MENENE MATSAYINA? CHAPTER A
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BISMILLAHIR RAHAMANIRRAHIM. INAMAI GODENAWA ALLAH SUBAHANAHU WATA’ALA, DAYASANYA NAKAMMALA LITTAFINA MAISUNA SAREENAH LAFIYA, INAKUMA ROK’ONSA DAYA SANYA YANDA NAFARA WANNAN LAFIYA, NAK’ARESA LAFIYA. INAGODIYA SOSAI AGAREKU MASOYANA ABUN ALFAHARINA, KUSANI INASONKU AKODAYAUSHE, INAKUMAYI MUKU ALBISHIR DA SABON NOVEL DINA MAISUNA MAINENE MATSAYINA ? ALLAH YASA ZAKU AMSHESA HANU BIBBIYU KAMAR YADDA KUKA AMSHI SAREENAH.*
*WARNING*
*WANNAN LABARIN K’AGEGGENE WANDA NA K’IRK’IRA DAKAINA, BALABARIN KOWA BANE, BAKUMA NASO AJUYAMIN SHI TAKOWANI SIGA, DUK WANDA YAJUYAMIN LABARINA BANYAFEMASABA.*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fectional story)*
*Written By*
Phatymersardauna
*🎈MRS SARDAUNA🎈*
*DEDICATED TO MY LOVELY AND SWEET SISTER MARYAM*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*Wattpad*
@fatymasardauna
*Page 1⃣*
K’arfe bakwai daidai tangamemen agogon dake Kafe Ajikin Bangon d’akin yabuga. Daidai lokacinne Kuma waya k’irar iPhone 8 plus, dake d’aure Kan bedsite Carbonate tasoma ruri Alamar Alarm d’in da’akayi setting yasoma aiki.
Ahankali tazuru kyawawan k’afafuwanta, daga kan bed zuwa k’asa . Had’i da Janye bargon dake rufe ajikinta, tatashi tsaye. Hakanne yabani Daman k’are Mata kallo, kyakkyawace Banawasaba Tanakuma da Kyau Sura duk dacewa Bazata Wuce 20 years ba. Sanye take acikin sleep gown, Amma hakan baisanya kyawun Surarta bayyanaba.
Kaitsaye toilet Tawuce, had’i dasakar mawa kanta shower .
Koda Tafito Acikin Bathroom d’in, Gaban dressing mirror tanufa, tashiga Shafe Jikinta da Mayuka kala-kala. Light mackup Tayi akan buety face d’inta, Kasancewar Ita ba Irin Matannan bane dasuke Cika Meckup akan Fuskarsu.+
Long Blue pencil Jeans Tasanya Wanda yayimatuk’ar Kamata. Had’i da Sanya Wata White tide shert Marar Hanu , anyimata Ado da blue paint, Wani Kimono Nai Santsi da shara-shara taji adon Stones tasanya asaman kayan, kokad’an kimono’n Bai b’oye Kayan dayake jikintaba Kasancewar sa shara-shara. Dogon gashinta tatufke Atsakiyar Kanta had’i dasanya big ribbon takamashi. D’an siririn mayafin doguwar Rigan tayafa , Wanda yatsaya daga kanta zuwa Wuyanta. Dogon Takalmi Mai uban tsini da igiyoyi blue colour tasanya ak’afafunta, had’i da feshe Jikinta da turarukanta masu dad’in k’amshi.
Tayi Matuk’ar Kyau Sosai da Sosai. Hand bag d’inta da phone dinta tad’auka tafice acikin d’akin.
K’aran Takalmanta shiya Janyo Hankalin, Way’anda Ke Zaune Cikin Falon.
Cike da Farinciki Taje tarungume, Wata kyakkyawar Mata Datake hada hadan had’a breakfast akan derny table. ” Gut mrng My Ummina,, budurwan tafad’a Tana k’ok’arin Kai kofin Tea bakinta.
“Mrng my daughter fatan Kema kintashi lafiya? Wacce akakira da Ummi tayimaganar tanashafa Kan Budurwan.
“Lafiya kalou Ummina Yau namakara zuwa school,, Budurwan Tayi magana tana b’ata Fuska.
” Hmm ai makara tariga datashiga, ciikin jiki da Jininki Farhana Matuk’ar Bazaki Daina Raba Dare, kina chatting ba. Wani Kyakkyawan saurayi dayake Sauk’owa daga Kan steps d’in Dake cikin falon yayi maganar.
” Kai My Brother Atif , nifa Jiya banyi chatt ba true out,, takai k’arshen Zancennata Tana tura Baki gaba.
” Gayawa Wanda Baisankiba Farhana,, Atif yafad’a daidai Lokacin dayake k’arasowa Kan Derny Table d’in.
Harya ja kujera daniyar zama, Farhana tarik’e masa hanu cikin muryar lallashi tace ” Pls Bro muje Kayi dropping d’ina a skull d’an Allah .
Bayanda Atif ya iya dolensa yamik’e suka fice Acikin falon.
Suna Tafiya Suna Hira harsuka, isa cikin babban University d’in su Farhana’n.
Tana fitowa Acikin Motar k’awayenta sukayo Kanta, Suna murnar Ganinta. Saida Tayi Hugging dukansu Ukun, kafun suka Rankaya zuwa cikin class, domin Alokacin har ankusa farayimusu lecture.
Zaune Suke akan wata kujera da’akayisa da Suminti, anyi shine Kuma Dan Zaman students .
Sarah tagyara Zamanta had’i daduban Farhana da tasanya wayanta agaba sai chatting take tana taunar Chewing Gum tace ” my Fana waike Baki gajiya da Chatting ne ?
Lumshe idanu Farhana Tayi had’i dayin Murmushin Daya bayyana Dimple d’inta afili, tace ” Oh My Sarah
Kinsosamin Zuciyata, Kokinsan My Man ne kad’ai yake kiranada Fana !! I miss You My Man ,,.
Fana Tayi Maganar Still Murmushine Kwance akan fuskarta.
Dariya Sarah Tayi had’i dacewa ” Farhana ta Farhan,,
” Wannan haka yake My Besty Sarah, inamatuk’ar Son Man d’ina because Ya’iya Soyayya, Haryanzu banga Namijin dayakaimin Man d’inaba!!!
Farhana Tayi Maganar cike da shauk’in love
Murmushi Sarah Tayi had’e dacewa “Koda *YAYA HAMEED* ne ?
Dam haka k’irjin Farhana yabuga, wani Irin fad’uwar Gaba Taji, Alokacin da Sarah ta ambato sunan Hameed.
“Please Sarah Nasha fad’amiki cewa banson Kinamin maganan Yaya Hameed, natsani Yaya Hameed fiye da Tunaninki banakosonjin Maganarsa.
Farhana Tayi Maganar fuskarta, cike da Damuwa.
“Maiyasa Kika tsani Yayanki Kuma d’an uwankine fanah ? Koda Yaushe zancenki kenan akan sa why ?
Sarah tatambeyeta.
” SBD shine mutum Nafarko dayafara Nunamin tsana, da k’iyayya Acikin Rayuwata, shiyasa Nima natsanesa kamar yadda yatsaneni.
Farhana takai k’arshen maganar nata, Alokacin da Hawaye suka Cika Mata idanu.
Zancigabane idan harna fuskanci, littafin Yasamu karb’uwa awajenku.
More Comment More Typing….
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(Fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Sweet Sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*Wattpad*
@fatymasardauna
[ Friday 16 August 2019]
*Naji dad’in Addu’a dakuma k’arfafamin Guiwa dakukayitayi, akan wannan sabon littafin Dana fara, ngd Kwarai Allah yabar kauna*+
*Gaisuwan bangirma da jinjina ga Aunty Fauza y’ar Amana, Ubangiji Allah yasanya haske,Alkhairi, farinciki , Acikin Rayuwarki, Allah ubangiji yak’ara muku so da kaunar juna, atsa kaninki da mijinki, Allah yabar Mana ke Aunty Fauzan mu, I really Love you.*
*Page 2⃣*
Numfasawa Sarah Tayi had’i dacewa ” For How Long , Zaku daina Wannan Abun ? Kuma Kekike hango Tsanar da Hameed yayi Miki, amma ni nakan hango wani abu agareshi game dake, Koke bakya hango abun ?
” Dan Allah Sarah kidaina way’annan maganganun Naki , Suna b’atan Raina wallahi.
Farhana takai K’arshen zancennata tana mik’ewa daga Zaunen datake.
” Afuwan My k’awallina Fana, banisakewa. Muje Cafeteria musamu Mud’ansawa Cikin mu abinciko, Dan Ni Yunwa Nakeji . Sarah takai k’arshen zancennata tanamai Shafa Cikinta, dake kukan Yunwa.
Karfe 6:00 pm daidai Sukafito daga Lecture d’in English dasuka Shiga tun 4pm . Amatukar gajiye Farhana tafito Daga Cikin Class d’in. All ready tasamu Driver’nta Najiranta Wanda yazo d’aukanta tun 5:30,, Sharp Sharp Sukayi sallama da Sarah Tashige Cikin Mota, Sukayi Gida.
Lokacin datashiga Cikin Katafaren Falonnasu, Babu Kowa ciki sai k’aran A.C dakuma k’atoton TV Plasma dayaketa aiki shikad’ai. Kaitsaye Sama tahaura inda Anan ne d’akinta yake.
Tanafitowa Awanka Taciro, wata y’ar yalolon doguwar riga,marar nauyi tasanya rigar Tanada guntun hanu haka kumatanada tsantsi . Sosai rigan talafe ajikinta tabayyana duk wani sura najikinta. Batare da tayi tunanin Sanya d’ankwali tarufe dogon gashintaba, tasa Kai tafice acikin d’akin.
Kaitsaye d’akin Ummi tanufa.
Ummi dakezaune kan bed tana shirya, wasu kud’ad’e dake gabanta , tajiyo sallaman Farhana . Amsamata tayi had’i dayimata iso cikin d’akin.
Bayan tagaishe da Ummin ne, tanemi waje tazauna had’i dacewa ” Ummi nadawo a skull dayunwa fal acikina,, tak’arasa maganar cike da shagwab’a .
Murmushi Ummi tayi had’i dacewa ” Abincinki yanacan Kan derny table yau favorite d’inki nayi,,
” Waw !!! I’m Proud of you my Ummina , Amma maizakiyi da makudan kud’ad’e haka Naga kina waresu gefe?
” Kud’in daza’asiyamawa Yayanku furnitures ne, za’asanyamasa a part d’insa kinsan This week zasu dawo Nigeria ,, Ummi tabata Amsa atak’aice.
Wani Irin fad’uwar gaba Farhana taji, Alokaci guda tabbas lokacin k’arancin farincikintane yazo, domin Tasan waye Hameed dakuma menene acikin zuciyarsa.
Ummi cetakatseta daga tunanin Datakeyi, tahanyar cewa da’ita taje taci abinci. Haka Farhana tamik’e cikin Sanyin jiki tanufi falo.
Batawani cin abincin Sosai bama tatashi tawuce d’akinta, kwanciya tayi akan makeken gadonta, had’i dajawo wayarta tadanna ma My Man d’inta k’ira, ringing Biyu tayi, Akayi picking call d’in .
Kafun tace Dashi komai , muryarsa yaratsa dodon kunnenta inda yakecewa ” I miss you my Sweet Dear I miss my sweet lips d’inki I miss my beutyfull eyes d’inki I miss my all …
Pls stop saying my Man, dan Allah kada kak’arasa kunyanka nakeji. Tak’arasa maganar tana rufe fuskarta da d’ayan hanunta tamkar yanaganinta.
Farhan dayake Kwance akan makeken bed d’insa , dariya yayi mai sauti had’i dacewa ” hin yau gaskia nayi missing Yaushe, my princess d’ina tasoma jin kunyana ? !!! yak’arasa maganar cike da Shaukin sonta.
Turo d’ank’aramin bak’inta gaba tayi tamkar yana ganinta tace dashi ” I miss u too My Man ,,
Lumshe idanunsa yayi had’i dasanya hanu Yashafi, sajen dake Kwance akan fuskarsa , cike da kauna yace da’ita ” very soon Ina hanya my sweet dear , Namatsu Nazo Naganki jinake tamkar nayi tsuntsu, kinsan Dady yayimin alk’awari inadawowa Za’a Turo komai dakomai gidanku, Kuma da yardan Allah aurenmu bazai wuce 1 month ba, kenida asonanema 1 week,, Yakai karshen zancennasa cike da zak’uwa.
Dariyan farin ciki Farhana tayi, had’i dacewa ” namatsu namallakeka My Man d’ina, nima zanso haka.
Harcikin ransa yaji dad’in kalamanta cike da k’arfafawa yace da’ita ” I swear My Fana zannunamiki Irin Soyayyar dabaki tab’a jin labarintaba aduniya, inatsananin sonki Fanah inayi Miki son dabansan adad’insaba, addu’ata akodayaushe shine Allah yamallakamin ke Amatsayin, Matata ta sunna intsotseki yadda Nakeso,, yakai k’arshen zancennasa Yana kashemata Murya.
Lumshe Idanunta tayi dasuka kad’a sukayi ja alokaci guda, cikin cool voice d’inta Tace dashi ” I miss You everyday,, pls kayi sauri kadawo My Man.
” Insha Allah My Fanah Nima nayi kewar komai naki, two weeks kenan bantsotsi zazzak’ar lips d’inki ba, harjina nake kamar Banda Lafiya .
Dariya Farhana Tayi Sosai, had’i dacewa “Nima Haka.
Hira sukayi Sosai da Sosai , jindatayi anakiran sallan magrib ne yasanya, sukayi sallama da juna cike da Tsantsar so da kaunar juna.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to my lovely Sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
[ Saturday 17 August 2019 ]
*Wattpad*
@fatymasardauna
*Not Edited 📵*
*Page 3⃣to4⃣*
Zaune Farhana take kamar kodayaushe, wayartace ahanunta Tana Aikinta Na chatting Dayazamemata Sana’a. Latifa Taturo kofar d’akin tashigo bakinta d’auke da sallama saidai kallo d’aya zakayimawa kyakkyawar fuskarta kafahimci cewa tanacikin Damuwa. Zama Tayi akusa da Farhana had’i dacewa ” wlhy Sister Sam banaso Bro yadawo Gidannan domin watan Shiga takuranmune yazo, harwani fad’uwar gaba nakeji innatuna cewa gobe zasu dawo Nigeria.
Latifa takai k’arshen Zancennata Tana yatsine fuska .
“Hmmm niko kinga dafari abun yadameni amma yanzu ko ajikina, saima farin cikin danakeciki jibi Man d’ina zaidawo. Takai k’arshen Zancennata cike da Shauk’i . Murmushi Latifa tayi had’i dacewa ” Laila Majnun ma sunsara muku indai tafannin soyayya ne ,,
Farhana tab’ude Baki zatayi magana Kenan, wayarta tasoma ruri alamar shigowan k’ira, ganin sunan my man d’inta akan screen d’in wayar, tayi Saurin picking wayar batare data bawa Latifa amsartaba.
Sanin da Latifa tayi cewa Idan Farhana tana waya da Farhan, tokan kwashe Awanni batare datagamaba, yasanyata tashi tabarmusu d’akin Baki d’aya.
Washe Gari.
Hidima Sosai Ma’aikata da Ummi keyi wajen tsara tarban abincin bak’insu, all ready Ummi tasa ansanya Sabbin furnitures abangarennasa haka Kuma ank’awata komai yadda Tasan yanaso, Duk dacewa d’an ra’ayine bakomai zakaimasa kaburgesaba. Ita dakanta tadafa abincin tarbansa sanin datayi cewa, bayacin abincin y’an aiki.
Karfe Uku daidai na yamma jirginsu yasauk’a a cikin Airport na Malam Aminu Kano .
Wani Kyakkyawan Matashi Wanda Akalla bazai Wuce 30 year ba Nahango Yana Sauk’owa daga Kan Matattakalar Jirgin , kallo d’aya zakayimasa katabbatar Cewa Kud’i hutu dakuma k’asaita sunzaunamasa, ahankali yake takunsa cike da’isa.
Sanye yake da Dogon wando bak’i and Black T-shirt , yayinda kansa kesanye da hula Irinna Sanyi, Kafarsa kuwa Irin takalmannanne Wanda ake Kira da Combat , Black Mai Igiyoyi Farare , Kyakkyawane Ajin Farko Kaitsaye Zaku Iya k’iransa da Handsome. Farine dogo yanada kakkauran Jikin dayake a murd’e Alamun yaji training, fuskarsa kuwa cike take da tarin k’awataccen k’asumba bak’a sid’ik Wanda tataimaka wajen bayyana kwarjininsa dakuma Kyaunsa, hanunsa rik’e da Wata Y’ar jaka itama black colour ce.+
Can bayansa Nahango Wata Kyakkyawar Mace Wacce batazata wuce 25 year ba Aduniya, Tasha Ado cikin black abaya had’i d’ayane kanta da d’an kwalin Abayar, tayi matuk’ar Kyau Sosai da Sosai Kasancewarta kyakkyawa saidai Kuma itama kallo d’aya zakaimata kafuskanci cewa Akwai Jinkai atattare da’ita.
Saida suka Gama sakk’owa daga Kan matattakalar jirgin ne , yasanya hanunsa yajawo ta jikinsa, kaitsaye Motocin dasuka zo d’aukansu suka nufa, Suna Shiga driver yayimawa Motar key sukad’au hanyar gida.
Adaidai haraban Tangamemen gidannasu driver yayi parking motar, jink’aran mota yasanya Ummi fitowa domin tana kyautata zaton cewa sune suka k’araso.
Cikin matuk’ar farinciki dajin dad’i Hameed yak’arasa ya Rungume Umminsa had’i dacewa ” I miss u Ummina takaina .
“Miss u too my lovely Son, Ummi tabashi amsa tanamai shafa bayansa Kasancewar yakereta Atsayi bazata iya shafo kansaba, matukar ba’azaune yakeba.
STORY CONTINUES BELOW

Amaimakon Matar dasuka Zo dashi itama ta k’araso tarungumi Ummin, saigani nayi ta tsaya daga can gefe fuskarta bayabo ba fallasa, tace ” barka da gida Ummi.
Cikin Irin Yanayin datayi mawa Ummin magana itama Ummin tamayarmata dacewa ” yauwa barka.
Amaimakon Hameed yanuna rashin jin dad’in yanda gaisuwan nasu yakasance saima hannayensa Daya mik’amawa Wacce suka taho dashi alamar tazo gareshi, bakunya ba tsoron Allah agaban Ummin tashige cikin jikinsa. Ganin haka yasanya Ummi juyawa tashige cikin part d’inta, Yayinda sukuma suka wuce nasu part d’in .
Sosai tsarin da’akayimawa part d’innasu yaburgesa, duk dacewa itadai Abokiyar Zaman tasa batawani yababa.
Yanashiga cikin bedroom yacire rigansa take 6 packs d’insa sukabayyana afili baro baro, Juyowa yayi dakallonsa Zuwa inda take tsaye tana k’aremawa d’akin kallo yace ” My Beedah Muje kiyimini wanka wlhy agajiye nakejina ,,1
Murmushi Beedah tayi had’i dacewa ” komai kace naimaka aishi zanma bakamar kai dabakason bin ra’ayinaba, takare maganar tana b’ata fuska.
Murmushin Daya bayyana Tsantsar Kyawunsa Yayi had’i danufowa Gareta, hanunsa yasanya Duka biyu yajawota jikinsa had’i dayimata kiss a kumatunta nadama cikin cool voice d’insa yace ” Yakamata kimanta Dawannan maganar my Beedah kinfasan nacemiki hakan Umarnin Abba nane banawaba kinkumasan bayadda za’ayi natsallake Umarnin sa ko, so mubar maganarnan. yakai k’arshen zancennasa Yana warwaremata nad’in d’an kwalin Abayar dake kanta.
Badan ran Beedah yasoba haka, tayi kokari wajen kawar da zancen Aranta.
Sungumarta Hameed yayi suka nufi bathroom.
Koda suka fito daga wanka, sake shiryawa yayi cikin Riga da Wando still, saidai su way’annan kalar blue Garesu” Beedah ku wa Shigar doguwar Rigan material Maroon colour tayi, balaifi tayikyau Kasancewarta kyakkyawa saidai matsalar ta d’aya shine batada cikan diri Mai d’aukar hankali, hanunta nasark’e Acikin Nasa haka suka nufi bangaren Ummi.
Ummi,Hameed Latifa Atif dakuma Beedah ne zaune akan derny table sunacin abincin da Ummi tagirkamusu, bakajin motsin komai acikin falon saikaran spoons , hakan Kuma yasamo asaline da dawowar Hameed cikin gidan Sam shi ak’a’idansa Idan yanacin abinci baya magana Kuma baiso wani daga gefensa yayi, hakan Shiya tilastamawa Latifa da Atif Yinshiru bawai Dan Kuma basuda abun cewaba, Suna guje mawa kawunansu masifarsa da idan yafarata tofa sai yakwana yanayi.
Ahankali Farhana take sakk’owa daga Kan steps d’in falon sanye take da pencil jeans ping colour Wanda yayi matuk’ar Kama Jikinta Sosai, hips d’inta sunfito sunyi d’as Ajikin, wandon tamkar zanasu akayi tsabar cika. yayinda tasanya wata white shert Wanda gabanta ke dauke da Zanen Wani Plower da’akayisa da Pink paint, gaba d’aya kafad’un rigan a fafake suke Haka daidai gefe da gefen cikin ta ma afafake yake, hakanne yabaiwa rigan Daman bayyana had’add’iyar Surar jikin Farhana bayyana, tayi Kyau Sosai Acikin shigartata Irin ta y’an matan turawa yayinda tasake Dogon Gashinta yakwanto har gadon bayanta, Babu abun da jikinta keyi saitashin k’amshi. Irin Shigar take Kenan kodayaushe, Kuma tanamatuk’ar son Shigar arayuwarta, yayinda wasu Kuma keyimata kallon y’ar Iska Ciki kuwa hadda Yayanta Hameed.
Samta manta dacewa yaune Yaya Hameed Zaidawo, danhaka batayi tsammanin ganinsa a Falon ba.
K’aran takalmanta shine yayi sanadiyar jan hankalinsu baki d’aya, suka Kai kallonsu gareta, Banda mutum d’aya domin Sarai shi tunkan yamai da kallonsa wajennata yasan kowacece.
tafe take kanta nakan wayan dayake hanunta tana chatting da Farhan d’inta saizuba murmushi take , Dagani kasan zancen love ake.
“Farhana !! K’iran sunanta da Ummi tayine yasanyata d’ago kanta had’i dacewa ” Na’am Ummina na…. Sauran maganartatace tamak’ale acikin mak’oshinta, sakamakon Ido hud’u dasukayi da Yaya Hameed , wani irin bugawar zuciya dakuma fad’uwar gaba taji sunziyarceta alokaci guda, saurin d’auke kanta tayi daga kallonsa had’i dajuyawa daniyar komawa d’akinta.
” Inakuma zakije Farhana batun d’azun natura Latifa Tayimini k’irankiba ?
Maganar Ummi ce tasanyata fasa komawa d’akin datayi niya cikin dakiya tak’araso wajen derny table d’in had’i dajan kujeran dake kusa da Ummin tazauna cike da girmamawa tace ” Ummi kiyi Hakuri nayi wankane shiyasa bansauk’o dawuriba.
“Shikenan badamuwa ga Yayanku yadawo saiki Masu sannu dazuwa,, Ummi tafa’a cike da kulawa
Sake tamke fuska Farhana tayi, had’e dacewa ” Yaya sannu dazuwa ,,
Ko Motsi baiyiba balle tasaran zai amsamata, dama Kuma tatsammaci hakan , because halinsane dabazai taba sanjawaba, itama basarwa kawai tayi gudun bacin ran Ummi yasanya , takai kallonta ga Beedah Wacce lokaci Guda tahad’e fuska tamkar Wacce akayimata Mutuwa,
“Sannu dazuwa ,, Farhana tafad’a atakaice had’i da d’age kanta sama tana tauna chewing gum d’in dake bakinta.
“Yauwa” itama Beedah ta amsamata atak’aice, had’i dayin maganar ciki ciki, lokaci Guda kuma tatashi daga Kan derny table d’in batare datace da Kowannensu k’alaba tasakai tafice afalon.
Hameed kuwa Ko’ajikinsa cigaba yayi dacin abincinsa, saidai fa kosau d’ayane baya K’aunar yad’ago kansa yayi arba da Farhana, wani Irin tsana da haushinta yakeji , kokad’an bayajin son yarinyar aransa dukda Kasancewarta y’ar uwarsa amma tsanar Dayakeji akanta special ne. Koda yakammala cin abincinsa shima mik’ewa yayi yafice Acikin falon. Yana fitakuwa Farhana da Atif nd Latifa suka kafa d’andalin Hira abunsu. Acewarsu ba mutuwa Akayimusu ba balle asanyasu yinshirun Dole, itadai Ummi tanajinsu Amma batace dasu k’alaba, dasurutunsu ya ishetama barmusu falon tayi.
Kwalliya sosai Farhana tadage ta, tsantsarawa jikinta, sanye take da rover pencil gown Wacce tayi matuk’ar kamata, gaba d’aya Kowani sura najikinta Saida yabayyana, Kama dogon gashinta tayi Atsakiyar Kanta had’i da yafa d’an karamin Vail dayatsaya iyaka wuyanta ko kirjinta dake acike dam vail d’in bairufeba . tayi Kyau sosai da Sosai , daidai lokacin datake shafa daddad’an turarentane wayarta dake aje Kan gado tahau ruri alamar shigowar k’ira.
Amaimakon tayi picking call d’in saigani nayi tasanya takalmanta masu uban tsini tayi hanyar fita daga d’akin.
Bakinta d’auke da sallama takutsakanta cikin falon,
Farhan dake zaune akan kujera ya’amsamata cike dafarin cikin ganita hanunsa yabud’e alamar tataho garesa, batare Datunanin Komaiba Farhana tak’ara sa garesa tashige cikin jikinsa, lumshe idanu sukayi atare gami dasauk’e ajiyar zuciya, hanunsa yasanya yak’ara rungumeta dakyau acikin kirjinsa had’i dasanya bakinsa dafda Kunnenta yace ” I miss you My Fana,, yakai k’arshen zancennasa yanamai tura harshensa cikin kunnenta.
Lumshe idanu Farhana Tayi had’i da k’ara lafewa Acikin jikin Farhan Tanamaijin Sonsa naratsa kowani sashi nazuciyarta.
Hanu Farhan yasanya yad’ago fuskar princess d’innasa cike da Shaukin so da Mararin juna yasanya bakinsa cikin nata, cikin salo da k’warewa yacafko tattausan Harshenta yasoma tsotsa ahankali, Cike da Soyayya itama Farhana ta cafko labbansa na k’asa tasoma tsotsa. Babu abun dake Tashi Acikin falon Sai sautin numfashinsu, hankalinsu yayi matuk’ar barin jikinsu , wani irin hot kiss kawai suke aikamawa juna cike da tarin sha’awa.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Sweet Sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*Wattpad*
@fatymasardauna
[ Sunday 18 August 2019 ]
*Ina matuk’ar mika godia dakuma jinjinata agareki my k’awa Nana Aicha, hak’ik’a kinada matuk’ar k’ok’ari wajen yad’a books d’inmu dakikeyi groups, Allah Ubangiji yabiyaki da gidan Aljanna, kisani inayinki sosai k’awata.🌸🌸*
*_Jinjina Agareku All Writers, na k’ungiyarmu mai Albarka, hak’ik’a kunada k’ok’ari sosai Allah yak’aromana Basira bak’i d’aya dama duk wasu Writers na Duniya, Ameen._*
*Not Edited 📵*
*Page 5⃣*
Sun d’auki kusan 10 minute suna kissing din juna, cike da so da kaunar juna bawai Dan tak’osa da kissing d’inbane yasanya tacire bakinta anasaba A’a k’afafuwantane suka gaza d’aukarta hakan yasa tazube akan kujeran dake gafenta tanamai da numfashi ahankali.
Daf da’ita yayimawa Kansa masauk’i cike da kulawa yasanya hanunsa yajawota Zuwa jikinsa. Bayanta yashiga shafawa ahankali yafurta cewa ” I love you more my Fana!!!
cikin sanyin murya farhana tace dashi ” love you too my Man !!! had’i dasake gyara kwanciyarta ajikinsa harwani lumshe idanu takeyi. Hira suka shigayi cikeda so da kuma kaunar juna Wanda rabin hiran tasu takasance Romancing junansu suke.
Harbakin Motarsa Farhana tarakosa kasancewar lokacin hargari yasoma duhu, hanunsa yasanya yasake jawota jikinsa cike da kulawa yace ” harbanason tafiya my Fana saboda nasan inakomawa gida zanfara missing d’inki,, yakai karshen zancennasa yana langwab’ar dakansa gefe tamkar k’aramin yaro.
Murmushin dayake matukar bayyana beauty face dinta Tayi, had’i dacewa ” Nima Haka My Man,, batare da tunanin komaiba Farhan yak’ara matseta had’i da Sanya bakinsa acikin nata yashiga tsotsan harshenta yanawani lumshe muna fukan idanunsa, gaba d’aya sun shagala sunmamanta cewa awaje suke.+
Wani Irin Bugawa zuciyarsa Tayi, yayinda tsikar jikinsa suka mimmik’e, Idanunsa kuwa tuni sun rune daga white colour zuwa red, tsananin bacin Raine kwance akan fuskar Hameed,
Tana ganin Farhan yayimawa motarsa key tajuyo zuciyarta cike datarin farinciki, daniyar shiga gida, wani irin tsalle zuciyarta tadoka Tamkar Zata fad’o Waje, had’i da fad’uwar gaba Mai tsanani, asakamakon ganin Yaya Hameed tsaye yahard’e hannayensa akan kirjinsa, fuskarsa amatukar had’e babu alamar d’igon annuri akanta, tamkar Wanda akayimawa mutuwa, bakomaine yafi bata tsoroba kamar kallon matsanancin tsanan dayake binta dashi.
Cikin sanyin jiki tasoma tafiya ahankali kanta duk’e akasa, cike datarin kunyarsa duk dacewa tasan bawannanne karo nafarko daya tab’a kamasu suna kissing juna itada farhan d’inba.
Cikin zafin nama Hameed yasanya hanunsa yadamk’i Nata hanun had’i da Sauke mata wani lafiyayyen marin dayayi sanadiyar d’auke mata jinta daganinta, kafun tasake wani yunk’urin Kuma yasake d’auketa dawani Marin, wani irin k’ara Farhana tasake alokaci guda wanda yaratsa ko inanagidan. Cike datsananin bacin rai Ya Hameed kenunata da d’anyatsansa cikin lion voice d’insa yace ” I hate you Never !!! had’i da tofa mata yawun bakinsa akan fuskarta Afusace yanufi bangarensa. Domin tsayawarsa awajen zai’iya sanyashi d’aukan mummunan mataki akanta.
Dagudu Farhana tashige cikin part d’innasu, cikin sa’a kuwa batasamu kowa acikin falonba danhaka kaitsaye d’akinta tunufa,
Kuka take tamkar ranta zaifita, batatab’a jin tayimasa mugun tsanaba kamar nayau, hanu tasanya akan fuskarta had’i dashafo yawun daya tofa mata akan fuskarta, k’ara Mai sauti tasanya tare da fashewa da kuka mancin rai da tab’a zuciya.
Kuka sosai farhana tayi Wanda yayi sanadiyar haifarmata daciwonkai maitsanani, batasan wani irin kalan tsana Ya Hameed yayimataba, batasan Mai tataremasaba yakeyimata irin wannan tsananba, hakika itama tatsanesa kamar yadda shima yatsaneta, ba’abun dayafi konamata rai kamar yawun daya tofa mata akan fuskarta, takuma sanyawa hakan alamar tambaya.
Dakyar ta’iya shiga bathroom tawanko fuskarta datayi jajur da’ita had’i da dauro alwala tazo takabbara sallan magrib da’ake ta k’ira, batatashi akan sallayanba har saida tayi sallan isha.
Komawa tayi kan gado takwanta had’i da jawo blanket tarufe jikinta dashi, zazzab’i da ciwon kai ne suka dirarmata alokaci guda, take jikinta yad’auki b’ari.
I’m sorry kuyi manage, banda enough charge ne.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Sweet Sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*I love you all my lovely fans*
*Not Edited 📵*
*Page 6⃣to7⃣*
Koda ya’isa bangarennasu kaitsaye bedroom d’insa yanufa, wani irin tsana dakuma kyamar farhana yakeji yanasake d’arsuwa acikin zuciyarsa, yatsaneta ne sbd halayenta, dakuma d’abi’unta marassa kyau, waishin maitanema tarasane aduniya data zabi yin watsi da tarbiyan da Umminsa tab’ata tsawon shekaru tana bata? Yayimawa kansa tambayar dabai da amsarta, haka yayita juyi akan wawakeken bed d’insa, haushi da tsanar Farhana nasake d’arsuwa acikin ransa.+
Shirun da Ummi tajine har 9:pm bataga Farhana tasakk’o k’asa ba, yasanya Ummin dakanta Tanufi d’akin Farhanan danjin ko lafiya.
Salati Ummi tayi alokacin data iske farhana Kwance sai rawan sanyi take yayinda, jikinta yayi zafi rau tamkar wuta.
” subahanAllah Farhanatu Baki da lafiyane dama?
Ummi tatambaya cike dadamuwa.
Kai kawai Farhana ta’iya gyad’amawa Ummi, alamar “eh”danzuwa lokacin ko’idanuwanta takasa bud’esu.
Batare da Ummi tasake ceda’ita komaiba, tafice ad’akin 2 minute tsakani Ummi tadawo, kai tsaye sif d’in kayan Farhanan tanufa had’i da ciro Hijab Wanda zata sanyamawa Farhanan sutafi asibiti.
Cikin kulawa da lallashi Ummi tasanya Farhana acikin mota suka d’au hanyar Asibitin Aminu Kano .
Koda Doctor yagama checking Farhana, gado yabata had’i da d’auramata drip, mintuna k’alilan Farhana tasamu bacci yad’auketa.
Kafe Fuskar Farhana Ummi tayi da’idanu, Tanamai k’arewa shatin Hanun datagani akan kumatun farhanan shimfud’e, tabbas shatin yatsune da’alama kuma marinta akayi, Waye ? Ummi tatambayi kanta, karar wayar Ummin shiya katsemata tunaninta, Ganin Alhaji ne maik’iranta yasanya tayi picking call d’in had’e da ficewa acikin d’akin.
Atakaicedai Saida Farhana takwana acikin Asibitin kafun daga safe akasallameta, Suka tarkato suka dawo gida.
Bayanda Ummi batayi da Farhana ba akan tagayamata, mainene dalilin zazzabin datayi domin taga Shatin hanu alamun mari akan fuskar farhanan, Amma fafur farhana tak’i fad’a, dole Ummi taja bakinta tayi shiru.
Yau Alhaji Mamuda Canji zaidawo danhaka tunsafe mutanen gidannasa suka tashi da hidima, girke girke Kala Kala masu kyau da k’ayatarwa su Ummi tatanadarmawa Mijinnata duk wani favorites d’insa saida ta tanadarmai domin cikar farincikinsa yafimata komai. Gaba d’aya ahalin gidan suncika dafarin cikin dawowar Abbannasu, bama kamar Farhana tafikowa jindad’in dawowar Abban.
K’arfe 2 narana jirginsu Abba yadira acikin Garin Kano.
Hameed dakansa yatafi d’akko sweet papa’nnasa a airport.
Farhana dake kwance akan gadonta kamar daga sama tajiyo muryan Abbannata, ai kuwa batare dab’ata lokaciba tayiwurgi dawayartata had’i darugawa aguje tamkar k’aramar yarinya.
Batadamu dasuwaye awajenba batadamu kuma da maizaije yadawoba, cike da tsantsar farinciki tarungume Abba had’e dacewa ” oyoyo my one and only father, I miss u so much !!!
Cikeda tsantsar kulawa, Abba yashiga shafa kan d’iyartasa had’i dacewa ” miss u too y’an matan Abba, yakaratu? Abba yatambayeta lokacin dayake zama akan d’aya dagacikin kujerun falon,
” karatu alhmdlh Abbana ” Farhana tabashi amsa bayan tazauna kusa dashi,
(tana matukar son Abbanta fiye da abubuwa dayawa.)
Hira Abba yashiga yi da familynnasa cike da So dakuma Kaunar juna, yayinda Hameed dazaman falon yazamemasa dole yaketa aikamawa Farhana dawani irin mugun kallo na tsana da kiyayya, sarai farhana talura dashi amma saita watsar tanuna cewa batasanma yanayiba.
Bayan kowa yanutsune Abba yarabamusu tsarabarsu, sunmatuk’ar jin dad’i sosai, wasu irin had’addun English wears Masu matuk’ar kyau Abba yasaimawa Farhana daga Malaysia, had’i dawasu dogin riguna guda biu masu kyau, ya yinda Latifa kuwa akakawomata zallan abayas dominsune favorite d’inta, Sunmatuk’ar jin dad’in kyautar, domin kayane new edition masu kyaun gaske.
Washe Gari kamar Yadda Farhan yayi alk’awarin cewa dazaran Abban Farhana yadawo zaitura magabatansa ayi maganar Aure, hakance takasance domin Daddy’n Farhan shak’ik’in abokinsa yad’auka suka nufi gidan Alhaji Mamuda Chanji.
Matuk’ar Karamci Abba yanunamusu, sunkoyi farinciki da hakan, domin duk kano dama babu Wanda baisan Alhaji Mamuda Chanji ba, mutum ne shimai karamci da mutumtaka baga talaka ba baga Mai kud’iba halinsane karrama d’an Adam.
Dama tuni Abba yasanda zaman Soyayyar Farhana da Farhan d’in. Sunkoyi magana cikin aminci dagirmama juna, Sadaki Alhaji Aminu wato daddyn Farhan yabayar Naira Dubu d’ari, batare dab’ata lokaciba Abba yasanya Ranan Aure nanda 1 month, Iyayen Farhan sunyi matukar farinciki dajin hakan, domin dama d’annasu yamatsa da’ayi Auren.
SALLAMA sukayimawa juna cike da mutuntawa, saida Abba yaga fitarsu daga cikin gidan kafun yashige cikin gida shima.
Dukansu Suka Hallara Akan derny table domin yin diner. Kowa cin abincinsa yakeyi cikeda farinciki, dakaga ahalin zakasan cewa bad’aya daga cikinsu dayake cikin damuwa, koko yanemi abu yarasa.
Bayansun kammala cin abincinne Abba yayi gyaran murya, had’i dacewa ” Kubani hanalinku inason magana daku,,
jinhaka yasanya dukansu maida attention d’insu ga Abban.
” kamar yanda nasan cewa kowa dake cikin gidannan yana sane da soyayyar Farhana da Farhan, wacce suka ginata shekara 4 kenan, to yanzu Allah yayarda Yau iyayen Farhan sunzo munyi magana dasu, ankuma yanke nanda 1 month zamud’aura musu Aure, sunkuma bani sadaki naira dubu d’ari gasunan,, Abba yakai karshen zancennasa alokacin daya ke mik’amawa Farhana kud’in sadakinnata.
” Alhmdlh !! Alhmdlh !! Masha Allah abu yayi kyau Alhaji dama haka akeso uba yakasance gay’arsa, Allah yanunamana lokacin ayi bikin daba’atab’ayiba acikin garin kano, Ummi tafad’a cike dafarincikin cewa d’iyarta takusa zama babbar mace.
Wani irin luguden farincikine yaziyarci zuciyar, Farhana Wanda batatab’a jin kalansaba, Masha Allah takusa mallakan Man d’inta amatsayin Miji kuma uban y’ay’anta.
Sunne kanta tayi k’asa karo nafarko data farajin kunyar Abba, saitakeji tamkar wani babban al’amarine yafaru.
” karb’i sadakinki kinji Mamana Halak d’inkine,, Abba yakatseta daga tunanin datake,
Cikin Nutsuwa da shiga gyad’a kanta alamar a’a ” bana buk’atarsu Abbana indai Halak d’inane tokaima nakane Dan haka nabarmakasu har abada, Farhana takai k’arshen zancennata tana sussunne kai. Ita adole taji kunya ance zatayi aure,lol
Murmushi Abba yayi had’i dacewa ” Allah yamiki albarka Mamana takaina, saidai bani amsar wannan kyautan naki, zandai adanamiki abunki sbd hakk’inkine.
Abba yakai karshen zancennasa yanamai k’ok’arin barin derby area’n dasuke zaune.
Bak’i Yaya Hameed yatab’e cike da tsana yawurgamawa farhana harara, azuciyarsa yace ” wazai iya aurenki aidama dole saishid’in dakuka gama lalatarku, Allah yasama yace yafasa muga d’an iskan dazai kwasheki, saidai kitabbata ba Aure, domin bawanda zai amince ya d’auki sauran wani k’ato ballagaza kawai,,
bayan Yagama soki burutsunsa shima yatashi yabar falon.
Latifa kam Dan tsananin farinciki rawa tashiga takawa waisuna da gagarumin biki.
Ganin Ummi tabar falonne yasanya farhana, sulalewa tashiga d’akinta wani irin tsallen Murna tabuga had’i da d’aukar wayarta tadannamawa Farhan d’inta Kira.
WhatsApp no 07069399224
More comment
More typing….
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to my lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
~[ 21 Wednesday August 2019]~
*Wattpad*
@fatymasardauna
*Editing is not Allowed 📵*
*Page 8⃣to9⃣*
Aranan kusan kwana Farhana da Farhan, sukayi da juna suna waya, had’i da sanarmawa junansu irin tarin, farincikin dasuke ciki marar misaltuwa, saida sukaga dare yaraba kafun sukayi sallama dajuna, Farhan jiyake inama da’ana iya d’auko mutum ta phone, dayau bamakawa saiya d’auko Farhanansa yabajemata kolin soyayyar dayakeyimata.
( Mutane dadama sukancewa ” duk namijin dayayi soyayyar shan minti damace baya yarda ya Aureta, toshikam anasa bangaren bahakabane, yanamatuk’ar son Farhana sosai baikumajin zai’iya kin aurenta, kokad’an tab’a jikinta da romancing d’inta dayakeyi bawai yanayibane dan yaudara, yanayine saboda tsananin soyayyarta datayimasa kamu, baikumajin zaidaina son Farhana arayuwarsa.)+
( k’alubale gareku y’anmata da Samari, kada kiji Farhan yace zai’iya auren Farhana, duk dacewa yasan abubuwa dayawa agame da’ita, kije kisaki jiki wani k’aton kawai yayita lalumeki da tsotseki, abanza batare da Aurensa nakankiba, kuma kiyi tunanin wai Aurenki zaiyi, Hmmm tonaji kodama ya’amince zai aureki, kinasane dacewa bazaitab’a d’okinkiba, because of what ? ,
Because yasan abubuwa dayawa agame dake yasan ya taushin lips d’inki yake, yakumasan ya taushi da girman breasts d’inki yake, kaiwanima yasan ya kike kekanki, tokinaga koda yayi jarumtan Aurenki zaiyi d’okinki kamar yadda Wanda baisankiba zaiyi ?, kada kigayamawa kanki k’arya koko kiyaudari kanki, wasu maza dakukagansu wlhy sunfi son jikinku fiye da komai naku, some times Maza nayaudaran y’an Mata surabasu da virginity d’insu, asunan wai So !!, kekinyarda cewa Sone hakan ? Wallahi duk namijin dayanemi wani abu dagagareki misali yace ” kiyi kissing nasa, kokibarsa yatab’a wani bangare najikinki dazaisanya yaji dad’i, toba sonki yakeba sha’awarki kawai yake, kekuwa shashasha dazaran kinbarsa ya moreki, wlhy mantawa dakezaiyi, watak’ilama bazaki sake ganinsaba har’abada, kuma yacuceki cuta tahar abada, Domin kinbiyemasa dakuma son zuciyarki data shaid’an, kun aikata sab’on Ubangiji batare da kunyar Allah ba, tofa kisani zunubinku yananan rubuce acikin takardan sakamakonku, matuk’ar baki tubaba wlhy kinacikin halaka, idan shekara d’ari zakiyi adunia, baza’ataba gogemiki wannan zunubinba matukar batuba kikayiba. Ya Allah kashiryar damu abisa sunnar ma’aiki S.A.W, kashiryar da duk wani d’an Adam dayake aikata sab’on dazaikaisa ga halaka yazama tab’ebb’e, Ameen.)
Tayi kyau Sosai cikin Shigarta datazamemata al’adarta, sanye take da long pencil jeans black colour, wanda tundaga kan cinyar wandon zuwa guiwansa akayimasa ado da pink stones masu kyau da d’aukar hankali, bakad’anba wandon yakama jikinta, hakankuwa bak’aramin Tona asirin hips d’inta yayiba, black T-shirt tasanya wanda yatasaya iyaka k’ugunta, yakumayi mata kyau ajikinta, Denim Jacket pink colour ta d’aura asaman rigan had’i dasanya black d’in hula irin nasanyi, tarufe dogon gashinta dashi, saitafito tamkar baturiyar London, ita kanta tanamatuk’ar son shigan sosai saboda tasan tanamata kyau aduk sanda tayi.
Wayarta tad’auka had’i dashiga camera tashiga d’aukan kanta hoto, wani wanda tad’auka dayafi kowanne kyau, shitayimawa Farhan sending d’insa, had’i da d’aurawa akan shafinta na Instagram, murmushi tayi alokacin dataga ruwan comments d’in da’akashiga yimata, akan hoton da ko 2 minute batayi da d’aurasaba, amma mutane sunyi caaa akai sunacewa tayi kyau, kashe data’n wayannata tayi had’i da cusa wayar cikin aljihun wandonta, tasakai tafice ad’akin.
STORY CONTINUES BELOW

Yanaganin tadumfaro cikin falon yayi kicin kicin da fuska, tamkar bashine yake murmushi d’azun ba, sarai Ummi talura dahakan amma saita basar, sanin datayi cewa Hameed d’in sam baison Farhana’n batakumasan dalilinsa nayin hakanba, bayankuma da, da Farhana take k’arama bawanda yakaisa nunamata soyayya aduniya, amma yanzu sam tarasa maiyasa suka sanya k’iyayyar juna azuk’atansu.
Kusa da Ummi Farhana taje tazauna, fuskarta d’auke da murmushin dayake k’ara bayyana tsananin kyawunta tace ” Barka da yammaci Ummina,,
” Yauwa d’iyata takaina kuma Amarya Insha Allah,, Ummi takai karshen zancennata cike da zolaya.
Wani irin kunya Farhna taji, hakan yatilastamata cusa kanta tsakan kanun cinyoyinta tana dariya, tawani bangare na zuciyarta kuwa, tanamaijin badad’i domin tasan idan tayi Aure, ita da Umminta kam sai sa’i da lokaci, zasuna ganawa.
Hira suka shigayi da Ummin jefi jefi, domin gaba d’aya hankalinta, yanakan series d’in da’ake haskawa ‘a tashar Bollywood maisuna ( Sarakat Zaujee ) tana matuk’ar son series d’in sosai, bakuma tayarda tayi missing nashi.
Beedah dake zaune awajen, jitake tamkar zuciyarta zata, faso k’irjinta tafito tsabar bak’in ciki, ta rasa wani irin tsana tayimawa Farhana Aduniya, sam koda saud’ayane bata bukatar, tabud’i idanu taganta tana numfashi, hakan kuma akan Farhana takejinsa kawai, bataji akan Latifa, kishin Farhana take sosai sosai, domin duk dacewa ita kyakkyawace amma Farhana, tad’areta akyau dakomai dakomai, inda take godewa Allah shine, sanin tsanar da Hameed yayimawa Farhana’n ba y’ar kad’an bace, to takanjin sanyi aranta idan tatuna wannan.
Shiko Hameed ganin dayayi zamansa , bashida amfani afalonne, yasanyashi kama hanun matarsa, sukayimawa Ummi sallama had’i daficewa afalon.
Kaitsaye bangarensu suka nufa, hakan kuwa yayimawa Beedah dad’i sosai, domin takan tsinci kanta acikin k’aton tashin hankali, aduk sanda taga Farhana da Hameed a inuwa guda, duk da tasanma ba jituwa sukeyiba.
Suna ficewa afalon Farhana tatab’e d’an karamin bakinta, dayasha pink lipstick, had’e damaida kallonta ga tangamemen T.V
Plasman datake kallo ciki, azuciarta kuwa cewa tayi ” ko’ajikina wai antsikari kakkausa, kufi ruwa gudu.
*****
Ranan yau takasance jumma’a, kuma a yaune akakawo kayan lefen Farhana, bak’aramin dukiya Farhan yakasheba wajen zubamawa Farhana, kayan k’yale k’yale namata, akwatuna goma sha hud’u yayimata, kuma kowannensu shak’e yakeda kaya.
Haka family’s d’in suka shiga shirye, shirye’n biki baji bagani, duk wani abu na k’yale k’yalen d’aki da k’awatasa, Abba duk yasaimawa d’iyartasa, domin dakansa yaje Dubai, yasaimata komai bakuma k’aramin dukiya yakasheba.
Bangaren Ummi ma shirye shirye takeyi bakama k’afan yaro, domin tuni tad’auko Hajiya Lailah, daga Niger domin a gyaramata y’artata.
( hajiya Laila kwararriyar Maigyaran Amaryace, domin wasu sukan k’iranta maida tsohuwa yarinya, tak’ware agyaran mata sosai, hakan yakesanyawa ake d’aukarta k’asashe k’asashe.)
Sosai Farhana takeshan durza awajen Hajia Lailah, domin bada wasa take aikintaba sosai take yimata gyaran jiki dana ciki, magunguna kuwa Farhana hartagaji dashansu, wani yayimata dad’i waniko yayimata bauri, cikin lokaci k’ank’ani saiga skin d’in Fana yasauya launi, yayi kyau sosai ya murje, yayinda ko’ina tawulga saita bar tsaraban k’amshi mai dad’in gaske.
Zaune yake cikin d’aya daga cikin kujerun falon, hankalinsa baki d’aya nakan, laptop d’insa dake aje kan d’an madaidaicin Stole d’in dage gabansa, dagani wani aiki yakeyi mai mahimmanci.
murmushi Beedah dake tsaye, bakin kofa tund’azu tana kallonsa tayi, had’i da k’arasowa cikin falon, batare da tunanin komaiba tafad’a jikinsa,
rumtse idanunsa yayi alokaci guda had’e da bud’esu, hanunsa yasanya yak’ara matseta, acikin jikinsa cikin wata irin murya yace ya’akayine My Beedah?.
Beedah tabud’e baki zatayi magana kenan idanunta, suka sauk’a akan kyakkyawar yarinyar da hotonta yacika Screen na laptop d’in nasa, take fari’an dake kan fuskarta yagushe, batasan wacece yarinyarnanba, amma tsanar datayimata nada banne, domin kuwa hatta wellpaper phone nasa hoton yarinyarne, tana da matuk’ar kishin Hameed sosai da sosai tayadda, bazata tab’a son duk wata mace aduniya dazata rab’esaba.
D’an takaitaccen murmushi Hameed yayi, had’i dacewa ” kawo min coffee ,, yafad’i hakanne saboda yakawar da maganar datake shirin fitowa daga bakinta, shi mutumne wanda bayason korafi, kokuma tuhuma, amma kwata kwata Beedah takasa fahimtan hakan, domin ita kodayaushe cikin k’orafi, da tuhumarsa take.
Haka tamik’e tana tura baki gaba tawuce cikin kitchine, domin had’a masa coffee’n daya buk’ata.
Gaba d’aya Farhan Yamatsa akan saiyazo yaga Fans d’insa, yayinda Ummi kuma takasa tatsare akan cewa ba’inda Farhana zatataka daga, Ranan da’akasomayimata gyara, har sai bayan and’auramata Aure.
Haka dolensa yahak’ura saidai anytime suna cikin waya.
Yau yakasance Auren Su, saura Sati 2 tuni kuma sungama tsara Events d’in dazasuyi , anko kuwa Kala 6 suka fitar kowani events da nasa ankon, su Latifa da Sarah sune kangaba, kuma big friends.
Yaukam Farhan gaba d’ya yarikicemata, akan cewa saiyazo yaganta, bayanda batayi dashiba akan yahak’ura zuwa afara gudanar da Events amma Sam yak’i, hakan yasanya dole ta’amincewa zuwannasa domin itama tayi missing nasa sosai…
Hanunsa yasanya yajawota gaba d’aya jikinsa, ” Wow !! My Princess d’ina kinganki kuwa saikace natural baturiya, I love this perfume,, Farhan yakai karshen zancennasa yanamai shak’ar daddad’an kamshin da kowani, kusurwa najikinta, kefitarwa.
Lafewa tayi luf acikin jikinsa tanamaijin sanyi naratsa zuciyarta, daga wani bangare na zuciyartata, kuwa raunine cike acikinsa.
Hanu yasanya yad’ago kyakkyawar fuskarta, data k’arayimasa kyau, cike da soyayyarta yace ” I Iove you My Fana, I love you so much, bansan damai zan misalta irin tarin kaunar danakeyimikiba, Inasonki daduka zuciyata, dakomai nawa, inayimiki soyayyar dabazata gusheba har’abada, amma daga wani bangare na zuciyata, inajin tamkar bazamu rayu dajunaba, Fana tamkar kowannenmu zaiyi nesa da d’an……
Saurin sanya hanunta tayi, tatoshemai Baki, batare databari yakai karshen zancennasaba, hawayene suka shiga rolling akan fuskarta, ” kada kace haka My Man, ninaji ajikina zamu rayu tare, har ‘abada dan Allah Man kadaina yimini maganar rabuwa, zakasanya zuciyata tabuga, bazan rayuba idan babukai, kaikafi kowa sanin hakan, soyayyarka itace numfashina, dazaran babu’ita kuwa to babuni,,
hanunsa yakai yasharemata kwallan dake kwaranya, daga kan fuskarnata tamkar anbud’e famfo, had’i darungumeta tsam acikin jikinsa, atare suka sauk’e ajiyar zuciya mai k’arfin gaske.
More comments
More typing……
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to my Sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
~[22 Thursday August 2019]~
*Wattpad*
@fatymasardauna
___________________________
*( I miss u more teemah kole, nayi kewarki sosai da sosai, Alkhairin Allah yakaimiki, aduk indakike, hakika nayi missing comment d’inki maisani nishad’i, amma saigashi zeetyna, tamaye gurbinki, ngd kwarai zeety da teemah, Allah yabarmu tare.)*
____________________________
*Editing is not Allowed 📵*
*Page 1⃣0⃣to1⃣1⃣*
Sunjima Manne dajuna, kafun daga bisani Farhan yayi ƙarfin halin, janye jikinsa daga nata, haɗi da ƙaƙalo duk wani kuzarinsa daya ragemai yashiga, yimata hira masu daɗi dazaisanya, taji sanyi acikin ranta.+
Sunyi hira sosai kafun daga bisani, sukayi sallama dajuna, sai da Farhana taga fice warsa acikin gidan, kafun ta juya itama ta shige cikin gida.
Wanene Alhaji Mamuda Chanji ?
Alhaji Mamuda Chanji, haifaffen ɗan jihar Kano ne, su biyu ne rak awajen Mahaifansu, shida ƙaninsa Alhaji Abba,
Alhaji Musa Mai Rasuwa, shine Mahaifinsu, Hajiya Hafsatu itace mahaifiyarsu, wacce suke ƙira da Mama, yayinda ƴaƴansu yanzu suka sauyamata suna zuwa ( Hajiya Kaka. )
Alhaji Musa yatsaya mawa ƴaƴansa sosai wajen, basu ilimin addini dana boko, kafun Allah yayimasa rasuwa, Alhaji Mamuda shine babba, kuma shine yayi karatu acikin Nigeria, yayinda Alhaji Abba kuwa yayinasa karatun a ƙasar India.
Koda Alhaji Mamuda yakammala karatun degree ɗinsa, baitsaya anan ba yayi masters ɗinsa, Saidai kuma shi mutumne da aikin Gomnati, bai wani da munsaba, domin koda suna yara ƙaninsa Alhaji Abba yafisa son aikin gomnati, zuwa lokacin kuma mahaifinsu Allah yayimasa rasuwa,
Alhaji Mamuda yana gama karatunsa, yafaɗa cikin harkan y’an chanji’n kuɗi, cikin ikon Allah kuwa yashiga harkan asa’a, Allah yasanyamawa abun Albarka. Bangaren Alhaji Abba ma tuni yasamu Aiki acan kasar India, domin kuwa sosai result ɗinsa yayi kyau.
Koda Hajiya Kaka taga cewa al’amuran ƴaƴannata sun daidai ta, hakan yasanya ta ɓullomusu da maganar Aure, batare da ɓata lokaciba Alhaji Mamuda, yace da mahaifiyar tasa tazama ɓamasa duk wacce tayimata, zaizauna da’ita domin shikam sam baida zaɓi.
Sosai Hajiya Kaka taji daɗin hakan, domin dama akwai wata ƴar aminyarta, datai mawa ɗaya daga cikin ƴaƴanta sha’awar Auren yarinyar, saboda tasamu tarbiya mai kyau daga iyayenta, gata bafullatanan Asali, mai alkunya da nutsuwa,
alokacin da Hajiya Kaka tayimawa Alhaji Abba maganar kawo mata, cematayayi tayi hakuri taɗan basa lokaci.
Koda Alhaji Isa ƙanin mahaifinsu Alhaji Mamuda yaje, tambayamawa, Alhaji Mamuda’n Auren Safiyya, Sam basu hanasaba saima tarba na mutumci da yasamu shida abokansa dasu kaje, hakan kuma yayi musu daɗi sosai, batare da ɓata lokaciba aka ba mawa Alhaji Mamuda auren Safiyya.
Koda Alhaji Mamuda yazo yaga Safiya yayaba da kyau da kuma tarbiyanta, kwarai hakan ne yasanya yaji lokaci guda, ya ji ta kwanta mai a rai .
Cikin Wata Guda akasha bikin Alhaji Mamuda da Safiyya, inda suka tare agidansu dake unguwar Lamiɗo cresent dake cikin garin kano.
STORY CONTINUES BELOW

Zaman lafiya sosai da sosai sukeyi, atsakaninsu, haka kuma soyayya mai ƙarfin gaske ta ƙullu, Tsakanin Alhaji Mamuda da matarsa Hajiya Safiyya.
Shekaran su ɗaya da Aure , Allah ya’azur tasu da ciki.
Tsananin kulawa da tattali, su Hajiya Safiyya take samu daga wajen mijinta dakuma family ɗinsa, harzuwa lokacin kuma Alhaji Abba baiyi Aureba, baima zuwa Nigeria sai lokaci lokaci.
Saida cikin Hajiya Safiyya yakai 10 month, kafun tahaifo kyakkyawan ɗanta Fari tas maikama da’ita domin ita ba baya bace wajen kyau, kowa yazo yaga yaro saidai yace
” masha Allah “
Baƙaramin dukiya aka kasheba ranar suna, domin bayan anyanka raguna biyu saida aka sake yanka shanaye biyu, yayinda yaro yaci suna *Abdoul Hameed* , tsabar yawan kaya kuwa maijego rasa inda zata sanyasu tayi, duk kuwa wanda yazo suna sai ambashi turmin atamfa, dasauran kayan alatu.
Hameed yanada shekara 5 a’duniya Hajiya Safiyya wato ( Ummi ) tasake haifo santalelen yaronta , wanda yaci sunan Alhaji Musa wato ( kakansu ) anaƙiransa da Atif.
Sai Alokacinne Alhaji Abba wanda su Hameed keƙira da ( DADY) yadawo Nigeria, bada da ɗewa ba kuma ya Auri masoyiyarsa dayake matuƙar so, maisuna MARYAMA, sun haɗu da’ita ne a Indian taje karatu, amma asalinta ƴar Nigeria ce, kuma shuwa arab ce, takasance ƴa ga Alhaji Yusuf , tsohon Gwamnan jihar Kaduna.
Suma a Kano’n suka zauna gidansu nakallon, na Alhaji Mahmud , komai da komai na ginin nasu iri guda ne, idan ma baka san nakowa acikinsu ba to baka iya banban cewa,
Mummy shine sunan da su Hameed keƙiran Hajiya Maryama dashi.
Hameed da Hajiya Maryama sun matuƙar shaƙu sosai, domin ƙodayaushe Hameed yana maƙale da’ita , duk da kasancewarsa miskili na gaske, amma ko da yaushe suna tare da Mummy’nsa daga’ita sai Iyayensa ne kaɗai keganin dariyarsa.
Saida Hajiya Maryama tashekara, Uku kafun tasamu ciki , tsananin farinciki da murna ara nan Dady yayishi,
Ranan da cikinta yacika wata tara da 2 weeks , ara nan tahaifo kyakkyawar baby girl ɗinta mai matuƙar shiga zuciya, kowa yazo ganin yarinya saidai yace tubar kalla masha Allah , domin dai gaba ɗaya kyawun Hajiya Mryam yarinyar takwashe.
Sunan Hajiya Kaka yarinya taci aranan suna wato hafsatu, Hameed dakanshi yace ana ƙiranta da ( Farhana ) haka kuma kowa yayi na’am da sunan,
Ranan da’akayi suna da dare, wani irin matsanancin ciwon ciki, yatashimawa Mummy, abu kamar wasa saida suka garzaya zuwa ga asibiti, haka doctors suka duƙufa akanta suna ƙoƙarin ceto rayuwarta, amma abun yafi ƙarfinsu, domin ciwon gaba gaba yake, sunyi iya ƙoƙarinsu domin su ceto rayuwarta amma abun ya ga garesu, abun da Allah yatsara ba wanda ya’isa ya hanasa afkuwa, haka sunaji suna gani, Allah ubangiji yaɗau ran abunsa, domin shi da yakawota duniya yafisu sonta.
Abakin ƙofar ɗaƙin Emergency’n kuwa, Abba, Dady, Hajiya Kaka da kuma Ummi, sunkasa zaune sunkasa tsaye burinsu baiwuce Doctors sufito susanar dasu cewa tasamu sauƙi ba.
Alokacin da doctors ɗin suka fito, caaa sukai musu akai sunason jin ƙarin bayani, da ƙyar doctor Aminu iya furta cewa ” Kuyi haƙuri duk kan mai rai mamacine s….. ai basubari yakai ga ƙarasawaba dukansu suka soma salati , Yayinda Dady kuwa yayanki jiki yafaɗi awajen sumemme, take likitoci suka shiga basa agajin gaggawa.
Har’aka kai Mummy gidanta na gaskia, Dady baidana kukaba , kuka yake wiwi baji ba gani, haƙiƙa yana matuƙar son matarsa, domin takasancemasa ɗayane tamkar dubu, yayi rashin macen da sake samun kamarta abune mai matuƙar wuya, to amma yazaiyi dolen sane yadangana lamuransa ga Allah.
Ɓangaren Hameed ma yayi kuka harya godemawa Allah, domin Mummy Uwa takasance aga resa, tawani ɓangare na zuciyarsa kuwa tausayin ƙaramar ƙanwarsa da’aka bari cikin maraici yake.
Haka kuma
Ba Ummi da Hajiya Kaka bane kaɗai sukaji , Mutuwar Mummy ajikinsu ba hadda
Mutane da dama sunji mutuwar Hajiya Maryam ajikinsu, domin macece mai halin ƙwarai da kyau tatawa, sam abun duniya bai rufemata idanuba, Saidai suyi mata fatan dacewa da rahaman Ubangiji.
bayan rasuwar Mummy da ƙwana uku, Ummi tahaifi tsohon cikin dake jikinta, saidai kasancewar suna cikin halin damuwar rashin da’akayi musu yasanya basuyi shagalin suna ba, yarinya dai taci suna Latifa.
Bayan Sati Biyu da Rasuwan Mummy ne, akayi zama atsakanin Family’n
Abba da kansa yayanke cewa shizai ɗauƙi Farhana Ummi zataci gaba da kula da’ita saidai kuma bazata shayar da’ita ba , zadai ana bata madara, kowa kuma yayi na’am da hakan,, shi ko Hameed farinciki ne yacika zuciyarsa nada wo wan Soul Mate ɗinsa garesa.
Dady kam zaman Nigeria gaba ɗaya yagagaresa, domin koda yaushe cikin ƙuncin rashin matarsa yake wuni, hakan yasanya tattara komai nasa yakoma India, Hajiya Kaka ma batai yun ƙurin hana saba saboda tasan halin dayake ciki, because tayi rashin miji itama taji yanda zafin mutuwar abokin zama yake.
Kulawa sosai Ummi kebamawa Farhana, domin ba ka ɗanba so da kauna, haɗi da tausayin yarinyar yashiga zuciyarta , saidai fa duk soyayyar da Ummi kemawa Farhana baikai wacce Hameed keyimataba.
Ƙuyi Manage
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~[23 Friday August 2019]~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
_____________________________
*Happy jumm’at kareem my dear and lovely fans🥂*
_____________________________
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣2⃣to1⃣3⃣*
Tsananin soyayya dakulawa, Hameed kebamawa Soul Mate ɗinsa wato Farhana, koda sau ɗaya ne Hameed baya ƙaunar yaga wani abu yataɓamai, habibatiensa, idan kuwa yajita tana kuka, take zai ruɗe shima idanunsa suka ɗa suyi ja, haka kuma zaiyita cizan lips ɗinsa, alamar kukan nata ɓasa harcikin zuciyarsa.+
ko Ummie Farhana bata shaƙu da’ita ba, kamar yadda ta shaƙu da Hameed.
Zuwa yanzu Farhana nada shekaru uku aduniya, Magana kuwa hatta fara zama aba kinta, koda yaushe cikin ƙiran sunan Appi’nta take ( wato Hameed ) , domin zuwa yanzu soyayya mai ƙarfin gaske ne, tasake shiga tsakaninsu.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya musu, cikin so da ƙaunar juna, yayinda Farhana kesamun kulawa, daga wajen Mutane da dama, ko ta’ina samun kulawa take, hakan yasanya take rayuwarta cikin farinciki.
Lokacin da Farhana takai Shekaru Shida Aduniya, Abba yasamamawa Hameed gurbin cigaba da karatu, a babban jami’ar dake Birnin London, inda zaikoma can da zama, natsawon 6 years.
Duk dacewa burin Hameed ne fita out side karatu, amma kokaɗan baison yayi nisa da Soul Mate ɗinsa, amma yasan haka Allah yatsara dolen sane yatafi, koda bayaso.
Cikin sati guda Abba yagama kammala masa komai na tafiya, aranan dazai tafi kuwa ba ƙaramin kuka yayiba, tausayin Soul Mate ɗinsa ne fal zuciyarsa, haɗi da tunanin yanda zaiyi kewarta sosai. Haka yanaji yana gani jirgi ta ɗaga dashi zuwa ƙasar England.
Koda Farhana ta farga cewa Appi’nta, bayanan tsawon ƙwanaki, kuka tasanya wa Ummie baji bagani, ita dole sai ankaita wajen Appien ta rabin ranta, da ƙyar Ummie ke lallamata hartayi shiru.
Kwanaki, satuttuka, watanni haɗi da shekaru, duk sun shuɗe ga Farhana batare da komai kama da Appienta taganiba, hakan yasanya tadaina yawan am batansa , sai dai kuma bawai tamanta dashi bane kwata kwata.
Sosai Atif yayi namijin ƙoƙari wajen maye mata gurbin Appienta da bayanan, takuma ji daɗin hakan sosai.
Saida Hameed yayi shekara Uku kafun yaziyarto Nigeria, saidai kuma da wani irin baƙon al’amari yadawo, ko kaɗan babu fari’a akan fuskarsa ga Farhana haka kuma dazaran ta nufo garesa, zai ɗauki bulala yace zai doketa, tsana yake gwada mata muraran, wanda hakan yahai farmata da tsananin tsoronsa, idan tagansa ma saidai tafa she da kuka, shiko ko ajikinsa, sosai sauyawar halinsa akan Farhana, yaba mawa su Ummie mamaki, sam basu taɓa zaton haka daga garesaba.
Ganin da sukayi Farhana tarasa sukuni da walwalanta adalilin sane , yasanya Abba tilas tashi yatar kata, komai nasa yakoma London, batare da time ɗin hutun daya ɗauka yacika ba.
Haka rayuwa taciga acikin familyn , Duk kwanan duniya Abba nasake samun buɗi a cikin sana’arsa, yayinda Hameed tun dayazo sau ɗaya , bai sake gigin zuwaba , Farhana kuwa gata take samu takowani bangare, domin kuwa idan bakasancewa Mahaifiyarta tarasuba, to bazaka taɓa cewa mahaifiyarta bata raye ba.
Farhana takasance mace mai son shigar turawa, tun sanda tasoma mallakar hankalinta, hakanne yasanya bata sanya wasu kaya matuƙar ba Englishi wears ba, da wuya take sanya atamfa nan ma saita kama dole. Tun da tafuskanci mugun tsanan da Hameed yakeyi mata, saita yi ƙoƙari wajen nisanta kanta dashi, wasa wasa har’itama taji yafice mata rai, domin dama ita batasan hidiman dayayi mata abaya ba, saboda tana ƙarama alokacin .
Hameed kuwa Acan London yayi karatun deegree ɗinsa na farko dana biyu, daga bisani yawuce America yayi P.H.D ɗinsa, bayan yakammala karatunsane yaga batarmawa da su Abba matar da yakeso, wato Abeedah wacce takasance ƴa ga Alhaji Uba, Tsohon Senator’n Kaduna , wanda ita taga Hameed ɗin tanuna tanasonsa, lokacin anturata wani course a America, tunda tagansa kuwa ta liƙemai, ba’ason ransaba yasoma kulata , hardai suka saba yasoma sonta.
Beedah irin matannanne masu jin kan tsiya da nuna isa, ko’ina tashiga takanjin tafi kowa , shiyasa tun sanda Hameed yakawowa Ummie ita amatsayin matar da zai Aura taji, bata kwanta mata arai ba, domin ko kaɗan Ummie bata hango ɗigon kunya da tarbiya a’idanun Beedah , amma bazata iya hanasa Auren zaɓinsa ba.
Ansha bikinsu lafiya da Beedah, satinsu ɗaya a nigeria suka ɗaga zuwa ƙasar Paris, domin acan Hameed yake aiki.
Wannan Shine Tarihin Ahalin, Alhaji Mamuda Chanji.
Cigan Labari.
Shirye shiryen biki ake sosai daga ɓangarorin gidaje guda biyun,
Yau take Laraba kuma yaune za’a gudanar da Bride Show , atan kamemen harabar gidan su Amarya.tuni ƙawayenta sun cika gidan kowacce kagani kasan hutu da naira , sunzau namawa mahaifinta, duka ƙawayenta suna sanye da Black pencil sket nd pink polo shirt , sunyi kyau sosai ba laifi yayinda Sarah da Latifa kesanye da dogin riguna , pink colour sunsha ɗinki kala ɗaya, kowacce kafaɗarta saƙale da”igiyar dake nuna matsayinta ga Amarya.
Farhana nahango tayi kyau sosai cikin Wata haɗaɗɗiyar doguwar riga, light pink wacce tayi matuƙar amsar jikinta haɗe da fidda duk wata surarta, mai ɗaukar hankalin maza ,tayi kyau matuƙa gwanin ban sha’awa, fuskarnan tata taji light meckup , saitashin ƙamshi take.
Sun cashe matuƙa awajen taron nasu, Farhan ma ya zo shida abokansa, yayinda shima yasha nasa kyaun, domin shima ba baya bane wajen kyau, sunyi hotuna sosai shida Farhana’nsa daka gansu kasan suna cikin matsanancin farinciki, haka taro ya watse kowa yana Masha Allah, domin abun ya ƙawatar sosai.
Washe gari kuma aka gudanar da Kamu, wanda tsara haɗuwarsama ɓata lokacine, ango da amarya sun sha kyau ƙwarai cikin shigar su iri ɗaya.
Yau takasance Ranan walima yayinda gobe ɗaurin Aure, dan haka gidannasu tun jiya yake acike maƙil da jama’a ƴan uwa da abokan arziƙi.
Tun tashinta takejin matsa nancin faɗuwar gaba, tare da tsinkewar zuciya wanda tarasa dalilinsa, daga wani bangare na zuciyarta , kuwa bugawa yake da sauri sauri.
Sake gyara kwanciyarta tayi akan bed, ɗinnata haɗi da lumshe idanunta, da sukai ja saboda ciwon kai dake damunta, ƙaran wayarta shi yafarkar da’ita daga tunanin data faɗa ,
*My Man*
shine sunan da ke yawo akan screen ɗin wayar tata, murmushin ƙarfin hali tayi haɗi da ɗaukar wayan takara akan kunnenta, muryarsane yadaki dodon kunnenta inda yake cewa ” missing yo more my wife “
murmushi tayi haɗi dacewa ” tun yanzu har na zama wife kenan ,,
” tun tuni ma’ai my Fana , jinake tamkar inyi wa gobe tsuntsu dan naga na mallakeki, saidai kuma tun jiya gaba na faɗuwa yake ,, Farhan yakai ƙarshen zancennasa cikin sanyin murya,
ajiyar zuciya Farhana ta sauƙe haɗe da lumshe idanuwanta tamkar yana ganinta tace ” Nima haka nakeji My Man saidai ina alaƙanta hakan da rabuwa da Ummie na da zanyi ,,
Ajiyar zuciya Farhan yasauƙe haɗi dacewa ” Inaso nazo naganki Matata ,, amma yanzu ina gidansu Jalal (tied friend nasa) idan natashi da wowa i promise zanzo naganki ,, yakai ƙarshen zancennasa cike da shauƙin soyayyarta.
Hira suka ɗan taɓa kaɗan kafun daga bisani, sukai sallama da juna cike da wani irin yanayi.
Wasa farin girki.
nabaku kaɗanne saboda kuma comment kaɗan kuke bani. 😜
Whatsapp no
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*1
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~[23 Friday August 2019]~
*Wattpad*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page1⃣4⃣*
Faɗuwar gabanta ne yatsananta, bayan sun gama waya da Farhan ɗin, cikin sanyin jiki tawuce bathroom haɗe da sakarmawa, kanta shower koda zataji sanyi acikin ranta.
Koda tafito doguwar riga marar nauyi na material tasanya, ba kaɗan ba kayan ya amshi jikinta, mayafin kayan kawai tayafa akanta, haɗe da sa kai tafice daga ɗaki, zuwa yanzu abun data keji ya girmemawa tunaninta.+
Kaitsaye wajen Ummie dake tare , da baƙinta afalo tanufa , kwan ciya tayi ajikin Ummien haɗi da kwantar da kanta abisa kafaɗan Ummi’n,, cike da kulawa Ummie kekallonta haɗi da cewa ” maike da munkine Farhana , keda zuwa yanzu yakamata ace kinshirya amma yana ganki haka ? ,,
” bazan iya shiryawaba Ummie, faɗuwar gaba nakeji kirjina yana bugawa da sauri sahanun ki kiji Ummie, ina tsoron abun da zai faru agareni ,, takai karshen zancennata alokacin data ɗaura hanun Ummie akan kirjinta.
Kallonta Ummie tashiga yi har na tsawon wasu sakanni, kafun ta nisa haɗi da cewa ” ki kwantar da hankalinki kinji Farhana, ba bu abun dazai sameki insha Allah, me yiyuwa kina jin hakanne saboda auren ki da za a ɗaura gobe, kar ki wani damu kanki dama duk Amare sukan tsintar kansu acikin irin wannan yanayin,, Ummie tafa ɗi haka dan ta kwantar mata da hankali.
Kwarai ta ɗanji sanyi acikin zuciyarta, dajin maganan Ummie’n dan haka ta miƙe daga jikin Ummien tawuce ɗakinta, da kallo kawai Ummie ta bita harta ɓacewa ganinta.1
tana shiga cikin ɗakinnata kan bed tafaɗa, haɗi da sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi , some minute bacci yayi awon gaba da’ita.
Farhan ne kwance cikin jini akan titi, yayinda Farhana ke tsaye agefensa tamkar statue bata ko motsi, hanun sa ya miƙomata cikin wata irin murya yace da’ita ” zomu tafi Farhana, kizo mutafi karki barni ni kaɗai ina da buƙatarki ako’ina zo mutafi,, daga haka kuma saitaga yadaina motsi komai nasa yadaina aiki,,
Arazane Farhana ta tashi daga mafarkin datakeyi, take jikinta yasoma ɓari zufa yashiga ketowa takowani , saƙo na jikinta , mafarkin datayine yashiga da wowa cikin kwakwalwarta filla filla, a ki ɗime talalumi wayarta dake aje gefen gado, haɗi da dannamawa numbern Farhan ƙira , abun da bata taɓa jiba idan taƙira wayarsa shi taji wato “Switchoff” batayi yun ƙurin sake ƙiraba, tayi cilli da wayar amatuƙar zabure ta mike daga kan gadon , aguje tafice daga cikin ɗakin.
Da gudu ta ƙarasa wajen Ummie dake tsaye idanunta cike tab da ƙwalla, sam bata lura da halin da Ummien take cikiba, rungumeta tayi ta baya haɗe da fashewa da kuka ” Ummie kitai makeni nayi mafarki wai Farhan ɗina ya rasu, kitai makeni Ummie wlhy bazan iya rayuwaba, idan babu shi nima mutuwa zanyi, kitai makeni Ummie kiƙira wayansa, kice yazo gare ni ina buƙatarsa acikin rayuwata,, tana maganar ne cikin kuka.
Hawaye ne suka sauƙo daga cikin idanun Ummien, haɗi da sanya hanunta ta rungume Farhana’n sosai tanamai jin tausayin yarinyar acikin zuciarta.
Janye jikinta Farhana tayi daga na Ummie , haɗe da bin Ummien, da kallon tuhuma , muryarta na rawa tace ” Ummie kuka kuka kikeyi , Ummie… ” Farhana !!! ,, Abba yaƙira sunan ta adai dai lokacin dasuka ida shigowa cikin falon shida Dady,
Fuskokinsu tashiga bi da kallo, wanda ala momin damuwa dana tashin hankali,suka baiyana akansu, kasa koda motsawa tayi daga inda take , sai kafesu da’idanu da tayi.
” Abba ina Farhan ? ,, taje famawa Abba tambayar da baizataba,
kallon kallo Abba da Dady suka shiga mawa juna,
“Yace zaizo gareni Abba kace masa yazo, ina jiransa, yace daga gidan su Jalal nan zai nufo, kaƙirasa kace mai ina jiransa” takai ƙarshen zancennata alokacin da ruwan hawaye ke gangarowa daga kan fuskarta.
Take tsananin tausayinta yacika zuciyar kowa dake falon, cikin rashin kuzari Abba yanufo gareta, hannayenta yakama haɗe da zaunar da’ita akan kujera, cikin tausasa zance dakuma nuna kulawa Abba yace ” haƙiƙa Allah shine ya haliccemu kuma shine yake raya mu , yake kuma kashemu, idan Allah ya ɗauki rayuwarka bawai baya sonka bane, haka idan yabarka aduniya, bawai yafi sonka fiye da wanda yaɗauka bane, haƙiƙa Duk mai aikata aikin alkhairi mutuwa hutu ce agaresa, duk kuma mai rai mamacine , Kiyi haƙuri Farhana haka Allah yatsaramiki, kinyi rashin mahaifiya tun kina ƙarama, yanzu kuma kinyi rashin, babban masoyi kuma ginshiƙi a rayuwarki, kiyi haƙuri da abun dazan faɗa agareki, Farhan Allah yayimasa Rasuwa !!!! ,,
Azabure Farhana tatashi daga zaunen datake, kai tashiga kaɗawa haɗi da ja da baya, wani irin ihu ta kurma daya ratsa dodon kunnen duk wanda ke falon haɗi da zube wa awajen sumammiya.
*😭😭 Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un, haƙiƙa nikaina naji mutuwar Farhan ba Farhana kaɗaiba, Allah yaji ƙanka da Rahama Farhan.😭😭*
*Allah kajiƙan musulmai, Ameen 👏🏻*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{24 Satutday August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣5⃣to 1⃣6⃣*
Akiɗime dukansu sukayi kanta, Ummie ce tashiga ƙiran sunan Farhana haɗi da jijjagata, kuka Ummie tafashe dashi na tsananin tausayin Farhana , batare da ɓata lokaciba Abba ya umarci Ummie data kaita ɗaki , zai ƙira doctor yazo yadu bata .+
drip doctor yaɗau ramata haɗi da bata wasu magun guna yace idan tafarka su bata, domin zata iya farkawa akowani lokaci.
Gaba ki ɗaya Ƴan bikin suna cikin Alhini da kuma tausayin Farhana, domin zuwa yanzu babu inda labatin rasuwan Farhan bai ratsaba, ta sanadiyar haɗarin mota da yayi, take kuma ya rasu batare da ko hospital an kaisaba.
Daga gidan su Farhan kuwa koke koke shiya maye gurbin farin cikin dasuke ciki, a ɗan awannin baya da yawuce, sosai mutuwar Farhan tataɓa ahalinsa, domin shi ɗin mutum ne maison kyau tatamawa ƴan uwansa, haka kuma mutum ne mai raha da shiga zuciya, Momynsa kam tayi kuka harta gode mawa Allah , domin duk cikin ƴaƴanta tafi ƙaunar sa fiye da kowanne, kasan cewarsa mai biyayya agareta. Haka ƴan uwansa suna ji suna gani akayi masa sallah, aka kuma wuce dashi gidansa na gaskia, inda kowannenmu sai yajesa (Allah yasa mucika da imani.)
Tun ana sa lokacin farfa ɗowar Farhana, haddai suka dangana ga Allah, domin kuwa har dare ya raba Farhana bata ko motsaba , haka Ummie taraba dare tana gadin ta waiko zata farfaɗo, amma shiru.
Washe Gari
Zuwa yanzu kam gaba ɗaya hankalin su Abba da Dady yagama tashi, domin dai haryanzun Farhana bata dawo cikin hayya cintaba, saida doctor Hassan yasake yi musu bayani “kan cewa zata iya farfa ɗowa akowani lokaci sannan suka ɗan samu nutsuwa acikin zuciyoyinsu ,,
kalaman Abba sune abun dasuka fara dawowa cikin ƙwaƙwal warta, wani irin ƙara tayi haɗi da ƙoƙarin fusge alluran dake hanunta, wanda tanan ruwan da’aka sanyamata kebi yana shiga cikin jikinta,, saurin riƙeta Ummie tayi haɗi da cewa ” kinutsu kada kiji mawa kanki ciwo,, jin muryan Ummie datayi ya doki dodon kunnenta yasanyata , fashewa da wani irin matsanancin kuka haɗi da faɗawa jikin Ummien, rungumeta Ummie tayi tsam ajikinta , tashiga shafa bayanta a hankali , burin ta baiwuce Farhanan tasamu nutsuwaba.
” da gaske ne Ummie Farhan ɗina yarasu, da gaskene bazan sake ganin saba ? kitayar dani daga wannan mumnunan mafarkin danake dan Allah Ummie kitasheni kicemin mafarki nakeyi, tun kafun nayi hauka, kitasheni kice mafarki nake dan Allah Ummiena takai ƙarshen zancennata tana mai rushewa da kuka, ba Ummie ba hatta Atif da Latifa da suke tsaye bakin ƙofar shigowa ɗakin, saida suka fashe da kukan tausayin ƴar uwartasu, hanu Ummie tasa tashare hawayen dasu ka sauƙa kan kuncinta, cikeda rarrashi ta ƙara jawo Farhana jikinta haɗi dacewa ” kiyi haƙuri Farhanatu haƙiƙa duk wani mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa, tabbas jarabawar kice tazo ahaka, babu kuma wanda ya’isa yasauya tsarin Allah , kiyi haƙuri ki ɗau dangana domin kuwa b……. bata bari Ummie ta karasa zancen nataba , tayi saurin fusge jikinta daga na Ummie haɗe da miƙewa tsaye, duk da kuwa cewa juwa na ɗibanta,
” Jarabawa ! Jarabawa !! fa kikace Ummie maiyasa jarabawata zata zo ahaka ? mai yasa jarabawata zata nisantani da abun sona ? wace kalan ƙaddara ce wannan ? mai na aikata wa u…….
” ya’isa haka Farhana, kada zafin mutuwa yasanya ki saɓi Ubangijinki, wannan bashine tar biyan dana baki ba !! ,, Ummie tafaɗa cikin ƙaraji, domin sam batason zafin mutuwar yasanya Farhana kasa karɓan ƙaddararta.
“Ina roƙon Allah yasanya haryanzu mafarki nake , domin kuwa bazan iya cigaba da rayuwa ba idan babu kai, kadawo gareni Farhan, kada katafi ka barni kokamanta cewa yaune ranar damuketa fatan tazo garemu, kasha faɗamin cewa Abadan munatare, maiyasa sai yanzu zaka tafi kabarni ? maiyasa baka kama hanunaba muntafi tare ? maiyasa zaka barni acikin duniyar da bata da amfani a gareni ? bazan rayu in babu kai ba Farhan , ina buƙatar ka acikin rayuwata kaine garkuwata …. take kuma duhu ya mamaye idanunta haka tatafi luuu ta zube aƙasa bata ko numfashi. Ummie da sauri tayi kanta, tana ƙiran sunanta , batare da ɓata lokaciba Ummi taɗauki wayarta haɗi da danna mawa Abba ƙira.
Ajiyar zuciya doctor Hassan yayi, bayan yagama checking ɗin Farhanan, cikin ƙarfafa guiwa yace ” Haƙiƙa sai kunyi ta katsantsan wajen kula da lafiyarta sbd mutuwar tashiga jikinta sosai, haka kuma tana buƙatar hutu na tsawon 2 days so hakan bazai samu ba dole sai dai, idan bata cikin hankalinta kada kudamu, nayi mata alluran dazasu taimaka wajen bawa jikinta, nutsuwa da kuzari, zata iya kaiwa gobe bata farkaba ,dazaran tafarka kuma zansake yimata wani alluran , because tana bu ƙatar nutsuwa sosai . Godiya sosai Abba da Dady sukayi mawa doctor Hassan , kafun yayi musu sallama yatafi .
Koda labarin rasuwan Farhan ya’isa ga Hameed, baiji koda ɗigon tausayin farhana aransaba, saima sab goginsa da yacigaba dayi, batare da damuwan komai acikin ransaba, duk da kuwa yasan cewa Farhana na kwance ba lafiya.
Kamar yadda dr Hassan ya faɗa hakan ce taka sance domin washe gari Farhana, tana farfa ɗowa yasake yimata alluran bacci.
Hawaye ne kawai ke gangarowa daga ida nun ta, zuwa yanzukam tagama aminta cewa ” Farhan ya mutu ya barta, takuma kudurta aranta cewa rayuwa mai daɗi yaƙare agareta, tana matuƙar son Farhan ɗinta fiye da yanda take son kanta, amma haka Allah ya ƙaddara mata, baza su rayu tareba, kuka mai sauti tafashe da shi asakamakon tunowa da kalamansa masu daɗi agareta datayi, daidai lokacin Ummie tashigo cikin ɗakin,
cike da kulawa Ummi takamo hannayen Farhana’n haɗi da cewa ” kiyi haƙuri Farhana ki ɗau ƙaddararki aduk yanda tazo miki, idan kikayi hakan saikiga Allah ya musanyamiki , da mafi alkhairi agareki ,,
” Nagama soyayya aduniya Ummie, nama tsani duk wani namiji da zai kusantoni , da kalmar soyayya , bazan taɓa yin aure ba Ummie tunda dai narasa Farhan, to Ummie bazan kuma yin soyayyaba ,, Farhana tayi maganar cike da raunin zuciya.
“kidaina faɗin haka Farhana, yakamata ne kizama mai tawakkali dakuma yarda da ƙaddara , zakiyi Aure Farhana insha Allah nan bada jimawaba,,
Wani irin kallo Farhana kejifan Ummie dashi, mai ɗauke da alamomin tambaya.
Sorry kuyi manage yau bansamu enough time nayi typing ba , wannan ma da ƙyar nayishi ,👏🏻
Whatsapp no
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{25 Sunday August 2019}~
*Wattpad*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣7⃣*
” Kada kice haka Ummie, dan Allah naro ƙeku kada kuce zaku sake yimin batun Aure daganan har ƙarshen rayuwata, domin bazan iya rayuwa da kowa ni namiji ba’a duniyarnan matu ƙar ba Farhan ɗina bane ya dawo gareni,, Farhana tayi maganar cike da raunin zuciya.
Ajiyar zuciya Ummie ta sauƙe , domin ta lura zuwa yanzu Farhana kam tayi nisa bata jin ƙira, sai dai addu’a .+
Hajiya Kaka ce taturo ƙofar ɗakin Farhana’n, ta shigo bakinta ɗauke da sallama, Farhana naganinta ta tafi zuwa gareta, haɗi da rungumeta ta fashe da kuka mai ta ɓa zuciya , a maimakon Hajiya Kaka ta lallasheta, sai itama ta fashe da kukan, tausayin jikarta tan, domin itama ta ɗanɗani zafin Mutuwar miji, dole kuwa ta tausayamawa ƴar marainiyar Allah Farhanatu.
Da ƙyar Ummie ta lallaɓa Hajiya Kaka tayi shiru, domin Farhana kam bamai jin rarrashi bane, koda yaushe idanunta cikin tsiyayar hawaye suke, tamkar an buɗe famfo.
Yau kwanan Farhan Uku da rasuwa, amma har yau ɗin Farhana bata dawo dai dai ba, tamai da kuka abincinta kuma ruwan shanta, koda yaushe tana kan gado tana kuka, salla ne kaɗai ke tada’ita, Ummie da Abba sunyi lallashin amma abun yaci tura, dole haka suka haƙura suka sanya mata ido. Yanzuma Ummie ce ta matsamata akan cewa tayi wanka suje gidansu Farhan, tayi mawa iyayensa ta’aziya, ko da tashiga cikin toilet ɗin saida tayi kuka mai isarta , sannan tasamu tayi wankan da ƙyar, kasancewar yawan kukan data keyi dakuma rashin cin abinci da ba tayi , ya haifar mata da wani matsanancin ciwon kai.
Ko mai bata shafa ajikintaba, balle uwa uba Powder , wata zun buleliyar doguwar rigan abaya, tasanya wacce dagani kasan tai mata yawa, haɗi da sanya wata ƙatuwar Hijab ,da tsayinsa yawuce guiwarta, ko mirror bata kallaba haka tafice daga cikin ɗakin. Sororo Ummie tayi tana kallon baƙon al’amarin da Farhana ta tsiro dashi, lalle tana da yaƙinin Mutuwar Farhan , shizai sauya Farhana daga ɗabi’unta na da, hanunta Ummie ta kama suka fice daga falon, dai dai zasu fita , shi kuma Hameed zai shigo.
Cike da ladabi ya rusuna yagai she da Ummie, ta amsa masa cikin sakin fuska haɗe da sanar dashi inda zasu,, ta ɓe bakinsa yayi haɗe da jifan Farhana da wani irin mugun kallo, yasakai ya wuce abunsa batare daya sake ce dasu ƙalaba,, itakamma Farhana batasan yana yiba domin bata da lokacinsa ayanzu. Mota suka shiga, yayinda driver ke jansu har zuwa gidan su Farhan ɗin.
Suna shiga cikin farfajiyan, gidan hawaye yashiga gan garowa daga cikin idanun Farhana, domin gani take kamar zatayi tozali da Farhan ɗinta, yace mata bai mutu ba da ransa.
Ganin haka ya sanya Ummie kama hanunta suka nufi bangaren, da zai sada su da falon Mahaifiyar Farhan ɗin.
Suna shiga cikin falon Farhana, ta ƙwace hanunta daga na Ummie,
da gudu tanufi wajen Momyn Farhan, dake zaune afalon riƙe da carbi tana lazumi, haɗi da karɓan gaisuwa, faɗawa tayi jikin ta , tare da fashewa da kuka mai sosa zuciya.
Momyn ma kukane ya ƙwace mata lokaci guda, domin ganin Farhana datayi yasake tado mata mikin dake ƙwance cikin zuciyarta.
Kowa dake falon saida ya tausaya masu, da ganin yanda suke kukan kasan cewa, mutuwar ta daki zuciyoyinsu.
Da ƙyar Momy ta’iya controlling hawayenta, haɗi da jawo Farhana jikinta tace ” Kinga yanda ƙaddarar ki taka sance ko Farhana, haƙiƙa ni dake munyi rashi, amma Allah’n daya ɗaukesa yafimu sonsa, haƙiƙa nasan mutuwar Farhan yata ɓaki, amma kiyi haƙuri duk mai rai mama cine, muma watarana haka za’a wayi ga ri babu mu ,,
” Momy bazan iya jure rashin Farhan a rayuwa ta ba, bansan wani irin so nake yi masaba, a she a kwai ranan da zata zo, da ba zan sake jin muryar kaba Farhan ?, a she a kwai ranan da zakayi nesa dani ?, kafa ɗamin dama cewa kanaji ajikinka, ba zamu rayu ta re ba, mutuwa ta rabani da kai Farhan, mai yasa kikayi mana haka mu….. ,, saurin toshe mata baki Momy tayi haɗe da cewa ” kada kiyi saɓo Farhana, zuwa yanzu ba hawayenki Farhan, ya ke da buƙataba addu’arki yake da buƙata ,, Momy ta fa ɗa tana mai sha re ƙwallan da suka cika ma ta idanu.
Cikin sanyin jiki Farhana ta miƙe daga jikin Momy, haɗe da nufar wata ƙofa dake cikin falon, ahankali tatura ƙofar ɗakin haɗi da cusa kanta ciki, rumtse idanunta tayi adai dai lokacin da daddaɗan ƙamshinsa, ya bugi hancinta , hawaye masu zafin gaske ne suka shiga sauƙa akan fuskarta ,, da wani tan gamemen hoton ta tafara yin arba, wanda bazata taɓa manta ranan da ya ɗauketa shiba, saurin ƙarasawa wajen wani hoton sa dake kafe a jikin bango tayi, ya sha kyau cikin wa ta coffee colour shadda , fuskarsa ɗauke da murmushi, saurin ciro hoton tayi haɗe da mannasa acikin, ƙirjinta ta fashe da ku ka mai tsuma zuciya, ” Maiyasa zakamin haka Farhan ? Mai yasa !!!,, tafa ɗi haka cikin ƙara ji,, kuka tashiga yi baji ba gani, tamkar zararriya , haka tashi ga bulayi a tsakiyar ɗakin, komai nasa ta gani saita ɗauka tamanna sa a ƙirjinta, hanu tasa ta ɗauki wani agogonsa, da ke aje kan dressing mirror ɗinsa, yana matu ƙar son agogon, shi da bakinsa ya fa ɗa ma ta ,, bakinta takai kan agogon tayi kissing, ɗinsa haɗe da dur ƙu she wa a wajen ta fashe da kuka,, sautin kukanta shine yajanyo hankalin su Momy gareta, ba tare da ɓata lokaci ba, suka nufi ɗakin da sauri.
Tsabar kukan da tayi har muryanta ya dashe, ya yinda idanuwanta suka kumbura sumtum, ko’i’ya bu ɗesu da kyau bata yi, sun rine daga kalar fari sundawo jajur dasu.
Da ƙyar su Momy suka’iya lallaɓata, suka fitar da’ita daga ɗakin.
Koda suka kama hanyar ko mawa gida, Farhana bata daina kuka ba, Ummie tayi rarrashin harta gaji,, kafun sukai gida tu ni zazzaɓi yaru feta, harta fara masassara,, ganin haka yasanya Ummie, taƙira doctor Hassan akan yazo gida yadu ba jikin Farhanan.
Suna isa gida suka samu tuni ma yazo yana jiransu. kamar koda yaushe yanzu ma allura yayimata, haɗe da sanya ma ta drip na ruwa, take bacci yayi nasaran ɗaukanta.
Numfasawa Abba yayi haɗi da mai da kallonsa ga Dady
yace ” Baikamata ace munzura ido muna kallon Farhana acikin wahala ba, yaka mata ne ace munbi maganar da Dr Hassan yafa ɗa, wato musama ma ta farinciki, saboda Samar da sauƙi acikin rayuwarta, koya kaga hakan ? abba yatam bayi Dady.
Gyara zamansa Dady yayi haɗe da cewa ” hakane amma Yaya kana ganin ta wani, hanya zamu samar mata da farincikin data rasa ?, aga nina mubarta kawai har zuwa lokacin, da Allah zai yaye mata da muwarta,,
Murmushi Abba yayi haɗe da cewa ” Aure zan yi mata nan ba da jimawa ba, kasa’ido kayi kallo, domin kuwa hakanne kaɗai zai sanya taka sance cikin farinciki, na tabbata mijin da zan aura ma ta, bazai kasance mai musguna mawa rayuwar taba, inaso naga Farhana tana walwala kamar yadda take a’da, Aure ne kuma kaɗai zai sanya hakan taka sance a gareta, fatana dai shine kabani haɗin kai.,,
” kada kamanta cewa Farhana ba ƴata bace ni kaɗai, hasa lima kaine kakasance mada dina agareta, kana da ƴancin da zaka yanke kowani irin hukuncine, akan ta bata re da amincewa taba, dan haka komai kayi akanta ba laifi bane,,
murmushi Abba yakuma yi haɗe da jinjina kansa, alamar gamsuwa da magan ganun ƙaninnasa, “Nagode ƙwarai daka fahim ceni Allah yashige mana gaba”
Da “Ameen” Dady ya amsa, daga nan kuma suka shiga hira akan sha’anin duniya.
*(balalle nadinga yi muku long typing , kamar yadda nakeyi a sareenah ba, saboda wani dalili nawa, so pls kuyi haƙuri, randa namuku kaɗan banda enough time ne randa kuma nayi maiyawa topa kusani nasamu lokacine, fatan zaku fahim ceni.)*
Whatsapp no
+23407069399224
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
”’ Phatymerh”’
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~[26 August 2019]~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
______________________________
*Thanks All my Wattpadian fans, ina alfahari daku comment ɗinku yana sani nishaɗi.*
*Nagode da Comment dakuma voted ɗinku.*
*Ina godia sosai sisters musammanma, Jiddab nd HafsaMuhammadHafsa, ana mugun tare 🤝🏻*
_______________________________
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣8⃣*
*Bayan Sati ɗaya*
Gaba ɗaya komai na Farhana ya sauya, kallo ɗaya za kayimata kafahimci cewa tana cikin damuwa.
Ido ta tsuramawa plate ɗin abincin dake aje gabanta, tamkar mai yin nazari ga me da abincin, amma a zahiri hankalinta da komai nata, yatafine izuwa tunanin masoyinta da yayi mata nisa na har abada, tsawon lokaci Ummi dake tsaye bakin ƙofar shigowa falon , ta ɗauka tana kallon Farhanan da’ayanzu ta naƙasta rayuwarta da yawan tunani,
Num fasawa Ummie tayi haɗi da sauƙe ajiyar zuciya, ta nufi inda Farhana’n take.+
Dafa kafaɗarta da ta ji anyine yasanya ta , saurin ɗago kanta don taga ko waye ,, ganin Ummie ce tsaye yasanya ta fashe wa da kuka, haɗi da rungume Ummien, , hanu Ummie tasanya bisa bayan Farhana’n, tashiga shafawa cikin alama ta lallashi,
ko kaɗan Ummie bata yi yunƙurin hanata kukan data keyi ba, saboda wani lokaci kuka rahama ne ga bawan daya ke cikin ƙunci,, saida tagaji dan kanta kafun ta tsagaita da kukan ta shiga sauƙe ajiyar zuciya..
Ganin haka
yasanya
Ummie kama hanunta suka zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon,
“Ba iya nutsuwarki nake soba Farhana, hadda hankalinki da kuma tunaninki, ya kamata zuwa yanzu ace, kin fauwalamawa Allah al’amuranki, kuka da damuwa basune zasu sanya kiji sauƙi acikin zuciyar kiba, bakuma sune zasu gusar miki da raɗaɗin rashin Farhan arayuwar kiba, kidawo cikin hankalinki Farhana, ki koma ga Ubangiji’nki ki ro ƙamawa Farhan, yafiyarsa da kuma rahamarsa, yafi ace ki zauna kina yimasa kuka, hakan ba bu abun da zai haifar, kin hana kanki ci da sha, duk sabo da mutuwan Farhan, so kike kema kikashe kanki ? ,, Ummie tatam baya.
“Zanyi matuƙar farinciki Ummie idan hakan ta kasance, nafiso nima na mutu , domin kuwa rayuwata bata da amfani matuƙar babu Farhan acikinta….
“Ya’isa haka Farhana !! tun da ni ban’isa nafaɗa miki kiji ba, kici gaba dayi !!! Ummie tafaɗi haka cikin ɓacin rai, haɗe da tashi tanufi ɗakinta, tanajin kukan da Farhana’n ta fashe dashi, amma ko juyowa batayiba tashige ɗakinta, domin zuwa yanzu abubuwan Farhana sun soma bata haushi, sai kace akanta aka fara yimawa mutane mutuwa, gaba ɗaya ta hana kanta da ƴan uwanta sukuni.
Kuka sosai tayi kafun daga bisani tasanya hanu, tashare hawayenta, haɗe da jawo plate ɗin abinci’n tasoma tsakuran, kaɗan tanaci, jitayi magani ma yafiye mata abincin daɗi, amma bayanda ta’iya haka tashiga turasa cikinta, domin tayi amanna cewa idan har batasanyawa hanjin cikinta, abinci ba yau, to fa balalle ta’iya kaiwa gobe ba, saboda tsabar yunwa dake nuƙur ƙusanta.
Ahankali tatura ƙofar ɗakin haɗe dayin sallama, cikin sassanyar muryarta da a yanzun ta dashe saboda yawan kuka..
Ummie dake zaune gaban dressing mirror , ta amsamata a taƙaice kuma ci ki ci ki..
jikintane yayi sanyi, dajin yanda Ummie ta amsa ma ta , domin tafuskanci har yanzu fushi Ummie keyi da’ita.
Kaitsaye wajen Ummien tanufa haɗi da ɗaura kanta, bisa kafaɗan Ummien, cikin muryar ta mai sanyi da tausayi, tace ” kiyi haƙuri Ummie dan Allah kada kiyi fushi dani, ki yafe min Ummiena, fushinki a gareni haɗarine,, kafun takai ƙarshen zancennata ma tuni ruwan hawaye sungama wanke mata fuska.
Tsananin tausanyinta ne yadaki, zuciyar Ummie , take itama zuciyarta, ta karye,
Hanunta ta sanya haɗi dajanyo Farhanan jikinta , ƙoƙarin gusar mata da damuwarta Ummie tayi, ta hanyar bata shawarwarin dazasu taimakamawa rayuwarta, dakuma nusar da’ita kan cewa tayi haƙuri da rayuwa aduk yanda taka sance mata.. Haka Ummie tayi ta bata shawarwari har sai da ta fuskanci taɗan sake ranta.
Cike da tarin mamaki Ummie ke kallon Abba, kafun daga bisani ta sauƙe ajiyar zuciya haɗi da cewa
” Banƙi ta ta ka ba Alhaji amma agaskia maganar auren Farhana, yanzu da am bashshi, saboda tana cikin wani hali, baikamata kuma ace ankawomata wani maganar da zai sake tada ma ta da hankaliba,, Ummie tayi maganar cike da al’ajabin halin da Farhana zata tsinci kanta idan labarin ya’isa ga kunnenta.
Murmushi Abba yayi irin nasu na manyan dattawa, haɗi da yimawa Ummie ƙarin bayani da kuma nusar da’ita dalilan daya sanya, yake son Auren Farhana’n kar yawuce 2 weeks masu zuwa .. Duk dacewa Ummie ta fahimcesa, amma tana matuƙar tausayin ɗiyarta da kuma halin rayuwa, da zata fuskanta.
Balaifi zuwa yanzu kam Farhana ta ɗan saki jikinta, domin tana cin abinci, har taɗi da Ummie sukan ɗanyi, saidai duk sanda ta tsinci kanta ita kaɗai a ɗaki, takan zama tayi kuka bana wasa ba.
Yanzuma kwance take kan doguwar kujera, yayinda tayima wa kanta matashi da cinyar Latifa, gefe kuwa Bro Atif ne yaza ge sai basu labaran nishaɗi yake, burinshi kawai shine Farhana taji daɗi, kuma tayi farinciki, balaifi kuma ya lura cewa labaran nashi sun sata nishaɗi…
Ummie ce tashigo cikin falon fuskarta cike da tarin fari’a, bata ko kalli Atif dake mata maganaba, ta kama hanun Farhana suka nufi hanyar fita daga falon,, tun data ga Ummie taji wata irin faɗuwar gaba, haɗi da tsinkewar zuciya wanda bata san daliliba…
Kaitsaye part ɗin Abba taga sunnufa, stiil Ummie nariƙe da hanunta bata sake ba. Abba da Dady haɗi da Hajiya Kaka suka tarar acikin falon, take taji faɗuwar gabanta ya tsananta.. Kusa da Ummie ta zauna, haɗe da soma ƙaremawa falon kallo tamkar wata baƙuwa.
Ƙamshin turarensa shiyafara Ziyarta falon kafun shi ya samu ƙarasowa.. Saurin rumtse idanunta tayi haɗe da kawar da kanta gefe, Allah yasani ta tsani ƙamshin turaren da kuma mamallakin turaren,, sam ko ganinsa bata sonyi.
Kamar koda yaushe haka yashigo cikin falon, fuskarsa ba yabo ba fallasa, haka yake koda wani lokaci abune mawuyaci, kagane farincikinsa, ko baƙin cikinsa,, Miskilin mutum ne na gaske …
Saida ya gaishe dasu Dady kafun yanemi, waje yazauna haɗe da duƙar da kansa ƙasa..
Abbane yayi gyaran murya haɗe da kallon Farhana , data takure waje ɗaya, da hanu yayi mata alama akan tazo, cikin sanyin jiki tamiƙe ta ƙarasa garesa haɗi da zama akusa da ƙafafunsa ta duƙar da kanta ƙasa.
Gyara zama Abba yayi haɗe dacewa ” Hameed da Farhana, inaso ku bani aron hankalinku kuji mai zan faɗa muku, amatsayina na mahaifinku, inada iko kuma da hujjar da zan yanke kowani irin hukuncine, akan Kowannenku … Abba bai kai da ida maganar ta saba,
zuciyoyi biyun suka shiga tsalle da bugawa, wani irin tarin fargaba da tsoro shiyayi nasaran ɗarsuwa azuciyar kowannensu…..
((Topa komai Abba zaice oho 🤷🏻♀))
Whatsapp no
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{27 August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page 1⃣9⃣*
Batare da Abba ya lura da halin da suke ci ki ba yaci gaba da cewa..
” kuyi haƙuri da hukuncin da na yanke a ga me daku, haƙiƙa Mamana (Farhana) kin haɗu da jarabawa da kuma ƙaddarorin rayuwa, kinrasa mahaifiya tsawon shekaru, yanzu kuma kinrasa mutumin da yakasance Garkuwa agareki,, nazauna nayi dogon nazari na kuma ga bai kyautu ace munbarki hakaba, yana da kyau musa ma miki abokin rayuwa, saboda samun nutsuwarki,, da fatan bazaki bani kunya ba ?+
Gaba ɗaya kalaman Abba sun ɗauremata kai, domin sam bata fahimci mai yake nufi ba.. Maganar Abba’nne yasake dawo da’ita cikin hankalinta, inda yake cewa
” Dady,Hajiya Kaka, Ummie, inaso kuzama shaida cewa nabamawa ɗana *Hameed* Auren ƴata *Farhana* wanda za’ayi nanda Sati biyu masu zuwa insha Allah..
Tashin hankali wanda ba’asa masa rana,, Jin maganganun Abban sukayi tamkar sauƙan guduma acikin kawunansu..
Hanun Farhana Abba yakamo cike da kulawa ya ce da’ita ” haƙiƙa nasan balallene kiji daɗin hukuncin dana yanke akanki ba, amma nasan cewa ke ƴa ce mai biyayya ga mahaifanta, inada tabbaci kuma bazaki watsamin, ƙasa a ido ba, ban yanke hukunci saboda son zuciyata ba, sai domin farincikinki, amma matukar kikace ba kyaso, tofa bazan miki dole ba, kada kuma kiji nauyin kowa da ke cikinmu, kisanar dani abun dake cikin zuciyarki, idan ba kyaso bamai miki dole…
Ganin dayayi bakinta yana motsawa, alamar akwai abun data keson furtawa,
yasanyasa sakin wata munafukar murmushi datafi kuka ciwo, haɗi da cewa.
“Alhamdulillahi, haƙiƙa kai mahaifine agaremu, kanada haƙƙin dazaka yanke kowani, irin hukunci ne akan mu, saboda haka dagani har Farhana mun’amince, zamu cika umarninka da yardan Allah babu kuma wanda zai saɓamaka acikinmu,, yakai ƙarshen zancen nasa still yana wannan munafukin murmushin nasa dake ƙunshe da ma’anoni dayawa..
Murmushin jindaɗi Abba yayi, haɗe da godemawa Allah daya basa ƴaƴa masu biyayya agaresa, nanfa kowa dake cikin falon yashiga, sanya musu albarka da nema musu zaman lafiya da juna, Hajiya Kaka kam babu wanda yakaita murnan, kasan tuwar hakan ,,
Farhana kuwa komai nata daina aiki yayi, yayinda tazura masa manyan idanunta da suke zubar da ruwan hawaye, kallonsa take cike da tarin mamaki, duk da cewa shi baiko kalli, inda take ba, tabbas murmushin data gani akan fuskarsa ma kaɗai, ya tabbatar ma ta da cewa yashiryamata wata ƙulleneniya..
Lura da Ummie tayi Farhanan bata cikin nutsuwartane, yasanya ta kama hannayenta suka fice daga cikin falon. Kai tsaye ɗakinta, tanufa da’ita ..
Ummie nafita daga ɗakin. Farhana tarushe dawani irin kuka mai ban tausayi, da tsuma zuciya, kuka take sosai baji bagani, tabbas mutuwan Farhan yajanyomata tonon asiri, lalle ta yarda cewa mutuwar Farhan shine, babban ƙaddararta a rayuwa, tunda gashi ana shirin haɗata aure da babban maƙiyinta Hameed. a ranan Farhana tayi kukan dako sanda labarin mutuwar masoyinta Farhan ya isketa batayi shiba ,, a ta ƙaice dai saida wani zazzafan zazzaɓi ya sauƙa ajikinta, a sakamakon kukan da tajima tana ruska, har yazamana bata ko iya ɗago kanta saboda, tsabar ciwon kai da zazzaɓi.
Tsabar tashin hankali ko ganin gabansa bai iyawa, da ƙyar ya iya kai kansa, part ɗinnasa, kaitsaye bedroom ɗinsa yanufa, yana shiga yasoma watsi, da duk wani abu da yayi arba dashi acikin ɗakin,, stull ɗin dake aje tsakiyar ɗakin, yaɗauka haɗi da wurgi da shi, take ƙaran fashewar tangamemen dressing mirror’n dake kafe jikin bangon ɗakin, ya ratsa kowacce kusurwa na ɗakin, domin kuwa stull ɗin akansa yasauƙa . .
gaba ɗaya yabirkice, idanuwansa sunkaɗa sunyi jajur da su, yayinda bakinsa ke fitar da hucin zazzafar iska,
sam baita ɓa tunanin wannan tashin hankalin zaitun karo saba, wani laifi ya aikatamawa Abba haka, da zai haɗa aurensa da Farhana ? yarinyar data zama tamkar karuwan gida, yarinyar daya kamata da wani ƙato yafi sau a ƙirga, mene sunan sa kenan idan ya auri Farhana ” Mijin Karuwar gida ” wata ɓangare na zuciyarsa tasanar dashi hakan, da ƙarfi yace ” No ! noo !! nooo !!! hakan bazai taɓa faruwa daniba, bazan taɓa zama mijinki ba Farhana, na tsaneki ! banasonki !! bana ƙaunarki !!!, Abba mai yasa kayanke mana wannan hukuncin ? Abba why !!! ? yakai ƙarshen zancennasa cikin ƙaraji, da kuma ƙunar zuciya.
Zama yayi abakin gado, haɗi da rumtse idanunsa, babu abun dayake hangowa acikin idanun sa, face lokacin daya ganta kwance cikin ƙirjin Farhan, yana kissing ɗinta, saurin datse lips ɗinsa yayi, alokacin da hawaye suka sauƙo daga cikin idanunsa zuwa kan fuskarsa, wutar tsanar Farhana ce, kawai ke ruruwa acikin zuciyarsa .. Wani irin mugun murmushi yayi, a lokacin da zuciyarsa tagama haɗa masa tarkon, dayake son jefa Farhana ciki, yajima yana saƙawa da kuncewa, kafun daga bisani ya miƙe haɗe da rage kayan jikinsa ya wuce bathroom..
Baƙaramin ruɗewa Ummie tayi ba, alokacin da ta zo ɗakin Farhana tataradda ita cikin mawuyacin hali, tabbas dama tasan hakan zai iya, faruwa da Farhana’n kasan cewar har yanzu, tana cikin al’ajabin da kuma jimamin rashin masoyinta.. Koda dr.Hassan yazo allurai da magunguna yayi mata, baji mawa tasamu wahalallen bacci yayi gaba da’ita.. Kafun yatafi saida yasake jaddadamawa Ummie cewa akiyaye shiga damuwarta, gudun samun matsala,, godiya Ummie tayi masa kafun sukayi sallama…
Ahankali tasoma buɗe idanunta, da suke cike da tarin ƙwalla. ” Sannu Farhana kintashi ?,,
muryan Ummie yadoki dodon kunnuwanta. Kai kawai ta’iya gyaɗawa alamar “eh” domin sam batajin ƙarfi acikin jikinta.. datai makon Ummie tayi wanka, haɗi da sanya doguwar riga marar nauyi. Saida Ummie tasanyata agaba kafun taci abinci, haɗi da komawa ta kwanta…
Hanunta Ummie tariƙo cike da tausayi haɗi da ƙarfafa guiwa ta soma cewa ” Haƙiƙa bani na haifekiba Farhana, amma soyayyar da nakeyi miki, bazan iya misaltataba, inayi miki soyayyar da banamawa ƴata ta cikina wato Latifa, nice nan naraineki tsawon sheƙaru 20, dan haka nafi kowa sanin halayenki, nasan abun da kikeso da kuma wanda bakyaso, nasan farincikinki nakuma san akasin hakan, kamar yadda nake matsayin uwa agareki, haka nakeso nacigaba da kasancewa agareki, har gaban abada, kimanta cewa nina haifi Hameed, kisanar dani sirrin zuciyarki, nasan a yanzu babu soyayyar Hameed a zuciyarki ko ɗigo, amma inaso ki sanar dani cewa “zaki iya rayuwar aure dashi ko a’a? kada ki ɓoyemin Farhana, amatsayina na mahaifiyarki”
Wasu zafafan hawayene sukayi nasaran, gangarowa daga cikin idanun Farhana, amma saitayi saurin sakin murmushi haɗi da cewa ” Idan Farhana zataƙi kowani namiji aduniya, to baza tataɓa ƙin yayanta kuma ɗan uwanta ba, bazan taɓa bijiremawa Abba ba Ummie, saboda inason Abbana, kowani yakawomin ba Yayana ba, zan Auresa Ummiee…. Kukane ya hanata ƙai ƙarshen zancennata, kawai saita faɗa jikin Ummie tasaki kuka mai taɓa zuciya……
Follow me…
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
~{28 August 2019}~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page 2⃣0⃣*
Rungumeta Ummie tayi tsam, a ci kin jikinta haɗi da shafa kanta ” haƙiƙa kincika ƴar albarka Farhana yanzu na tabbatar da cewa kin riƙe tarbiyan dana baki, bakiyi watsi da shiba, Allah yasanya albarka da aminci haɗi da so da ƙauna acikin *Tarayya* ‘nku da Hameed, Allah yayi miki albarka, yakuma faranta ranki tamkar yadda kika faranta namu ran ” Ummie tafaɗa cike da jin daɗin amincewar Farhana’n+
Murmushin daya zame mata dole tayi, haɗi da sake rungume Ummien tace ” Ameen Ummiena keda Abba kunwuce haka a wajena ,, miƙewa Ummie tayi haɗi da cewa tana zuwa, tafice a ɗakin. Ummie nafita Farhana ta rushe da kuka, wani irin ciwo da raɗaɗi take ji acikin zuciyarta amma yaza me ma ta dole ta amince da zaɓin iyayenta, ko da hakan nanufin rasa ranta , baza ta taɓa bijiremawa maganar Abba ba, domin shi ɗin yayi ma ta abun da a duniya babu wanda yayi ma ta shi. Ya nuna mata soyayya tsa gwaransa, duk da cewa ba shine mahaifinta ba amma yabata ilimi, tarbiyya, haɗi da kulawa, uwa uba kuma Ummie wacce ta za me mata uwa ɗaya tamkar dubu, batason ganin ɗigon damuwa ya bayyana akan fuskarta, ta shaida cewa Ummie tsananin, soyayya, take yi mata, tun tana yarinya har kawo yanzun, Ummie bata taɓa musguna mawa rayuwarta ba, bakuma ta bari wani ya musguna mata,, me sunanta kenan idan harta butulce masu, ta hanyar ƙin auren ɗansu, duk da cewa shiɗin yakasance maƙiyinta, amma bazata ƙi mawa iyayenta biyayya sabo dashi ba.. Hanu tasanya akan fuskarta, haɗi da share hawayenta, ta ɗaukar mawa kanta alƙawari’n cewa zatayi biyayya ga mahaifanta, zakuma ta cigaba da roƙamawa Farhan ɗinta gafaran Ubangiji, amma tasan cewa abune mawuyaci zuciyarta, tasake son wani namiji a duniya, bayan Farhan ɗinta…
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗani, Beedah ke kallon Ummie , cikin sarƙewar murya haɗi da tashin hankali tace “Wallahi bazai taɓa yiwuwaba, bazan taɓa amincewa ba, Hameed nawa ne ni kaɗai, bazan kuma taɓa yarda wata banza ta mallake shi bayan niba, dama najima da sanin cewa ba sona kukeyiba, shiyasa kuka ɓullo da maganar ƙarin Aurensa, amma zanyi maganin abun, domin ni Beedah ba irin matan nan bane da ake mawa kishiya. Tana kai ƙarshen zan cennata tafice acikin falon tamkar kububuwa,,
sam Ummie batayi mamakin rashin kunyar da Beedah tayi mata ba, domin ita tajima da gane cewa ” yarinyar bata samu kyakkyawan tarbiya ba, bata kuma iya girma ma nagaba da ita ba, kuma Aurene dole sai anyishi, koda hakan nanufin barin Beedah gidan…
Tanashi ga cikin bedroom ɗinta, tashiga watsi da kayan shafanta dake, gaban dressing mirror haɗi da cewa ” ƙaryane wallahi, bazai taɓa yiwuwaba indai ina da rai , Hameed bazai taɓa yin Aure ba daga kaina ya rufe, babu wanda ya isa ya rabani da mijina, natsaneki Farhana ! natsaneki, tsana mai tsanani kuma ni ce nan ajalinki, matu ƙar ki ka auri mijina !!!
tana maganar ne cikin ihu da ƙaraji haɗi da buge buge, tamkar wata mental problem, durƙushewa tayi awajen tana kuka, gaba ɗaya tayi buji buji da ita, yayinda wasu daga cikin kwalaben da ta fasa, sukai mata rauni a hanu..
Sautin kukanta shiyayi nasarar janyo, hankalin Hameed da yanzu shigowarsa cikin falon, batare da ɓata lokaciba ya nufi ɗakinnata, hankalinsa tashe…
Lokacin daya isa ɗakinnata kwance yatarar da’ita , sai kuka take baki ɗaya tafice a hayyacinta..
Saurin ƙarasawa gareta yayi cike da mamaki yace ” Beedah lafiyanki kuwa ?
” Kada kasake ka matso kusa dani !!!,, Beedah tafaɗa cikin ƙaraji.
Tsayawa yayi cak daga inda yake, haɗi da kafe ta da mayun idanunsa da suka fi komai ɗaukar hankali ajikinsa, wani irin kallon mamaki yake jifanta dashi, yayinda ita kuma ta cigaba da rera kukanta,,
ƙoƙari yayi wajen danne tarin damuwarsa haɗi da ƙarasowa gareta,, ɗagota yayi ca ɗak zuwa jikinsa, batare daya kulata da yanda take turje masa ba yanufi bathroom da’ita..
Duk da turjewan da takeyi, bai hanasa yi mata wankaba, haɗi da naɗota acikin towel tamkar ƴar jaririya, kai tsaye kan gado yakaita ya shimfiɗeta.. Lotion ɗinta yaɗauko yashiga shafamata, koda yagama shafamata mai ɗin, wata rigan bacci marar nauyi yasanya mata, ba laifi tayi mata kyau ƙwarai, saida yatabbatar yagama kimtsata kafun ya shiga gyara wajen data hargitsa,, yana gamawa yashiga bathroom shima don yin wanka ..
Koda yafito daga wanka, Brown jallabiya, yasanya haɗi da feshe jikinsa da dadaɗan turarensa, mai sanyaya zuciya, kaitsaye kan gadon yanufa, ya kwanta haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.
Koda taga ya kwanta haɗi da juyamata baya batare, da ya ce da ita ƙalaba yasanyata, fashewa da kukan munafurci, da kisisina.. Jin kukanta yasan yashi saurin juyowa gareta haɗe da jawota jikinsa, Yashiga shafa kan cikinta a hankali,
Yanda yaga bakinta na motsine, yasanyasa gano cewa a kwai abun da take son faɗi , dan haka baijirayi komaiba ya haɗe bakinsu, waje ɗaya,, wani irin hot kiss yake yimata, haɗi da sanya hanunsa abayanta yashiga shafa wa ahankali,, Sosai ya ƙware wajen iya sarrafa mace, da sanyata cikin feeling, koda kuwa itaɗin dutse ce, idan ya raɓeta saita tsinci kanta cikin feeling, lol.
Wani irin hot romance yake yimata, wanda yayi sanadiyar mantar da’ita duniyar da take.. gaba ɗaya numfashinta ɗaukewa yayi, alokacin da taji tattausan labɓansa sun sauƙa akan nipples ɗinta, cike da salo haɗi da ƙwarewa yashiga sucking nipples ɗinnata, daga ƙasanta kuwa hannayensa yasanya yana wasa da’ita… Saida yatabbatar da cewa Beedah tagama fita hayyacinta , kafun ya cillata wata duniyarsa ta daban..
Washe Ga ri
Tsaye yake agaban Mirror ɗin ɗakinsa, yayi kyau matuƙa cikin shigar blue sute ɗin dake jikinsa, mai matu ƙar kyau da tsada, yayin da parking shirt ɗin ta kasance milk colour , sosai tsantsar kyawunsa ya bayyana, yayinda mans pride ɗinsa dake kwance luf kan ƙuncinsa yake ƙyalli da walwali, because yasha gyara ba kaɗan ba…
Yayi mata matuƙar kyau sosai, kyau da adonsa haɗi da ajinsa, su suke tai makawa wajen ƙara ruramata wutar ƙaunarsa, acikin zuciyarta. Wasu zafafan hawaye ne suka samu damar sauƙowa akan ƙuncinta, asa kamakon tunowa da maganar ƙarin aurensa da tayi.
Sarai ya fuskanci irin tarin da muwar data ke ci ki, dan haka yasanya hanunsa yajawota jikinsa, haɗe da matseta cikin faffaɗan ƙirjinsa, cikin sigar lallashi yace da’ita
” Nasan daga jiya zuwa yau kina cikin damuwa, abisa maganar da Ummie taga yamiki, So ki kwantar da hankalinki my Beedah ,insha Allah zan kasance Adali atsakaninku. Yana kai ƙarshen zancennasa yajanyeta daga jikinsa haɗe da sa kai yafice daga ɗakin..
Wani irin kuka ne yaƙwace ma Beedah alokaci guda, haɗe da ɗaukan wayarta ta danna mawa aminiyarta Murja ƙira , bugu biyu Murja ta ɗauki wayar haɗe da cewa ” Ƙawata kuma mata agidan *Gwarzon Na miji* ya akayi ne ƙira da…
Kasa ƙarasa maganar Murja tayi, asaka makon kukan da taji aminiyar tata nayi baji ba gani.
Cikin tsananin tashin hankali Beedah tace da Murja ” ƙawata kizo gida kisameni please ,, tana kaiwa ƙarshen zancennata ta kashe wayar haɗi da jifa da’ita kan gado,, damuwa ne fal cikin zuciyarta, haƙiƙa tasan Hameed mutum ne mai tsananin biyayya ga mahaifansa, kuma idan tayi sake to fa tabbas tanaji , tana gani zai auri Farhana , duk da tasan irin tsanar da Hameed ɗin yayi mawa Farhana’n..
Haka Beedah tazauna tacigaba da ruskan kuka, zuciyarta cike da tarin baƙin ciki..
Mintuna ƙalilan Murjanatu ta iso cikin gidan, kai tsaye part ɗin aminiyartata tanufa..
Beedah na ganin Murja ta shigo cikin ɗakin, tatashi ta faɗa jikinta haɗe da fashewa da kuka.. Amamakance Murja ke kallon aminiyartata, yanda take kuka, tsakaninta da Allah. Lalle tasan babban abune ya faru ga Beeda’n yanda taga tana kuka, a iya saninta da Beedah bakowani, abune yake sanyata kuka ba, sai abu mai girma kama hanunta tayi suka zauna akan gado….
Follow me….
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MENENE MATSAYINA ?_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to My Lovely sister Maryam*
*🌈Kainuwa Writers Association*
~https://www.facebook.com/kainuwawriterassociation~
*Wattpad*
@Fatymasardauna
*Editing is not allowed 📵*
*Page 2⃣1⃣*
Kama hanunta Murja tayi suka zauna akan gado haɗi da cewa ” kisaurareni Beedah kidaina kukan nan haka, kina ɗaga min hankali, kisanar dani maike faruwa ?,,
Ƙoƙarin daidaita nutsuwarta Beedah tayi haɗe da cewa ” ina cikin gagarumin matsala Murja, kinsan girman masifan danake ƙoƙarin fuskanta kuwa Murja ?,,+
Cike da mamaki haɗe da tsoro Murja, kekallon ƙawar tata domin abun yasoma bata tsoro ji datayi Beeda na ambato masifa.
” Murja yazanyi da rayuwata, idan har Hameed yayi min kishiya ina zansanya kaina kinfi kowa sanin wacece ni, dakuma yanda natsani kishiya amma wai sai gashi ana ƙoƙarin tozartani, ta hanyar yimini kishiya !!! Beedah tayi maganan cikin fushi.
Dariya Murja ta kwashe da shi , haɗe da tauna chewing gum ɗin dake bakinta ,
har sai da yayi ƙara ƙass, hanunta tashiga tafawa haɗe da cewa ” kin bani mamaki Beedah, ashe har yanzun baki da wayo, dama kekinsa kankance akan cewa Hameed dake kaɗai zai rayu ? hmmm to kifarka daga nannauyan baccin daya ɗaukeki, domin kuwa Hameed baya yimiki soyayyar da zai zauna dake ke ɗaya har tsawon ƙarshen rayuwarsa …..
” Ya isa haka Murja !! bana ƙiraki bane dan kiɓata min rai, naƙirakine domin kiban shawara , kinsan cewa ina matuƙar son Hameed zan kuma iya kashe kowa sabo da shi,, Beedah ta katse Murja daga maganar da takeyi.
Lura da Murja tayi cewa ƙawartata ta ɗauki zafi tamkar wuta, yasanyata gyara zamanta haɗe da sanya hanu ta dafa kafaɗun Beedah cikin ƙarfafa mata guiwa tace ” Kinutsu Beedah musama wa kanmu mafita, domin sanin kankine cewa damuwarki damuwata ce,,
“tayaya Murja kike ganin zan iya samun nutsuwa, bayan kinsan cewa a duniya ina matuƙar son Hameed, mafita nake nema Murja cikin gaggawa,, Beedah tayi maganar a ƙagauce.
Ajiyar zuciya Murja ta sauƙe haɗi da cewa ” Mafita ɗaya ce Beedah ,,
” Wace mafita kenan ?,, Beedah tatambaya.
” Dole ne ki daure zuciyarki Beedah kibar Hameed yayi aure ,,
” kinsan abun dakike faɗa kuwa Murja !! Inbari Hameed yayi aure fa kikace ? ni Beedah inzauna da kishiya ? hakan bazai taɓa yiwuwaba Murja,, Beedah ta faɗa cikin hasala da maganganun Murja.
Murmushi Murja tayi haɗi da cewa ” Amatsayinki na matarsa kinfi kowa sanin halinsa, kinkuma fi kowa sanin wanene shi, duk wani hargaginki bazai sanya shi bijire mawa maganan iyayensaba, bawai nace miki ki barshi yayi aure bane saboda , inason ayi miki kishiyaba, a’a , inaso nanu namiki cewa yanzune lokacinki zai soma, haka kuma yanzune burinki, zai cika wajen ganin kin mallake Hameed batare, da wata matsalaba, kawo kunnenki kiji ƙawata,, batare da Murja tabari Beedah ta miƙomata kunnen nata ba taja wota jikinta haɗi da gayamata wasu magan ganu acikin kunnenta… Dariya Beedah ta kwashe da shi, haɗe rungume ƙawarta ta, ” Inasonki ƙawata, haƙiƙa ke ta dabance, shawararki mai amfanice agareni,, inji cewar Beedah.
Dariya Murja tayi haɗi da cewa ” ba godiya a tsakaninmu ƙawata, kinwuce haka, sai daifa duk maƙircina ina tsoronki, domin kema fa tawani wajen ba sauƙi, tamkar wuta haka kike,, dariya Beedah tayi haɗe da bamawa Murja hanu suka tafa.. daga haka suka shiga kitsa makircin da zasu ƙulla…….
Abu kamar wasa, saigashi maganar auren Hameed da Farhana ya kankama, domin zuwa yanzu har anfara shirye shiryen biki, duk da cewa bawata hidima za’ayiba.. Itadai Farhana duk abun da’akeyi idone kawai nata, domin ganin abun take tamkar almara, amma idan ta tuno cewa babu abun da yagagari ikon Allah, saita dangana lamuranta ga Allah.
kwance take akan gadonta, ta rufa da blanket, yayinda idanuwanta ke kallon sama, aza hirin gaskia, hankalinta baya tare da’ita domin tayi zurfi ƙwarai wajen tunanin masoyinta, da yatafi ya barta cikin kewa.
Da ƙarfin gaske aka banko ƙofar ɗakin, wanda hakan yayi sanadiyar dawo ta’ita cikin hankalinta,, Wani irin mugun kallo yawatsamata alokacin da sukayi four eyes da juna, saurin ɗauke kanta tayi daga gareshi haɗi da sanya hanunta tajawo blanket, anufin tasake rufe jikinta da kyau kasancewar daga ita sai ƴar rigan bacci …
Cike da salon mugunta yasanya ƙafarsa, dake cikin takalmin combat ya takemata hanu,, wani irin ƙaran azaba Farhana tasake, wanda yaratsa ko ina na ɗakin, batakai ga rufe baki ba, ya kuma sanya hanunsa ya daki kan ƴan siraran laɓɓanta, wani irin azaba da raɗaɗi, suka shiga yawo acikin kwakwalwarta, ganin haka yasan yasa yin murmushin mugunta, haɗi da sanya ɗaya ƙafansa yataka kan gadon, da take kwance, take kuma yahaɗe rai, tamkar baita ɓa dariya ba, cike da isa haɗi da taƙama ya ce..
” Bansan zuwa wani tsawon lokaci, zaki fuskanta kinashan azaba a wajenaba, matuƙar kika yarje mawa kanki aurena, haryanzu kinada zaɓi guda biyu, ko kije kisanar mawa Abba cewa ” kinfasa aurena ” kokuwa ki amince ki aureni, wannan ya rage naki, amma inason duk wuya duk tsanani kada kimanta da wannan kalman “Natsaneki !!!” hanu yasanya acikin aljihunsa, haɗi da ciro naira dubu biyu, ya watsamata akan fuskarta, cike da gadara yace ” mace mai mahimmanci da aji ita ake mallakawa soyayya, har kuma abata kuɗin gyaran tsabtataccen jikinta, wanda babu algus acikinsa, haka kuma iya mutumcinki, iya farashinki, ƴan mata,, yana kaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga ɗakin, batare da ko wai wayenta yasake yiba….
Wani Irin kuka Farhana tashiga yi, mai matuƙar taɓa zuciya, yayinda kalamansa suka shiga yi mata yawo acikin ƙwaƙwalwarta,, cikin matsanancin kuka ta soma cewa “Na tsaneka Yaya Hameed !! fiye da yanda kai katsaneni, da inada daman bijiremawa maganar iyayena, to tabbas da a yau na bijiremawa maganar aurenka, ya Allah nayi mawa iyayena biyayya, inaso kazama gatana…. kukanta ne ya tsananta, yayinda zuciyarta keyimata zogi da ƙuna…… Awannan rana Farhana tayi kuka bana wasaba, domin har zazzaɓi saida tayi…..
Rana bata ƙarya..
Domin kuwa yau take asabar kuma ayaune za’a ɗaura auren Hameed da Farhana, gaba ɗaya family ɗinnasu cike suke da murna, domin haɗa auren Hameed da Farhana, da Abba yayi ya matuƙar musu daɗi. Yayinda ɓangaren amarya Farhana kuwa, tatashi da matsanancin rashin lafiya, kasan cewar kwana tayi tana kuka. Da ƙyar Aunty Balaraba (ƙanwar mamanta) ta lallaɓata tayi wanka, Aunty Balaraba da kanta tashiryata cikin, wani tsadadden leshi mai kyau da ɗaukar hankali, wanda yasha ɗinkin riga da skat, duk da cewa Farhanan tayi muguwar rama, amma hakan baihana kayan amsar jikintaba, domin dai hips ɗinta da boobs ɗinta haryanzun suna nan ayanda suke, duk yanda Aunty Balaraba taso, Farhanan ta tsaya ayi mata meckup ƙitayi, da Aunty Balaraba’n ma ta matsa sai ta fashe mata da kuka, ganin haka yasanya Aunty Balaraba, sallaman mai yin meckup ɗin tatafi, domin kuwa yanda taga Farhana na kuka ta tabbata ba yarda zatayi, ayi mata meckup ɗinba…
Ƙarfe 11:00 am daidai dubbannin jama’a manyan Malamai da ƴan kasuwa haɗi da ƴan siyasa, suka shaida ɗaurin auren *Abdoul Hameed Mahmud Chanji* Tare da amaryarsa *Hafsat Ibraheem Abba (Farhana)* Akan sadaki naira dubu ɗari.
koda aka kammala ɗaurin auren, hayaniyan mutanene yacika wajen, kowa da kowa suna taya ango da ahalinsa farinciki, yayinda ango kenuna zallan farincikinsa afili, a baɗini kuwa tashin hankali da kuma tsananin ƙiyayyan amaryar tasa ne ke cinsa a cikin zuciyarsa…
Ɓangaren Farhana kuwa batasan cewa batai komai a kuka ba, saida taji labarin cewa anɗaura mata aure da Hameed, kuka tashiga rerawa baji bagani, domin kuwa mutuwar Farhan ne yadawo mata sabo……
*( Yanzu game ɗin zaisoma )*
Follow me…
Whatsapp no +234 07069399224.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FsboDRFhzcuLvDUNLJLxsr1
*MENENE MATSAYINA ? FANS*
*Idan kinsan bakya karanta book ɗinnan kada kishiga, haka kuma idan kinsan bazakina magana da comment ba kada kishiga dan Allah, domin kokin shiga zancireki.*
*Banason Links, bana son Talle, banson Vedios ko wani irine, banson kowani irin Post ne, only novels kawai.*
*Gareku masoya Menene matsayina ? danku nabuɗe group ɗinnan, fatan bazaku bani kunyaba, wajen yimin comment.*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*_MANENE MATSAYINA_*
*(fictional story)*
*Written by*
Phatymerhsardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*
*Dedicated to my lovely sister Maryam*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
~https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation~
*Editing is not allowed 📵*
*Page 2⃣2⃣*
Haka Farhana ta wuni gaba ɗaya sukuku, yayinda hawayenta kuwa suka kasa tsayawa, ba irin rarrashin da ba’ayi mataba amma taƙiyin shiru, hakan yasanya kowa fita sha’aninta…+
Kwance yake akan makeken gadonsa, wanda yaƙawatu da adon zamani, yakuma sha shimfiɗa ta alfarma. Idan akwai abun da yake da munsa ayanzu, bai wuce wannan laƙabebben auren da aka liƙamasaba, domin kwata kwata shi a tsarin rayuwarsa ma, bai sha’awan yin mata biyu, sai gashi hakan ta kasance dashi. tsuka yayi alokacin da wayarsa taɗau ƙara alamar shigowar ƙira, sam baison damuwa ahalin yanzu, hutu yake buƙata, dan haka amaimakon ya ɗauƙi wayan saima kasheta dayayi haɗi da gyara kwanciyarsa. Haka yayita saƙawa da kuncewa hardai bacci yayi nasaran ɗaukansa,, duk da cewa ba al’darsa bace bacci a kowani time, ko da kuwa dare ne bai kwanciya da wuri…
Kuka Farhana dake durƙushe agaban Abba da Ummie keyi baji bagani, abubuwa biyu ne suka haɗe mata a lokaci guda, na farko shine yau gata zata gidan wani amatsayin mata, ba Farhan ɗintaba, haka kuma yau zata rabu da Ummie da Abba, tatafi can wani gidan da ba’asan daraja da mutumcin taba…
Nasiha mai ratsa jiki, da zuciya, Abba da Ummie suka yimata, wanda rabin nasihar tasu, suna nusar da’itane akan tabi mijinta sau daƙafa, haka kuma tayi haƙuri da halin rayuwa, takuma zamanto mai haƙuri da riƙe sirrin mijinta, da kuma gidan aurenta.. bayan sun kammala yi mata nasihanne kuma suka kaita ga Dadynta do min yayi mata nasa nasiha’n..
Hanunta Dady ya kamo cike da kulawa, haɗi da ƙaunar ƴar tasa, yace da’ita ” Haƙiƙa ke kinsace ƴa mai biyayya ga mahaifanta, ina kuma alfahari dake, akoda yaushe, inada tabbacin bazaki bani kunyaba wajen kyautata rayuwar auren ki, duk da cewa bana tare dake amma nasan cewa ke ɗiyace mai matuƙar hankali, nakuma san abun da kikeso da kuma wanda bakyaso, nasan cewa babu soyayya atsakaninki da Yayanki Hameed, amma ina kyautata muku zato nan gaba, kiyi koyi da mahaifiyarki, Farhana domin ita takasance mace mai matuƙar biyayya agareni, bata taɓa bijiremawa umarni naba koda kuwa sau ɗayane, haka kuma ita macece mai haƙuri, idan kika yi koyi da halayyarta zanyi matuƙar farinciki da hakan ,, kuka Farhana tasanya haɗi da rungume Dady’n nata, daga cikin xuciyarta tana mai jin tausayinsu su duka, kasancewar kowannensu ya ɗanɗani zafin mutuwar masoyi. Ahanakali Dady yasanya hanunsa yashiga shafa kan ƴartasa, yana mai jin tsananin tausayinta, acikin ransa…
Jin da Dady yayi cewa motocin ɗaukar Farhana zuwa gidan mijinnata sun ƙaraso, yasanyashi yimata addu’o’in alkhairi da nasara, haɗi da bata kyautar mota sabuwa dal, ƙirar Matrix, duk dacewa tana cikin tarin damuwa amma kyautar da mahaifinnata yayi mata yafaranta ranta sosai…
Haka Farhana tanaji tana gani aka sanyata a mota, sai gidan Malam Hameed,, (domin tun da aka fara maganan auren nasu yatattara nasa ya nasa shida matarsa suka koma sabon gidan da yagina mai kyau da tsari, dake Gomna road)
Koda suka isa cikin gidan kaitsaye, babban falon dake cikin gidan suka nufa, wanda acikinsa ne ɓangaren Farhana yake, babban falone dake cike da kayan ƙyale ƙyale na more rayuwa, an ƙawatasa da haɗaɗɗun kujeru, na alfarma, cikin falon yana ɗauke da ɗakuna guda uku, daga can sama ma wasu ɗakunanne guda uku, kasan cewar falon mai bene ne, daga cikinsune kuma mallakin Farhana yake shine kuma na ƙarshe,, baƙa ramin dukiya Abba yakashe wajen ƙawata mata ɗakintaba, sai dai ace masha Allah…
Aunty Balaraba da kuma wasu ƴan uwansu nakusa sune suka kawota, koda zasu tafi saida suka sake yimata nasiha, mai ratsa zuciya kafun sukai mata sallama,, koda Farhana taga dagaske tafiya zasuyi su barta ita ɗaya saita sanya musu kuka, haka dai suka ɗan lallaɓata sukai tafiyarsu…
Ganin datayi cewa ta kwashe awanni azaune cikin mayafin daba tasan dalilin sanya mata shiba, yasanyata yaye mayafin tafito da fuskarta dake lulluɓe waje, ahankali tashiga ƙaremawa ɗakin kallo, tabbas ɗakin nata yayi kyau sosai, kasancewar komai na ɗakin favorite colour ɗinta aka sanya.. Kallon haɗaɗɗen agogon dake kafe jikin bango tayi, inda yanuna mata 10:30 pm , ahankali ta zuro da ƙafafunta dake kan gado zuwa ƙasa, batare da ɓata lokaci ba tashiga rage kayan jikinta, haɗi da kutsawa cikin inda take tunanin toilet ne.. tana shiga kuwa tatarar da toilet ɗinne, saidai haɗuwar toilet ɗin ya matuƙar bata mamaki, cox an ƙawatasa sosai gwanin burgewa,,
taɓe bakinta tayi domin ita ba wannanne agabanta ba yanzu. Shower ta kunna haɗi da tsaya wa dai dai saitinsa ruwa na dukanta, tayi hakanne kuma ko zata samu relief daga tarin damuwar dake narke acikin zuciyarta…
Ɗaure tafito daga ita sai towel daya tsaya iyaka guiwarta, kaitsaye gaban dressing mirror tanufa, tashafa mai ajikinta,, wata zundu memiyar rigan bacci mai kauri da duhu ta sanya ajikinta, ko turaren da tasaba shafawa duk daren duniya idan zata kwanta bacci, yau kasa shafasa tayi, haka tanufi kan gadon ta kwanta, haɗi da takurewa waje ɗaya,,
“” Zannuna miki soyayya irin wacce baki taɓa ganin irinta ba My Fana duk ranan da aka kawominke gidana amatsayin mata “”
Wani irin siraran hawayene suka yi nasaran gangarowa daga cikin idanunta, alokacin da maganar Farhan ɗinta yadawo mata cikin ƙwaƙwalwa da kunnuwanta, awani hira da suka taɓa yi dashi can da jimawa, afili ta furta cewa
” lalle nayi rashin masoyi mai matuƙar nuna mini ƙauna. Allah ya jiƙanka Masoyina “”
kasancewar tagaji yasa bata wani jimaba bacci yayi nasaran ɗaukanta…
Ɓangaren Hameed kuwa yanacan tare da Beedah suna shan love ɗinsu tamkar sabbin amare, yama manta da wata wai ita Farhana, saboda zalunci haka yabiye mawa matarsa suka bar Farhana ta kwana ita kaɗai, batare da yaje gareta ba amatsayinta na sabuwar amarya, wacce take buƙatar kulawa…
Cike da mugunta yake juya goran ruwan swan ɗin dake hanunsa, wanda har raɓa yayi sabo da sanyi, ɗan guntun murmushi yayi haɗi da buɗe murfin gorar batare da tunanin komaiba, yashiga tuttulamata akan fusƙarta. Amatuƙar gigice Farhana ta buɗe idanunta, domin kuwa ruwan ya fara shiga cikin hancinta,, dariya yayi wanda yabayyana dimples ɗinsa, haɗi da kashe mata ido ɗaya, lokaci guda kuma ya haɗe fuskarsa tamkar baitaɓa dariya ba cikin lion voice ɗinsa yace ” In 20 minute inaso break fast ɗina yazama ready, ruwankine kitashi ki ɗaura yanzu, ruwankine kuma kizauna.” yana kaiwa nan azancennasa yasakai yafice daga cikin ɗaki,, kuka Farhana tafashe dashi, na baƙin ciki da takaici…….
Pls manage 👏🏻
Follow me on whatsapp.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