MISBAH CHAPTER 19 BOOK 1 END BY SA’ADATU WAZIRI
WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Mun tsaya
Doctor ,kaga nima doctor ne ,likita ne cikakke,sai dai ban kware ba,ni ba professional bane,hala ilminka ya kai inda za’a iya yiwa mutum wankin kwakwalwa?ka bude mun kwakwalwata da zuciyata ka wanke mun su tas ,ina son manta dukkan mutanen nan a rayuwata,bana son tuna su balle in tuna abinda ya faru. Kaga wannan painful memories din abinda ya faru dani ,ina so ka bude ka wanke mun su duka saboda ba zan iya rayuwa da su ba,suna min ciwo sosai ,baza su barni in rayu ba ,ni kuma inaso in rayu. Please Doctor ka taimake ni..””
Tun yanayi a hankali har ya fara da tsawa,lokaci guda ya haukace musu,da kyar aka samu aka masa allurar bacci ya kwashe shi.
Ba mama ba har baba ya shiga cikin mummunan tashin hankali da Abba ,har suka yi nadamar abinda suka aikata masa.
Mama tana kuka tana tofa masa addu’a haka daga farida har shamsu kuka suke bamai lallashin wani
Wasa gaske al’amarin Deeni ya tsananta,wani lokaci ka ganshi lafiya wani lokaci ya haukace musu,gana daya baya hayyacinsa,bai san me yake yi ba,hankalin iyayensa da masoyansa ya kai kololuwar tashi. Daga karshe Alh ya fita dashi kasar india ,anan aka ci gaba da duba lafiyar kwakwalwar sa,saboda abin yamatukar taba masa kwakwalwa,kwakwalwarsa ta kasa dauka da jurewa wannan damuwar.
Ana duba lafiarsa a asibiti kuma ana masa rokon Allah,tare da sauke masa Alkur’ani ,da haka da taimakon ubangiji Deeni ya soma dawowa hayyacin sa. Sai ya zamana ya daina surutu tunda suka dawo gida,ba ya kula kowa ,baya cewa kowa komai. Kullum yana zaune a dakinsa,baya fita sai dai wani ya tafi masallaci ya dawo. In an kai masa abinci wani lokaci zai ci ,wani lokaci kuma haka abincin zai kwana wani ya tarar da wani
Lokaci guda rayuwar Deeni ta canja ,ya yi baki,ya rame ,kuma baya aikin komai sai kwanciya da zaman gida. Ya dawo rayuwar sa sam bata da wani manufa. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
A duk lokacin da Deeni zai kwanta bacci,to yakan rufo ido ya hango shi da farida,lokacin da hoton farida da shamsu zai bayyana a fuskar sa yakan yi saurin bude ido wanda a nan za su rine suyi ja,yaji kansa ya fara sarawa ,ya kama kai da kirji . Wani lokaci sai dai a shigo a same shi a sume.
Halin da Deeni ya shiga ya daga hankalin kowa a zuri’ar su,musamman iyayensa da kuma shamsu da farida. Wani lokacin mahaifin sa sai ya zubar da hawaye saboda bakin cikin halin da dansa ya shiga. Rayuwarsa ta dawo useless bata sa wani amfani ,ya yi da na sani tare da jin bakin cikin abinda ya yi.
Kulum yana binciken asibiti ko masu maganin gida da za su dawo da shi dai dai,sai dai abu guda yake ji kullum,shi ne abin ya mugun taba masa kwakwalwa da zuciya,wanda fitar sa a wannan hali sai a hankali . Sai dai dayawa masu magani ko likitoci na bashi shawarar cewa ya canja masu wuri,wato ko dai ba ya bar garin ko kasar ,ko dai wani wurin da zai nesanta deeni da rayuwar da yayi ta baya.
Wannan yasa Alh Umar ya tattara nasa ya nasa da kasuwancinsa ya raba su biyu ya koma lagos ,ya yin da ya barwa Shamsu sauran kasuwancin sa a kaduna .WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Alh Umar ya tattara iyalinsa,wato hajia A’i da Deeni da lukman suka koma garin lagos ,ya bar Arewa gaba daya. Saboda ya san Deeni yana da sha’awar zama a garin ,sannan yana ga zai ji dadin tafiyar da kasuwancin sa. Haka Deeni zai samu kyakkyawan canjin yanayi ,yayin da ya bar Shamsu da Farida a kaduna.
Tabbas Alh.Ahmad ya yi bakin cikin rabuwa da abokinsa,makwabcinsa,wanda yake kamar dan uwansa Alh. Umar . Ya daukar masa amanar dansa da kuma hakkin kula da shi da kasuwancin da ya bar masa,da ya dinga kokarin sa ido inda yaga ya karkace ya yi masa gyara.
Farida da mama sun rabu cikin kuka tare da bakin cikin rabuwa da juna.
*** *** *** **** **
“”ALHAJI ! ALHAJI !!
Haj. A’i ta shigo falonsa tana kwada masa kira .
Ya kalleta a firgice ,” lafiya cikin daren nan ?
Ta mika masa wani farin takarda ,ya kalleta cike da mamaki.
“Menene wannan ?
Tace ,Address ne na samu,inda zamu kai Deeni,yanzu na kasa bacci na kunna tv kenan naga suna tallen wurin nan. Na lura masu matsala irinta Deeni sun samu waraka..””
Ya kalleta ransa bace ,ya ce,”Dana ba mahauci bane ,kuma ba dan shaye shaye bane da za a kaishi REHABILITATION CENTER
Cikin nuna damuwa Haji. A’i tace. Alhaji ka duba ka bincika ,wannan wurin ba mahaukata ko ‘yan shaye-shaye bane,kafin in baka sai da nayi bincike naji komai akan su. Abinda yafi jan hankalina gare su ahi ne,sun hada da Addini da kuma magungunan musulunci . Deeni yana bukatar taimako na Addini da na asibiti duka,wanda duk sun hada.
Dakyar ta samu ta shawo kansa ya yarda zai binciko,in ya masa yadda hankalin sa zai dauka to zai yi tunanin tura Deeni wurin…..