MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 23

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 23
Dakyar suka bareta daga jikinsa har rigarsa na yagewa da yake wani yadi ne ajikinsa 3 Quarter yayi saurin ficewa daga dakin lokacin gidan ya cika da mutane kasan cewar an kawo gawar.
INdo kuwa sam bata yadda da cewar Abubakar ya mutu ba sai dai ta kasa dena kuka ganin yadda kowa yake kokarin ganar da ita. Da gudu ta shige toilet ta kulle kanta a ciki tana ta faman kuka da surutai barkatai, anyi-anyi ta bude taki kunsan cewar dama akwaita da taurin kai. Mintuna kalilan aka shirya Abubakar aka shigo aka sanar musu, Umma da Mama zasuje gurin gawar Abba yace su taho da Aisha. Kofar bandakin Umma ta tsaya tana kiranta 
amma fur taki amsawa sai da Umman tace. “Aisha fito muje ki gansa da kanki.” Tanajin haka ta fito da sauri ko ganin gabanta batayi hijjab din jikinta yayi sharkaf da hawaye da majina suka riketa suka fita zuwa sitting room inda Abubakar yake a kwance a nannade, Sadeeq na ganinta yayi wuf yafice ga wani irin sarawa da kanshi keyi ko gani bayayi sai dai ya dafa bango. 
Ganin mutum a kwance sambal anrufeshi ta ko’ina yasa jikin INdo ya fara rawa ita kanta bata san lokacin da take fitsari ba sai da Mama ta durkusa kasa saitin kafarsa tasa hannu kasan carpet din taji ruwa, kallon INdo tayi taga ta kurawa gawar ido tamkar wata gunki kam ta janyo ta tuni INdo ta karasa wajan kanshi tana niyar budewa cikin azama uncle Ahmad ya janyeta ta kallesa tace. “Kana nufib bazan ganshi ba? Niko..Niko? Shikenan Allah ya sakamin.” 
Su Mama na tashi daga gurin maza suka shigo aka dauki gawar dan fita ayi masa sallah. INdo na kallansu aka fita dashi uncle Ahmad ya bawa Umma INdo sannan shi ma yafice. Bata yadda sun shiga ciki ba anan suka zauna Mama ta shiga ciki ta kira su Fateema suka koma can dakin, duk suna jiyo sanda ake mai sallah bayan an gama akayi addu’a sannan maza suka fita danyi masa rakiya zuwa gidansa na gaskiya. Sunaji aka fara tada motoci, mashina da sauran abin hawa aka tafi INdo ta kuma fashewa da kuka tana rike hijabinjikin Fateema. Babu abinda take tunowa face rabuwarsu da safe da magannanunsa najiya da lokacin daya dakkota daga gidan kunshi nan da nan tafara girgiza Kai cikin ranta gani take taya za’ai ace ya mutu daga yin aure bayan duk ga wadanda suka rigasu yin aurenan ba harsun tsufa sai mijinta shine zai mutu bazai yuwuba. 
Har kusan magriba INdo kuka take amma hakan be hanata duba wayarta time to time ba sabida yace daya sauka zai kira ta amma shiru ko please call me babu. Kowa na tashi yayi sallah amma ita takiyi babu azahar da la’asar ga magriba tana kawo kai haka kuma gidan damkam yake da jama’a maza da mata. A kofar gida ma Sadeeq duk da cewar akan idonshi aka saka gawar dan uwan nashi amma hakan be hanasa tunanin Abubakar zai 
dawo garesa ba, gani yake kamar tafiyar daya sabayi ce yayi zai dawo duk kuwa da 
kunnuwansa suna jiye mai gaisuwar da akeyi mai. 
Ana kiran magriba su Inna na futowa daga mota, driver din daya kawosu ya kira wayar Sadeeq ya sanar mai da zuwan su. Dakyar ya iya mikewa yana fitowa daga cikin motane sai tsayar dashi suke suna yi mai gaisuwa harya fito yaje ina da suke tsaye. Kan Inna na kasa ta rufe fuska da hijjabinta sai Nafeesah Sageeru da Shehu, shi kuma malam Hamza ya shiga cikin mutane yana gaida su dayi musu gaisuwa. Rabon da Sadeeq yaga Inna tun randa malam Hamza yaje ya tasa keyarsa akan kincin abincin INdo lokacin da yace su dinga brush yaje gidan be sake sanyata a idonsa ba, ko lokacin daya bata dari biyar besan ita bace. 
Karasawa yayi yana tangadi sabida tsananin ciwo da kanshi yake masa, gaidashi su Shehu suka dinga yi gani suke suma kamar Abubakar d’inne sai dai shi sajansa ya kewaye mai baki sabanin Abubakar dashi har a kumatu yana da gashi. Gaidashi suka yi shi kuma ya 
gaida Inna sannan yayi musu jagora zuwa cikin gidan. 
‘Dakin su ya nufa sabida nan yaji ance matar Abubakar din naciki, suna shiga dakin cike yake da mutane Nafeesa ce ta fara magana tana tambayar su ina lNdo matar kusa da ita tace bata Santa ba sabida su da Humaira suka santa sai da Sadeeq yace. “Fateema Ina Aisha ga Maman su…” 
INdo najin muryar Sadeeq ta mike a zabure fuskarta na bayyana fara’a ta mike duk ta tsallake mutanan gurin tayi gurinsa yana ganin haka shi kuma ya juya zai gudu tayi saurin riko mai hannu. 
Kasan me?dama nace musu baka mutuba amma sunki yadda, wallahi nasan dama 
bazaka mutu ba ko mutuwar ce toh malam Sadeeq ne zai mutu kayi…” Da sauri ya fide hannunsa ya nunata da yatsansa cikin daurewar fuska yace. 
“Aisha kin rainani ko? Toh ban mutuba zoki kasheni ki tado da wanda ya mutu kinji? Haba ance miki shine ya rasu a tunaninki da ana zabar wanda zai mutu zan yadda ya mutune? Ko kinfini sonshi ne? Ki kuka da kanki karna kuma shigowa gidan nan ki rikeni wallahi 
wawuya kawai.” Matsawa tayi a hankali mutane kuma sai kallonsu sukeyi Sadeeq ya juya ya fita ita kuma INdo ta sanya kanta cikin kafafuwanta sai kuka kukan da batayi shi a dazu ba. Nafeesah na hawaye taje tana rungumeta kafin mutane suzo su zanyeta gabaki daya Inna ta kasa koda motsi kwakwara, tasan lNdo akwai kulafuci idan tanayi dakai toh duk wulakancin da zakayi mata baxata barka ba hakan ne yasa suka shaku da Rukayya makociyar su a can kauyen Sani. “Ya tabbata cewar dacta ne ya mutu wannan malam Sadeeq ne, Umma kinsan Allah tun a makaranta da dacta ya ganni ina satar amsa ban sake kulashi ba heda yaje Saye ya dawo dani kauyan sani yace zai maidani in waye inyi karatu zai dinga siyo min kaya masu kyau bamu sake yin wani fada dashi ba, kunga ya siya min kaya duk garinmu babu me irinhi da kayan kwalliya ya koyan inda zanje a gyara min gahina karhe yace zai aureni, gahi ya aureni amma ya mutu wayo Allahna nahiga uku…!” 
lNdo ta fada tana kuka har lokacin bataga su Inna ba sai afkin bawa mutane labari takeyi. Mama ce ta shigo sabida Fateema taje ta gaya mata cewar an tasata a tsakiya sai surutu takeyi shine Maman tazo. Hannunta ta kama suka shiga ciki bayan Mama tace su Inna su shigo. A d’aki suka zauna sai a lokacin INdo taga Nafeesah tayi saurin rikota tare da cewa. “Nafi yo kuma gaisuwar dacta kuka zo? Tun yauhe? Ina lnnata…?”Gata nan.” Nafeesah ta fada tana nunawa lNdo Innarsu, da gudu INdo ta ruga jikinta suka kusa faduwa ta dinga kuka domin ganin su Inna yasa ta sake tabbatar da hakan. Da kyar da sidin goshi da nasiha Mama tace. 
“Aisha ya kamata kije kiyi sallolin da baki ba fateema tace bakiyi kodaya ba, kinga idan yanzu kika mutu toh bazaki hadu da Abubakar acan ba domin duk wanda baya sallah Allah baya hadaku da wanda kukeso…” Ai tanajin haka ta mike, toilet ta shiga tayi alwala tazo tayi sallolin. Fura da nono Mama tasa aka siyowa lNdo amma duk kwadayin INdo ji tayi cikinta a koshe yake batajin yinwa tun safe da sukaci abinci dashi. Ranar basu rintsa ba har washe gari. Da safe ma bataci komai ba sannan tana sanye cikin hijjab Mama ta debo ruwa a baho tazo ta tsulmiya kafar lNdo a ciki tana goge mata kunshin kafarta wanda yake sabo dal shi ya kaita akayi mata, ganin be fitaba gaba daya yasa Mama ta bata safa tasa dan ta rufe kunshin. 
A haka suka ci gaba da karbar gaisuwa bayan INdo ta tabbatar da cewarta rasa dacta shi kenan zata koma kauye ta cigaba da rayuwa kamar yadda take da. Sadeeq kuwa baya shigowa gidan iyakarsa kofar gida, ko abu yake so saidai ya bugawa Fateema waya tayi mai kota karbo mai a haka har akayi uku wanda aranar ne mutuwar ta kuma zama kamar sabuwa. Sunyi kuka sunyi kuka sosai INdo kuwa har ta saba da zama daki da bata iyawa a ranar Rukayya tazo da zasu koma suka tafi dasu Inna aka bar mata Nafeesah kasan cewar 
sai anyi bakwai za’a maida ita kauyan Sani. Sai Ranar da aka yi bakwai Sadeeq ya shiga gidan ransa a hade dan karma ta kuma yin gigin tabashi, bayan sun gaisa da mutane harda su Inna da sukayo tafiyar sassafe ya shiga ciki gurin Mama dake nemansa. Zaune ya tarar dasu INdo ta jikinta ya raba ya zauna kusa da Fateema dake zaune jikin gado yace. “Mama gani.” 
Yauwa Sadeeq dama cewa zanyi zaka kai Aisha ta dakko kayan da zata bukata, idan ta 
dibo sai ka rufo gidan.” “Okey toh, Fateema idan kun shirya kimin magana ina waje.” 
Fateema tace toh shi kuma ya mike yabar dakin INdo ko dago kai bata yi ba bare asaran zatayi wani abun. Sai wajan la’asar sannan aka samu tasha tea sabida ciwon ciki daya 
kamata wanda a lokacin Sadeeq saida yaji tsoro kar ace cikinta yayi wani abun domin 
yanzu burinsa da fatansa yasa INdo nada cikin dan uwansa hakan ne kawai zai sanyaya 
ransa har soyake ya tambayi Mama amma ya kasa. 
Da dare bayan sunyi sallan isha’i Fateema ta buga mai waya cewar zasu fito yace yana jiransu a waje, cikin zurmeman hijjab INdo ta Fito suda Fateema dasu Haleema, Nafeesah da yayya Hawwah. Duk baya suka shiga Fateemah kuma gaba suna tafiya kowa na fadar maganarsa ta karshe da ganin karshe da yayiwa dacta Abubakar ita kuma lNdo tayi shiru domin nata ba mefad’uwa bane, suna tayi har suna fadan halayyar kowa amma Sadeeq be kulasu ba har suka karasa gidan ya tsaya ya bude gate din sannan ya koma motar ya karasar dasu ciki har parking space. Duk da cewar duhu hakan be hana INdo gane gurin da sukayi parking ba, kawai ta fashe da kuka Sadeeq ya karasa inda injin gidan yake ya tayar musu yace idan sun gama tayi mai magana ya fita. 
Suna shiga gidan INdo ta shige daki tare da fadawa gadonta, kullum idan zasu kwanta cewa yake anan zasu kwana gadonta yafi dadi duk dan kartayi tsammanin ita nata bekai nashi ba amma kullum sai yayi santi, ita kuma tace nashi yafi idan yaga ta dage sai ya barta su tafi can din sabida yana son farin cikinta yau gashi zata koma kauyan su inda ko katifa babu bare tayi zabin da tayi na sati biyu. Alawar tom-tom dinsa ta hango wadda yake sha idan zai kwanta a kasan pillow ta janyo ta tare dayin murmushi tunawa da daran dazai tafi yana sha ya zura mata ragowar ta bakinsa cikin nata ta kuma fashewa da kuka su yayya Hawwah na lallashi. 
Bata iya daukar komai ba sai Fateema ce duk ta dibar mata komai da komai tasa cikin trolley. Tashi INdo tayi ta shiga ko’ina na gidan a kitchen ma sai ta tsinci kanta da murmushi idan ta kalli wani abun ta tuna a yadda ya koya mata musamma farkon yin markade a blender. A d’akinsa kuwa ta dad’e har saida suka biyota suka fito da ita sannan suka yiwa Sadeeq waya yaje ya d’auke su tasan shikenan itada gidan wanda ya hada ya 
raba. Washe gari Sadeeq ya shirya zai maidasu, hatta Abba saida yayi kwalla lokacin da aka rako INdo tayi mai sallama, Fatan alkairi yayi mata tare da addu’ar samun miji nagari wanda zai sota kamar yadda marigayi yayi. Su Mama har mota suka rakasu suna ta kuka Sadeeq yaja motar harda Fateema suka tafi maida lNdo kauyan Sani… 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *