MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 6 Na Samira Harouna

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 6

Na Samira Harouna


👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨


                   *NA*



_SAMIRA HAROUNA_



       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *’YAN AMANA TA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_



                    *21*



“Mimi dan Allah ki tafi gida kinji, karki fahimceni ba daidai ba, ni ubane dole na so ganin ‘ya’yana cikin kykyawan tarbiyar da za’a yi misali dasu, idan da hali dan Allah ki fita a harkar Asma’u, bana son k’awancenki da ita ko kad’an, dan in na bari kuka ci gaba da k’awance to ita ma tarbiyarta zata iya samun matsala, kuyi hak’uri kinji.”

Yana gama fad’a ya sa kai ya bar gidan da sauri, Mimi data kasa tashi tana d’ora kalamanshi a mizani tana basu kyakyawan muhalli tana son ta tantance me yake nufi, bata samu sahihiyar amsar da take buk’ata ba Sahura ta fizgi hannunta da k’arfi suka fita a gidan tana fad’in “Aikin banza kawai, ka raba k’awancen mana sai me, da me take k’aruwarta dashi da yanzu hakan zai zamar mata illa? Mtssssss! Kawai mutane baku da lissafi kudai jiran tab’i kuke kuce dama kunyi zaton haka.”


Suna shiga gida Mimi da gudu ta fad’a d’aki tana fashewa da kuka, da kallo mama da Shapi’a suka bita sai Shapi’a ce tace “Lafiya? Me aka mata?”


Tsaki ta kuma yi tana zama akan tabarmar ta fad’a musu abinda ya faru, da k’yar Mama ta had’e wani mak’ulloton abu a wiyanta na bak’in ciki tare da share zancen kamar bai dameta ba.


Sun jima gida suna tattaunawa da hira ta yan uwa tsakaninsu, sai kusan la’asar suka bar gidan, suna tafiya Mama ta sameta d’aki bayan sunyi sallama, kofi ta mik’a mata tace “Shanye wannan.”


Karb’a tayi tare da kifa kanta ta shanye tas saboda zak’in da taji da kuma k’anshin karanfani, karb’an kofin mama tayi ta juya tana murmushi da mamakin yanda Mimi ta karb’i maganin nan ta shanye, duk da dai tasan akwai zak’in mazark’waila amma kuma ana jin d’and’aon sassak’en b’aure. Shi ma kuma yanzu Sahura ta bayar a dinga dafa maata tana sha zai mata maganin zafi da wanke mata dattin mara sosai kasancewarta mai son kayan da suka shafi yaji da maik’o.



                  *Sheikh*



Yau kam Allah ya nuna sun bar k’asarsu Niamey inda suka shiga air france wanda ya saukesu Paris cikin awa hud’u, taxi suka samu ta kaisu babban masauki dan huta gajiya, da kan shi ya kama musu lafiyayyen d’aki da rakiyar ma’aikacin hotel d’in suka isa d’akinsu, tare suka fad’a wanka tare da rama sallahr data kubce musu, suna idawa sukayi oder abincin da zasu iya ci, saida suka gama sun samu nutsuwa kafin sheikh ya kira Aisha da wayar daya bar mata, hira sosai suka sha da yaran har da Hajia ma wanda wurinta suke kafin suyi sallama, daga nan ganin babu lokacin sallah da zai riskesu sai suka shiga bacci a tsanake cikin kwanciyar hankali.



                 *Mimi*



Yanda ta k’urawa littafin idonta da suke taf da hawaye zaka san ba karatun take ba, tun yamma sheikh ya fad’o mata a rai, haka kawai ta samu kanta tana mai jin wata matsananciyar kunyar sake had’uwa dashi, daki-daki take tuna tun daga had’uwarsu har jiya, lallai tayi kuskuren yi mishi k’arya, me yasa tayi tunanin daga waya ne ba zasu sake had’uwa ba? Me yasa bata zama mai taka tsantsan ba? Yanzu gashi sun had’u a matsayin surukai, zata shiga cikinsu a yanda lokaci yake nunawa, shin wace irin rayuwa zatayi a cikinsu idan ta je? A hankali ta nisa tare da sauke numfashi a zuciyarta tace “Abdul Waheed ka zama mai hak’uri da manta baya kaji, dan Allah ka manta da komai ka yafe min.”


Motsin da taji yasa ta d’aga kanta ta kalli Abba da mama dake fitowaa daga d’aki, tsaye Abba yayi a kan ta tare da mik’a mata kud’i masu yawa yace “Ki tashi kije yanzu ki kai d’inkin kayanki.”


Hannu biyu tasa ta karb’a tana fad’in “Abba nagode.”


Cikin had’e fuska yace “Ke dakata ba godiya ba, minti talatin na baki ki je ki dawo, kuma ga k’aninki nan Yaseen kuje tare.”


Juyawa yayi ya kalli Yaseen yace “Kai kuma kaji da kyau, wallahi karka yarda ta baka tsoro ko ta zare maka ido tayi wani wajen, umarnina ne wannan dan haka kar ka bari ta firgita ka, ka tabbatar ka saka k’afarka a duk inda ta saka ta ta k’afar, ka ji da kyau?”


Jinjina kai yayi yace “Eh Abba.”


Wani irin babbakewa taji zuciyarta na yi na rad’ad’i da zafin rasa yardar iyayenta, shikenan ta b’arar da kimarta a wajensu, sun daina yarda da ita kenan har abada? Mik’ewa tayi tana sakin murmushin da mai ido ‘a gani zaka san kuka ne take dannewa, a kwana uku kawai idonta har sunyi fari fat, fuskarta kanta ta canza kamar ba Mimi sarauniyar adon nan ba. D’aki ta shiga ta d’auko wanda zata fara dasu ta fito, jiki a sanyaye suka kama hanya ita da Yaseen suka fita, Abba ma fita yayi zuwa masallaci dan lokacin sallah isha’i ya matso.


Hawayen da take tafe tana sharewa ya saka Yaseen kallonta yace “Mimi ki daina kuka kinji, Abba zai yafe miki kawai yayi hushi ne.”


Saida ta sake share hawaye ta ja majina tace “Na sani Yaseen, amma dole nayi kuka saboda yanda nake ji a zuciyata, ka duba kaga yanda su Abba suka sauya min gaba d’aya.”


Matsawa yayi kusanta sosai ya d’aga kai yana kallonta yace “Kiyi hak’uri kinji, bana son ganin kina kuka, kuma jiya da yaya Asas ya zo yace na fad’a mishi idan baki daina kuka ba.”


Share hawaye ta sake yi tace “Shikenan na daina, karka fad’a masa kaji.”


Da haka suka isa bakin titi ta samu taxi, duk da ba nesa bane sosai amma lokacin da Abba ya bata ba zai isheta ta tafi a k’afa ta dawo ba tare data sab’a ba, suna zuwa ana ta sallah isha’i a masalatai, cikin sanayya sosai suka gaisa da mai d’inkin har yana fad’in “Mimi manyan duniya kwana biyu ina aka shige? Nasan dai ba kya wata d’aya baki yi sabon d’inki ba, amma wannan karan naga har an share wata d’aya na biyu ya ci rabi, sai na fara tunanin ko aure kikayi.”


D’an murmushin yak’e tayi cikin muryarta mai kama da wacce tayi mura tace “Banyi aure ba amma dai na kusa, dan yanzu ma kayan bikina na kawo maka.”


Dariya yayi yace “Haba ko da na ce, ni kam wannan wane babban yaro ne haka Mimi? Wai kinsan da ranarki ta k’arshe a shagon nan kina fita wani Alhaji ya shigo yana tambayar wacece ke.”


Cikin son kawar da zancen tace “Allah sarki, gasu nan kayan ina fatan dai zan samu a kan lokaci.”


Kallonta yayi da mamaki yace “Mimi lafiyarki kuwa? Ko an miki wanka da ruwan lalle ne? A sanina dake rik’e k’ugu kike yi ki nunani da yatsa ki ce idan ban gama kika dawo sai kin wareni na zama zakka a cikin zarma.”


Yar dariya tayi tana girgiza kai tace “Can ma ai k’uruciya ce.”


Girgiza kai yayi yace “Ban yarda ba.” Yaseen ya kalla yace “K’ane na wanene mijin da zata aura?”


Cikin murmushi Yaseen yace “Sunanshi Ashraf.”


Cikin zolaya yace “Amma dai ustaz ne ko?”


Girgiza kai yayi yace “A’a, amma dai k’annin sheikh Abdul Waheed ne.”


Zaro ido yayi kamar zasu fad’i k’asa ya d’auki ledar data aje yana fad’in “Ahh! An gama, Mimi bar d’inkinki an wuce wurin kawai, yanzu zazzago min yan uwan nima na soka aljihu.”


Mimi dai banda murmushi babu abinda take yi, saida ya nuna mata sabbin d’inkuna a wayarshi ta zab’a kafin sukayi ciniki ta biyashi ta bar shagon da zuwan zata dawo nan da sati biyu kamar yanda ya mata alk’awari.


Har ta tsaya dan tare taxi sai kuma Yaseen yace “Haba Mimi mu tafi k’asa dan Allah, ni bana son shiga taxi nan da can kawai.”


Kallonshi tayi tace “Ba zaka gaji ba?” Dariya yayi yace “Gajiyar me? Baki ga tare da Abba har saï muje masallacin kaddafi sauraren wa’azin sheikh ba.”


Numfashi kawai ta sauke tare da rik’o hannunshi suka shiga duba titi dan su tsallaka, da k’yar suka tsallaka suka d’auki hanyar komawa gida, suna tafe suna hira dashi jefi jefi, yana so ya k’wace hannunshi dan shi dai ba yaro ba, duka shekara uku ce tsakaninsu dan kaf Mimi shekararta *goma sha bakwai* ne a duniya, hakan yasa wani abun idan tayi shi har da wauta a ciki da zallar haukar k’uruciya, sam k’in sakin hannunshi tayi har suka kusanto unguwarsu.


Da gudun tsiya ya sha gabansu da motar ya ci birki, take gabanta ya shiga luguden daka dan in akwai wanda ta fi tsana ma a cikin tarikicenta to Muttak’a ne, tsaye tayi sunaa kallo ya fito yana washe mata baki, kallonta yayi ya kalli Yaseen, cike da rashin sanin darajar d’an adam da mahimmancinsu gareta yasa hannu ya shafi kan Yaseen yana fad’in “Kai me sunanka? Wannan kai haka?”


Da k’arfi cikin jin zafi ta buge hannunshi ta nunashi da kakkauren yatsanta tace “Karka sake tab’ashi, wai ke me yake damunka ne?”


“Sonki.” Ya fad’a yana kallonta kafin yace “Ranar na zo gidanku ai muka had’e da babanki, bai fad’a miki sak’o na bane? Me yasa ina kiranki ba kya d’agawa.”


Wani wawan tsaki cikin takaicin rashin girmama mata iyaye tace “Ban yi mamaki ba, ni nasan dama wani jakin ne ya jaza min sababi a gidanmu.”


Tsaki tayi ta kama hannun Yaseen zata wuce ya sake tare gabanta yana fad’in “Ke ni ne jakin?”


A harzuk’e tace “E kai d’in, an fad’a da abinda zakayi ne?”


Wani sakaran murmushi yayi ya sha wani d’an iskan sajenshi yace “Ba komai yarinya, soyayya ta jawo haka, yanzu fad’a min me yasa wai ba kya d’aga wayata ne?”


Kai tsaye tace “Saboda zanyi aure.” A firgice ya waro idonshi a kan fuskarta yace “Me! Aure fa kika ce?”


“Eh.” Ta fad’a tana yatsina fuska tace “Ko da matsala ne?”


Gyara tsayuwa yayi yace “Babba ma Mimi, kinga fad’a min gaskiya?”


Gyara tsayuwa tayi ita ma tace “Wallahi gaskiya nake fad’a maka, yanzu haka ma daga kan d’inki nake na shigar biki na, aure zanyi da wanda ya dace dani.”


Girgiza kai yayi tare da sunkuyar da kanshi, ya d’an jima kafin ya d’ago ya kalleta ba alamar wasa yace “Mimi, na fad’a miki a baya cewa idan har ban sameki ba babu wani d’an iskan da zai sameki, wallahi wallahi Mimi idan na rasaki kowa ma saidai ya rasaki.”


Cikin rashin tsoro tace “Me zaka min? Kasheni? To bismillah kasheni Muttaka, idan ka min haka ni ka hutar dani dakon tunanin abinda ke neman lalata min rayuwata, amma ka sani hakk’i’a da alhakina zasu rataya a wuyanka ne.”


Sama da k’asa ta harareshi zata wuce ya rik’e hannunta gam, jujjuya hannun ta shiga yi tana son k’wacewa amma ya rik’e jim a hannunshi, had’e fuska ya sake yi sosai cikin dakakkiyar murya yace “Na rantse miki da Allah indai ina raye babu wanda zai sameki Mimi, ko dai ki aureni hankalinki ya kwanta, ko kuma ki ci gaba da shirye shiryen bikinki da wani amma fa tabbas ba za’a d’aura auren ba.”


Cikin tsiwa da haushin rik’e mata hannu tace “Insha’Allahu zaka ga d’aurin aurena da mutumin da bakayi zato ba, sunanshi kawai zaka ji ya jijjigaka dan ko kusa dashi ka tsaya sai kayi fitsari a wandonka, kallon fuskarshi kula yafi k’arfin idaniyar mashayi kamar ka, kusa dashi ma idan ka tsaya sai zuciyarka ta buga tsabar tsoro da kwarjinin *mijina*.”


Sakin hannunta yayi yace “Shikenan zaki gani kuwa, ba dai ni kika wa haka ba saboda nace ina sonki? Wallahi ko a haukace sai kin zauna dani, banza ‘yar k’ananan mutane.”


Juyawa yayi a fusace Mimi kam takaicin an tab’o iyayenta yasa ta duk’awa ta kwashi tsakuwa ta watsa mishi cikin k’arajin murya tana fad’in “Kai ne banza d’an k’ananan mutane, mashayi da baisan ciwon kanshi ba, kai baka san miye soyayya ba ma bare har ka samu wacce zata so ka, banza alade kawai.”


Da matsiyacin mamaki ya juyo ya kalleta, takowa yayi a hassale yana zuwa ya d’aga sangamemen hannunshi ya kasheta da mari yana fad’in “Ni ne banza alade? Ni ne aladen? Bari na nuna miki abinda dabba irina take aikatawa.”


Yanda ta fad’i k’asa ne yasa shi yunk’urin fad’awa kan ta, cikin k’arfin hali Yaseen ya jawo rigar Muttak’a yayi baya dashi da k’arfin da Allah ya hore mishi, yana tangal tangal kamar zai fad’i ya kalli Yaseen, cikin zafin nama ya sake kawo mata hari, durk’usawa yayi duka gwiwoyinshi k’asa ya shiga kiciniyar rik’e hannayenta da take kai mishi duka dasu. 


Cike da jarumtar data samo asali a jinin yan uwantaka, cike da rashin tsoro da kuma yarda da cewa Allah ya bashi makaminshi Yaseen yayi kukan kura ya bugawa Muttak’a faffad’an kanshi. Yanda abun ya zo a bazata yasa Muttak’a jin wani gummmmmmm! Cikin kanshi, duk yanda ya so ya bud’e ido kasawa yayi saboda gaba d’aya kanshi kamar ba’a jikinshi yake ba, suna ganin ya fad’i kwance a wuri dafe da kai yana mirginawa Yaseen ya kama hannunta ta mik’e da sauri da gudu gudu suka barshi nan wurin, saida suka kai daf da gida ta kama hannunshi ta durk’usa tana sauke numfashi, kallon hannunta yayi dake ta rawa yace “Mimi ba zan fad’a musu ba, nasan abinda zaki rok’a kenan, amma kiyi k’ok’ari ki dakatar da rawar da jikin naki ke yi, zasu iya ganewa.”


Ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina kai, shafa kanshi tayi tace “Baka ji ciwo ba?”


Girgiza kai yayi yace “Ai babu abinda na ji.”


Murmushi tayi tace “Lallai kaine magajin Abba, tunda gashi ka ceceni.”


Murmushi yayi shi ma yace “Kullum fa muka ji fad’anki a unguwar nan akan mu ne ko iyayenmu, ni ma zan tsaya miki babu abinda zai sameki.”


Murmushi tayi ta shafa fuskarshi tace “Nagode k’anena.”


Mik’ewa tayi suka shiga gidan da sallama, Abba na tsaye ya maida hannaye baya alamar su yake jira, ko sallamar babu wanda ya amsa Abba yace “Me ya tsaidaku har minti shida ya hau kai?”


Kallon Yaseen tayi da yayi saurin cewa “Abba k’asa muka dawo, har zata tare mana taxi na ce mu taho k’asa.”


Harara ya dalla mishi hakan yasa Mimi durk’usawa tace “Wallahi Ab…” Hannu ya d’aga mata yace “Dakata, bana buk’atar rantsuwarki.”


Hanyar fita ya nufa yana fad’in “Gobe ku k’ara.”


Suna ganin fitarshi Mimi ta mik’e ta shiga d’aki ta cire hijabinta ta d’an kwanta a kan gado ta shiga dawo da had’uwarsu da Muttaka baya, tsoro ne fal taji ya cika mata zuciya da tunanin abinda zai iya yi mata, d’an k’waya kam tasan zaiyi abinda ya fad’a, saidai me zaiyi? Kasheta zaiyi ko fyad’e zai mata? Idan kisan ne ta wace hanya zai kasheta? Idan fyaden ne wani iri zai mata? Da wannan firgitaccen tunanin har bacci ya d’auketa a kan gadon.




🥰 *Comment masha’Allah, shiyasa kuka sameni dayawa.*🥰




*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *22*

Saida ta wayi gari ne ta lura da illar da marin Muttak’a ta haifar mata, dan fuskarta kumbura tayi ga kuma shatin yatsunsu kwance a kai, haka tayi ta fama da hijabi har ta shiga wanka ta fito ta shirya a sauk’ak’e, Mama kam dama tun jiya da tayi baccin ta fahimta shiru ne ta mata, Abba kuma da safen daya gani sai hankalinshi ya tashi sosai, amma bai nuna ba saida ya fita daga gidan sai kuma ya lek’o ya kira Yaseen, da ladabi ya amsa mishi yayi tsaye yana jiran yaji me zai ce, cikin magiya ya kama hannunshi yace “Yaseen, kaga dai jiya tare kuka fita da uwata ko? Kuma kaga ina tafiya da ku wurin karatun malam, kuna jin yana yawan fad’a k’arya ba kyau, sannan kaga k’aryar da uwata ta mana ne ya sa mukayi hushi da ita, indai baka so kai ma nayi hushi da kai to ka fad’a min abinda ya faru bayan fitarku jiya?”

Tsatsareshi yayi da ido yana tunanin me zai fad’a, baya so dai wani wulak’ancin ya sake biyowa baya akan yar uwarshi, dan haka ya gyara tsayuwa yace “Abba, ai tare muka tafi ko? To wani ne muka had’u dashi bamu san shi ba, saiya tsaidata zai mata magana, amma kuma sai yake tab’a kaina yana min izgilanci, shine ta ji haushi ta buge hannunshi a kaina ta ce mishi jaki, shi kuma yace mata banza yar wadanni, shi ne ta sake ce mishi banza alade sai yaji haushi sosai ya mareta.”

Sakin hannunshi Abba yayi yana binshi da kallo yace “Ka tabbatar?”

Jinjina kai yayi yace “Eh Abba.”

Jinjina kai yayi tare da shigowa cikin gidan Yaseen ya biyo bayanshi, Mimi zata shiga d’aki kenan taji yace “Ke uwata.”

Tsayawa tayi tare da durk’usawa tana kallonshi gabanta na fad’uwa, cikin fad’a yace “A garin nan da ma kewayenshi, duk uban da ya sake cin zarafinki a kan wulak’anta miki iyayenki to ni ki fad’a min, ba a iya k’asar nan ba wallahi zan iya tsayawa da mutum a kowace kotun shari’a.”

Juyawa yayi zai fita mama tace “Lafiya malam? Wani abu ne ya faru kuma?”

A hassale ya juyo yace “Maganar banza, ya za’a mayar min da yarinya kamar wata mahaukaciya ko marar gata, ko wane tsinannen albarka da baisan darajar mutum ba sai ya dinga tsokanar hallitarmu a gabanta, idan tayi magana har a dinga tab’a min lafiyar yarinya, to na daina hak’ura daga yau, duk wanda yake son mu zauna lafiya a shirye nake, wanda ke buk’atar daru ma a shirye nake da shi.”

Juyawa yayi ya fita a gidan Mama na kallon Yaseen tace “Me akayi?”

Maimaita mata abinda ya fad’awa Abba yayi, hakan ya sata satar kallon Mimi dake kallonshi da mamakin lauyar da yayi, saidai kuma tana farin ciki akan abonda Abba ya fad’a, ko ba komai ya nuna zai hak’ura nan gaba kad’an.

                   *Asas*

A gaggauce yake shiri yana kallon wayarshi dake kan gado, sosai hoton da aka had’a shi da ita ya birgeshi, dama an ce lamarin duniya baya b’uya, yayi mamakin ta inda hoton ya fito har aka had’ashi da ita da kayan lefenta, sosai yaga dacewarshi da ita sunyi machtin sosai, agogo ya d’auka zai d’aura sai kuma yaji cikinshi ya tsamuka mishi kamar yanda ya saba mishi, da sauri ya aje agogon tare da zaunawa bakin gadon ya rik’e ciki yana fad’in “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!”

Shiru yyi jin kamar da sauk’i, sai kuma ya sake murd’a mishi da tsananin azaba, a tare ya durk’ushe k’asa yana neman yin sujada yana wash wash cikinshi, da iya k’arfinshi yake k’wala kiran sunan Hajia amma tayi nisa, b’angarenshi zuwa nata da yar tazara kam, murk’ususu ya dinga yi a d’akin baccin nashi ga masifar gumin da yake idonshi har sunyi jajir.

Hannu ya kai yana son ya d’auki wayarshi yayi kira amma ya kasa lalabota akan gadon, a hankali jikinshi ya fara yin sanyi ya fara lumshe ido yana cije leb’enshi, numfashinsji na yin sama da k’yar kamar zai suma ko ya mutu, a daidai lokacin Sadeeq ya sallamo d’akin na shi yana fad’in “Asas zan maka iskanci fa wallahi, kai kasan sauri nake muna da wurin zuwa, ya zaka…”

Da sauri ya k’araso ya durk’ushe yana kiran “Asas, lafiya? Me ya sameka?”

Da k’yar Asas ya d’an mirgina yayi kwance a k’asa yana sake matse cikinshi, da sauri ya tallabeshi suka mik’e yana fad’in “Muje asibiti, cikin ne ko?”

Durk’ushewa ya sakeyi yana fad’in “Bâ…ba zan.”

Bai iya magana ba sai komawa da yayi ya kwanta a k’asa, da sauri Sadeeq ya fita yana hango mai gadi ya k’wala masa kira, da sauri ya taho suka koma d’akin, tare suka tallaboshi suka fita dashi, saida ya suka sakashi mota ya kalli mai gadi yace “Ka kira Hajia sai mu tafi tare.”

Da gudu ya juya yayi b’angarenta yana ta sallalami, jim kad’an kam sai gashi tare da Hajia har ta fara kuka da Salamatu a bayanta tana bar mata sallahun ta kula da yaran idan sun dawo daga makaranta gyalenta a hannu, baya ta zauna inda Asas yake suka bar gidan zuwa asibiti.

Da isarsu aka karb’eshi kuma kamar kullum taimakon da yake kwantar masa da ciwon aka fara basho kafin a k’ara masa ruwa ya samu nauyayyen bacci. Lokacin kad’ai Hajia ta samu damar kiran sheikh ta fad’a masa halin da ake ciki, a sanyaye ya shiga fad’in “Hajia insha’Allah Asas ya kuma samun sauk’i, yanzu haka ina neman k’wararran likita a nan da zai iya bamu randez vous na had’uwa dashi sai na zo da Asas ko da kuwa hakan na nufin a d’aga bikinshi ne.”

Cikin muryar kuka tace “Sheikh ko dai za’a dakatar da bikin nan ne? Gaskiya hankalina yafi karkata kan lafiyarshi, idan ba damuwa a barshi ya samu lafiya mana.”

A tsanake yace “A’a Hajia, a kullum Asas yana fad’in yana ji a jikinshi aurenshi shi ne silar warkewarshi, watak’ila Allah ya nuna mishi ne a ilhama, muyi k’ok’ari muga an gama bikin nan lafiya, ko da anyi auren ne zai iya tafiya ai.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Shikenan sheikh yanda ka ce, Allah ya bashi lafiya.”

“Ameen Hajiarmu.” Ya fad’a a tausashe kafin ya d’ora da “Zan sake kira anjima.”

“To shikenan, sai anjima.” Suka datse kiran a haka suna mai mishi fatan samun lafiya.

                *Washe gari*

Ko da Abba ya shigo da yamma yake fad’a ma mama ya samu labarin Asas na kwance asibiti har lokacin, dan haka yayi alwala zai fita sallah magriba daga nan yaje ya ganshi, har yana fad’in “Ba dan uwata ta zama wata kala ba ai ita ma ya ci taje ta dubashi, amma ba komai zan wakilceta.”

Murmushi mama tayi tace “A gaidashi da jiki, Allah ya bashi lafiya.”

“Ameen.” Ya fad’a yana fita daga gidan, Mimi na d’aki tana jin komai dake wakana, saida taji kamar ta nemi alfarmar taje ta ganshi, dan kwanan baya ya fara labarta mata ciwon nan dake sakashi suma idan ya taso, amma babu halin zuwa ganinshi da kanta dan haka ta bishi da addu’ar samun sauk’i.

                     *Asibiti*

Cikin dattako yayi sallama da muryarshi da bata da maraba data yara, duk zubawa k’ofar ido sukayi dan ganin me shigowa, da sauri k’anin Hajia wanda shi yasan kowanene dan tare suka nemo auren Mimi ya mik’e da fara’a yana fad’in “Kai malam Adam, kai ne tafe?”

Cike da murnan yanda ya karb’eshi ya bashi hannu sukayi musabiha yana fad’in “Ni ne, anwuni lafiya.”

“Lafiya lau, bismillah zauna.” Ya fad’a yana nuna masa kujerar daya mik’e, d’an zaunawa yayi yana kallon Asas dake bacci da k’arin ruwa, a hankali kuma ya kalli Hajia dake binshi da kallo yace “Ina wuni.”

Kafin tayi magana k’aninta yace “Maryama ai shine surukin Ashraf, mahaifin yarinyar nan takwararki.” 

Da k’yar ta k’ak’aro mirmushi a fuskarta tace “Ayyah! Ina wuni? An zo lafiya?”

Murmushi yayi shi ma yace “Lafiya lau, ya mai jikin?”

“Jiki da sauk’i, angode ma Allah.”

Sake kallon Asas yayi yace “Allah k’ara afuwa.”

Sai lokacin Aisha dake zaune sun kawo abinci tare da dreba tace “Ina wuni Abba.”

Da fara’a ya kalleta yace “Lafiya lau yarinya, kina lafiya?”

“Lafiya lau.” Ta fad’a cike da alhinin halin da kawunta yake ciki, k’anin Hajia ne yayi murmushi yace “Jika ce ga ita Maryama, ‘yar sheikh ce ta fari, sunanta Aisha.”

Fad’ad’a fara’arshi yayi yace “To to masha’Allah, ah abu yayi kyau.”

Kallon Aisha yayi yace “Allah ya shi albarka, malam d’in ma kwana biyu na ji shiru ko ba’a gari?”

Da murmushi Hajia tace “Baya nan ai, sun tafi Paris amma sun kusa dawowa insha’Allah.”

“Allah sarki, Allah ya kawosu lafiya.” Ya fad’a da fara’a, jim kad’an kuma saiya mik’e yana fad’in “Alhaji *Saleh* ni zan wuce, dama na samu labarin bai da lafiya ne na zo na gaisheshi, ita ma yarinyar da mahaifiyarta duk sun ce a gaisheshi da jiki.”

Cike da jin har ranta an kula da d’anta tayi murmushi tace “Har zaka koma? To angode Allah ya saka, a gaishesu da kyau.”

Saleh kuma hannu ya bashi suka sake musabaha yana fad’in “Idan ya farka za’a sanar mishi.”

Saida ya rakashi har k’ofar fita kafin ya dawo, hakan y’a ma Abba dad’i sosai da bai ga k’yama ko izgilanci a tare da Hajia ba, hakan ba k’aramin kwanciyar hankali ya haifar masa ba. Ita ma kanta Hajia wannan dubiya da kuma ganin shi ya tabbatar mata dattijo ne na arziki ba tsoho ba, dan haka sai taji wani shauk’in auren Asas da Mimi tare da fatan tabbatar lafiyar da yake ikrarin zai samu idan yayi aure.

                 *A gurguje*

Tuni jikinshi yayi sauk’i har ma sun ci gaba da shirye shirye, komai yana tafiya musu daidai dan komai a walale yake, sheikh ma sun gama hutunsu sun dawo, saidai a ranar da suka shigo a daren kuma ya d’auki hanyar Maradi sakammakon wa’azi na k’asa da k’asa da ake yi duk shekara, hakan yasa Hafsat mayar da hankalinta ita ma kan bikin.

Mimi kam bata ji dad’i ko kad’an, ana sabgar bikinta amma babu k’awarta kuma aminiyarta Asma’u, daga Jamila sai su Salma kawai ke yawan shige da fice, hakan yasa ma yanzu haka daya rage sati d’aya Sahura ta zo gidan kawowa Mama sabuwar katifar data siya ta kalli Sahura kamar zatayi kuka tace “Aunty Dan Allah idan kika koma gida ki turo min Zeinaba, ina so ta zauna a nan har a gama bikin nan.”

Da mamaki Sahura ta kalleta tace “Zeinaba kuma? Ke kuwa Mimi me zata zo tayi a cikin ‘yan mata kamarku?”

Tsuke fuska tayi tace “Aunty ni dai dan Allah ki turo min ita, idan ba haka ba wallahi zan fasa auren ma.”

Zaro ido tayi tace “Fasa aure saboda ban turo ta ba Mimi?”

Cikin shagwab’a tace “Eh mana, aunty ki duba fa ki gani dan Allah duk yan uwana babu wanda ya zo inda nake, bansan me yasa suke min haka ba, har gayyatarsu nayi amma da sun zo zasu dinga yin baya baya.”

Ajiyar zuciya Sahuta ta sauke tace “Maganar gaskiya Mimi abinda yasa kika ga suna ja baya saboda kinga ke da k’awayenki duk dogaye ne, yan uwanki kuma tsaranki duk kusan hallitarsu irin ta mu ce, sannan k’awayenki duk wayayyi ne yan boko, shiyasa suke ja baya a lamarin.”

Kamar zata fashe da kuka tace “Yanzu aunty saboda hallitarsu sai su k’i zuwa inda nake, ni fa tun farko ban b’oye ma Asas daga ina na fito ba, sannan danginshi ma sun san komai dan haka dole zasu ga mutane kala biyu, aunty Sahura, wallahi na rantse da Allah zan iya fasa auren nan idan aka ci min mutumcin yan uwa.”

Mik’ewa tayi zata shiga d’aki tace “Kuma a turo min yan uwana, ina so na gansu kewaye dani suna kai da kawo a sabgar bikina, dan ni abun kunya ne ma gareni ace ba’a ga gajera ba a cikin yan mata, ni yar halak ce kuma ba butulu ba.”

Da kallo kawai suka bita har ta shige d’akin, murmushi Sahura tayi tace “Mimi kenan, ita dai ba ruwanta da k’yamar mutane.”

Tab’e baki mama tayi ba tace komai ba, haka suka ci gaba da tattaunawarsu kafin Sahura ta bar gidan.

