MISBAH BOOK 3 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI
Mun tsaya
Haka nan suke, abokan shawarar juna. Nan ya dagota tare da kifata bisa faffadan kirjinsa, wanda har sai da dukiyar Fulanin ta shiga kogon kirjinsa, ya ji ta tana tadar mashi da wani irin tsananin sha’awa, lallausar fatarta da mamanta masu laushi suka taba shi, ya ji tsananin son ta tare da kaunarta suna ratsa shi, tuni ya ji ya fara fita daga hayyacinsa, take ya soma sumbatar ta da tsotsar duk illahirin jikinta. Ba ta yi kasa a gwiwa ba ko nuna gajiyawa ta ba shi hadin kai tare da yi masa abin da yafi so, tana faranta masa rai. Nan take suka biya bukatun junansu cikin so da tsananin shaukin juna. Abu guda da ya fi burge shi da Misbah ke nan, ba ta taba gundurar sa ko yau ta fita a ransa ba, abin sha’awarta ko da yaushe ya kalleta sai ya ji tana attracting dinsa.
Bayan sun kintsa, sai ya kalle ta ya ce, “Thank you my Misbah, Allah ya yi maki albarka, ina jin dadin kasancewa tare da ke, kina faranta min rai,
Allah ya bar mu tare, ya bar mu har a gidan aljannah.” “Ameen, wannan fata da addu’ar taka suna faranta min rai fiye da komai, ina ji na kamar
sarauniyar mata, Allah ya sa mutuwa ce kadai za ta
iya raba mu, ga kabarina ga naka.”
Ya yi murmushi ya ce, “ga kabarina ga naki, in kin riga ni zan nemi kabari kusa da naki, haka in na riga ki ke ma ki nemi kabari kusa da nawa, zan bar wasiyya a bizne min Misbah kusa da ni.”
Nan ya kara da fadada murmushi ya ce, “yanzu dai kafin a kai ga can, ina’son ki cika min burina, ki ba ni cute girl mai kama da ke,” ya sa hannu ya ja hanchinta ya ce, “irin wannan dogon hancin da wadanna dara-daran idanuwa da dogon gashin nan.
Ta yi murmushi ta ce, “na ji, ni dai namiji nake so mai irin wannan karisma din irin na babansa, tsayayyen namiji mai nagarta mai gaskiya, wanda ba ya tsoro sai dai irin wanna mishkilancin, banda shi mai irin wannan murmushin mai gashin gira mai cute lips da kyakyawan hakora, dogon namiji mai tausayi mai adalci wanda bai taba bin ra’ayin wani, ko kwaikwayon wani sai nasa, wanda wani ko wasu ba sa gabansa, mai yin magana daya, mai rikon alkawari man of his words, zan yi alfahari da samun namiji kamarka da samun da irinka. Tabbas, na san wannan sai godiyar Allah, don ya gama ba ni duniya, sai kokarin samun mu cika da imani, mu sa mu lahira.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi murmushi ya ce, “Allah ya ba mu ikon aikata abin da zai kai mu ga wannan kyakkyawan sakamako duniya da lahira.”
“Amin” ta amsa.
Ya ci gaba ya ce, “Misbah, magana nake so mu yi, da fatan za ki fahimce ni, ba na fatan ki min rashin fahimta, saboda iya gaskiyata zan fadamaki.”
Ta ce, “To, ina jinka Deeni, insah Allah zan fahimce ka ya sauke ajiyar zuciyarsa ya ce, “maganr Farida ce,” ras!ras!ras! ta ji gabanta yana bugawa, tuni taji hankalinta yana kokar gushewa daga jikinta, ta yi mugun rikicewa da rudewa.
Amma sai ta daure ta ce, “ina jin ka.’
Ya ce, “maganr da muka yi da Farida, ta ce ta amince mani, sai dai kin san tsakanina da ke ba boye-boye.”
Ta ce, “haka ne,” a zuciyarta ta fara tafasa da kuna, kafin ma ta kai ga jin mene ne. Ya gyara kwanciya ya kalle ta ya ce, “ba zan samu sukuni da kwanciyar hankali ba har sai na fada maki, saboda fahimtar da kika yi mani zai sa ki fahimchi cewar akwai wani boyayyen al’amari a zuciyata, wanda zai iya kai mu ga rashin fahimta ko kamuwa da zargin juna da zukata da dangartakarmu gaba daya, MISBAH ke ce sirrina kuma ni ne sirrinki.”
“Kwarai, wanna haka yake Deeni.” A hankali ya ba ta labarin yadda suka yi da Farida ta sako game da waya da kuma text, tana tuno masa da irin soyayyar da su ka yi a da, da kuma irin son shi da
Www.bankinhausanovels.com.ng
take, har yanzu ba za ta yi aure ba, kuma ba za ta yi karatu ba, duk da dauriya irin ta Misbah, amma sai da Deeni ya ga rudewa da tashin hankalin karara a fuskarta da tashin hankali mai muni, da yake nuna masa dukkan wani karshen farin cikinsu ya zo karshe, ta kasa furta masa komai domin duk wani attitude ya gani a fuskarta, wanda rabon da ya gan shi tun kafin su yi aure, ya yi saurin jawo ta ya mannata a jikinsa ya ce, “da ma sai da na ce kar ki min rashin fahimta, yadda muka yi na fada maki, ban ce zan auri Farida ba, in kin ji da kyau na ce gudun haduwa nake da ita, saboda na gaya mata karara ta bar rayuwata HAR ABADA tunda ta auri dan ‘uwana duk da ba ya duniyar nan.
Ta dago dara-daran idanuwanta da suk suka yi jajur ta ce, “abu daya na sani, shi ne kai mutum ne mai magana daya, mai gaskiya, mutum ne mai cika alkawari, shi ne Deeni da na sani (A) MAN OF HIS WORDS), kar ka yi kokarin canza wannan sanayyar da nai maka, kar kai kokarin nuna min kai mai fuska biyu ne, ko mai wata boyayyar manufa a zuciya, wanda ya boye min tun farko, har yanzu akwai yarda da aminci a tsakanin mu, na yarda da duk wasu maganganu ka da yi, duk wasu alkawurana ba na fatan hakan, amma in har ka karya naka alkawarin, ni kuma a ranar nawa alkawarin zai cika no excuses.
“Magana daya muka yi muka ajiye kuma har yanzu a kanta muke, daga ni har kai mun san
Www.bankinhausanovels.com.ng
muhimmanci alkawari.” Ta mike tana cewa, “ina ganin dare ya yi, ya kamata mu koma gida.” “Kin san ai nan a jeji kike kuma kina tare da wani ba mijinki ba.”
Maganar ta sosa mata zuciya kamar yadda maganganunta suka sosa masa nasa zuciyar, ta juyo ta kalle shi ta ce, “Ba a jeji muke ba kuma tare da mijina nake ba da wani ba, sai dai nan ba gidan kwana ba ne, ba wajen zamanmu ba sannan kuma ka san garin nan akwai go slow, wannan ya ishe mu a kan hanya duk da dare ne.”
Amma ba ta saurare shi ba, ta zari jakarta ta fita a zuciyarta tana ta mita tana cewa, “Deeni akwai iya fada wa mutum bakar magana ba tare da ya san irin zafin da mutum zai ji a zuciyarsa ba.”
Shi kuwa ya bi ta da kailo yana jin zafin abin da ta yi masa ya ce, “yau Bahijja ta fara nuna min halin nata na cewar ita isshesshiya ce, wannan jin kan take son bullo min da shi,” zamansa ya yi har na mintuna talatin, domin ya nuna mata ita ba ta isa ba, ba ta san halin Deeni ba, ai ba bakonta ba ne don ya nuna mata iyakarta, bai fito a lokacin domin su tafi sai ya nuna mata ba ta isa ba, don haka ta zauna a mota ta zaro (i-pad) dinta tana research da ta saba da karance-karancenta na fanin aikinta, tana yi tana jin zuciyarta na zafi game da zancen Farida da Deeni, ta shiga wani mugun tunani mai zurfi tare da wani irin kishi mai zafi da kuna. Rufe ido ta yi tana addu’a Allah ya yaye mata abin da yake
Www.bankinhausanovels.com.ng
damun ta a yanzu, amma tabbas ta hango masu wani abin da ba ta fatan ya faru.
Har Deeni ya shigo motar amma ba ta san ya shigo ba, sai da ya tayar da motar sannan ta ankara, wannan shi ne ya kara ba shi haushi, a tunaninsa karatunta take ta yi banza da shi saboda yadda ya kura ma (i-pad) din ido, har suka isa gida babu wanda ya ce wa wani ci kanka, tun daga gate maigadi ya ba su l
abarin an yi baki daga Kaduna. Bai kai ga rufe bakinsa ba sai ga su Deeni karami da gudu suna oyoyo yaya uncle Deeni. Kamar a mafarki suka gan su, daga ido da Misbah za ta yi ta hango Farida tsaye bakin kofa tana murmushi, ta sha kwalliya tamkar wata sabuwar amarya mai jiran angonta ya shigo daki.
Nan ta ji gabanta ya vi mugun faduwa, amma saboda ita mishkilar kanta ce kuma yadda ta ji ta a dai-dai saboda abin da ya hada su da Deeni a gidan gonarsu, murmushi ta sakar masu ta bi kan yara tana shafasu tana cewa,
“A’a yau manyan baki muka yi, mai gida na kaina ni kadai, yau sauka a gari babu labari, ta turo baki kamar yadda yara suke shagwaba ta ce, “Ni gaskiya na yi fushi.”
Ya rungume ta yana fadin “sorry Aunty Bahijja, mama ta sa muka zo ba shiri wai dan mu ba ku surprise.”
Misbah ta girgiza kai kana ta kalli Farida ta ce, “Lallai mama ta kyauta dan kuwa ina son surprise wash sannun ku da zuwa.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG