gidan idan baka yi dace ba, mutum daya na yarda ya zama abokinki wato Yayanki Muhammad kamar yadda kuke a nan gida a can ma haka zaku zama.
Ban yarda da kula samari ba domin babu abinda za su fada miki sai karya babu so na gaskiya a gurin, idan har zaki bi duk abinda na fada miki to zaki zauna lafiya. ko da wasa ban yarda naji ance kina kula saurayi ba kin dai ji na fada miki tunda babu komai aran su sai tarin karya da yaudara da kasa cika al’kawari akan komai idan sun daukar maka.” Shi Kenan Mama naji insha Allah zan yi dukkan abinda kike so sai dai abu daya zuwa biyu zan fada, Mama yanzu haka zan zauna babu kawa sai kawai ina ta yawo da yaya Muhammad a ko ina kalan a makarantar ana tsokana na bani da kawa sai Yaya na please Mama ki. barni nayi koda daya ne musamman Room mate.” ta fada tana mai turo baki irin na shagwa ba.
Na ji na yarda ki yi guda dayar na biyu dole ya zama Yaya Muhammad ne saboda baki shawarwari masu kyau, amma da zaki bi ta tawa kin gani haka na rayu bani da wata kawa ko aboki domin gudun tsegumi da saka damuwa, amma fa ba nace basu da muhimmanci bane suna da shi matuka amma idan ka samu na gari.”
Shi Kenan Mama zan yi komai a hankali sai na fara karantar mutum kafin na yarda mu fara mu’ amala. Baba Audi ne ta fito daga dakinta tace “‘ah su
indoriya an shirya Kenan sai ta fiya a barmu ko.”
Cikin yanayin shagwaba tace “Granny kina rai na
wallahi zanyi kewarki musamman wannan cinya
da zan dai na jin laushinta.
Cikin barkanci tace “Yar nema baki da abinda
zaki yi kewata da shi sai kafata to tafi abinki nima kafar tayi min sauki na huta da wahal min da ita da
kike yi.
Nan ta turo baki tace “Au haka ma zaki ce korata
kike yi?”
Baba Audi ta rike haba tace “Wace ni da kin tona
zuciyata kin gani da ba zaki fadi haka ba idan a so
nane kada kije ko ina.”
Da sauri taje ta rungume Baba Audi tace
“Yawwa Granny na kada ki damu kullum zamuna
waya dake.”
“To shi Kenan zanke zuba ido.” gaba dayan su suka saka dariya dai dai lokacin da Muhammad da
Abbansu suka yi sallama.
•Da sauri Aisha taje ta rungume shi kamar yadda
ta saba. cikin murna da jin dadi nan tayi masa
sannu da zuwa, ta kalli Yaya Muhammad ta wani
Harare shi har da murguda masa baki. tace
“Abba nasan Yaya Muhammad ne ya tsayar da
kai yasa kuka Makara gashi zamu Makara.”
“To yar rainin wayo nine kika rai na ko sannu da
zuwa baki yi min ba zaki fara min sharri ko ga
wanda kika rai na.” “Eh,
din nasan halin Abba yana mutukar
respecting time a ko wane yanayi yake zai ajje don ya cika alkawarin abinda ya daukarwa kansa na san failure din naka ne.”
Nan ya daga hannu ya kawo mata tayi saurin komawa bayan Abbansu ta boye.
Baba Audi tace To fa ai mai hali baya fasa halinsa yar tsamar nan dai har yau ba zaku dai na ba kai son girma ita kuma tsaurin ido, to haka Kenan zaku na yi a can makarantar taku, idan kun je can tunda ba ni sai ku samu mai rabo a tsakanin ku.
Muhammad yace. “A haba dai Granny sai dai tayi min a iya gida amma a can idan tayi min babballata zan yi babu mai.”Cikin murmushi Bahijia tace “Yawwa My Boy ina bayan ka idan ta yi maka ba dai dai baka hora min ita.”
Farouk yace “Ai kuwa da yaga inda ake hora muutum mutukar ya yarda hannunsa ya kai ga taba min My Princess zai ga yadda zan zo nayi da shi cikin makarantar.”
Duk suka saka dariya bayan sun danyi barkwanci sannan suka gaisa ba bata lokaci ba suka fara haramar tafiya domin jirgi zasu bi suwuce daga nan Gomben. Da Aisha ta ga tafiyar fa ta gaskece nan da nan sai taji zuciyarta ta karaya take hawaye ya fara zubo mata ta rike Baba Audi tana kuka. Me Muhammad zai yi ban da dariya nan fa abin nemaya samu ya shiga yi mata dariya har ta kufula ta fara kuka sosai.
Abban su yace “My Princess rufe bakin ki na baki labarin lokacin da ya fara zuwa da zan tafi ya rike ni katonsa da shi yana Kuka wai Abba baza ka tafi ka barni ba nan ya shiga kwatanta yadda yake yin kukan a wancan lokacin.
Me Aisha zata yi banda dariya nan ta shiga dariya mai isarta nan da nan ta manta tana cikin damuwa shi kuwa Muhammad ya kufula yayi waje abin shi ta shiga fadin Yaya Muhammad yi hakuri zoka daukar min handbag dina.”
Yana jinta yayi banza da ita yai fice warsa.
Bahijja tace “Ni fa na gaji ba za’a na taba min dana ba kai ne dama mai daure mata gidin yi masa rashin kunya bari na bishi na ziga shi. ta fita ya bita da kallo yana dariya.
Nan suka yi sallama da kowa suka kama hanya shine da kansa ya raka su makarantar ya dawo.
Har kullum Dr. Bahijia ta na kara nuna jinjinnawa Farouk yadda yake ma yarta nuna tsananin kulawarsa ga yarta duk da kuwa wanda hakan yasa ta ga bai kamata ta cigaba da zama da shi a haka ba tare da yasan kowa ce ce itaba a wannan lokacin ta gama zayyane masa dukkan tarihin rayuwarta babu abin da ta bari sai dai abu daya da ta fada masa yayi hakuri ta san yana son ta so mai tsanani amma a yadda ta tsara rayuwarta a yanzu babu ita babu aure ta bawa da namiji dama a rayuwarta ya kuma raunana, don haka ta tsarawa kan ta babu ita babu komawa sake aure zata iya rike kanta idan ta rungumi aikin ta da harkokin ta. Bai ce da ita komai baya ce zai cigaba da jiranta har lokacin da Allah yasa ta huce ta nemi ya aure ta da kansa ya nuna mutukar tausayin labarinta a yadda ya nuna mata bai san komai ba sai a wannan lokacin. ya kuma roki ta bashi dama shi baya cikin masu karya alkawari ta dage tace ta gama Magana idan zai yarda da abin da tace to idan ba zai yard aba zata tattara ta koma inda ta fito.
Dole haka ya hakura ya zauna zaman jiran tsammani sai dai Hajiyarsa tayi ta gaji dole ta saka masa idon haka ita ma bata takura Bahijia akan lallai sai ta auri dan ta ba. haka suka cigaba da rayuwa ya dauke ma Aisha duk wani abu da uba zai ma yarsa shakuwarsu da Muhammad dansa tun suna yara har suka girma a nan yake zuwa ya kwana sai da ya fara zama saurayi ne sai dai ya zo ya wuni ya koma. wannnan Kenan.
A wannan lokacin Bahijja bata wani damuwa don haka yanzu hankalinta ya kwanta kawai sai ta ji a yanzu tana da sha’ awar dawowa da rubutun ta sai dai ko kadan bata burin dawo da labarin soyayya sai dai yawan rubutun ta tana yine na fadakarwa akan yaudara da maza kewa mata da zaman ta kewar auratayya. wannan karan salon labarinta ya sauya sosai. Yadda ta tsaya take rubutunta mai ma’ana da kuma fadakarwa dole abun ya tsaya maka a rai
Hmmm