MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 26
A bangaran su Sadeeq kuwa dakyar ya iya fita lecture, itama Fateema bata fasa yi mai breakfast ba sai dai duk babu wanda ya iya ci. Yana tafiya Fateema ta shiga cikin daki taci kuka sannan ta d’auki wayarta ta k’ira Ummanta, tana dagawa ta fashe da kuka hankalin Umma yayi matuk’ar tashi tana tambayar lafiya.
“Kiyi shiru kiyi min magana dan sai kin min bayani sannan zansan matsalarki.” Cewar Ummanta cikin lallabata dan ta gaya mata. Cikin kukan Fateema tace. “Umma Sadeeq ne ya kara aure jiya…”
Tayi maganar muryarta na hardewa hankalin Ummanta ya tashi tace. “Fateema a ina yayi auran bako labari?””Umma yazanyi matar d’an uwansa aka aura mai jiya shima be sani ba, sai da Abban su ya kirasa ya gaya mishi.” Ji tayi Umma ta sauke ajiyar Zuciya hankalin Fateema ya tashi tana cikin bargo amma wani irin mugun sanyi takeji yana ratsata,jita yi Umma na cewa. “0ho Allah sarki, Fateema toh karki damu kinga kema wannan kaddarar ba taki ta sauka a kanki ba, kiyi hakuri ki zauna ki taya mijinki zama da ita ba’a san abinda Allah ya shirya ba akan al’amarin. Ina son ki kwantar da hankalinki karki sake ki nuna masa cewar kina bak’in cikin wannan auran idan kikayi haka nan gaba kezakiji kunya sabida shirin na Allah ne dan da be dauki Abubakar ba da hakan baxata faru ba, ki kankaro mana mutuncin mu ta hanyar k’arbar wannan auran cikin nuna farin ciki koda ba hakan bane a ranki.” Wani irin kuka Fateema ta kuma fashewa dashi wanda da kyar ta iya yin sallama da Umman tata. Kuma kudindinewa tayi a cikin bargo tana cigaba dayin abinta har zazzafan zazzabi ya sake rufar mata. Sadeeq kuwa yana kammala lecture ya fito daga school din, kai tsaye ya wuce gidansu Fateema ya samu ba kowa sai Umma. Shiga yayi har cikin falonta ya zauna suka gaisa cikin fara’a ba tare da ta nuna mai komai ba.
Cike da ladabi Sadeeq yayi ma Umma bayanin yadda lamarin ya wakana sannan ya dada da nunawa Umma ta yiwa Fateema nasiha tare da tayashi bata hak’uri, Umma tayi murmushi tare da cewa. “Karka damu Sadeeq Allah ne yasan abinda ya shirya har akan ta faru, insha Allahu kuma zanyi mata nasiha kaima sai kayi hakuri kasan irin wannan lamarin sai mutum yana kawar dakai dan zakaga ban-banci dabi’a akan ta baya da kuka yi.” Sadeeq yana sunkuyar dakai yace, “lnsha Allahu Umma na gode Allah ya kara girma.” “Amin a gaida mutanan gidan ace muna yi musu Allah ya sanya alkairi.” Batare daya amsa mata ba yayi tafiyarsa baya tunanin ma zai sake zuwa gidan harsai ya samu labarin cewar Indo bata gidan. A kwance ya tarar da ita ko gidan bata bude ba sai da ya sanya mukulli ya bud’e. K’arasawa yayi tare da yaye bargon da ta rufa dashi ya taba jikinta mai dauke da zazzafan zazzabi nan da nan hankalinsa ya tashi ya hau gadon gabaki daya ya d’agata zuwa jikinsa yana kokarin san su hada ido amma taki bari hakan ya faru.
“Baby na kinji jikinki kuwa? Meya sameki?!” Wani kukan ne ya sake zuwar mata cikin rawar murya tace mai.”Banajin dadin jikina kaina ciwo yake.”
“Oya tashi muje asibiti Allah yasa ma nayi ajiya.” ‘Dan janye jikinta tayi ba tare da ta kallesa ba ta koma ta kwanta tana cewa… “Karka damu basai munje asibiti ba dan yanzu ma haka ciwon mara nakeji.” “Wayyo Allah baby na bana son wannan abun wallahi, nida da yadda za’ayi ma da nasa an tsayar miki ki denayin sa.” Shiru tayi mai batayi magana ba shi kuwa duk so yake yi ta dawo daidai yadda suke amma ina sai tashi yayi ya koma falo dan bazai juri ganin yadda take sharesa ba, ba kuma yason ya dinga baata mata rai. Yana zaune a falo yana transfer din kudi a account din mutanen daya karbi kaya yaji wayarsa na ruri, d’auka yayi yaga Mama sai da kirjinsa ya buga. Addu’a ya fara yi Allah yasa kartayi mai zancen INdo domin sam baya kaunar yaji sa. “Hello Mama antashi lafiya?!” “Eh Alhamdulillahi tunda bakaga damar zuwa ba, mekakeyi yanzu?!” “Kiyi hakuri Mama bakin zuwa nayi ba yanzun nan na dawo daga lecture, ina gida nazo?!” Eh dama cewa zanyi ka shirya kazo kakai Aisha garinsu ta danyi musu kwana biyu kafin ka samar mata gurin zama.” Hade rai yayi tamkar a gaban Maman ransa na suya baya son kuma komawa garin nan duk da cewar sunyi zaman amana dashi amma a yanzu ga Fateema ba lafiya sannan ance yazo yakai INdo garinsu sabida kawai shi aka sakawa ido komai sai ace shi dama shi ya mutu ba Abubakar ba da duk ba’ayi mai wadannan abubuwan ba. “Kayi shiru Sadeeq kona shirya tunda nina dakkota sai na mayarda ita.”
Yaji Mama na fada cikin fada-fada. Lumshe idanuwa yayi tare da shafar sajansa yace.
“A’a Mama kiyi hakuri bari nayi wanka zanzo.”
“Toh shikenan kazo kowane lokaci ne sai ka kaita duk ka gama walagigin naka muna nan muna jiranka.”
Tana kammala fada ta katse kiran shi kuma yabi fuskarwayar da kallo, shikam ya shiga uku wannan wace irin kaddara ce ta hau kansa. Ya kasa gane abinda Abubakar ya gani a gurinta har yaji yana sonta, ita ba ilimi ba sannan ba Kudi ba, ba wani shegen kyau ne da itaba sai shashanci gabuntaka kauyanci da rashin wayewa duk ita kadai shikam a takaitashi da auranta da aka bashi.Tashi yayi cikin sanyin jiki ya shiga daki, fuskar fateema ya kalla sannan yaje ya shafa fuskar yana kallonta. A hankali ta bude sukayi ido hudu yace. “Tashi kisha magani kici abinci zansa su Haleema suzo su tayaki zama Mama ta kirani wai zankai Aisha gidan su yanzu kinji.?!
Kirjin Fateema ya fara harbawa ganin tun yau sun fara raba abubuwa tsakaninsu, da kyar ta daure tace. Toh sai kun dawo amma kabar su Haleema basai sunzo ba babu abinda zasu yi min.” Magani ya dakko ya fita kitchen ya dakko ruwa sannan ya zauna kusa da ita, dakyar tasha maganin sannan ta kwanta shi kuma ya shiga cikin bathroom yayi wanka gaba daya ma besan abinda zaiyi ba akan INdo. Fitowa yayi daure da towel a k’ugunsa ya karasa wajan mirror duk Fateema na kallonsa a sace ta cikin bargo. Sai daya gama goge ruwanjikinsa sannan ya zauna kan stool yana shafa mai. Yana gamawa ya nufi wardrobe ya zaro wata shadda blueblack ya sanya tare da dakko bakar hula zannah ya kafa kan goshi, ya sanya agogon hannu ya zura takalmi baki tare da feshe jikinsa da turare ya dauki comb brush ya kwantar da gashin daya zagaye kyakyawan bakinsa.
Duk abinda yake yine yayi amma da Fateema tasan inda zashi sai taji kirjinta na harbawa zuciyarta na zafi wani bakin kishi ya mamaye ciki da wajan zuciyarta bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba tayi saurin maida fuskarta cikin bargon ganin zaijuyo. Sadeeq ya k’arasa gurinta bayan ya durk’usa saitin fuskarta ya kura mata ido. “Babyna karki dinga sanya ranki cikin damuwa, kece mace ta farko dana faraso na kuma fara aura na fara baiyana mata sirrina na kuma yadda da ita, ina so ki dinga alfahari da hakan kina cikin zuciyata bazan taba yadda wani ya bata miki rai ba k0 ya gaya miki ba dadi in kyalesa. Ke ko Aisha da aka aura min idan batayi miki biyayya ba sai na saba mata wallahi ke nine nace ina sonki ita kuma mutuwar twinnie dinane yasa aka bani auranta karki dinga damuwa kinji ko.?!” Sai a lokacin Fateemah taji sanyi ko ba komai ya kwantar mata da hankali da dadadan kalamansa masu zak’in zuma. Kallonsa tayi idanuwanta duk sunyijah tsabar kuka sannan ta zuro hannu ta shafl fuskarsa tace. “Nagode da wannan matsayin daka bani, ka tashi kaje kaga da nisa Allah ya dawo min dakai laflya, a gaidasu Mama.” Murmushi yayi mata tare dakai bakinsa kan nata yayi kissing d’inshi sannan ya mike tsaye yana ce mata. ‘ “Amin babyna sai na dawo.” Fita yayi ya shiga mota yabar gidan. Kai tsaye gidan Mama yayi, a k’ofar gate yayi parking sannan ya fito ya shiga gidan cike da takama dan yaujinsa yake tamkar akan iska. Yana shiga kannansa suka hau gaidashi ya amsa musu sannan ya lek’a dakin Umma ya tarar tana sallar azahar ya koma ya shiga dakin Mama.
cike dakin yake da kamshin turaran humra Sadeeq ya bude hanci yana shaka, tsaye yaga lNdo ta gama daurin d’ankwali ya kalleta tare dajinjina kai. ldan besan asalin lNdo ba da ace yau shine karo na farko daya fara ganinta toh bazai mata hausa ba dan babu abinda zai hanashi dauka cewar batayi degree ba a boko. Sai dai kashhh shine yasanta yasan ko wacece a fannin dakikanci da rashin son karatu tun batakai haka ba dan haka yana shiga gurin Mama ya nufa yana mai cire hular kansa. “Mama na ina wuni?!”
“Lafiya lau Sadeeq na d’auka ma bazaka zo yanzu ba, ya gidan ya Matar taka?” Sadeeq ya koma bakin gado ya zauna yana cewa.
“Haba Mama na isa inki zuwa, lafiya lau take tana gida ma batajin dadi Yayi maganar yana kuma karya karin hularsa. lNdo kuwa ci kanka batace masa ba Mama na ganin ikon Allah taga wazai fara yiwa wani magana sai taga kowa yana harkar gabansa. Kasa yin shiru Mama tayi sai da tace. “Aisha wai bakiga Sadeeq bane, naga ko gaidashi bakiyi ba!“ Ba kunya INdo tace, “Mama ai yace idan na sake ganinsa na kulasa tom dina, har wawuya yace min a ranar.” Baki bude Sadeeq ya kalleta, rabon daya ganta tun rasuwar Abubakar sai jiya da Abba ya hadasu sai kuma yanzu ammaji sharrin da tayi mai cikinjin haushin ta yace. “Karki rainawa mutane hankali yaushe na fada.?” Nan ma ba tsoro bare kunya tace.
“Lokacin rasuwar marigayi sanda nazata bashine ya mutuba Ina murba na rikeka ka tureni kace karna sake kulaka, a lokacin ne na tabbatar da cewa Kaine malam Sadeeq, shi yasa bazan gaida kaiba tunda kace haka.” Tsaki yaja tare da maida hularsa kansa, gaba daya ma besan ya fada ba yasan dai lokacin ta bashi haushine. Lallai yarinyar nan akwaita da riko toh kar Allah yasa ta gaidashi sai me
(so what). Mama ce ta kalleta cikin nuna mata martabar miji tace. “Aisha ya kamata ki ajiye komai daya wuce tsakaninki da Sadeeq, yanzu mijinki ne dole zaki mai biyayya kamar yadda musulinci ya gindaya. Yanzu ki gaida shi bana son wani tashin zance.” Babu yadda zata yi domin a haka tana ganin kima da darajar Mama, cikin turo baki tace mal. “Ina wuni?!”
Dan kar shima Mama tayi mai magana yasa shi amsawa a takaice yace. “Kalau.” Mama tajijjiga kai tare da rike habarta, Sadeeq kawai zatajawa kunne domin shine miji kuma shine da INdo duk abinda ya dorata akai shi zatayi ta kuma kara akan wanda take dashi zama tazo yaki dadi suji kunya amma zata bari sai ya dawo daga kaita tukunna. Tashi yayi ya fita bayan yace su sameshi a waje. Sosai sukayi sallama da mutanen gidan suna mata fatan sauka lafiya lNdo na amsa musu. Gaba Haleema ta bude mata babu gaddama ta shiga shi kuma Sadeeq yaja motarsa suka wuce INdo sai dariya take tanajin dadin yadda duk suke sonta. Tunda suka fara tafiya yake amsa waya duk ya cika mata kunne, hannu ta zura ta kunna redion motar dan ta riga ta iya Abubakar ya nuna mata sannan ta kunna A.c ta zuge glass d’in kusa da ita. Sadeeq ya sanya hannu ya kashe redion yana wayar sa itama ta kuma kunnawa tare da cewa.
“Haba Malam Sadeeq kana wayarka mana ni kuma inajin redio na bashi kenan ba.”
Wata muguwar harara ya watsa mata ta tabe baki tare da juyawa tana kallon hanya. Abinda yake kona mata rai da turanci yake maganar sai Hausa da yake dan cillawa. Wayarta ta dakko wadda tun Abubakar ne daya sai mata ta fara daukar photo tana selfie style kalakala ko kulata beyi ba harya gama wayar ya ajiye ta.
Gajiya yayi kunnuwansa sun cika da karar camera ya warce wayar daga hannuta tare da cilla mata ita kan cinya yace.
“Ke bana san kauyan cifa.”
Kallansa tayi hannunta rike da habarta tana cewa …..
Hmm ko mai zai faru muje zuwa