MISBAH BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

“Baba Audi matumin nan yana son raba ni da yata wadda nake jin sonta kamar me, mai yasa na bari suka shaka haka wanda idan bata ganshi ba take damuna da rigima haka sai taje wajansa, Baba Audi ina jin tsoran ranar da Aisha zata fi son wannan mutumin da ni ina son raba DANGANTAKAR su ina so na nuna Aisha tun yanzu ta gane Farouk ba mabaifinta bane bata da kowa a duniyar nan daga ke sai ni ina son ta saba da haka tun tana karamarta ba sai ta girma ba.

Dubata tayi tayi murmushi tace “Bahijia ki

• kwatar da hankalin ki babu wani dan adam da zai iya raba ki da yarki Kima daina wannan tunanin, ki godewa Allah da ya baki wannan mutumin daya mayar da yarki kamar yar cikinsa na tabbata ba yana yin haka bane don yaraba ki da itaba kaunace da kuma haduwar jini na yaro da mai nuna kulawa gareshi: *

Na yarda da Alhaji Umaru na kuma jinjina masa abinda yake mana ni dai abinda nake so a gurinki kina iya daure fishinki akan DANGANTAKArsu da Aisha Allahene ya sa kounar juna a tsakaninsu yake jinta kamar shine yo haifeta.

Sannan b’azan hanaki kin fadawa Aisha wanene ubanta ba tundda dai nasan ko ba dade ko ba jima zata yi miki maganar ina dangin ubanta suke kuma a wannan ne lokacin da zaki nemo amsar da zaki bata amma a yanza yorinyace zaki kirkirar mata damuwa idan kina son raba ta da matumin da take

ganinsa tamkar ubanta kada ki yi haka ki rabu da ita a hankali idan tayi wayo zata gane.

Sai Magana ta karshe shine ya kamata ki gane mai Alhaji Umaru yake nufi akan ki nasan kin san yana sonki son da yake miki yasa ya kamu da kaunar Aisha ni dai idan har zaki tsayar da wani to ni ina goyan bayan ki tsayar da shi.”

Wani irin kallon tashin hankali tayiwa Baba Audi tace “Baba Audi har kin manta abin da ya faru dani kike min wannan kalaman Baba Audi sau nawa nake fada miki cewa bani ba kara aure HAR ABADA kin manta halin da na shiga ko kina tunanin wannnan tabon da mikin da aka yiwa zuciyata ya goge, na roke ki da kada ki kara yi min wannan maganar mutukar kina son gani na cikin farin eiki.

Nan da nan hankalin Baba Audi ya tashi ta shiga rarrashin Bahijja da bata hakuri akan ba zata karayi mata wannan maganar ba mukukar zucigarta zata shiga damuwa ita ma dalilin fadin haka ganin dawainiyar da shi Farouk din yake ne yasa ta fadi haka.”To ya dai na domin bani na saka shi ba.”

Baba Audi tace To shi Kenan duk yadda kika tsara dai dai ne amma dai ina mai baki shawara kina kai zuciyarki nesa akan bawan Allahn nan bai cancanci kina daga masa murya ba ko ba komai anzama daya idan kin ki ba shi zuciyarki bai kamata ki shiga tsakanin sa da Aisha ba amma fa ni anawa ganin.” Tana gama fadin haka ta suri Aisha da ta jima ajikinta tana ta barci suka nufi dakin ta.

Jikin Bahija yayi sanyi ta shiga juya zancen da tayi mata lallai ta fadai gaskiya amma dai zata duba ta gani maganar aure ma sam bata taso ba a tsakaninsu.

Kamar cikin mafarki taji muryar Aisha na tare da bugunta tana cewa “Mama Abba yazo”! “Mama Abba yazo”!! ta shiga fada cikin karaji. nan ta mike tana murtsuka ido nan ta ta shiga kokarin fara mata mita kawai sai da ganta rike da pakage na Bounty a hannunta take ta gane da gasken yazo

Kallonta tayi sosai ta ganta cikin murna da farin ciki na zuwan Abbanta kamar yadda take fadi.

Cikin surutunta domin baki ne da ita sosai ga wayon tsiya domin wayonta har yafi shekarunta yawa, nan tace “Mama ki zo Abba yana waje cikin mota.”

Kamar tace ba zata zo ba domin ta gaji da wannan kwarzabar da Farouk yake mata gwara ta taka masa burki abin nasa ya fara yawa kuma. ganin ta ki mikewa ta shiga jan hannunta ala dole sai ta tashi sunje gurinsa.

Mikewa tayi ta je ta wanke fuskarta tace *ki je kice masa gani nan zuwa.” A guje ta fita tana murna

Hijabi ta danka ta bi bayanta. A cikin mota ta hango shi yasa ta gaba suna ta wasa sai dariya take tayi masa yana tsokanarta, har cikin ranta ta ji dadin yadda yake ma Aisha nan abinda yake mata

sau tari idan tayi niyar yi masa tsiya sai ta fasa ta kara ganin girmansa amma idan ya tabo ta takan iya ajje dukkan kwarjin da girman da take bashi ta fada masa duk abin da yake ranta.

Sallama tayi musu bayan ta kwankwasa glass din motar domin suna ta wasa da Aisha ta dauke masa hankali bai san ta fito ba.

Motar ta bude ta shiga ta zauna a gidan gaba sai dai bata rufe ba duk da kuwa AC din da suke sha ta bar kafarta daya a waje. bai mata Magana ba domin yasan idan bata so zuwan ba ta kan yi masa haka.

Ta fara gai dashi tare da tambayar Muhammad da

Hajiya ya amsa da duk suna lafiya kuma suna gaida ke. Ina amsawa.”Nan ya gyara zama yace “dama zuwa nayi mu yi wata Magana da ke.”

Jin haka nan da nan ta wani daure fuska alumun ranta bai so ba. Murmushi yayi yace “Allah ya kyauta ni dai Doctor zan ga ranar da zan yi miki magana ki saki ranki cikin jin dadi ki bani amsa wannan rashin sausaucin naki yaushe ne zan samu.”

Ta dan saki fuskarta kadan tace “kai nake sauraro.”

“Hmmmm! Dama zuwa nayi nayi mik Magana akan na gaji da zaman ku a nan kauyen lokaci yayi da zaku koma cikin gari domin a saka Aisha na a school ba zan iya jure ganin ta tana zaume a

wannan environment din ba, zaiyi wuya a ce

kullum a dauketa akai ta school a dawo da ita baNa roke ka da ka janye wannan magana babu ita

Aisha a nan zamu rayu da ita har karshen

rayuwarmu ‘ya ta ce ni nake da ikon yadda zan

tsara mata rayuwar da zamu yi ba wani ba.”*

Har cikin ransa yaji ciwan kalamanta nan ya

kalleta yace “ki yi hakuri na yi mantuwa cewa ba

nine mahaifin Aisha ba sau tari na kan manta wa idan ina tare da ita cewa ba ni ne na haifeta ba,

nagode da kika tunatar da ni hakan, bani zan tsara

muku yadda zaku yi komai ba gaskiya ne babu

damuwa ni zan wuce sai anjima.”

Nan ya mai da kallonsa ga Aisha da ke ta wasanta a bayan mota yace “My princess maza zo kije

gurin Baba Audi ta baki kayanki ki zo mu wuce

gida maza sauri ji ki dakko mu tafi.”

Jin haka ta shiga munar da doki da sauri ta dawo

gaban motar ya bude mata ta tafi gudu gudu sauri sauri tana juyowa ta gani ko yana nan. tana

shiga ciki yace ni zan tafi sai an jima,

Jikinta a sanyaye ba tare da ta kara cewa da shi

komai ba ta fito daga cikin motar. fitar ta ba wuya

ya ja motarsa cikin fushi ya bar gurin. Tabbas yau ne rana na farko da ta taba jin damuwar abin da

tayi ma Farouk ko ba koma bai cancanci haka a gurin taba ya wuce komai a gurin ta bai kamata ta

gaya masa wadanna maganganu ba masu zafi har

ta nuna masa cewa shi ba uban Aisha ba ne.

Hmmm