Saida tayi sallah magriba ta shirya tare da Yaseen zasu tafi karb’an d’inki, a k’ofar fita suka had’e da Maimuna ta shigo gidan, gaisawa sukayi sosai kafin ta shiga ciki dan tunda aurenta ya matso take zuwa suna yan shawarwari da Mama, fita sukayi ita kuma a daidai k’ofar suka had’e da Asma’u, cak duk suka tsaya suna kallon juna, tunda abun nan ya faru ko sautin muryar juna basu ji ba bare ganin juna, cike da murna Mimi ta fashe da kuka ta ruga a guje ta fad’a jikin Asma’u, ita ma kukan ta saka tana k’ara rumgumeta.

Cike da k’aunar juna Mimi ke fad’in “Asma’u me yasa zaki bari su rabamu? Kinsan yanda nayi kewarki kuwa? Babu masifa babu fad’anki bare nusar dani daidai da ba daidai ba.”

D’agowa tayi tana sake fad’in “Bikina sati d’aya ya rage, amma Asma’u ko ki lek’o ki ganni kin shareni kawai.”

Cikin kuka ta shiga girgiza kai tana fad’in “Ba shareki nayi ba Mimi, Abbana ne ya hanani shiga gidanku, ya ce ko bisa hanya bai yarda na kulaki ba.”

Jinjina kai tayi tace “Na sani Asma’u, dan nima na zo gidan ya hanani shiga na ganki.”

Hannunta ta kamo jim ta jimk’e tana fad’in “Dan Allah Asma’u ki zo ayi hidimar bikina dake, idan baki zo ba ko an d’aura auren ba zan yarda a kaini gidan ba.”

D’an murmushi tayi tace “Na miki alk’awari Mimi ko da satar hanya ne na zo gidanku.”

Da sauri tace “A’a! Banda satar hanyar Asma’u, ba zan so ki jefa kanki a halin dana jefa kaina ba, a dalilin abubuwan dana aikata har yanzu gidanmu bana sakewa, iyayena sun daina sakin jikinsu dani kamar bak’i muke, duk yanda na motsa sai mama ta kalli kalar motsin da nayi, idan na sauke numfashi saita kula da wane iri ne na sauke, uwa uba ace na fita waje, tsaf take cajeni taga miye a jikina.”

Wani murmushi mai kama da kuka tayi tace “Ranar ma tsaf tasa na kwab’e kayana ta dubani saboda kawai Asas ya zo da daddare munyi hira ya tafi.”

Fashewa tayi da kuka mai cin rai, share mata hawayen Asma’u ta shiga yi tana fad’in “Kiyi hak’uri ki daina kuka dan Allah, komai zai wuce kinji daina kuka, kinga ynzu…”

Cak ta tsaya saboda jin Abbanta ya fito daga gida yana fad’in “Asma’u.”

Da sauri suka kalleshi suna rarraba ido, a tsawace ya kauce daga bakin k’ofar yana fad’in “Maza shiga ciki, ban hanaki tsayawa da ita ba.”

Da sauri Asma’u ta taka zata shiga Mimi ta rik’e hijabinta gam, takawa tayi saida taje gabanshi ta durk’usa, kamar zata rik’e k’afarshi tana kuka tace “Abba dan Allah na rok’eka ka taimaka ka bar Asma’u ta halarci bikina, Abba ban da wata k’awa sama da ita, ita ce aminiyata da ita nayi wasar k’asana, ita ce take da zarrar fad’a min gaskiya gaba da gaba ba tare da tsoro ko shakku ba, bani da wacce take so na sama da ita a duniyar nan a cikin mutanen da ba iyayena ba, dan Allah dan Annabi karka raba k’awance da ita dan ni ce mai k’aruwa da hakan, ita take d’orani a hanya take nuna min bâ daidai ba. Wallahi ban tab’a k’ok’arin kama hannun Asma’u ba na kaita a hanyar da zata halaka ba, na maka alk’awari Abba Asma’u zata ci gaba da zama a kamilalliyarta har ka damk’ata a hannun mijin daya dace.”

Shiru tayi tana ci gaba da kuka ba tare data saki hijabin Asma’u ba, tabbas jikinsa yayi sanyi da abinda ta fad’a, hakan yasa ka shi jinjina kai yace “Shikenan tashi daina kukan?”

Girgiza kai tayi tace “Ba zan tashi ba Abba har sai ka hak’ura.”

A hankali yace “Na hak’ura mana, tashi tsaye.”

Mik’ewa tayi tana kallonshi, d’orawa yayi da “Na amince ku ci gaba da shagulgulanku, amma ki cika min alkkawarin da kika d’auka, bana so wani abu marar kyau ya faru daku kinji.”

Jinjina kai tayi tace “Insha’Allah Abba, nagode sosai.”

Murmushi yayi yace “Ba komai, Allah ya muku albarka.”

Da Murmushi ita ma tace “Ameen Abba.” Sakin Hijabin Asma’u tayi ta juya tana fad’in “Sai gobe, karb’o d’inki zamu je.”

Abban Asma’u ne yace “To ku tafi tare mana, ba ita ce babbar k’awa ba?”

Wata dariyar data jima batayi bane ta kubce mata tace “Ita ce Abba, ita ce.”

Da zumud’i ta sake kama hannun Asma’u ita ma Asma’u tayi ram da hijabin Mimi suka shiga takawa da k’arfinsu kamar zasiyi gudu, a baya Yaseen ya bisu shi ma yana murmushin jin dad’in ganinsu tare.

*Da safe* tana farkawa bakinta kawai ta wanke mama ta mik’a mata dahuwar tamtabarun data mata tun asuba, karb’a tayi ba musu dan duk wani abu da mama ke bata ko ci bata cewa, saidai ta mik’a mata kawai ita tasan yanda zatayi tasha ko ta ci, yanzun ma ba dan tana so ba take ci duk da dahuwar tayi, amma ba wasu isashin kaya aka saka ba, tana ci tana b’ata rai kamar za tayi amai. Tana ji su Zeinaba sukayi sallama, murmushi ta saki na jin yan uwanta sun zo inda take, tanna jin su suna gaisawa da Mama kafin tace “Ku wuce ciki ku aje kayanku.”

Da fara’a suka wuce suna sake sallama, amsawa tayi da farin ciki tana fad’in “Marasa mutumci kenan an taho?”

Dariya duk sukayi suna aje kayan hannunsu, Zeinaba irin gajerun nan ne sun fi wada tsayi kuma basu da tsayi sosai (ba wada haushi), Rauda ma bata da laifi amma Zeinaba ta fita tsayi, gaisawa suka dinga yi sosai har Mimi na fadin “Yanzu da ban nemeku ba kenan ba zaku zo ba?”

Dariya sukayi Zeinaba tace “Kin san me? Ni bana jin dad’in shiga cikin dogaye ne, sai na saké zama ‘yar duk’ul dani.”

Wani wawan tsaki taja tace “Dallah ni karku b’ata min rai, wai me yasa kuke hakane?”

K’yaci tayi tare da ci gaba da abinda take, sama sama suka dinga hira har ta sake saukowa suka ci gaba da hira, suna haka Asma’u ma ta shigo, gaisawa sukayi kafin Asma’u tace “Kinga ba zama zanyi ba, siyan ankona zan tafi yanzu saina dawo.”

Kallon Zeinaba tayi dake sun san juna tace “Zeinaba muje ki rakani mana.”

Mik’ewa tayi tana fad’in “Nawa zaki biya to?”

Dariya tayi tace “Karki damu, muje zan biya.”

Mimi ce ta kalli Asma’u tace “Asma’u dan Allah karb’i kud’i wajen Mama ki siyo min madara peak.”

Kallonta tayi tace “Me zakiyi da ita?”

Kashe mata ido tayi tace “Ina ruwanki? Sirri ne.”

Dariya duk sukayi Asma’u tace “Wato kin raina gyaran Mama ko?”

Murmushi tayi tace “Ni na fad’a miki haka? Kawai ina buk’atarta ne dan nasha.”

Girgiza kai Asma’u tayi tare da ficewa a d’akin ita da Zeinaba, tana jin sautin Asma’u sanda take tambayar Mama kud’in, da fari ta shiga zulumi na tunanin ba zata bayar bâ, amma da taji ta bata saita saki murmushi.

*Masu comment nagode, wanda basa comment ma godiya nake*😁🤝

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *23*

Sosai suke shan hirarsu ita da Rauda suna raharsu, Mama saidai ta shigo tayi wani abun ta fita tana jinsu, 09:05 Hafsat ta zo gidan tare da rakiyar Salamatu, yanda ta shigo da nutsuwa da sallama ya saka mama d’aga kai tana amsawa, masha’Allah ta fad’a a ranta saboda ganin Hafsat d’in, indai had’uwa, kyau, aji, kamala ake nema a gurin mace tabbas alamun Hafsat sun nuna mata hakan, gata jajir da ita gwanin sha’wa ta fito a bafulatanarta sak, ga bak’in hijab kuma dogon daya fito da doguwar fuskarta har k’asa.

Mik’ewa Mama tayi tana fad’in “Lale maraba, sannunku da zuwa.”

Da fara’a da girmamawa tace “Yawwa sannu Mama.”

Da fara’a ita ma tace “Sannu, ina wuni?”

“Ina wuni?” Ta fad’a a matuk’ar tausashe, saida mama ta d’auko kujera ta aje tace “Lafiya lau, anwuni lafiya?” 

A ladabce ta zauna tana sauke numfashi kafin tayi murmushi ta sake gaisheta da mutumtawa, ruwa ta kawo ta aje musu Hafsat kam saida tasha dan kar Mama ta ji ba dad’i duk da bata da k’ishin ruwa, shiru ne ya d’an biyo baya kafin Hafsat tace “Mama baki ganeni ba ko?”

Da fara’a tace “Gaskiya kam ban shaidaku ba? Dan na fara tunanin ko b’atan kai kukayi.”

Dariya Hafsat tayi ta kalli Salamatu dake k’arewa gidan kallon tsaf har zuciyarta take jin haushin wannan zab’i na mai gjdan nata Asas, sam abun bai mata ba sai take ganin kamar wannan shi ne *kaska* rab’i mai jini, matsayinshi da dukiyarshi yafi k’arfin a ce yarinyar da zai aura kenan. D’an gyaran murya Hafsat tayi hakan yasa ta maido hankalinta gareta, da ido ta mata alama hakan yasa Salamatu aje ledojin hannunta gaban Mama tana fad’in “Wannan ai ita ce yayar Alhaji Asas, uwa d’aya uba d’aya suke.”

Da fad’ad’a fara’a sosai mama tace “Masha’Allah, ko ita ce Hafsat d’in da nake ji?”

Da murmushi Hafsat tace “Ni ce mama.”

“Abu yayi kyau kam, ya su Hajiar suna lafiya?” Ta fad’a cike da kulawa, amsa mata sukayi kafin Hafsat tace “Mama dama sak’o na zo kawowa amarya, nasan kunsan babu wani shagali da za’ayi a bikin kamar yanda addini ya tsara, amma daga baya sai muka yi shawara duba da yanayin zamani da kuma ita kanta amaryar, shi ne ango yace za’ayi kamu kawai na amarya, amma fa shi ma ita da k’awayenta ban da shi da abokanshi, haka kuma kowa a dangi ma ga mai buk’ata zai iya halarta.”

Shiru mama tayi tana saurarenta tana jinjina kai, saida ta kammala kafin tace “Wannan ai ba wata matsala bace, duba da kwana nawa ya rage Mimi ta shiga a k’ark’ashin ikonku? Ko yanzu kaso mafi girma yana hannunku ai, dan haka ba wata matsala wallahi, saidai idan mahaifinta ya dawo shi ma zan sanar dashi dan yasan abinda ake ciki.”

Cike da gamsuwa da maganganun Mama Hafsat tace “Masha’Allah, mun gode sosai Mama, wannan ba matsala bane dama.”

Ledar da Salamatu ta aje gaban mama ta nuna mata tace “Wannan kayan da amarya zata saka ne ango ya turo mû dasu, insha’Allah ranar alhamis za’ayi kamun washe gari kuma d’aurin aurensu a babban masallacin juma’a.”

Cike da jin dad’i mama ta jinjina kai tace “Hakane, Allah ya nuna mana ya kai mu lokacin da alkairi.”

Cikin dariya Hafsat tace “Ina amaryar ne wai mama? Ko bata nan?”

Cike da kunya mama tace “Tana ciki kam, ai kusan wata d’aya ma kenan ta daina fita, shiga ciki tana nan.”

Mik’ewa Hafsat tayi tana fad’in “Lallai mama kina kula mana da amaryarmu, Allah ya biyaki da aljanna, wannan sai mun bayar da tukuici ai.”

Dariya mama tayi tana amsa addu’arta a zuciya tana kallo har ta shiga d’aki, Salamatu kuma na zaune tana ta yatsina fuska tana wa mama wani gani-gani, mama kam har ga Allah bata ma kula ba bare ta sa wani abu a ranta taji ba dad’i ko kuma tunani.

Mimi kam da suka kasa kunne tunda taji wacece ta d’auko hijabi ta labta ta haye gado tayi shiru, tana shigowa da sallama suka amsa mata da fara’a Mimi kuma na sinne kai k’asa, zaune tayi kusanta tana fad’in “Amaryarmu sannu? Ya hidima?”

Da d’an murmushin jin kunya tace “Alhamdulillah.”

“Masha’Allah, yanzu ma na kawo kayanki ne na kamu ranar alhamis insha’Allah.” Ta fad’a tana kallonta, k’ala ba tace ba sai ma sunkuyar da kai k’asa, cikin kulawa Hafsat ta sake fad’in “Gashi dai har kin kusa shigowa hannunmu baki sake zuwa gidana ba, na so ya kaiki ki wuni amma Allah bai nufa ba, dan zuwanki na ranar naga kuna sauri.”

Murmushi ta sake yi tace “Zan je.” Dariya Hafsat tayi tace “Yaushe kuma amayar? Kwana biyu ana uku fa zaki shiga lalle, ai k’anena ba zai yarda ki fita ko ina ba.”

Cike da kunya ta sake sinne kai tace “Zan je insha’Allah.”

Dariya ta sake yi tace “Na yarda zaki je, amma fa bayan aure.”

Murmushi tayi sosai tana rufe fuska da hijabi, cike da jin dad’in ganin Mimi ta mik’e tana bud’e jakarta, enveloppe ta fito da ita ta aje kusa da Mimi tace “Wannan angonki ne yace na baki saboda ranar kamu zasu miki anfani.”

Juyawa tayi bata jira me zata ce ba ta fita tana fad’in “Sai anjima amaryarmu, sai ranar kamu insha’Allah.”

Da kallo Mimi ta bita kafin tayi saurin kallon enveloppe d’in, zaro ido tayi ta kalli Rauda dake ta murmushi tana saurarensu tace “Rauda na shiga uku, ta bani abu ta juya ta fita, ya zanyi da mama?”

Jin su Hafsat na fita a gidan suna ban kwana yasa ta d’aukar enveloppe d’in tana fad’in “Shi ma fa na fad’a masa bana buk’atar komai daga gareshi, me yasa zai min…”

Bata kai k’arshe ba mama ta d’aga labule ta d’auko kayan da aka kawo mata, cikin rashin gaskiya da tsarguwa da kuma sabawa da sabon halin Mama na cajeta yasa ta saurin sakin enveloppe d’in ta durk’ushe tare da fad’in “Na rantse da Allah mama bansan menene a ciki ba, ita kawai ta d’auka ta bani ban tambaya ba, kuma ga Rauda ki tambayeta zata fad’a miki.”

Girgiza kai Mama tayi ta zuro k’afarta d’aya ta aje ledar tace “Miye anfanin rashin gaskiya yanzu? Gashi abinda bai kai ya kawo ba ya firgita miki nutsuwarki, me yasa mimi kika dinga yi mana k’arya? Da kina ganin yanzu haka ta faru?”

Girgiza kai tayi ta juya tana fad’in “Ko me suka baki a yanzu indai ba rok’onsu kikayi ba su suka ji suka gani zasu iya.”

Tana ganin ficewar Mama ta share yar guntuwar k’wallarta ta d’auki enveloppe d’in ta zauna bakin gado ta bud’e, wani irin fad’uwa gabanta yayi sakamakon ganin kud’i ne sababi far dasu yan jaka jaka, mayarwa tayi ta aje ta kalli Rauda tana fad’in “Nufinshi nayi lik’i da kud’in nan?”

Wani murmushi tayi kawai ta girgiza kanta ta gyara kwanciyarta akan gadon ta shiga neman bacci.

                   *05:30*

Su Salma na fita a gidan sakamakon k’aratowar magriba yasa ta d’aukar madararta a kofi data b’oye k’ark’ashin gado had’e da yar zuma a ciki da karanfani da dabino data saka Asma’u mata a gida ta kawo mata, da sauri ta kifa kai ta shanye abinta, dan a gaskiya ranar taji su Sahura na fad’in har yanzu fa maganin zahi da kuma na sanyi (infection) ne aka mata, sai shi dai na zafi yanzu haka idan tasha tana jin yana saukar mata da d’umi a jikinta har ya saka ta kama ruwa. Yanzu ma da su Zeinaba zasu fita maltina ta basu su siyo mata amma tace su b’oye kar Mama ta gani (ba’a daddara ba kenan uwata?😥). 

Asma’u na shigowa da sauri taa fad’a d’akin hankali tashe, cikin rad’a ta shiga fad’awa Mimi “Ke yanzu na ga Muttak’a a k’ofar gidan nan, ya ce wai na kiraki na fad’a masa an hanaki fita saboda aurenki ya matso, ke kinga tashin hankalin?”

Gyara zama tayi tace “Wallahi rantsuwa ya mana wai ba zaki auri wani ba shi ba, tunda har kika wulak’antashi kika yaudareshi to zaki gani.”

“Zan ga alheri.” Ta fad’a tana mik’ewa dan shiga wanka, cikin nuna damuwa Asma’u ta mik’e ita ma tace “Mimi bana son matsala fa, mutumin nan tunda ba hankaline dashi ba me zai hana ba zaki fad’awa Asas ba? Watak’ila ya mana maganinshi.”

Kallonta tayi tace “Na ce masa me? Saurayi na ne dana ci kud’insa kamar hauka shine ya ke min barazana kayi wani abu a kai?”

Tab’e baki tayi ta d’auki hijabi zata saka ta fita Asma’u tace “To ya kike so a yai? A barshi har sai wani abu ya faru marar kyau? Sannan mu sake shiga damuwa da tashin hankali.”

Dafa kafad’arta tayi tace “Ba abinda zai faru Asma’u, kwantar da hankalinki.”

Ture hannunta tayi tace “Kwantar da hankalin banza, wai me yasa kika cika taurin kai ne Mimi? Haka a baya kike fad’a min kwantar da hankali babu abinda zai faru, da nayi shiru kamar yanda kike buk’ata miye bai faru ba?”

Tsaki tayi tace “Kinga idan wani abu ya faru wallahi babu ruwana ni dai, na fad’a miki d’an giyane mutumin nan kuma yana mana rantse rantse da cin alhwashi.”

Gyara tsayuwa tayi tace “D’an giya miye baya fad’a? Rantsuwa ko ruwa zai sha sai yayi rantsuwa da alhwashin shan su alhalin gasu sa gabanshi, dan haka ba zan saka matsalarshi a kai na ba.”

Jinjina kai Asma’u tayi cike da jin haushi ta fita tana fad’in “Ke kika sani ai.”

Ganin yanda ta fita ya tabbatar mata sunyi fad’a kenan ba zasu shirya ba sai kuma gobe, girgiza kai tayi tana murmushi a ranta take ayyana irin k’aunar da Asma’u ke mata, indai zasuyi fad’a to akan wani abu da Mimi tayi ba daidai bane musamman mai barazanar cutar da ita game da lafiyarta ko kuma zai shafi mutumcinta.

                    *Sheikh*

Dake a jirgi suka shigo hakan yasa suka zo bayan magriba, tunda yasan yau asabar yasan a lokacin Hafsat tana cikin gidan a b’angaren karatu tare da matan da suke karatun dare, kai tsaye b’angarenshi ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya ya nufi masallaci, saida sukayi sallah isha’i sukayi karatunsu kafin duk da gajiya kam kafin suka tashi k’arfe tara. Yana shigowa gidan a falo ya sameta tare da Aisha da wata budurwa mai d’inkinsu, gaisheshi tayi da ladabi ya amsa haka ma Aisha kafin ya wuce ciki, mik’ewa tayi a sanyaye ta kalli Aisha tace “Ki duba kayan kiga idan sunyi sai ki bata kud’in, idan akwai wanda bai yi ba saiki bata ta koma dashi a gyara.”

Kallon budurwar tayi tace “Dan na sanki da shiririta wani lokacin.”

Dariya tayi tace “Insha’Allahu ma anti daidai wannan Mamar Aisha.”

“Allah yasa.” Ta fad’a tana murmushi ta shige falon yallab’ai, a tausashe a sanyaye ta furta “Assalama alaika sheikh na wa.”

Tsura mata ido yayi har ta k’araso sannan yace “Wa’alaiki salam *Manga* ta wa.”

Murmushi tayi tare da zama kusanshi tace “Sannu da zuwa uban gidana, an zo lafiya?”

Saida ya d’ora hannu a cikinta yana shafawa yace “Yawwa sannu abokiyata, na sameku lafiya?”

Da fara’a ta amsa da “Lafiya lau muke, ya k’ok’ari?”

Murmushi yayi yace “K’ok’ari muna ta fama da taimakawarku.”

Murmushi tayi tace “To yanzu me ye abunyi? Nasan dai mijina sarkin tsafta ne bare nayi tunanin baiyi wanka ba, yanzu abinci zaka ci ko kuma karatu zamu shiga?”

Gyara zama yayi yana kallonta yace “Sanin matata sarauniyar tsafta ce yasa na fara wanka kafin ta sakani dole, abinci kawai za’a taimaka min dashi yanzu dan yunwa nake ji, amma kafin nan a amsa min tambayoyi na.”

D’an bud’a idonta tayi sosai tace “To fa! Wane tambayoyi kuma?”

Hannunta ya kamo ya rik’e yace “Hafsy na, yanzu kina ji kina gani da had’in bakinki da yardarki da kuma tallafawarki su Asas zasuyi wani abu wai kamu? Miye ma kamun nan ne? Shin bidi’a ce ko sunna? Me ake yi a wurin? Maza da mata ake tarawa ayi rawa a ci a sha a fita tsirara? Mi ye ma anfanin yin shi kamun?”

Wata ajiyar zuciya ta sauke tace “Da fari dai ba sunna bace zamu iya cewa bidi’a ce tunda al’ada ce aka rik’e gam, na biyu kuma ana tara maza da mata amma wannan iya zallar mata ne insha’Allah, abu na gaba kuma ba zamu saka kid’a ba bare har ta kai ga rawar ma, dan mu ba iyata mukayi ba.”

Ta k’arashe tana k’yalk’yalewa da dariya, shi ma yar dariyar yayi yace “Yanzu kenan a matsayinki na ustaza kin bada goyon baya d’ari bisa d’ari akan al’ada marar tushe?”

Marairaicewa tayi tace “Dan Allah ayi hak’uri a barmu, kaga fa har na kai wa amarya kayanta da zata saka a ranar, insha’Allah babu abinda zamuyi da ya sab’a k’aida.”

Zura mata ido yayi sakamakon fad’uwar da gabanshi yayi sanda ta ambaci amarya, Ryam! Lallai yarinyar ta koya mishi darasi na rayuwa akan karatun mata, hakan ya cire mishi sha’awar k’ara aure gaba d’aya, ita ce ma dai yake ta koyon yanda zai yakiceta a zuciyarshi, ma wani ikon Allah sai ma k’ara samun muhalli take tana zama, babban tashin hankalin shi ne ko waje ya fita aka kirashi da sunan sheikh ko wani suna na ladabi da girmamawa saiya tuna wacce ta iya kallonshi ta ce Abdul, wasu lokuta sai ya ji kamar ya biya kud’i ayi zaune gabanshi ayi ta kiranshi da Abdul, saidai tasirin ba d’aya bane ko kad’an, gashi lokaci na sake kusantata da d’an uwanshi da zasu zama abokan rayuwa mata da miji, shi kuma zuciyarshi na sake daffaruwa da tunaninta.

Jinjina kai kawai yayi bai ce mata komai ba, hakan ya sata mik’ewa tace “Godiya muke sheikh, bari na kawo maka abinci a nan.”

Yana kallo har ta fita a d’akin kafin ya gyara zamanshi yana sauke numfashi, cire babbar rigarshi yayi ya aje tare da hula ya shiga shafa kanshi yana lumshe ido yana tuna abinda ya faru a waccen ranar, abunda yafi tsaya mishi a rai shi ne da likitar tace zata je ta samu mahaifinta suyi magana, da sauri ya bud’a idonshi yaja wani dogon tsaki a zuciyarshi yake fad’in “Me yasa Ryam? Me yasa kika ballagazar da kanki haka? Baki san cewa mutumcinki shi ne darajarki ba? Me yasa kika zama mai arha haka? Kika wofantar da abu mafi daraja?”

Wani tsakin ya kuma ja tare da sake muskutawa ya gyara zamanshi, yana haka Hafsat ta shigo da sallama da babban tire a hannunta d’auke da kwanuka masu kyau na alfarma saï d’aukar ido suke.

           *Safiyar lahadi*

Su hud’u suka gama shirinsu har da Asma’u da sukayi fad’a jiya amma an shirya da safe, suna zaune tsakar gidan k’aramar wayar Asma’u tayi kuka, d’auka tayi tana fad’in “Abokin ango barka.”

Daga b’angarenshi ya amsa da “Barka k’awar amarya, kun shirya ne?”

“Mun shirya ai ku muke jira.” Ta fad’a tana kallon Mimi, daga can ya amsa da “Da gaske? Ko kuma dai maganar yan matan amarya za’a mana.”

Cike da tabbaci tace “Da gaske mana, idan baka amince bâ gwada cewa mu fito ka gani, sai mu tabbatar su waye yan matan amarya da abokan ango tsakaninmu.”

Dariya yayi yace “Da gaske? To ku fito mu gamu a k’ofar gida.”

Saida ta mik’e tsaye suma suka mik’e tace “Kuma ka yarda idan baku k’ofar gida ku zama yan amatan amarya?”

Dariya yayi sosai yace “Anya Asma’u kina son gaskiya? Yanzu so kike ki rabu da abokin namu?”

Ita ma murmushi tayi tace “Ina so ne dai na nuna muku mu ma jarumai ne zamu iya d’aukan duk wani caji da yan matan amarya zasu mana.”

Cikin d’aga sauti yace “Iyeeh! Lallai Naanah Asma’u kin iya azanci, amma dai kina da sha’awar siyasa ko? Ko kuma dai a gidanku akwai d’an siyasa.”

Dariya tayi sanda suka fito k’ofar gidan tace “Ko kad’an, wayo ne dana fara koya a wajenka.”

A lokacin shi ma ya karyo kwanar gidan yana fad’in “To gashi mun iso tare, yanzu kowa sai ya zauna a matsayinshi ko?”

Shiru tayi ba tace komai ba har ya tsayar da motar, sauke glas yayi yana aje wayarshi yace “Sannunku.”

Duk amsa mishi sukayi banda Mimi dake lab’e bayan Asma’u tana sunkuyar da kai, murmushi yayi yace “Ina amaryar ta mu? Asma’u ya zaki b’oye mana ita haka?”

Kama hannun Mimi tayi ta bud’e motar ta shiga haka ma su Rauda, har zata shiga Sadeeq yace “A’a ya haka? Ki dawo gaba mana, ko ba kya son hira dani ne?”

Murmushi tayi tace “Ni dai ban fad’a ba.”

“Amma ai aikinki ya nuna haka.” Ya fad’a yana kallonta tana zagayawa, bud’ewa tayi ta shiga ta zauna kafin ya tayar da motar, a hankali suke tafiya yana jansu da hira irinta yan matan amarya da abokin ango wacce duk rigima ce a cikinta su ja ya ja, da haka har suka isa salon d’in da Asas ya umarceshi ya kai su. Duk ajin Mimi da son k’aryarta saida ta ji ta raina kaita da suka shiga ciki, babban wuri ne katafare daya tsaru ya had’u, ga ma’aikata suna ta aikonsu ga manyan mata na shiga da fice.

Mai saloon d’in ba musulma bace amma tana ganinsu dake tasan su Sadeeq da fara’a ta mik’e ta tarbesu, fita yayi ya barsu bayan ta tabbatar masa ya dawo bayan awa uku. Nan fa ta shiga yi wa Mimi aiki da kan ta su Asma’u kuma yaranta suka kama musu, gyaran kai aka fara musu da wankin k’afa da hannaye, Mimi kuma saida ta shafa mata wani had’i na gyaran fuska tare da rufe mata idonta da kokonbre, minti k’alilan suka rage Sadeeq ya dawo aka kammala musu, dan haka yana zuwa ya damk’a mata kud’i suka tafi suna godiya inda suka ji Sadeeq na fad’in sai jibi idan ya maido su kuma.

Suna dawowa gida  ta samu Iya Delu da mama suna hira ta ‘ya da uwa, gaisheta duk sukayi sai Mimi da tace “Ni dai ba zan gaisheta ba dan ina daf da shiga gidanki a matsayin kishiyarki.”

Duka Iya ta kai mata tana fad’in “Ke kauce can ja’ira, naga inda zaki je d’in ai.”

Dariya sukayi suka shiga d’aki sai su Iya da suka ci gaba da hirarsu akan dangin malam da har yanzu babu wanda ya tako k’afarshi, malam da kan shi ya basu goro ya kuma fad’a musu, sannan jiya ma da kan shi ya sake komawa k’auye ya tunashesu lokacin, amma babu wata gamsassen amsa daga garesu kowa yayi gum da baki saboda su aurenshi da Iya ne basu so ba, abu kuma an ja shekaru gasu da ‘ya’ya da jikoki amma a ce sun kasa fahimtar hakane Allah ya nufa. Dan haka jiya d’in yace ma Iya suyi hidimarsu kawai, tsirarun danginshi ba zasu hana yiwuwar wani abu ba, auren ‘ya’yanshi ma aka yi shi ba dasu ba bare kuma jikanyarshi, dan haka za’ayi bikin Mimi kuma dama ba wata tsiya suke buk’ata daga garesu ba.

        *Yammacin litinin*

Daga farfajiyar gidan take jin shewarsu suna shigowa, kallon Asma’u tayi tace “Su Salma ne fa da Ruky, nasan sun samo muku d’inkin.”

Da zumud’i Asma’u tace “Allah yasa.” Suna shigo d’akin ya gauraye da hayaniyar yan matan suna murnar samun d’inkinsu na anko wanda zasu saka ranar kamu dana kan amarya, zaune Salma tayi kusan Mimi tana nuna mata hotunan wasu amare da fad’a mata sunan wanda suka musu kwalliya, a haka ta kawo wata amaryar da kwalliyarta tayi kyau sosai kamar inji (ingine) ya mata, da zumud’i Mimi tace “Wannan tayi kyau, wa ya mata?”

Salma ce tace “Sara ce.”

Da sauri Zeinaba tace “Baa ita ce jiya Sadeeq ya kaimu salon d’inta ba?”

Asma’u ce tace “Ita ce.”

Mimi ce tace “Gaskiya aikinta na kyau, dubi kiga hannayena data wanke min jiya sun k’ara wani d’an banzan laushi wallahi, kinji k’afafuna.”

Asma’u ma dariya tayi tace “Ai ni k’afata a hannuna ta kwana wallahi, dan sai nake jin kamar b’era zai iya gwaguye min k’afa.”

Dariya suka kwashe da ita inda Salma tace “To kinga tunda ma kun tab’a zuwa dan Allah ki ma Sadeeq magana ya sama mana rendez-vous a wurinta ranar alhamis ta mana kwalliya, akwai tsada fa amma nasan zata mana sauk’i ai.”

Asma’u ce tace “Yace fa sun san ta sosai tare sukayi karatu da ita a université, kuma jiya daya kaimu yace Asas yace gobe ma a koma saboda gyaran amaryarshi.”

Dariya sukayi inda Salma ta bawa Ruky hannu suka kashe tana fad’in “Shegiya Mimi, ta fa d’auko mai zafi wallahi, gayenta ya had’u k’arshe, komai na kece raini ya ke mata.”

Yatsina fuska Mimi tayi tace “Ba kamar ke ba da zaki auri sa’an babanmu ba.”

Dariya akayi saï Salma data had’e fuska tace “Mimi bana son wulak’anci wallahi, wai me yasa kike min hakane? Kinga fa sati uku ya rage aurena amma saboda kece na zo ina ta zirga zirgan aurenki.”

Murmushi tayi tace “To yi hak’uri na daina.” Da haka yan matan suka ci gaba da shirye shiryen bikinsu inda kowace ta gwada doguwar rigarta da aka musu iri d’aya mai kyau da dogayen hannaye, saidai babu wacce rigarta ke da d’an kwali hakan na nufin dole su nemi wanda zasu d’aura.

Sun jima a gidan suna hirarsu kala kala ta nishad’i da k’aruwarsu dan Mama ta fita tare da Sahura da Shapi’a, har bayan azahar kafin suka ci abinci da Rauda ta musu mai sauk’i kafin suka bar gidansu suka barta tare da yan uwanta suka ci gaba da farin cikinsu.

*Indai da comment to da aiki tuk’uru insha’Allah.*

*Alhamdulillah*👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

        *MATAR MUTUM*

            _(K’abarinsa)_

👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

                   *NA*

_SAMIRA HAROUNA_

       *SADAUKARWA*

                   

               _GA DUKA_

     *’YAN AMANA TA*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_🤝

  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

_Bismillahir rahamanir rahim_

                    *24*

*Asubar talata* tana cikin bacci bata riga ta farka ba Mamar Asma’u data shigo gidan yanzu ta shafa mata lalle a kan ta da hannaye da tafin k’afa, zunbur ta tashi zaune tana kallonta tana mata dariya, ganin ta fita a d’akin sai kawai ta cire lallen na hannayenta ta shafawa fuskar Zeinaba dake baccinta, a firgice ta tashi tana fad’in “Waye? Mimi.”

Dariya ta kwashe da ita tare da mik’ewa ta fita a d’akin ta shiga ban d’aki da d’an kwalinta a kai.

Safiya na yi Mama ta dinga aikinsu Yaseen suna raba alawa ta wankan amarya da yamma, Mimi kam banda fad’uwa da gabanta keyi duk jikinta ma yayi sanyi sosai, sai taji tana rasa karsashinta da zumud’inta da ma farin cikinta, misalin 08:00 Mimi dasu Rauda suka shirya suka shiga gidan Maimuna, anan k’awayenta suka dinga zuwa suna shan hirarsu da haka har aka samu wuni, dan kuwa saida la’asar tayi kad’ai aka kirasu suka shigo gidan, lokacin gidansu kuma ya cika da mutane yan uwa da yan unguwa an zo wankan amarya. Daga gurin angaye aka turo da motoci guda takwas dan kai su inda za’ayi wanka, kusan mutanen babu wanda bai je ba saboda wadatar motoci da aka samu, gidan yar uwar su mama dan waankan farko ana yin shi ne a dangin uwa.

Gaba d’aya basu d’auki minti arba’in ba tafiyarsu da dawowarsu, Mimi kam ta jik’a tayi laushi sosai dan tasha wankan ruwan lalle masu d’auke da itatuwan da kakaninmu suka yarda cewa yin wanka dasu yana zubar da duk wata shiririta da shirme, yana k’ara maka hankali da nutsuwa, tun a mota take hawaye har suka zo gida bata daina ba, tunda ta shiga d’aki kuma k’awayenta duk suka watse zuwa nasu gidajen aka barta da su Zeinaba kad’ai.

Alhamdulillah kam aure rahama ne kuma alkairi ne, a dalilin auren Mimi Abba da Mama sun samu gudumuwa sosai daga dangi da kuma abokan arziki, hatta da Alhaji Saminu ya aiko da gudummuwar buhun shinkafa da kuma kud’i har jaka hamsin, duk da dai baya bayar bane cikin dad’in rai, kawai yayi ne dan kar ace bai yi ba amma sosai ya ji zafin yanda Mimi ta banzatar da shi ko wayarshi bata tab’a d’agawa ba. Wasa wasa sai gashi lokaci na ta tahowa kamar almara.

              *Ranar kamu*

Ko da k’arfe 08:00 ta buga suna salon ana ma su Asma’u kitso da k’unshi Mimi kuma saida aka fara mata gyaran jiki, ana idawa aka shiga zana mata k’unshi da jan lalle, mai salon d’in ce ta tsaya kan ta zata fara mata kitso k’anana, da sauri ta janye kanta tace “A’a, a’a bana so.”

Da mamaki tace “Ban gane ba kya so ba? Kina amarya?”

Kamar zatayi kuka tace “Bana so ni dai, zafi ke akwai wallahi, bana son kitso.”

Kamar da wasa Mimi ta ko dage ba za’a mata kitso ba ita kuka zatayi, dole k’arshe ta k’yaleta amma suna ta mata nasiha ta gyara a matsayinta na mace, ita dai saurarensu take bata kula kowa ba. Da azahar su Salma suka zo suma sunyi lalle da kitson su tsaf, dan haka ko da 03:00 tayi na rana suka fara shiri dan dukansu da kayansu suka zo, mimi ma ana ida lallen aka mata siraci ta shiga wanka, tana fito a sauk’ak’e kuma a nutse aka fara mata gyaran kakkauran gashin girarta, kad’an aka rage mata shi hakan yasa yayi kyau sosai tuni fuskarta ta fito shar da ita dake gashin nata bak’i ne wulik, kayan da Hafsat ta kawo mata ranar ta fara sakawa.

Doguwar riga ce abaya kalar ja mai duwatsu da kwalliya, tun ranar da aka kawo kayan Mimi bata duba su ba har Asma’u ta so bud’ewa ta hana, yanzu kam data saka sai suka saki baki suna kallonta, yanda rigarta ta zauna mata d’as a jiki ta mata kyau, ga tsarin rigar na ban mamaki wanda ya birgesu, wato idan sun fahimta komai a mutumce ne ya mata shi dan kar a sab’a k’aida, rigar zubin babbar riga aka mata na maza saidai a rufe take kirip har k’asa tana jan k’asa, gashi hula ce a bayanta irin na rigar sarauta alkyabba, sannan tana da kallabi ware daban wanda ake fara d’aurawa.

Kwalliya aka mata mai kyau da sauk’i wacce zaka rantse abonda aka shafa mata a fuska dama a fuskar ta ta yake, ana gama salllah la’asar dukansu yan matan sun fito sun haska a cikin rigunansu kalar pink na kakkauran yadi mai taushi, inda dukansu aka d’aura musu d’an kwali kala d’aya wanda suka siya.

Dogayen takalma k’afa ciki aka saka mata da jakarsu k’arama mai kyau da walk’iya, ga agogo data kama tsintsiyar hannunta dam ta zauna, kallabin abayar yanda aka d’aurashi daga ciki da kuma hular da aka d’ora mata sai ta fito sak gimbiyarta yar sarki jikar sarki.

Yamma sosai motoci guda uku dukansu k’irar benz suka paka a k’ofar salon d’in, a hankalce kuma a tsare yan matan duka suka kewayeta suka shiga takawa har waje, suna fita Asas ya hangesu daga cikin motar, wani murmushi ya sub’uce masa tare da jin yana sha’awar ya tsokaneta kamar ita d’in *matar yayanshi ce*, a sanyaye ya bud’e motar ya fito tare da bud’e mazaunin da zata shiga ta zauna, duk tsaye sukayi a bayanta saida ta shiga ta zauna ya rufe ya kallesu yace “Nagode k’awaye da gyara min amaryata.”

Murmushi sukayi Salma tace “Mu ba k’awayenka bane, ga k’awarmu nan kana shirin rabamu da ita.”

Murmushi yayi yana tsaye yana kalli duk suka shiga motar, sai Asma’u data zagaya d’aya b’angaren da Mimi take ta shiga, a hankali suka bar wurin suka d’auki hanyar gidan saukar bak’i na sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif.

Kecup! Suka ji k’arar waya tare da hasken daya d’auke idonsu, da sauri suka kalleshi sai kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da kai, murmushi yayi yace “Maah kin ga yanda kika had’u? Har saida na ji gabana ya fad’i tsabar razana.”

A hankali ta d’ago matsakaitan idonta da suka sha eyeshadow a tausashe kamar mai rad’a tace “Me yasa gabanka ya fad’i?”

Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Sadeeq yace “Saboda ganin kamar *matar manya* na d’auka, bana so na zama tururuwa uwar jaye-jaye.”

A sauk’ak’e ta kalleshi tace “Wannan maganar kamar dani kake, kar kasa na ji ba dad’i mana.”

Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma ya kalli Sadeeq dake fad’in “Ba wannan ba ma abokina, na ga amaryar ta mu kamar jinin sarauta, dan Allah daga wace masauratar take?”

Yar dariya tayi cikin sanyayyar murya tace “Ni ba yar masarauta bace, hasalima ko gidan sarauta ban tab’a shiga ba daidai da gaisuwa, idonku ne kawai suke yaudararku.”

Dariya sukayi sai Asma’u data rik’o hannunta tace “Mimi gaskiya ya fad’a, jininki da zubi na tsarin yanayinki kamar na wacce aka haifa a cikin masarauta ne.”

Murmushi Asas yayi yace “Kin gani, k’awarki ma haka take gani, amma ba komai karki damu, gaba kad’an zan mayar dake kamar sarauniya.”

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta sosai, Asma’u ma dariya tayi tace “Allah yasa.”

“Ameen.” Ya fad’a yana gyara zamanshi, Sadeeq ne ya saci kallonta ta madubi yace “Ke ma da zaki bada dama ai gaban kad’an sai a mayar dake sarauniyar.”

Dariya Mimi tayi tana sinne kanta wani dad’i na ratsata Asma’unta zata samu babban yaro, Asma’u kuma cike da zolaya tace “Wa zai mayar dani sarauniya bayan bana da suffar ko gimbiya?”

Dariya yayi yace “Gani, Allah da gaske nake Asma’u.”

Kallon Asas yayi yace “Abokina fad’a mata mana.”

Hararanshi yayi yace “Rainin hankali, ban tabbatar dana rik’e tawa a hannu ba zan zauna tayaka jefa k’uri’a? Kowa ya ji da kansa.”

Da mamaki ya kalleshi yace “Au! Hakane kenan?”

“Eh d’in.” Ya fad’a yana d’auke kai, jinjina kai yayi yace “Ba komai zan rama.”

Sake kallon Asma’u yayi ta madubi yace “Asma’u kinji ko? Dan Allah ki bashi kunya mana ta hanyar amince min.”

Kunya ce tasa ta sadda kanta k’asa tana wasa da yar wayarta a hannu, jin shiru yasa shi sake marairaicewa yace “Dan Allah *Asma’ul Husna* ki amince min kar na zauce.”

D’aga kai tayi ta kalleshi da mamaki, ita ina zata kai babban yaro haka kamar Sadeeq? Bata tab’a saurayin daya taka ko da matakala ta farko na a b’angaren aji bare hawa na uku, ita kam ya zata ce mishu ne yanzu? Tabbas tunda suka san juna yake nuna mata kulawarshi da abubuwa masu wuyar fassara, ta d’auka mutumci ne kawai ashe abinda ke ransa kenan?

Mimi ce ta d’an tsamiketa a cinya hakan yasa ta fad’in “Washhhh!” Da sauri ta kama bakinta tana kallonta, da ido Mimi ta mata alamar ki amince mana, ita kuma ta mata alamar ni a wa? D’an tsaki tayi tare da yin kamar zata daketa, hakan yasa Asma’u jinjina kai tace “To zanyi tunani ko?”

Cikin murmushi Sadeeq yace “Ba matsala, zan jiraki har kiyi tunanin.”

Bud’e baki sukayi da mamakin ashe ya ji me ta ce, da hirar raha da nishad’i har suka isa katafaren gidan daya had’u sosai aka k’watashi saboda hidimar da za’ayi.

Tabbas gidan ya cika mak’il da mata manya da yara ga kuma yan mata, saidai maganar gaskiya sun zo ne ganin zahiri da idonsu, tabbas su d’in ahali ne masu ilimi da sani sosai, amma fa suna da wani abu da saika rantse gidan jahilai ne, maganar talaucin gidansu Mimi a yanzu ba shine gabansu ba kamar da aka fad’a musu su waye iyayenta, sai suka zo tabbatarwa da tambayar kansu dame yarinyar tafi na su yaran da dayawa daga ciki aka so had’a Asas dasu amma ya k’i. Yan matan kansu suna so suga yarinyar ne dan su mata kallon hadarin kaji idan da hali ma har su yaga mata rigar mutumcinta.

Ai kuwa yamma na k’ara yin sanyi sai ga motocin angaye sun aje dangin Mimi, yanda suka fara shigowa harabar d’aya bayan d’aya yasa duk akaa kafesu da ido, su Shapi’a ne a gaba suka fara shigowa, hakan yasa wani gungu na ‘yan mata kecewa da dariya ganinsu dunk’ul dunk’ul kamar yara amma kuma da fuskar dattijai, ajiyar zuciya Sahura ta sauke tace “Allah gamu gareka, nagode Allah da Mimi bata wurin nan da anyi b’atacciya.”

Shapi’a ce tace “Ni kam fatana yanzu ta zo dan naga yanda zata ci uwar yarinya idan aka nemi wulak’anta mu.”

Ido Sahura ta zaro tace “Rufa mana aisri Shapi’a, kai tsaye fa zata ce ta fasa auren d’an uwan nasu.”

Cike da rashin dana sani Shapi’a tace “Idan tayi haka ma ai sai ta birgemu, wannan ai rashin sanin darajar d’an adam ne kamar ba gadon ilimi Sharif ya bar musu ba.”

Murmushi Sahura tayi tace “Ya bar musu gadon ilimi, amma yayanshi kuma sun bar musu gadon dukiya, hakan ya jawo dayawa daga ciki dukiyar ce tafi aiki a tunaninsu.”

Tab’e baki tayi tace “Allah ya kyauta musu.”

Dogaye da gajeru ne suma haka duk suka samu wuri suka zauna ana d’an gaggaisawa sama sama, hakan ya jawo kowa ware nashi ya koma gefe ana k’us-k’us-k’us, tubarkallah farfajiyar ta cika har kujeru na neman yin k’aranci duk yawansu, dan kuwa kafatanin ahalin Sharif duk sun hallara, kama daga iyalin Aliyu Sharif, Usman Sharif, Salmanu Sharif da sauran abokan arzik’i, sosai Hafsat ke k’ok’arin ganin an samu sanayya da kuma fahimtar juna tsakanin danginsu da dangin Mimi, hakan yasa take ta nunawa iyayensu su Shapi’a a matsayin iyayen Mimi, wasu suna sakin jiki su karb’esu a gaisa, wasu kuma gaba da gaba suke yatsina fuska suna musu yak’e, hakan bai ma Hafsat dad’i ba amma ya ta iya, sharesu tayi ita ma tana fama da cikinta da wunin yau ta ji bai motsa mata ba ga wata muguwar kasala, jefi-jefi kuma sai taji gabanta ya fad’i kawai ba dalili, saidai bata bar ambaton ubangiji ba a bakinta da haka take jin sanyi sanyi a ranta.

Sanda motocinsu suka tsaya angayen ne suka fara fitowa suna shigowa filin, sai k’awayen Mimi da suka jera gwanin sha’awa suka sakata tsakiya tare da Asas dake ta doka murmushi, Mimi kan kanta na k’asa tana fama da rik’e jakar hannunta rigarta kuma na jan k’asa.

Kowa sake waro idanu yayi dan tabbatarwa kanshi abinda yake gani, dangin Mimi da dama sun san kayansu ba daga nan ba indai wajen d’aukar wanka ne da iya gayu, saidai yanda ta zama tamkar wata balarabiya ya k’ara birgesu da kashesu a game da ita.

Inda yan matan nan kuma suka shiga tamtama wai dama haka yarinyar take, sam babu wata makusa a tare da ita da zasu kushe, duk da kwalliya tana canza hallitar mace ta gyarata amma dai sun tabbatar zata yi kyau, na farko tana da dogon hanci ga ta jar fata, su kam idan aka barsu sai su ce wata baralabiya ce, duk sai suka kasa motsawa a wurin dan kwarjini ma suka ji tayi musu yarinyar, sai yan matan amaryar ne da angaye da suka dage suna ta d’aukarsu hotuna, da haka aka isar da Mimi kan kujerarta sai su Asas da suka bar wurin dan dama fa anyi ba dasu za’a yi hidimar ba.

A cikin taron yan matan nan akwai guda d’aya wacce ita ba fa abinda ya kawo kowa ya kawota ba, na ta k’udirin babba ne daya girmi na kowa dan kuwa sak’on Muttak’a ta zo isarwa, tasan kasada zatayi amma kud’in daya bata tare da yi mata alk’awarin aure yasa ta ji zata iya yin koma menene, tun shigowarsu Mimi ta mik’e ta shige zak’ewa akan komai tana kamkamba kamar wata yar uwa. Dangin Mimi kallonta suke yanda rawar kanta yayi yawa suna tunanin wata yar uwace makusanciya ta Asas. Inda suma dangin Asas suke kallonta wata marar hankali daga b’angaren Mimi take, da wannan kallon da duka kusurwoyin ke mata aka kasa samun wanda zaiyi mata maganar shishigewa da take musamman ta b’aangaren abinci.

Magriba na gabatowa Hafsat ta gabatar da masu ruwa da tsaki ayi kamun amaryar, ana idawa Hafsat tasa Aisha da su Fanna suka kawo cake dan ta yanka tunda ba wani abun ci aka ware mata ba ita, da taimakon Asma’u ta yanka Asma’u ta d’an saka mata a baki aka musu tapi ana dariya, *Feena* ita tayi babakere ta d’auki lemu ta tsiyaya a cup na glas, a hannunta dama akwai k’aramar k’waya babu wanda ya kula da tsiyarta bare ya lura har ta saka, mik’awa Asma’u tayi ita kuma ta mik’awa Mimi, amsa tayi ta d’an kurb’a zata aje Feena ta sake fad’in “Ki k’ara mana, ko ruwa baki sha ba fa.”

Dayawa kallonta sukayi sai Mimi da take kallonta a matsayin dangin wanda zata aura, wannan kunyar tasa ta d’an k’ara kurb’awa kafin ta aje, Feena kam murmushi tayi duk da bata ji dad’i ba da bata sha sosai ba, amma dai tunda Muttak’a ya bata tabbacin guba ce mai had’ari sauta share kawai, a hankali ba tare da lurar kowa ba tayi kamar tana amsa waya ta fita a wurin.

Ana kwad’a kiran sallah magriba su Asas na dawowa d’aukar amarya, Hafsat ce ta rik’e hannunta saï Asma’u a gefenta sauran yan mata a gaba wasu a baya suka nufi hanyar fita, Mimi dake jin matsanancin murd’awar ciki da jin kamar an rik’e mata numfashi ba tare da ankarewar kowa ba ta tafi baya luuuu! Ta fad’i a wurin, da sauri Hafsat ta kalleta tare da sakin hannunta tana furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Mimi.”

Asma’u ma da sauri ta durk’ushe tana kiran “Mimi, Mimi lafiya.”

Take aka rufe wurin ana tambayar lafiya, cikin tashin hankali Hafsat ta d’ago kanta ta kalli Aisha tace “Eesha kira Asas a waje.”

Mayar da kallonta tayi kan Mimi, a hankali ta lura da jinin daya fara b’ullowa ta hancinta, cikin tsananin tashin hankalin da take jin bata tab’a riska ba ta daure ta d’ora hannu a kai tace “Na shiga uku, me ya sameta?”

Da gudu Asas ya shigo tare da rakiyar zaratan mazan a bayanshi, suna zuwa suka bud’a musu hanya, da sauri ya durk’usa yana fad’in “Me ya sameta? Me aka mata?”

Shapi’a ce tace “Ba abinda aka mata, ni fa ina ganin ko mayya ce ta kamata a wurin nan?”

Dayawa daga cikin mutanen suka kalleta sai wata mace mai aji sosai da tace “Nan ciki akwai wanda ya miki kama da maye ne?”

Hafsat ce tace “Bana tunanin haka, mu kaita asibiti jini ne yake fita a hancinta fa.”

Wata dattijuwa ce tace “To ko tana da iska ne?”

A sukwane Asas ya mik’e tsaye tare da tattara k’arfinshi ya d’auki Mimi cak ya fita da ita da gudu, duk rufa masa baya akayi hankali tashe da tunanin miye zai faru, yana sakata mota yaja da gudun tsiya zuwa asibitin sheikh data fi kusa dasu har da ma gidanshi duk yana kusa da masaukin bak’in na shi, duk tarin tilin motocin dake wurin kad’an ne suka bi su zuwa asibiti dan su san halin da take ciki.

*Gobe d’aurin aure fa*😁

*Alhamdulillah*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *