MISBAH CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kwanci tashi ba wuya,bikin su farida ya matso,an gama shirin komai ,’yan uwa da abokan arziki sun gama cika gidajen duka biyu cike yake da jama’a.
Duk wanda ya kalli fuskar shamsu da farida yasan suna cikin damuwa da tashin hankali,kowa kuwa yasan dalili ,don haka dai aka dinga binsu da fatan alkhairi.
Ana gobe daurin auren da safe mahaifin farida yayi kiranta falo,fuskarta a kode kuma a kumbure saboda kullum tana cikin kika. Nan ya sata a gaba yana mata nasiha.me ratsa jiki sosai tare da fada da kuma gargadi na taji tsoron Allah tayi biyayya ga mijinta,ta rungumi kaddarata hannu bibbiyu.
Tana kuka tayi masa godia ,tare da alkawarin zata yi masa biyayya,ta rungumi kaddara ,ta saduuda,Allah ya bata ikon jurewa.
Yaji dadi kalamanta sosai ,ya sa mata albarka sannan ya ce mata Deeni ya kira shi yana son magana da ita saboda duk wayar da zai saneta ya kora a rufe.
” Inaso in ya kiraki ki nutsu ki amsa,kar ki nuna masa komai . Sannan karki fada masa abin da bai sani ba ,kar kiyi yadda zai zargeki. Ki tuna karatu yake yi ,idan yaji wani abu yana iya barin karatun ya dawo,kuma ya samu an daura miki aure,yazo aita rigima dashi ,shi ya rasa ki kuma zai rasa karatun ,kinga ya yi biyu babu kenan. Ni na tabbar in kina son deeni ba zaki so haka ya faru da shi ba “.
Nan ya mika mata wayar,” zai iya kira a kowanne lokaci””.
Gabanta na tsinkewa ta karba tana tunanin me zata ce masa ? Ya zata yi ta fara magana da deni ?
Tana cikin wannnan tunanin kuwa ya bugo ,nan ta zurawa wayar ido da lambobin nasa tana kallo,idonta ya ciko da hawaye ,da kyar ta iya hadiye kukanta ta dauki wayar .
Murya kasa kasa tayi sallama,nan Abba ya mike ya bar falon,don ya basu wuri suyi magana.
Farida na!!!. Deeni ya fada cikin muryar shauki .
Farida I missed u so much,nayi rashinki sosai wayarki da ta umma sam ba a samu,na san dai hidimar biki ne ko ?
Lumshe ido tayi tana jin muryarsa hade da soyayyarsa mai karfi suna ratsa ta .
“Farida kinyi shuru ,kina jina kuwa ?
Ina jinka deeni,ina sauraron daddadar muryar da nayi matukar kewa ne. Deeni kunnuwa na sun jima suna son jin wannan muryar,kasan mun jima bamu yi waya ba ,wayarka ba a kira ,sai dai kai ka kira,in kuwa an kira ma za a ji baya shiga.”
Jikinsa ne taji yayi sanyi,ya rasa dalili muryarta duk ya kashe masa jiki.
_” Farida kiyi hakuri ,ki kuma dada hakuri akan wanda kikeyi ,kinga yanzun mun gama jarrabawa har na samu nasarar shiga aji biyu ,kinga kuwa na fito da result me kyau irin wanda ban taba ba . Inasha Allah kamar yau ne zan gama in dawo “”.
“Nayi murna matuka deeni,Allah ya baka saa ,Allah ya taimake ka. Ina nan ina maka addu’a.
” na gode farida,shi yasa nake sonki,nake kuma jin kamar duk duniya zai yi wuya a samu mace kamar ki. Ya shirin biki? Naji har da ya shamsu ma zai yi biki,ranar muna magana da shi su mama wayar ya yanke ,da na sake kira kuma bai shiga ba. Ya ce mun a unguwarmu take ko ? Kin san wacce yarinya ce ?
Nan da nan ta rude ,ta dabarbar ce ,ta rasa inda zata sa kanta ,baki na bari ta ce.
Ban sani ba “.
Tayi saurin cewa ,baka tambayeni karatu na ba””
Haka ne fa faridana ,in na dawo zaki hada matsayi biyu ai ,mata da kuma malamata,don kuwa darasi zan dunga dauka a gurinki. Tabbas farida inna aureki nayi sa’ar mace ,’ya’yana sai sun min godia da sama musu uwa ta gari.
Kuka me karfi taji yazo mata,tayi karfin halin cewa ,
Deeni umma na kirana ,zan mata wani aikin,sai mun sake waya””
To farida na ,ya amsa .
Kullum kina tuna inasonki ,kullum sonki karuwa yake ,ina nan na rike miki amanar kaina kamar yadda kika rike mun amanar kanki”.
Ba shiri ta kashe wayar ta kwanta a wurin tayi kukanta ta koshi,ta tuno gobe in Allah ya kai mu war haka ta zama mallakin shamsu ,ta rasa deeni har abada.
Bayan ta fita ta mikawa Abba wayar sa ta nufi gidansu deeni ,kai tsaye ta wuce dakinsa domin yin bankwana da shi da memories dinsa. Haka ta dinga bi tana tsince duk wani hotunanta,wasikunta da duk wani tarkacenta da zai tuno masa da ita. Duk wani gift data taba bashi sai da ta tattara . Sai dai tana da tabbacin ba za ta rasa wasu a wurin sa ba,yayin da ta dakko nata gaba daya da ya taba bata ta dawo da su. Duk randa ya dawo yaga haka yasan ehh sun rabu har abada,taci amanar kaunarsu da soyayyar da suke wa juna ,bata rike alkawari ba.
“”KAYI HAKURI DEENI “
Nan tayi kuka tayi kuka har ta gode Allah,yayin da take kallon dakin tamkar yana ciki,tana ganin duk wani shiga da fita nasu da suka taba yi a dakin,fadan su,wasan su,dariyar su da kukansu . Ta tuno da zolaya tare da tsokana irin na Deeni ,sai da tay murmushi.
Ba shiri ta dinga tuno irin ran da ya dinga daukar ta hoto ranar da zai tafi. Bata da yadda ta iya sai hakuri da abinda ya fi kardinta.
Nan ta share hawayenta ta fita,aja kofar.
Tuni taji zuciyarta ta bushe ,hawayen idanunta ma sun bushe ,bata da sauran abinda zai kara daga mata hnkli ko sa ta kuka ko daria ,ko wani farin ciki tunda ta riga ta rasa DEENI ……..
Hmmmmmm…..
Washe gari bayan an sauko daga masallacin juma’a aka daura auren Shamsuddeen da farida,dubban jama’a ne suka shaida ,kasancewar daurin auren dana yan uwanta yasa jama’a sukayi yawa,aka cika,manya da kananan ,talakawa da masu kudin duka wannan ranar unguwar ba masaka tsinke,cike take da jama’a ‘yan daurin aure,’yan uwa da abokan arziki. Bayan daurin aure mahaifansu maza suka shirya gagarumar walima wanka aka gayyaci manya manyan malaman sunnah ,suka zo suka gabatar da wa’azi me tsoratarwa da kuma shiga jiki game da aure. Daga shamsu har farida sun sha jinin jikinsu ,wa’azin ya shige su,suka kara tabbatarwa da fa aure ibada ne ba son rai ko zuciya ba,haka nan aikin ibada zasuyi . In kuwa aka samu akasin haka za su iya fadawa ga halaka,ya zame musu dole su ji tsoron Allah ,suyi aikin auren don Allah don tsoron sa da kuma kwadayin samun rahamar sa. Anan dukkuansu suka kara sakankancewa,suka saduda,suka rungumi kaddara.
Da yamma lis aka tashi daga walimar ,jama’a suka watse ,wanda suke nesa kuwa suka koma cikin gidajen da suka zo,sai washegari su tafi ,saboda su Abba dai sunce ba wani sauran taro ko bidi’a ,wannan daurin aure da walima ya isa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sallar isha’i Abba da kansa ya raka sauran ‘ya’yansa gidajensu,yayin da farida take karshe kasancewarta kusa,nan ya kira farida da kara jan kunnenta da taji tsoron Allah,kada ta kuskura ta biyewa wani son zuciyarta tace zatayiwa mijinta wani rashun kunya ko saba masa,don kuwa aljannarta na karkashun kafar sa,don haka ta bi a hankali tayi masa biyayya ,ta manta baya. Ya kara sa mata albarka na biyayyar da
tayi masa,tare da mata alkawarin cewa zai mata duk abinda take so a duniya muddin bai fi karfinsa ba .
Bayan angama iyayenta mata ma suka bita da tasu kalar nasihohin,sannan Abban da kansa ya rike hannunta tare da kishiyar mahaifiyarta suka kawo ta har gidansu deeni.
Falon baba sukayi da ita,inda mama da Baban tare da shamsu da kuma wasu ‘yan uwan suke jiran zuwan su,nan kuwa suka mike suka tarbe su cikin murna da farin ciki,inda mama ta jawo hannun farida dake ta rusar kuka tace.
” Bari ni dai in amshi ‘yata da ke ta rusa kuka,an rabaki da mama bayan kina tare da daya maman naki ,me zai dame ki?
Nan suka yi daria duka,amma ban da farida da shamsu. Nan dai akayi gaishe gaishe tare da barkwanci ,yayin da aka gabatar musu da abinci da sha ana hira. Sannan Abba ya bada amanar farida ga Alh umar da mama da kuma shamsu.
Sun karba hannu biyu tare da mishi alkawarin farida ba zata taba fuskantar wata matsala ko damuwa ba ,zasu riketa tamkar yar cikinsu . Haka shamsu ma yayi alkawarin riketa amana da kula da ita ,tare da yin hakuri da duk wani abu dazata masa.
Abba yaji dadin maganar sa kwarrai ,nan aka ta saka musu albarka ,yayin da suka hadu duka suka yi musu nasiha sannan suka kara jaddadawa juna yanzu zumunci ya kullu,an zama yan uwan juna .
Bayan tafiarsu baba yasa shamsu a gaba yana gargadin sa da ya rike farida hannu bibbiyu ,ko da wasa kada ya musguba mata . Anan shamsu ya masa alkawarin rikera da gaskia .
Mama kuwa alfarma ta nema abarta tayi rikon farida na tsawon sati biyu a wurinta kafin su tafi gidansu da shamsu.
Baba yace wannan tsakaninki da ita da mijinta ,in sun amincen to,in kuwa ba su amince b babu dole,..”
Nan farida tayi saurin mannuwa a jikin mama tace ,”na amince” Www.bankinhausanovels.com.ng
Mama tayi murmushi tace ,”yawwa yar mama “
Shamsu ya kalle su yana daria ,ya ce
Nima na amince”
Baban shima ya kallesu yace ,” To nima na amince .”
Nan suka sa daria duka,sun jima suna hira a wajen kafin suyi sallama. Shamsu ya nufi dakinsa na gidan ,baba ya yi bangarensa,mama ta ja farida suka yi nasu bangaren. Ta sa mata ruwan zafi tayi wanka saboda tasan tana tattare da gajiya ,ta bata gashasshiyar kaza mai zafi tare da tea me zafi. Bata so haka ta sa ta ci sosai,sannan ta ce to maza ta haye gado ta shige bargo tayi bacci don ta samu hutu.
Bata musa mata ba saboda ita dai farida ko ummanta bata sakewa da ita kamar yadda take sakewa da mama tun tana kankanuwa.
Washegari kuwa ‘yan biki suka watse kowa ya kama gabansa,gida ya saura daga mama sai farida ,shamsu,lukman da masu aiki. A wannan lokacin mama ta samu damar yiwa farida gyara na musammana wanda ta san mahaifiyarta bata samu damar mata wannan ba ,sboda wai kunya da kuma ba wani shakuwa tsakanin su. Dan haka mama ta daukarwa kanta nauyin farida da kula da ita.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
A hankalin ta dinga mata nasiha akan aure,da kuma tadda rayuwar aure take. Ra dinga fahimtar da ita abubuwa da yawa wanda bata sani ba ,ta wani bangaren tana shiga da ita kicin tana koya mata girke girke kala-kala saboda ita mama Allah ya bata baiwar iya girki. Ba anan tsaya ba,hatta kwalliya da iya dressing kamar ba dattijiwa ba ,,sai da ra koya mata tana nuna mata wani…… ²¹