MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 2
Na Samira Harouna
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*5*
Tana shiga kusa da mamanta ta zauna tana fad’in “Mama lafiya? Ya naga baki d’ora girki ba har yanzu?”
Kallonta tayi tana sauke ajiyar zuciya, juyawa tayi ta kalli su Yaseen dake duba littafinsu suna karatu, girgiza mata kai tayi tace “Ba komai Mimi, zan d’ora yanzu.”
Da alamar tuhuma ta kalleta tace “Mama, ko dai babu abinda za’a dafa ne?”
Da sauri ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kan ta, cikin k’aguwa Mimi tace “Mama ki min magana mana, idan baki fad’a min damuwarki ba wa zaki fad’a ma?”
Kallonta ta sake yi a hankali tace “Hakane, Mimi ba tunani na abin da zamu ci yanzu bane, tunanin yanda zamuyi da dare nake, har malam ya bar gidan nan babu tabbacin zai samo mana wani abu, saidai abu na ubangiji kawai.”
K’ura mata ido tayi tana kallo, dafa kafad’arta tayi tace “Amma mama shi ne ba zaki fad’a min ba, har yanzu ina da canji a hannu na na kud’in da Mas’ud ya bani a ranar dana siyi kayan makaranta, bari na d’auko.”
Da kallo ta bita har ta shige d’akin, jim kad’an ta fito ta tsuguna gabanta ta nuna mata jaka guda tace “Kin gani mama, yanzu me za’a siyo sai naje da kaina.”
Girgiza mata kai tayi tace “A’a Mimi ba sai kinje da kan ki ba, kawo sai na ba Yaseen ya je.”
Ita ma girgiza kai tayi tace “A’a mama zan je, kinsan aikensu yanzu ba zasu dawo da wuri ba.”
Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, dan haka tace “Mimi ko garin tuwo babu shi bare shinkafa, ki siyo mana wani abun da zamu iya sarrafawa da wuri kafin lokacin tafiyarku islamiyya.”
Jinjina kai tayi ta mik’e tace “To mama, bari na siyo mana ko ledar macca guda biyu.”
Bata jira me zata fad’a ba ta koma d’akin ta d’auko hijab ta saka ta fita, gungun yan matan unguwarsu ta wuce suna zaune a kan dakali suna hira, babu wacce ta kalla a ciki bare ta musu ko da sannu, hakan yasa suka kafa dandalin yi da ita dan dama haushinta dayawa ke ji. Tana zuwa ta siyo abinda tasan zasu buk’ata ta juyo ta dawo, tana kawowa daidai su suka bushe da dariya har da tapa hannu zabayar ciki na fad’in “Sarauniyar kuri, ji da kai da nuna isa, ka ganta a hanya tsabal tsabal gidansu kamar rudun tamtabaru.”
Cak ta tsaya tare da juyowa ta kallesu, gyara tsayuwa tayi ta tofar da yawu ta bisu da harara tace “Idan mutum ya na da k’arancin abun yi dama ya kan zama mai neman fitina, ni kuma a halin da nake ciki yanzu ban da lokacin masu abun yi ba bare marasa shi.”
Yatsina fuska tayi tare da takawa zata wuce, tsaki wata tayi tace “K’aryar banza da wofi, da bamu san asalin balbela bane da sai tace mana daga masar take.”
Wata ce tayi saurin cewa “Dan kawai Allah bai miki hallita irin ta iyayenki ba, shikenan kin d’auki girman kai da raina mutane kin d’ora a kan ki, sai ka ce wata ‘yar shugaban k’asa.”
Sama da k’asa ta juyo ta hararesu taja dogon tsaki ta wuce ta barsu, hakan kuma zafi ya musu sosai dan sun so ta kulasu yanda zasu k’addamar da abinda suka tsara mata, da dukan tsiya zasu mata su mata baja-baja sai fatar nan ta canza kala, dan su har yau sun rasa gano dalilin da yasa fatar jikinta da surarta suka zama kala daban, idan ka dubi Mimi da gidansu da iyayenta, dole ka tuna da ayar da Allah mad’aukakin sarki yace *ya na fitar da duhu a cikin rana, kuma yana fitar da rana a cikin duhu, sannan yana fitar da rayayye a jikin matacce, kuma yana fitar da matacce a jikin rayayye, sannan yana azurta wanda ya so ba tare da hisabi ba*.
*Sheikh*
Tagumi ya buga yana kallonta yanda take ta cika mishi plate d’in gabanshi wanda tasan ba zai iya cinye abincin ciki ba, saidai har k’asan ranshi dad’i yake ji yanda Hafsat bata wasa da abincin shi, tunda ya aureta shi dai yayi hannu riga da yunwa, saidai ko baya gari amma yana gari kam yafi k’arfin nan. Zaune tayi tare da matso kujerarta kusa da shi ta d’auki cokali ta d’ebo ta nufi bakinshi, murmushi ya sakar mata tare da yin bismillah ya karb’a, sake d’ebowa tayi saiya nuna mata had’in kokombre da tayi da hannu alammar shi yafi so, yar harara ta cilla mishi ta d’ebo tana fad’in “Allah dai yayi walk’iya na ga mutum, domin kuwa nima nayi bincike na gano sirrin kokombre nan.”
Yar dariya yayi ya kanne mata ido d’aya yace “Kuma ai kinji dad’i da mijinki ya zama mai son kula miki da kanshi ko?”
Cikin jin kunya ta sunkuyar da kan ta, d’ago hab’arta yayi yace “Bana so ki fara kallona a matsayin *tsoho*, shiyasa nake bin duk wata hanya data inganta dan na inganta miki lafiyata.”
Dariya tayi mai birgewa tace “Na ji dad’i, amma a baya na damu sosai da son sanin sirrin nan amma ka k’i fad’a min.”
Murmushi yayi yace “Ina rok’on Allah ya ma rayuwarki albarka, tunda na nuna miki ina son kokombre sosai da kabewa da kuma miyar albasa, baki tab’a gazawa ba wajen sarrafa min su, wasu lokuta abu daban kike dafawa dan ku ci, amma ni saikin d’ora min wanda na fi so.”
Murmushi tayi tace “To ai dan hidimarka nake zaune a gidan, idan ba zanyi ba miye anfani na?”
Da sauri ya rik’o hannunta yace “Kina da, *Hassy* ko babu wannan ni zan iya zama da ke, karki manta ke fa ‘yar uwata ce, mahaifinki da mahaifina ciki d’aya suka fito, kinga kuwa ko babu aure tsakaninmu zan iya rik’eki.”
Murmushi ta kuma yi tana sunkuyar da kan ta, karb’an cokalin yayi ya fara cin abincin yana bata ita ma yana fad’in “Ki shirya k’arshen wata zamu fita hutu insha’Allah.”
D’aga manyan idonta tayi ta kalleshi sai kuma tayi k’asa da idonta, ba sabon abu bane wannan kam a wurinsu, idan har kaga bai fita da ita k’arshen wata ba to baya gari ko kuma sabgogi sun mishi yawa, amma ya kan ware k’arshen wata ya d’auketa su keta hazo wani lokacina ita ke zab’ar inda zasu tafi, ba dan komai ba sai dan ita ma ta huta na kwana uku kawai ba tare da aikin gida ko kula da yara ba.
Jinjina kai tayi tace “Insha’Allah, Allah ya saka da alkairi, Allah ya k’ara bud’i.”
Da murmushi yace “Madalla da *mata ta gari*.”
Da sauri ta d’ago tace “Ga *miji na gari*.”
A tare suka lak’aci hancin juna suna had’a baki wajen fad’in “Bisa koyarwa *addinin islama*.”
Cin abincinsu suka ci gaba da yi har ya kammala ya shiga dan shiryawa dan ana daf da kiran sallah la’asar ne.
*Madarasatul darul tauhid*
_(04:35 na yamma)_
Duk girman unguwar nan cike yake da mutane sakamakon sabkar nan, bak’i ta ko ina sun halarta bisa gayyatarsu da akayi, har yan makaranta sun zo kowane da kalar nasu uniforme, kusan makarantarsu Mimi sun zo a makare, dan ko da suka zo tuni an fara gabatar da karatu, gashi kuma ajin da aka ware dan sauke bak’i ‘yan makarantar sai ta tsakiyar filin dole zasu bi su wuce.
Mai kula da bak’in na ganinsu mata da fararen hijabai da siket bleue maza kuma farar hula da farar riga ya tarbesu, da ‘yar bulalarshi a hannu ya shiga gaba yana bud’e musu hanya suna wucewa, ta tsakiyar filin suka bi suka wuce ta bayan babbar rufar alfarma dake d’auke da manyan bak’i. Sam Mimi bata kalli wajen ba dan daga nesa ta hango duk manya ne a wurin, daga kujerun da aka aza musu zuwa babban carpet d’in dake shinfid’e zaka gane haka.
*Kamar tsautsayi* idonshi suka sauka a kan ta, kuma wani hukunci na ubangiji bai kalli kowa ba sanda kallonshi ya juyo a lokacin da ‘yan makarantar ke wucewa, saida ta zo d’an nesa dashi wanda da a lokacin ta juyo zasu fuskanci juna ne ya kalleta da kyau, nutsatsiyar fuskarta ta kamala wacce babu d’igon kwalli a kai, tafiyarta ta wahainiya cikin sand’a da ladabi, hannunta jimk’e dana Asma’u suna takawa a hankali. Baisan lokacin daya furta ” *Tabarakallah, masha’Allah, tabarakallah ahsanul kalik’in*.”
Wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, a hankali ya d’ago hannunshi ya d’ora daidai zuciyarshi ya dafe sosai, wani k’ayataccen murmushi ya saki yana bud’e idonshi, a k’asan zuciyarshi ya furta “Hak’ik’a nan ya amsa da k’arfi, da fatan zaki zama *alkairi a gareni*.”
Mayar da hankalinshi yayi kan karatu amma ta wani b’angare tunanin yanda zai yi da sabo kuma bak’on lamarin yake, shin ya tuntub’i malamin makarantar a game da lamarinta? Ko kuma dai ‘yan barandarshi kawai zai sa su nemo mishi gidansu ya gabatar da kan shi? Ko kuma dai ya fara shiga jikin yarinyar har ya fahimci *wacece* ita? Miye halayenta? Ya d’abi’arta take? Daga wane gida ta fito? Shin zata so shi ta zauna da shi? To amma ko zai san wacece ita dole sai ya fara sanin inda take rayuwa, dan haka yanzu wannan ne yafi mahimmanci a gareshi sanin *gidansu*.
Sam bai samu halin da zai ci gaba da wulk’ita idonshi dan sake ganinta saboda tururuwar da jama’a sukayi a kan shi, kowa son yake su gaisa wasu daga nesa suna d’aukar hoto, da k’yar jami’anshi guda biyu da tallafawar ‘yan agaji suka taimaka har ya shiga mota suka bar wurin.
Tare da k’awayensu suka taho, amma sannu sannu duk suka rabu ya rage daga ita sai Asma’u kowace rik’e da ledar wainar da aka basu ta sadaka, suna karyo layin gidan taja wani birki ta tsaya tare da rik’e Asma’u suka koma baya, yanda ta zaro ido kamar an tsorata ta ne yasa Asma’u d’an juyawa sannan ta kalleta tace “Mimi lafiya? Me kika gani?”
Cikin rashin gaskiya tace “Ke baki ganshi bane? D’an wahala ne fa.”
Da mamaki Asma’u tace “D’an wahala? Waye haka kuma?”
Tsaki tayi tace “Ki gane mana, *Muttak’a* ne.”
Zaro ido tayi tace “Muttak’an ne d’an wahala?” Murmushi tayi tare da fad’in “Ya ci sunansa kam, dan kati ma na kud’i dayawa yake turo miki.”
Cikin rad’a tace “Asma’u ki bar wasa mana, bai san gidanmu ba fa, ya akayi ya zo nan?”
Da alamar tuhuma tace “Idan ba ke kika fad’a masa ba ya akayi ya zo?”
Hararanta tayi tace “Idan ni na fad’a masa kuma saina tambayeki?”
Dafe k’ugu tayi tana feso iska a bakinta tace “Matsala kenan.”
Tab’e baki Asma’u tayi tace “Ke kika jawota da kan ki, duk da kin bawa Mas’ud dama ya kawo kayanki shikenan.”
Wata harara ta cilla mata ta jin haushi tace “Ana maganar arziki zaki sako min ta tsiya, Mas’ud d’in dana gama rufe babinshi ne zaki wani tado min zancenshi.”
Da maamaki tace “Ban gane kin rufe babinshi ba? Me kika masa Mimi?”
Kallon idonta tayi tace “Abinda kike so mana, ba ke kika fad’a min idan nasan bana son mutum na fad’a masa gaskiya ba? To gaskiyar na fad’a masa.”
Girgiza kai tayi cike da jimami da rashin jin dad’i tace “Gaskiya Mimi baki kyauta ba, haba dan Allah.”
A k’ufule ta kalleta tace “Kinga ba wannan ba, fad’a min yanda zanyi na shiga gidanmu ba tare da mutumin can ya ganni ba?”
Tab’e baki tayi tace “To shi banga aibunsa ba, ki tsayar dashi mana tunda kin kori Mas’ud.”
A hassale tace “Ke Mas’ud d’in banza, idan kina son shi ki fad’a min saina had’aku, shi kuma waccen lek’a kiga yanda yake mana, sam baya da tsari da iya ado wani sakarai da shi, kud’i ne Allah ya bashi amma babu aji.”
Da mamaki Asma’u tayi murmushi tace “Wasu ko mahaukaci ne suna so indai yana da kud’i, amma ke ko kana da kud’in sai ka iya d’aukar wanka, sannan ka zama mai k’ananan shekaru, dan na gama fahimtar kina gaba da duk wanda yake d’auke da shekaru arba’in da sama.”
Dariya ce ta kubce mata ta kalli Asma’u tace “Ba haka bane, ba gaba nake da masu shekarun ba tunda ubana ba shekarunsa kenan, kawai dai nasan a wannan shekarun babu abinda zan samu na soyayya a gurin mamallakinsu, mafi aksarinsu kuma zaki ga suna fama da shirgegen tunbi da nonuwa, sannan in k’ara tuna miki *sa’an babana ne*, ni kuwa me zai sa na auri sa’an babana a shekaru? Ai da kunya ma.”
Girgiza kai Asma’u tayi tace “Mimi ina jin tsoron ranar da zata zo kiyi nadama a kan wannan fariya da kike.”
Farr tayi da ido tace “Ba fariya bace.”
Jujjuyawa tayi da sauri ta k’arasa kusan dakalin dake k’ofar wani gida, zaune tayi tare da yaye hijabinta ta baya ta dawo dashi a gaba, Asma’u data k’araso ne tace “Ba zaki shiga gida bane?”
Yatsina fuska tayi tace “Sai ya tafi.”
Da mamaki Asma’u tace “Mimi ko dai ba kya so yaga gidanku ne?”
Da sauri ta kalleta tace “Saboda me? Ke tunda muke dake kin tab’a ji ko ganin na nunawa wani gidan da ba namu ba?”
Kawar da kai tayi tace “Asma’u duk iskancina wallahi bana jin kunyar a ga gidan, hasalima alfahari nake a ga daga ina na fito, haka-zalika bana jin kunya nuna iyayena duk da zubin hallitarsu, ina son kayana a haka kuma duk wanda ya nemi raina min su wallahi zamu saka k’afar wando d’aya da mutum.”
Ajiyar zuciya Asma’u ta sauke tace “To in hakane ki shiga gida mana kar dare ya miki a nan.”
Tab’e baki tayi tace “Nasan waye Muttak’a, dan magriba ba zata sa ya bar k’ofar gidanmu ba, ni kuma haka kawai na tsani na ganshi kusa da ni.”
Ita ma tab’e baki tayi tace “To kinga ni tafiya zanyi, dan bana tsaya na biye miki ba har magriba ta mana a waje.”
K’ala ba tace mata ba sai binta da kallo tana d’an jujjuya ledar wainarta, wucewar su Yaseen yasa ta cewa “Kai ku zo nan.”
Da kallo ta bi gajerun k’fafunsu har suka k’araso, ledar hannunta ta mik’a musu tace “Ku kai wa mama ta ci ta baku sauran.”
Yaseen dake babba ne ya karb’a yace “Mimi ina kika samu waina dayawa haka? Mu fa hak’uri aka bamu aka ce bamu samu.”
Wani murmushin gefen labb’a tayi tare da girgiza kai, ita fa tana zaune aka biyota da wainar ma tare da Asma’u da ta ci albarkacin ta, wanda ya bata wainar abokin d’an ajinsu ne dake ikrarin wai yana son ta, kallo d’aya ta mishi ta d’auke kanta daga gareshi bata sake kulashi ba har yau, amma ko yanzu da zai ganta tsaye zata siyi pure water zaiyi tsal ne ya biya kud’i, ko da ba ita kad’ai bace yawansu ya kai dubunnai. D’an kallonsu tayi tace “Ku tafi gida.”
Juyawa sukayi sai kuma tace “Ku zo.” Dawowa sukayi suna kallonta, cikin gargad’i ta kama kunnenta tace “Akwai wani mutum a k’ofar gida, idan ya tambayeku ina nake ku ce an rik’emu a aji muna hadda, sannan idan kun shiga gida ku fad’awa Mama na tafi duba jikin Iya Delu.”
Saida ta sake zaro ido tace “Kun ji ko?” Da sauri suka jinjina mata kai alamar to tare da juyawa suka wuce.
*Alhamdulillah* munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d’umbin yawa a k’asarmu Niger da d’ayar K’asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak’a ce, Mage* da *Badak’ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d’umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK’IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)👌 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_’Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.🥰
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*6*
Saida ta ji kiraye kirayen sallah kad’ai ta mik’e ta sake lek’awa, ido ta zaro samakkon ganin ya fito daga motar shi yana alwala, girgiza kai tayi tace “Na shiga uku, wannan jaraba da me tayi kama? Na tabbata ya kirani baya samu ne shiyasa ya zo ya girke mana a k’ofar gida.”
Tana kallo ya kammala ya juya ya shiga kwanar da zata sadashi da masallaci, ai da sauri ta shiga takawa har ta k’arasa gida, tana shiga ko sallama ba tayi ba mamanta ta jefeta da harare tace “Daga ina kike?”
Tsuru ta mata da ido tare da yin tsuguno saboda ita tana tsaye ne, a hankali ta kalleta tace “Mama Yaseen bai fad’a miki bane?”
Cikin tsawa tace “Ke ba ruwana da shiririta, na tabbata k’arya kike dan daga yanda suka fad’a min ya tabbatar ke kika saka su fad’a.”
D’an sosa kan ta tayi tace “Mama ba inda naje fa, wani ne na gani a k’ofar gidan nan shiyasa ban shigo ba.”
Jinjina kai tayi tace “Ko da naji, Allah yasa ba wani abun kika masa ba.”
Girgiza kai tayi tana kallonta ta k’arasa saman tabarma ta saka hijab ta kabbara sallah, da sauri ta shiga d’aki ita ma bayan ta duk’a kafin ta shige, kayan ta canza a gaggauce ta fito tayi alwala ta kabbara sallah. Tana idawa bata tsaya yin azkhar d’inta ba ta mik’e da saurita saka takalmi zata fita dan ta samu ya bar k’ofar gidan nan, tana juyawa suka kwatse da mahaifinta yana binta da kallo.
Da sauri ta duk’a tana fad’in “Abba gaisuwa.”
Saida ya k’araso yana gyara carbinshi a hannu cikin fad’a yace “Mimi waye a waje yake nemanki? Wanene shi da ban san shi ba?”
Sunkuyar da kai ta sake yi tayi shiru, a zabure yayo kan ta yana sake fad’in “Ba dake nake magana ba? Mimi naga nema kike ki fi k’arfina ko? Kullum da kalar da zai zo nemanki gidanki.”
Daga tsugunnon ta ja baya tana fad’in “Abba kayi hak’uri, wallahi ba ni na fad’a masa gidanmu ba, bansan zai zo ba.”
A hassale yace “To ki je ki fad’a masa ya bar nan, kuma ya fita a sabgarki dan ni da mahaifin yaron nan mun tsayar da magana za’a saka muku rana.”
Da sauri ta d’aga kai ta kalleshi sai kuma ta sauke idonta k’asa, jinjina kai tayi alamar to tare da mik’ewa jiki a sanyaye ta fita, da wayarshi a hannu yana dannawa ko da ya ganta ya sauke ajiyar zuciya, shi sam ba wai gidansu ko ganin mahaifinta bane ya dameshi, hasalima ba wannan ne a ganshi ba, ita d’in dai ita yake so kuma ya ji ya gani zai iya. Murmushi ya sakar mata yana fad’in “Mimi dama zan iya ganinki? Ai har na cire rai da zan tafi.”
Fuskarta a had’e ba alamar wasa tace “Me ya kawoka nan? Wa y’a fad’a maka gidanmu?”
Murmushi ya sake yi ya rufe motar ya gyara tsayuwarshi yace “Tunda na turo miki kati jiya ina ta kiranki ba kya d’agawa, yau ma tun safe nake kiranki Mimi amma shiru, shiyasa na nemi gidanku aka fad’a min, dan dama na fad’a miki ni aurenki nake so nayi.”
Waina idonta tayi tare da sauke ajiyar zuciya tace “Kaga, dan Allah kayi gaggawar barin nan, kaga mahaifina bai sanka ba kuma sam bai ji dad’i ba, haka nima ban ji dad’in wannan ziyarar bazatan ba.”
Cikin rashin jin dad’i yace “Kiyi hak’uri kinji Mimi, wallahi na damu ne sosai shi ya sa, zan tafi amma ki d’auki wayarki zan kiraki.”
Cikin k’aguwa tace “Bana da waya yanzu, ta fad’i.”
Wani murmushi ya saki yace “Haba Mimi, yanzu dan wayarki ta fad’i har zaki yarda ki kwana babu waya a hannunki.”
Nuna mata wayarshi yayi yace “Wannan ta miki?”
Kallon wayar tayi a tafin hannunshi, saida taji wani murmushi zai sub’uce mata, a ranta ta ambaci “IPhone.” A zahiri kuma d’aure fuska tayi tace “Ta ya zan karb’i wayar hannunka? Bana so gaskiya.”
Murmushi yayi yace “Shikenan, yanzu fad’a min ina zamu had’u zuwa gobe da safe saina kawo miki wata.”
Kallonshi ta yi tana tunanin abun yi, ko ba komai ai zata iya siyarwa, idan kuma iPhone ya siya mata ta samu ta d’aukar kan ta selfie da vidéo, bugu da k’ari duk k’awayenta idan aka cire *Salma* bbu mai iPhone, ita ma dan zata auri mai kud’i ne. Nulfasawa tayi tace “Zuwa goben na kiraka na fad’a maka.”
Juyawa tayi tana fad’in “Sai anjima.” Shigewa tayi ya bita da kallo yana murmushi, a ranshi ya furta “Allah kai damo ga harawa.” Saida ya soka wayar aljihu kafin ya shige motar ya bar k’ofar gidan.
*Litini*
Kasancewar yau zai shiga ofishin gwamnati ne yasa shi fita kan lokaci saboda bin dokar aikin da yake yi dan al’umma, saida ya fara biyawa ya ga jikin Ashraf kafin ya wuce, cikin ikon Allah kam yana zuwa aiyuka ya samu tari guda a gabansa da kuma bak’in daya bawa lokacin da zasu zo ganinshi, haka ma akwai wanda suka zo da fatan samun lokacinshi ko da ba yau d’in ba. Kaf wayoyinshi kashesu yayi idan ka cire fax d’in dake ofishin da kuma k’aramar samsung d’in da duk wani daya shafi aikinsa zai iya kiranshi ko sak’o.
Sauri yake ya kammala ko ya samu damar barin ofishin da wuri, so yake ya yi yak’in da kan shi ta hanyar neman gidansu, amma abun ka ga babba sai ya zamana yana aiki ne kuma yana karb’ar bak’untar wasu manyan bak’in da sun fi k’arfin a sharesu, wasu kuma tausayinshi da karrama d’an adam ke saka shi tsayawa sauraren kokensu. Madadin sauka k’arfe 01:00 na hutu sai gashi har k’arfe 01:16 sannan ya tsaya cin abinci, yana tsaka da cin abincin sakataranshi ya shigo dan a lokacin waya ma ana yanke sadarwarta ne dan bashi damar hutawar yana fad’in “Yallab’ai, kayi bak’o.”
Lumshe ido yayi yana feso iska a bakinshi, bud’e ido yayi ya kalleshi yace “Waye?”
Cikin ladabi yace “Ya ce a fad’a maka Muttak’a ne, wanda kukayi magana a kan passepord d’in nan.”
Da sauri ya kalleshi yace “Oho! Shigo da shi dan Allah.”
D’aga kai yayi alamar to tare da juyawa ya fita, aje d’an take away d’in yayi ya d’auki tissue yana goge jajayen leb’unansa, jim kad’an ya shigo da sallama yana fara’a, da ladabi kamar zai sunkuya ya shiga gaishe shi yana amsawa shi ma da fara’a, cikin fara’a sheikh yace “Ina so ne nasan tsarin fitar da marar lafiya a station d’in ku?”
Da fara’a shi ma yace “Sheikh ai ba wani matsala bane, ana had’a visarshi ne tare da takardar shaidar rashin lafiyarsa da kuma asibitin da zai je gani, idan ciwon yayi k’amari da baya iya tafiya, ana iya tanadar masa wurin zama a vip, kamar yanzu ga mai buk’ata yana biyan kud’in vip ne, sannan zamu so sanin kalar rashin lafiyar, idan wacce bata da tsanani ne zata iya tafiya da yanayin jirginmu, awwanin da za’a d’auka a wajen tafiyar da kuma yanayin da marar lafiyar zai shiga idan jirgin ya tashi, idan akwai wata barazana dan mu sani da wuri mu kuma d’auki mataki.”
Ajiyar zuciya sheikh ya sauke yace “Nagode sosai, insha’Allah zan gabatar maka da duka abinda kuke buk’ata, ko ba ni ba zan iya aikawa.”
Da ladabi yace “Shikenan sheikh, ina jira.” Lumshe ido yayi ya bud’e yace “Masha’Allah, insha’Allah.”
Da haka ya mik’e ya fita ya bar shi, har zai d’auki abincin shi ya kalli agogonshi data nuna masa 01:32, da sauri ya danna madannin da zai kawo masa sakarantashi a take, wanda dama dan kiran gaggawa aka yi shi, yana shigowa ya bashi take away d’in yana fad’in “Akwai bak’i ne a waje?”
Da rusunawa yace “Eh yallab’ai, akwai wasu dattawa guda biyu da suka zo tun d’azu, sai kuma professeur *Yacoub Sumana* da ya zo yanzun.”
Saïda ya kalli gabanshi yace “Ka shigo da dattawan.”
Jinjina kai yayi tare da ficewa a ofishin, da irin haka fa aiki ya rik’e sheikh bai yi abinda yayi niyya ba, gashi kuma dolenshi ya halarci karatun *Umdatul ahkam* da yake gabatarwa duk ranar litinin da k’arfe 07:00 zuwa 08:00 na dare.
*Maryam*
Tun a hanyarsu ta dawowa ta rok’i Asma’u ta mata alfarmar da zata fita daga gida, da k’yar ta yarda tace za tayi amma ba zasu jima ba, suna zaune tare da mama a farfajiyar gidan tana gyara mata alaiyahu Asma’u ta shigo da sallama, har k’asa ta duk’a ta gaishe da mama dan haka ta ga k’awarta ma na yi, da sakin fuska ta amsa mata tana tambayarta mamanta? Da murmushi tace “Lafiya lau suke, sun ce na gaisheku.”
Da fara’a tace “Ina amsawa.” Jim tayi tana satar kallon Mimi da ta sunkuyar da kai kamar bata ganta ba, kallon mama tayi tace “Mama, dama anjima zan tafi gidan aunty *Rayya* ne na ce bari in fad’a miki ina so Mimi ta rakani.”
Kallonta tayi sai kuma ta kalli Mimi, d’an jinjina kai tayi ta kalli Asma’u tace “Ba zaku kai magriba ba dai ko?”
Girgiza kai tayi tace “A’a mama, nima haka mama ta ce kar na kai magriba.”
Jinjina kai ta sake yi tace “Shikenan Asma’u, na amince kuje Allah ya tsare, ko da mahaifinta ma ya dawo ya tambaya zan fad’a masa.”
Da fara’a tace “To mama mun gode.”
Kallon Mimi tayi tace “Mimi ki shirya da anyi la’asar sai mu tafi.”
Gyad’a kai tayi alamar to tare da fad’in “Na ji, nima dai da ina da aunty haka zan dinga jan ki muna tafiya.”
Dariya Asma’u tayi tace “Sai dai idan kinyi aure su Yaseen su je gidanki, ke kam sai hak’uri.”
Dariya Mama tayi tana girgiza kai har Asma’u ta fita a gidan, Mimi kam farin ciki kamar zata zuba ruwa k’asa ta sha dan murna, dan haka ta dinga aikinta da sauri amma ba yanda Mamar zata gane tana gaggawa ba. Suna kammalawa saida ta share gidan tas ta wanke ban d’aki kafin ta shiga wanka ganin la’asar ta gabato, kafin ta fito aka fara kiran sallah dan haka tayi alwala ta shiga d’aki, mai ta shafa da sauri ta d’auki wata watsetsiyar doguwar rigar leshe wacce aka yi ta sak da zubin bubu, gaban rigar zuwa wuya a tamfatse yake da duwatsu, hijabi ta saka ta shara yin sallah a nutse, tana idawa mama ma ta idar ta k’ara gyara zaman hijabinta tace “Mama zan tafi, sai mun dawo.”
Kallonta tayi tace “Ina d’an kwalin kayan kuma?”
Nuna mata k’aramar jakarta tayi tace “Gashi nan ciki, mama kinsan leshe yana da cin rai musamman lokacin zafi.”
Jinjina kai tayi tace “Sai kun dawo, karki manta kuma ku dawo kafin magriba.”
Saida ta d’auko wasu takalmi confence da suka dace da kayanta da jakar tace “To mama.” Fita tayi tana sake gyara zaman Jakarta a kafad’a. Gidansu Asma’u ta shiga ta gaishe da mamanta sosai kafin ta fito suka wuce, taxi suka shiga abun mamaki Asma’u sai taji Mimi tace a kai su *nouveau marcher*, ko da taji haka tasan gidansu Salma zasu je, dan haka kawai ta biye mata suna hira dan karsu fara fad’a yanzu yanzu.
A bayan kasuwar aka aje su suka k’arasa cikin gidan, kyakyawar budurwa na zaune tana cin kwad’on dambu, tana ganinsu ta mik’e da sauri ta zo ta rumgume Mimi tana fad’in “Bestyna, daga ina haka?”
Da farin ciki Mimi tace “Daga gida mana.” Raba jikinsu sukayi inda suka shiga gaishe da matan gidan, wanda cikin sauk’i zaka fahimci yanayin zaman, dan da alama uwar Salma ita ke buga mulki a gidan, watak’ila yanayinta ko yarenta ya jawo haka, dan kuwa daga ita har yaranta fatarsu jajir take kamar wasu larabawa, sannan gata ‘yar caras sab’anin guda biyun da suke da k’iba mai yawan gaske. Ciki suka shige inda ta musu masauki a d’akinta, suna shiga Mimi ta cire hijabin ta jefa kan gado ta cire jakarta ta zazzage kayan ciki, kallon Salma tayi tace “Besty taimaka min da kayan kwalliyarki, ni ban d’auko ba saboda mama zata gane.”
Dariya tayi ta juya ta d’auko mata jakar kayan tana fad’in “Muguwa, wani wuri zaki tafi shine baki fad’a min ba.”
Saida ta zauna da kyau ta kanta a madubi da alk’alamin zana ja-gira (crayon) ta shiga bin tsatsaren girarta da bata da yawa sosai kuma ba siririya ba tana zanawa, kallonta suka shiga yi inda Salma ke nuna mata sababin vidéo d’in data samu na wak’ok’i, jin wata wak’a dake birgeta sosai ta wani mawak’i da suke gari d’aya da shi wato Niamey mai sunan *Auta mg boy* tayi saurin cewa “Besty bar min wak’ar nan.”
Aje mata wayar tayi gabanta tace “Besty kinsan da jibi za’a kawo kayana kuwa?”
Da sauri ta kalleta tace “Dan Allah? Da gaske?”
Cike da tabbaci tace “Allah kuwa.”
Cikin farin ciki tace “Kai amma dole na yi waya kafin ranar, dan wallahi ni zan zama farko da zata fara had’a hotunan kayan lefenki.”
Dariya tayi tace “To ina wayarki?” Yatsina fuska tayi sanda take saka conciller tace “Dama ai na fad’a miki bana son Samsung d’in nan, ya rasa wayar da zai bani sai Samsung ? Samsung d’in ma duos.”
Tab’e baki tayi sai Salma da tace “To ai ke besty ba’a gane gabanki ne wallahi, kin ga fa har abokin ‘ya’yana yace yana sonki ki fad’a min na fad’a masa ya ma fita harkarki, wallahi dan baya son raini ne amma har yanzu yana son ki, ke nan fa saida ‘ya’yana ya fara min mad’e a kan ki yana nuna min son ki yake, ko da na fara tuntub’arki da lamarin kika kalli idona kika ce bai miki ba.”
Wata shak’iyar dariya tayi sai Asma’u dake saurarensu tun tuni tace “Tsakani da Allah? Yayanki fa?”
Kallon Asma’u tayi tana gyara yaloluwar rigarta data fito mata da ‘yan tsirarun nonuwanta tace “Wallahi haka ya faru, bansan wane irin namiji take so ba?”
Tab’e baki Asma’u tayi tace “Ai indai Mimi ce namiji zai tsallake jarabawar tantancewar fara kula ka ne idan ka haye wad’anan matakan, na farko ka zama dogo ne da ka iya d’aukar ado da tsafta, na biyu ka zama wayayye d’an zamani da zaka iya aje ta gaban mota ku zaga gari, idan ta kama har k’asar waje ka dinga fita da ita dan shak’atawa, na uku ya zama matakin karatunka mai zurfi ne yanda zaka iya cireta kunya a ko ina kuka shiga, na hud’u ka zama mai d’an abun hannu da zaka iya d’aukar d’awainiyarta, ko da baka kasance d’an babban gida ba ita wannan bai dameta ba, na biyar kuma shi ne ka tabbatar *shekarunka daga talatin* ne k’asa da haka, dan ita a tunaninta a wannan k’adamin ne yake ganiyar k’uruciyarsa, duk zai iya yin wad’ancen abubuwan dana lissafa ne idan wannan ne adadin shekarunshi, sama da haka tana ganin ya jima da tsufa a duniya, ita dama bata damu sai kyakyawa ba, indai kana da wancen to an wuce wajen a wurinta.”
Wani nauyayyen numfashi Salma ta sauke ta kalli Mimi da har tayi nisa a kwalliyarta tace “Lallai besty burinki babba ne, ko ni da zan auri mai kud’i ban saka ran ya dinga fita da ni ba.”
Jinjina kai tayi sai kuma tace “Indai hakane kenan duk sanda kika ganni tare da alhaji na dariya kike min?”
Mimi kam bushewa tayi da dariya dan gaskiya abin da ke faruwa ta fad’a mata, ganin haka yasa Salma hararenta tace “Allah indai hakane zan hanaki halartar bikina.”
Tsagaitawa tayi da dariyar tace “Haba besty wa ya fad’a miki? Ni na isa na wa mijin da zaki aura dariya.”
Hararanta tayi tana turo baki tace “Allah yasa gaskiya kika fad’a.”
Dariyarta kawai ta ci gaba da k’yalk’yalawa can kuma saita kalli Salma sanda take shafa man leb’e tace “To wai besty me yasa zaki aureshi? Dubeki ki dubeshi, wallahi wannan tsaf zai kasheki da tumbinshi a daren farkonku, kuma fa zai kai hamsin mutumin nan.”
Waro ido Salma tayi tace “Ke Mimi bansan wulak’anci, wallahi arba’in da hud’u yake, haka ya fad’a min da bakinshi sanda na yi shagalin murnar k’arin shekarata.”
Asma’u dake ta dariya ne tace “Wato Mimi ke dai idan kika k’i abu kina da hanyoyi dayawa na kusheshi.”
Salma ce tace “Gane min hanya dai yar uwa.”
Kallon Salma tayi tace “Baki yarda ba kenan?” Shiru tayi sai kuma ta kalli Asma’u tace “Yar uwa fa tayiwu dan baki san shi bane, gaskiya ta fad’a indai zan cire son zuciya, ina jin fa Allah ne yayi ni d’in matarshi, dan nima da fari babu yanda ban yi ba dan mu rabu, dan gaskiya idan na tsaya kusanshi yanda kika san gwiwa ce da kaza.”
Wata dariya suka kuma tintsirewa da ita har Asma’u, hakan yayi daidai da mik’ewar Mimi ta shiga kashe d’aurin d’an kwali kamar wacce ke koyar da kwalliya, kuma a haka duk ta koya ne ta hanyar kalle kalle a waya da saka kai, hakan yasa k’wandalarta bata shiga hannun mai kwalliya ko mai lalle, indai tayi niyya zata zauna tayi abun ta, kitso ma ta iya tsaf kan ta dai ne bata yi wa, kuma a haka bata d’aukeshi sana’a, a ganinta ajinta ya wuce nan gaskiya, tun mama na mata fad’an tayi har ta daina, mama kawai take ma sai Iya Delu sai kuma k’awayenta idan ta so. Sassauk’an d’auri tayi ta d’auki gyalenta ta rub’ashi biyu ta d’ora a kafad’a d’aya, turarenta ta d’auka ta fesa sosai kafin ta kalli Salma tace “Besty kira min lambar Muttak’a.”
Yatsina fuska Salma tayi tace “Shi ne dama zai zo kika d’au wannan wankan?”
Kallonta tayi tace “Zaki d’aukeni hoto ne, idan ya kawo min wayar na ga kalata saina rik’eta na d’ora hotunan a statu na gaishe da mutane.”
Girgiza kai Asma’u tayi ita dai ta zuba mata ido kawai, wayar Salma ta d’auka ta kira lambarshi da tasan ta saka sunan mace dan kar ta samu matsala da na ta alhajin ta kira, tana jin an d’aga ta mik’a mata wayar ta karb’a, saida tayi kamar ba za tayi magana ba kafin tace “Ina gidansu Salma, minti ashirin gareni na komawa gida, idan na tafi gaskiya ba zamu had’u nan kusa ba.”
Da farin ciki yace “Gimbiya Mimi an gama, gani nan zuwa cikin minti goma.”
D’inn? Ta yanke kiran tare da mik’awa Salma wayar tace “D’aukeni.”
Sauka tayi daga kan gadon da take ta shiga snapchat ta fara d’aukarta, duk da rigar dake gareta haka ta matsa mata suka d’auka tare, Asma’u ma da k’yar ta iya tsayawa suka d’auka guda uku da hijabinta a jiki, har hoto mai motsi saida ta mata abun kamar na hauka ko gajiya basa yi. Tsawon mintuna suka d’auka saida ya kira yace gashi ya zo ta kallesu tace “Ina zuwa ‘yan mata, ku tayani da addu’a Allah yasa IPhone zai bani.”
Dariya Salma tayi tace “Zai zaki iya fasa mishi da kai da duk wacce ya baki idan ba IPhone d’in bâ ce.”
Dariya sukayi ita kam ta juya ta fita a takonta d’aid’ai, da kallo Asma’u ta bita tana jin ina ma Mimi zata kimtsu ta rumgumi halin da suke ciki, tana tsoron wata rana ta jawo musu abinda zai fi k’arfinsu, idan wani ya maka kyauta dan Allah wani ba haka bane, idan wani ya yafe maka sanda ya maka wani neman hanyar fanshewa zai yi, wani kuma zai iya bin kowace irin hanya dan ya fanshe wahalarsa a kan ka. Gata dai yanzu sun fito daga gidan babu kwalliya a fuskarta, ta zo gidan k’awa ta cab’a ado na d’aukar hankali, sassauk’ar kwalliya tayi amma da za’a tambayeka *wacece ita* sanda ka ganta a kan titi, ko shakka babu zaka ce k’aramar autar shugaban k’asar ne baki d’aya, sabida yanda kayan suka karb’eta ta haska tayi matuk’ar kyau, ka rantse da Allah yar babba ce zata je wani babban taro na manyan mutanen da ke fad’a aji a k’asa baki d’aya, amma kuma a gidansu nan suna can ta barsu sun yi faten tsakin masara da alaiyahu, ta tabbatar sanda Mimi ta baro gida basu da abinda zasu ci na gode da safe kawai, amma ita ba wannan ne a gabanta ba rayuwarta take yi mai cike da burirrika da saka kai a uku.
Gaba d’aya gigicewa yayi ya shiga sakin baki yana kallonta, a matsayinsa na sojan jirgi sai yaji ina ma wata ‘yar hatsaniya ta faru a yanzu yanzun a layin nan, da zaiyi ram da ita ya saka a motarshi ya tafi da ita a zuwan cikin rububi ne na tashin hankali, kai shi a gaskiya zai iya rayuwa da Mimi ko babu aure, a yanda yake ji zai iya tarben tsinin wuk’ar da aka turo dan illata ta shi ya tarwatsa rayuwarshi, a kan baiwar Allahn nan zai iya yin komai. Hakan yasa bayan ya damk’a mata ledar mai kyau ya ciro kud’i yan jaka goma goma (Kwate😰 kin ga almubazzaranci) guda uku ya bata wai ya siye kwalliyar nan, bata yi k’asa a gwiwa ba kam ta sa hannu duka ta karb’a tana mishi godiya, yatsina fuska tayi saboda tsarguwa da kallon da yake mata na wuce k’a’ida tace “Ni zan koma ciki zamu tafi gida.”
Tangale hab’a yayi yace “Mimi bana so ki tafi, kamar nayi ta kallonki.”
Wulwul tayi da idonta tace “Saï anjima, kaga idan mu kayi magriba za’a mana fad’a, kuma dan had’uwa da kai kawai na zo nan.”
Jinjina kai yayi yace “Shikenan Mimi ta wa, sai anjima ba dan raina ya so ba.”
Juyawa tayi zata koma cike da jin haushin Mimi ta shi da yace, tsayar da ita yayi yace “Mimi sai yaushe zaki bani dama na fito ayi maganar aurenmu?”
Juyowa tayi ba wani d’ard’ar tace “Sanda na shirya.”
Marairaicewa yayi yace “Kamar yaushe kenan? Mimi ba kya so kiyi aure ne?”
Fuskarta a had’e tace “Ina so, amma ba yanzu ba.”
Lura zaiyi magana yasa ta saurin juyawa tana fad’in “Sai munyi waya.” Shigewa tayi ya bita da kallo har ta shige, d’an lashe leb’enshi yayi na k’asa daya bushe tare da shiga mota ya bar unguwar.
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d’umbin yawa a k’asarmu Niger da d’ayar K’asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak’a ce, Mage* da *Badak’ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d’umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK’IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)👌 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_’Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.🥰
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*7*
Tana shiga cikin sauri ta ciro kwalin wayar daga ledar, saida ta daka tsalle ta rumgume Asma’u tana murna ganin IPhone duk da k’aramar tashi ce, amma dai taji dad’i sosai da ganin wayar, Asma’u kam mamaki ne ya hanata magana sai kallonsu suna ta murna har da yin zaune tasa Salma turo mata abubuwa da dama har da hotunan data d’auka yanzu, suna idawa a gaggauce sukayi sallama da cewa sai sun zo ranar da za’a kawo kayanta, suna fita suka samu taxi ta nufi dasu unguwar yayar Asma’u.
Ko da suka je gidan basu wani jima sosai ba sai sak’on da Asma’u ta bawa yayar ta ta wanda uwar ta bata ta kawo sanda ta ji zasu taho, 05:50 suka baro gidan suka shiga takawa a k’afa dan isa bakin titi, dama idan aka kawoka ne kake samun mai kai ka har k’ofar gida, amma idan ba haka ba masu taxi basu cika kai kawo a layin ba.
Cikin fad’a Asma’u ta kalleta tace “Gaskiya Mimi kina ban haushi wasu lokutan, wai ke ba kya tsoron abin da zai je ya dawo ne?”
Yatsina fuska tayi tana d’an goge zufar data tsatsafo mata a hanci, kallonta tayi tace “Ba ma zaki kulani ba ko?”
Kallonta tayi ta sake yatsina mata baki tare da d’an mata gwalo ta sake d’auke kanta, jinjina kai tayi tace “Ba komai ki ci gaba, Allah na gani nayi iya k’ok’ari a kan ki Mimi, bana so k’awance na da ke ya zama irin k’awance da aka ambata ranar lahira mu had’u ni da ke muna zagin junanmu, ko kuma na rok’i da ki haska min gabana dan na tsallake sirad’i ko ke ki rok’i hakan, na fi so mu wuce a tare cikin aminci.”
Wata bak’ar Prado ce ta sha gabansu ta tsaya wanda dole su ma suka tsaya cak, da sauri Asma’u ta rik’e hannun Mimi tana fad’in “Shikenan, Allah ya taimaku yasa ba cikin samarinki bane wani zai sace mu.”
Kallonta Mimi tayi, saidai kafin tayi magana Ashraf ya zuro farar k’ararshi mai d’auke da takalmi k’afa ciki irin na matasan da suka san kansu wayayyu yan zamani k’irar polo, kafin suyi wani yunk’uri ya gama fitowa gaba d’ayanshi ya tura murfi da k’arfi ya rufe, a sanyaye ya shiga takowa gabansu yana cire bak’in glass d’in fuskarshi, gabanta ya tsaya cak yana mai k’arewa duk ilahirin jikinta kallo, faffad’an bakinshi mai d’auke da tsararun hak’ora ya bud’e ya nunota da yatsa kamar zai tsokale mata ido yace “Ke wacece da zaki wuce ta nan baki gaishe dani ba?”
Mimi da tun fitowarshi ta saki baki tana kallonshi, a take ta tambayi ” *Wanene wannan*? Yaushe ya zo garin nan?”
Dan kam ita daga tsarinshi zuwa fatarshi da gyaran kanshi ya bayyana mata ba mai jin yaren hausa, zabarmanci, barbarci, tubanci, fulatanci ko buzanci bane, tunda take bata tab’a jin namiji ya birgeta a kallonshi ba sai yau, hasalima samarinta kallo d’aya take musu bata sake sha’awar kallonsu. Amma wannan sai take jin zata iya zaunawa tayi ta kallonshi ba zata k’osa ba ita kam. Sanda ya shiga nuna ta da yatsan nan a karo na farko a rayuwarta da taji a ranta zata shanye wulak’anci ta kuma had’e, dan wannan ba guy da zata ma rashin kunya bane, yanayinshi ma ya nuna mata zai iya tsinka mata mari, babbar asarar da zatayi kuwa bata wuce su rabu ba tare da yace yana son ta ba, dan gaskiya ita duk ajin shi da yanda ya birgeta ba zata tab’a sauko da k’anta k’asa tace tana son shi ba, ina! Ba zata iya ba, gwara idan sun rabu tayi takaicin rasashi a gaba kuma zata samu wani kamarshi ko wanda ya fi shi.
K’yasta yatsunshi yayi daf da fuskarta hakan ya sakata lumshe idonta da suka fara kawo ruwa sabida jimawa tana kallon abu d’aya, daidaita nutsuwarta tayi ta saka idonta a na shi sosai, hakan ya bashi damar sakar mata murmushi yace “Wasa nake miki, kin tsorata ne?”
Tarrr ta masa tana kallo inda a hankali ta shiga canza yanayin fuskarta daga shagala da mamaki har ta d’aure fuskar, kallo ne ta shiga yi masa irin na zuru d’in nan cikin jin haushi. D’an kallon Asma’u yayi da ita tayi galala take kallonshi yace mata “K’awarki bata magana ne?”
Da sauri ta zabura tace “Tana yi mana.”
Kallon Mimi tayi ta sake jimk’e hannunta gam tana d’an motsa bakinta, a hankali ta sadda dubanta tayi k’asa da idonta tana sauke ajiyar zuciya, murmushi yayi mai sauti yace “Masha’Allah, dan Allah ya sunanki?”
Da sauri ta sake d’agowa ta kalleshi, dan Allah ya sunanki? Kamar wata ‘yar talla ko kayan miya? Sama da k’asa ta harareshi tare da kaucewa ta rab’ashi zata wuce, da sauri ya sake tare gabanta yace “Dan Allah ki saurareni, ko na biyo bayanku ne har na ga gidanku?”
Asma’u ce tayi saurin cewa “A’a dan Allah ka rufa mana asiri, zaka sa a mana fad’a a gida.”
Kallon Asma’u yayi yace “To in hakane ki sa k’awarki ta min magana mana.”
Cike da tausayin kan ta ta sake kallon Mimi, numfashi kawai ta sauke dan bata ga abinda zaisa tayi maganar ba idan ba niyya tayi ba, sake matsowa yayi kusanta yana fad’in “Dan Allahana ‘yan mata, ki taimaka ki fad’a min sunanki da unguwarku, nasan bai kamata na tsareku a kan hanya ba, amma babu yanda zan yi ne, ina ganinki naji zuciyata ta doka da k’arfi ta yanda ba zan juri ki sub’uce min ba.”
Kallon Asma’u tayi ta mata alama da ido mu tafi, zata taka k’afarta yace “Ki fad’a min abinda zanyi mana da zai sa ki min magana, dan Allah kada ki bari ki kubce min *Naana*.”
Kallon juna sukayi ido cikin ido, da sauri ta d’auke na ta saboda marayan kallon da yake mata, a marairaice yace “Ko sai na duk’a har k’asa ne?”
K’asa ta k’urawa ido ba tace komai ba, a hankali ya nemi zemewa ya durk’usa k’asa yana fad’in “Wannan ba kom…”
Ba ta barshi ya k’arasa ba tayi saurin kallonshi tare da fad’in “Maryam.”
Da mamaki Asma’u ta kalleta jin ta fad’i cikakken sunanta yau ga saurayi, a iya saninta saidai ta fad’a maka Mimi amma ba zaka ji Maryam a bakinta ba. Mik’ewa yayi yana sakin murmushi tare da fad’in “Alhamdulillah, *Mimi*, suna mai dad’i.”
D’an kumburo bakin da tayi yasa shi yin murmushi yace “Kina da aji, hakan kuma ya tabbatar min da na samu matar aure, fatana Rabbi ya dafa min kar ki k’i kulani a matsayin wanda zakiyi soyayya da shi ma bare aure.”
Hannu yasa aljihu ya jawo tartsetsiyar wayarshi ya mik’o mata yana fad’in “Zan iya samun agajinki ta hanyar rattab’a min lambobin da zasu sadani da inda kike?”
Wani wallll! Tayi da ido tare da k’ura mishi ido, kunnenshi d’aya ya kama alamar ban hak’uri, fari tayi da ido hakan ya k’ara narkar dashi tare da fad’in “Ko na sake zubewa k’asa ne?”
Har yayi haramar zubewa k’asa tayi saurin fizgo wayar ta shiga saka mishi lambarta, mik’a mishi wayar tayi a hannu suna kallonshi ya saka suna kafin ya kalleta ya sumbaci wayar, irin kallon firgitarwar nan ta bishi da shi, shi kam murmushi yayi yace “Yanzu musaya ta fara shiga tsakanina da ke, a sannu sannu wata rana zamu gauraya mu zama babban iyali da zai tsiro da kyakyawa kuma hazik’an yara.”
Kallon mamaki ta mishi shi kuma ko a jikinshi, saima rusunawa da yayi yace “Dan Allah zan iya saukeku inda zaku je?”
Asma’u ce ta girgiza kai tace “A’a gaskiya, an hanamu.”
Kallonta yayi sannan ya kalli Mimi, cikin taushin murya yace “Hakan ne a ranki kema? Ba zaki shiga ba?”
A hankali ta lumshe idonta wanda suka sha mascara suka yi tsayi sosai alamar eh, jinjina kai yayi yana jinjina al’amarin wannan mai kama da jinin sarautar, idan da za’a barshi da hasashenshi sai yace ‘yar k’usa ce a gwamnati sun samu matsalar abun hawa ne, dan duk da baya da sani akan suturar mata yasan kayan dake jikinta ba masu arha bane, ko da akwai mai arha to sai dai ko ‘yan kunnenta dake k’anana sosai mak’ale a kunnen. Saidai a wajenshi kam ko ta kasance ‘yar babba ko ta kasance ‘yar takala wannan bai dameshi ba, tunda ya karyo kwana idonshi suka sauka a kanta ya ji zuciyarshi ta fizga a guje ta rakito duk wani abu daya shafeta ta killace da jin cewa zata dage a kan ta ko ma wacece ita.
Saida ya kalli k’wayar idonta ya daidaita gilashinshi da kyau ya manna mata shi a fuskarta, hakan kuma ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba. Dariya yayi data fito da kyawunshi da kyau yace “Sai na kiraki, Mimi.”
Da kallo ta rakashi sai Asma’u da tace “Dama kasan inkiyarta ce Mimi?”
Juyowa yayi yana shafa tarin sumar kanshi yace “Ban sani ba, amma duk mai sunan Maryam ina kiranta da Mimi, saboda sunan *mahaifiyata* ne.”
A tare suka saki murmushi ita da Asma’u, haka kawai ta ji abinda ya fad’a ya sata nishad’i, da kallo suka bishi har ya shiga motar ya barsu nan tsaye. Kallonta Asma’u tayi sai taga har yanzu idonta na kan shi, da sauri cikin jin haushi ta cire gilashin daya saka mata tana fad’in “Malama ya tafi to sai ki kama bakin.”
Da sauri Mimi ta kalleta sai kuma taja tsaki tare da k’watar gilashin ta saki murmushi ta kalleta tace “Dan Allah mutumin nan bai birgeki ba?”
Girgiza kai tayi tace “Ko kad’an, tunda saurayinki ne.”
Cike da damuwa tace “Ke ba haka nake nufi ba, ina nufin tsarinshi, kalamanshi, kyawunshi da kuma yanda ya iya shiga zuciya lokaci d’aya.”
Galala Asma’u ta kalleta tace “To fa, da alama wannan kam shi ne *zakaran* da ya zubar da ‘yan maza warwas a wajen Mimi.”
Kallon gilashin hannunta tayi ta sake mayar dashi ga fuskarta ta kalli Asma’u ta d’aga mata gira tace “Ya kika gani dan Allah? Ya min kyau?”
D’aga mata gira tayi ita ma tace “Kinyi kyau kam sosai.”
Hannunta ta kama cike da jin dad’i suka fara tafiya tana fad’in “Asma’u a rayuwata ban tab’a tunanin zan had’u da irin wannan namijin ba?”
Da mamaki ta kalleta tace “Me yasa? Naga ai burinki kenan samun irin wannan namiji.”
Saida ta saki hannunta tace “Hakane, amma ni ban tab’a tunanin zan samu kyakyawa haka ba ai, to wai wanene shi?”
Ta fad’a tana kallon Asma’u, tab’e baki tayi ta d’aga kafad’a tace “Ina zan sani, sai ki bari idan ya kiraki ki tambayeshi.”
Wani murmushi ta saki tare da d’agawa wani d’an taxi hannu tana fad’in “Ba ni zan tambayeshi ba, shi ne zai fad’a min.”
K’ala Asma’u ba tace ba har suka k’arasa kusa da mai taxi, saida ta kalleta tace “Gida muka nufa yanzu ko kuma dai kina da sauran gurin zuwa ne?”
Murmushi ta mata tace “Gida zamu koma mana ke ma, magriba ta kusa ai.”
Girgiza kai tayi ta kalli mai taxin tace “Tallague.”
Jinjina kai yayi alamar su shiga, bud’ewa sukayi suka shiga inda ya jasu, wayar ta ciro a jakarta ta shiga saitata zuwa yanayin da take buk’ata, saida ta tabbatar komai ya mata kafin ta ciro wani k’yalle a jakarta a hankali ta shige goge kwalliyarta na fuskarta tana kallon madubi, saida ta goge duka kafin ta kwance d’aurin d’an kwalin ta saka a jaka ta ciro hijabinta ta saka, sak yanda ta fito daga gidan hakan yasa ta kallon Asma’u tace “Zasu gane wani abu?”
Girgiza kai tayi tare da juya mata baya tana kallon titi, tyab’e baki tayi tace “Asma’u kar kisa na fara tunanin ke ‘yar bak’in cikina ce.”
Ita ma juya gabanta tayi daga kallonta, a zaman kuramen nan suka isa gida, babu wacce tayi wa yar uwarta sallama kowace ta shiga gida dan suna da tabbacin zasu shirya zuwa gobe a makaranta.
*Sheikh*
Sauri yake sosai dan ya fita masallaci da sunyi sallah a d’ora karatu kasancewar masallacin na shi ne dake manne da gidan, haka kuma ga asibitinshi dake kallon gidanshi wacce yake d’aukar nauyin ma’aikatan ana duba mutane kyauta, kawai zaka ciri kati ne da d’an abun da baiyi tsamari ba, amma daga maganar rashin lafiyar da zata kwantar zuwa mata masu haihuwa da yara k’anana duk kyauta ake dubasu. Suna alwala amma ya cikashi da surutu, har suka fito daga ban d’akin dake cikin falon zasu fita yana fad’in “Ustaz kana ji na? Wallahi da gaske nake fad’a maka, dama na ce maka zanyi budurwa yau ba? To na yi yanzu aiki ya rage naka ka nemo min aurenta.”
Hafsat dake jinsu tana neman tashi tsaye ne ta kalleshi tace “Wai auren wasa ne aka fad’a maka da za kace kayi budurwar yanzu kuma a nema maka aurenta?”
Da sauri ya kalleta yace “Aunty Hassy bari maganar nan dan Allah kada kisa mijinki ya baud’e min, wallahi daga ganinta tana da hankali da nutsuwa, wai kin ganta kuwa? Ga mugun aji yarinyar na tabbata ba kowa take kulawa ba.”
Da sauri ya mayar da dubanshi ga sheikh zaiyi magana sai kuma ya yi shiru yana sunkuyar da kanshi saboda k’ura masa ido da yayi, a hankali cikin gyara ma hularsa zama da nad’in dake kanta na farin rawani yace “Kai yanzu har ka tabbatar da sahihancinta ne?”
A marairaice ya kalleshi yace “Allah kuwa sheikh, yarinyar daga ganinta sam alamunta da yanayinta ba suyi kama da na wacce zata iya cutar da kowa ba.”
Juyawa sheikh yayi cikin takon hanzari ya nufi hanyar fita, da sauri shi ma ya bishi yana fad’in “Ustaz, indai kana so na kana son Hajia to ka nema min auren yarinyar nan.”
Ba tare daya juyo ya kalleshi ba yace “Ta fad’a maka tana sonka ne? Ko kuma dole za’a mata?”
Da murmushi yace “A’a ba haka bane, dama amincewarka nake buk’ata kan zaka nema min auren na ta, idan na samu yarda daga gunka shikenan sai nayi yak’i dan k’wato zuciyarta.”
A daidai zasu shiga masallack suna cire takalminsu yace “Allah yasa alkairi, zan nema maka auren nata idan nayi bincike na gane yar manyan mutane ce, akasin haka kuma zaka hak’ura da ita *Asas*, ka yarda?”
Jinjina kai yayi alamar to shikenan, shigewa sukayi cikin masallacin ana ta kiran sallah, lokacin tayar da sallah nayi ya shiga gaba dan jan su ba tare da mai jiyawar ba, da kan shi yake d’aga sauti yanda zai jiyar da kowa musamman daya zama ga lasipika.
Suna kammala sallah aka shiga shirye shiryen karatu, cikin k’ank’anin lokaci aka had’a komai kamar yanda aka saba inda masu d’auka ma ana watsawa a kafafen sadarwa da gidajen tv da redio kowa ya shirya. A nutse sheikh ya fara bud’e katarun da muk’addima kafin su tashi a inda suka tsaya. K’arfe 08:10 suka kammala dan ma an amsa tambayoyi kenan, yana mik’ewa zai fita yan agaji da masu tsaronshi d’aya daga ciki suka shiga kakkareshi suna son mutane su gyara ya wuce, gashi k’ofar da zata fitar da shi ta baya kuma mai sadashi da cikin gida ne, gashi kuma yana son fita shi kad’ai ba tare da ‘yan koren nan ba. Sosai aka rufe hanyar fitar masu tsaro na ta k’ok’arin a bud’a hanya ya wuce, musamman matasa sune a sahun gaba kowa burinshi su gaisa wasu kuma takardar tambaya ce da su suna son sai sun bashi hannu da hannu.
Allah ne ya so shi ya rufe musu ido sanda ya kutsa ta cikinsu ya fice a masallacin ba tare da ma sanin jami’an ba, bai kuma tsaya komai ba yayi gaggawar fad’awa cikin gida, kai tsaye wajen motoci ya wuce inda ya d’auki wata jibgegiyar Honda crv ya danno hancinta waje sanda mai gadi ya bud’e mishi k’ofar yana bin shi da addu’a, har k’ofar gidan suka fito cigiya mmai gadi na fad’a musu sai hankalinsu ya kwanta tare da tunanin kuma ina ne sheikh zai tafi da baya buk’atarsu? A k’ofar gidan duk suka gyara tsayuwarsu da jiran ya dawo su tabbatar lafiya lau yake.
*Maryam*
Idar da sallarta kenan mahaifinsu ya shigo yana kiran sunanta, tasowa tayi daga kan tabarmar ta durk’usa kanta a k’asa tana fad’in “Abba gani.”
Cikin fad’a ya shiga fad’in “Mimi me mahaifin yaron nan yake fad’a ne? Me ya had’aki da shi da suka ce sun hak’ura da tura kayan? Wani abu kika masa na rashin kunya ko?”
Girgiza kai tayi murya k’asa k’asa tace “Abba babu abinda na masa.”
A tsawace yace “To me yasa suka ce sun fasa? Yace ke da kanki kika ce ba kya son shi.”
Shiru tayi kanta a sadde ba tace komai ba, a zabure ya matso kamar zai daketa yana fad’in “Ba dake nake ba kina ji na?”
Da sauri ta d’ago tace “Abba ni bana son shi ne.”
Baki sake ya shiga kallonta yace “Iyeeeeh! Ba kya son shi fa kika ce? Kuma kika kawo mana shi gidan nan har muka shiga maganarku.”
Turo baki tayi tana kunkuni, da sauri ya k’arasa duk’awa ya d’auki takalminshi yana fad’in “Kinga ‘yar butan uban nan…”
Da gudu ta shige d’aki tana fashewa da kukan shagwab’a, girgiza kai mamanta tayi tace “Allah ya kyauta.”
Shi kam tsaki yayi tare da k’arasawa wajen Yaseen dake kwance yace “Har yanzu jikin nashi da zafi?”
A sanyaye ta sake tab’a goshin Yaseen tace “Da zafi malam, ko zamu kaishi asibiti ne? Ina tsoron zazzab’i wallahi musamman ma na dare.”
A tausashe shi ma yace “Rabi’a ta ina zamu fara to? Abinda muka ci ma waccen ja’irar ce kika ce ta bayar da kud’in data samu a hannun yaron da muke tsammanin zai zama mijinta, yanzu kud’in taxi ma da zata kaimu asibitin kawai bana da shi.”
Jinjina kai tayi kanta a k’asa, laluba aljihunsa yayi ya mik’o mata wasu canji yace “Kinga karb’i wannan, ba wa Mimi ta karb’o masa ko paracétamol ne ya sha zafin ya rage, bari naje gidan Iya Delu na ga idan malam na nan ba zai rasa wani taimakon da zai mana ba.”
Hannu biyu tasa ta karb’a ta bishi da kallo har ya fita, a sanyaye ta k’wala kiran Mimi dake d’aki, tana fitowa da k’aton hibajinta fari na makaranta da tayi sallah da shi, kud’in ta mik’a mata tace “Inji mahaifinki ki siyo paracétamol a bawa Yaseen.”
Karb’a tayi tare da komawa d’akin ta d’auko sabuwar wayarta da har yanzu bata bari kowa ya gani ba, ficewa tayi a gidan ba tare da ta kula kowa ba.
***************
Tsaye tayi bakin titin tana jiran shawagin ababen hawan ya tsagaita ta samu ta tsallaka dan ta isa ga mai shagon dake siyar da maganin, ta jima a wurin kafin tayi nasarar tsallakawa ta siyo ta juyo. Watak’ila Allah ne ya k’addara had’uwarsu, shiyasa ma ya fito shi kad’ai har ya buk’aci ruwa dan mak’oshin shi a bushe yake, gefe ya paka motar ya tsallaka titin ya siyo swan water, zai tsallako ya dawo ne ita kuma ta k’etara ta siyo maganin. Tunda ya ganta ya gane wacece, tsaf ya shaida kamanninta da ita ya had’u da ita na farko, babban abun da ya masa dad’i bai wuce ganinta da yayi a suffar daya fara ganinta a wurin sabkar nan ba, dan tun daga k’asa ya kalli k’afafunta da ake gani da k’yar saboda girman hijabin, gashi da k’yar take kallon gefe da gefe ba irin idonta a tsaye yake a kan titin bâ, dan har rintse ido take ko ta kawar da kanta idan wani abun hawan ya hasketa sosao. Hakan yasa ya ji cewa lallai ‘yar babban gida ce (yar masu tarbiya).
Da kallo ya bita har ta wuce ta gefenshi ta siyo magani ta dawo bakin titi, yanzu haka tsakaninshi da ita bai fi tako biyar zuwa shida ba ya isar dashi gareta, amma tunanin rashin dacewar yi mata magana a kan titi, da kuma hangen ta yanda zata kalleshi yasa duk sai yaji gwiwarsa tayi sanyi. Amma dake zuciya da abinda take so kuma take muradi, sai yaji a ranshi ai kamar dama ce da zaka san asalin d’abi’ar dake lullub’e a cikin zumbulelen hijab d’in nan, hakan yasa shi takawa a nutse tare da d’an sakin jikinshi ya b’oye k’irarshi ta kakk’arfan dattijo har ya tsaya gefenta, shi ma kallon titin yayi cikin wata daddad’ar murya kuma sanyayya yace “Bayan nema miki amincin Allah, ko zaki iya kawo hannunki na k’etaraki?”
A hankali ta juyo tana yatsina fuska alamar za tayi halin na ta, amma ganin Sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif ya saka ta waro idonta tare da bud’e bakinta, murmushi ya sakar mata sanda suka had’a ido tare da cewa “Sannu.”
Rufe bakinta tayi gam tare da yin k’asa da idonta, a hankali har ta sauke kanta k’asa tana d’an jujjuya kanta cikin siririyar murya tace “Assalama alaika, ina wuni?”
Da mamaki ya kalleta, mamakin shin bata ganeshi bane? Yasan dai fuskarshi ta gama garin nan da kewayenshi baki d’aya, ko baku da telebijin zaka iya ganinshi a telebijin d’in wasu, idan ba a nan ba kuma ga waya data game ko ina, wa’zinzikanshi masu tsayi da gajeru suna cikin wayoyin mutane dayawa, idan ka tara mutum goma zaiyi wuya ka kasa samun karatunshi a wayar mutum biyar ko ma sama da haka. Kowa yana son ya ganshi, kowa ya ganshi haba-haba yake da son su gaisa har su tattauna ko na minti d’aya ne, dan hakan ya zama abun alfaharin wani ko abun nishad’i.
Amma ita ta kalleshi da fari kamar zatayi mamaki amma kuma sai ta wani d’auke kai tace wai wani sannu a k’arshe. D’an d’auke kanshi yayi daga kanta ya kalli titi yace “Muje, karki yarda na barki a nan, hakan zai jawo miki kwana a bakin titin nan, ki saka k’afarki a inda na d’auke tawa.”
Da sauri ta kalleshi da tunanin shi ne kuwa? To me zatayi? Tayi yanda yace ko kuma shi ma ta d’an gurza mishi ne kamar sauran? Wata zuciyar ce tace da ita “Malam ne fa! Kiyi yanda yace.”
Sake kallonshi tayi ta kalli titin a hankali ta d’aga kan ta tana jinjina shi tace “…
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d’umbin yawa a k’asarmu Niger da d’ayar K’asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak’a ce, Mage* da *Badak’ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d’umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK’IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)👌 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_’Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.🥰
*Alhamdulillah*👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*MATAR MUTUM*
_(K’abarinsa)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA*
_GA DUKA_
*’YAN AMANA TA*
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d’umbin yawa a k’asarmu Niger da d’ayar K’asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.
Ina masoyan *Sajida* da *Samira* littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak’a ce, Mage* da *Badak’ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d’umbin soyayya da kaunar da kuke musu inda suka zo maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK’IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.
Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)👌 zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.
_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479* Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._
_’Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_
Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.🥰
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_Bismillahir rahamanir rahim_
*8*
Sake kallonshi tayi ta kalli titi a hankali ta d’aga kan ta tana jinjina shi tace “To.”
Tana kallo sheikh ya fara kutsa titi a wani gadarance, motocin dake kai kawone suka shiga rage gudu wasu dan ganin mutum na wuce kuma ko kallonsu baya yi gabansa kawai yake kallo, kamar wutsiya haka ta ji tana biyarshi har suka k’etara, wani numfashi ta sauke tana kallon k’eyarshi, tana ganin zai juyo tayi saurin yin k’asa da kanta tace “Nagode, sai anjima.”
Zata gifta ta wuce yayi saurin cewa “Dakata.”
Cak ta tsaya amma kan ta a k’asa, dan fatanta d’aya ne su rabu ba tare da yace ga abinda tayi da bai kamata ba har ya shiga jawo mata ayoyi da hadisai, ita kam sauri take bare ta tsaya ta saurareshi. Hakan yasa ke iya k’ok’arinta wajen ganin ta sauke idonta k’asa karsu had’a ido, sosai take k’ok’arin yin sanyi har tana ta wasa da maganin a cikin hijab d’inta, ta nutsu sosai ta kuma bashi hankalinta matuk’a, ta yanda duk wanda ya ganta a lokacin zaiyi zaton ba ita bace, zaka d’auka tsuntsu ne a kan ta kuma aka saitata da bakin bindiga idan ya tashi a bakin ranta.
Ta b’angaren shi ma kallo yake sake k’are mata duk da dai yasan bai dace baa kan titi,saidai yana son sanin wata makama dazata isar dashi ga ahalinta, a lokacin da zai nemi aurenta garesu kuma shari’a ta bashi damar ya kalleta son ranshi dan ya tabbatar komai ya masa. A sanyaye cikin muryar nutsuwa yace “Ya sunanki?”
Saida ta gilgid’a kanta kamar k’adangaruwa tana sake kwantar da murya tace “Maryam.”
D’an murmushi ya saki ya furta “Masha’Allah, *Ryam*, ina ne gidanku?”
A hankali ta d’ago ta kalli fuskarshi, amma sai taji kamar fuskar babanta zata kalla daga tsaye, sai kawai ta sunkuyar da kai tana jin gabanta na wani dum dum dum. A d’an kallon nan ta fahimci wani irin kwarjini da haiba dake tattare a fuskar mutumin, ashe dai yayi arha ne sosai da har suke iya had’a kallon fuskarshi a majigin wayoyinsu ko kuma telebijin, wani babban abu data fahimta a game da dattijon shi ne ma’abocin iya kwalliya ne, ko a wa’azi ka ganshi tsaf tsaf cikin d’aukar ado, yau kam data ganshi a zahiri saita sake tabbatarwa, gashi dogo da kuma wata murdadd’ar sura a cikin manyan kayan nan, uwa uba k’amshin da yake zubawa na d’aukar ran bawa ya killace shi, wani irin k’amshi ne mai k’arfi da sanyi ga mai shak’arshi wanda hakan ya tabbatar mata turare ne irin na manya masu tsadar nan.
Saida ta had’e yawu sosai kafin tace “Nan kwana.”
Kallon hannunta yayi da tayi nuni dashi daga cikin hijabi ya kuma kalli kwanar, bai gane komai a kwatancen ba dan haka yace “Ya sunan mahaifinki?”
Da sauri ta d’ago kai sai kuma tayi k’asa da shi, cikin raunin murya da rawar murya kamar zatayi kuka tace “Dan Allah *Abdul* kayi hak’uri idan wani laifi nayi kar ka fad’awa Abbana, ka fad’a min ni zan gyara kuskure na wallahi, ba’a sani na bane nayi.”
Rigiji-gabji! Shi dai da kan shi shine yau aka kira a gabansa da Abdul? Hakan ma k’aramar yarinyar daya tabbatar ko ta girmi Eesha shekarun basu wuce d’aya zuwa biyu ba, tun yana shekara ashirin da biyar a duniya ya rasa duk mutanen da zasu iya kallon cikin idonshi, a wannan shekarun na shi akwai masu daka mishi tsawa har ma su kirashi da *Abdul Waheed*, hatta Hajia sarakuwarshi wacce yake kallo kamar uwa bai tab’a jin ta kirashi da sunan da ba sheikh ba, uwa uba kuma Hafsat ko Ashraf, kowa dai sheikh sheikh ko gafarta malam ko ustaz ko ranka shi dad’e, a ko ina kallon wanda zaiyi alfarma ake masa, girmama shi ake kamar za’a masa sujada. Shine yanzu aka kira da Abdul, lallai ko ba komai yarinyar ta ciri wata tuta da ba kowa ya cira ba, watak’ila a dalilinta zai iya gano wasu abubuwa da suka jima da shige masa duhu.
Saida ya gama tsareta da ido ya kuma d’aureta da su kafin yace “Kin sanni ne?”
A hankali ta jinjina kai tace “Waye bai san fuskar nan ba, ai sai dai makaho.”
A dak’ile yace “Kenan ke ma makauniya ce?”
Da sauri ta girgiza kai alamar a’a, numfashi ya sauke ya gyara tsayuwarsa yace “Ina son magana da iyayenki mai mahimmanci, zaki lamunce min na je.”
Da sauri ta kalleshi tace “Abbana baya nan.” Da sauri ta rintse ido tana danne harshenta daya sakata yin k’arya, sai kuma ta ji ai hakanne zai rabasu lafiya kar ya sake tunanin neman gidansu. Ba tare daya d’auke idonshi ba yace “Ina ya tafi?”
Murya k’asa k’asa tace “Ya je k’auye.”
Jinjina kai yayi yace “Kenan zaki iya bani lambarki dan na samu labari idan ya dawo.”
Tsuru tayi tana kallon k’afafunshi masu kyawun fasali, hummm! A zuciyarta take jin idan fa ta ciro IPhone d’inta ya gani misali zai bayar da ita wajen wa’azi, sai kawai ta girgiza kai tace “Bana da waya ni, dama data mamana nake kiran k’awaye na, shi ma ba kullum take bari na ba.”
Wani sanyayyan murmushi yayi saboda jin dad’in abinda ta fad’a, dan gaskiya kai tsaye ya fad’i hakane saboda yaga kalar ta ta k’awar (wayar), cikin farin ciki yace “Ki bani lambar mamar, kafin ki isa gida zanyi kira dan kiga lambar, idan kinje ki saka suna.”
Da mamaki ta d’an kalli gefen fuskarshi sai ta jinjina kai alamar to, murmushi ya saké yi yace “Idan Abba ya dawo saiki fad’a min idan na kiraki.”
Sake jinjina kai tayi alamar to, gyara tsayuwa yayi yace “Saida safe Ryam.”
A nutse tace “Saida safe.” Takawa tayi d’aya biyu uku taji yace “Wane suna zaki saka a lambar?”
Juyowa tayi taga ya hard’e hannayenshi a k’irji ya zuba mata ido, cike da kunya tace “Ku fad’i wanda kuke so to.”
Murmushi yayi da a lokacin ta kalli fuskarshi wanda ya birgeta sosai, saida ya lumshe ido yace “Ki saka *Abdul*.”
Da sauri ta bud’a baki irin zatayi mamakin nan sai kuma cak ta tsaya ta shkga tariyo kalamanta na d’azu, sunan Abdul na fitowa ta ji kunya ta kamata kawai ta juya da d’an sauri tana murmushi ta bar gurin. Shi ma murmushin ya shiga sakar mata har ya ga ta shiga kwanar hannun hagu, girgiza kai yayi ya bud’e motar ya shiga yana bud’e ruwan hannunshi, saida ya d’aga kai ya tsiyaya a mak’ogwaronshi yasha sosai kafin ya rufe ya aje, wani murmushi ya sake yi y’a shiga juyawa yana fad’in “Abdul, hmmm! K’uruciya kenan, ni ne Abdul ko Ryam?”
Kamar jiran gusawarta yake daga gaban sheikh sai kuwa ya kirata, da rawar jiki ta shiga lalubo wayar a k’ugunta da tunanin guy nan ne, amma ganin sunan d’an wahala saiya sakata jan wani dogon tsaki, saida wayar tayi daf da tsinkewa kafin ta d’auka tana sake yin k’asa da tafiyarta a sannu sannu, shiru dukansu sukayi saida ya tabbatar ba zatayi magana ba sannan yace “Mimi, kina ji na?”
A dak’ile ta amsa da “Um! Ina aji.”
Numfashi ya sauke mai sauti yace “Mimi me yasa kike son wulak’antani?”
Yatsina baki tayi ta harari wayar tace “Me yasa ka ce haka?”
Ba alamar fara’a yace “Saboda na ga take-takenki ne, Mimi ki fad’a min gaskiya idan kinsan ba kya so na, bana so duk abinda nake a kan ki ya zama wahalar banza ce.”
Cikin jin haushi da rashin bawa abun mahimmanci tace “Ba komai, ka daina tunanin haka.”
“Kin tabbata Mimi?” Ya tambaya kamar yana gabanta, ba tare da shakkun komai ba tace “Umm.”
Daga inda yake y’a jinjina kai yace “Mimi, ina da karamci ga wanda ya min karamci, ina da alkairi da kuma bâ wa abubuwa baya, saidai Mimi bana son yaudara da k’arya, na so ki fad’a min ba kya so na dana barki na nemi wata, amma tunda kika ce babu komai shikenan, saidai fa Mimi kiji da kyau, wallahi duk randa na fuskanci akwai cin amana a tafiyar nan ta mu wallahi zaki sha mamaki na, indai har kina so na Mimi ni mai iya jure duk wani wulak’anci ne saboda ke, amma ki wulak’anta ni akan wani? Wannan abu ne da ba zan d’auka ba ko kad’an, akan kuma haka zan iya komai wallahi.”
Tunda ya fara magana ban da gwalo da marmad’a masa ido babu abinda take yi tana turo baki da jan tsaki, saida ya kai k’arshe tace “Me zaka iya yi to? Ba zaka hak’ura ba kenan? Amma ai kasan ance *matar mutum* k’abarinsa ko?”
Cike da tabbaci yace “Haka aka ce, iya gaskiya na gad’a miki Mimi, wallahi saidai duk mu rasaki daga ni har masu son na ki.”
Da d’an k’arfi tace “Kamar ya duk ku rasani? Kasheni zakayi?”
Tab’e baki yayi yace “Kusan haka.” Wani murmushi kuma ya saki yace “Mimi ina da zuciya da bana so ki san kalarta, saida safe kawai ki kula min da kan ki.”
Datse kiran yayi ta bi wayar da kallo, sai kawai ta tab’e baki tace “Baka da wuta, baka da aljanna, ba a hannunka arzikina yake ba, dan haka baka da rayuwa ko mutuwa, banza jahili mummana kawai.”
Da haka ta k’arasa gida, da sallamarta mamanta ce ta fara kllonta tace “Sai yanzu daga siyan maganin?”
Saida ta sunkuya ta mik’a mata tace “Mama da k’yar fa na tsallaka titi, kinsan dare baiyi ba sosai?”
Shigewa tayi d’aki ta cire hijabi ta haye gadon k’arfen mai rumfa da knarfi hakan yasa ya shiga d’an yin k’asa da sama da ita tana lilawa, wayar ta ciro bayan ta rage haskenta duka ta shiga chat da k’awayenta, ta wani b’angare kuma tunanin sheikh take yi, sai kawai ta tab’e baki tace “Watak’ila ma ko taimako ne zaiyi wa Abbana.”
D’aga kafad’a tayi alamar ohon d’in nan, hakan yayi daidai da shigowar kira a wayarta na bak’uwar lamba, wani sharme ta saki ganin wata k’asaitacciyar lamba mai tsari da sauk’in hardacewa a kai, saida ta gyara kwancinta ta kashe murya sosai ta d’auka tayi shiru, daga wajenshi ne ya fara fad’in “Amincin Allah su tabbata a gareki *maah*.”
Wani sanyayyen murmushi ta saki tayi shiru kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta lusmhe idonta tana tsinkayo amon muryarta tana fad’in “Kai ma haka, *bak’o*.”
Murmushi yayi har tana jin sautinshi kafin yace “Ba sunana bak’o ba, sunana *Ashraf Sabi’u Aliyu Sharif*, amma dai dayawa daga cikin mutane sun fi kirana da *Asas*.”
Jim tayi tana sauke numfashi tana jin yanda muryarshi ke ratsata, a sanyaye ta sake maimaita “Asas?”
Da fara’a yace “Eh, amma fa ba sunan gaskiya bane, gaba d’aya sunana dana iyayena ne aka had’a akayi abrégé suka tayar da Asas, lokacin ina makaranta ne aka lak’aba min shi.”
D’an murmushi tayi tace “Asas.”
Murmushi yayi yace “Da alama sunan ya miki dad’i ko? To nawa zaki siya sai ki d’auka gaba d’aya na bar miki.”
Murmushi tayi tace “Ban siya ba, idan na siya ai bâ zan samu alfarmar kiranka da shi ba.”
Ajiyar zuciya ya sauke yace “Maah, ina *sonki*, ke ma kina so na? Zaki iya bani dama na zama abokin rayuwarki.”
Lumshe ido tayi ta sauke wani numfashi, haka kawai taji wata k’walla kamar yau aka fara fad’a mata kalmar nan, bud’a ido tayi ta sauke numfashi tace “Zanyi tunani a kai.”
Waro idonshi yayi yana sake kallon shukokin da iska ke d’an kad’asu, kai duk yanda aka yi yarinyar nan yar sarkin abzin ce, dan wannan shan k’amshin nata da ajin abun ba’a cewa komai. Wani numfashi ya sauke yace “Maah ki taimake ni, ina sonki da zuciya ta, ina son aure sosai a rayuwata, ki amince min na zo gidanku ta yanda ba zan sha wahala ba kafin dogaren gidanku su barni shiga.”
Da mamaki tace “Dogarai? Wane iri?”
Da d’an sauri yace “Oh! To ina nufin jami’an gidanku?”
Tashi tayi zaune ta gyara zamanta da kyau tana k’arewa d’akinsu kallo tace “Ni ba ‘yar kowa bace, k’yalek’yale ne kawai na zamani ya haskani, mahaifina talaka ne da a kullum saiya fita yake samo mana abinda zamu ci, mahaifiyata ba ‘yar kowa bace ita ma, duka iyaye na suna da wata baiwa da Allah ya hallicesu da ita, watak’ila kai ma idan ka gansu ka tuna cewa su suka haifeni zaka iya gano wannan baiwar, karatu na ba wani mai zurfi bane, a matakin bac kawai na tsaya, islamiyya ce har yanzu nake kai kuma ina ci gaba da nema har gobe, a tak’aice ni ce *Maryam Adam Shehu*.”
Wani basaraken murmushi ne ya kubce mishi ba dan komai ba saidan jin dad’in yanda ta fad’a masa gaskiyar wacece ita, kai lallai ta dabance wannan, saidai wace irin baiwa ce take magana a kai? Ajiyar zuciya kawai ya sauke yace “Maah, naji dad’i sosai yanda kika fad’a min wacece ke? Na yarda dake d’ari bisa d’ari, kuma ni dama nasan bakiyi kama da wacce zata iya cutar da kowa ba, Naana ki min alfarma d’aya dan Allah?”
A hankali tace “Wace irin alfarma?”
Cikin zumud’i yace “Ki min alfarma na zo gidanku, a gaban mahaifinki zan durk’usa na nemi ya taimaka ya bani aurenki, wallahi zan kula dake Mimi, zan tallafi rayuwarki data iyayenki da dama duka yan uwanki, dan Allah na rok’eki kinji.”
Shiru tayi tana sakin murmushi mai tsadar gaske, jin bata amsa ba yasa shi saurin cewa “Dan Allahhhh! Kada ki ce a’a mana mai sunan mamana, Hajiata tana da tausayi da kawaici, sannan ga ta da magana d’aya tak, dan Allah ki kasance mai irin halinta kema.”
Yanda yake mata magiyar yasa ta cewa “Shikenan na ji, a karon farko na ji kaine mutum na farko daya shiga zuciyata, na amince Asas.”
Da wata irin k’ara ya saki ihu a kunnenta yana fad’in “Yess! Yess! Ta amince, kai naji dad’i sosai, maah, insha’Allah gobe zan zo gidanku na ga Abbanki, idan ya amince ya bani ke saina turo mgabata na, amma fa maah ni maraya ne uwa kawai gareni, amma ina da wanda ya zame min kamar uba, sheikh.”
Murmushi tayi tace “Daga gobe zamu yanke kai maraya ne ko akasin haka, idan Abba na ya amince zaka zama kana da mahaifi kai ma.”
Murmushi yayi yace “Nagode da wannan karramawar Mimi, sai kin ji ni gobe.”
Jinjina kai tayi tace “Saida safe.”
Shi ma a nutse yace “Saida safe *beauté* (beauty).”
Lumshe ido tayi har taji ya datse kiran, wani farin ciki ne ya mamayeta ta shiga murna sai kawai ta kashe wayar gaba d’aya ta gyara kwancinta jin mamanta na fad’in “Amir shi ga ka ga wai Mimi tana ciki kuwa?”
Tan jin shi ya shigo ya fita yana fad’in “Mama bacci take.”
“Bacci?” Ta maimaita da mamaki.
Bata sake fitowa a d’akin ba har baccin na gaskiya ya d’auketa, saida mamansu ta mik’e ta shiga d’akin ta daddab’ata, tana bud’a ido tace mata “Nan kike kwana ne?”
Saukowa tayi daga kan gadon tana murza ido tace “Mama an gama shinfid’ar ne?”
Dak’uwa ta mata tana fad’in “Ni ce zan miki shinfidar?”
Hanyar fita ta nufa cikin sumalin bacci mamanta tace “Ke zo nan?”
Dawowa tayi ta zube durk’ushe dan a tsaye take ita, da hannu ta mata alama tace “Mik’e tsaye.”
Mik’ewa tayi amma duk da haka saida ta d’an rank’wafa sabida nauyi take ji sosai ta tsaya a kansu kamar zata ci tuwo a kawunansu, matsawa maman tayi ta jawo rigarta tare da zura hannunta a k’asan rigarta, a tsiyace taja baya tana fad’in “Mama?”
Wani kallo ta mata tace “Ba ki da gaskiya kenan?”
Girgiza kai tayi tace “A’a mama, ba abinda nayi fa.”
Da d’an gajeran hannunta tace “To zo nan.” Sunkuyawa tayi cikin dubara ta yaran zamani ta zage wayar dake k’ugunta tayi baya da ita ta b’oye, tana ji ta shiga zura hannunta a cikin rigarta saida ta kai kan mamanta, dama rigar t-shirt ce dan haka ta fizge bras d’inta da k’arfi tana fad’in “Wannan jarabar ba zaki dinga cirewa kina hutawa ba.”
Tsaki tayi tare da damk’ar nononta na dama da k’arfi, cije leb’e tayi ta rintse ido tace “Washhhhhh!”
Zage hannunta tayi tana mata kallon tuhuma tace “Me yasa nonuwanki keta cika suna batsewa Mimi?”
Girgiza kai tayi tana sunkuyewa tace “Ba komai Mama.”
Sama da k’asa ta kalleta tace “Kin tabbata?”
Jinjina kai tayi, k’ofa ta nuna mata alamar ta wuce, saida ta b’oye hannayenta a cikin riga kafin ta fice a d’akin, ganin har su Yaseen ba’a musu shinfid’a ba yasa ta jan tsaki tace “Yanzu nan duk sai nayi shinfid’ar nan?”
Cikin hushi ta shiga shinfid’a musu tabarmarsu da ta ta wacce suke kwana da mama, duk da wani lokacin ta kan farka a tsakiyar dare ta nemi maman ta rasa, amma kuma idan aka wayi asuba zata ganta a gefenta (😎 Yo mamana ina Abba yake? Caskalewa ake).
*Alhamdulillah*