MISBAH CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI

MISBAH CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

A cikin taxi din Deeni yana ta sake sake tare da tunanin shin wa zai fara zuwa ya gani?masoyiyarsa farida ko kuma iyayensa ko yaya shamsu da matar sa? Yaba son basu surprise ne shi yasa ko baba bai fadiwa yana zuwa ba ,yafi so sai dai su ganshi kawai,mahaifinsa ya zata sai wani watan zai gama ya dawo.

    Ya yi murmushi,”Farida zata ganni bazata,zanga ni da ita wa zai fi farin ciki da ganin dan uwansa?

   Yana wannan sake saken har suka iso cikin unguwarsu,a nan ya tsaya yana tunanin ina zai fara shiga gidnsu ko na su farida ,ko kuma gidan ya shamsu…………..??

  Can dai deeni ya yanke hukuncin zuwa gidan dan uwansa ,ya cewa direba ya juya. Dama ya riga yasan gidan da mahaifinsu ya bawa shamsu,don haka ya yanke hukuncin wucewa gidan shamsu ya ga mai sunansa Deeni da dan uwansa,ya yi masa murnar aure,ya ga kalar matar da yayansa ya aura…😭

    Yana daria ya fito hannunsa dauke da akwati wanda cike yake da kayan sawa da kayan wasa na mai sunansa Deeni karami. Nan ya cewa mai taxi din ya jirashi zai shiga ciki ya amso masa kudinsa. Nan ya yi ciki ya bar sauran kayansa a motar.

       Tura gate din gidan ya yi yana jan akwatin da ke hannunsa,yana ratsa tsakiyar gidan,yana kallon ginin da cikin gidan yana murmushi. A ransa yana fadin,kwanannan shima zai mallaki nasa gidan tare da farida. Www.bankinhausanovels.com.ng 

     “Anya kuwa in na auri farida ina da wani sauran buri kuwa a rayuwa?

  Yana cikin wannan tunanun yaci karo da security na gidan wanda dama ya shiga ciki kai wani sako ne ,ganin Deeni yasa shi washe baki yana dariya saboda dama tsohon mai gadinsu ne Alh ya bawa shamsu shi yana masu gadi.

     Nan ya karbi akwatin tare d a bude masa kofar falo,anan ya ci karo da Deeni karami a tsakiyar falon ,an baza masa toys yana wasa .

   Da sauri ya isa gare shi yana dariya,yasa hannu ya daga shi, Deeni kuwa kamar ya sanshi ya wangale baki yana dariya.

      Deeni yana zura masa ido yana kallon irin kamar da yake yi da shamsu,son yaron da kaunar sa yaji ya shiga zuciyar sa,nan ya dinga masa wasa yana cilla shi sama shi kuma yana daria.

      Nan ya bude akwatin ya ciro masa sabbin toys din da ya siyo masa ya bashi,anan wurin deeni ya zauna yana ta wasa da Deeni. Shi dai megadi ya tafi ya barsu don Deeni ya hana ya musu magana ,ya ce suprise zai basu.

     Tsawon minti goma yana tare da Deeni har ya soma mamakin me yasa yaji tsit ba wanda ya fito duba Deeni karami shi daya? 

Nan ya daga shi ya nufi falon ciki yana fadin…

 ” zanci tarar iyayenka ,sun barka kai kadai na tsawon lokaci ba wanda ya leko ka,kar ka damu ga uncle Deeni ya dawo ,zai dauke ka ya tafi da kai su kuma suyi ta zaman su a ciki….”””

   Deeni dai sai dariya yake masa tare da fadin mommy ko daddy. Www.bankinhausanovels.com.ng 

  Ya ce “uncle zaka ce,uncle Deeni “

  Nana ya yi kokarin kwaikwayon sa ya fada cikin maganar yara ‘yan koyo. Shekararsa biyu amma ba baki sosai,sai girma da yayi kamar dan shekara uku.yaro ne lafiyayye mai ji da karfi. Da alama ya sami kyakkyawan raino da kula daga iyayensa.

    ” Salamu Alaikum ,mutanen gidan suna nan kuwa ko sai na tafi muku da yaro za ku fito?

 Deeni ya fada yana kokarin kutsawa cikin daya falon tare da daga labule.

 Wani abu idonsa ya gane masa me kama da mafarki ko almara,,wani abu da kwakwalwa ko hankalinsa ba zai iya dauka ba.

    Farida ya hango kwance jikin shamsu ,shi kuma ya rungumota yana ta kokarin massaging kanta,yana matsa mata kai alamar yana mata ciwo ,tana ta zuba shagwaba.

   ” Daddy kaina zai tsage,daddyyn deeni inajin mura””

     Yi hakuri mommyn Deeni,zai bari,kwanta ina ci gaba da matsa miki tunda kin sha magani zaki samu bacci yanzu,kiyi shiru kar ciwon kan ya karu”

 ” Daddy deeni fa ?  Ta fada cikin shagwaba da kuma ciwo .

  Yana can yana wasa ,ki samu bacci zan fita da shi in kaishi gun mama tunda bakya jin dadi. Wannan babyn namu dai da yazo yanzu yana wahalar min da farida na,sai mun masa bulala in yazo.

  Tayi murmshi ta ce , Ya shamsu mace zamu haifa mai sunan mama,kaga kuwa ba a yiwa mama bulala ba,in kuwa ka mata sai hannunka ya nade” 

    Dariya sukayi duka,sam basu kula da Deeni da ke tsaye a kansu ba,wanda tsananin firgita da kaduwa da abinda ya gani sai da ya saki deeni ya sha kasa ,bai ma san yayi hakan na. Gaba daya hankalin sa ya bar jikin sa,baya hayyacin sa.

    Ihun deeni ya jawo hankalinsu ,shamsu ya mike a firgice gabansa ya mummunan faduwa,yayin da farida ta ji wani irin hajijiya ,sabon zazzabi ya lullubeta ,tsananin firgita da ganin Deeni bata san lokacin da taji mararta ta juya ba ,wani azabar ciwo taji ya kamata,tuni jini ya soma bin kafarta yana gudu ,alama ne na cewa cikin jikinta wanda bai wuce wata biyu ba ya bare saboda tsabar tsorota da tashin hankali data shiga. Haka nan shamsu duk kokarinsa ya kasa ko da motsi a wurin ,kansa sunkuye ya kasa hada ido da Deeni,ya kasa ko da motsawa balle yaje ya daga deeni dake ta kwala ihu a wurin Www.bankinhausanovels.com.ng 

   Farida dai dakyar ta samu ta zauna bisa kujerar da suke sabida hajijiya da wani abu da taji yana yawo a tsakiyar kanta ,ko ciwon marar ma bata lura da shi ba sai dai tabbas tasan abu na bin kafarta wanda batasan menene ba.

  Tsawon minti biyar suna cikin wannan halin,duk wani farin ciki da murnar da jin dadin da ya dawo da shi nigeria sai da ya neme shi ya rasa,kunci ,bakin ciki ,takaici, da bacin rai ya maye gurbin su.

  Halin da ya gansu ya ganar da shi dukkan abinda yake faruwa ya fahimci cin amana da. yaudarar da farida da shamsu suka masa.wani abu da bai taba zata ba balle tsammani ,ko a mafarki ko. A tunaninsa bai taba giftawa ba.

   Wani abu yaji ya tokare shi a zuciyarsa,haka ya dinga jin wani azabar radadi a kansa,wani irin azabar ciwo da bai taba jin makamancin sa ba . Amma duk da halin da yake ciki sai ya sa hannu ya dauki Deeni ya nufi gabansu ya mika musu shi,sai dai dukkansu ba wanda ya iya motsawa balle ya sa hannu ya karbe shi. Hakan yasa ya ajjye shi. Akan cinyar farida ya juya ya fita.

   Yana shirin barin falon ya ci karo da su umma tare da baba ,da kuma Abba da umma ,wato mahaifiyar farida.

    Ashe Alh Umar ya yi waya can America aka ce masa ai tun tuni Deeni ya taho nigeria,tun daga nan hankalin sa ya tashi ya aina tsawon lokacin da aka ce masa ya taho yasan tabbas ya iso,haka nan tunda bai je gida ba ko gidansu farida ,to tabbas yasan gidan shamsu zai nufa. Ranar da suke gudun zuwanta ne dai ta zo.

     Tunda mama ta sami labari hankalinta yai mummunan tashi,Alh ya tattaro su duka don su yiwa Deeni bayani,su fahimtar da shi ,wanda a zatonsu zai fahimta,(hmmmm atunaninsu akwai wani bayani da deeni zai fahimta ne🤔)
,to amma mama tasan dama za’a rina…..

   Mama na ganinsa da yanayin da ya shiga hankalinta ya kara tashi,ta jawo shi ta rike gam tana fadin .

Deeni addu’a zaka yi kaji,ka dinga maimaita hasbunallahu wa niimal wakil,ko la’ilaha illah anta subhanaka inn kunti minazzalimin””

     Gaba daya kansa suka yi kowa da irin abinda yake fada masa ,da irin bayanin da suke masa . Sai dai deeni ya dawo kamar zararre,tamkar mara hankali,kallon su kawai yake bakinsa na motsi amma baya ma jin me suke fadi balle ya gane.Ya kalli mahaifiyarsa yace,,Mama kinada kudi ki bani in biya me motar da ya kawo ni ?

    Deeni na biya shi,har mun sa ya sauke maka kaya ya sa a motar mu,zo mutafi gida”” Www.bankinhausanovels.com.ng 

    Deeni ya kalleta,”Mama farida ,jini na zuba a jikinta ku kaita asibiti”

    Sai a lokacin suka mai da hankalin su kanta,umma ce da mama sukayi kanta,suka dagota hankalinsu a tashe suna salati,sukai mota da ita. Tare da Abba suka tafi,yayin da baba ya tsaya tare da shamsu da deeni,ya jawo su duka.

    Bayani ya fara da nasiha ,da kuma fadin ba laifin shamsu da farida bane ,su suka yi hadin nan saboda wani dalili nasu,su kuma suka musu biyayya.

     Bana son ji Baba ,duk wani abu da zaka fadamin ko wani dalili bana son ji,ka rike dalilinka,duk abinda zaka fada ba zai cire min ciwon da nakeji yanzu a zuciyata ba.  Kasan me nakeji Baba ? Da kasani da baka tsaya yi mun wani magana ba …  Baba ka sama mun magani ,ciwon da nakeji a kwalkwata da zuciyata yanzu za su iya kashe ni,Baba yanzu ina jurewa amma anjima ba zan iya jurewa ba. Baba zai kashe ni ka kaini asibiti ko ka min addu”a ,kamin duk abinda zaka iya mun ko zan samu saukin ciwon da nakeji …..     

      Kai Babana ne ,ME SONA ,me yanke dukkan wani hukunci na rayuwata saboda ka kawo ni duniya ,ka bani ci da sha, ka kula da lafiyata da karatuna ,ya zamar min dole in maka biyayya.

   Nayi biyayya baba da abinda kayi ,sai dai baba ka taimake ni wannan abinda nakeji baba ban taba jn irinsa ba,baba bana ganinka sosai ,duhu na rufe mun ido,ina jin duniyar na zagawa dani ….

     Kama kansa yayi da karfi,basu ankara ba sai ganinsa sukayi ya fadi ,ya zube kasa a sumeeee………….

   HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *