kanta cewa har yanzu bata gama sanin wane Deeni ba, da dane wani ya fada mata wanna rana zata zo ta sameta zata karyata ko a cikin mafarki bata taba tunanin Deeni ya fito fili ya fada mata cewa yayi nadamar son da yayi mata a baya. «
Lallai yau ta yarda da abin da Deeni ya taba fada mata na cewa shauki na canzawa yau ta ga
SAUYIN SHAUKI ta tsananin gaskiyar abin da
Deeni ya fada a kwayar idonsa na cewa baya sonta yayi kuma nadamar son da ya nuna mata abaya.
Bahijja na tsane kin a tsane ki tsana mai mutukar yawa domin zuwan ki cikin rayuwar Deeni kika tarwatsa min dukkan farin ciki na kin cire sona cikin zuciyar Deeni yadda bazan kuma wani tasiri cikin rayuwarsa ba. Bahijja kin kassara min rayuwata har naji bana wani farin ciki da auran Deeni da nayi don haka naci alwashin ko kin dawo cikin rayuwar Deeni nima sai nayi miki sanadin da ba zaki taba yin farin ciki ba.
Deeni kai ma tunda kace zaka hanani farin ciki na HAR ABADA nima zan yadda na zauna da kai mu zauna cikin kuncin da damuwa. nan kuka ya ci garfinta.
Zaman Farida da Deeni sai gyaran Allah domin kullum cikin tashin hankali da Konawa juna rai suke yi yadda baya ragawa Farida haka ita ma bata raga masa. zaman nasu ya dawo sai addu’a.
A kullum Deeni ya kalli Farida sai ya kara jin tsananin kiyayyarta ta zo masa amma haka yake
hakura ya barta domin zama da ita a haka shine zai sa ya rama dukkan abinda ta yi masa.
Kamar yadda ya saba idan ya dauki lokaci yakan je can Kaduna da duba mahaifansa yau ma haka yayi shi kadai ya zo ba tare da su Farida ba.
Zaune yake gaban Mama suna hira ta dube shi tace “Deeni ka ga kuwa yadda ka koma sam har yanzu baka cikin walwala kamar da anya kuwa Deeni a ce rayuwarka a haka zaka karasa ta cikin kunci da hana kanka cikin farin ciki, ka hana zuciyarka nutsuwa Deeni ina jin tsoran yadda nake ganin yanayinka a kodayaushe ina jin toro kada ka koma halin da ka shiga a baya wai ba zaka hakura ka fitar da Bahijja daga ranka ba .”
Wani irin kallo yayiwa Mama cikin jin zafin abinda ta fada masa yace “Mama don Allah mu bar batun Bahijja komai yakare kuma ko mai ya wuce tunda bana tare da ita a yanzu bana son ana saka ta cikin duk bayanin da zamu yi kunci da damuwa kuwa ban son lokacin da za su barni ba tunda dai anyi nasarar raba ni da su.”
Mama na roke ki da ki bar zancen Bahijja ki manta da komai a yanzu tayi nisa damu babu wani abu da zai sa a dinga kawo ta cikin maganar da zamuyi dake mu barta haka.”
Mama banyi tunanin zaki iya rufe ido ki hanani damar yin farin ciki ba, nayi tunanin zaki na ganin na girma sabanin da da na kasa gane dai dai da rashinsa, amma dai komai ya wuce mu bar wannan maganar ina son ganin Baba mu gaisa da shi
Jiki ba karfi ya tashi bari na shiga mu gaisa da su
Umman Farida.”
Mikewa yayi bai jira ya saurari abinda Maman zata ce ba ya fice abinsa. Hawaye ne suka dinga
•fita daga idanunta sosai tabbas furucin da Deeni yayi mata gaskiya ne itacemafarin komai idan da batadage ta hada auren Deeni da Farida ba da duk haka bata faru ba to amma abin ka da kaddara tun da Allah ya tsara faruwar haka ai dole ne hakan ya faru.”
“Ba kuka zaki yi ba hajiya Aisha ko da yake kece kika so yin kukan kome ya faru a wannan tabarbbarewar ke ce sila.”
Tana jin wannan furucin ta gane mai yinsa
Alhaji Umar ne. nan ta juyo ta kalleshi yana tseye cikin jallabiya mai gajeran hannu idanunsu dauke da glass medicated.
Sannan ya cigaba da cewa “duk naji abinda kuka tattauna ina bayanku ina jin ku. lallai ba muyiwa yaron nan adalci ba a baya na yi alkawarin bazan sake shiga sabgar gidansa ba amma daga baya da kika yi min bayani har na yarda bayan jajircewar da nayi da bazan goya miki baya ba, lokacin idanunki ya rufe da son ganin ya auri Farida.
Hajiya Aisha zuwanki gidan Deeni duk shine ya haddasa haka da kin barsu ya tsara gidan sa yadda yake so da duk haka bata faru ba maganar Deeni ya fitar da tunanin Bahija duk bai taso bana gama karantar Deeni batun yau ba shi namiji ne tsayayye akan abinda yake so idan yana son abu babu mai
iya raba shi da abin haka idan yana kin abu babu wani mahaluki da zai saya so abin nan dole to haka Bahijja da Farida suke a gurinsa.
Idanunmu sun rufe tun farko ga nuna son kanmu sabanin bawa yaron mu abinda yake so, yanzu ya zama dole mu dauke hankalinmu ko yin shishshigi a ravuwar danmu mu barshi ya tsara rayuwarsa yadda yake so tunda mu dukka abinda muke masa sai ya zamo masa matsala amma rashin tsayawa mu bashi damarsa yasa hakan yake ta faruwa don haka mu yi kokarin ganin mun dawo masa da farin cikinsa farin cikinsa kuwa a nan shine mu nemo masa Bahija.”
Kuka Hajiya Aisha ta cigaba da yi tana cewa
“Alhaji a wanna na yarda nice na rusa rayuwar farin cikin Deeni, ni na jefa shi cikin wannan lamura da kai na, domin nayiwa Bahijja Magana da munanan kalamai wanda har yanzu idan na tuna irin kalamn dana jefeta da su nakan ji kunya da nauyin ta na kamani, na zama butulu na manta tarin alherin Bahijja a tare da mu son ganin farin cikin Farida yasa na manta da dukkan alherin da tayi min a baya.
Tunda Deeni ya baro Kaduna ya ji sam baya son komawa domin ya fuskanci can ma idan yaje can sai ya dawo da wani damuwa bayan wadda yake tare da ita a yanzu.
Rayuwar gidan Deeni a yanzu sam babu wani dadi kullum haka zai kebe kansa yana tunanin
MISBAH da yawan tunano yanayin da suke shiga a lokacin suna tare.
Don haka ya ware gidan gonarsa nan ne kadai zai ke tuno masa da rayuwar jin dadinsu da suka gudanar na karshe domin a tun wanna ranar da suka baro gidan gonar basu kara shiga wani
SHAUKI mai dadi ba.
Haka zai shiga tunanin wane abu zai yi a rayuwarsa wanda zai saka shi farin ciki wanda idan ya hadu da Bahija zata yi farin ciki nan kullum zai zauna yana ta tunani.
Farida kuwa kullum damuwa ce take kara daduwa a kanta domin yanzu tsananin kiyayyar da
Deeni yake nuna mata abin yana mutukar bata tsoro domin sashi take a gaba tana kuka akan ta gaji ya saketa amma sai yayi banza da ita sai dai dukka da irin zaman doya da man da suke hakan bai hana shi sauke hakkin auranta akan su. sai dai ita idan tayi masa bure haka zai tattarata ya watsar.
Da haka dai tayi kokarin danne duk wulakancin da yake mata ta rungumi karatunta ta tattara ta watsar dashi sai dai duk abinda suke bai bari abin ya taba rayuwar yaransu idan yaso nishadi zai dauke su ya fita yawo da su ya barta a gida sai lokacin da ya ga dama ya dawo da su wanda ta fuskanci nan ma salo ne ya dakko don ganin ya kona mata rai.
Hmmm