MATAUL HAYAT COMPLETE

 MATAUL HAYAT COMPLETE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

.

¤Wannan Sadaukar wa ce zuwa ga….. Boss dina, Yaya na, Dan uwa na, Bappa na, wanda adomin sa na ke nan, Allah ya ba shi sa’a da nasara a komai nasa da sauran en uwa musulmai gabaki daya…

(MARABAS DAN ANTY) jinjina gare ka.¤

.

Ci gaban labari…

.

Yace; Me zan taho miki dashi? Tana murmushi tace; ”Goba” Yayi dariya yace; Kedai kam ina ga sai kin haifi da mai kalar goba…Shikenan sai na iso.

Ya kashe wayar ya dauki makullin motarsa. Yana shirin fita ke nan Basiru masinja ya shigo ofishin rike da zungureren fayil(file) a hannunsa suka yi kici6us ya rusuna yace:

Yalla6ai ga takardun injinan nan da akayi bonanza daga ofishin peter yace akawo maka kasa hannu.

Ya kar6i fayil din ya dora akan tebur ya dauki biro yasa hannu(signing) sannan ya mikawa Basiru. Yana fita yaci karo da Alh. Sammani Sabo. Don haka dole suka koma cikin ofishin, suka gaisa Alh. Sagir yana dan fara’a yace;

Alh. Sammani jiya nake tunanin na kira ka ban samu sarari ba. Alh. Sammani yayi murmushi yace; kada ka damu ni gani nazo da kaina. Alh. Sagir ya dan yi shiru na wani lokaci sannan yace;

Gaskiya nayi tunani mai zurfi naga hakan bazata samu ba, musamman idan nace zan 6ullo da hakan a kungiya baza a aminta ba, don haka kawai nake ganin mu hakura……

Alh. Sammani ya bugi teburin da hannunsa yana dan murmushi yace; Kada ka damu Abokina,Aminina ni na san kai masoyi nane ko bayan ba raina zaka iya taimakon iyalina. Nagode da bayaninka yanzu yaushe ne za a dauka?

Alh. Sagir yace; Eh, to kamar yadda aka soma fada tun can baya. Alh. Sammani ya yunkura yace; shikenan aminina ba matsala, amma ni zan yi tafiya zuwa Dubai har sai bayan komai ya kammala zan dawo. Don haka ina neman afuwa ga kowa-da kowa, a kuma kula da ci gaba da abubuwan da ake yi yadda ya kamata.

Alh. Sagir yace; Yauwa aminina nagode kwarai da yadda ka hakura ka sadaukar. Babu komai.

Ya rako shi har bakin kofa, sannan shi kuma ya koma cikin ofis din ya dauko makullunshi daya ajiye cike da farin ciki ya fito ya tunkari inda suke ajiye motoci.

Ya kusa karasawa kenan yayi tuntu6e da wani ‘Kashi ya kife kasa, bisa tsautsayi ya kama aman jini.

Mutanen dake shawagi a gurin suka ankara da abinda ya faru don haka da sauri suka tunkaro shi, don kawo masa dauki.

Aman jinin yake kashir6an saboda haka sai ba a tsaya 6ata lokaci ba aka kwashe shi aka nufi Asibiti dashi. Ko kafin a isa Asibitin ya gala baita sosai, da gaggawa aka shiga dashi Emergency room.

Alh. Saminu wanda ya jagoranci zuwa Asubitin yayi amfani da wayar Alh. Sagir ya lalubo lambar Alh. Ahmad ya kira shi. Bugu daya wayar ta shiga. Yana dauka yace; Yane Baban gobe? Ko an sauka ne? Alh. Saminu yace; Bashi bane Daya daga cikin ma aikatan gidan gonarsa ne, don Allah ka same mu a NAJNOOR HOSPITAL, Saboda oga yazo hawa mota yayi tuntu6e ya kama aman jini. Shine muka kawo shi Asibiti.

Cikin tashin hankali Alh. Ahmad yace; To gani nan zuwa. Mintin sha biyar a tsakani Alh. Ahmad ya iso Asibitin. A lokacin suna da damar shiga inda yake saboda an samu aman jinin ya tsagaita.

Suna shiga suka tarar dashi dik ya yamutse kamanninsa dik sun sauya,tamkar wanda yayi ciwon shekara. Alh. Ahmad ya matsa kusa dashi yaga idanunsa sunyi jajur kamar jan gauta. Wani irin siririn haske ne acikin idonshi,sai kace yana saitin hasken kwan lantarki.

Cikin tausayawa Alh. Ahmad yace; sannu Alh. Sagir. Bai iya amsawa ba, sai dai idanu kawai da ya zuba masa,kai kace wannan shine karo na farko da yayi tozali da shi…..

ada Hausa Book stories

MATA UL HAYAT (JIN DADIN RAYUWA)

¤¤03¤¤

Dama baka lafiya ne ko kuwa sanadin tuntu6en ne? Har yanzu bai iya tankawa ba sai Alh. Saminu ya amshi zancen da cewa; Gaskiya nima ina tunanin bashi da lafiya, domin yaui sukuku yake a gidan gona,tunda ya shiga ofis dinsa bai fito ba sai da wannan sanadin ya faru.

Alh. Ahmad yace; To Allah ya bashi lafiya? Gaba daya suka amsa Ameen. Sun shafe mintuna goma babu wanda ya sake magana daga cikinsu. Sai zuwa can Alh. Sagir ya lumshe ido Alh. Saminu yace; Ina ga ma ya samu bacci.

Alh. Ahmad ya dago kai ya dubi Alh. Sagir, sai ya ga ya bude ido, amma kwayar idon ta sauya launi ta koma KORE shar, sannan ta koma DORAWA, sai ta koma BAKI. Shikenan ya maida idon ya rufe.

Gaban Alh. Ahmad ya fadi, bai fahimci abin da ya gani ba, ya dubi Alh. Saminu da sauri yace; Ku duba ku gani yadda kwayar idonsa ke sauya launi.

Da sauri suka dubi Alh. Sagir amma sai suka ga kwayar idonsa a rufe Alh. Saminu yace ai bacci yake. Alh. Ahmad ya dunga tunanin anya kuwa bai ga wani al’amari ya faru da dan’uwansa ba? Amma jin amsar da suka bashi yasa ya share maganar.

Alh. Saminu yace ya kamata a sanar da maidakinsa. Alh. Ahmad yace; Eh ba ma ita kadai ba harda mahaifanmu. Ya ciro waya yana niyyar doka kira kenan, Alh. Sagir ya mike a firgice ya dafe kansa da hannunsa guda da ba a dora masa ruwa ba? Alh. Ahmad ya maida wayar a aljihu ya matso da sauri kusa da dan’uwan shi yana tambayar; Ya jikin? Amma shiru bai tanka ba daga karshe sai ya koma yaraf! Akan gado. Gaba dayansu suka saka sallallami, daya daga cikinsu yayi saurin kirawo likita. Ya duba shi ya tabbatar musu da RAI YAYI HALINSA.

Kwalla suka sirnanowa Alh. Ahmad cikin karfin hali ya kirawo mahaifinsu ya shaida masa halin da ake ciki. Sannan ya kira Alh. Sada shima ya bayyana masa abinda yake faruwa.

Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankalinsu a tashe.

Cikin kankanin lokaci suka gurfana a asibitin hankali a tashe, aka gama dik abinda ya dace sannan aka basu mota (Ambulance) da zata kai musu gawar a gida.

Suka taho,kowannensu cike da wannan jimamin wannan BABBAN RASHIN da sukayi, Saboda rashin irinsu Alh. Sagir yana da matukar ta6a zuciya.

Jan gwarzo jarumi wanda ya tsayu da kyautatawa na kasa dashi, zai yi wuya talaka ya kawo kukansa ga Alh. Sagir ba tare da an share masa hawaye ba. Amma duk wannan yakana tasa bata hana ya amsa kiran mahaliccinmu ba.

Laillai Allah baya barin wani don wani yaji dadi!!! Kuma dik jarumtar rai da nuna hazikanci, dole ne ta dandani mutuwa.

(Dacin mutuwa mai ta6a zuciyar wadanda aka yi wa komai, ma’ana juriya da jarumta basu isa su hana rai dandanar mutuwa ba, yayin da suka rasa wani nasu)

mu samman ma Alh. Sagir da ya zamto tamkar shugaba a wannan tsatso, saboda yapi kowa kudi a cikinsu.

.

(ALLAH YA JIKAN MARUBUCIYAR WANNAN LITTAPIN YA GAFARTA MATA DA SAURAN MUSULMAI BAKI DAYA AMEEN)

.

Ci gaban labari…

KADDARA TA RIGA FATA Haj. Karimatu tana zaune a falo Haj Asmo ta shigo dauke da faranti a hannunta, fuskarta kunshe da fara’a tace; Yau dai ina sauke hakkin da ya rataya a wuyana. Haj karima tayi murmushe tace; uhm kaji manyan masu gida, don anyi min sanwa shine ake koda kai? To dama kin bari domin ba gwaninta kikayi ba tunda ba ci zanyi ba shi dai na karfen ya dawo yaci. Haj Asmo ta zauna a gefenta tace ke kin isa? Ai bazan wahala a banza ba. Haj Karima tace ; Ko yanzu ba kiyi wahalar banza ba,tunda dan’uwanki zai dawo,kinga kin hutashshe dani. Tace wlh kuwa ke nifa yau tinda na tashi nake jin gabana na faduwa komai ba yayi min dadi,hatta yawun bakina daci yake min. Ga shi dan da yake cikina yana ta yamutsamin ‘ya’yan hanji. Haj Asmo ta danyi murmushi tace; To ko dai haihuwar ta zone? Don dama naga cikin naki yayi kasa sosai. Haj Karima tayi murmushi ita ma tace; Wai ita mai tsohon ciki babu wani ciwo ko damuwa da zata shiga sai dole nakuda? Ni fa wallahi tsoro ma nake kada na zo haihuwar nan na wuce. Haj Asmo tace; Ai haihuwa ba mutuwa bace ke dai Allah ya sauke ki lapiya, amma ki daure kici abincin nan zama da yunwa yana azabtar da mai ciki. Haj Karima tace; Bazaki gane me nake nufi ba, sam ba na jin yunwa kuma bana iya kai komai a bakina. Ke dai kici kawai ba ra na shiga daga ciki. Haj Asmo ta dan harare ta, ta wutsiyar ido tace; Ke dai ko wayo kike so ki yi min ki shiga daki ki haihu sai dai na jiyo kukan jariri? Dariya Haj Karima tayi tace; A’a wallahi kinga ma na fasa shiga dakin shike nan? Za tayi magana suka ji karar tsayuwar mota Haj karima tace; Ina ga ma gashi nan ya iso. Haj Asmo tace mai yuwuwa bashi kadai bane naji kamar karar tsayuwar motoci ne ba daya ba. Tace kila shi da Abokanensa ne Kafin su gama tantancewa Alh. Sada ya danno kanshi cikin falon fuskarshi babu annuri suka amsa sallamarsa. Haj Asmo ta dora da cewa: Ai naje gidanka baka nan shine na wuto nan kafin anjima na koma. A takaice yace; Ai gwara ma da kika zo nan din. Ya dubi Haj Karima yace ina makullin sitroom? Kafin ta bashi amsa sai da suka kalli juna ita da Haj Asmo sannan daga bisani tace; Yana daki, yace kawo min. Zata tambayeshi ya daga mata hannu yace: Hanzarta ana jirana a waje. Haj Asmo jikinta yayi sanyi ta dubi Haj. Karima tace; Ko ki fada min inda yake sai na dauko, tace; yana kan dressing mirror. Haj Asmo ta nufi dakin a hanzarce ta dauko makullin sitroom ta kawo masa. Ya kar6a ya fice ba tare da yayi musu bayanin komai ba. Sai da aka shigo da gawar Alh Sagir tukunna Alh Rabi’u ya shigo falon. Ga ninshi da suka yi gabansu ya tsananta faduwa, tabbas ya nuna musu akwai wani al’amari da yake faruwa sai dai basu san ta ina abin yake ba. Suka durkushe su duka biyun suna gaishe da shi. Bayan ya daidaita zaman shi akan kujera ya amsa musu ya dubi Haj Karima murya a taushe irin ta dattako yace…..

.

.

Gaskiya ban gane canzawar idanuwan sa ba!!!

Se ku cigaba da biyo mu, dan jin yanda za a kaya…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *