MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 8
INdo kuwa tunda ta koma gida take wanke hakorinta ko abinci k’in ci tayi sabida kar yayi daud’a malam Sadeeq ya hana‘Ta kyauta. kwanciya tayi male-male a tsakar gida kan tabarma tamkar me yin azumi, takaici da haushi suka cika inna ta kalleta tana daga tsaye Innan tace.
“Ke! ‘Yar nan ki rufawa kanki asiri kizo kici abinci kin gamin sakarya, banda malamin naku mugune taya zai hanaku cin abinci sabida wai an goge baki, toh bari ki kashe kanki ai kinyi wa kanki…” INdo tayi shiru tana ci gaba da rik’e ciki tana birgima, baban su ne ya shigo ganin yadda
INdo keyi ne yasa shi tambayar inna nan ta sanar mishi aikuwa ya fara fad’a tare da cewa ta tashi taci abincinta amma ko motsi INdo tayi shiru sai hawaye da take fItarwa a hankali. Juyawa baban nasu yayi direct ya wuce gidan da Sadeeq yake ciki, kwankwasawa yayi yazo ya bud’e sam be san shiba dan haka ya fara mai kallon rashin fahimta baban INdo yace. ‘ “Sunana malam Hamza uban INdo d’alibarku ta makarantartsefawa, ga ‘yata can zata mutu tak’ici tak’i sha sabilida kunsa musu dokar yin buruhi. Toh bazai yiwuba, tun wuri kaje kasa taci abinci dan idan ta mutu akan wata kyautar ku ba yafewa zanyi ba
kur’anikuwa..” “Subahanallahi malam ai ni ba haka nake nufi ba itada ma ba…” Sadeeq be k’arasa magana ba malam Hamza ya cafe zancen ta hanyar d’aga masa hannu yace. “Karkayi min wani batukaji k0, tanacan tana malan geruwa dagani har uwarta munyi munyi taci abunci tak’iya wai kar bakinta yayi daud’a. lta Uwata ai batada jimirin yinwa ko azumi goma bata iyawa dan haka kokaje kasa taci abinci konaje har gidan protocol (principal) d’in nayi mai bayani zaka kashe mana ‘ya’ya.” Tsaki Sadeeq yaja a k’asan zuciyarsa sannan ya rufe gidan ya kalli baban INdo yace “Muje toh amma ni ba haka nake nufin suyi ba.” Kwance suka tarar da ita tayi shame-shame tamkar wadda zata mutu gaban malam Sadeeq ya buga mamaki da tsoro suka dirar mai cikin sanyin jiki ya kalli INdo bakin sa yayi mai nauyi ya daure dai yayi mata magana cikin dakiya. “Aisha tashi zaune please.”
Da kyar INdo ta samu ta iya d’ago kwayar idonta tana kallon malam sadeeq d’in yayi mata alama daka nan ta mik’e zaune da kyarjikinta duk yayi fututu da k’asargurin data kwanta rigarjikinta daga wajan hammatarta ya yage sikert d’in ma duk yasha faci tana son mik‘ewa amma ta kasa, hankalinsa ya kuma tashi lokacin wayarsa na ta faman ringing amma ya kasa d’agawa bare yasan ko waye. Daurewa yayi ya kuma matsawa kusa da ita yana kallonta yace. Aisha tashi kici abinci ai ni ba haka nake nufl ba, kinga idan kin gama cin abincin ma zaki iya yin brush d’in amma ba’a zama da yinwa idan ba haka ba mutuwa ake yi tashi kinji.” Kasa mik’ewa tayi saida baban ta yace da innar ta mik’ar da ita sannan aka zaunar da ita ta jingina da jikin bango jikin duk babu kwari tayi zuru-zuru da ita kai daka ganta kasan tana cikin wani hali. Kallon Inna malam Sadeeq yayi gabaki d’aya tausaya musu yake sabida ganin halin da suke ciki na rashi, ya karyarda baki yace. “Mama a kawo mata abincin taci.” Sai Inna taji wani banbarakwai daya kirata da Mama yayin da INdo take numfashi da kyar dan da kyartake iya bud’e ido. Inna ta kawo dambun masara ta turawa lNdo gabanta Sadeeq ya kalli kwanon sam babu alamar akwai mai a ciki ya kuma kallon INdo wadda ta luma daddaud’an hannunta wanda duk k’asa ta batashi yaga ta fara watsa danbun cikin bakinta, mamaki yasa shi yin shiru ba tare da yayi magana ba harta cinyee besani ba yana tsugunne yana tunani. Sai da ta gama cinyewa sannan Malam Sadeeq ya mik’e, ya yiwa Inna sallama sannan ya flta. A k’ofar gida ya tarar da baban lNdo nan ya kuma bashi hak‘uri da kuma k’ara yi mai bayanin abinda yake nufi akan su, mahaifln INdo naji ya dinga boye hakoransa wad’anda sukejawur sabida tsabar cin goro da rashin kula dasu. Yana shiga gida ya zaro wayarsa missed call ya tarar na Abubakar, sai da ya zauna a bakin katifarsa sannan ya kira layin har sai da ta kusan yankewa sannan yaji an d’aga. “Sadeeq ina ka shiga ne inata kira baka d’aga ba..?!”CewarAbubakar cikin sanyin muryarsa da jan aji, Sadeeq ya shafa kai yana kuma sauke ajiyar zuciya yace.
“Twinnie inajin sai na d’auki shawararka, wannan kauyan yafi karfina wallahi haukan su yayi yawa sosai.” Yayi shiru yana sauke numfashin takaici kafin Abubakar d’in yace. “Da kyau gara tun yanzu ka fara gane cewar kafi karfin secondary teaching ka dawo nan gara ko FCE kano ne kaje kayi lecturing.” Shiru suka yi na d’an lokaci kafin Sadeeq yace. “Toh zan kuma yin shawara amma nima abun kauyan nan ya fara isata, abun nasu yayi yawa ga gidadanci.”
“Twinnie kullum haka kake cewa yanzu kawai aiwatarwa zaka yi mudai muna nan muna yi maka fatan alkairi.” “0k insha Allahu sai munyi waya anjima a gaida min da qibdiyyah.” “Zataji dakyau gata nan ma muna tare.” Beyadda sun gaisa da itaba ya kashe wayar dan yaji ta flye shiru da yawa kuma shima ba surutu garesa ba.
Tun ranar laraba Rukayya ta wanke mata kai bayan tasa mata flya-f’lya kwarkwatar sun mutu sannan tayi mata zanan Hausa shuku, kai idan kaga kan bazakayi tunani na jiya bane sabida ya kitsu sai daijan gashi gareta ba bak’i ba. Uniform d’inta kuma ranar alhamis tasa zare da allura ta d’inke gabaki d’aya inda ya yage ta kuma wanke su duk da sun riga sun kod’e kuma bata da wasu ba kud’in yin sabo ta goge fason k’afarta k’afar tayi kyau duk kuwa da be fitaba gaba d’aya. ‘ Gidan innatuwa me kunshi taje tasiyo lallen goma da talatin din da rukayya tabata,da kanta rukayyan ta yarfa matajan lallen ta rufe mata fason kafarnan,a ranarda yamma indo tatafl kasuwar dakali wajen idi shoe shiner hannuwanta rike da wasu jemammun takalma kambos duksun fatattake, “Idi xaka iya gyara wannan takalman” “Mugansu”cewar idi “Gasu kambas(kambos) ne idi kaga insipehen(inspection)malamin mu xeyi ranar juma’ar nan kuma bakaga kyautar dayake ba nikuma so make naci shadda ma yasin” “Bari na gwada nagani xasu gyaru mana sede xaki biya kudi dayawa” “Kai idi nawa?!” “Nera hansin”
Rantsuwa lndo ta dinga kwasowa tana kalallame idi da kalamai tana faman xabga masa roko ta karkare da, “Dan manzon salati idi kayi hak‘uri ka temakamin nice fa indo..lndo Malam hamza ta makarantar tsefawa nan nan kusa dakai‘” Cikeda isar nacin da take masa idi ya wafci takalman yashiga gyara su,yadau lokaci yana dinkecan nane can da gum sannan yai polish d’insa se kyalli yake Kai kace bashi bane sannan ya mikawa lndo ,cikin murna ta karba harda lashe kasan takalmin “da kwarankwatsa ya flta kuma,lalle aiki seme hi,Sannu idi yasin kaci abaka hinkafa da miyarja me nama” “Allah ko Indo?”
“Yasin idi” Cikin sake gyara kananun kayan da sukai yawa ajikinsa Wai shi gaye yace, “Toh lndo nikuwa ina lami?(kawar lndo)”
“Oh lami tana nan,oho de bansan mata bama kasan makarantar gangare take tunda mijin kanwar babarsu ixama chayamen(chairman)” Kada Kai idi yai yana murmushi,cikin tsokana lndo tace,
“Wai haryanxu kana ciki ne?!” “Eh mana Inason lami wallahi kawaide bata sona ne tafison shehulle” Cikin karkad’a kugu had’e da rausaya idanuwa lNdo tace, “To ai kaine idi,dole lami taflson shehulle kullum fa tanada daurin tsire da leman roba na yangayu Kai kywa se mammakon bala,i “Ba haka bane lndo amma xan gyara..”
Da haka sukai sallama da ita tana tafe tana jujjuya takalmanta ranar kuwa barkakkiyar safar da tayi shekaru batako kallansu hasalima kama tukunya ake dasu ta dinga durxa tana wankesu ruwa uku tai musu ,Kai kowa mamakin lndo yake har inna tafara sanyata a sujjada idan tai sallah don gani take aljanun tsafta ne suka shafeta kwanan nan..
Rana bata Karya sedai uward’iya taji kunya yau take juma’a tashin lndo uku kafin asubah inna tana korata waita xata safiya tai,asubar fari kuwa ta mike tai bandaki ranar de atakaice baccin kirki lndo batai ba. Sega lndo tai wanka abinda yabawa kowa mamaki agidan nasu sede basu da man shafawa sai dai manshanu ko na girki shi kuma bashi garesu ba dan haka tana saka kayan makaranta ta fita zuwa gidan Rukayya lokacin mijinta na nan INdo ta kwankwasa musu k’ofar d’aki tare DA cewa, “Rukayya kina ciki kuwa? Zuwa nayi ki aramin kayan kwalliyarki inyi zani makaranta..”ne ta k’arasa fad’a tana me shiga cikin d‘akin sukayi kicib’is da ita, “Au ashe kinji ni.” “Eh INdo bari na d’akko miki su nan tsakar gida.” ‘ Cikin d’akin ta koma ta d’ebu mata su lokacin mijin ta shima yazo zai fita INdo ta ganshi ta dashare baki tace “Au kaima d’anlami ashe kana ciki yanzu ka tashi a bacci ne?” Ya tsaya kusa da ita yana kallonta yace “Eh lNdo yau kuma za‘a makarantar kenan.”
Tace “Eh gahima kuwa.” Rukayya ce ta fito ta mik’awa INdo kayan kwalliyar shi kuma d’anlami yasa kai ya fita. Tana zaune tana yi Rukayya na kwarzanta ta wai tayi kyau ai yau sai dai in bak’in ciki ne zai hana malam sadeeq ya bata kyauta. Zuciyar INdo ta kuma shiga cikin wani irin yanayi najin dad’i, ita dakanta tanajin sauyi a Cikin jikinta sabida iskar da take shigarta ta k’ofofln gashin jikinta. Da sauri ta kammala kwalliyar Tashi Rukayya tayi bayan ta kwashi kayan kwalliyar ta shiga cikin d’aki ta mayar dasu ta mik’awa INdo turare sai faman dariya take sabida yadda take jin ta wani daban yau. Tafeshe rigarta Rukayya tayi saurin cewa. “Haba lNdo ya kike kuma bata kayan makaranta salan yaga jirwaye ya hanaki…?Ajikin hammatarki zaki fesa.!” lNdo tayi yadda ta gaya mata sannan tace.
“Sai nazo kawo miki kayan da zan samo Rukayya…” Tayi dariya itama cikin jin dad’i da fatan alheri tace “Toh lNdo Allah ya baki sa’a sai kun dawo.“ Gida ta shiga yau ko karin kumallo bata tsaya yi ba sabida kar bakin yayi daud‘a tayiwa Inna sallama tabar gidan yau harda littattafanta da suka yayyage tazuba a leda ta tafl burinta yau ta samu atamfa k0 ya bata wani abun da zata dinga alfaharl’ dashi, yau sai da ta riga kowa a makarantar zuwa principal ne kawai da masu kula da makarantar bata riga ba taje ta zauna kusa da farkon aji da niyar ko masu gurin sunje bazata tashl’ ba tafi son a fara ta kanta yau. Lokacin 8:15am yana gafda shiga ajin aka yo mai waya hakan yasa shi tsayawa dan ya amsa. Dubawa yayi sai yaga ansa my twinnie yayi murmushi sannan ya d’anyi baya da ajin sabida hayaniyar da suke yi ya d’aga tare da karawa a kunnansa. ‘
“Twinnie how far..?l”Sadeeq ya fad’a yana d’an sosa k’eyarsa da k’asan biro, daga can bangaran Abubakar yace. “Surprise..!”
Sadeeq najin haka yayi murmushi tare da cewa. “Kana gate ko..?!” Abubakar yayi dariya yace “yah kana ina yanzu.?”Sadeeq ya kalli ajin sannan yace “twinnie kashigo ciki ina aji uku jss 3c nima yanzu zan k’arasa shiga ciki.””Okay…” Suka kashe wayar Sadeeq ya shiga hannunsa d’auke da ledar viva yana shiga ‘yan aji suka tashi ana gaida shi da k’arfin tsiya dan yanzu ba k‘aramin so suke mishi ba, ya ajiye akan teburin sa ba tare daya kallesu ba yace su zauna nan ma suka ce “thank you Sir…” Shima da k’arf’ln su kamarkuma had’in baki. Waje ya lek’a ya gani ko ya k’araso yana hangosa ya d’aga mai hannu suka yiwajuna murmushi tundaga nesa har Abubakar ya k’araso suka yi musabuha sannan suka shiga cikin ajin, nan ma yaran suka sake tashi suka gaida d’ayan daya shigo amma kotakan su bebiba ya tsaya suna magana sai Sadeeq d’inne yayi musu alamar su zauna da hannu tunda shi ba yadda zaiyi d’alibansa ne dole ya kulasu. “Twinnie ga abin zama ka zauna.” Abubakar ya kalli kujerar sannan ya juya yana kallon ‘yan ajin sai ya gansu fes-fes dasu hakan ya bashi mamaki ya kuma rasa wadda zai kira ta goge mai kujerar dan bazai zauna a haka ba. Shi duk a tunaninsa ba wad’anda ya sani bane ya kalli Sadeeq yana shafa sajen fuskarsa yace. “Twinnie congrats an sake ma class.”
Sadeeq yayi murmushi tare dajuyawa ya kalli ‘yan ajin sannan ya kalli Abubakar yace, “twinnie sune dai wad’anda ka sani kawai canjin yanayi aka samu.” Woww good of you.” “Thanks twinnie.”
Abubakar ya kalli ‘yan matan ajin kawai ya nunu Maryam Ali ya yafitota,jikinta na rawa ta mik’e ta k’arasa inda yake tace. ’
“Malam gani.” Mtwww “wai ban hanaku ce min malam bane? Ko kunga nayi kama da teacher?” “Allah baka hakuri.” Maryam ta fad’a bakinta na rawa,yayi banza da ita sannan yace “daga yau kar wanda ya kuma ce min malam ko sir suna na doctor Abubakar Salman Harun, karna kuma zuwa ajin nan wata tace min malam ko wani sir ku kirani da doctor Abbakar or doctor ASH.” Ajin yayi tsit babu meyin motsi yaja tsaki tare da kallonta yace “Oya tashi ki goge min kujerar da zan zauna.”
Da sauri Maryam ta zaro idojin abinda yace sabida ta tuno sanda yasa lNdo ta gage mai da hijjab d’inta, ya zata yi gashi ba’a duba taba yau ta shiga uku zai ja mata. “Ko baza kiyi bane.?!” Ya tambayeta ganin bataje tayi abinda ya sanyata ba, hawaye suka zubo mata shi kuma Sadeeq yak’i yin magana jiki a sanyaye tana kuka taje tasa hijabinta ta goge mai tasss sannan ta koma gurin zamanta sai kuka takeyi shi kuma yaje ya zauna tare da d‘ora k’afa d’aya kan d’aya yana d’an kad’asu. Sadeeq ya kalli Abubakar yace. “Bari sai na fara yi musu inspection.” Abubakarya kallesa yace “na ina kuma..?!” Sadeeq ya d’auki rular yana cewa “na jikinsu har kyauta nake basu that’s why kazo ka gansu neat.” Abubakar ya tabe baki sannan Sadeeq ya tafi farawa wanda har lokacin bemasan lNdo na ajin ba, Abubakar yace “okey twinnie duk wani wanda beyi maka wani abunba ka turosa nan gurin.” Ya fad‘a yana d’aukar wayarsa dan kiran Qibd’iyya yace mata ya sauka lafiya kuma yaji sassanyar muryarta mai sanyi. ‘Yan aji najin abinda ya fad’a kowa ya fara duba abinda beyi ba dai-dai lokacin da Sadeeq ya k’arasa gurin bencin da yake farawa kuma INdo ce a farko dan haka kafin ta gama duba abinda bata yiba har ya k’arasa. “Ohh my God..! Wacece wannan kamar Aisha?” INdo ta dashare baki kamar gonar auduga yayin da ‘yan aji suka bita da kallo shi kuma malam Sadeeq ya saki wani tattausan murmushi ganinta yau tsab-tsab da ita sai dai makeup d’in da tayi ne duk ya cuceta dan duk ta cika fuskar da d’ige-d’igen baki dajanbaki sai dai yaji dad‘i dayaga tayi wanki yace. “Toh muga bakin.” Ta bud’e mai hak’oran nata ya gani ya d’aga kai sun d’an fl na baya ya kuma cewa “muga kanki.” Nan ma ta bud’e da saurinta ya kalla gashin nan yayi d’as da kitso ya kuma kad’a kai domin tayi k’ok’ari sosai lallai hakan yana nuna masa cewar ba k’aramin son a bata kyauta takeyi ba yayi murmushi yana wani sak’e-sak‘e cikin ransa kafln yace. “Toh kinyi komai Aisha muga farcanki.” Sai a lokacin ta tuna sam bata yanke ba sai ta bata rai idanunta yayi rau-rau zata yi kuka dan tasan rashin yanke farcen ba k’aramin asara zai janyo mata ba Sadeeq ya kuma cewa “muga farcan ki Aisha.”A hankali ta mik’a mai hakan yasa shi saurin kallanta domin beso ta fad’i tausayinta ya kamashi ba yadda zaiyi dole yace.”Aisha baki yanke farce ba, tashi kije wajan doctor Abbakar…” Tana hawaye tace “Amma malam hikadai nefa banyi ba kuma wabillahillaxi mancewa nayi dan Allah kayi hakuri kabani atamfar..”
“Tashi ki fito Aisha.” Tashi tayi tana kuka domin ba k‘aramin haushi takeji ba ta k’arasa wajan Abubakar wanda waya yake kare a kunnansa shi kuma Sadeeq ya cigaba dayi idan yaga wanda beyi wani abunba sai ya turasa wajan Abubakar, shi kuma ganin yara sun taru a gabansa yasa shi cewa Qibd’iyya. “My love bari na barki zan…” Ya kasa k’arasawa sabida ido hud’u da sukayi da INdo zuciyarsa tayi wani rass gashi idanta yayi jah sabida kuka sai kawai yaji zuciyar sa nayi mai wani irin zillo ya kashe wayar bema sani ba sannan ya mik’a hannunsa yajanyo na INdo ita kuma ta fara dak’ilewa a tunaninta dukanta zaiyi ta fara ihu tana bashi hakuri shi kuma ya damk’e hannun nata sabida yadda yaji shi cikin wani irin mood akanta….
Hmmm kodai Abubakar ya kamu ne
Muje zuwa