MISBAH CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Kamar yadda kace baka da damuwa da MISBAH sai brains dinsa ,to nima bani da damuwa dashi,damuiwata shine deeni,in kuwa labaransa na dauke hankalin deeni a kai na ,to inada matsala da hakan ,don haka inada matsala da brain dinsa,da intellegent dinsa,i have a problem wit his stories”
Ya dan fadada murmushinsa tare da fadin “” anyi an gama ,daga yau bani ba karanta littafin MISBAH ;nayi alkawari””
Tayi daria har da tsallen farin ciki ta ce ” shiyasa nake son deeni na ,he care for me yana jin maganata ya damu da farin ciki na ,,my deeni is d best”””
Dariya yake mata shima yace my farida is d best”ki tsaya a gabana in ta kallonki ina jin dadi . Haka kawai kin hanani jin dadi da sukuni ,kwana uku ban ganki ba ,meyasa kika ki zuwa ki ganni ? Kinsan baba kulle yakemun inmun fara jarrabawa ya hadani da wannan manya manyan takardun ina karantawa, bana ganewa,daga na bude littafin sai inga furkar farida tanamun murmushi,bana iya komai sai kallon fuskarki a littafin “tayi murmushi tace meyasa baka dirko ta window ba ? Www.bankinhausanovels.com.ng
Yace ” so kike in karye a ce mijinki gurgu?
Tayi daria tace “to ina ruwansu ,inma gurgun ne ba mijina bane ? Deeni na ne ni daya ”
Yace haka farida na ni daya “”
Farida ta dubeshi tace deeni yaushe zamuyi aure ? Ya kalleta ya ce ko yau Abbanki ya shirya aura minke zan aure ki ” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta masa hararar wasa ta ce ina zaka ajiyeni baka da gida baka da aiki ? Ya ce,shine damuwarki ? Kalli girman dakin nan bazai ishemu ba ? Ya jawota ,”zo kiga yawan abincin da mama take samun kullum so uku so hudu a rana ,ko ke rumbu ce zaki koshi. Awani lokaci mama nasamun abinci fiye da kala hudu a rana ,wani lokaci ma bana ci ake fita dashi .
Bari in fada miki ni mrs deeni NURADDEN dan gatan mama da baba ne auren gata zatamun dakina ya ishemu,abincina ya ishe mu ,balle ma inkin zo mama zata kara kara. Kayan sawa zan sai miki ko wanne ,inada kudi enough a account dina ,kullum baba samun yake bana kashesu . Zan iya kula da lafiyarki ,babban shine zan kula da farin cikin ki,kullum zan dunga saki daria ,har funny faces zan dunga miki in kina so .
Zan so ki sosai my farida ,ki rayu a dakina ,gado na,wardrop dina,toilet dina ,komai na baki . Ni zan rayu a jikin ki” yana magana yana lumshe ido.
Murmushi tayi ,kunya tasa ta sunkuyar da kai.
Ya kira sunanta yana mata murmushi,wannan tunanin da halayyar tasa yake kara haukata zuciyarta cikin soyayyarsa, itama murmshin take masa,ganin yana matsowa gareta yasa ta fara ja da baya ,tayi hanyar fita tana kallonsa,bataki tai ta kallon sa a haka ba. Sai dai ya zama dole tayi gidan dan an fara kiran sallar magriba,za’a nemeta a gida in anji shuru bata dawo ba . Haka tana tsoro kar mama ta leko su . Bata ankara ba kuwa taji tayi karo da abu,da sauri ta juyo tare da daga kai. Yaya SHAMSU ne yayan deeni ,ya kalleta . Haba farida yi a hankali maba,bakya gani ne?”
“Yi hakuri yaya ai duk laifin deeni ne ” ya zaro ido ,sharri zaki mun ? Yaya laifinta ne” girgiza kai ya yi tare da murmushi ,ya ce “Deeni da Farida sai Allah ,ba’a gane muku kuma ba’a shiga tsakaninku . Ni kan nayi masallaci ,maza kaima kayi harama ,kema ki shige ciki ayi sallah,in yaso kuyi soyayyar daga baya “
Kunya tasa ta rufe fuska ,ta fita da gudu ko sallama da mama batayi ba, deeni yabita da kallo yana murmushi ,sonta na bin jikinsa . Ya Shamsu ya kalleshi yace wai wani irin so kake wa farida ne ?
“Yaya nima ban sani ba ,ni kaina na rasa wane irin so nake mata da yawansa “
Girgiza kai shamsu ya yi ya wuce ya barshi a wurin … Www.bankinhausanovels.com.ng
nhausanovels.com.ng