MUGUWAR KISHIYA COMPLETE
: MUGUWAR KISHIYA
**** Part 1 ****
Repost by AYS ZA
Yau asabar gobe daurin
auren Abbanmu umma
tacewa Baffah? Nace
Na’am Umma, Sai ta
kira Sunan Kanwata
Aisha, Sai ta amsa, Sai
umma tac” saboda haka
banaso kuyi wani abu
da zaisa wani ko wata
yace baku da tarbiyya
inaso ku kasance masu
nuna farin cikinku akan
wannan al’amari, gaba
daya muka amsa da
cewa to umma “Tace
allah yayi muku albarka,
mukace amin, abbane
ya shigo megadi na
binsa da akwatuna,
megadi ya aje ya fita,
abba yace sannanku da
zaman gida, Muka amsa
gaba daya yauwa abba,
yasa hannu yajanyo
akwatunan nan ya bude
kayane niki niki aciki
yace hajiya wannan
nakine,
umma ta nuna farin
cikinta sosai nida
Kanwata aka bamu
namu kayan amma fa
mu bamu nuna farin ciki
ba, Yau litinin kwanan
amarya daya agidan
abba, umma ta tura Ni
da Aisha s Muje mu
gaida amarya, Aisha ce
tafara shigewa gaba
muka shiga bangaren
amarya muka tarar
abba yana dakin Aisha
tace aunty good
mornng, amarya tajuyo
ta kalli Aisha a
wulakance tace ke
dama a tsaye kuke
gaida uwarku? Ni ne
nace daga gaisuwa saiki
zagi umman mu to
wallahi badai uwarta ba,
amarya tace kai dan
uwarka ba’a koya maka
tarbiyya ba? Nace badai
uwata ba, amarya ta
juya wajen abba alhaji
yanxu kanaji yaronnan
yana zagina?
abba baiyi wata- wata
ba ya daga hannu ya
zabga man mari, Muka
juyo a gigice domin abin
ya matukar bamu
mamaki kasancewar
abba ko tsawa bayaso
ayi muna amma da
mamaki gashi yau shine
ya daga hannunsa ya
mare Ni, nan take Aisha
ta fashe da kuka domin
abin ya tsoratata,
mukayo waje mu duka
muna kuka, umma ta
taho da sauri tatare mu
tana tambayarmu
lafiya? Aisha ce tayi
mata bayanin abinda ya
faru’ abba ya fito a
fusace yana ta kwala
wa umma kira’ umma
ta amsa’ abba yafara
magana cikin fada, ke
tsabar rashin mutunci
shine zaki turo
wadannan yaran naki
suzo suyiwa amarya ta
rashin mutunci? Umma
tace alhaji anya kuwa
acikin hayyacin ka kake?
Ke ni kikeyiwa wannan
tambayar to wallahi sai
nayi maganinku duk
wanda yace zai tabamin
amaryata bazamu
zauna lafiya dashiba
agidannan, abba ya fice
a fusace, duk abinda
yake faruwa amarya
tana tsaye tana yiwa
umma dariya’ Nine na
xabura da niyar dukan
amarya amma umma
tai caraf ta rike
hannuna tajamu mukayi
daki muka bar amarya
atsaye tana yimana
dariyar mugunta
amarya tace kadan
kuka gani indai nice sai
kunbar gidannan,
KADUNA N,D,A Samar
ya shiga damuwa
matuka kasancewar
rashin ziyarar da su
abba basu kawo
masaba kullum sukai
waya da umma sai tace
masa suna nan zuwa
har ya gaji, dama ba,a
maganar abbansa
wanda idan ya kirasa
baya daga wayarsa
hakan yasa ya tambayi
umma lafiya abba baya
daga waya ta? Amma
sai umma tace masa
lafiya aikine yake
hanashi kula da kiran da
ake masa, duk da haka
Samar yana xargin
akwai abinda yake
faruwa agidanmu dan
haka yake ta fatan
karasa shekara dayan
data rage masa. a N.D.A
domin yaxo gida yaga
abinda yake wakana
agidanmu,
Umma ta gargadi mu
akan kada mu sake mu
fadawa yayanmu
Samar halin da muke ciki
kuma kada mu sanar
dashi cewa abba ne ya
hanamu zuwa visiting
dinsa Abba ya shigo
gida Aisha ta tashi
domin tarar abbanta
takarasa da sauri ta
tsugunna agaban shi
tace abba sannu da
zuwa, ya juyo ya daka
mata wata harara ke
dalla can munafuka
tashi ki bani waje Aisha
ta tashi jikinta a
sanyaye, umma wadda
take zaune ranta yai
matukar baci amma
abinka da mai hakuri sai
dai kawai tace allah ya
kyauta axuciyarta,
Aisha ta fada jikin
umma tana kuka tana
cewa umma me
mukayiwa abba baya
son ganin mu? Umma
tace yi shiru kinji “yata
ba laifinsa bane akwai
makircin amarya acikin
wannan shirin amma
allah zaiyi mana magani,
Aisha taci gaba da rusa
kuka ba kakkautawa
umma tana lallashinta,
Na gama shirin
makaranta kaf domin
yaune zamu zana
english waec dinmu
naxo gurin abba ya
tsugunna nace abba
aban kudin makaranta
abban namu ya kalleni
sannan yasa hannu a
aljihu ya dauko naira 30
ya mika mani,
Nace abba ai 200 kake
bani 30 baxata kaini ba,
amarya ta daka mani
tsawa kai!! Shashasha
mahaifinka ya baka kudi
kace yayi maka kadan?
Abban namu ya kalleni
sannan yasa hannu a
aljihu ya dauko naira 30
ya mika mani, Nace
abba ai 200 kake bani 30
baxata kaini ba, amarya
ta daka mani tsawa
kai!! Shashasha
mahaifinka ya baka kudi
kace yayi maka kadan?
Abba yace kai tashi
kaba mutane waje, Na
tashi nayi waje,
zuciyata cike da tsanar
amarya, Amarya ta kalli
abba tace Honey gobe
kannena Zasu zo, abba
yace su nawane?
Su biyu ne kadai, abba
yace to ai inbanda abinki
kamata yayi ace sunfi
haka yawa nan
agidansu ne, amarya
honey ai akwai wasu
xasu xo suma amma
sai nan gaba, abba yace
to gskya yakamata
suxo da fatiman nan da
kike ta bani labari,
amarya ai ita da abdul
xasu xo, abba yace to
allah ya kawo su lpy,
ameen amarya tace,
Can kuwa bangaren
umma ba abinda take
sai addu,ah akan allah
ya warware kullun da
amarya tayi akan
mijinta da kuma allah ya
mu hadu a whatsapp 09033627792 Group
»Click Here And LIKE us On Facebook«
»Click Here And Follow us on Twitter«
↓Help Your Self ↓
→»ku dinga comment
→»yan mata da samari ayi invite
→»dan momy na gaisuwa
↓Yauwa haka nakeso comment↓
class= class= class=
Ayuba powar boy
on-line 2.02 23:43
Can kuwa bangaren
umma ba abinda take
sai addu,ah akan allah
ya warware kullun da
amarya tayi akan
mijinta da kuma allah ya
dawo mata da babban
danta Samar daga N.D.A
lafiya Su fatima da
abdul suka iso gate din
gidan suka shigo kai
tsaye domin alhaji ya
sanarwa da mai gadi
zuwansu, kana ganinsu
kaga marasa tarbiyya,
sukayi karo da Ni
Alokacin ina kokarin
fitowa daga gida’
fatima ce tace kai
makahon inane kanaji
kana buge mutane?
Duk da baisan gurinwa
zasu ba sai nace allah
yabaki hakuri, fatima
taja wani dogon tsaki
banza mahaukaci, Naji
xafin kalmar sosai dan
haka banyi wata-wata
ba na daga hannu na
sharara mata mari, ta
kwalla wata kara ta
tilasta umma da
amarya fitowa
aguje,suna zuwa suka
taradda da abinda ya
faru, umma ta tambaye
ni Tace Baffah me ya
faru na kwashe kaf
abinda ya faru Nafada
mata, amarya tace sam
bazata yarda ba nan
take dauko waya takira
alhaji tace masa yai
sauri yazo gida ba
lapiya, ba’a dade ba sai
ga alhaji yadawo, Ya
taramu gaba dayanmu
mutanen gidan, alhaji
yafara magana kamar
haka:- Kai dai wannan
yaro anyi dan iskan
yaro, yanzu ace kadaga
hannu kamari kanwar
amarya kuma kayi
tunanin zan kyaleka to
wallahi baka isa ba don
haka ko ka tattara
kayanka kabar gidan
nan ko kuma ita uwar
taka ta bar gidan,
agigice umma tajuyo ta
zaro idanu tace alhaji
kasan me kake fada
kuwa?
abba yace ke kina nufin
kice ni mahaukaci ne to
abinda kunnenki yaji shi
nafada, dan haka ku
tashi ku bani guri,
amarya da kannan ta
suka tashi suna dariyar
mugunta, alhaji ma
yatashi yabisu, Ni kuwa
tuni ya dauko jakar
kayana abinka da mai
xuciya, umma da
Kanwata Aisha suka
rike ni suna kuka, nima
hawayen bakin ciki suka
fara zarya a idanuna,
Aisha kuka take kamar
ranta zai fita Nayo waje
nakama hanya batare
da sanin inda zani ba,
Umma da Aisha suna
xaune suna ta rusa
kuka, wayar umma ta
fara ringtone Aisha ce
ta duba wayar
yayanmu Samar ne
yake kira cikin hanxari
ta daga tana
shashshekar kuka hello!
Yaya tace, a firgice
Samar yace my sister
lpy kike kuka??Umma
tayi sauri ta kwace
wayar daga hannun
Aisha domin bataso
Samar yasan halin da
Muke ciki, tayi magana
cikin karfin hali tace lpy
lau Samar, Samar
yacewa Umma Wai
meke damun kanwata,?
Umma tace tana
kukane saboda rashin
ganin ka akusa damu,
Samar yace to inbanda
abin sister ai saura
wata bakwai nadawo,
yace umma bata wayar
na lallashe ta umma ta
mika wa Aisha wayar
tare dayi mata nuni
akan tadaina kukan
datake Aisha ta karbi
wayar, yace sister kiyi
hakuri kinji zan dawo
nan bada dadewa ba,
Aisha tace yaya wallahi
kullum haka kake cewa,
Samar yace to sister
wannan karon dai tinda
nace nakusa dawo wa
to nakusa kinji? Tace to
yaya, Samar yace yanxu
kina Ss3 ko? Tace eh
yaya, to ki maida
hankali kinsan nurse
nakeso kixama, tace to
yaya, yace Baffah sun
gama waec dinsu last
week ko? Tace eh, yace
to kice masa yadage
sosai, tace to, yace
yauwa sister bye, tace
bye yaya, ya katse
wayar, Can kuwa a
bangarena tuni nayenke
shawarar tafiya gidan
kakannina na bangaren
uwa dake unguwar
Kaura na isa gidan na
kwashe duk abinda ya
faru na fada musu nan
mahaifin umma yace
kayi zamanka ko gidan
kada ka kara zuwa ni
zan dauki nauyin
karatun ka shikuma
abban naka xan neme
shi,
Ni kuma naci gaba da
karatuna ba abinda
yake damuna sai dai
idan natuna halin da
umma da Aisha suke
ciki, a duk sanda mukai
waya da yaya Samar
sai naji kamar nafada
masa halin da Muke ciki
amma idan na tuna
gargadin da umma tayi
mani akan kada na
kuskura na fadawa
yayan namu, sai kawai
nafasa fada masa,
Amarya da kannenta
abdul da fatima suna
xaune a falo, abdul yace
aunty nifa gaskiya
yarinyar nan nake so,
amarya tace wace
yarinya? Abdul yace “yar
kishiyar ki mana Aisha. ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009
|ADINGA COMMENT| →YAN` MATA↠↓BIGBOY NA GAISUWA↑
→Copyrightsâ†
[7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA
*PART 2*
RE POST BY AYS
Amarya da kannenta
abdul da fatima suna
xaune a falo, abdul yace
aunty nifa gaskiya
yarinyar nan nake so,
amarya tace wace
yarinya? Abdul yace “yar
kishiyar ki mana Aisha,
amarya tace ai dama
tunda naga take
takenka nasan akwai
magana, don haka kada
kaji komai kamar ka
mallaki Aisha ka gama,
abdul yayi tsallen murna
yace thank you aunty,
fatima tace ikon allah ni
banga abinso ajikin
wannan yarinyar ba,
amarya tace ina
ruwanki? Fatima tace
ba ruwana, Dare yayi
abba yadawo ya shigo
gida tare dayin sallama
umma ta amsa tace ta
tashi domin karbar
kayan da suke hannusa,
ya daka mata tsawa
tare dacewa ina
ruwanki da kayana?
Umma taja da baya,
abba yamika wa
amarya kayan amarya
ta karba’ tare da yiwa
umma gwalo, abba
yajuyo yacewa umma
duk da cewa yau
kwanankine inaso kiyi
hakuri domin yau adakin
amarya nake son
kwana, yajuya ya nufi
dakin amarya batare da
yatsaya jin amsar da
umma zata bashi ba
Bayan sun zauna shida
amarya tace alhaji
akwai maganar
danakeso nafada maka,
abba yace ina
sauraronki, amarya ta
gyara xama cikin
kisisina tace dama
wallahi yaron nanne
abdul yace yana kaunar
Aisha shine nikuma
nace masa ya kwantar
da hankalinsa kamar
yasamune, abba yace
ikon allah to ai Aisha
“yarki ce kuma duk
hukuncin da kika yanke
akanta dai-dai ne,
amarya tace yauwa
alhaji shiyasa kullum
nake kara son
kasancewa da kai, abba
yace nima haka, amarya
tace amma yakamata
kasanarwa da yarinyar
da mahaifiyarta don
kada inyi magana abin
yazama rigima, abba
yace nida “yata akwai
wanda ya isa yayi min
iko da ita don haka kice
masa yasameta yayi
mata magana, amarya
tace nagode alhaji,
Da safe abba yakwallah
wa Aisha kira, ta amsa
taho da sauri domin
kuwa yanzu duk duniya
ba wanda take tsoro
sama da abba da kuma
amarya, taxo ta
tsugunna tace abba
gani, yace saura wata
nawa kigama secondry?
Wata takwas abba,
Abba yacewa Aisha to
nayi miki mijin aure,
agigice Aisha tace abba
aure?? Abba yace eh
kuma bawani bane sai
wannan yaron abdul,
abba bai tsaya jin
amsar Aisha ba ya tashi
yayi waje, umma wacce
take jin duk abinda yake
faruwa taxo ta kama
Aisha suka shiga daki
umma tai ta lallashinta,
Aisha tace umma idan
akwai wanda natsana
aduniya bewuce amarya
da danginta ba, gsky
umma yakamata yaya
Samar yasan halin da
muke ciki, umma tace in
banda abinki shima
yayan naku ai akarshin
abban naku yake, kuma
in kin kwantar da
hankalinki saura wata
biyar yadawo kiyi
hakuri, Aisha ta sake
fashewa da kuka mai
tsanani, Yau gari ya
waye umma ta tashi
tana cikin matsanancin
zazzabi don haka
tashirya domin zuwa
asibiti, bayan abba ya
shirya, suka taho shida
amarya zata rakashi
mota, tana tafiya tana
ta wata yangar banza,
umma ta karasa, tace
yauwa alhaji dama so
nake ka ajeni a asibiti,
abba ya juyo
yaharareta, yashiga
motarsa batare daya
kula da umma ba, yaja
motarsa yana yiwa
amarya bye bye itama
tana yimasa, amarya ta
juyo tayiwa umma
dariya, umma tafito
tanemi adai-daita sahu
ta tafi asibiti, Aisha ta
fito daga wanka
matsanancin ciwon da
kanta yake mata shiya
tilasta mata xama akan
gadon ta tayi tagumi
hawaye ne yake
gangarowa daga
idanunta, jitai ana turo
kofar dakin nata, ta
tashi da sauri domin ta
samu abinda rufe
jikinta, amma kafin
takai ga yin hakan tuni
yashigo, abdul tagani
yashigo yana mata
murmushi,
cikin fushi tace kai
mahaukacin inane zaka
shigowa mutane daki?
Murmushi yaci gaba dayi
tare da kura mata
idanu, saikace mai kallon
TV, kunya tagama rufe
Aisha saboda daga ita
sai daurin kirji, a hankali
taga abdul ya fara
matsowa kusa da ita,
tafara ja da baya, tana
bashi hakuri akan kada
ya cutar ita, shikuwa
dariyar mugunta kawai
yake yana kara
kusantar ta,
Aisha tana ja da baya,
shikuwa abdul yana
kara kusantar ta hardai
taje karshen bangon
daki, abdul yayo kanta
gadan-gadan, Aisha
tana dubawa gefanta
taga wukar da umma
take amfani da ita,
batayi wata-wata ba ta
dasa hannu ta dauko
wukar nan ta nuna
abdul da ita, tace kada
kamatso wallahi zan
caka maka wukar nan,
wanda tuni idonsa ya
rufe yayo kan Aisha, ita
kuwa batasan sanda ta
labta masa wukar nan
akai ba, abdul ya kwalla
kara a zube akasa,
amarya da fatima suka
jiyo karar abdul su taho
aguje, ita kuwa Aisha
tuni ta rude sakamakon
ganin yadda jini ke zuba
daga kan abdul, su
amarya suka karaso
suna zuwa sukaga
Aisha rike da wuka a
hannu, basuyi jinkirin
kiran abba ba tare da
daukar abdul zuwa
asibiti, Bayan sun
karasa asibiti ne, likita
ya fara duba abdul, su
amarya da fatima suna
zaune sunyi tagumi,
alhaji ya shigo arude, ya
nufi wajen likita, yace
likita yajikin nasa likita
yace da sauki, domin
yanxu anyi masa duk
abinda ya dace saboda
haka zaku iya komawa
dashi, alhaji yabiya kudin
komai,
sannan yadauko su a
motarsa yana tafiya
yana xage-xage akan
Aisha, Amarya tana
kara xuga shi, Ita kuwa
Aisha tuni hankalinta
yagama tashi domin
sanin abinda zai biyo
baya, tayo waje domin
barin gidan kafin abba
yadawo, tana zuwa
kofa sukai karo da
umma, umma tace
lapiya Aisha? Aisha ta
fada mata duk abinda
ya faru’ don haka umma
tayi saurin bawa Aisha
kudin mota, umma tace
kiyi sauri kitafi gidansu
kaka idan abin ya lafa
saiki dawo, Aisha tace
to umma, aiko min da
kayana na makaranta,
umma tace to, Aisha
tayi waje, kana ganinta
kasan arude take,
Umma tana zaune tayi
tagumi, taji shigowar su
alhaji ko sallama babu
sai masifa yake,
yashigo dakin umma
yatsaya akanta, yafara
magana cikin fushi, Ke
ina wannan “yar iskar
yar taki?
Maganar tayiwa umma
xafi matuka, hakan
yasa mikewa cikin
fushi, tace alhaji duk
abinda zakai kada ka
kara kiran “yata “yar
iska, ga “yan iska nan
kana tare dasu wannan
yaron yayi kokarin yiwa
“yarka fyade amma
kuma sai gashi kai kake
kare……… Saukar mari
umma taji a fuskar ta,
tana dubawa taga
amarya ce ta zabga
mata mari, itama batayi
wata-wata ba ta daga
hannu ta sharara mata
mari, abba dake tsaye
yana kallo tuni shima ya
daga hannu zabgawa
umma mari wanda sai
da ya tilastawa umma
dafe kumatu, umma ta
fashe da kuka mai
tsanani wanda duk
wanda yaji dole ya
tausaya mata,
alhaji ya kara da cewa
kuma idona idan Aisha
sai na karya ta, suka
juya suka fice daga
dakin suka bar umma
tana kukan bakin ciki,
Aisha bata tsaya ko ina
ba sai gidan kakanninta
ta fada musu duk
abinda yafaru, hakan
yasa kakanta yace
gaskiya abin nashi
cigaba yake don haka
bari naje wajen malam
nasanar dashi abinda
yafaru, Bayan dare yayi
amarya da abba suna
zaune, abba yana ta
lallashin amarya amma
taki, sai abba yace
kifadi abinda kike so
nayi miki komai
wahalarsa don ki daina
fushin nan, amarya tayi
murmushi da alama taji
dadin maganar abba,
sannan tace ni abu hudu
nakeso, alhaji yace fade
su duka indai kudi ke
yinsu kamar angama
ne, amarya tace 1 inaso
kadawo min da yan
uwana mutum takwas
gidan nan da zama 2
inaso ka cika min
alkawarina na motar da
kace xaka sai min 3
inaso mufita kasar
waje shakatawa, na
hudun kuma baxan fada
ba sai mun dawo daga
shakatawa,
abba yace wannan duk
mai sauki ne indai zaki
huce, don haka gobe
zan tura driver ya dauko
“yan uwan naki, mota
kuma muna dawowa
xaki ganta, don haka
wace kasa. Kike so mu
tafi? Amarya tace
maleyshia, abba yace to
kada kidamu tawan,
farin ciki ya lullube ta,
Abba ya gama shirin
tafiya maleyshia shida
amaryarsa gida kuma
ya cika da “yan uwan
amarya, wanda yanxu
su goma ne tara daga
ciki dukkansu maza ne
majiya karfi daya ce
mace wato fatima, sai
sharholiyar su suke
kamar gidan ubansu,
umma kuma bata da
damar sakewa haka
umma tayi ta hakuri
tana lissafin dawowar
danta Samar wanda
kullum takeyiwa addu’a,
Yaune ranar tafiyarsu
abba da amarya
maleyshia don haka ya
tara kowa nagidan,
yafara jawabi kamar
haka:- ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009
|ADINGA COMMENT| →YAN` MATA↠↓BIGBOY NA GAISUWA↑
→Copyrightsâ†
[7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA
*PART 3*
Yaune ranar tafiyarsu
abba da amarya
maleyshia don haka ya
tara kowa nagidan,
yafara jawabi kamar
haka:- kamar yadda
kuka sani yau zamu
tafi, to don haka duk
abinda kuke so ku
tambayi wannan matar
ya nuna umma, wadda
kanta yake a tsugunne,
yace kuma idan kika
sake naji ance kin fita
to allah ya isa, fatima
tace alhaji yaushe kuma
zaku dawo? abba yace
bazamu wuce 3 weeks
ba, aka raka su abba
airport, bayan
dawowarsu ne umma
tafara fuskantar
wulakanci kala-kala,
badon allah ya isar da
alhaji yayi akan fitar ta
ba da ba abinda zai
zaunar da ita A gidan, A
kwana a tashi yau
saura 2 weeks Samar
ya dawo zaria domin
yayi gagarumar nasara
anan akayi posting
dinsa ya kagu domin ji
yake kamar ya janyo
ranar domin yansan
ganin su umma da
Aisha da Ni, Rashin
mutuncin da “yan uwan
amarya suke wa umma
ya tsananta, umma
tana ta hakuri da
jurewa, yau saura sati
daya su abba su dawo
daga maleyshia, Bayan
dawowarsu abba da
kwana daya abba ya
siyowa amarya
dalleliyar mota mai suna
(BUGATTI) motar da a
america ma kungiyar
rich gang ne suka fara
hawanta, idan ka hauta
xa,ai tunanin governor
ne, ya bawa amarya
mukulli, tayi murna
sosai ganin motar mai
tsadane yasa taki
hawanta tace sai ranar
da zata unguwar kece
raini, haka aka bar mota
sabuwa kar a ajiye,
umma tace to alhaji
kacika min alkawari
saura daya danace sai
mun dawo, abba yace
wanene? Amarya tace
ya kira umma tukunna,
abba ya kwalawa
umma kira ta taho da
sauri, tana zuwa ta
tsugunna agaban abba,
Amarya tace alhaji
sonake kasaki wannan
matsiyaciyar ta nuna
umma, umma ta dago
kai a da sauri, shima
abba agigice yace
saki!!!?
Amarya ta fashe da
kukan munafinci tace
yanzu alhaji zaka iya
karya alkawarina, abba
yace yi hakuri, yanda
kike so haka za ayi,
yace wa umma nasake
ki saki 1 batare da ya
iya hada ido da ita ba,
umma tafashe da kuka
mai tsanani, wanda duk
wanda yaji sai ya
tausaya mata, amarya
tasa kannen ta
sukayita watsi da
kayan umma, umma ta
koma gidansu suka
hadu gata ga Aisha ga
Ni, Yau ne allah yayiwa
Yaya Samar dawowa.
NDA ya taho da “yan
rakiya ta mota uku na
sojoji, Ya dauko hanyar
zaria, baisanar da
umma yau xai dawo ba
sakamakon yafison
muyi mamakin ganinsa
suna tafiya har suka
shigo Zaria Suna tafiya
a kan titi duk inda suka
zo sai kaga motoci sun
basu hanya, yana cikin
dalleliyar motar da yasa
aka yimai order kafin
Yataho, motocin sojoji
biyu abayana daya
agabansa, kai idan
kagansa bazakai
tunanin soja bane, zakai
tsammanin wani mai
mulki ne, idan ka kalli
jikin motar zakaga
sunanta kamar haka:-
[LAMBOGINY] Suka
karaso unguwar suna
shigowa yaga layin ya
canza mashi gaba daya,
jama’a kallonsu suke
suna tunanin ina zasu
tsaya suka karaso
kofar gidanmu,
sojojine sukai saurin
fitowa su wajen, arba’in
suka ka budemai mota
yana fitowa suka
kame, Suit ce fara ajikin
Yayana Samar, yasa
black shoe dinsa mai
suna [deZaria] ya sa
space mai farar kwalba,
ga agogonsa, diamond,
kana ganin dressing
dayayi kasan kafin
yazama soja nigger ne,
ya kalli jama’a da suka
cika wajen kallonsa
kawai suke, Yaga
abokansa dayawa aciki,
take yakarasa cikin su
suka gaggaisa sunata
mamaki shikuwa
tambayarsu yake, ya
kowa da kowa? Suka
amsa mai lafiya, yace
bari nashiga naga su
Aisha yanzu zan fito,
sai yaga duk sunyi
sororo, Yajuya ya
sallami sojojinnan, suka
nufi janguza barreck
dake Sabon garin zaria
shikuwa yagoya jakar
sa, ya nufi kofar gidan
mu, gadan gadan,
Yana shiga yaji
hayaniyar mutane
yarabka sallama,
mazane sun cika gidan,
suka juyo suka kalleshi,
bawanda ya amsa,
suka ci gaba da abinda
suke, ya wuce dakin
umma yaga anrufe, sai
ya tambayesu dan allah
ina umma? kallonsa
suke kawai ba wanda
yacemai. Komai, waje
yayo yashiga gidan su
MEEMEE domin sune
makotan kuma itace
yarinyar dasuke
mutunci a unguwarmu,
tana ganinsa tazo da
gudu dan murna, tafara
cewa oyoyo oyoyo ga
Samar ga Samar yayi
murmushin karfin hali
Yace wai bazaki girma
ba, tace au hakama
zakace? Mamansu suka
fito suka tareshi da
murna, yatambayesu
ko umma ta sanar dasu
inda xata? MEEMEE
takalli mama yaga sunyi
shiru,
MEEMEE ce ta kwashe
labari kaf ta fadamai,
tuni yaji zuciyarsa tana
tafarfasa’ yayo waje
MEEMEE tabiyoshi, suka
shiga mota sai gidan
kaka inda muke tare da
umma, Suka karaso
suna shiga sukai ido
biyu da Aisha, a rude
tace yaya Samar su
umma da su kaka suka
juyo umma Aisha da Ni
ne muka taso aguje
shima shararawa yayi
da gudu Yakarasa inda
muke’ muka rungume
juna kuka kawai muke,
yace yanzu umma
abinda yafaru akanku
kenan amma bansani
ba?
Umma tace dana
banaso natada maka
hankaline, nan dai muka
zauna aka kawo mashi
abinci yaci amma abincin
daci yake mai, saboda
zuciyarsa tana ta saka
mai yadda zan ramawa
umma ta abinda akai
mana, Bayan kakanmu
yadawone yace min
abinda nakeso da kai
kada kayi wani abu
domin yanxu kana
yimata wani abu
mahaifinka zai iya tsine
maka, saboda haka dole
a fara warware kullin
data yi masa, MEEMEE ce
tace nasan wajen wani
malami mutumin kirki
ne, ya juyo yace kada fa
ki kaimu wajen boka,
tayi dariya tace idan
munje zaka gani,
Suka karasa wajen
malamin shida MEEMEE,
makarantace babba,
sukarasa akayi masu
magana malam, suka
gaisa yayi masa bayanin
komai malam yace to
abinda nakeso daku ga
wasu ayoyi zan baku ku
karanta su aruwa
kubawa mahaifiyar
taku, da sunyi ido hudu
duk wani sihiri xai lalace,
domin dama ansa masa
kiyayyar tane aransa,
sukai godiya suka ba
malam abin sadaka
suka kamo hanya, suna
iso wa MEEMEE tayi
abinda malam yace ayi
ta bawa umma tasha,
yamma tayi yadauko
MEEMEE yakawo ta
gidansu, Washe gari da
safe suka nufi office din
abba Shida umma suna
zuwa suka shiga kai
tsaye, abba yana
rubuce rubucensa,
sunayin sallama ya dago
kansa yana hada ido da
umma kawai sai gani
mukai ya fadi kasa, da
hanzari suka karasa
yakama abba wanda
tuni yasuma, suka dauki
abba sai wajen malamin
nan,
suna zuwa malam
yafara karatu akan
abba, cikin kankanin
lokaci abba ya mike
kamar ba shiba, suka
hada ido da umma yace
hajiya tace alhaji yace
me nake anan? Umma
ta fashe da kuka, abba
tuni hankalinsa yatashi,
domin baisan abinda
yasa Umma kuka ba,
malam ne yayi masa
bayani, akan komai,
abba yayi kuka akamar
karamin yaro,
yarungume yaya Samar
yana kuka tare da bamu
hakuri, tuni malam yayi
bayani akan saki 1 da
abba yayiwa umma’ aka
daidaitasu, sukai addu’a
suka tashi, abba yanufi
office domin bai dakko
motarsa ba, mukuma
mukai gida, Tun muna
mota umma taji ina
waya ina cewa akawo
min sojoji kurata mota
uku, umma tace lpy?
Yaya Samar yace umma
inaso muna. Komawa
gida ku koma gidan
abba kedasu Aisha,
umma tace to amma
me zakai da sojoji? Yace
umma inaso nayi musu
hukuncine amma dan
allah kada ki hanani,
umma tace Samar in
banda abinka ai hakuri
shiyafi, yace umma
nasani amma zuciyata
bazata gafartaminba
idan aka ci mutuncinki
nakyale, ahaka dai
umma ta yarda da
abinda yace’ muna
karasawa gida su
umma suka dauki kaya
sai gidan abba, MEEMEE
ce tajagoranci shigarsu
umma gidan, suna shiga
yan uwan amarya
sukayo musu ca!!!
Amarya ce taxo wajen
umma tafara cewa
mara zuciya ansaketa
amma ta dawo, ♥MU HADU A WHATSAPP♥ 08096831009
|ADINGA COMMENT| →YAN` MATA↠↓BIGBOY NA GAISUWA↑
→Copyrightsâ†
[7:36am, 4/24/2016] Bigboy 2: MUGUWAR KISHIYA
*PART 4* end
Amarya ce taxo wajen
umma tafara cewa
mara zuciya ansaketa
amma ta dawo, Aisha
tayi caraf tace ke dallah
can allah ya tona asirinki
matsafiya kawai,
fatima tace wa Aisha
uwarki ce matsafiya,
tuni Na daga hannu na
zabgawa fatima mari
nanfa fada ya kaure
MEEMEE kokarin kare
umma kawai take, Yaya
Samar yana fitowa
daga wanka yaji ana
sallama dashi Yagama
shiryawa kakin sojojine
ajikinsa kamu nasa
black spaces a
fuskarsa, yana fitowa
yaga kurata kowa da
DG bellet a hannu sai
muzurai suke, yayi wani
murmushin mugunta
yana xuwa kowa ya
kame,
suka hau motoci sai
gidan abba, mutanen
unguwa kuwa tuni
kowa yafara dauko abin
hawansa don ganewa
idonsa HUKUNCIN yaya
Samar, Suna zuwa ya
sauko yakunna kai cikin
gidan kurata suka
takemai baya, jama’a
kuwa sun taru sai kace
taron daurin aure, yana
shiga yaga wani yadaga
hannu yana kokarin
marin MEEMEE da take
kare umma, saukar DG
yaji abayansa,
wanda hakan ya tilasta
masa yin wani wawan
ihu, nanfa kurata suka
shiga aikinsu, ihun maza
da mata kawai kake ji,
nikuwa amarya na
samu sai zura mata DG
nake tana ihu, aikin
kurata yayi tsamari
domin kuwa aje DG
sukai suka fara
karyawa, duk wanda
aka karya sai asashi a
mota, amarya tayo
waje aguje na bita tana
zuwa tsakiyar layi nasa
kafa na daki kafafunta
tuni zube ta kasa tashi
domin da alama itama
ta karye, mutane sun
zagayemu anrasa
wanda zaice yi hakuri,
motar abba ta faka,
abba yafito da sauri
yaxo yarikeni, wanda
hakan yasa kurata
tsayawa da aikinsu,
amarya tasa hannu
tarike kafar abba, abba
yasa aka dauki amarya
aka kaita gidan yan
uwansu suma sauran
can aka kaisu, suka kira
mai dori yabisu daya
bayan daya, Mukuwa
muka dawo sabuwar
rayuwa. Inda abba yasa
akayiwa umma da Ni
oder ta motoci guda
biyu masu tsada, ita
kuwa Aisha aka bata
motar amarya
(BUGATTI) dama
amarya bata taba hawa
ba, umma takira yaya
samar tayi mai
maganar aure,
ya sunkuyar da kai
domin bashi da ko
budurwa, umma tace
kayi shiru nyace umma
ai bawata tsayayya,
Aisha tayi caraf tace ga
MEEMEE yajuyo na
harareta, umma tace
yauwa kanwarka tayi
maka zabi, aikuwa haka
akai tuni aka sanar da
iyayenta, soyyayaya ta
kulli, har aka sa rana
amma ba asa da
yawaba, don haka tuni
ranar biki taxo aka sha
gagarumin biki, abba
yagina sabon gida su
umma suka koma,
shikuma shida
amaryarsa Sukai
barreck, rayuwa ta
dawo mana sabuwa,
Abba yaje gidan
amarya, yana shiga
yagata zama abin
tausayi, ta taso tana
rusa kuka tana neman
gafara abba baiyi wata-
wata ba ya mika mata
ta kaddar saki, yajuya
ya fita, amarya
tabiyoshi tana neman
gafara, amma ina tuni
yashiga mota ya yo gida
domin duk duniya ba
wadda yatsana sama
da amarya, kuma ba
wadda yakeso sama da
umma da “ya”yanta.
Idan su umma suna
zaune takan tunawa
abba abinda yafaru cikin
wasa amma abba sam
baya so, Yaya samar
shikuwa da MEEMEE ta
soyayyar kawai suke
shekawa.
THE END
Me zakuce game da
wannan labarin?
TAMMATBIHAMDULILLAHI GDY TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKIDAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI