MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 21

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 21
Ganin yaki denayi mata dariya yasa ta lalubo towel dinta ta daura ta kwanta tare da janyo bargo ta rufa sabida wani sanyi dataji yana shiga cikin jikinta. A hankali ya matsa kusa da ita tare da zura hannunsa ya rungumeta tana jinsa amm ta kasa yin koda kwakwaran motsi sabida jikinta duk ya Iafa a haka bacci ya dauketa shi kuwa kasa yi yayi se tashi ma yayi yaje yayi wanka sannan yayi sallah ya d’auki sallayar ya maida ita inda zai dinga kallon fuskarta. Yana jan carbi yana shafar gashinta tare da shafar fashin goshinta wanda yake dansiriri. Har aka kira asuba lNdo bata koyi juyi ba bare asaran zata tashi ya mike daga kan sallayar yashiga bathroom ya tarar mata ruwa sannan ya fito, a hankali cikin nutsuwa ya fara tashinta amma babu alamarzata motsa sai ya yaye mata bargon ya fara kokarin kwance mata towel tayi saurin tashi tana rarumarsa tana furta “barawo.ta dauka barawo ne sabida a tunaninta wannan uban gidan baza’a rasa barayin dazasu shigo yi musu sata ba. A mamakin ce Abubakar ya kalleta ganin yadda ta cakumeshi tayi saurin sakinsa tare da saurin komawa ta kudindine a barge yace mata. “Humairah a mimakwan yin auziya saiki furta barawo? Toh ina barawon tashi ki gaya min ko mafarki kikayi..?!” Tana cikin bargon tace “Allah mafarki nayi kayi hakuri.” “Toh tashi kiyi wankan tsarki sai kiyi sallah.” “Wane iri kuma dacta?!” Ta tambaya da mamaki yace “na janaba ko bakisan anayi bane?” 
Sai yanzu ta gane kenan a makaranta da aketayi musu bayanin wanka haila, wankan janaba da wankan biki shi yanzu wanda zata yi shine na janaba ikon Allah dan ita a karatu idan ba practical ba koh theories dakyar suke shigarta. “Kin iya ko..?!” Ya tambayeta tayi shiru ya kwanta a bayanta tare da janyota ya matseta, ihu ta farayi sannan tace. .. .. Toh sai nayi ne, ka gaya mana. ‘ 
Yace “Okey kin iya wankan tsarki na haila?” ‘Daga kai tayi yace “tashi ki nunin in gani k0 dai-dai kikeyi?” Dakyar ta tashi zaune tana gwada mai ya gyagyara mata sannan yace taje tayi amma ta canza zani.Ta shiga bathroom din da sauri wai dan yana kallonta, tana fitowa sukayi sallah sannan yace tazo suyi karatu, tundaga Nasi ya fara mata har akazo inda ta iya sannan yace toh zai dinga koya mata kullum da asuba indai yana gari. Gadon ya sake janta ita INdo bata sabayin baccin safe ba hakan yasa tace mai ita kallo zataje tayi ya hanata dole taje suka kwanta, romance dinta kawai yayi mai tsayawa a wuya dan tana karbar sakon yadda ya kamata kamin kace mene tuni lNdo tayi baci shima ya samu yayi har kusan 9:16am sannan ya farka yana zare jikinsa itama ta farka a kunyace dan ko kallonsa bata iya yi. Muje kitchen yau dakan mu zamuyi breakfast.” 
Kama hannunta yayi suka fita suna zuwa kitchen ya sargafe hannu a kirji yana jiran yaga ta ina zata fara, itama tsayawar tayi tana kuma bin kayayyakin kitchen din da ido. 
“Jiya na shigo da slender bari na hada sai ki soya kwai da tea.” 
Tace “Toh akan slimba din Zan dora.” “No Humairah slender itace abinda za’a zuba kalanzir toh ba shi za’a zuba ba gas za’a saka 
ajona na wannan sai idan kin kunna zai kawo wuta idan ya kare kuma zakiga yaki kawowa.” Jinjina kai tayi tamkar ta fahimta, shi kuma dayake yasan dawa yake tare sai ya kamo hannunta suka nufi bayan kitchen din, a kan idonta yasa dan watarana idan ba kowa ya zama na ta iya. Komawa cikin kitchen din sukayi sannan ya kunna cooker din saiga wuta INdo ta dinga murmushi kusan duk shi yayi komai tana kallonsa suna yi yana nuna mata amfanin komai na kitchen din komai saida ya nuna mata sannan suka kwashi breakfast din suka kai dining. Yauma kamar jiya daddare shi yayi feeding dinta taci sannan shima yaci suka koma wajan TV lokacin injinsu ya mutu suka kalli juna yace. “Muje daki ki gani.” 
Yana rungume da ita suka shiga ya dakko laptop dinsa ya kunna mata kallon yaga alamar tana masifar son yin kallo tana zaune a tsakiyar gado ya dora kansa a cinyarta tayi dariya tana kallonta. Hannunta ya kamo ya dora akansa tare da cewa. “Sweetie bazaki dinga shafani ba, please inason ki koyi soyayya fa ni Ina son love.” Shafa mai ta farayi ya danke hannun tare da cewa, “Bafa haka akeyi ba, haka…!” Ya fada yana rike da hannunta yana shasshafa kansa, haka Abubakar ya dinga tarairayar lNdo yana nuna mata abubuwan da zata dinga mai cikin ko wane irin abu ko yanayi sai daya nuna mata irin abinda zata yi mai tun tanajin nauyi da kunya harta fara sakin jiki tana yi mai ba tare da ya nema ko ya nuna bukatar hakan ba. Cikin sati daya INdo ta kuma wayewa da wasu abubuwan tayi kyau abinta ranar da ta cika kwana takwas ya dauketa sukaje gida su Mama suka dinga shi musu albarka lNdo bajin kai kannansa duk babu wanda bata wasa dashi sun dade Kafin su tafi gidan Sadeeq sai lNdo tayi mamaki ganin gidanta yafi kyau sai akayi sa’a bata kwafsa tayi maganar ba. Sosai suka sha hira shima Sadeeq ya sakar mata fuska Fateema taja ta suka kule daki, nan ma sun dade kafln Abubakar yace tazo suka tafi
Washe gari ya dauketa suka jajje gidan abokansa na nan sannan ya kaita har Munjibur park wayyo farin ciki a gurin lNdo ba’a musallatawa duk abinda taga anhau sai tahau shi kuma ya biya duk bata san saiya biya ba sha’aninta kawai takeyi sukayi hotuna wasu tare wasu kuma ita kadai. Sun dade kafin suka koma gida lNdo cike da murna ya kalleta shima cikin shaukinta da soyayyarta sannan yace. “Zo kimin tausa tunda yauma kin gajiyardani.”Zuwa tayi tana shan ice cream tana mai sannan shima ta bashi yasha wani shauki yana fisgarta bata san lokacin data kwanta a bayansa ba a hankali ta furta mai. “I love you mijina.” 
cikin dariya lNdo ta bugeshi a baya yajuyo tare dajanyo ta aikuma ice cream din ya zube a saman kirjinshi yace. “Aikuwa sai kin lashe shi kuma ki gama ki wanke ni ah bazan yadda ba.” “Ah my key nifa bani ce silaba kai kaiwajikinka haka.” Ta fada tana masa  tana diban na kirjin nasa tana sha yanzu duk ta waye bata 
kyama ganin shima baya nuna mata akan komai na jikinta. “Nifa inajin zafin na cukalin nan ki ajiyeshi.” 
“Toh baki zansa?!” Ta tambaya kai tsaye shima kai tsaye yace mata “Eh shi nake so.” 
Harshe tasa ta fara lasa har sai data sude tass sannan shima ya faki idonta ya dakko ragowar na robar ya barar mata a kirji yace. 
“Ashhh sorry bari na rama miki kema.” 
Dariya suka saki tare cikin dariyar tace. “Kaifa kana sane.” Ya rikota yasa baki tass shima ya lashe mata daga nan kuma al’amra suka canza. Ana gobe zai koma abuja suna kwance duk sun makale juna suna sauke ajiyar Zuciya kadan-kadan Abubakar yana shafar kanta yace. “Humairah banson tafiya na barki anya bazan tafi dake ba?!” Shiru INdo tayi babu amsa ya kumajanta jikinsa yana dan shafarta tana biye mai ya kuma cewa. “Kinyi shiru Humaira ko dama kin kagara na tafi ne.?” 
Tace “A’a bansan abinda zance ba nima shi yasa nayi shiru fa.” “Okey kema kina son ki bini ko?” 
Tace “Eh mana.” Hannunta ya riko ya dora a kirjinsa tare da cewa. “Ina sonki Humaih ina kaunarki ban tabajin Ina kaunar mutum ba kamar yadda nake sonki, please kema ki soni koda bekai yadda nake miki ba kinji..?!” “Toh ai Ina sanka nima.” Ta fada cikin sanyin jiki suka rungumi juna da haka sukayi bacci, washe gari tunda asuba suka yi wanka INdo tayi kwalliya irinta kauye tasa zani daban riga ma haka da dankwali. Abubakar na shigowa dakin daga shi sai boxer da singlet ya kalleta yana murmushi yaga kwalliyar tayi mata kyau ya karasa ciki yana cewa. “Woww sweetie gaskiya sai na biya wannan wankar I like it.” “Toh nawa zaka biya domin da tsada…?” Ta tambayesa tanajan hancinsa, bakin gado ya zauna yana rike da kugunta yace. “Bari kigani.” Kissing din bakinta yayi duk ya kwashe janbakin datasa ya matseta ajikinsa yace. “Allah ya miki albarka matata kafln in dawo Zan samar miki makaranta damun koma saiki shiga.” “Kanason nayi karatu da yawa, nikuma kaga ban iya turanci ba.” Ta fada tana shafar sajansa ya sanya kansa tsakiyar kirjinta yana goga fuskarsa ajiki yace. “Zaki iya kema sweetie ai da koyo akasan gwani, abaya ma dandai baki tsaya kin koya bane amma yanzu kisa aranki cewar kema zaki iya turanci kinji ko..?!” “Allah yasa toh..” Ta fada yace “Amin sai kuma abani bye~bye dan bazan tafl haka ba” 
Rufe fuska tayi ta zauna kan cinyarsa wannan karan itace ta fara sanya mai mouth nata cikin nashi ya kara tabbatar da lallai tana daukar maganar tana kuma jinta tare da aikata ta a aikace. Sai daya samu nutsuwa sannan sukayi wanka kamar karsu rabu duk da yace mata kwana biyar zaiyi yazo yayi weekend amma gani yake tamkar rasa ta zaiyi, itama haka ta dinga cewa ya barta su tafi abuja tare dama bata taba zuwa ba amma ya dinga kwantar mata da hankali yace kila ma jibi ya dawo idan yaje ya rage wasu abubuwa. ‘Dakinsa suka koma ya shirya duk ta nanike mai ya kalleta yace. 
“Idan na tafi kiyi tafiyarki gidan Mama ko gidan twinnie ki zauna kuyi hira zuwa yamma sai ki dawo dan nace dasu Haleema suzo su zauna a nan harna dawo kinji.?!” “Toh..” Tabashi amsa ta fesa mai turare sukaci abincin daya dafa musu suna gamawa sadeeq nayin knocking. Sai data fara sanyo hijjab sannan Abubakar yaje ya bude masa kasan cewar ya hanata zama a haka idan wasu suka zo. 
“Aishatu Hamza…” Cewar Sadeeq cike da zolaya tayi murmushi tare da cewa. “Malam Sadeeq ya gida..?!” “Kalau.” Yabata amsa Abubakar yace. “Twinnie gidana a hannunka please ka kular min da babyna.” “Au wai kana nufin sai an kula da ita? Tab Aisha ai ta iya haura katanga bakada case da ita ka kwantar da hankalin ka.” 
lNdo ta turo baki haushinsa ya cika ta Abubakar ya janyo ta tare da cewa. “Kabari twinnie ai dane kuma kaima ai kayi kana yaro.” Ya kalli INdo tare da cewa “Sorry sweetie karki kulasa Zan dawo na daukeki.” Suna dariya dukansu suka fita Abubakar ya shiga mota shida Sadeeq zai saukesa gidan Mama idan yaje, INdo ta zagaya Bangaran Abubakar idonta yayi ruwa murya na rawa tace.”Allah ya kiyaye hanya.” “Amin.” Ya fada yana zuro hannu sukayi musabuha yaja motar suka bar gidan, tana share hawaye ta rufe gate din tare da shiga cikin gidan. Suna hanyar zuwa gidan Mama Abubakar ya dinga ba Sadeeq hakkin lurar mai da gida musamman ma lNdo abin ya dinga bawa Sadeeq mamaki wai yau lNdo ce take da matsayi a zuciyar dan uwansa, koda yake yafishi sanin lNdo tun a kauyan Sani. Bayan sunyi sallama da mutanan gidan ya kama hanya ya tafi bayan ya bugawa lNdo waya yace mata ya tafi tayi mai fatan sauka laflya. 
Karfe 11:36am tana zaune a falo tana kallo bama taje gidan Maman ba ganin an kawo wuta, shigowa yayi kai tsaye gidan tana ganinsa ta mike da gudu taje ta rungume shi kamar yadda ya sabar mata. Jin jikinsa yana rawa ne yasan ya lNdo dagowa tana kallonsa kirjinta ya fara bugawa sam bata gane bashi bane ta sha’afa da kayan dayasa tace. “My key menene? lnzo mutafi Wani kallo dataga yayi mata ne yasa hankalinta dawowa jikinta ta zaro ido tana kallon 
fuskarsa tace. “Malam Sadeeq kayi hakuri na dauka Yaya Abubakar ne.” Da kyar Sadeeq ya samu ya bude baki yace. “Aisha jeki dakko hijjabinki zamu gidan Mama.” 
lNdo ta kallesa cikin sauke numfashi tana warware dankwalinta tayi mayafi dashi tana cewa . 
“Ah ai inajin sai anjima zani idan ma banjeba ai yace su Haleema zasu zo.” “Ki dakko hijjab nace miki ke nake jira bawai surutu ba.” Juyawa tayi tana kunkuni ta dakko ta fito shi kuma ya juya ya fita. Saida ta fito sanye cikin atamfa blue da zanen ganye fari ta sanya blue din mayafi suka fita ya rufe gate din suka shiga mota. Kasa tukawa yayi jikinsa sai rawa yake yi INdo ta bishi da kallo cikin mamaki karshe ya fito daga motar yace. “Fito muje.” A kafa suka taka har bakin titi ya tarar musu napep suka shiga aka kaisu gidan Mama lokacin har mutane an fara taruwa a kofar gida Sadeeq ya cewa INdo. “Shiga ciki gurinsu.” 
Yana fada ya juya yabarta ita kuma ta nufi ciki tana bin mutanan da kallo. Tana shiga parking space taji abbansu yana waya yana cewa. 
“Eh wallahi Abubakar dinne…. 
Tofa shin meya faru da Abubakar kodai kodai muje zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *