MISBAH BOOK 4 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

aiki da su sai kina biyana da kudin albashin da kike dauka ko ya kika gani.”

Jin haka tayi cikin saurin tace na amince a rubuta kuma, zan baka takarduna ka sama min aikin amma dai babu mai raba ni da kauye duk ranakun aiki zan zauna a nan idan ina off zan koma can da rayuwata.”

Cikin farin ciki yace “duk daya ni dai idan kudina zai dawo bani da matsala kin san mu yan kasuwa bama wasa da kudi duk kankwantarsa.”

“Baka da matsala indai ta nan ne.” ba su jima ba suka bar gidan daga nan ya wuce da su suka gaisa da Hajiya. Hajiya taji dadin ganinsu musamman Baba Audi da basu hadu kwana biyu ba taji dadin dawowarsu kusa da ita anan suka bar Aisha domin taki ta bisu dole Bahijja ta barta suka dawo gida.

Bata koma sabon gidan ba sai da ta tabbatar da samu takardar aikin ta nan a nuna a yi rubutu yace mata kada ta damu yana sane meye abin sauri.

Haka dai ta kama aikin cikin sati biyu da bata offer dama likitar kwakwalwa ce. Cikin jin dadi da walwala ta cigaba da aikin ta kamar yadda ta tsara wata ran tun ranar alhamis take dawowa kauye ta ci gaba da gudanar da aikin ta da kuma duba marasa lafiya. hakan ya kara kwantar da hankalinta.

A yanzu kam Bahijja ta fara mantawa da komai domin yanzu akwai kyakkyawar alaka ita da Farouk sun saba sun kuma shaku abu daya taki yarda masa shine maganar aure haka idan Hajiya ta

• saka shi gaba zai zo yana mata Magana tace ta fada

masa ita bata da wanna burin a rayuwarta. haka zai hakura ya cigaba da lallabata idan ta ga ya takura mata su yi fada.

Ita kanta yanzu ta sakko ta kuma yarda cewa lallai Farouk ya cancanta a so shi amma ida ta tuna yadda suka yi da Deeni yadda ta sakar masa ragamar komai ya zo ya rusa ta yasa take ganin ba zata taba bawa Farouk wannan damar ba duba da sanin halin da namiji da tayi. ta dai fada masa idan zai yarda su zauna matsayin yaya da kanwa to zai samu dukkan kulawa da kauna amma banda maganar aure.

Shi kuwa ganin yadda yake son Bahijja jikinsa kuma yana bashi dole wata rana zata iya futowa da bakin tace tana zata aureshi hakan yasa ya ce da

Hajiyarsa ta kara wani lokacin.

A yanzu dai Bahijia da taimakon Farouk sunyi komai a rubuce na rasu taimaki AL’UMMAR kauven ya gina karamin Clinic da makaranta.

A wannan bangaran kuma haka ya kara bakanta ran Haruna wanda yake shima haifafan kauyen ne dukkan abinda Bahijja take yi burinsa ne amma ta riga shi yi gashi kuma yadda kaf kauyen babu wadda aka daukaka sama da ita maimakon ya fito fili a hada qarfi da shi sai ya boye ya shiga kokarin kirkiro tashi don kawai baya kaunar Bahijja.

Aisha tuni an shiga makaranta mai kyau sai dai a wannan lokacin babu hannun Bahijja akan karatun

Aisha shi ke iko da yarsa kada tayi masa shishshigi dariya tayi tace to ni na isa.

Haka dai rayuwar ta cigaba da gudana. 

Bayan Wasu Shekaru

Lagos

Can ya hango samarin yaran su ciki garden suna zaune cikin nishadi da walwala yaji wani farin ciki yana kama shi yadda kodayaushe zai gansu cikin kaunar juna da farin ciki da juna ya gode Allah yadda ya hada kan yaransa babu wani ki ko wariyar juna haka suke komai cikin so da kaunar juna.

Sanye yake cikin wani farin danyen boyel mai mutukar santsi da laushi. fuskarsa dauke da farin glass wanda ya kara karbar fuskarsa ya karaso gurinsu suna ganinsa gaba dayansu ukun suka mike suka ce barka da fitowa Abba.

Ya dube su cikin sakin fuska yace “Yawwa sannunku ku zauna mana bari na zauna a yi hirar da ni na fuskanci yau yammacin yana muku dadi yanayin garin yau sai godiyar Allah.”

Gaba dayansu suka amsa da “wallahi kuwa.” nan ya zauna ya dube su yace “komawar ku makaranta jibi ne ko sai wani satin ya fada yana mai murmushi.”

Deeni karami cikin murmushi yace “Haba Abba harka manta ne jibi fa zamu koma ba wani satin ba.”

Ok Allah ya nuna mana sai ku fada min abubuwan da kuke bukata ko Mamana da

Muhammad sai kowa ya fadi abinda yake so.”

Shiru suka yi suka zubawa Deeni karami ido suna sauraron mai zai ce. ya bata fuska yace “A na muku magana kunyi shiru kuna kallon mutum ni zan ba da amsar ba duk mu aka tambaya ba.”

A tare suka amsa da cewa Yaya Nuren (sunan da suke kiran Deeni karami da shi Kenan)kai ne babba kai ne ya kama ta ka fada.”

Ok tunda ni zan shiga zuciyarku na zaba muku abinda kuke bukatar.”

Dr. Deeni yayi dariya yace “A’ah babban Yaya banda daukar zafi mana a zatona girma suka baka amma tunda haka ne ina sauraranku kowa ya fada min abinda yake so Mamana ta kanki zan fara fada min naki.”

Cikin jin dadi tace “Abba ni dai dinky zan kara kasan hutun session ne sauran kaya duk sun tsufa kuma gashi zan shiga level two dole sai na kara wanka.” ta fada tana dariya.

Shima dariyar yay yace “A wannan kurarran lokacin mai ya hanaki fadi tun farko ba naga ranan kin ce min kin kai dinki ba.”

Nan ta langwabe kai tace “Eh Abba na kai basu isheni ba ne idan kaban a can Zaria na kaiwa tailor sai yayi min.”

To Mamana babu laifi an gama za’a yi miki abinda kike so.”

” To sai Yaya Muhammad, kai kuma me kake bukata kafin naji ta bakin yayanku.”

Murmushi yayi yace “Abba duk abinda Yaya

Nuren ya fada nima shi nake so. Ok kana son ka fada min baka da choice na abinda dan uwanka ya fada Kenan.”

Tun kafin yace wani abu Aisha tayi karaf tace

“Abba kai ma dai kasan halin Yaya bashi da wani choice na kashin kansa sai abinda Yaya Nuren ya fada gwara ka bar shi kawai tunda shi baya canzawa.”

Cikin nuna girma da son rashin rai ni Deeni karami yace “ke kuma kina bakin ciki idan baki rufe bakin ki zan ballaki.”

Gum tayi da bakin ta don ta san halinsa yanzu tasha bug. Deeni yayi dariya yace “Babban yaya duk abin bai kai haka ba bare har a dora hannu akan Mamana naji na kuma gane ra’ ayin kowa zan turawa kowa kudin da zaku je ku yi siyayya a gobe Alabashi idan akwai wani abu da kuke kuma bukata sai na kara muku tunda dama tuni kowa yayi registration ko.”

Suka amsa baki daya “Eh.”

Yace to babu laifi amma dai sai kun fara sauka a Kaduna gidan Mama kafin ku wuce makarantar ai ko.” suka amsa da “Eh Abba.” nan suka shiga hirarsu. daga nan yace idan basa wani abu za suraka shi wani guri Nuren da Muhammad nan Aisha tayi zagal tace “Abba nima zani.”

Nan Nuren yace “Babu inda zaki je ke kenan kulin kina like da mu.”

“To yaya Nuren wa take da shi bayan mu.” cewar

Muhammad.

Hmmm