawo daga makaranta, saida ta daidaita komai ta fito a madafar bayan ta kalli mai aikin tace “Ki duba min dan Allah zan je na d’anyi shara a d’akina kafin magriba.”

Jinjina kai tayi tace “To aunty.”

Fitowa tayi ta samesu suna ta labartawa Hafsat labarin abinda ya faru a islamiya, da gudu Munzeer ya tarbeta yana fad’in “Aunty.”

Rumgumeshi tayi tana dariya tace “Munzeer an dawo?”

“E.” Ya fad’a yana kallonta, kama hannunshi tayi tana kallon su Aswan da suke fad’in “Aunty sannu da gida.”

Da fara’a tace “Sannu Aswan, Heezam, har an sauko?”

A tare suka fad’i “E.” Satar kallon Aisha tayi da ita ma take kallonta, wucewa tayi tare da Munzeer d’akinta yana mata hirarshi ta yara, zaunar da shi tayi falo ta shiga ciki ta d’auko chocolat d’in da jiya suka siyo ta kawo mishi, da fara’a ya karb’a da hannu biyu yace “Nagode Aunty, Allah ya biya.”

Da fara’a tace “Ameen yaron Abbanshi.”

Mik’ewa yayi yace “Na tafi na cire kayan makaranta na.”

Jinjina kai tayi tana kallonshi har ya fita a falon, aikinta ta shiga yi ta d’anyi goge goge ta saka turaren wuta dana tsintsiya, tana gamawa ana kiran sallah magrib da sauri ta shiga madafa ta duba tukunyarta, ganin komai ya daidaita ta kashe wutar suka zuba a kwanuka suka kai table kafin ta koma d’aki tayi alwala.

Kwalliya ta d’auka ta ban mamaki cikin doguwar rigar shadda ta kashe d’aurin d’an kwallin da d’azun nan ta kalleshi a YouTube, tana fitowa ita kanta sai ta ji kamar tana tsarguwa dan yanda suke kallonta jefi-jefi sai yasa ta ji d’ar a jikinta, haka ta samu wuri ta zauna suna kallon kallo ita da Aisha, sai Hafsat dake ta danna wayarta tana d’an hira da Munzeer.

Odar da akayi da kuma k’arar bud’e k’ofa ya tabbatar musu da sheikh na shigowa, suna zaune har saida ya shigo da sallama a bakinshi da alamun gajiya a tattare da shi, kusan a tare suka amsa mishi sai Hafsat da sabo yasa ta mik’ewa tana d’orawa da fad’in “Sannu da zuwa sheikh.”

Da fara’a ya amsa mata da “Sannu Manga, ya gida?”

Da fara’a tace “Alhamdulillah, ya aiki ya fama da jama’a? Yau juma’a nasan ansha fama.”

Murmushi yayi ya kalli Mimi da ita ma ta mik’e tace “Sannu da dawowa.”

A tausashe ya amsa da “Sannu da gida.”

Kallon Hafsat yayi yace “Gaskiya kam ansha fama, shiyasa ma na kubto da wuri dan na dawo gareku na samu nutsuwa.”

Dariya tayi tace “Allah sarki, Allah ya k’ara maka lafiya jigonmu, wannan d’awainiya da kake Allah ya baka wanda zasu tallafeka sanda kake neman taimako.”

Wani k’ayataccen murmushi ya saki tsabar farin ciki yasa shi jawo hannunta ya dafa kanta yace “Ameen ya Allah, Nagode sosai Hafsa, Allah ya miki albarka, ke ma kuma Allah yasa yaranki su zama masu jin k’anki.”

Mimi dake kallonsu bata san sanda ta saki murmushi ba dan gaskiya sun birgeta, kuma yana daga cikin abinda yasa ta kasa samun k’ofar rainin a wajen Hafsat d’in shi ne, yanda ta ga shi kanshi wanda take zaune dominshi yana girmama matarshi, sannan ita kan ta matar ta rik’e girmanta kam, ko irin d’an kishinta ta k’i nunawa, shiyasa ita kanta sai taji Hafsat na mata wani kwarjini.

D’auke hannunshi yayi akan Hafsat d’in yana fad’in “Yaran nan basu dawo bane?”

“E, amma na tabbata suna kan hanya yanzu.” Cewar Hafsat, jinjina kai yayi ya sunkuya ya d’auki Munzeer ya nufi d’akinshi yana fad’in “Bari nayi wanka na fito, ina fatan kun kammala abinci?”

Dariya Hafsat tayi tace “Amaryarka ta kammala maka komai, yau idan ka ci abincin nan saï ka manta hanyar shiga d’akinka.”

Dariya sukayi banda Aisha dake kumbura baki sai sheikh da yace “Idan hakane kuwa ya dace a had’ani da d’an jagora ai.”

Zaune Hafsat tayi tana fad’in “Idan zaka biya ai ba matsala.”

Juyowa yayi ya kalleta yace “Yanzu Manga a gidan nan ba za’a min alfarma ba?”

Girgiza kai tayi ta kalli Mimi ma data zauna tace “Ko kad’an, ban sani ba dai ko amarya zata iya.”

Shigewa yayi yana fad’in “Sawwama Allah ya shiryaki.”

Da k’yalk’yala dariya tace “Ameen malam.” Yana shigewa ta kalli Mimi cikin rad’a tace “Mijinki fa yana son kulawa sosai, ki sameshi hakan zai faranta mishi rai.”

Sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ita har yanzu jin abun take babba idan aka had’ata da shi matsayin miji da mata, d’an dukanta Hafsat tayi a cinya tace “Haba Mimi, tashi mana, wallahi zai ji ba dad’i, ki yarda da maganata, ina fad’a miki hakane saboda na sanshi sosai.”

Jinjina kai tayi ta mik’e ta nufi d’akin na shi, hararanta Aisha tayi ta d’auke kanta, kallonta Hafsat tayi banka mata harara tayi tare da k’wafa ta jinjina kai alamar zaki sani, turo baki Aishar tayi tace “Kiyi hak’uri Amie.”

A dak’ile tace “Hak’urin me Aish? Tunda kin gama rainamu ai shikenan sai kiyi, nasan dai burinki bai wuce ki ji ana fad’a a gari cewa Aisha yar malam ce ta k’i halin malam, na tabbata abinda kunnuwanki suke so su ji shi ne ke kamar ba ‘yar sheikh Abdul Waheed ba saboda halayyanki.”

Da sauri tace “A’a Amie, dan Allah ki daina fad’in haka, na tuba Amie ki yafe min.”

Jinjina kai tayi tana d’aukar wayarta tace “In gaskiya ne abinda kika fad’a idan Mimi ta fito ki bata hak’uri, hakan zai sa na yarda gaskiya kike fad’a.”

Kumburo baki tayi ta d’an jinjina kai alamar to, d’auke idonta Hafsat tayi daga kallonta, dan tana so dole ta ga canji a tare da Aisha, idan tace zata fito da kishinta ne yanda Aisha ke buk’ata gidan nan ba zai d’aukesu ba, idan ta ce zatayi kishi da Mimi ne to zata cinyeta ta had’eta. Amma duba da wasu abubuwq yasa ta d’auke kai da kawar da kanta, duk abinda zata gani yanzu tasan na d’an lokaci ne, a shekaru kamar na sheikh arba’in da bakwai zuwa da takwas ya samu yarinya kamar Mimi yar sha bakwai da zata shiga takwas, me zata tsammani dama? Idan ma baiyi rawar k’afa ba ai sai tace mijinta ba namiji bane, dan haka zata had’e komai har sanda ita ma zatayi cikar d’aki su zama d’aya, tabbata hakan zai sa ta tashi da riba biyu, ta farko shi ne daraja da mutumcinta basu zube ba a wurin mijinsu, sannan ita kanta Mimi ba zata samu k’ofar rainata ba, dan kuwa tayi ‘ya da ita, miji da suka had’a ba zai sa ta rainata ba.

*Barkanmu da sallah yan Uwa.*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *47*

Tana shiga ta sameshi yana cire kaya Munzeer kuma na gaban madubinshi da wayarshi a hannu, k’ura mata ido yayi har ta k’araso habanshi ta tsaya kanta sadde, shafa kuncinta yayi yana murmushi yace “Ryam kin ganki kuwa, a gaskiya kinyi kyau ba kad’an ba.”

Cike da kunya da ladabi ta amsa da “Nagode.”

Saida ya aje rigarshi babba daya cire ya sa hannu aljihu, kud’i ya d’ebo da shi kanshi baisan adadinsu ba ya kamo hannunta ya damk’a mata yace “Wannan tukuicin wannan kwalliyar nan, kuma a shirye nake na dinga biya kullum indai ba ayi wacce zata fi k’arfin aljihuna ba.”

Murmushi tayi tana son zame hannunta tace “Nagode, amma ba sai ka biya ba, yabawa ma da kayi ya wadatar dan shi ne k’arfin gwiwar, zan iya siyan kayan da gumina ma indai zaka yaba.”

Girgiza kai yayi yana dariya yace “A’a Ryam, ni fa ina d’aya daga cikin masu fad’a a waje a dinga yi wa mata kyauta musamman idan sunyi abinda ya birge, sai kuma ni na zama mai hannun jarirai a gidana? A’a wallahi baki isa ba.”

Ya fad’a yana damk’a mata kud’in, karb’a tayi da hannun biyu tace “Nagode, Allah ya biya.”

Da fara’a yace “Ameen.”

D’an kallon Munzeer tayi dake ta tak’ular waya tace “Zan fita na barku ka shirya.”

Shi kanshi dake akwai hirar da yake son yi da yaron sai bai hanata ba, da kallo ya bita ganin yar car da ita a fuska amma mazaunanta sai wani kad’awa suke, lumshe ido yayi ya girgiza kai yana d’an lashe leb’e.

Mayar da kallonshi yayi kan Munzeer da hankalinshi ke kan waya yace “Yau an fad’a min kun makara a zuwa makaranta da yamma? Me yasa?”

Zaro ido yayi ya kalleshi ya girgiza kai cikin muryar yarinta yace “Abie inji wa? Mun isa akan lokaci fa, a can mukayi sallah la’asar.”

Murmushi ya masa jin ya amsa tambayar daidai ya d’ora da fad’in “To amma ai da kuka tashi an ce kun tsaya a hanya ko?”

Nan ma da sauri ya girgiza kai yace “A’a Abie, bamu tsaya ba, ka tambayi dreba kaji.”

Jinjina kai yayi yace “To amma me yasa Aswan bai bayar da sallah ba yau a masallaci?”

A tsorace yace “Abie ya bayar fa, ka tambayi su Anas kaji.”

Kallon tuhuma ya masa yace “Amma ba a gaban Heezam ya tsaya kula yaran unguwar nan dana hanashi ba?”

Turo baki yayi yace “Abie ba kulasu yayi ba, sun mishi magana sai shi ma ya musu saboda yace ka fad’a mana ba kyau wulak’anta mutum.”

D’auke kanshi yayi yace “Me suka tattauna?”

Jim yayi alamar tunani sai kuma yace “Gaisawa ne sukayi sai kuma ya fad’a musu zai shiga majalisi, shi ne sai wani yace shi ma yana so ya fara karatu tare da shi.”

Murmushin jin dad’i yayi yace “To me yasa yau a gidan akayi ta fad’a? Baka tsawatar musu bane?”

Galala ya kalleshi sai kuma yace “Abie yaushe?”

Kallonshi yayi yace “Kana nufin baka san lokacin ba?”

Girgiza kai yayi yace “Abie babu wanda yayi fad’a.”

Kallonshi yaayi da zolaya yace “Halan yawo ka tafi?”

Girgiza kai yayi yana dariyar jin kunya yace “A’a Abie, ban fita ko ina ba.”

Dariya yayi cikin farin ciki da jin dad’in babu abinda ya faru marar kyau bayan fitarshi, ban d’aki ya shige ya barshi da wayar a hannu yana ta latsawa yana buga game wanda dama saboda shi yake a wayar, shi ma kuma dan abune na wasa da ta wani fannin yana anfanar tunani da k’walwar yaro yasa ya barshi har yake bugawa lokaci lokaci.

Ya d’auki lokaci sosai kafin ya fito rik’e da hannun Munzeer, dukansu zaune ya samesu har su Heezam da basu jima da shigowa ba, gaisheshi sukayi su ma ya amsa da fara’a har da tambayarsu darasinsu sanda suke zama kan table, Hafsat da Mimi ne suka tsaya zasu zuba abinci Mimi ta kalleta tace “Aunty ki barshi ma zan zuba.”

Murmushi tayi ta zauna tana aje plate d’in data d’auka, a nutse ta shiga zuba abincin ta fara ajewa gaban sheikh, kafin ta zubawa Hafsat da a lokacin ta kalli sheikh take fad’in “Sheikh gaskiya satin nan ina so na je na ga ‘yata, wallahi kewarta hanani bacci take.”

Dariya yayi yana kallonta yace “Kewarta na hanaki bacci ne jiya na sameki kina ta juyi akan gado?”

Dariya tayi tana rufe fuska da tafin hannu, jinjina kai yayi ya kalli Heezam yace “Ki shirya sai kuje tare da shi ya rakaki, idan kuma zaki je gobe to ki shirya mu tafi tare.”

Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta tace “Kai amma naji dad’i, zan shirya goben sai mu tafi.”

Jinjina kai yayi yana kallon plate d’in gabanshi, shinkafa ce mai curry da jar miyar kaji, saidai yanda yaga naman a ido ya tabbatar masa da ya samu aiki mai kyau kuma zaiyi dad’i, ga k’amshin dake ta shiga hancinshi tunda ta aje gabanshi, kallonta yayi sanda take zuba wani a plate yace “Ryam.”

A ladabce ta gaggauta kallonshi tace “Na’am yallab’ai.”

Kallon plate d’inshi yayi yace “Da alama abincin nan ba zai isheni ba, a k’aro min gaskiya.”

Dariya sukayi dukansu ban da Aisha da Munzeer dake cakalar waya, ganin Mimi bata ce komai bayasa Hafsat fad’in “Allah gafarta ka jira ka cinye na gabanka mana.”

Kallonta yayi a marairaice yace “Na sani ne ba zai isheni ba, amma tunda kince haka shikenan.”

Kallon Mimi yayi yace “Ki rage min saura kinji.”

Jinjina kai tayi tace “Angama yallab’ai.”

Aje plate d’in tayi gaban Aisha dan girma ne take bi wajen zuba abincin, d’an ture plate d’in Aisha tayi ta yatsina fuska tace “Na k’oshi ni.”

Kallonta duk sukayi sai Mimi da tace “Kin k’oshi? Kin ci wani abu ne?”

Kumburo baki tayi amma ba tace komai ba saboda sheikh dake wurin, Heezam daya gama lura da kallon da sheikh ke ma Aisha ne yayi saurin cewa “Aisha ki ci abinci mana.”

Kallonshi tayi tace “Na k’oshi na ce.”

Hafsat ce tace “Ku barta mana, cikin waye? Dan kanta.”

Kallonta Mimi ta sake yi tana k’ak’aro murmushi da tunawa da maganar Mama ta turawa Aisha plate d’in tace “Aisha ki ci abinci kinji, idan ni ce ba kya son girki na saina daina.”

Cikin b’acin rai Hafsat tace “Ki daina kamar ya? Nan ba gidan mijinki bane? Ke da ita waye yake da iko a gidan nan? Ita fa kwana kad’an ya rage mata a gidan, ke kuma gidan mijinki ne da muke muku fata har mutuwa, shikenan saiki daina girki saboda ita, wacece ita? Kar Allah yasa ta ci mana taga idan wani zai daina rayuwa akan haka.”

Sharrrr! Wasu hawaye masu zafi suka taho ma Mimi, dan wani iri take ji a zuciyarta kamar ta koma gidansu tayi rayuwarta cikin yancin, aje cokalin da take zuba miya tayi ta juya da sauri ta nufi hanyar da zata sadata da b’angarenta, tana shigewa ta fashe da kuka ta fad’a kan kujera.

Suma suna ganin shigewarta sheikh daya rasa me ke masa dad’i ganin abinda ke neman kunno masa kai ya kalli Aisha, a tsanake ya shiga kallon duka yaran sai kuma ya jawo plate d’inshi da kyau ya d’auki cokali yana shirin d’ibar lomar farko yana fad’in “Mu ci abinci.”

Kallonshi sukayi duk sai suka tsargu, duk da basu san shi da duka ba amma sun san shi da fad’a, Heezam ne ya mik’e ya fara zubawa kanshi abinci hakan yasa Aswan jawo na gaban Aisha da tace ba ta ci. Kallonshi Hafsat tayi tace “Sheikh kuka fa take? Ka bata hak’uri dan Allah, karta damu da haukan yarinyar nan.”

Yi yayi kamar bai ji ta ba ya lumshe ido yana fad’in “Gaskiya abincin nan yayi dad’i.”

Cike da damuwa da kulawa Hafsat tace “Sheikh.”

“Um.” Ya fad’a yana kai wata lomar bakinshi dan ji yake kamar ya tsinke harshenshi, a sanyaye tace “Dan Allah kayi wani abu a kai.”

Sake shareta yayi hakan yasa ta mik’ewa a hassale tace “Shikenan nagode.” D’akin Mimi ta nufa dan bâ ta hak’uri akan wautar Aishar.

Ko kallonta baiyi ba har ta shige, cike da rashin jin dad’i Heezam ya kalleshi a ladabce yace “Abie.”

A k’asan mak’oshi yace “Ina ji.”

Cike da tsoro yace “Dan Allah kayi hak’uri.”

Kallonshi yayi da idonshi da suka fara canzawa alamar b’acin rai, aje cokalin yayi ya tallabe hab’arshi da bayan hannu yace “Hak’uri akan me? Wani laifi kukayi ne?”

Kallonshi Aisha tayi kamar zatayi kuka tace “Abie dan Allah.”

Wani kallo ya wurga mata kamar zai had’eta, da nuna rashin damuwa yace “Me ye a ciki? Kuka ne take, ku barta tayi mai isarta ta k’oshi zatayi shiru dan kanta, idan kuma ta ji ba zata iya zama a haka ba ta tafi gidansu, iyakarta dai idan taje ta ce Abdul Waheed azallumi ne wanda bai san darajar aure ba, sai iyayenta kuma su ce ni d’in ashe dama tsohon banza ne da bai san mutumcin mace ba, sai mutanen gari kuma idan suka ji su ce ashe ni d’in babban mak’aryaci ne kuma mutumin banza wanda ya kasa tarbiya a gida, wanda yaranshi basu da tarbiya da sanin girman mutum, su d’ora da fad’in *dama ba’a aikin da abinda malamai ke yi, kawai kayi aiki da abinda suka fad’a maka*, shikenan idan aka fad’i haka? Kunji dad’i kenan?”

Cokalinshi ya d’auka zai ci gaba da cin abinci yace “Matata ce ita ma, ko bana sonta ba zan wulak’anta ta ba, ku kuma ‘ya’yana ne da babu yanda zanyi na rabu da ku, tunda ba kwa so na da aurenta shikenan, ku fad’a min da bakinku yanzun nan sai na korata gidansu na ci gaba da zama da uwarku kamar yanda kuke buk’ata.”

Heezam ne yayi saurin fad’in “A’a Abie dan Allah, ka yafe mana mun tuba.”

Kallonshi yayi sai kuma ya mik’e ya bar wurin duk da kuwa yana son cin abincin sosai saboda yana jin yunwa kuma ya masa dad’i.

Heezam ne ya kalleta rai b’ace yace “Aisha kin gani ko? Kin ga kina so ki ja mana hushin iyayenmu ko? To wallahi ba zai yiyu ba.”

Mik’ewa yayi shi ma ya bar wurin, Aswan ma harara ya galla mata ya mik’e yana fad’in “Ai gwara ma da zai aurar dake? Haka kawai zaki b’ata mana sunan gida.”

Da kallo ta bisu baki sake sai kuma ta mik’e ita ma da sauri ta nufi d’akinta tana fashewa da kuka.

Hafsat na shiga ta samu Mimi a falon tana kuka, da sauri ta k’arasa tana fad’in “Subhanallah! Mimi kuka?”

Da sauri ta d’aga kanta tana share hawayen ta k’ak’aro murmushi, saida ta zauna kusanta suna kallon juna tace “Mimi kuka kike? Kiyi hak’uri dan Allah, wallahi ban san a ina Aisha ta d’auko wann…”

Da sauri Mimi ta rik’e hannunta data dafa kafad’arta tace “A’a aunty, dan Allah karki bani hak’uri, ba ina kuka bane saboda abinda Aisha ta yi, kiyi hak’uri idan na d’aga miki hankali.”

A marairaice ta ci gaba da kallonta da tausayi tace “Mimi bana so mu shiga hakk’inki, ni kaina dake uwarta bansan a ina ta samo sabbin halayen nan ba, hakan yasa har na fara matsuwa a d’aura aurenta dan kar ta ja min wata maganar.”

Da mamaki ta kalleta tace “Aunty Aisha dama aure zatayi?”

Jinjina kai tayi tace “E, ranar juma’a za’a d’aura aurenta.”

Sak’e tayi tana saurare sai kuma tace “Allah yasa alkairi.”

“Ameen.” Ta fad’a a sanyaye, kallonta ta sake yi da kyau tace “Kin daina kukan yanzu?”

Jinjina kai tayi tana k’ara share hawaye tace “Na daina aunty, karki damu.”

Murmushi ta mata ta mik’e tana fad’in “Saida safe, zan shiga na kwana.”

Da fara’a ta amsa da “Saida safe aunty.”

Da kallo ta bita har ta fita a d’akin, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin lallai Allah ya had’ata da yer uwar data rasa, tana jin k’aunar Hafsat d’in har ranta kuma zata ci gaba da girmamata iya iyawarta.

Hafsat na ganin falon ba kowa kawai ta girgiza kai ta k’ara gaban table d’in ta tattara kwanukan sannan ta zauna ta k’arasa cinye na ta, saida ta ji ta k’oshi tasha ruwa ta mik’e da plate din ta kai madafa sannan ta wuce d’akinta.

Ta jima zaune a falon tana tunanin shin zata kama ma Aisha ne su zama abokan fad’an juna? Ko kuma dai ta nuna mata na gaba yayi gaba, ta nuna mata lallai fa ita d’in matar ubanta ce? Da wannan shawarar ta mik’e ta fita a falon, shiru babu alamar kowa kamar ba kowa a gidan, table ta wuce kai tsaye ta d’ibi abincin da zata iya ci ta koma falonta ta zauna, yaghourt ta d’auko da ruwa ta zauna ta dinga cin abincinta cikin nutsuwa, dan tun shekaran jiya da suka wuni gidan can sunyi waya da Rakiya ta fad’a mata ta dinga ci tana k’oshi hakan zai sa d’inkinta ya warke da wuri, tas ta cinye abinta ta sha yaghourt din nan kafin ta sha ruwa, d’auke kayan tayi ta mayar sannan ta dawo kai tsaye ta wuce d’akin baccinta, cire kayanta tayi ta shiga wanka.

Saida ta fara zama a ruwan d’umi har ta laluba ta ji d’inkinta yana warkewa kafin tayi wankanta ta fito, bata shafa mai ba dan tana da jin zafi, humra ta shafe jikinta da ita sannan ta d’ora da shafa turarenta na kullum mukhallat, riga mai dogayen hannaye da wando dogo ta saka na bacci masu taushi ta haye gado bayan ta kashe wuta taja bargo ta tofe jikinta da addu’a.

*11:00* daidai ya gama da karatun da sukeyi tare da su Anas ya shigo gidan bayan sunyi waya da mahaifin Anas d’in kan maganar aurensu da Aisha, yana shigowa ma ya rufe kowace k’ofa dan yasan kowa ya kwanta yanzun, k’ofar shiga d’akin Hafsat ya fara bud’ewa, yanda ya sameta tana bacci a wannan lokacin ya d’an bashi mamaki, sai kuma ya share kawai ya k’arasa a hankali, kusanta ya sunkuya ya sumbaci kuncinta tare da shafa kanta, k’ara gyara mata rufar yayi sannan ya kalli Munzeer dake gefenta shi ma yayi bacci, murmushi yayi ya shafa kan yaron sannan ya juya ya fita. Duka d’akunan yaran ya duba saidai dukansu babu wanda yake bacci, Aisha na karatun Alqur’ani sai Heezam dake ta cakular na’ura kasancewarshi mai son zama mahaddacin hadisai, sai Aswan kuma da littafinshi na islamiya, babu wanda ya ma magana a cikinsu saidai ya rufe k’ofar kawai ya yi gaba.

D’akin Ryam ya wuce yana sakin murmushi saboda yarda da yayi lallai yarinta na damunta, a zuciyarshi kawai yake fad’in “Ban da abun Ryam ta ya zaki daina girki a gidan mijinki?”

Yana bud’a k’ofar ya ga shiru falon ya rufe ya nufi d’akin baccin, yanda yake takawa cikin sand’a kamar marar gaskiya, yana bud’e k’ofar ya hangeta da alama tayi nisa a bacci, ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido, k’arasawa yayi ya zauna bakin gadon yana kallon fuskarta, yanda ta kumburo baki fuskarta tayi fes babu d’igon kwalli sai ta masa kyau, shafa lallausan gashin kan ta yayi mai sulb’in gaske, d’an rank’wafawa yayi ya sumbaci goshinta sannan ya rad’a mata a kunne “Ina sonki Ryam.”

Motsawa tayi kamar zata farka sai kuma ta sake lumshe ido, jim kad’an baccin ya sake figarta yayi gaba da ita, ganin yanda tayi kamar wata jaririya yasa shi sakin murmushi yana mik’ewa tsaye, doguwar rigarshi kalar ruwan k’asa ya cire tare da sibglet d’in shi, haurawa yayi kan gadon daga shi sai dogon wando yaja bargon ya shige ciki, jawota yayi jikinshi ya rumgumeta tsam.

Kamar zaiyi bacci sai kuma ya zura hannunshi a rigarta ya fara shafa k’irjinta, lumshe ido yayi saboda abunda ke tsarga masa har kwanyar kanshi, a hankali ya fara fita hayyacinshi yana sauke wani marayan numfashi mai fitar da sautin gurnani, sosai ya fara rikitata a cikin baccinta, neman rabata da rigar ya neme yi hakan yasa ta farkawa a tsorace tana rarraba ido, suna had’a ido ta sake jawo bargon ta zuba mishi ido, jawoya ya sake yi jijinshi yana son sumbatarta a baki, zillewa tayi ta kawar da kanta a ladabce tace “Abdul.”

A k’asan mak’oshi ya amsa da “Ummm!”

Saida ya kwantar da ita ya d’ora harshenshi a kan mamanta yana zagayawa da shi ya kalli fuskarta yace “Uhum.”

Marairaicewa tayi tace “Ka daina.”

Da shanyayyun idonshi ya kalleta yace “Saboda me? Ina so na raya dare na Ryam.”

Cikin shagwab’a ta b’oye fuskarta cikin bargon tace “Ban warke ba fa har yanzu.”

Tsam ya kalleta yace “Da gaske?”

D’aga kai tayi alamar eh, yatsina fuska yayi yace “Amma ke kika fad’a min kinji sauk’i.”

Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace “Gaskiya ban warke ba.”

Shafa cikinta yayi daya d’an taso saboda k’oshin da tayi har yayi sama da hannun zuwa nonuwanta, shafawa ya dinga yi tare da saka d’aya a bakinshi yana tsutsa a sanyaye, shiru ta masa tana saurarenshi jikinta har kakkarwa yake na tsoron abinda yake mata, dan ba zata tab’a mantawa da daren ranar laraba ba, dare na daya shiga tarihin rayuwarta, dare ne da sheikh Abdul Waheed ya kafa mata tarihi da ba zai gogu ba, ya bata wahalar da ita kanta tasan tayi juriya sosai data sauk’ak’a masa hukunci, dan haka a yanzu dai da wuri ba zata bari ya saké saka mata wannan al’amari ba da a ranar ya kwana a cikinta ba, dan abu ne da kad’an ya rage ta ji shi a cikin bakinta, abu ne da idan ya zungurota har amai ke neman b’allowa ya taho mata.

Wasa tayi nisa sosai sheikh yana neman gangarawa dan ya rabata da komai na jikinta haka shi ma, yana neman hanya madaidaiciya tare da d’orawa da addu’ar neman kariya kawai Mimi ta fashe da kuka ka rantse da Allah cizonta yayi, dakatawa yayi yana kallonta da jajayen idonshi ya fizgo kalamai kamar haka “La..fiy…ya?”

Girgiza kai tayi tace “Kayi hak’uri sheikh kar kayi, wallahi akwai ciwo.”

Rintse idonshi yayi jim leb’enshi na k’asa a cije gam, ya d’an jima kafin ya bud’e ya kalleta ya had’a goshinsu har numfashinsu na gauraya yace “Ryam…ina cikin wani hali, dan Allah ki barni nayi…kinji, na kai matakin da ba zan…”

Sai kuma ya had’a bakinshi da na ta da sauri yana tsutsa tare da ci gaba da saita hanyarshi, hannayenta tasa duka biyu ta rufe gabanta duk da k’azantar da take ji sharkaf a gaban na ta, a rikice ta nemi tashi zaune tana wani kukan na shagwab’a tana fad’in “Abdul wallahi ciwo zan ji, ban warke ba har yanzu.”

Kwantar da ita yayi da k’arfi ya kai hannunshi k’asanta yana fad’in “Bari na ji to.”

K’asa yayi da kan shi ya janye hannayenta ya d’an bud’e k’afafunta…😎 (gyara kimtsi).

Sosai take kuka da hawayenta har da majina, salon da yake mata ya girmi shekarunta bare kuma tunaninta, a nutse ya dinga kashe mata da bakinshi, ko ina ya kai hannunshi kuma ya kai bakinshi, tun jikinta na yin lak’was dan sanyin har ta fara zabura tana jin kamar zata mayar mishi da raddin abinda yake mata, hakan yasa ta yin kuka dan ba zata iya sakin jikinta ta dinga mishi abinda yake mata ba. Wannan kukan data fara ne kad’ai yasa shi sarara mata ya barta haka bayan shi kanshi ya d’an samu nutsuwa, shafa bayanta ya fara yi yana fad’in “Shiiiiiii!”

A hankali gumin da yayi ya fara tsanewa saboda acn dake kunne, sai kuma bacci daya fara neman d’aukarshi, da sauri ya jayeta daga jikinshi ya sauka a kan gadon, bakin k’ofar ban d’aki ya k’arasa ya d’auki towel ya d’auka a k’ugu sannan ya dawo ya d’auketa cak yayi ban d’akin da ita.

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *48*

Tunda tayi sallah asuba ta shiga madafa ta fara da dafa dankalin turawa, kafin su dahu ta fara yankan albasa da tamatir ta jajjaga tarugu ta aje gefe, k’wai ta buga adadin da zai isheta ta ajiye gefe shi ma, dankalinta na gama silala ta juyeshi ya rage zafi kafin ta fara b’are bayan, tana gama b’arewa ta yankashi k’anana ta aje gefe guda, k’wanta data buga ta gyarashi ta d’auki abun suyarta (frying pan, casserole) ta d’ora a wuta, tana d’aukar zafi ta zuba mai kad’an ko da yayi zafi ta d’auki k’wanta ta zuba, yana fara soyuwa daga k’asa ta d’auki dankalin nan ta zuba tasa cokalin katako ta juyeshi da kyau suka had’e tare da k’wan, saida ya soyu ta juyeshi a kwano mai rik’e zafi sannan ta ci gaba da soyawa, cikin d’an lokaci ta gama ta bud’a fridge ta d’auki zobon da Hafsat ke ajiyewa dafaffe kuma tattacce, zubawa kawai tayi a roba ta d’auki markadadden citta da na’a na’a da flavour ta saka, kokonbre ta d’auko ta wanke ta yankashi ta saka a blender ta markad’a ta tace a ciki kafin ta d’auki zuma ta saka kamar yanda Hafsat ta fad’a mata zuma suka fi aiki da ita, tana gamawa tasa a fridgr ta rufe sannan ta d’auki kular abincin ta kai akan table, madafar ta koma ta gyara komai kamar ba tayi aiki ba sannan ta wuce d’akinta dan har lokacin bata jin motsin kowa a gidan.

*08:05* fitowarta daidai da fitowar Hafsat falon, suna had’a ido suka sakarwa juna murmushi inda Mimin tace “Aunty ina kwana?”

Da fara’a sosai ta amsa da “Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?”

“Lafiya lau, ya k’arfin jiki?”

 Ta fad’a suna k’arasawa falon gaba d’aya, da sakin fuska ta amsa da “Alhamdulillah, ina d’aki ai ina jin motsi nayi tunanin ke ce, ban lek’o bane saboda ina d’aukin zan je asibiti ganin Khadija.”

Da yar dariyarta tace “Hakane aunty, dama abun kari na had’a.”

Saida ta aje jakarta kan kujera tace “Sannunki da k’ok’ari Mimi.”

Kallon k’ofar d’akunan yaran tayi tace “Ina su Munzeer ne? Ko basu tashi ba.”

Kallonta Hafsat tayi tace “Suna shirin islamiya ne, yanzu zaki gansu nan.”

K’ofar falon sheikh Hafsat ta kalla tace “Bari na duba yallab’ai na fad’a mishi na shirya.”

Jinjina kai tayi alamar to ta bita da kallo har ta shige, zaune tayi tana murmushi da mamakin yanda Hafsat d’in ke kula da jikinta kamar bata haifi Aswan ba ma bare kuma Aisha, dan masha’Allah yanda yaran sukayi jikin girma Heezam kan shi sai ya d’auki uwar ta shi idan aka shiga halin rintsi. Kuma ba komai bane ya kawo haka sai hutu da jin dad’i, sannan da gado, dan yanda ta ga Hafsat doguwa shi kanshi sheikh dogo haka Asas da ita kan ta Hajiarsu, da ma dayawa a cikin danginsu ya nuna dama can mutanen tsayi ne su d’in.

Da sallama ta shiga falonshi tana sauke idonta akan kujerar da ta san ya fi zama a kai a wannan lokacin, a sanyaye ya amsa sallamarta tare da rufe littafi mai tsarkin dake hannunshi, saida ta k’arasa kujerar kusa da shi ta zauna tana sunkuyar da kanta tace “Barka da safiya yallab’ai.”

Da fara’a yana kallon fuskarta yace “Barka matar sheikh, kin tashi lafiya?”

Da murmushi tace “Lafiya lau, ya himma?”

Saida ya muskuta zai mik’e tsaye yace “Angode Allah, har kin shirya?”

“Um.” Ta fad’a a tak’aice tana kallonshi, mik’ewa yayi yana yar gajeruwar mik’a yace “Bari na gaggauta na shirya sai mu tafi, kinsan yau asabar babu aiki.”

Mik’ewa tayi ita ma tace “Idan muka dawo kenan ba zaka fita ba?”

Saida ya nufi shiga d’akin na shi yace “E to gani dai, sai yanda kuka zab’a mana.”

Jin haka yasa ta yin jim kamar mai tunani, sai kawai tace “In kuwa hakane zaman gida ya kamace ka gaskiya.”

Murmushi yayi yace “Yanda kike so haka za’ayi yar aljanna.”

Shigewa yayi ita ma ta fita a falon dan bashi damar shiryawa a tsanake, tana zuwa ta samu Mimi zaune ta saki murmushi, haka kawai har zuciyarta ta ji ta bata tausayi, ba dan komai ba sai dan yanda ta ga yarinyar bata wani damu da kulawa da mijin na ta ba, kawai babu ruwanta da shi bare al’amuranshi, k’arasowa tayi ta zauna kusanta dan tana zzune ne kan kujera zaman mutum biyu, murmushi suka sakarwa juna inda Hafsat d’in tace “Sheikh na magana.”

Da sauri ta kalleta sai kuma ta mik’e tana fad’ad’a murmushinta tace “To.” Nufa d’akin tayi da saurinta ita tsakani da Allah shi ne ke kiranta, da kallo Hafsat ta bita sai kuma ta ji wata suka a zuciyarta, d’auke idonta kawai tayi a kan ta tana fad’in “Allah kasa na fi k’arfin zuciyata.”

Fitowar yaran a d’akinsu yasa ta juyawa tanz kallonsu, kowanensu cikin kayan makaranta sun shirya tsaf, da yake sun gaisheta tun safe sai kawai tace “Ku hanzarta ku ci abinci ku wuce lokaci ya kusa.”

Gurin table d’in suka nufa suna aje kayan karatunsu, mik’ewa tayi ta fara zuba musu da kan ta dan yau asabar mai aiki bata zuwa, ita kanta ta yaba ta kuma fara amanna cewa Mimi k’arshe ce a fanin girki da kwalliya. Yaran kansu suna fara cin abincin saida suka yaba musamman ma Aswan, ita ma zaunawa tayi ta fara cin nata kafin sheikh ya fito su wuce.

*Mimi* kam na shiga ban d’aki ta ji motsinshi yana wanka, d’an k’wank’wasa k’ofar tayi tare da fad’in “Kana magana ne?”

Shiru yayi yana rarraba ido sai kuma yayi gyaran murya, turo baki tayi ta bubbuga k’afafu ta sake fad’in “To ni kayi magana ko na ji me kake so.”

Kashe panpon yayi tare da takowa ya zo ya bud’e k’ofar, jin motsin yasa ta zubawa k’ofar ido tana kallo, yana bud’ewa yaja k’ugunta zuwa ban d’akin da k’arfinshi, k’ara tayi lokaci d’aya kuma tayi shiru tana zazzaro ido, tabbatarwa dai babu komai a jikinshi yasa gabanta wani mummunan fad’uwa ta rintse idonta gam, had’a jikinshi yayi da na ta hakan yasa shaddar jikinta d’aukar damshin ruwan jikinshi, kallon fuskarta yayi yana kashe mata ido yace “Ya dai? Me kike nema?”

Ba tare data bud’a ido ba cikin gigicewa tace “Ni fa wallahi, ni fa cewa akayi kana kirana, ban san wanka kake ba ai da ban shigo ba, yanzu dai kayi hak’uri ka sallameni to.”

Sake matseta yayi a jikinshi yace “Tunda har aka ce ina kiranki to hakane, aljanin daya fad’a miki haka bai miki k’arya ba, ina son wanda zai min wanka ne dama sai kuma ga ki.”

Da sauri ta bud’a ido tana ware bakinta tace “Dama akwai aljanu a gidan nan?”

Lumshe ido yayi ya d’an jinjina kai kad’an yace “Sosai, kin tab’a ganin gidan malamin da babu aljanu?”

Da k’arfin bala’i cike da gasgatawa tayi ram da k’ugunshi da hannayenta biyu ta d’ora kanta a k’irjinshi tana kukan shagwab’a tace “Wayyo Allah, Mama kin gani ko, saida na fad’a muku a’a amma baku saurareni ba.”

D’aga kai tayi ta kalleshi duk da alamunshi ya nuna yana gumtse dariyarshi ne tace “Abdul, ka rantse da Allah akwai aljanu a gidan nan?”

Bushewa yayi da dariyar daya rantse da Allah ya shekara baiyi irinta ba, shi wai ya rantse da Allah? K’yalk’yala dariya yake sosai har da sakinta yayi yana ja baya, kamar sakara ta bi shi da kallo da mamakin me yake ma dariyar? Saida yayi mai isarshi ya tsagaita yana kallonta yana girgiza kai, da k’yar ya iya fad’in “Da gaske Ryam, kina so na kira miki autansu yanzu ya zo ya gaisheki?”

Matsawa tayi daf da shi ta shiga d’an jujjuyawa tana kallon ban d’akin.

Rumgumeta yayi a jikinshi yace “Ryam ba yanzu ba fa, saida dare suke shawaginsu.”

Kallonshi tayi tace “Abdul tsoro nake ji, ina tsoron marin aljani fa.”

Shafa bayanta yayi da sigar rarrashi yace “Haba wa ma ya isa? Wane marar kunyar aljani ne zai mari amaryar Abdul a gidan?”

Sake lafewa tayi a k’irjinshi tace “To ka daina tsorata ni ka ji.”

Jinjina kai yayi alamar to, d’agata yayi daga jikinshi yana kallon fuskarta yace “To za’a min wankan yanzu?”

Da sauri ta kalleshi ta zaro ido tace “Wa? Ni d’in?”

Da gudun tsiya ta juya ta bar ban d’akin tana rufowa tace “Ban iya ba Abdul.”

Da dariya ya bita yana kallonta yana jin kamar shi ma ya shek’a da gudu, hakan yasa shi jin ina ma su kad’ai ne a gidan ai da sai yayi koyi da fiyayyen hallita da matarsa Nana Aisha, amma duk da haka ba komai zai jira ya samu wata damar zai d’abbaka wannan sunnar ita ma.

Yana fitowa a gaggauce ya shirya yace Mimi ta kawo masa abun karinsa, falon ta samesu su ma suna ta hanzarin gama na su karin, a nutse ta d’auki plate ta fara zuba soyayyen k’wan da dankalin, yanda ta zuba shi a plate d’in yayi kyau a ido ma, kafin ta d’auki robar yaji ta d’an zuba kad’an ta d’auki mayonnaise shi ma ta zuba a gefe, sai Hafsat ta samu kanta da kallonta dan ita data zuba ma yaran duk bata zuba wannan abubuwan ba, saboda bata d’auka haka ake zubawar ba ma, wani plate ta ga ta d’auka ta rufe da shi sannan ta d’auki juge d’in lemun ta d’ora a babban faranti sannan ta nufi d’akin na shi, suna ganin shigewarta suka mik’e suka ma mahaifiyarsu sallama suka bar gidan.

Da sallama a bakinta ta shigo yana tsaye yana gyara mab’ullan hannun rigarshi, aje farantin tayi ta k’arasa kusa da shi ta kama hannun na shi ta shiga gyara mishi, murmushi ya mata yace “Nagode.”

Ita ma murmushin tayi tace “Sheikh.”

Zuba mata ido yayi cikin sangarta yace “Ryam.”

Kallonshi tayi saboda shagwab’ar da ta ji yayi sai ya bata kunya, d’orawa yayi da fad’in “Na fad’a miki’a fi so naji sunan Abdul daga bakinki, fad’in sheikh baya miki kyay ko kad’an.”

Cikin rangaji da rausaya tace “To Ab-dul.”

Murmushi yayi saboda yanda ta ja sunan yace “Ina jinki.”

Cikin shagwaba da turo baki tace “Ina so na ga Mama na da Abba na da su Yaseen, zaka kaini?”

Girgiza mata kai yayi yace “Um um! Amarya bata fita sai ta kwana biyu.”

Da sauri tace “To amma ai ni na kwana uku a gidanka.”

Dariya yayi yana girgiza kai yace “Ba irin wannan kwana biyun ba, ina nufin sai kin jima.”

Bubbuga k’afafu ta fara yi a k’asa tana kuka tana fad’in “Ni dai wallahi sai na je.”

Da mamaki ya kalleta yace “Saï kin je? Ta ya ya?”

Kallonshi tayi tana kumburo baki tace “Kana fita ni ma zan tafi, tunda ai na fad’a maka kai ne baka barni ba.”

Kyalkyalewa yayi da dariya ya nufi wajen farantin data aje yace “To ki je ga hanyar nan, ina dawowa aljanuna zasu fad’a min kin fita ba da izini na ba.”

Matsawa tayi kusanshi a marairaice tace “Yanzu Kenan ba zaka barni na tafi ba? Gidanmu ne fa? A can ka d’aukoni ko ka manta ne?”

Girgiza kai yayi yana jefa lomar farko bakinshi, lumshe ido yayi yace “Uhummm! Ryam wai a ina kika koyi girki ne?”

D’an hararanshi tayi irin ranta ya b’acen nan tace “Ban sani ba nima.”

Hanyar fita ta nufa yayi saurin cewa “Ina zaki je?”

Juyowa tayi tace “To miye na ka a ciki? Ba ka hanani ganin iyayena ba.”

Ficewa tayi a d’akin ya bita da kallo yana cin abincin shi, murmushi kawai yake saki a zuciyarshi yana fad’in “Da alama sai na koma makaranta dan na k’ara fahimtar yanda ake zama da yara irinki.”

A gaggauce ya gama cin abincin ya mik’e ya fita ya samu Hafsat na jiranshi, basu b’ata lokaci ba suka fita a gidan, a hanya ita ma Hafsat ke fad’in “Sheikh na wa dan Allah me zai hana idan kayi niyya ka aje ni wajen Hajia, ina so zamuyi magana dasu akan auren Aisha ne.”

Wani kallo ya watso mata yace “Idan banyi niyya ba fa?”

Murmushi tayi tace “Dan Allah kayi niyya to.”

Dariya yayi ya dangware mata kai yace “Ja’ira.”

Murmushi ta sake yi tace “Sheikh na wa.”

Shi ma murmushin yayi yace “Hafsat ta wa.”

Da haka suka isa asibitin suka shiga ciki, saida aka fara killacesu aka basu kayan kariya suka saka har da takalmi da hula duka suka rufe jikinsu kafin aka shiga dasu d’akunan da yaran suke, ba’a barsu sun shiga ciki ba daga k’ofa kawai ta madubin k’ofar suka iya hangen yarinyar dake nad’e a cikin farin bandeji da oxygène a hancinta a cikin kwalba. Wata ajiyar zuciya Hafsat ta sauke mai k’arfi tare da lumshe ido, hakan yasa hawaye sauko mata a kumatu cike da tausayin yar ta ta, jawota sheikh yayi ya rumguma a jikinshi yana fad’in “Kiyi hak’uri kinji, yar ki zata warke har ma ki ganta tana gudu a gabanki.”

Cikin shsheka tace “Allah ya yarda sheikh.”

“Ameen.” Ya fad’a yana kallon yarinyar shi ma yana jin wani imani da tsoron Allah na k’ara shigarshi, wannan kad’ai idan ka gani zai k’ara maka tsoron Allah a zuciya.

Suna barin asibitin gidansu Hajia ya sauketa ya wuce sabgar gabanshi, saidai Ryam na zuciyarshi da tunanin rabuwarsu ta safiyar yau, hakan yasa shi saka dreban Hajia Kabiru ya je gidansu ya d’auko su Yaseen ya kaisu gidan, yasan hakan ne kawai zai faranta mata rai.

Tana falonta ta dinga jin muryar Yaseen da Amir suna ta sallama, ai da gudu ta taso ta bud’e k’ofar ta fito, tana ganinsu da farin ciki ta k’araso tana fad’in “Yaseen, Amir, Ku ne dama?”

Rumgume Amir tayi ta zauna k’asa tana kallonsu suna ta washe mata baki suna k’ara daga kai suna kallon gidan, gaisawa sukayi sosai kafin su fad’a mata wanda ya kawosu da wanda yasa a kawosu, murmushi kawai tayi tace “Abdul kenan, ni ce ba zai bari na fita ba.”

Da mamaki Yaseen ya kalleta yace “Abdul fa kika ce? Mimi sheikh d’in?”

D’an kyaci tayi alamar kai share dallah tare da mik’ewa tace “Me kuke so na dafa muku?”

Da sauri Amir yace “Miyar nama da shinkafa.”

Tintsirewa tayi da dariya ta dunguri kan shi tace “Amir kwadayi ko?”

Dariya suma sukayi suna kallo ta wuce madafar, aiki ta shiga gadan gadan na gaba daya gidan, cikin nutsuwa da hankali ta kammala girkinta mai rai da lafiya, saida ta kwashe kamar yanda take yi kwana biyun nan sannan ta zubawa su Yaseen ta kawo musu, tare da ita suka ci a kwano daya a lokacin 12:00 tayi, mik’ewa tayi ta gyara falon sannan tace su wuce falonta, su Aisha na dawowa daga makaranta basu samu Hafsat ba, saida sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abinci, ban da Munzeer babu wanda ya je inda take, ita ma tana falonta tare da kannanta suna ta kwasar hirarsu.

04:07 Kabiru ya dawo d’aukarsu dan dama Mama ta ce su dawo dan su tafi islamiyya, tare suka fito tana rik’e da ledar kayan makulashen data siyo ranar zata basu, suna fita farfajiyar su Aisha na tsaye jiran drebansu su ma zasu tafi islamiyya, da wani kallon raini ta shiga bin su Yaseen Wanda tsaf a idon Mimi hakan kuma ya mata ciwo. Da mutumtawa su Heezam da Aswan suka gaisa dasu Yaseen har Aswan na d’an tsokanar Yaseen ma dan suna had’uwa da shi a babban masallacin Kaddafi wajen karatun sheikh.

Wucewa sukayi ta bude musu k’ofar motar zasu shiga, taimakawa Yaseen tayi ya shiga ya zauna dan tsayinshi bai kai ma, zata d’auki Amir ta saka kawai Aisha tayi yar dariya tare da fad’in “Sunan wata waina wai ita ‘yar k’unbu.”

Sake fashewa tayi da dariya, da k’arfin bala’i Mimi tayi kan ta bata ankara ba ta kasheta da mari tare da shak’ar wuyan hijabinta ta had’ata da bango. A kid’ime kuma a tsorace duk suka kalleta suna zaro ido, kallonsu suka tsaya yi cirko cirko kowa cikinshi ya d’uri ruwa, cikin b’acin rai da fitar hayyaci tace “…

*Alhamdulillah*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *