MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 30
Hannu ya kai zai taba ta amma sai ya kasa, kallon bayan ta yake yi kawai zuciyarsa na tsananin harbawa.Tashi yayi ya koma gefen gadon ya dan zauna a hankali ya kira sunanta
cikin sanyin murya a kuma dai-dai kunnanta yace. “Aisha bari muyi magana kota minti daya ce please.” Motsi INdo ba tayi ba bare yasa ran zata juyo ko ta tashi zaune, yana jin yadda take sauke ajiyar zuciyar ta amma ji yake tamkar tashi ake bubbugawa sabida tsananin yadda yakeji. Hannu ya kai ya riko kafadunta ta baya amma ko motsi bata yi ba ta dakire mai daga kwancen sai ya samu kanshi da kwanciya a bayan ta ya rungumeta a jikinsa tsam amma still bata motsa ba, ya dora kansa a wuyanta yana shafar kitson kanta zanan hannu, nan ma ko gezau lNdo bata yi ba.
Duk wani hanyar lallashi da Sadeeq ya sani yabi lNdo dasu amma taki motsi duk da cewar tana numfashi hasalima idanunta biyu amma ya gagara ko mirgino da fuskarta gurinshi
sabida yadda tayi mai taurin kai ta kafe a guri d’aya tamkar mutum mutumi.
“Aisha me yasa bakya jin maganata ne? Shin baki san matsayina a gurinki bane kike yimin haka? Nace ki tashi dan Allah zamu yi magana kinji ko..?!” Wayyo Allah..! ko pillown kanta be motsa ba bare ta mike, Sadeeq yayi ya kada ya raya, yayi magiyar yayi lallamin tare da lallashi amma tayi gardama. Ya manta INdo amma yanzu ya tuna ko wacece, ya tuna lokacin da tace ta dena zuwa makaranta kuma hakan aka yi ta dena zuwa sai da taji labarin ana bada kyauta sannan ta fara zuwa, ya tuna lokacin da tazo dan samun kyautar atamfa bata yanke farce ba ya hanata tace ta dena zuwa k’arshe ma tayi hijira daga kauyan sani zuwa kauyen saye bata dawo ba sai da marigayi yaje ya dawo da ita. Wannan suna d’aya daga cikin taurin kanta daya sani dan haka yanzu ya zai yi mata gashi zuciyar sa na buk’atar kasancewa tare da ita, shin me zai yi mata ta huce gashi tace bazata sake mai magana ba, meya kai shi haike mata bayan duk basu shirya yin hakan ba daga shi har ita.
“Ya ilahi…Ya fada cikin zuciyar sa. Har kusan k’arfe biyu na dare yana kusa da ita, haka ya gaji ya mik’e ya shiga toilet wanka yayi sannan yayi alwala yaje falo yana fita ta sakko daga kan gadon ta rufe d’akin tamkar dama jira take yi. Yana shimfida sallaya yaji ta rufe ya kalli k’ofar cike da mamaki kafin ya tayar da sallah. A ranar Sadeeq be runtsa ba ya dinga sake sake da neman hanyar dazai sassauto da zuciyar INdo, haryayi asuba a gurin sannan ya samu barawon ya sace sa bayan ya gama samun dama.
INdo kuwa tana kulle kofarta hau kan gado sai kuka take yi, tasan yayi mata ne dan mugunta amma tayi alk’awarin ba zai sake taba ta ba bare har yayi gigin yi mata wani abun
wata sabuwar tsanarsa ta kuma shiga cikin zuciyarta.
Sai da asuba sannan tayi wanka tayi sallah duk a nan cikin d’akin sannan ta koma ta hau gado dan ta san yana nan kuma idan ya ganta zai iya yi mata magana abinda ta tsana yanzu kenan ko kallon ta bata son yayi. Misalin karfe bakwai na safe ya nufi: d’akin ya bubuga mata amma tak’i bud’ewa haka ya hakura yabar gidan kasan cewar yana da lecture da k’arfe takwas. Tana jiyo shi ya fita ya rufe gate tayi saurin hantsilowa daga kan gadon taje ta garkame gidan da padlock sannan ta koma falo ta zauna sai zabga tsaki take tana harara-harare tamkar ance mata yana gurin ranar bakin ciki ya hanata yin zobo da kunun aya sai gurin kaji da taje ta kwashe kwan da suka yi.
Shi kuwa Sadeeq yana zuwa gidan Fateema yasa key ya bud’e, shiga yayi a kwance ya tarar da ita tana ta bacci ya lallaba ya kwanta a bayanta tare da shiga cikin bargonta ya rungume ta tsam ajikinsa yana cizon lip’s d’in sa tare da goga goshinsa a bayan ta. ‘
Yadda taji ya naniketa ne yasa ta riko hannunsa da ya makalota dashi ta d’ora akan kirjin ta shi kuma ya matse tajikinsa sai rawa yake yi. Gabaki d’aya ransa INdo ce daya rufe ido zai tuno abinda ya faru tsakaninsa da ita, haka ma daya bud’e idon zai dinga ganinta gashi ya tabbatar da yana da mugun tabo a gurinta. Yanzu ya zai yi wajan ganin ya wanke kansa a gurinta? sam beyi tunanin cewar hakan zata taba faruwa a tsakaninsa da ita ba sabida tsananin yadda yake ganinta tun zamanin tana INdon ta ba yanzu ba da ta koma aunty Humairah ko aunty Aisha ba. Da kyarya iya shiryawa yaje yayi lecture ya dawo, directly ya wuce gidan INdo, cikin tsananin mamaki ya tsaya yana kallon gate d’in gidan ganinsa a garkame. Mota ya koma ya wuce gidan su yana tunanin can ta tafi amma abin mamaki sai yaji su Mama suna
tamyarsa ita amma ya matse tare da cewa. “Tana nan Lafiya lau.” Ya danjima a gidan ya mik’e ya fita, Haleema ya kira a waya tana dagawa yace. “Haleema dan kira Aisha a waya naji ina ta kiran ta not reachable please yanzun nan amma.” “Toh Yaya bari naji.” Wayar INdo Haleema ta k’ira, tana d’agawa tace. “Aunty Humaira ina kika shiga ne keda wayar ki?” INdo ta yatsina fuska tamkar a gaban ta take cikin takaitawa tace. “Ina gida..”
“Okey tom shikenan.”
Haleema ta kira Sadeeq yana dagawa tace. “Yaya tana gida wai.” “Okay thanks.”
Suka kashe wayar, Sadeeq ya dinga mamaki wato ma ashe tanajin matarsa amma tak’i bud’e mai lallai yarinyar nan ta mugun raina sa gashi ya kuma siyowa kansa wani sabon rainin. Juyawa yayi ya koma gidan Fateema yak’i kuma bari ta gano yanayin sa.
Haka Sadeeq ya dinga sintiri a ranar daga gidan Fateema zuwa gidan INdo amma abin mamaki har kusan magariba bata bud’e gidan ba, sannan ya kirata a waya yafi sau ashirin amma bata d’aga ba ya san ba karamin bata mata rai yayi ba.
Harya kammala kwanaki biyun sa a gidan Fateema lNdo bata bud’e gidan ba haka kuma duk wanda yaje bata bud’ewa. Sadeeq kuma ya rasa yadda zai yi tsoransa d’aya karta mutu a gidan besan mezai ce ba. 10:35pm yana zaune a falon Fateema ya shiga cikin tunani yaji Fateema na shafar sajan sa ya kalleta yana murmushi tare da lumshe ido tamkar ya sha
kwaya don sunyi wani iri tace. “Baby ya kamata ka tashi kaje gidan Aisha dare nayi maka fa.” “Ai bata nan taje garin su.”
Ya samu kanshi da fad’ar haka yana kallonta, Fateema tana da kyau sosai domin tafi INdo haske da idanuwa ga gashi amma cikar hallitta gaba da baya INdo tafi Fateema. Ya lumshe idanuwa tare da janyo ta jikinsa yana shafar bayan ta, sai dai cikin ransa so yake yaga INdo kota halin k’a-k’ane amma ya rasa hanya. ‘
Friday morning INdo ta shirya tsab ta tattara littattafanta tasa mayafl ta Fita, bude gidan tayi sannan ta rufeshi daga waje ta tari napep ta wuce makarantar M.M HARUNA. Submitting din books na Home work din da aka basu aka yi dan malamin ya duba yana zuwa kan na lNdo yaga ba kanta hakan yasa ya kira sunanta da ya gani a jikin littafin yace idan an tashi taje ta samesa a office. Hakan kuwa aka yi ta sami M.m harunan a office d’insa ya nuna mata guri ta zauna yace. “Aisha Hamza daga wace school kika taho nan..?” INdo tace “Gaskiya malam ban gama makaranta ba, ni yanzu ne dai nake son yi sabida gaskiya kaga mijin da aka bani d’an rashin mutunci ne kuma a jami’a yake koyarwa, nidai malam dan Allah kuyi iya kokarin ku wajan ganin na iya nima shida matarsa duk malamai ne yana min gori kar nan gaba itama tazo ta fara yi min..” M.M HARUNA yace “Toh karki damu Aisha tunda dai har kinsa a cikin ranki zaki koya toh nasan ba zaki sha wahala ba, yanzu zaki fara tun daga kan alphabets kije ki kwafe su cikin note book d’inki gobe ki kawo min ki kuma dinga kokartawa wajan yin magana da turanci koda kuwa za’a yi miki dariya ne dan ni daga yauma ki dena min hausa da yawa understand.?!” “Toh malam yes.” Ta fada tana rufe fuska yayi dariya shima tare da cewa “Good.” Littafi ya dakko sabo ya rubuta mata from A-Z yace taje tayi irinsu duka. Allah sarki da yake tana so ba taji wani girman kaiba ta karba tana komawa gida a kwance ta tarar da Sadeeq har ya shigo gidan da yake babu padlock daga waje, ta wuce cikin d’akin ta yayi saurin tashi ya
bita a baya ya tsaya a wajan wardrobe ko kallansa ba tayi ba bare ta gaida shi yace.
“Aisha fitsara.., wato ni kika hana shigowa gidan k0? I think nawa ne, koda yake kin ce gidan hayane amma wayake biyan kudin gidan.?!” Ko kallansa ba tayi ba ta zare hijjab dinta ta ninke tasa a wardrobe taje zata shiga toilet Sadeeq ya fizgota nan ma tak’i yin magana ganin haka yasa shi fita yabar gidan, yana tafiya ta kuma kullewa taje tayo ta shiga kitchen ta dafa abinda zata ci ta koma falo taci ta koshi sannan ta fara assignment din ta tana gamawa tayi bacci bata sake bud’e gidan ba sai washe gari da zataje makaranta. kullum haka take yi bata bari su had’u dashi kwata kwata.
Ranar litinin Fateema ta fara zuwa gurin aiki, damuwa da shiga tashin hankali suka taru suka yiwa Sadeeq yawa ya rasa yadda zai yi da INdo, sam ta dena bari ya kwana a gidanta sabida da anyi magariba zata Garkame gidan har Fateema ta gano suna da Matsala a tsakaninsa da Aishan sai dai bata nuna mai san jin abinda ke faruwa ba kasan cewar bata son shiga cikin abinda duk be shafeta ba.
“Abba wannan karan ina son tafiya da Aisha sai dai taki yadda ma muyi maganar da ita.” “Sadeeq kenan yanzu kai da iyalinka ka kasa shawo Kansu waye toh kake son yaje ya shawo maka kanta? Duk tsaya ai kaine kafi mu kusanci da ita ya kamata kasan yadda zaka yi ta yadda har Ku tafi tare.” Shiru Sadeeq yayi ya rasa ya zai yi gashi ranar Thursday yake son komawa, ga Fateema tunda ta fara zuwa makarantar nan yasan itama ba yadda zata yi ta bishi ba kasan cewar ya mata alk’awarin idan har takardar aikinta yafito toh zai barta tayi, gashi bazai iya tafiya shi kad’ai ba tunda ya riga ya saba kasancewa da mace. “Sadeeq ya kayi shiru? Idan ita Aishan taki binka ba saika tafi da wadda kuka saba tafiya tare ba.” “Abba ai Fateema ta fara aiki dan tun yanzu ma ta fara nuna k’in bina wallahi.” “Toh ya zaka yi da rashin iya yaren su da ita Aishan bata iya ba? Kar taje tana baka matsala
fah tun da a baya haka kace.”
Kan Sadeeq a k’asa yana goga yatsansa a k’asan carpet d’in d’akin, shi kansa yasan ba zai iya tafiya kwara state ba sai da matarsa a kusa dashi gashi abban da zai temaka mai shima yace yaje su sasanta da d’aya a cikin su.
“Shikenan Abba zanje na kuma tambayar su, sai da safe Allah ya k’ara girma.” Abba ya kallesa tare da cewa “Amin Sadeeq a gaida min dasu baki d’aya. Fita yayi ya wuce gidan Fateema ranar ma anan ya kwana. Washe gari ta kasance Wednesday bayan Fateema ta tafi: gurin aiki misalin karfe goma Sadeeq ya shirya cikin wani rantsatsan yadi mai matuk’ar taushi sky blue ya dora hula yasa turare sannan ya fita. Gidan lNdo ya wuce yayi niyar yau kota halin k’akane sai ya shiga gidan ya kuma nuna mata kuskuranta na rainin da tayi masa.
Cikin sa’a ma yana zuwa ya tarar da gidan a bude nan da nan zuciyarsa ta sanyaya, a kofar gidan yayi parking sannan ya shiga gida bakinsa d’auke da sallama. Takalma ya gani a k’ofar dakin hakan ya tabbatar masa da cewar bak’i tayi, ya shiga ciki da mamaki sai yaga
su Nafeesa, Sagiru da Shehu sai wani wanda besan ko waye ba amma da alama tare suke. “Yaya Sadeeq ina kwana?!”
Yaji Nafeesa ta fada bayan ta durkusa kasa, murmushi yayi tare da karasawa ciki yana amsa mata su kuma Su Sagiru ya basu hannu suka yi musabuha. Yasu Inna da malam Lafiya dai k0?”
“Lfya lau, sunce suna gaida kai.””Ina amsawa yaushe zaku koma..?!” Sagiru yana shafa keya kasan cewar yanzu duk sun girma yace. “Nan da anjima zamu wuce.” “Okey tom Allah ya kaimu.”
Yana fad’a ya wuce d’akin INdo a tunaninsa zata biyo shi irin abin nan na tsakanin mata da miji da idan ya dawo zata bishi taji abinda yake da bukata ko kuma a sake yin wata special Oyo yon amma yaji shiru sai ma dariyar ta da yake jiyowa ya dafe goshi tare da rintsa idanuwa daga bisani ya mik’e yabar gidan. Tunda ya fita be sake dawowa ba sai da akayi magriba sannan ya shiga gidan lokacin bata rufe gidan ba suna zaune da ‘yar makotansu Mansura suna kallo suna hira. Ganin ya dawo ne yasa Mansura tayiwa INdo sallama ta tafi shi kuma ya zauna a falo yana kallonta. Sanye take cikin atamfa me ratsin green, white, brown, da purple d’inkin riga da zani sun cika ta sunyi mata d’as tayi kyau sosai ya kalleta amma ita hankalinta na kan TV, sadeeq ya dauki remote ya kashe TV d’in tare da kallonta sai yaga tana kokarin mikewa ta shiga d’aki yayi saurin rik’ota ta fara fisgefizge zata kwace yajingina ta jikin bango bayan ya rike mata hannuwa.
Murya tamkar ta marayan daya kwana biyu be samu abin kaiwa baki ba Sadeeq yace.
“Aisha what’s wrong with you ne ah? Dani zaki yi gaba? Kin manta matsayi na a wajanki ne? Ko baki san wannan abin da kikeyi min ba kina cikin fushin ubangiji ba? Please Aisha ki bari mu fahimci juna I beg of you please…”
Still shiru tayi Sadeeq yakai fuskarsa saitin kirjinta yana goga fuskarsa yaji tayi magana. ‘ “Wai malam Sadeeq ya haka ne?!” “Aure ne haka if you don’t know.”
INdo ta dinga mai-maita if you don’t know cikin zuciyar amma ta kasa gane me if d’in take nufi dan tasan don’t know da you dan haka tayi tunanin ko wata maganarya gasa mata dan haka ranta ya kuma baci ta zabga mai harara yakai bakinsa ta kauda kai amma duk da haka sai daya laso idon rashin kunyar da harshensa yace. “Aisha you don’t know me shi yasa kike min duk abinda kikaga dama k0,?!” lNdo ta tabe baki tare da yatsina fuska ta daddage tace. “Tab I know you’re noun, ko banda malam sadeeq kana da wani sunan..?!” “I know you’re noun.” Ya maimaita a fili yana kallon gefen fuskarta still yana rik’e da ita a
jikin bango ya rasa gane me take nufi hakan yasa shi lek’a fuskarta yace. “Mene kuma noun a cikin maganar da kika min Aisha?” Ta murgud’a baki tare da cewa. “Sakar min hannu malam Sadeeq, kace ban sanka shine na nuna maka nikuwa na sanka, noun is a name of person, animal, place or tins (things) ko ka dauka yanzu ma banajin abinda kake fadane? Never past tense kenan wallahi (Da kenan).”
Sadeeq ya cuno baki, so yake yayi dariya amma baya son yayi taji haushi dan so yake ya lallaba yayi mata wayo ya samu ta bishi dan haka ya dinga gumtse dariyarsa ita kuma tana kokarin kwatarjikinta yace. “Very Good Aisha you’re trying, but kin san menene? Ki shirya kayanki gobe mu tafi kwara state a can wallahi zaki iya komai domin su basa Hausa sosai kafin kiga bahaushe sai kin
dade, muje ki shirya kayan ki sai na taya kima.” Ya fada tare dajanyo tajikinsa ya rungume ta. Cikin sauri lNdo ta fisge tare da cewa….