MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER34
—Tana fita napep ta tare ya kaita gidan su. Tana shiga ta fashe da kuka tare da fad’awa kan kujerar daya daga cikin falon.
“Ke lafiya kuwa kamar wadda aka yiwa mutuwa?”
Cewar yayan ta Shamsu yana kallonta, Fateema bata yi shiru ba tana ta kuka Shamsu ya tashi ya dinga mata fada yace idan baza tayi magana ba ta tashi ta koma inda ta fito. Mama ma kallonta take yi tanajiran jin abinda zata fad’a ranta cike da addu’ar Allah yasa ba tsakaninta bane da mijin.
“Ke wallahi karki bari na tashi tsaye dan sai na fasa miki baki, aikin banza kawai kiyi magana shine zaki tsaya yiwa mutane kuka.”
“Mama Sadeeq ya munafurce ni, Mama be taba gaya min matarsa Aisha nada ciki ba sai yau da muka gani gashi har ya fito. Wallahi bazan koma gidan saba yaje can su karata munafiki kawai, dama ance duk wacce ta dauki namiji uba toh lallai zata mutu ma…”
Mtwww “Shut-up Fateema, bakida hankali ne? Toh sakinki kike so yayi?!” “Nidai kam bazan koma ba yaje can su karata.”
“Toh idan ya sakeki sai kizo na aureki nine kawai idan na aureki za‘a haramta min kara aure bare har matar ta rigaki haihuwa.”
“Yaya Shamsu ka aureni kuma?!”
“Eh toh kince maza ba ‘yan goyo bane, kinga ni uwa d’aya uba d’aya muke ki goyani na goyaki babu mejin haushin wani, amma ko barin Sadeeq kikayi toh wani mijin zaki aura kuma shima wata ran zai miki wani abun sannan ba lallai ki kuma samun saurayi ba sai da kema ki shiga gidan wata.”
“Umma….”
“Karki min magana Fateema, dai-dai gwargwado kina da ilimin addini shin na zamani ne ya rinjayi na addininki ko kuwa wani saban iskancinne haka? Karki manta wannan auran nasu had’in Allah ne duk wanda yace zaija da ikonsa akan lamarin toh bazai kwana cikinjin dadi ba. Fateema karki manta nima da yanzu bani bace mahaifiyarku, amma kinga da yake Allah yayi ta hanyata zai samu haihuwa sai ya dauke matarsa ta farko da kyar mahaifinku
ya yadda ya aureni da yace ya gama aure amma a satin da na tare a satin na samu cikin
yayan ku ki gaya min da mahaifinku yayi butulci ya kafe akan bazai sake aure ba ta wace
hanya zai sameku tunda Allah yayi yana da rabonku a duniya?!” ‘
Fateema ta kuma fashewa da kuka tare da mikewa zaune tace.
“Toh Umma kiyi hakuri wallahi sharrin shaid’anne, amma kuma me yasa koda wasa be gaya min ba yayi min shiru sai yau naji na kuma gani?!”
“Hmm Fateema kenan, toh ko tunda kuka yi auran Sadeeq be taba kusantarki bane har sai da aka yi musu aure da ita Aishan?!”
“Kai Umma..”
Fateema ta fada da alama nauyi tambayar tayi mata, kallon Yaya Shamsu tayi k’asa-k’asa kawai suka hada idanuwa ya zabga mata harara tare da cewa.
“Ke..! Kallon me kike yi min haka? Ko kin d’auka bansan meye auran ba saike kika sani.??”
Da sauri ta zaro idanuwa hannunta a baki tana girgizawa tare da kallon Umma Fateema taga Umman ma ita take kallo, lallai Yaya bashi da kunya ma wallahi a gaban Ummansu. Koda yake itace ta kallesa dole yayi mata bayani.
“Fateema karki yadda ki nunawa mijinki bakin cikinki akan cikin matarsa, ina son ki nuna masa kinfishi son cikin ma. Sannan karki bari abban ku ya dawo ya ganki a cikin gidan nan
wallahi kinsan ranki ne zai baci abanza, gara kije kiyi zaman aurenki har Allah ya baki kema wata rana idan kina da rabo.”
“Toh Umma, amma dan Allah ki tayani da addu’a dan wallahi ina jin zuciyata nayin zafi da nauyi.”
“Kidena sawa a ranki insha Allahu zakiji bakya ji shaidan ne kawai yake son shiga cikin lamarinki, ki yawaita azkar zakiji dadin ranki.”
Wayarta ce dake cikin jaka taji tana ta ringing amma taki dagawa dan tasan baxai wuce Sadeeq ba ita kuma bata shirya abinda zata ce masa ba. Tashi tayi suka yi sallama Yaya Shamsu yace bari ya kaita gidan da kansa, suna taflya yana kara bata shawarwari wani maganar ma har mamakinsa takeyi lallai yayan nata aure kawai yake jira amma babu abinda be sani ba
Shi kuwa Sadeeq karfe tara yaje daukar su amma akace Fateema bata nan, duk an duba bata gidan ya kira ta yafl sau goma amma ba’a d’agawa hakan yasa yace INdo ta fito su tafi Gidan Fateeman suka fara biyawa amma akulle hakan yasa Sadeeq tafiya yakai INdo gida tunda ranar a gidan Fateema yake.
“Malam Sadeeq dan tsaya a can gurin me balangun can na kan kwana ka siya min.”
Kallonta yayi sai yaga ita kalle-kalle takeyi abinta cikin mamakin daya makale mai a wuya yace.
“Cutie ballangu kuma.” “Eh dan Allah kace su sa yaji daban.“ “lkon Allah shi kike son ci kenan.”
“Eh, akwai fura da nono da ake damawa a gurin, ana sa kwakwa da ayaba da madara please dan Allah itama ka siyo min.”
Dai-dai lokacin suka tsaya a gurin ya kalleta tare da cewa. “Toh ke ya akayi kika san nan gurin harda abubuwan da ake siyarwa.?!” Juyawa tayi ta kallesa suka kalli junansu tayi murmushi tare da cewa.
“Bafa zuwa nake yi ba dakai na, a’a ina dai bawa khaleefa yana siyo min nima rannan ne Abba ya aiko min dashi. Naci naji dad’i shine nake bayarwa yana siyo min.”
“Okey yanzu naji batu na d’auka kinyi tunanin nan ma kauyan Sani ne, kowa zai iya fita san
ransa.” Baki ta turo tana yatsina fuska ya fita, leda biyu yayo musu sannan ya dawo motar yana kallonta yaga still a shagwabe fuskarta take ya shareta domin so yake su karasa gida zaifl jin dadin lallashinta.
A bakin gate ya tsaya ta fitO suka shiga gidan, tun a parking space ya rikota tana turesa yayi niyar daukarta sai dai yana ganin bazai iya ba sabida cikinta gashi ba laifi INdo kamar .
“Goya ni toh.“ Sadeeq ya zaro idanuwa jin abinda ta fada, yana kamo hannunta suna tafiya yace.
“Ina tunanin yadda zan iya daukarki ke kina cewa na goyaki kin manta abinda yake cikin ki k0.” “Toh gaskiya tunda kayi niyya malam Sadeeq to ka goya ni.” “A’ah cutie ni ba niyya nayi ba, cewa nayi Ina tunanin yadda zan daukeki kekuma ma goyo zaki ce.”
A bakin kofar dakin ta tsaya ya ajiye leda daya kusa da kofar yaje ya tayar da gen ya dauka ta shiga ciki amma sai ya ganta tayi kalar tausayi ta kuma turo baki yayi dariya.
“Mata problem. Nan kiyi can tayi Allah yasa in iya muku.”
‘Daukarta yayi suka shiga ya dinga kakaro nishi tana dariya, yana ajiyeta ya zauna ya
daura kansa akan cinyarta. ’
“Masha Allah sati dayan da nayi a garin nan yasa kin kuma yin kiba, nan gaba sai kin kasa tashi cutie Aisha.” “Ni kadena cemin nayi kiba.” “Na dena ina balangun naki?ko bazan ci ba?!”
lNdo tace. “Kaje kuci kaida Fateema nima kaga mu biyu zamu ci wannan.” “Naki wayon wannan zanci.”
Tashi yayi yaje ya shigo da ledar ya kuma zuwa ya dakko plate tare ya ajiye, anan falon ta rage kayan jikinta ta zauna daga under wear sai have vest kasan cewar yanzu bata sanya bra tana dan takura mata ciwon kirji.
Kallonta yake tamkar zai shige cikin jikinta farat d’aya, remote ta dauka tare da kunna TV ta juyo zata ci naman taga sai kallonta yake cikin mamaki tace.
“Wai ya haka ne?!” Sadeeq ya shafa keya tare da komawa kusa da ita ya zauna ya sanya hannu ya rikota tare da kwanciya a bayanta murya sassanya yace.
“Aisha banyi tunanin zaki dawo haka ba, lokacin da kuna j.s one ko kirg…“ Bata bari ya karasa ba tayi saurin rufe mai baki da hannunta. Dariya ya dinga yi ta dauki naman tafara ci sannan ta sakar mai baki yace. “Zanci.”
‘Daukowa tayi ya rike mata hannu, fuskarta ya kama sannan ya sanya bakinsa a hankali cikin nata sai faman zaro ido takeyi. Gani tayi ya ciro na cikin bakin nata yana karasa taunawa ta bishi da kallon mamaki, yanzu kam ta tabbatar da cewa Sadeeq yana sonta, a shirye yake tsab da ya shiga cikin rayuwarta yayi mata duk abinda take so. Jiyayi kawai ta rungumesa tsam a jikinta a hankali kuma yaji tana zubar da hawaye ya dagota yace.
“Sorry na bata miki rai ko? Bazan sake ba, bana son ganin hawayenki musamman ace nine silar zubar su.”
Sabo ta dakko tasa mai a bakin yayi murmushi ya fara taunawa idanunsa akanta, tana ganin ya fara taunawa itama ta rintse ido tare da kai nata bakin cikin nasa kamar yadda taga yayi mata ya tura mata shi a bakinta da kanshi sabanin shi da ya ciro nata da harshensa. “Ashe ba haushi kikaji ba dazu ba?!”
Ya fada yana lasar lips d’inshi. Juyawa tayi tana murmushi ta fara dangwala yaji tana sawa a baki. Mik’ewa yayi yana gyaran rigarsa yace.
“Na tafi na tabbata duk inda taje yanzu ta dawo, idan na isa zan kiraki.” “Toh a gaida ita.” “Ba rakiya?”
Dariya tayi ta mike suka fita tare, kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi dole ya fita ita kuma ta rufe gidan ta koma ciki zuciyarta fal Sadeeq domin ya tafine ya barta da abinda bazata taba manta shi ba koda da second daya ne.
A falo ya zauna tare da daukar laptop dinsa daya bari jikin charge. Fateema na jinsa ta dan Leko har lokacin tunanin abinda zata cemai takeyi, ganin tana karasa bata lokaci yasa tayi shahada kawai ta shiga falon tana sanye cikin kayan bacci me wando karami wanda ko cinyarta be gama rufewa ba.
Kusa da kafarsa taje ta zauna, shafar kafar ta farayi wanda take cike da kwantaccen bak’in gashi. Sake makalo kafar tayi sannan ta sakar mai kuka a hankali hawayen na sauka a kafarsa, har cikin zuciyarsa yakejin kukan amma ya shareta yana aikinsa, ganin haka yasa ta fara magana.
“Baby kayi hakuri dan Allah, wallahi raina ne ya baci akan abinda ka Goye min kaida Aisha. Jin abinda ta fada ne yasa shi cewa, “Me kuma muka yi? Duk abinda muka yi Fateema ya dace idan har na kiraki ki amsa min amma kikaki toh ina kikaje ma tukunna..?”
“Kayi hakuri baby, yanzu duk matsayin da nake a gurinka na matarka ace ka kasa gaya min cewar Aisha ciki gareta? Ko kana ganin kamar zan cutarda itane? Wallahi kaji dalilin da yasa kawai dana gani yau kawai sai na tafi gida, can kuma ina zuwa Yaya Shamsu ya dinga min fad’a, baby kayi hakuri da bata maka rai danayi dan Allah.”
Zuciyarsa ce tayi sanyi jin itace ma take basa hakuri, ture laptop d’in yayi tare da janyo ta jikin sa. Gashin kanta da bata mai kitso ya dinga shafawa sannan ya numfasa yace.
“Kamata yayi tunda nine na kaiku duk abinda zai faru ki tsaya nazo na dauke ku, amma ba komai nasan sharrin iblis ne. Sannan kuma ke ya kamata nayiwa wannan korafin cewar baki sanar min da cewar Aisha nada ciki ba sabida ku na bari tare har tsawon 3months amma baki gayan ba sai dana dawo na gani why baby?!”
Fateema ta dago tare da kwantar da kai cikin maganar tace.
“Wallahi ban taba lura ba kuma dai gaskiya bana wannan tunanin ganin nima haryanzu babu. Sai dazu da naji Hawwa na fad’a kuma na gani a zahiri.” Sadeeq ya sake kamota tare da cewa.
“Kinga kenan duk babu me laifi, Fateema bana son ki tashi hankalinki domin ina sonki a
duk yadda kike. Kema Allah ba mantawa yayi dake ba domin da yawan aikin ne toh da yaci
ace kema yanzu kin kusa ma saukewa amma fa Allah me meyi, yanzu three months da
taflya ta ita kuma cikinta wata hudu kinga kenan bayin kaina bane. Ina son dan Allah karki tayar da hankalinki rashin haihuwarki bazai rage soyayyarki ba a cikin Zuciya ta ‘I love you’ Fateema Allah shine shedata.”
” ‘I love you ” baby nima ka taya ni da addu’a na samu kafin na mutu.”
Shhhiiii yayi mata bayan ya dora yatsansa akan lips dinta. Shiru tayi sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita taje ta dakko cup’s ta zuba musu furar suna manne da juna suna cin abin su idansa akan agoga yana son ya kira INdo kamaryadda yayi mata alk’awari.
Daya rasa yadda zai yi kawai sai ya tura mata text message.
“Affuwan cutie na ba credit da yawa a ciki gashi masu shops sun rufe, zamu hadu gobel love nd miss you (DeepKiss).”
Yana ganin sakon ya tafi ya gogesa tas daga cikin wayar
INdo na kwance ta gama duba littafin ta taji shigowar sako, a hankali d’aya bayan d’aya (word by word) ta karance sakon kafin ta tattarashi ciki kwakwalwarta ta sake nanata sakon gaba d’ayan sa sannan tayi murmushi ta kashe wayar ta kwanta, wani sabon yanayi na soyayyarsa yana shigarta haka ta dinga murmushi ita kad’ai a kan gado har bacci ya d’auketa. Yayin da shi kuma yake can suna soyewa da Fateema wadda itama fatanta da burinta da
Hmm