MISBAH BOOK 3 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
watansu guda suka tattaro suka dawo gida Nigeria.
A nan suka tarar da mummunan labari da kuma mummunan tashin hankali na rasuwar Shamsuddeen tare da mahaifin Farida.
Satin su biyu da tafiya hatsarin ya faru da su a cikin garin Kaduna, mahaifin Farida ya je duba Shamsu a ma’aikatar su don ganin ya yake
Www.bankinhausanovels.com.ng
da yadda ayyukan su ke tafiya, dama ya saba kai masa irin wannan ziyarar. Anan Shamsu ya bar motarsa a (office) ya biyo Alhaji Ahmad don dawowa gida tare, a hanyar su ta dawowa tsautsayi da karar kwana suka hadu da doguwa ta taho ba birki ta hada motoci da yawa tayi barna wasu sunji rauni wasu sun rasa rayukan su ciki har da Shamsuddcen da Alhaji Ahmad.
Cikin tashin hankali da damuwa Deeni da Bahijja suka nufi Kaduna inda ake zaman makoki.
Deeni sun iso Kaduna cikin tsananin tashin hankali da dimuwa, musamman Deeni da ya rikice ya tsinci kansa cikin tsananin damuwa da ta sa ya fita daga hayyacinsa, har ma ya kasa jurewa. Idanunsa suka kada suka yi jawur, kukan ma kasa yin sa ya yi, sai tsanannin azabar zafin zuciya.
Rufe idanunsa ya yi tare da daura habarsa bisa hannayensa shi kadai ya san me yake ji a cikin zuciyarsa, mutuwar dan’uwa ba wasa ba, tabbas da akwai ciwo, musamman irin yadda suka taso tare tun suna yara cikin shakuwa da kaunar juna.
Shamsu ya sha karbar laifin Deeni tun suna yara, ya kan sha duka a kan laifin da ba nasa ba, su yi fada, su yi wasa, su yi kuka, su yi dariya tare, haka nan mahaifin Farida ya dauke shi tamkar dansa, ya nuna masa so da kauna tamkar shi ne ya haife shi. Duk wani rikici da tashin hankalin da suka samu a baya bai taba canza so da kaunar da yake musu ba, duk kuwa da cewa ya ji zafi da ciwon abin da suka yi masa. Allahu akbar, duniya ke nan.
MISBAH ta kalle shi cikin damuwa da tashin
hankali, “hakika mutuwar ta taba ta amma tashin
hankalin mijinta ya fi komai daga mata hankali a
yanzu. Cikin mota a hanyarsu ta zuwa gida, Bahijja ta jawo shi jikinta tare da rungumar sa tana shafar sa tana lallashin sa tamkar wani karamin yaro, burinta a wannan lokacin ta samu zuciyar mijinta ta yi sanyi ta samu nalsuwa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Deeni ta dago kansa suka kalli juna cikin fuskar damuwa ta girgiza masa kai tare da shafa masa gefen fuskarsa ta ce: “kar ka yi haka please, ka yi kokarin rike kanka, ka jure, ka yi ta masu addu’a, ka dau tawakkali wanda shi aka san kowane musulmi nagari da shi, shiga damuwa ko nuna tashin hankali ba zai sa su dawo ba, kuma ba zai yi masu wani amfani ba, me zai hana ka yi musu abin da za su fi bukata daga gare ka, addu’a da kuma sadakatul jaziriya, wannnan shi ne kadai abin da zai amfane su ya kuma taimake su.” “Idan muka isa gida mama da baba suka gan ka a birkice, babu abin da za ka kara masu face tashin hankali a kan wanda suke ciki. “
“Yanzu girma ya hau kanka, haka kumal (responsibility) dinka ya karu, ba kula da ayyyukan baba kadai ba hatta kula da su kansu baba da maman da kwantar masu da hankali, kula da abin da yaya Shamsu ya bari, yaransa yanzu ka san kai ne uba garesu. Takalmin yaya Shamsu za ka saka, girma da nauyin gaske ya hau kanka, yana da kyau da matukar muhimmanci kai ma kanka ka samu natsuwa da juriya kafin ka iya daukar wannan nauyin. Cikin sauki, ka yi ta addu’a, ni ma zan taya ka. “
“Na yi maka alkawarin fahimtar ka da ba ka dukkan goyan baya tare da hakuri da juriya a matsayina na matarka kuma abokiyar rayuwarka ka, zan taya ka daukar nauyin da ya hau kanka,
Www.bankinhausanovels.com.ng
kuma na daukar maka alkawarin kula da kai da ba ka natsuwa da kake bukata,”
Rungume ta ya yi sosai a jikinsa yana jin tsananin son ta da wani irin natsuwa da juriya tare da kwanciyar hankali, sai ya ce: “Na gode Bahijja da kika tunatar da ni, tabbas an min mutuwa mai ciwo, amma zan jure in ci gaba da yi masu addu’a tare da daukar nauyin da ya rataya a wuyana, ina alfahari da ke Bahijja, duk rintsi duk wuya kar ki taba juya
min baya. ” “Na yi alkawari Deeni, zan kasance tamkar inuwarka insha Allah.”
Suna isa gida sai suka tarar jama’a duk yawancin sun watse, kasancewar yanzu wajen sati biyu ke nan da rasuwar, sai dai masu zuwa gaisuwa su tafi. Kai tsaye suka wuce bangaren baba. Zaune yake kan kujera, ya dora kafa daya kan daya, idonsa a rufe, alamar tunani mai zurfi yake yi don kuwa sai da Deeni suka yi sallama gurin sau uku sannan ya bude idonsa ya amsa. Ganin Deeni ya sa ya ji wani sabon tashin hankali, ya ji mutuwar Shamsu ta zame masa sabuwa, Deeni ya matso kusa da shi ya zauna kana ya dora hannunsa a kan nasa tare da fadin “sannu baba ina wuni.”
Ya amsa, “lafiya Deeni, ya hanya ya muka ji da
abin da ya faru?” “Alhamdu lillahi,” ya amsa cikin tausayawa sannan ya ci gaba da cewa, “baba mun yi rashi mai ciwo, sai dai shi al’amarin Allah babu yadda ba ya yin abinsa, wannan shi ne iya lokacin da ya dibar
Www.bankinhausanovels.com.ng
masu a duniya, ka ga duk yadda muka kai ga son su, ba za mu kara masu ko minti daya ba a duniya, mu ma lokaci muke jira, wata rana duk wucewa za mu yi. Dan haka sai mu bi su da addu’a don ita suka fi bukata.”
“Haka ne Deeni, Allah ya kara mana hakuri da juriya da su kuma Allah ya jikansu da sauran musulmai baki daya.” Deeni ya amsa da “Ameen.”
Nan suka gaisa da Bahijja kuma taji dadi kwarai ganin yadda Deeni bai nuna wa mahaifinsa abin da zafi ba ko ta sigar da zai daga masa hankali, Ciki ta shiga gurin su mama ta bar su, su sake gaisawa da juna irin na da da mahaifi.
A cikin gida ta gaisa da su mama da sauran jama’a da ba, su tafi ba sannan ta nufi bangaren Farida ta yi mata gaisuwar, ta tausaya mata kwarai, mutuwar miji da mahaifi lokaci guda ba abin wasa bane, dale ne a tausaya wa Farida, tana bukalar jin maganganu masu dadi tare da kwantar mata da hankali a wannan lokacin.
Don haka, ba ta yi kasa a gwiwa ba, ta zaunar da Farida ta dinga mata nasila da fadakarwa tare da buga mata misalai da yawa a kan wasu magbata, ta nuna mata duk mutumin da ya rungumi kaddara mai kyau da mara kyau, ya yarda da ita, tabbas – ladarsa mai yawa tana wurin Allah.
Farida ta ji dadin maganganunta har ma ta saki ranta a kan da, ta mika al’amuranta duka a wurin Ubanginji.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Misbah ta je gidan su Farida tare da Deeni suka yi wa iyayenta gaisawa tare da sauran jama’ar gidan ta’aziya, yayin da shi ma suka yi masa ta’aziyar dan’uwansa, ba karamin kokarin rike kansa ya yi ba, sai ya ji mutuwar dan’uwansa da na mahaifin Farida sun dawo masa sabo, ya tuno shakuwarsu da mahaifin Farida tun yana yaro, bai san lokacin da ya mike da sauri ba ya juya yana sharar kawalla ya fita ba
Misbah ta lura da hakan, sai dai ba ta yi yunkurin hana shi ba, saboda ya samu sauki a zuciyarsa. Tare suka wuce wurin Farida, Deeni ya yi mata ta’aziya tar
e da yi mata nasiha sannan ya fita ya nufi nasu bangaran don ya samu ya dan huce gajiya ya kuma rintsa, nan Misbah ta shiga yi masa hidimar abincin da ya dace ya ci tare da shirya masa bayi don ya yi wanka ya kimtsa.
Yaci abinci. Tabbas, yana jin dadin irin yadda Misbah ke kula da shi, tana kuma ba shi hakkinsa ta kowane bangare.
Deeni ya koma bangaren mahaifinsa, yayin da ita kuma Misbah ta hau hidimar cikin gida da kula da bangaren abincin mama da baba da na Farida tare da yaransu, ta sa ido sosai, sai ta tabbatar kowa an masa abin da ya dace tare da na sauran baki masu zuwa. Haka nan tana kula da yaran Farida sosai har sunyi SABO DA JUNA
Watansu guda a Kaduna sannan suka yi shirin dawowa Lagos domin kula da kasuwancin
Www.bankinhausanovels.com.ng
mahaifinsa na can, wanda kusan ya fi na Kadunan, ga kuma nashi (Poultry farm) din, ga Misbah kuma Asibitinta na bukatarta, yayin da suka yanke shawarar cewa baba zai zauna a Kaduna ya kula da nashi kasuwancin dake wurin, Farida kuwa za ta zauna a nan gidan ta ci gaba da takabarta, ita da yaranta da su mama.
Haka rayuwar Deeni da Bahijja ta ci gaba da tafiya cikin kaunar juna da Girmamawa da sabo mai tsanani da ya shiga tsakaninsu. Rayuwarsu gwanin ban sha’awa, daga aikinsu sai rayuwar aurensu suka saka a gaba. Haka kuma Deeni yana kula da iyayensa sosai Misbah kuma tana ba shi shawara daidai saninta.
Rayuwar Deeni da Misbah, ba mutum na uku. su biyu ne abokan shawara juna, ba sa barin wani ya yi masu shishshigi a rayuwarsu, ko da kuwa sun samu sabani da rashin fahimta, babu mai ji bare ya sani, haka kuma ba sa daukar tsawan lokaci cikin rashin fahimta sai sun yi kokarin fahimtar juna, sabo da shakuwar da suka yi da juna ya sa da wuya daya ya yi zama ba daya, ba su da abokan da suka wuce junansu. A yanzu burin Deeni da Misbah shi ne su samu haihuwa, sai suka dage da rokon Allah ya azurta su da samun zuri’a.
Lokuta da dama Misbah na tsintar kanta cikin kewar danta, sai dai ba ta barin hakan ya dame ta na wani tsawon lokaci. Bahijja, mace ce mai dauriya da juriya tare da zurfin ciki, zai yi wuya ka
Www.bankinhausanovels.com.ng
iya ganin damuwarta ko fahimtar abin da ke damun ta, takan iya hadiye ta shanye shi a cikin ta.
Sai dai irin kyakykywan sanin da Deeni ya yi mata ya sa ya fahimci damuwarta a game da danta wanda ya sanya wa ransa sai ya nemo wa Bahijja danta wata rana ya dawo hannunsu da zama, saboda irin kyautatawa da biyayya tare da soyayyar da Bahijja take nuna masa, hakan ya sa kullum yake so ya ga ya faranta mata, kula da tattali da Bahijja take masa ko shi baya kula da kansa haka.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG