MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 4 Na Samira Harouna

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 4

Na Samira Harouna


👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨


                   *NA*



_SAMIRA HAROUNA_



       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *’YAN AMANA TA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_



                    *13*



Saida ta shiga gidansu Asma’u kawai ta samu damar amsa wayar Asas, sun jima suna hira wacce duk rabinta hange-hangensu ne na yanda zamansu zai kasance da kuma bikinsu, mafi yawa kam shi ne yake fad’in tsarinshi da yanda yake so ayi, ita kuma da ta ga yana fad’in duk wani abu da ita ma take da burinshi ne sai take amsa mishi da hakan ma yayi, saida ta ji sallah isha’i ta tabbatar Abba yanzu zai shiga gida sukayi sallama ta dawo gida.




                   *Sheikh*



A hankali ya d’aga idonshi ya sauke a kan ta yana murmushi, da kallo ya bita yanda take takawa a cikin doguwar rigarta ta bacci da cikinta daya fito sosai, saida ta zo daf da shi ta sunkuya ta aje farantin hannunta tana fad’in “sheikh na wa, ga shayinka.”


Ba tare daya d’auke murmushin ba yace “Nagode, Allah ya miki albarka.”


Saida ta nufi wajen wadrob d’in kayanshi tace “Ameen, nima nagode.”


D’aukar kofin yayi ya shiga had’awa kan shi lipton d’in a tsanake, ita kuma gyara zaman kayanshi ta ci gaba da yi cike da fara’a da son wahaltawa mijin na ta, tana cikin gyaran ya kalleta yace “Ki had’a mana kayanmu mana, mun kusa tafiya ai.”


Juyowa tayi tace “Angama sheikh, yanzu kuwa.”


Murmushi ya mata ya ci gaba da kurb’an shayin, juyowa ta sake yi tace “Wannan karan ma ba zamu tafi da ko da *Saifil islam* ba?”


‘Yar harara ya cilla mata yace “Rashin samun isashen lokacinki fa yasa nake ware miki k’arshen watan nan, idan muka tafi dashi me zamuyi?”


Da murmushi a fuskarta tace “Me za muyi to dama? Na d’auka hutu zamu tafi.”


Wani malalacin murmushi yayi yace “Za muyi yak’i ne.”


Girgiza kai tayi ta juya tana dariya tace “In an girma a san an girma, ka fa tuna miji kake nemawa Eesha, kuma ka ce ko yanzu ka samu wanda ya dace zaka aurar da ita ne.”


D’an zaro ido yayi yace “To auren Eesha zai hana nawa auren farin ciki ne? Haihuwar Eesha ba zai hanani sake yi miki wani cikin ba idan kika sauke wannan, saidai ku haihu tare da ‘yarki.”


Zaro ido tayi tace “Lahhh! Har da surukin na mu sai yaga mun haihu?”


Jinjina kai yayi yace “Ai da gani na yasan banyi tsufan da zan kasa abinda zai iya yi ba shi ma.”


Girgiza kai tayi sosai tana dariya tace “Gafarta malam, gyaran kimtsi.”


Kallonta yayi ba fara’a a fuskarshi yace “Gafarta malam, ina ma laifin ki ce Abdul.”


Da sauri ta juyo tana fad’in “Wace ni? Ka rufa min asiri malam, ai fad’in wannan suna yafi k’arfin bakina.”


Murmushi yayi yace “A haka kuma babu wanda ya kai ki sani na.”


Murmushi jin kunya tayi tace “Wannan kuma ai daban ne ko sheikh na wa.”


Girgiza kai yayi yana sakin murmushi kawai saboda tuna wacce kai tsaye tace masa Abdul, Abdul! Har yanzu sunan na mishi amsakuwa a kunnenshi, duk da a cikin rud’u da kid’imewa da tsoro ne ta fad’a saboda tsoron mahaifinta, amma dai sunan data kira yayi tasiri sosai ta yanda har yanzu idan ya tuna ya kan saki murmushi shi kad’ai.



                  *Asas*



K’atuwar sanda ce a hannun Hajia ta d’aga tana fad’in “Ashraf zan buga maka sandar nan a kai idan baka shanye magasin nan ba kaban kofin.”


Yatsina fuska ya sake yi ya kalli Hajia dake tsaye gabanshi ta zaunar dashi ta tisashi a gaba, a hankali ya kalli kofin data jik’a maganin na gargajiya a ciki, kamar zaiyi kuka yace “Hajia wai dole sai na sha ne? Ki aje min har a jima mana.”


Girgiza kai tayi tace “Ko kad’an, ai dole ka shanye ka bani yanzu yanzun nan, kasan daga ina nasa aka amso min maganin nan?”


Sake had’e fuska yayi yace “Wallahi ni dai Allah yana gani na gaji da shan maganin nan.”


Buge mishi baki tayi tana fad’in “Uwa ka, mutumin banza kawai, god’e-god’e da kai amma baka san shan magani, kuma kafi kowa sanin larurarka, yanzu da ka sa aka nemo maka auren ‘yar mutane haka zaka sakata titseyeka kasha maganin?”


Turo baki yayi yace “Hajia ni Mimi ma nasan ba zata titseyeni da sanda ba ai, zata lallab’ani ne har na shanye saita bani sweet na sha.”


Yanda yayi maganar da kanne ido d’aya yasa ta dungure masa kai tace “Maza bani kofin na gaji da tsayuwar nan.”


Rufe ido yayi yasa yatsa biyu ya rufe hancinshi ya kifa kofin a baki, da k’yar ya shanye kamar zaiyi amai kafin ya mik’a mata kofin ya mik’e ya nufi fridge, zaune tayi tana aje sandar hannunta tace “Shan magani ya zama aiki, kamar ba namiji ba.”


Dariya yayi ya kurb’i ruwa ya fita waje yana kuskure bakinshi, dawowa yayi yana fad’in “Hajia magani fa ba dad’i ne dashi ba, ai ke k’ok’ari ne dake da har kike zuba guda biyar a bakinki lokaci d’aya.”


Girgiza kai tayi tana tab’e baki, kallonta yayi yace “Hajia zan fita, saina dawo.”


Kallonshi tayi ita ma tace “To ina aka nufa yanzu? Nasan dai ba’a zuwa zance da yamma haka.”


Dariya yayi yace “Zan je zance amma sai anjima, yanzu zan je gidansu ” Sadeeq ne ya kirani yace babu mota a hannunshi.”


Jinjina kai tayi tace “Yayi kyau, amma ni yaushe zaka kawo min surukuwar ta wa ne na ganta? Ko sai randa ta shigo gidan zamu ga juna.”


Dariya yayi yace “Hajia karki damu, da zaran na je yau zan mata magana, idan iyayenta sun amince saina kawo miki ita ta wuni.”


Jinjina kai ta sake yi tace “A’a ba sai ta wuni ba, ni da bana da wasu yara yan mata a gidan, kaga ai indai mai kunya ce ko numfashi ba zata sauke ba har sai tabar gidan nan, tsawon wuni d’aya kuwa ai akwai takura.”


Jinjina kai yayi yana shafa sumar kanshi yace “Shikenan Hajiata, yanda mukayi da ita zan fad’a mki.”


Jinjina kai tayi ta bi shi da kallo har ya fita, daga nan b’angarenshi ya wuce ya shirya ya fita ya bar gidan bayan yasha gargad’i a wurin Hajiar ce wa kar ya jima a waje ya dawo.



                *Mim-Sas*😜


Ana idar da sallah isha’i ta hana kai da kawon su Yaseen ta k’unshesu a d’aki suna karatu, ta k’alk’ale gidan tsaf ta kawar da komai yanda ya samar da fili kuma a tsaftace, kujeru ta aje guda biyu na roba kafin ta bankawa d’akinsu turaren tsintsiya, wanka ta shiga a k’alla minti ashirin ya d’auketa ka rantse canza fatarta take yi a ciki, haka ma a gurin shafa mai da tsantsara sassauk’ar kwalliyar data fito mata da tsarin ainihin kakkauran fuskarta, wata galleliyar rigar shadda ta saka wacce bata jima da d’inka ta ba da kud’in data yafata hannun wani Alhaji Bukar, tunda ta karb’i kud’in ta yi bloquén lambarshi ta rufe duk wata k’ofa da zasu had’u. Wani shara-sharan mayafi ta d’auka ta shafeshi da turarenta mukhalat, fitowa tayi farfajiya ta d’auki jug d’in data wanke sabuwa da sai azumi mama ke aiki da ita, zata shiga d’akin ta ji wani sassauk’an numfashin mota a k’ofar gidan, da sauri ta kalli k’ofar ta tabbatar a nan mota ta tsaya, shigowa tayi d’akin ta kalli Yaseen da suke binta da kallo tace “Fita waje ka gani idan shi ne sai ka masa iso ya shigo.”


Gyad’a kai yayi shi dai ya mik’e ya fita, mik’awa mama jug d’in tayi tare da d’auko d’an k’aramin bokitin data had’a jus a ciki a abarba ta saka k’ank’ara tace “Mama juye min shi a ciki.”


Karb’a tayi ita ma tana kallonta kawai ta shiga yin abinda tace, dan tunda rana take wannan kimtse kimtsen da shirin tarbanshi, abinci ma yau da kanta ta girka na musamman inda mama tayi ta mamakin inda ta iya sarrafa wannan abu data ga ta had’a, domin kuwa kud’i ta kashe sosai wanda ta amsa a hannun maman ita ma wanda Abba ya bata ne tayi abun buk’atar ta.


Mayafin ta d’auka ta rataya a kafad’a tana k’ara kallon kan ta a madubin, d’aurin d’an kwalin ya zauna mata a kai yayi kyau dan irin mai hawa-hawan nan ne ta yi sai kuma ta ja shi baya sosai ta yanda ya bayyanar da cikon dandazon gashinta bak’i, kallonta mama tayi tace “Ki d’ora mayafin da kyau mana, haka zaki je masa?”


Kallon mama tayi tace “Mama, ai haka shi ne daidai, kinga had’uwarmu ce ta biyu, waccen lokacin da hijab ya ganni, kuma kinga ai addini ya yarda ka fito yanda mai son aurenka zai kalleka ya tabbatar komai ya masa yanda yake buk’ata.”


Galala mama tayi da baki ta sake d’aga kan ta da kyau ta kalleta dan a tsaye take tana k’ara gyara fuskarta tace “Kenan idan ya shigo zaune zaiyi ke kuma a tsaye kina jujjuyawa yana k’are miki kallo?”


Murmushi tayi tace “A’a mama ba haka ba kuma.”


Girgiza kai tayi tana fad’in “Allah ka shirya mana zuri’a.” Da murmishi Mimi tace “Ameen mama.”


Daga farfajiyar suka ji murya a tausashe a nutse a hankalce ana sallama a sirrince, Yaseen dake gaba ne ya sake amsa mishi yana fad’in “Suna ciki, bari na musu magana.”


D’akin ya shigo da sallama shi ma yana fad’in “Mama gashi nan ya shigo.”


Zaro ido tayi tace “To ya zanyi? Ni zanje muyi zancen?”


Dariya Mimi tayi murya k’asa k’asa tace “Mama ki shirya da kyau dan zaki fito ku gaisa.”


Girgiza kai ta shiga yi alamar a’a, d’an turo baki tayi tace “To nan zan shigo dashi ya gaisheki.”


Takalminta ta saka kalar ruwan hoda da suka dace da shaddar da kuma gyalenta, a hankali cikin tako kamar d’awisu ta shigo takowa tana fitowa harta yaye labulen ta fito bayan ta d’an sunkuya gaba d’ayanta, tarr! Idonsu suka sark’e dana juna domin kuwa akwai hasken fitila a k’ofar d’akin, a tare suka saki murmushi kowa na sake kafe d’an uwanshi da kallo.


Shi kan shi saida ayar nan ta sake fad’o masa a rai da take magana akan buwayar Allah, mai fitar da matacce a jikin rayayye, ya kuma fitar da rayayye a jikin matacce, Allah mai yin yanda ya so, mai yin sakamako ba tare da hisabi ba. Yanda ta fito kamar wata yar sarkin Istanbul, ko waye kai ka had’u da ita a waje ba zaka ce ta tab’a shiga wani wai gidan k’asa ba, amma a ciki take rayuwarta, kuma bata kunyar a san da haka.


Ita kan ta irin kyawun da yayi sai take tabbatarwa kan ta lallai ta ciro *fure a cikin k’aya*, dan kuwa irinsu Asas bibiyarsu ake kamar a yi farautarsu, da k’ok’on bara yan mata ke neman irin su, yanzu data samu sai take ji kamar tayi hannun riga da kwanciyar hankali kenan, dan tasan dole tasha fama wajen tsare da kula da mutumcinshi, musamman a yanda ita ma ta kula mazan wasu, dan ita tana da ma tsari da idan ka nace mata ne zata kula ka. A nutse ta k’araso gabanshi ta tsaya kamar yanda shi ma yake tsaye cikin wata dakakkiyar shadda bak’a k’irin sai k’yalli take tana d’aukar ido kamar zaka matsata mai ya fito, ya had’u sosai yayi kyau a cikin shaddar da ke d’auke da d’inkin zamani.


Sunkuyar da kan ta tayi cikin jin kunya murya k’asa k’asa tace “Barka.”


Murmushi ya sakar mata yace “Barka madame Asas, gani na zo.”


D’an d’ago da idonta tayi ta kalleshi da fara’a tace “Barka da zuwa kurkukun mu.”


Lumshe ido yayi yan ci gaba da murmushi yace “Kurkukun dake d’auke da mace kamar Mimi ta a ko ina yake zan iya nemanshi na zauna a ciki.”


Murmushi tayi har yana bayyanar da hak’oranta tace “Ka zauna to.”


Cikin kafeta da ido yace “A ina kenan?”


Nuna mishi kujerar tayi tace “A nan.” Murmushi yayi yace “Tabarma nake so, domin na zo nan ne da niyyar na ci abinda kika girka min da hannayenki.”


Rarraba ido tayi tace “Tabarma kuma?”


Jinjina kai yayi yace “E, tabarma.” Murmushi tayi tace “To me kake so ka ci?”


Rumgume hannaye yayi yana kallon fuskarta yace “Me kika dafa min na tarbena?”


A sanyaye tace “Tuwon masara, miyan kuka.”


Wani sanyayyen murmushi yayi shi ma yace “Masha’Allah, abunda na wuni ina buk’ata kenan yau, kawo min tabarma da tuwo na ci Maah, yunwa nake ji.”


Da mamaki ta kalleshi da son gano wai gaskiya yake fad’a kuwa, cike da tabbaci yace “Ki kawo min mana.”


Rarraba ido ta shiga yi dan yau ba tuwon suka dafa ba, sai kawai tayi murmushi tace “A gaskiya ba ma da tuwo, yau ba shi aka girka ba saboda zuwanka.”


Da mamaki ya nuna kan shi yace “Ni kuma? Me yasa?”


Sunkuyar da kai ta sake yi ba tace komai ba, girgizz kai yayi yace “Maah, ni fa ke nake so ba matsayinki ko abinda kuka mallaka ba, rayuwar da kuke yi ita ke bani sha’awa kuma ita nayi niyyar farawa tare da ke, dan haka duk wata wacce kika san gwana ce ita a harkar tuk’a tuwo to zai fi kyau ki nemi kusanci da ita, dan a kowane dare na rayuwarki gidana shi zaki tuk’a min nayi ta sulmar kayana.”


Kecewa tayi da wata siririyar dariya saboda maganarshi ta k’arshe, jinjina kai tayi tace “Ai ni ma na iya, na iya tuwon masara, tuwon hatsi, tuwon dawa dana shinkafa, sannan na iya na garin doya ma da kuma na semovita.”


Jinjina kai yayi yace “Yawwa *maah le* ta, haka nake son ji.”


Juyawa tayi tana fad’in “Bari na kira mama ku gaisa.” Shiga d’aki, tabarmar dake jingine a farkon shiga ta d’auko mama ta kalleta da alamar tambaya, ita ma da ido ta amsa mata da “Shi ya ce na d’auko.”


Saida ta juyo zata fito tace “Mama muje ku gaisa.”


Sunkuyar da kai tayi ba tace k’ala ba, cikin shagwab’a tace “Mama muje, ko na ce ya shigo ne?”


Da sauri ta kalleta da mamakin wai me yasa wasu lokuta bata gane cewa tana jin nauyinta a matsayinta na babbar ‘yarta ne? Girgiza kai tayi ta mik’e ta d’auki d’an gajeran hijabinta ta saka har k’asa, gaba take mama na baya hakan yasa sam bai kula da mutum a bayanta ba, saida ta duk’a dan shinfid’a tabarmar ya ga mama, har ga Allah tunaninshi bai bashi mahaifiyarta ma haka take ba, gashi fuskar maman ba wani tsufa ko dattijantaka, tarrr! Ya kalli fuskar mama da murmushi ya d’an d’ago hannunshi irin yana jiran ta k’araso d’in nan a cabke hannu tunda ga k’anwar matar da zaka aura. Mik’ewar da Mimi tayi ne ta juyo ta nuna mishi Mama tace “Ga mama ku gaisa.”


Luuuuuu! Yayi ya sauke hannunshi tare da durk’ushewa yayi tsugunno irin na maza kan shi k’asa, gaba d’aya sai ya rasa bakin magana daya tuna yanda ya dinga kallon fuskarta, har fa yayi shigo dafa kan ta ya bata hannu su gaisa yace mata ” *beby ya kike? Ya sunan k’anwar ta mu*?”


Lallai ashe da ya tabka kuskuren da har abada ba zai daina jin kunya ba, ganin ya kasa fad’an komai sai mama ce tace “Ina wuni?”


Da sauri cikin kunya yace “Ina wuninku?”


Da fara’a tace “Lafiya lau, an zo lafiya?”


“Lafiya lau, na sameku lafiya?” Ya fad’a kan shi a k’asa sosai, ita ma kan na ta a k’asa tace “Lafiya lau, ya mutan gida?”


Da fara’a yace “Lafiya lau, sun ce na gaisheku.”


Da fara’a ita ma tace “Muna amsawa, a gaishe su sosai.”


“Insha’Allahu zasu ji.” Juyawa tayi tana fad’in “Allah ya shi albarka, a gaida ‘yan gidan.”


Saida y’a ji shigewarta ya sake d’ago kai, eh lallai Mimi baiwar Allah ce daya jarabeta ya cirota daga tsatson bayin Allahn nan.


Alama ta mishi da hannu ya zauna, saida ya cire takalminshi a nutse ya zaune tare da jingina a bango, d’aki ta koma ta d’auko duk abinda ta tanada domin shi ta kawo ta aje mi shi, cire takalminta tayi ita ma ta zauna kan tabarmar ta fara tsiyaya masa jus d’in, mik’a masa tayi ya karb’a yana murmushi yace “Nagode gimbiyar mata.”


Murmushi tayi ita ma tana k’ara gyara zamanta irin na tsakiyar sallah (zaman tahiya), izinin shi ta nema ta zuba mishi abinci, jinjina kai yayi alamar eh, cikin nutsuwa ta fara zuba mishi farar macca da soyayyan nik’ak’en naman da aka nad’e cikin k’wai, sai soyayyen dankali da ta yi wa jus na mayonnaise da waken gwangwani.


Tura mishi tayi gabanshi ya gyara zamanshi yana fad’in “Da nasan wannan shagalin zan tarar ai da na taho da tsohuwar katifa ta.”


Dariya tayi tace “Ka me da ita?”


Cike da zolaya yace “Da na ci nayi kwance mana.”


Murmushi tayi ta girgiza kai tace “Gashi gidanmu baya d’aukar bak’on da baisan da zuwanshi ba.”


Dariya shi ma yayi yanaa fad’in “Da alama dai baki son bak’o saboda karki raba shinfid’arki da shi, amma karki damu a gidana gadona zan ara miki kina kwana a kai.”


Kunya ce ta rufe ta kawai ba tace komai ba, a nutse ya fara aika lomar abincin nan yana lumshe ido, da yatsa ya shiga nunata yana fad’in “Kar ki ce santi ne nake fa, dama ina so na tambayeki kalar kayan da zaki saka a ranar aurenmu?”


Waro ido tayi tana doka murmushi tace “To me kake kenan?”


Girgiza kai yayi yace “Na kare kaina tun kafin na yi magana fa.”


Murmushi kawai tayi tace “Ka zab’a mana kawai.”


Kallonta yayi yace “Kin yarda dani kenan?”


Lumshe ido tayi tace “D’ari bisa d’ari.”


Jinjina kai yayi yace “Insha’Allah gobe zan turo d’an sak’o ya kawo miki wanda na zab’a.”


Zaro ido tayi tace “Da wuri haka?”


Hararanta yayi yace “Ban gane da wuri ba? Wata d’aya ne fa, ni fa ranar kawai nake jira ta zo dan na gama komai, Maah kawai nake jira ta sameni gidana.”


Sunkuyar da kai tayi cike da kunya, da haka suka ci gaba da hirarsu cikin farin ciki har yayi shirin tafiya, duk mik’ewa sukayi inda ya ce ta kira masa k’annanshi sannan ta fad’awa mama ya wuce, yanda ya buk’ata haka tayi dukansu tare suka isa har k’ofar gidan, saida y’a fara sallama da ita ya nuna mata cikin gidan yace “Koma ciki, nagode da rakiya.”


Ba musu ba d’ard’ar tayi abinda ya ce, saida ta shigo kuma saita samu kan ta da tunanin wai ita ce yau namiji ba ubanta ba ya umarta haka, da yatsa fa ya mata wani fit fit koma ciki, murmushi kawai tayi tana fad’in “Allah kar ka kawo ranar da wani zai ramawa yan uwanshi maza abinda na musu, dan ba zan iya d’auka ba gaskiya.”


D’aki ta samu mama ta shiga cire kayanta, Mama kam kallonta take har ta cire rigar ta saka riga da wando na bacci, tana idawa su Yaseen suka shigo da sallama da murna, duk gaban mama suka zube suna nuna mata ledar hannunsu, da sauri Mimi ta zauna gabanta ita ma ta jawo ledar ta shiga duba kayan, kayan k’walam ne sai turaruka da kuma kud’in daya zuba a ledar, d’aukar kud’in tayi ta ware jaka bibbiyu har guda goma ta ninkesu tace “Wannan na Abba ne.”


Ragowar mama ta mik’awa tace “Mama ga na ki.”


Kallonta su Yaseen sukayi suka ce “Mû fa aka ba, shi ne komai ba zaki bamu ba.”


Harara ta dalla musu ta nuna Amir da yatsa tace “Daina kumburo min bakin nan kafin ka ji jini a ciki.”


Kud’in data d’ora kan cinyar mama ta koma ta d’auka ta zagi jaka bibbiyu ta mik’a musu tace “Ku yi abinda zakuyi.”


Farin ciki ne ya lullub’esu wanda ko dala biyar suka samu a hannu murna suke. Mama dai bata tanka musu ba sai al’ajabin lamarin Mimi, ta d’auka zata d’auki wani kaso a cikin kud’in ita ma, amma ba wannan ne gabanta ba mahaifinta ne yafi damunta, dama kuma ko bata cire mishi ba dole ita zata damk’a mishi, kawai ta bar ta tayi yanda take so ne, dan tsabar kawaici ko d’an abun tab’awa wata rana Allah ya hore Abba ya kawo indai Mimi na gidan ita ke rabawa.




*Alhamdulillah*

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *14*

Washe gari tsaf ta shirya ta kama hanya zata fita Abba dake cin d’umame ya kalleta yace “Mimi.”

“Na’am.” Ta fad’a tana juyowa, saida taje daf dashi ta tsuguna kafin yace “Yanzu ba zaki fara jaraba cin tuwo ba? Ki gwada mana ko dan halin rayuwa.”

D’an yatsina fuska tayi tace “Amma ba zan iya ci ba, idan na je makaranta na ci alala ko meat pae.”

Gyara zamanshi ya d’anyi yace “Mimi, zan amince ki je gaida mahaifiyar yaron nan, amma abisa wani sharad’i.”

Da sauri ta d’aga kai ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar, d’orawa yayi da “Zan amince ne saboda sanin d’an wane gida ne shi, a sanina da iyalen Aliyu Sharif ba mutanen banza bane, mutane ne manya masu dattako, matsalarsu d’aya shine auren *k’warya* ta bi *k’warya* da suke yi, gaba d’aya ahalinsu sun dunk’ule sun zama d’aya saboda suna auren zumunci ne a tsakaninsu,  idan har kika ga wani wanda ba daga cikin ahalinsu ba to tabbas akwai huld’a ta kasuwanci ko abinda yayi kama da haka, idan kika ga wanda ba ahalinsu ba kuma d’an talaka to rabo ne ya kai shi ahali, amma yana fuskantar tsangwama daga garesu da wariyar launin fata, a hakan ma dan akwai dattawan arzik’i da suke son dak’ile wanna’ d’abi’a ta iyalin, saidai duk abinda aka ce maka mata sun rik’eshi da hannu biyu sai an sha wuya ake cin nasara.”

Shiru tayi har saida yace “Abu na farko ina so ku min alk’awarin yin hak’uri da duk kalar tarban da kika samu daga danginshi, na biyu kuma kiyi hak’uri da duk irin wulak’anci ko cin zarafin da zai biyo baya, na uku shi ne ban yarda ba bayan gidan mahaifiyarshi da kuma yayarshi ki yarda ki k’ara binshi wani wurin ba, ko da hakan na nufin ki b’ata masa rai ne, sharad’i na gaba kuma shi ne dole sai in kin yarda zaku tafi da Asma’u ko d’aya daga cikin k’annanki dan su rakaki.”

D’aga kai tayi ta kalleshi a ladabce tace “Abba, hakan na nufin tarayyata da Asas zata iya jawo cin mutumci kenan?”

Girgiza kai yayi yace “Ban da tabbas Mimi, amma daga gidan da kika fito da tsatson da kika fito nasan dole wani abu makamancin haka zai iya biyowa baya.”

Girgiza kai tayi tana hawaye tace “Amma a dakatar tun yanzu, a dakatar kawai indai aurena da Asas zai sa a zagi hallitarku ko talaucinmu, bana son auren na fasa na hak’ura dashi.”

Duk da mamaki suka kalleta sai Abba daya zura hannunshi ya dafa kafad’arta yace “Uwata, me yasa zaki ce haka? Kiyi hak’uri kinji, komai zai wuce kamar ba’a yi ba ai, abinda nake so ki sani shine yaron nan bai k’yamace ki ba duk da sanin wacece ke, dan haka kiyi hak’uri da k’alubalen da zaki fuskanta daga danginshi.”

Ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana shashek’a tana jinjina kai alamar to, d’auke hannunshi yayi daga kafad’arta yana fad’in “To yanzu fad’a min wa kika zab’a dan ya rakaki?”

Cikin rawar murya tace “Zamu tafi da Asma’u.”

Jinjina kai yayi alamar gamsuwa yace “To ki fad’a mata saita nemi izinin iyayenta ita ma sai ku tafi.”

Tab’e baki Mama tayi ba tace komai ba, har zata mik’e yace “Gashi ke baki da waya, da gobe saï ki je ku gaishe da mahaifiyar yaron nan.”

Satar kallonshi tayi tana tunanin abinda ya fad’a, sai taji kunyarshi ta kama ta sosai duba da yanda take munafurtarsu haka, cikin ladabi tace “Abba dayake ina da lambarshi daya bani yace ko da ina buk’atar wani abu saina kirashi.”

Zaro ido yayi yace “Amma dai ai baki kirashi ba ko?”

Girgiza kai tayi alamar a’a, jinjina kai yayi yana sauke b’oyayyar ajiyar zuciya yace “Yayi kyau, kuma idan kina buk’atar wani abun ki tuntub’eni zan miki.”

Jinjina kai tayi alamar to, d’orawa yayi da “To ya za ayi ki fad’a masa?”

Jinjina kai ta sake yi tace “Zan kirashi ko da wayar Asma’u ne.”

Da sauri ya girgiza kai yace “A’a karki kira, ki bari idan kika taso lokacin na dawo nima da rana saina baki wayar ki kirashi.”

Jinjina kai tayi tace “To Abba, nagode.”

Murmushi ya mata yace “Allah ya miki albarka, tashi kije.”

Mik’ewa tayi ta fita a gidan tana share ‘Yar k’walla da hijabinta mama na binta da kallo har ta b’ace ma ganinta.

                   *12:06*

Kamar kullum tafe suke tare da Asma’u cikin nutsuwa suna hirarsu, saida suka kusa k’arasowa gidan suka hangi gungun su Maryam tare da k’awayenta, tab’e baki Mimi tayi irin ko a jikina d’in nan, Asma’u kuma data lura da yanayin fad’a ne suke yasa ta kallon Mimi tace “Mimi dan Allah da manzonsa ki wuce cikin gida karki kula gayyar tsiyar nan.”

A yatsine ta kalleta tace “Ke! Bana da lokacin wanda suka fi su aji ma bare kuma su karan kad’a miya.”

Murmushi Asma’u tayi tace “Yawwa Mimi, rabu dasu kawai, kinsan fa amarya da tsautsayi”

Murmushi sukayi a tare, zasu wuce kawai suka zagayesu su shiga, wasu sun d’aure k’ugu wasu kuma da itace a hannu, Maryam fake shugabar ce ta tsaya gaban Mimi tace “D’aukar fansa na zo Mimi, dan wallahi dukan da kika min baki wa banza ba.”

Wani luuuu! Tayi da idonta tare da jefanta da wani kallo sannan ta yatsina bakinta tace “D’aukar fansa? Da wannan zugar?”

Tsaki tayi tare da d’auke kai daga gareta, hannunta Asma’u ta kama tana fad’in “Muje ke.”

Saké tare gabansu sukayi Maryam na fad’in “Babu inda zata je sai jikinta ya gaya mata, idan sauri kike ki tafi.”

Wani dattijo ne ya zo wucewa ya kalli yanayinsu yace “Kai! Me yake faruwa ne? Ba daga islamiyya kuke ba? Maza ku wuce gida kar kuyi mana fad’a a nan.”

Gyara tsayuwa Maryam tayi tace “Ba ruwanka Baba kai dai yi tafiyarka kawai.”

Asma’u ce tace “Wai ke Maryam me yasa baki da tarbiya ne? Yanzu wannan ba yayi sa’an babanki ba.”

Tsaki tayi tace “Ke rufe min bakinki, ba dake nake ba.”

Tab’e baki tayi ta sake kama hannun Mimi tace “Mu tafi Mimi, karki kulata dan Allah.”

Cire hijabinta tayi ta wani jijjiga da fad’in “Ke babu inda zata je fa sai na…”

Muryar Alhaji Saminu sukaji a bayansu da fitowarshi kenan yana fad’in “Mimi lafiya?”

Duk kallonshi sukayi sai Mimi data wurga masa harara, juya baki Maryam ta fara yi tana fad’in “To fa! Ga kwarton na ta nan ya fit…”

Bata rufe baki ba Mimi ta kasheta da mari a hassale tana cin kwalar rigarta da fad’in “Kwarton wa? Wa kike had’awa da shi?”

Kacamewa sukayi duk su biyar d’in suka taran ma Mimi, Asma’u ma na ganin haka shigar mata tayi dan haka da gudu Saminu da mai gadinshi suka taho, haka ma yayan Asma’u daya fito yanzu sai wata mata da zata wuce ita ma, da k’yar suka rabasu su Maryam na ta aika musu zagi, a nutse Saminu ya kalleta yace “Haba Mimi, wannan ai ba girmanki bane fad’a a titi, me yayi zafi haka?”

Cike da fitsara Maryam tace “Ka fad’i haka mana saboda karuwarka ce, kun d’auka bamu san me ye tsakaninku ba? Ai ko kallon da take zuwa yi bana Allah da Annabi bane.”

Da b’acin rai ya kalleta yace “Wai wace yarinya ce wannan fitsararriya marar kunya?”

Juya baki ta shiga yi kamar zata cira shi, yayan Asma’u ne yace “Jikanyar Kaka ce mana, tarbiyar da aka bata kenan zank’amar banza.”

Shi ma harara ta wurga masa tana sake d’auke kan ta da gunaguni, Mimi dake hararenta ne ta nunata tace “Wallahi Maryam kika koma shiga harkata saina b’allaki, saidai kakarki tayi jinyarki.”

A fusace tayi cikin gida tana sab’a kakarta a kafad’a, hakan yasa Maryam binta da shewa har da bubbuga bakinta tana fad’in “Yeeeeeehu! Ku duneta karuwa kawai, karuwar gida daga nan zaune, ita ke ciyar da iyayenta da kud’in iskanci, yeeeehu anji kunya dai, har wani felek’e ake mana wai ita zatayi aurean kawo kud’inta, shi ma baisan ragowar samarin unguwar nan zai kwasa ba.”

A harzuk’e ta sake juyowa ta dawo kan ta da Sauri Asma’u ta rik’eta saboda ganin Abban mimi ya karyo kwanar layin, cikin jin haushi yayan Asma’u yace “Wai ke wace irin dabba ce? Wannan shi ne matsalar rainon Kaka kenan, mtssss?”

Abba na zuwa ya shiga bin mutanen wurin da kallon tuhuma musamman ma Mimi, da k’yar yace “Me yake faruwa ne?”

Asma’u ce tace “Abba wallahi su Maryam ne kawai suka mana taran dangi ni da Mimi.”

Kallon Mimi yayi data sunkuya kan ta a k’asa yace “Shiga cikin gida.”

Wucewa tayi tana kumbura hakan yasa shi kallon Maryam d’in dake fad’in “Dole ki shige mana anji tsoro, wallahi da sai mun miki terere a unguwar nan, kuma naje an fad’a karuwa karuwa karuwar gida.”

Rintse ido Abba yayi yana furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.” Sake bud’ewa yayi ya kalleta, Asma’u ce cikin jin haushi tace “Saidai in kece karuwar amma ba Mimi ba, banza jahila sai tsayin kawai babu lissafi.”

A zabure tace “Ke rufawa kanki asiri, ai ke dama yar abi yarima asha kid’a ce, tunda duk hôtel d’in da za taje ke kika rakiyarta, sannan tana sammiki wani kaso a cikin kud’in tazubar d’in, gaba kad’an ke ma zata fara had’aki da alhazan birninta.”

Wani mahaukacin mari Saminu ya kifa mata cikin b’acin rai yana fad’in “Ke ashe mahaukaciya?”

A hassale ya juya y’a kalli yayan Asma’u yace “Kai ina ne gidan? Yau sai kun bar unguwar nan fitinanniya kawai.”

Wani kuka ta fashe dashi tana fad’in “Kaka, Kaka.”

Ai kamar jira take ta kira sunanta ta fito ko mayafi babu tana fad’in “Waya tab’a min yar amanata? Wani tsinanne ya daki marainiyar Allah?”

Saminu ne ya nuna kanshi yace “Ni ne nan, wannan jikarki ce Iya?”

Saida ta kutsa ta kama hannun Maryam tace “Jikata ce? Me tayi ka daketa?”

Cikin bud’e baki da rashin wayo Maryam tace “Wai kawai dan na ce Mimi karuwar gida ce tana bin samarin unguwar nan, shi ne ya mareni a fuska yana zagina yana kirana mahaukaciya, kuma ai gaskiya na fad’a ko Kaka? Waye baisan tana iskanci ba ana bata kud’in kashewa, kuma ai har IPhone gareta ma.”

Duk kowa babu wanda yace wani abu saboda mamaki, sai Abba dake jin knashi na sara mishi da k’yar yace “Wace irin IPhone kuma?”

D’aya daga cikin yan matan ne wata tace “IPhone dai daka sani, waya salula ba.”

Zurum ya fad’a cikin gidan hankali a tashe, anan kam wannan hayaniyar suka ci gaba da yi inda muryar Kaka ta karad’e unguwar tana cin zarafin Saminu, saidai ya shiga mota ya barsu amma fa yayi niyyar sai sun bar unguwar nan, dan ta tab’a masa Mimin sa ba kuma zai lamunta ba.

Abba na fad’awa gidan a d’aki ya sameta ta cire hijabi tana share k’walla, kalmar karuwar nan ta mata zafi sosai, Mama kam kallonta tayi tace “Ke da wa kuma?”

Majina ta ja amma ba tace komai ba, tana shirin zame rigarta dan ta watsa ruwa Abba ya shigo d’akin bâ sallama, saida ta tsorota ganin yanda ya shigo d’akin, wani kallo ya tsareta dashi ya jefa mata tambayar “Da gaske kina da waya?”

Zaro ido tayi tana sulalewa k’asa ta shiga rarraba ido, dafe cikinta tayi daya shiga murd’a mata tana addu’a a zuciyarta, a tsawace ya sake fad’in “Ba dake nake magana ba kina ji na kinyi shiru?”

Da sauri tace “K’arya ce Abba, bana da waya ni.”

Da sauri yace “To IPhone d’in da ake magana a kai fa ta uban wacece?”

Cikin alaamar rashin gaskiya tace “Abba…IPhone kuma? Ni wa ya bani IPhone ? Ban tab’a ganinta a zahiri ba wallahi.”

D’an gajeran yatsanshi ya nuna mata yace “Uwata, wallahi fa duk randa na kamaki da waya a hnanu zaki ci ubanki a gidan nan.”

Tare suka kalleshi ita da mama, mamaki suke yanda ya b’angaro wannan ashar haka shi da ba mutumin ashar ba, jinjina masa kai tayi alamar to hakan yasa shi ciro k’aramar tecno d’in shi ya mik’a mata yace “Ki kira ki fad’a masa, idan kin gama wayar sai kije ki tambayi iyayen Asma’u idan zasu barta ku tafi tare.”

Karb’a tayi da ladabi tana fad’in “To Abba.”

Saida ya fita kafin ta zauna bakin gado tana saka lambobin Asas, ta jima tana kururuwa kafin aka d’aga tare da sallama, murmushi ta saki tana amsawa taare da fad’in “Na d’auka ba zaka d’auki kiran bak’uwar lamba ba.”

Murmushi yayi shi ma yace “Wane ni? Ban cika d’auka ba kam, haka kawai na ji wannan kiran na musamman ne saboda yanda zuciyata ta shiga bugawa.”

Yar dariya tayi tana satar kallon mama tace “Da baka d’auka ba ai da na ce na fasa auren.”

Jin haka yasa mama mik’ewa ta bar mata d’akin cike da kunya, Asas kuma d’orawa yayi da cewa “Maah da kin kasheni ashe, kinsan burin da na ci akan auren nan namu kuwa?”

Yar dariya tayi tace “Idan na kashe Asas ai Mimi ma mutuwa zatayi, ka d’auka zan rayu ne babu kai?”

Wani k’asaitaccen murmushi yayi yace “Mimi kar kisa na kuma durk’usawa gaban Abba na ce ya jawo lokacin aurenmu nan da sati.”

Dariya kawai tayi mai d’an sauti bâ tace komai ba, a hankali cikin sanyayyar murya yace “Naanah wannan lambar waye?”

A hankali ita ma tace “Lambar Abba ne, ya bani ne na kiraka dan na sanar da kai ya amince na je na gaishe da mama, saidai yace bayan gidanku da gidan yayarka kar na k’ara gaba sai gida kawai.”

Wani murmushi ya sake yi yace “Na ji dad’i sosai maah, hakan kuma yayi kyau sosai, ba komai zamuyi yanda Abba yace, yaushe zaki shirya.”

A tausashe tace “Abba yace gobe.” Murmushi yayi mai sauti yana fad’in “Kinsan da kuwa yanzu haka na dawo daga gidan aunty Hafsat, kuma ina zolayarta ina fad’a mata gobe zaki zo, har take tambaya ta wai me zata dafa miki? Ni kuma na ce mata ta yanka miki bijimin sa.”

‘Yar dariya tayi tace “Ni kam ina zan kai bijimin sa? Ai zaka sakani na tafi da babbar jaka dan na yi wa ‘yan k’annaina guzurin abinda suka jima basu ci ba.”

Wani d’an siririn murmushi yayi cike da tausayin yarinyar a ran shi, a tausashe yace “Ina wayarki? Me yasa zaki cinyewa Abba katinshi?”

Murmushi tayi tace “Abba ne ya bani ai saboda ta wa babu caji, amma idan na saka a caji zan kiraka.”

Jinjina kai yayi kamar yana gabanta yace “Shikenan ina jira, kuma fa karki manta dani.”

Girgiza kai tayi ita ma tace “Wace ni na manta da angona? Ai sai na ji sammacin kotu ban shirya ba.”

Yar dariya yayi yace “Mimi girmanki ai ya isa kiyi laifi kuma babu mai k’arfin halin hukuntaki.”

Murmushi tayi tace “Zaka fasa min kai na fa, yanzu dai sai na kiraka d’in.”

Da haka sukayi sallama ta kaiwa Abba wayarshi a tsakar gida yana kallon mama dake tsintar shinkafa, tana durk’usawa ta mik’a mishi ta mik’e ta koma d’aki, kayanta ta cire ta fito da d’aurin k’irji da hijabi saboda kunyar uban ta shiga dan watsa ruwa, jim kad’an ta fito ta shiga d’aki doguwar rigar kanti kawai ta saka ta fita a gidan zuwa gidansu Asma’u, duk da kallo suka bita sai dai mama ta k’asan ido take kallonta saboda kunya.

Saida ta fice Abba ya sauke ajiyar zuciya y’a kalli mama yace “Ina zaune lafiya da kowa a unguwar nan, ina k’ok’arin kiyaye hakk’in mak’wabtaka, wallahi duk ranar da yarinyar can ta sake kira min ‘ya da karuwa sai nayi shari’a da ita a kotun musulunci, ba zan lamunta ba wallahi dan na yarda da ‘yata.”

Mama kam a sanyaye tace “Ayi hak’uri dai malam, Allah ya kyauta kawai.”

K’wafa Abba yayi yana jinjina kai bai ce komai ba, ita kam mama a ranta take jin zafin maganar kamar zatayi kuka, ko da da gaske ne abinda suka fad’a ai akwai cin zarafi da tozarci, ita kan ta bata jin zata iya yin shiru idan aka sake maimaita haka gaskiya, dan ‘yarsu mutumcinsu ce, babbar darajarsu kuma Mimi ce.

              *Mim-Ma’u*

Labarin fad’ansu da Maryam babu inda bai shiga ba, shiyasa ma tana shigowa gidansu Asma’u suka sakar mata ido aka yi shiru, ita kam dake ta saba da irin wannan kallon dama sai bata kula da tsiyar kowa ba, maman Asma’u kawai ta kalla tace “Mama Asma’u fa?”

Nuna mata d’akin tayi tace “Yanzu ta shiga ciki.”

Wucewa kawai tayi ba tace da ta jira izinin shiga ba, samunta tayi tana saka kaya da alama wanka tayi ita ma, cire hijabi tayi ta jefa kan gadi ta zauna tana fad’in “Asma’u wurinki Abba ya aikoni.”

Kallonta tayi tace “Wuri na kuma? Me y’a faru?”

Saida ta kalleta da kyau tace “Asas ne ya nemi izinin na je na ga Hajiarsu, shi ne Abba ya amince amma dole sai in tare zamu je da ke.”

Da mamaki Asma’u ta zauna kan kujera tana gyara rigarta da fad’in “Da gaske Abba ya amince? Yaushe ne tafiyar?”

Yatsina baki tayi tace “Gobe.”

Da fara’a tace “Ba komai Mimi, zan fad’awa mamanmu insha’Allah sai mu tafi.”

Gyara zama tayi tace “Asma’u, bana so ki je gaskiya.”

Da mamaki ta tsareta da ido tace “Ban gane ba? Me yasa?”

Cikin rad’a tace “Kin gane Asma’u, shi fa Asas ni kawai ya buk’ata sannan ni ce zai gabatar a gaban mamanshi, Abba dai nasan tsoron faruwar wani abu suke, insha’Allah zan kare kaina babu abinda zai faru.”

Da mad’aukakin mamaki tace “Yanzu Mimi tsarin na iyayenki ne bai miki ba? Ina laifin kariyar da suke son baki ma?”

Yatsina fuska tayi tace “Ban ce bai min ba Asma’u, kawai dai ina so ne na tafi daga ni sai shi, bansan wace kalar tarba zan samu ba idan na je.”

Cikin tsareta da ido Asma’u tace “To kinsan da haka me yasa kika zo kika fad’a min?”

Ita ma idonta cikin nata tace “Saboda tare zamu bar gidan nan.”

Da mamaki tace “Kamar ya?”

Gyara zama tayi tana wani malalacin murmushi tace “…

*Muna barar addu’arku yan uwa? Allah ka bawa Khadija lafiya. Kwate na ma Allah ka k’ara mata lafiya mai inganci*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *15*

“Zamu fita daga nan muje gidan Iya Delu, ke zaki zauna a nan ni kuma saina wuce.”

Girgiza kai tayi tace “Mimi kina ganin ba matsala? Ya zakiyi idan Abba ya ganeki? Gaskiya ni dai ina jin tsoro ba za’a yi haka dani ba.”

Cike da tabbaci da tsaurin ido tace “Babu abinda zai faru Asma’u, kwantar da hankalinki kawai.”

Da alamar jimami sosai a fuskarta tace “Zamu ci amanarsu kenan? Yaudarar Abba zamuyi fa Mimi.”

Girgiza kai tayi tace “Ba yaudara bace, Asma’u ki fahimceni mana, kinga yanzu idan…”

D’aga mata hannu tayi tace “Matsalata dake taurin kai, indai kikayi niyyar abu babu mai hanaki.”

Mik’ewa tayi ta fara k’ok’arin d’aura zanenta bata sake tankata ba, ita ma mik’ewa tayi ta d’auki hijabinta a hannu ta fito dan tasan sunyi fad’a kenan ko zasu shirya sai sun had’e a islamiyyar yamma, takalminta ta saka a k’ofar d’akin ta wuce tana k’ok’arin saka hijab d’in, da kallo yayan Asma’u ya bi k’ugunta yana murmushi, lura da hakan yasa kishiyar maman Asma’u (mahaifiyarshi) cewa “Kai!”

Wannan tsawar data daka mishi tasa har Mimi juyowa ta kalleta, kallonta shi ma yayi yana zazzare ido, cikin jin haushi tace “Dan ubanka me kake kallo baki sake?”

Yatsina baki Mimi tayi ta juya ta saka hijab d’inta ta wuce ta barsu tana jin yana fad’in “To wai mama bani da ikon kallon abinda na ga dama ni da ido na?”

Ita kuma cikin fad’a take fad’in “Dan ubanka duk zalamarka waccen tafi k’arfinka, na d’aya dai kaga taxi ce ita da kowa ma shigarta yake, na biyu ba kowa take kulawa ba sai wanda taga akwai mamora a jikinsa.”

Mimi kam ko fa a kwalar rigarta sai ma fita da tayi daga gidan, ita indai ita zaka tab’a kai tsaye to bata da matsala da kai, ka dai saka iyayenta ne ko da ta hanyar zaginta ne bata lamunta ko kad’an, dan taana da tabbacin ko mijin aurenta zata iya tsinke fuskarshi da mari idan ya nemi fad’a ma iyayenta magana.

                 *Sheikh*

Cikin nutsuwa ya sake tank’washe k’afafunshi yana had’e tafukan hannayenshi ya ci gaba da fad’in “A duk inda zaku shiga a fad’in duniya, a duk halin da zaku tsinci kanku a ciki yarana kada ku yarda kuyi wasa da addininku, addininku shi ne gatanku, addinin islama shi ne alk’iblarku, addinin nan shi ne madogararku, dan haka duk inda zaku samu kan ku kuyi alfahari da addininku, kada bambamcin yare ko k’abila yasa ku ji kunyar nuna kanku a matsayin musulmi, kada wani rud’i na duniya ko kuma muzgunawa tasa ku wofantar da addinin daya baku madafa a sanda baku da tudun dafawa, addinin musulunci rahama ne a garemu kuma alfarma.”

A hankali ya kalli Aisha yace “Aysha, ke ce babba a gidan nan, ina sake gargad’inki da ki kula sosai da yan uwanki ki tayasu rik’e sallarsu ta farilla, kada ki barsu suyi wasa da ita a kowane hali, nasan macece ke kuma a halin yanzu kowane lokaci zaki iya shiga d’akin mijinki, amma hakan ba zai hanani sake jadadda miki rik’o da zumuncinku ba, a duk inda aure ko ratuwarki ta gaba zasu kaiki, zaki iya tsayawa tsayin daka wajen ganin kun rik’e zumuncin nan, ko bayan babu ranmu zaku zama gatan junanku.”

Cikin tsareta da ido yace “Kin fahimta?” Jinjina kai tayi alamar eh cikin sanyayyar murya tace “Eh Abie, insha’Allah zamu rik’e zumuncinmu, wannan alk’awari na ne a gareku iyayena.”

Jinjina kai yayi yace “Masha’Allah, sai kuma kai *Heezam*.” Ya fad’a yana kallon k’annan Aisha mai bi mata, a nutse yace “Bana da d’ar a kan ka dan na saka maka ido sosai ina lura da duk wani tako da motsinka, a tak’aice kuma a yanzu dai banga wani abu daya nuna shagala akan sallahrka ba, haka kuma ban ga alamar wasa a cikin karatunka ba, kamar yanda banga wani b’ataccen aboki da zai iya b’ata tarbiyarka ba, saidai hakan ba shi zai sa na zuba maka ido ina kallonka haka kawai ba, Heezam.”

Ya kira sunanshi cikin dakakkiyar murya, amsawa yayi a ladabce yace “Na’am Abie.”

D’orawa yayi da “Daga yanzu zamu fara fita tare da kai zaman majlisi, sannan ina so kai ma ka fara wani k’ok’ari akan matasa yan uwanka dan bayar da ta ka gudummuwar.”

Da ladabi ya jinjina kai yace “Insha’Allah Abie.”

Kallon *Aswane* yayi ya saki murmushi yace “Manya masu gari, macijin k’aik’ayi kenan sari ka nok’e, wato yarona Aswane duk gidan nan babu wanda ya kai ka karatu, haka kuma babu wanda ya kai ka iya shegantaka.”

Duk dariya aka d’auka a wajen har Hafsat dake shafar cikinta saboda juyawar da yaron cikin ke yi mata, cikin muryar laushi tace “Akwai son gayu fa kamar ya ga ubanshi Asas, amma kuma yafi kowa tsanar irin shigar da matasa keyi ta k’ananan kaya.”

Dariya sheikh yayi sosai yana fad’in “Wannan ikon Allah yana bani mamaki, wai kai ka saka riga da wando na zamani ka d’aure k’ugu da ceinture (belt), amma idan ka fita waje ka ga wani matashi zai wyce da shiga irin ta kai saika gyara tsayuwa ka tsayar ka dinga yanko mishi hadisai da ayoyi harda karatun d’ab’ia na d’an adam ma kana nuna mishi rashin dacewar haka.”

A sanyaye ya kalli Aswa’ne daya d’aure fuska tamau yace “Sheikh Aswane ya kake nufi ne to? Shin kana so ka koyar da hallacin shigarka ne ga matasa a aikace? Ko kuma dai kana son su k’yamaci abinda kai suka ga kana yi ne?”

Saida ya sauke ajiyar zuciya ya shafa tarin sumar dake kan shi a gaban yace “Abie, ai ni ba irin waccen shigar nake yi ba da ake zazzago wando ana takawa, kuma nima ina so na daina saidai Allah ne ya saka min soyayyar kayan a raina, kuma sun fi yi min kyau idan na saka.”

Girgiza kai yayi yace “Kash! A gaskiya tunani da idonka sun fad’a maka k’arya yarona, taya kake tunanin suturar yahudawa zata fi yi maka kyawu fiye data ka suturar? Wa ya fad’a maka kawai kana son su ne saboda Allah ne ya saka maka soyayyarsu? Aswane magana ta gaskiya sutura ta hausa ita ce cikakkiya kuma kamilalliyar sutura, na yarda idan ka ce sun fi maka kyawu a jikinka, to amma kamala fa? Ita ma suna fito maka da ita ne?”

Shiru yayi kan shi a k’asa hakan yasa shi girgiza kai ya gyara zama tamkar zaiyi magana da d’an shekara ashirin ba wanda shekarunsa duka goma sha biyu bane yace “Aswane, wannan suturar da kake sakawa ta hayudu ce, manufa ce dasu data sa suka k’irk’iri wannan suturar, kuma sun cimma burinsu tunda har suka yi nasarar ribatar ire-irenku, amma ka sani cikar kamala na cikin tufafin hausa, fito da asalin haiba da kwarjinin mutum sai tufafin bahaushe, da wannan nake kira gareka d’ana ka siyawa kanka mutumci ta hanyar yafa shigar mutumci a jikinka.”

Jinjina kai Aswane yayi yace “Insha’Allah Abie, zan kiyaye.”

Jinjina kai yayi ya kalli d’an k’aramin yace “Wannan shi ne autana kuma ba autana ba, *Munzeer* yaron kirki ne, ba ruwanka da rigima ko fad’a, karatu kawai ka saka a gaba ko yaron kirki?”

Cike da jin dad’i yaron mai shekara biyar ya jinjina kai alamar eh, dafa kanshi yayi yana jinjina kai da murmishi yace “Allah muku albarka, Allah ya k’arawa karatun albarka, Allah ya k’ara had’a kanku, Allah ya wadataku da lafiya mai anfani.”

Gyara zama yayi yace “Ku tashi ku tafi.” Mik’ewa sukayi bayan sun amsa a ladabce, duk da kallo suka bisu har suka b’ace ma ganinsu, saida suka shige ciki kafin ya mik’e shi ma, hannun Hafsat ya kama yana fad’in “Muje ki kwanta ki huta, dare yayi fa.”

Murmushi tayi tana ci gaba da shafa yaron cikinta daya dunk’ule wuri d’aya kamar baya motsi, suna shiga d’akin ta fahimci yau kenan zai kawo mata ziyara, dan baya zaune sai mace ta sameshi d’akinshi, da kanshi yake zuwa inda kike sannan ya lallab’aki ya amshi hakk’inshi, dan haka saita daure sosai ta saki jikinta bata yarda ta nuna bata jin dad’i ba, saida ya tayata yin wanka kafin suka k’arasa gadon girma, duk da tana jin d’an cikinta ya dunk’ule mata a mara haka ta jure bata nuna bata ra’ayi ba, har tambayarta yake ya isa haka saita sunkuyar da kai tace “Sai ka gamsu.”

Shi kuma a duniyar Allah yana matuk’ar son mace mai raki, rakin ma irin na tsiyar nan, wallahi a duniya yana son y’a ga mace dake mayar da masassara ciwon kai, wacce zata dinga billi tana kuka akan abinda bai kai bai kawo ba, yana so wata rana Hafsat ta gwada yin haka ko sau d’aya ne, da zai yi zaune ya aje hularsa da babban riga da hirami ya dinga mata hidima yana rarrashinta. Da k’yar ya samu gamsuwa ya taimaka mata ta tsarkake kanta ta dawo ta gyara shinfid’ar ta kwanta a matuk’ar wahale.

              *Washe gari*

Tana tsaka da tsantsara kwalliyarta a fuska ta ji wayarta dake cikin k’aramar jakar da zata fita da ita tana vibrations, saida ta d’an d’aga labulen d’akin ta tabbatar suna waje suna harkar gabansu kafin ta ciro wayar, zaro ido tayi ganin lambar sheikh ce wacce tsabar mahimmancin data bata har ta iya hardaceta a kan ta, ita kan ta bata san ta bashi wannan mahimmancin ba. Sam bata son d’aukar wayar a lokacin, amma abun mamaki lambarshi kanta kwarjini take mata ta yanda ba zata iya share kiran ba, hannunta da zuciyarta na kakkarwa ta d’aga kiran tana jan sallama, a sanyaye sosai ya amsa da “Wa’alaiki salam.”

Shiru ne ya d’an ratsa na dak’ik’u kafin yace “Ki gafarce ni Ryam na sake kiranki, zuciyata azalzalata take a game da lamarinki, dan Allah ki fad’a min idan Abbanki ya dawo na zo na ganshi.”

Wani sanyayyan murmushi ta saki a ranta tana fad’in “Allah mai iko, ni Maryam ba kowa ba kuma ba ‘yar kowa ba, yau ni ce har babban malami kamar wannan yake min magiya haka?”

Ajiyar zuciya ta sauke tare da tunanin ai Abba ya karb’i lefenta har da ma kud’in aurenta, dan haka tasan duk girmanshi Abba ba zai yarda yayi magana biyu ba, dan haka ta saki murmushin jin dad’i tare da bud’a bakinta tace “Abba ya dawo jiya, dama na rasa yanda zanyi na kira ne.”

Wani sanyayyan murmushi yayi shi ma har tana jin sautinsa yace “Na ji dad’i sosai Ryam, zan zo gidanku yau insha’Allah.”

Cikin rashin jin dad’i a zuciyarta ganin yanda zata sakashi zama wani wawa haka tace “Shikenan, Allah ya amince.”

Da fara’a yace “Ameen, nagode, sai anjima.”

A k’asan mak’oshi tace “Uhum.” Tana aje wayar ta kalli agogon screen d’in, da sauri ta aje wayar ta shiga gaggawar k’arasa shirinta, ta mik’e kenan tana gyara zaman rantsetsiyar abayar data saka bak’a wulik wacce ta fito da hasken fatarta ta yana kallabin y’a mata kyau sosai, Asma’u ce ta shigo da sallama mama ta amsa, tana shigowa suka kalli juna suna murmushi, ko gyara kayan data barbaza batayi ba ta d’auki jakarta tace “Muje kinji.”

Fitowa sukayi Asma’u na fad’in “Wa zai d’auke waccen kayan kuma?”

Kafin tayi magana mama da taji ta tace “Ta bari jakarta ta d’auke mata mana.”

Dukansu dariya sukayi kafin Mimi tace “Mama zamu wuce gidan Iya, kinga idan ya gaishesu ita da malam sai mu wuce.”

Jinjina kai tayi tace “Allah ya yarda, ku kula dan Allah kunji.”

“Insha’Allah.” Ta fad’a tana kama hannun Asma’u suka fita daga gidan.

Kamar dai kullum zaka rantse da Allah wata ‘yar hamshak’in mai kud’i ce, hatta takonta d’aukar hankali yake yanda duk da duhu ne ana k’are mata kallo, ga k’amshin da take bari a duk inda ta gifta ta wuce, da haka suka isa gidansu Iya D’élu, da raha suka shiga zolayar juna ita da kakanin nata data samu malam na cin abinci, kamar yanda tun a kan hanya ta fad’awa Asas dan haka suna zuwa ba jimawa ya iso.

Da kan ta ta fito ta mishi iso zuwa cikin gidan, sosai suka gaisa har malam na fad’in “Ai bansan zaka zo ba da ban yarda ka sameni ba.”

Cikin shagwab’a Mimi ta kalleshi tace “Angona.”

Dariya yayi tare da shafar kumatunta yana fad’in “To ai bana so ya gane kishina ne a kan ki, zan iya cakumarshi yanzun nan mu hau sama.”

Dariya sosai Asas yayi yana sunkuyar da kai cike da kunya, Iya Delu ce tace “Ni kuma farin ciki nayi dana ganeshi, dan a take naji na samu miji nima mai jini a jika.”

Kallon Mimi tayi tace “Ba kullum cika baki a kan ni na tsufa bane ke kuma sabon jini? To ni ma na k’wace miki miji.”

Dariya sosai ake yi har Asas yace “Gaskiya ne, ni ma yanzu dana ganki na ji bana buk’atar sabuwar jinin, dan kuwa da tsohuwar zuma ake magani.”

Da irin rahar nan suka musu sallama suka fita tare da Asma’u, saidai a k’ofar gidan ita suka rabu inda Mimi ta sake jadadda mata “Asma’u ki zauna gidansu Jamila, idan na zo zan kiraki a waya saiki fito waje mu k’arasa gida, kin gane?”

Jinjina kai tayi tace “Na gane, sai kun dawo.”

Murmushi ta mata tace “To.” A raunane tace “Dan Allah Mimi ki kula da kanki kinji.”

Jinjina kai tayi alamar to, gidansu Jamila ta nufa ita kuma ta bud’e motar ta shiga, kallonta yayi yace “Ba tare zamu tafi da ita ba?”

Girgiza kai tayi tace “Dama akwai inda zata je, hanya ce kawai ta had’amu.”

Jinjina kai yayi tare da tayar da motar suka d’auki hanya.

A k’alla sun d’auki minti talatin kafin suka isa gidan, a sanda ya shiga gaba yana mata jagora zuwa babba kuma k’ayataccen falon, tsoro, fargaba, al’ajabi da kuma kunya ne suka taru suka baibayeta, da haka suka shiga falon Asas na fad’in “Hajiata, fito ga sarakuwarki na kawo miki, zo kiga yar beautyna.”

K’asa ta sake yi da kanta tsabar kunya tana sake rik’e jakarta tamau a hannu, da fara’a da kuma al’ajabin ganin kyakyawar yarinyar mai kama da larabawa ta shiga takowa tana fad’in “A’a masha’Allah, yau kam autana ya cika alk’awari.”

Tana zuwa ta ja Mimi a jikinta ta rumgume wacce ke neman sulalewa k’asa, sosai tayi mamakin yanda mahaifiyarshi ta tarbeta, bata zame da ita ko ina ba sai kan teburin cin abinci, zaunar da ita tayi tana k’walla kiran “Salamatu! Salamatu.”

“Na’am Hajia.” Aka amsa daga ciki ana fitowa, tana zuwa Hajia tace “Kinga bak’uwa na yi, ki kawo mana abinci.”

Saida ta kalli Mimi da kanta ke k’asa, d’an k’ara lek’a fuskar tayi da son gano a ina ta san fuskar, tunawa da tayi yasa ta jinjina kai ta kalli Asas, murmushi ta k’ak’aro tace “To Hajia.”

Juyawa tayi ta koma tana mamakin shi kuma yallab’ai Asas me ya had’ashi da yarinyar? Ita ce zai aura? Wacce ake kira da karuwa, karuwar ma ta samarin unguwa, bugu da k’ari kuma ‘yar wada, dan kuwa duk fad’an nan da akayi na jiya a gabanta, ita ce ma suka zaburo suka rabasu sanda suka kacame da fad’a. Haka ta gama duk abinda ya dace ta kawo ta kuma kula da komai amma bata daina kallon Mimi ba, gashi taga daga Hajiar har Asas d’in sai hira suke jan ta da ita da raha alamar dai ta samu karb’uwa a wurinsu sosai.

Saida ta gama ta koma ciki Hajia ta kalli Mimi tace “Takwarata, ci abinci kinji, nan gidan fa ba bak’onki bane.”

Murmushi ta sake yi ta sunkuyar da kanta k’asa, da zolaya Asas yace “Kunyar Hajia wai kike ji? Kinga yanzu fa ke ce autarta ko, ni na bar miki yanzu dan na girma, tunda nan gaba kad’an zaki haifa min yara.”

Satar kallonshi tayi da mamaki baki bud’e, sai kuma tayi shiru kawai kan ta k’asa tana jin Hajia na fad’in “Matsalata da kai kenan rashin kunya.”

Jawo kujerarta tayi ta koma kusa da Mimi ta d’ebo abincin zata kai bakinta, sinne kai ta sake yi cike da kunya tana murmushi, tallabo hab’arta tayi tace “Maryam, ni ma fa mahaifiyarki ce, kinga bana da ‘ya’ya dayawa sai guda biyu, ki saki jikinki dani kinga zaki shigo ahalin nan ba da jimawa ba.”

Jinjina kai tayi alamar to, sake kai mata cokalin tayi a baki haka yasa ta karb’a cike da kunya, duk yanda ta so zillewa bata samu dama ba haka ta dinga ciyar da ita da hannunta, tana tsaka da cin abincin ne ta kalli Asas tace “Kaga takwarata sai tayi kama da *Fanna*, ko dai ‘yar uwarta ce?”

Girgiza kai yayi yace “Bana jin ma sun tab’a had’uwa.”

Kallon Mimi tayi tace “Takwarata, waye mahaifinki? Ina ne gidanku?”

Da sauri Asas ya kallesu yana neman k’warewa, to shi dai bai wani zauna ya fad’a mata wacece Mimi ba, yasan danginshi kuma farin sani zasu iya kawo mishi tangard’a, gata ita kuma bata b’oye komai daya shafi asalinta yasan tsaf zata fad’a mata komai.

Mimi ma satar kallonshi tayi kafin tayi k’asa da kanta tace “…

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *16*

“Mama ni ba ‘yar kowa bace, mu talakawa ne da muke fafuta akan abinda zamu ci, sannan iyaye na…”

“Mutanen kirki ne.” Cewar Asas da sauri yana tsare Hajia da ido, duk kallonshi sukayi da mamaki sai Hajia data d’an basar ta kalli Mimi tace “Ke ‘yar talakawa ce?”

Jinjina kai tayi ba tare data kalleta ba, a hankali Hajiaa ta aje cokalin hannunta tare da yab’awa fuskarta yanayin rashin jin dad’i, kallon Asas tayi ta mik’e tace “Ka sameni a d’akina.”

Lumshe ido yayi irin na ohh shiit d’in nan tare da kallon Hajiar bai ce komai ba, da kallo suka bita har da Mimi dake al’ajabi da mamaki, kallonta yayi ya mik’e yace “Ina zuwa Maah, karki damu kin ji, ki ci abincin.”

Da kallo ta bishi kafin ta kalli farantin gabanta, hak’ik’a tana son cin wannan gara da aka wadata gabanta da ita, saidai zalamarta bata kai wannan matakin ba, da taga fuska ne ma zata iya d’iba ta kai wa ‘yan k’annanta su goge hak’ora, amma daga yanda ta ga fuskar matar kam tasan sai ta Allah aurenta da Asas yayi wu.

*Suna* shiga a zafafe ta juyo tana fad’in “Asas dama yarinyar nan ‘yar talakawa ce?”

Cikin rashin karsashi yace “Hajia miye dan ‘yar talakawa ce? Shikenan mu dake da hali ba zamu iya auren ‘ya’yan marasa k’arfi ba dan a tallafawa juna.”

A kausashe tace “Kaga Asas ba kasancewarta ‘yar talakawa ba yasa nake maka maganar nan ba, babbar matsalar shi ne dama ba daga ahalinmu ta fito ba, dangi zasu ga laifina ne na barka ka auri yarinyar da ba nasabarku d’aya ba sannan yar talakawa, kafi kowa sanin yanda ake son had’aka da ‘ya’yan dangi amma ka k’i, larurarka tasa na ce a rabu da kai zaka zab’a da kanka, shi ne yanzu zaka zo min da waccen yarinyar.”

Sanyaya murya ya sake yi sosai yace “Hajia ta, dan Allah karki hanani auren Mimi, ina sonta da zuciya d’aya ba zan iya rabuwa da ita ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Yanzu ka je kusa da ita ka zauna, idan ta kammala ka kaita gidan auntynka tunda an fad’a mata zaku je can.”

Marairaicewa yayi yace “Hajia ba zaki hanani aurenta ba?”

Yatsina fuska tayi tace “Ka je kawai zanyi tunani.”

Sake shagwab’ewa yayi yace “Hajia haka zaki tarbi bak’uwarki?”

D’an murmushi ta k’ak’aro tace “Muje to.”

Da fara’a ya biyo bayanta suka fito falon, yanda suka barta haka suka sameta, bata yarda ta had’a ido da ko d’aya daga cikinsu ba, zaune sukayi Asas na fad’in “Maah, mun barki ke kad’ai? Kiyi hak’uri.”

Murmushin yak’e tayi haka ma Hajia murmushin yak’en ta shiga yi, jim kad’an ya kalli Mimi da kanta ke k’asa bata cin abincin yace “Kina lafiya ko?”

Jinjina kai tayi ta kalleshi tace “Abba yace kar na jima.”

Murmushi yayi ya kalli Hajia yace “Hajiata zamu wuce gidan Aunty Hafsat.”

D’an kallon Mimi tayi tace “To Allah ya tsare, ku gaishesu da kyau.”

Mik’ewa Mimi tayi hakan yasa shi ma ya mik’e haka ma Hajia, k’wala kiran Salamatu tayi tana zuwa ta sunkuya tace “Hajia gani.”

A gadarance tace “Ki d’auko min sak’on nan dana ware dan bak’uwata.”

D’an d’aga ido Mimi tayi ta kalli Hajia, a kuskure kuma idonsu suka had’u ita ma tana kallonta tana mamakin yanda tace yar talakawa ce ita amma fatarta wata irin fresh da ita, uwa uba ga abayar jikinta wacce ta shekarar bara ta siyowa Hafsat su dayawa da shegiyar tsada, to a ina ta samesu kenan? Bayan tace talaka ce ita. Tana wannan tunanin Salamatu ta kawo manyan ledojin kalar pink guda biyu, ajewa tayi k’asa tana fad’in “Gasu Hajia.”

Cike da wulak’anci tace “Ki bata, zasu mata anfani.”

D’agowa ta sakeyi ta kalli idon Hajia tsaf kallo na ki fahimceni naa fahimceki, Hajia kan ta saida ta ji wani shakkun yarinyar saboda yanda ta kalleta babu tsoro a ciki da kuma rashin d’aukar raini, mik’o mata ledojin Salamatu tayi tana fad’in “Gashi k’aramar Hajia.”

A yangance ta kalli Salamatu ta yatsina fuska dan hakan d’abi’arta ce kafin tace “Nagode, Abbana ya hanani karb’an kyauta irin wannan.”

Da mamaki Hajia ta kalleta, sai kuma ta tab’e baki ta kalli Asas tace “Ka d’aukar mata kayan, watak’ila kunya take ji.”

Girgiza kai tayi a hankali tace “Bana so Abbana ya min fad’a sakamakon aikata abinda ya haneni.”

A ladabce ta juya zata fita tana fad’in “Nagode da karramawa, sai anjimanku.” Da kallo Hajiar ta bita haka ma Salamatu, Asas kam tuni ya juya zai bi bayanta Salamatu tace “Alhaji ka d’aukar mata kayan mana, ina ga fa kunya ce kamar yanda Hajia ta fad’a, ai bâ kyau mayar da hannun kyauta baya.”

Murmushi ya mata tare da d’aukar ledojin nik’i-nik’i ya bi bayanta da su, cikin al’ajabin lamarin yarinyar Hajia ta juya zata zauna kan kujera tana fad’in “Amma yarinyar nan akwai yar rainin hankali, wacece ita? Me take tak’ama dashi?”

Cikin ladabi kamar wata jakadiya Salamatu ta bi bayan Hajia tana fad’in “Ai ni banyi mamaki ba Hajia, bansan yarinyar ba ko kad’an, amma bansan me yasa jiya muka had’u da ita ba.”

Kallonta tayi tace “Kun had’u da ita ne? A ina?”

Zaune tayi k’asan k’afafun Hajiar tace “Hajia zaki tuna jiya kin aikeni gidan Kubra karb’o turarukan da kika saka a ledojin bak’uwarki?”

Jinjina kai tayi alamar eh, d’orawa tayi da “To ai unguwar take basu da nisa sosai, a titi na gansu suna fad’a ita da ‘yan makarantarsu Hajia, dambe kamar maza wallahi haka na ganta, kuma kalaman da abokiyar fad’an take fad’a mata sune suka fi d’aga hankali, dan bata musa ba sai dai kuka da take.”

Gyara zama Hajia tayi tace “Uhum! Ina jinki.”

Tas Salamatu ta kwashe duk abinda ta ji kuma ta gani ta fad’a mata, hankali a matuk’ar tashe Hajia ta zaro ido tace “Wada fa kika ce? Kina nufin ubanta wada ne?”

jinjina kai tayi tace “Wallahi wada ne Hajia, da idona naga sanda ya shiga da ita cikin gida.”

Mik’ewa Hajia tayi a hassale ta juya zuwa d’akinta tana fad’in “Ina! Ba zai yiwu ba wallahi, yar wada? Shin ina hankalinshi ya tafi ne da zai jawo min wannan iskancin, baisan cewa wannan larurar jini take bi ba, ko ita ba kalarsu bace kuma ta auri dogo zata iya haihuwar irin ubanta.”

K’wafa tayi ta shiga d’aki dan d’aukar waya ta kira k’anninta wanda su suka karb’o mishi aurenta, shi ma bai fad’a mata komai ba kawai yace dai mutanen kirki ne, bayan haka babu wanda yace mata komai uwa uba kuma sheikh da tasan dama babu abinda zai fad’a mata na aibun mutanen.

                 *Mim-Sas*

Sam sai taji aurenshi ya fita a ranta, kawai tasan ma aurensu ba zai yiwu ba daga yanda mahaifiyarshi ta nuna mata d’in nan. Saidai tasan zata rasa namiji da yayi daidai da muradinta, numfashi ta sauke a hankali tare da d’an k’amk’ame jikinta saboda sanyin ac, d’an tab’e baki tayi data tuna a gidan ma ac ce ga mota ac, shiyasa masu kud’in nan zaka ga jikinsu ma daban yake da saura, wani taushi da laushi zaka ga fatarsu na fitarwa na musamman kamar dai yanda a ido ne kawai take ganin fatar Asas d’in zatayi wannan taushin.

Lura da yanayinta ya sakashi fad’in “Mimi, ni kam wace k’asa ke birgeki a duniyar nan?”

Kallonshi tayi ba yabo ba fallasa tace “Me yasa ka tambaya?”

Da fara’a yace “Ina so ne na sani dan na fara nema miki visa, dan a can zaki ci amarcinki.”

Wani farin ciki ne ya kamata tare da yin murmushi ta sunkuyar da kai, shi ma murmushin yayi yace “Ina jinki.”

Saida ta tsagaita tace “Umm! K’asar Madina, sannan k’asar Saudia.”

Jinjina kai yayi yace “Da kyau, kinga kenan zaki jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya, zaki sha amarcinki sannan zakiyi aikin hajj.”

Wani murmushin ta sake yi kawai ba tace komai ba, shi kam dan ya sa ta saki jikinta yasa shi cewa “Akan maganar bikinmu, abokanaina sun fara hura min wuta wai dole na musu wata walimar tare da ‘yan mata, me kika ce a kai?”

Numfashi ta sauke tace “Duk yanda kayi d’aya ne.”

“Da gaske?” Ya fad’a yana satar kallonta, jinjina kai tayi tace “Da gaske.”

Jinjina kai shi ma yayi yace “Shikenan, zanyi tunanin abinda ya dace, matsalar da zaran mun d’auko maganar party sheikh zai taka mana burki, bansan ya zanyi ba gaskiya.”

Kallonshi tayi da mamaki da son jin waye sheikh d’in nan? Na biyu kenan tana jin sunanshi a bakinshi, a hankali tace “Wane sheikh?”

Da mamaki shi ma ya kalleta yace “Wane sheikh? Kina nufin baki sanshi ba? Shi ne fa wakilina a wajen d’aurin aurenmu, kuma shi ne yake auren yayata Hafsat, banda kamarsa a cikin abokai da ma yan uwa.”

Jinjina kai tayi tace “Da alama yana da mahimmanci a gareka?”

Murmushi yayi yace “Fiye da tunaninki, zan iya yin komai saboda sheikh, ina sonshi fiye da yanda nake son kaina, shi ma kuma yana so na sosai.”

Murmushi kawai tayi ba tace komai ba, kallonta yayi yace “Wai da gaske baki tab’a jin sunan sheikh Abdul w…”

K’arar da IPhone d’inshi ta d’auka yasa ka shi yin shiru yana d’aukar wayar da dubawa, murmushi ya mata yace “Kinga shi yake kirana ma.”

Ya fad’a yana nuna mata wayar, saman kawai ta gani sunan daya fito b’aro-b’aro wato *d’an uwa na*, yana d’auka ita dai tana jin yana fad’in “Allah sheikh gamu nan a hanya, kad’an ya rage ka ganmu gabanka.”

Bata ji me aka fad’a bâ amma taga yayi dariya yace “OK sai mun zo.”

Aje wayar yayi yana girgiza kai yace “Ya min alk’awarin tarbanshi da kanki ne, shiyasa ya matsu mu iso dan akwai inda zai je.”

Jinjina kai tayi tana murmushi tace “Allah sarki.”

Da haka suka isa k’ofar tamk’amemen gidan, irin ginin nan ne na zamani mai d’aukar ido, gashi had’e da masallaci abun gwanin birgewa, ga hasken fitilu masu kyau wanda suke ship ship a cikin shukoki, ita dai baki ta saki tanaa kallon ikon Allah, wato can data bud’e ido tana kallon gidansu Asas ashe bâ komai ta gani ba, yanzu ne zata yi kallo uya son ranta, mai gadi na bud’e musu suka shiga ciki, a gaban wata jibgegiyar reng rover bak’a ya tsayar da motar, a hankali ta shiga fitowa tana sake kallon girman gidan lai d’auke da tsaki da kyan gaske, wani irin iska ne ta gauraye gidan na shukoki mai sanyin gaske da saka bacci. 

Gaisawa Asas yayi da jami’an sheikh dake jiranshi ya fito, gaba ya shiga ita kuma tana take masa baya tana kuma satar kallon gidan, suna zuwa k’ofar falon ta kalli kanta ta madubin dake k’ofar, tura k’ofar yayi daga ciki ya shiga, ita ma a hankali ta cire takalminta ta taka k’afarta akan pause pied d’in dake bakin k’ofar mai taushi kamar bargo, a sanyaye ta lumshe ido ta furta “Masha’Allah.”

Falon akwai girma amma kuma an cikeshi da kujerun alfarma kujerun dake birgeta, wanda take da burin lallai in zatayi aure dole Abba ya siya mata royal, ga ni’imtaccen k’amshi da kuma sanyi dake fita, yaran da mahaifiyarsu duk zaune suke a nutse sai hira da suke k’asa k’asa.

Da farin ciki da kuma karramawa duk suka mik’e suka nufi Mimi yaran na fad’in “Aunty sannu da zuwa.”

Hafsat kuma tana fad’in “Sannu da zuwa yar uwa.”

Turo baki Asas yayi yana fad’in “Yau kuma a gidan nan babu wanda zai min lale?”

Murmushi Eesha tayi tace “Kayi hak’uri tonton, na yau dai ka barwa auntynmu wannan ranar.”

Mayar da kallonta tayi kan Mimi tana jin ta samu k’awa tace “Aunty Mimi barka da zuwa.”

Da murmushu tace “Anwuni lafiya.”

Kama hannunta Eesha tayi suka zauna kan kujera, kallonta Hafsat tayi tace “To fa sarauniyar gwandagi, wato kin ga k’awa ko? To ai zaki kawo mata ruwa ko.”

Mik’ewa tayi da murmushi ta nufi wata kusurwa, ita ma zaune tayi kusan Mimi tana fad’in “Mai sunan Mama ya gida?”

Sunkuyar da kanta tayi tace “Ina wuni.”

Gaisawa sukayi sosai, su Aswane ma gaisheta sukayi ta amsa, a kadabce ta kama hannun Munzeer dake k’arami tana fad’in “Ya sunanka?”

A hankali yace “Munzeer.”

Da fara’a tace “Masha’Allah, suna mai dad’i.”

Shafa kan shi tayi sai Aswane da yace “Aunty ni baki tambayi sunana ba? Yafi na shi dad’i fa.”

Dariya tayi tace “Ya sunanka?”

“Aswane.” ya fad’a yana murmushi, girgiza kai Hafsat tayi tace “Allah ya shirya.”

“Ameen.” Mimi ta fad’a tana satar kallon matar mai matuk’ar dattako, gata cikin shirin doguwar riga ita ma abaya tayi tsaf duk da ba kwalliya ce a fuskarta ba, haka ma cikin jikinta ya mata kyau dan bâ wani girma ne dashi ba. Muryar Asas ce ta dawo da ita daga kallon Hafsat yana fad’in “Wai ina shehi ne kuma ya shige? Nan fa yake ta zura min kira kamar zan sameshi a k’ofar gida yana jirana.”

Dariya Hafsat tayi tana kallon Eesha data aje faranti a gaban Mimi tace “Nan yake zaune ma, yanzu ya shiga ciki amsa waya, da alama wani wurin zai je mai mahimmanci, dan na ji yana k’orafin ba zai fita da masu tsaron ba yau.”

Murmushi Asas yayi yace “Ustaz kenan, shi fa idan tashi ne yayi ta tafiyarshi sakaka a gari.”

Ita ma murmushin tayi tace “Ni kaina na fi son haka, duk abinda Allah ya rubuta zai faru ai shi ne zai faru, babu abinda zasu iya tare masa wanda aka rubuta zai same shi.”

Jinjina kai duk sukayi sai Asas da yace “Duk da haka, kula da lafiyar yana da kyau.”

Kallon Munzeer tayi tace “Munzeer, shiga librairie (labrary) kaga Abienka ya gama wayar.”

Jinjina kai yayi tare da nufa kusurwar da zata sadashi da d’akin karatun sheikh d’in, zai bud’e k’ofar shi kuma ya bud’e ya fito bayan ya gama wayar, dama shi da Muddaseer ne da yake k’ara kwatanta mishi gidansu Ryam d’in shi, dan yanzu can zai nufa dan ganawa da iyayenta.

Sanyayyan k’amshin turarenshi mai matuk’ar tsada ne trésor ya fara musu maraba, bud’add’en alkyabarshi irin ta malamai fara k’ar wacce ya d’ora akan farar shaddarshi mai k’yalli, fararen takalmi k’afa ciki da kuma farin hirami daya d’aure hular dake kanshi, siririn farin glas ya saka duk da bai cika sakawa ba, amma dake yau ranar ta musamman ce saiya saka.

Takowa yayi ba tare da ganin fuskarta ba dan ta bashi baya ne daga inda take, saidai yana kallonta yaji fad’uwar gaba tare da tsanantawa da gudun jinin jikinshi, fararen hannayenta masu kauri yake kallo da take shafar kan Munzeer. 

Saida ya zo daf ita kusa da Hafsat ya tsaya, kafin kowa yace wani abu Asas yace “To malam ga amaryata dai na kawo maka.”

Murmushi yayi tare da kallon fuskarta dake sunkuye, a lokacin Asas yace “Maah ga sheikh da nake baki labari.”

A hankali, a ladabce kuma a nutse ta d’ago da innocent fuskarta, *ido biyu* sukayi k’uru k’uru suna kallon juna, dukansu babu wanda bai firgita ba haka kuma kowanensu ya kad’u. Da sauri tayi k’asa da kanta ta rintse ido sosai tana ambatar “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un.”

Saida ta maimaita sau uku, a take wata irin kunya da matsananciyar nadama ta rufeta a gurin, bata tab’a tsammanin haka zai faru da ita ba, ko a mafarki bata tab’a jin cewa zata iya hakaito haka ba, me kenan yake shirin faruwa da ita? Me ta aikata haka data tsinci kanta a wannan halin? Duk sanyin wurin saita samu kanta da jin wani irin gumi na tsatsafo mata, gashi komai na jikinta ya daina aiki hatta da jinin jikinta ma, ta kasa motsawa bare ta fita a guje ta bar gidan.

Sheikh kam da kanshi ke neman yin bindiga gaba d’aya saiya rasa me zaiyi tunani a kai, a dai lokacin kam babu ta yanda zai fara tunanin lamarin, sai kawai yayi k’arfin halin cewa “Sannu ko?”

Shiru Mimi tayi dan bakinta ya mata nauyi ta kasa furta komai, muryar Asas ce ta samar mata d’an k’wari k’wari yana fad’in “Sheikh gashi zaka fita, mu ma kuma tafiya zamuyi yanzu.”

Da k’yar da sud’in goshi ya k’ak’aro murmushi yace “Hakane, amma ai zaku iya zama, da alama ma tafiyar ta fasu, dan dama zan je ganin wani muhimman bak’o, amma ganinku ya tuna min da wani abu.”

Da sauri ta d’aga kai ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana d’an ciza kakkauran leb’enta, wasu hawaye masu zafi na takaicin halin data samu kanta ciki kawai taji sun zubo mata, a hankali tasa bakin kallabin abayarta ta share cikin dubara.

Mik’ewa Asas yayi yana fad’in “Aunty Hassu, zamu wuce fa dan bâ jimawa zamuyi ba dama.”

Mik’ewa tayi tana fad’in “Da wuri haka? Amma dai zaka sake kawo min ita ta wuni ko?”

Murmushi yace “Gaki nan gata nan kuyi magana, idan ta amince ni mai sauk’i ne.”

Kallonta Hafsat tayi ta matso kusanta sosai tace “Mimi zaki sake dawowa ko?”

Shiru tayi kanta a k’asa tana kuma jin yanda idanun sheikh ke yawo a kan ta, ta tabbata kallon mamaki yake mata da al’ajabi, ita kam ina zata saka kanta ne yanzu? Shikenan aurenta da Asas ya gama rugujewa, ta gama samun lasisin rabuwarsu kawai, kallonta Asas yayi yace “Maah.”

A hankali ta kalleshi shi kanshi wata kunyarshi take ji, a sanyaye yace “Muje ko?”

Da ido ta amsa da “To.” A hankali ta yunk’ura ta mik’e tsaye tare da Hafsat, Eesha ce tace “Gaskiya tonton ka sake kawo mana aunty, ko ruwa fa bata sha ba.”

Murmushi ya mata yace “Ki shirya duk randa kike so saina kaiki wurinta.”

Da farin ciki tace “Yawwa tonton nagode, zan tambayi Abie sai na je.”

Kallon Eesha Hafsat tayi da ido ta mata alama, amsawa tayi tare da juyawa ta shiga d’akin uwar, jim kad’an ta fito da tsaraba ita ma ta mik’awa Asas tace “Tonton inji Mamie ka bawa aunty Mimi.”

Karb’a yayi yana fad’in “Mutanen nan kirkinku kad’an ne fa, babu wanda ya tab’a bani wata leda sai yau da na zo da bak’uwa.”

Hararanshi Hafsat tayi tace “Idan ka ji haushi mana ka daina zuwa kai kad’ai.”

Hannu ya saka aljihu yana lalubar wayarshi dake k’ara yana fad’in “Dole ai, daga yanzu tare zamu dinga zuwa.”

D’ora wayar yayi a kunne, daga yanda ya amsa wayar zaka san wani abu ya faru na tashin hankali, hakan yasa yana kashe wayar hankali a tashe ya juyo ya kalli Mimi yace “Mimi akwai matsala, masu min gyara gida ne wallahi wani wai ya samu mummunan rauni, zan wuce asibitin ne yanzu na ganshi, zaki bini muje?”

Sak’e tayi tare da tuna maganar Abbanta, a haankali ta girgiza kai da k’yar a karo na farko tun bayan fitowar sheikh tace “Gaskiya Abba ya hana, yace na koma gida kawai.”

“Hummmm!” Suka ji sheikh ya fad’a daga bayansu, kallonshi Asas yayi yace “Sheikh mi ye abun yi yanzu, suna buk’atar kud’i a asibitin wallahi da gaggawa, gashi ita kuma bata so tati dare.”

A hankali ya shiga takowa hakan ya haddasa fad’uwar gabanta sosai, jikinta har wata rawa ya d’auka saboda jin yana kusantota, saida ya tsaya inda yake hangen fuskarta kafin yace ” *Zan mayar da ita gida* idan Abbanta zai amince, dama yanzu can unguwar zan tafi.”

Da farin ciki Asas ya rumgumeshi kafin ya kalli Mimi da take jin kamar tace “Mutuwa.” Ita kuma ta amsa mata yace “Maah, na yarda dashi, kiyi hak’uri kuje tare kinji, insha’Allah komai dare na dawo zan sameki a gida na fad’awa su Abba abinda ya faru.”

Idonta taf da hawaye ta kalleshi tace “…

*Alhamdulillah*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *