MISBAH BOOK 4 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOBE

Lagos

Zaune yake cikin dakin ya kura ma hoton idan yanajin wanin irin tsananin

kaunarta da kewar ta a tattare da shi, a bayyane yake magana kamar yana kallonta ya shiga fadin.

“Bahijia na Misbah na ina kika shiga

kika je kika buya ban ganki ba, bayan kin san bazan iya rayuwa ba ke ba bazan iya farin ciki babu ke ba bayan kin koyar da ni rayuwa tare da ke.

Misbah na mai yasa kika yi min haka bayan kin san na gama shakuwa da ke mun yi SABO DA JUNA wanda dayan mu ba zai taba jin. dadin rayuwa idan baya tare da dan uwansa ba.

Misbah na nasan ban kyauta mika ba, ban cika miki dukkan alkawarin: dana daukar miki ba na manta da komai na rufe ido har sai da naraba igiyar aure na dake, Misbah na cancanta da dukkan hukuncin da zaki iya yanke min amma ban da yin nisa dani, rashin ki cikin rayuwata, ba karamar min illa ne gare ni ba kin tafi da komai nawa na rayuwata kin tafi da farin ciki na da nishadi na kin na ji rayuwar ta dai na min dadi saboda SAUYIN SHAUKI da na tsinci kaina a ciki.

Misbah ki daure ki yafe min ki dawo cikin rayuwa ta bazan taba samun wani farin ciki ba mutukar ba kyau tare da ni.”

Ji yayi an fuzge hotan daga hannunsa nan ya cira kai cikin zafin zuciya da ciwon abinda a aka yi masa. Farida ya gani tana kallonsa tana wani irin huci da kamar wanda ta wuni tana gudu.

Cikin muryar kuka tace “Deeni nagaji! Deeni nagaji!! Nagaji da wannan rashin adalci da kiyayyar da kake min wai yaushe ne zaka manta Bahijja a cikin rayuwar ka kai Kenan kullum idan zaka kebe kanka baka da wani abu da zaka yi sai dai kawai ka saka hoton Bahija a gabanka kana kallo sai kace tana jin abin da kake fada.

Qarfi da yaji kana son ka zautar da kanka akan wata can wadda bata san kana yi ba da kasan kana son ta mai yasa ka saketa ni da wannan abin da kake min gwara kaje ka dawo da ita na huta amma kai Kenan ka hana min kwanciyar hankali duk sabo da rashinta nifa na gaji idan ka gaji da ni ka sake ni . naje na huta da wannan bakin cikin naka da kullu kake kunsa min ko so kake ka kashe ni, ina son ka fada min yaushe zaka cire Bahijia a ranka dan nima na samu damar morar soyayyyarka da kullum take karuwa a zuciyata?” nan ta karasa fada cikin sautin muryar kuka da garfi.

Murmushin takaici yayi yace “Farida amma dai ke baki da hankali da bakinki kike fada min haka kin gaji kike cewa, kuma har kina tambayata yaushe zan manta da Misbah cikin rayuwata, amsar ita ce HAR ABADA bazan taba mantawa da ita ba, domin ita ce rayuwata, itace farin ciki na, itace nishadi da dukkan wani SHAUKI nawa na duniya ta gaba daya. bari ki ji na fada miki ba wata guda ba, ba shekara ba HAR ABADA Misbah tana cikin zuciya babu wani guri da na bari wandaba itace a ciki ba don haka mutukar ina raye ba zaki taba mallakata ba.

Kamar yadda kika ji dukkan wadannan abu dana fada miki Misbah ta tafi da su kuma nayi miki alkawarin mutukar ina rayuwa sai na dawo da

Misbah cikin rayuwata duk inda take a cikin duniyar nan sai na shiga na dawo da ita mun cigaba da rayuwar mu ta farin ciki kamar yadda muka fara tun farko.

Kina Magana na sake ki wannan shene ganganci na farko da zan taba kamantawa a rauwata, idan kina zaton zan sake ki to tun wuri gwara ki cire wannan tunanin a kwakwalwarki ni da ke babu saki ko yaji idan kin yi ma yaji da kaina zan je biko.

Kamar yadda kika yi nasarar rusa min dukkan

– farin ciki na haka nima na shirya don raba ki da naki, Farida ba karamin kuskure kika yi ba da kika shiga tsanina da farin cikina.

Farida da na so ki so da ban san irinsa ba amma tuda na hadu da Misbah na gane ashe wanda nayi miki na wasa ne na yarinta ne, har yanzu ina kallon ki a matsayin mace mai son kanta mace mara zuciya, Farida har yanzu ina jin zafin wai ina hankali na da tunanina suke da na tsaya na bata lokaci akan ki idan na tuna haka ina yin nadamar bata lokaci na da nayi akan ki. don haka ina mai fada miki baki ga komai ba cikin rayuwarki akan abinda zaki gani nan gaba farida babu son ki ko digon allura a cikin zuciyata duk sona da kaunata gaba daya suna gurin Bahijja.”

Wani irin hawaye ne ya fara zuba a fuskarta tace “Deeni mai nayi maka haka ka tsaneni, bani da kyau ko wani tsari da ba zaka iya dubana kace kana sona ba, ina da wani ciwo ko Nakasa da baza iya kallona kace kana sona ba ka fada min naji kai nake sauraro” ta fada cikin tsawa da tarin masifa akan fuskarta.

Farida kin riga da tuni kin fita a rai na kuma bani da lokacin da zan kara iya dubanki nace ina son ki, ba karya a baya na so ki fiye da tunani na amma a yanzu lokacin haka tuni ya shude dan haka bani da lokacin baki wannan amsar da kika jure min ke da kanki ya kamata ki nemo amsoshinsu da kanki.

Duk da taji zafin kalaman da yayi mata amfani da su sun shigeta sun kuma taba mata zuciya sosai amma haka ta danne sannan tace “Ko mai zaka fada ka fada har kayi nasarar rasa hankalinka idan na tuna haka nasan ko ba komai ba zaka taba manta sona cikin ranka ba, amma na rantse saki ya zamo maka wajibi ka yi min ko kaki ko ka so domin bazan zauna bakin ciki ya kasheni ba.”

Nan zuciyarta ta karye take ta fashe da kuka. bai sake cewa da ita komai baya duka ya dauki hoton

Misbah yayi gaba ya barta cikin dakin tana ta kursheken kuka.

Bin bayansa tayi da kallo cikin a kunar rai da takaicin da ya sata hakika ta kara. tabbatarma da

Hmmm