MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 4 BY REAL FAUZAH TASIU

MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 4 BY REAL FAUZAH TASIU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Batace masa qala ba Amma ta qudurce a ranta ko wuta yake fesarwa qarshen bala’i bazata bisa yayi Mata uku babu ba da wannan ta janye ta shiga bathroom ta tsarkake jikinta ta fito ta iskeshi yayi bacci ta zubawa fuskarsa ido da gaske kyakkyawa ne kamar yanda Ni’imah tasha fada Mata Amma bata taba ganin kyansa ba sai yau ajiyar zuciya taja ta haye gadon zata kwanta ya janyota jikinsa yace “kin gama kallon nawa?” Kunyace ta kamata tayi luf a jikinsa da haka bacci ya kwasheta Basu suka farka ba sai asuba shine ya fara tashi ya tsarkake jikinsa yayi alwala ya dawo itama tayi sukayi sallar ya koma ya kwanta ita Kuma ta shiga kitchen tana hada musu abin karyawa bayan ta gama da qarfin hali da komai tayi wanka tayi kwalliyarta sosai yau jin kwalliyar takeyi musamman badan kanta ba sai domin kalaman Ni’imah da suka kwana suna yawa a kwanyarta Wai snatcher itace snatcher, bayan Allah shaidane tayi duk me yuwuwa taga ta gocewa wannan qaddarar hakan ya kasa samuwa ta qudurce a ranta tunda har ta yarda ita snatcher ce to zatayi duk me yuwuwa ta boye Mata baraka tsakaninta da mijinta bazata yarda Koda wasa ta fahimci akwai rashin jituwa tsakaninta da Ja’afar ba, da kanta ta tambayi kanta Ashe da gaske ne abinda Ni’imah ta dade ta fada mata ita Koda uwarta zata iya raba gari akan mijinta,

Murmushi tayi ta matsa inda yake kwance tabbas yakamata ta nutsu aikine ja a gabanta da gaske batajin Ja’afar a ranta shafa fuskarsa ta rinqayi da hannunta cikin baccinsa me hade da mafarkai masu dadi yaji qamshinta ya cika hancinsa ga wani dumi da yakeji a tsakiyar hannunta ya saki ajiyar zuciya tare da bude idonsa ya saukeshi akanta, mamakine yasashi sakin baki ta sunkuyar dakai tana murmushi tace “jiya naji kana waya kana cewa zaka hadu da wani a fada 9:00am Kuma naga takwas harta wucce Ina fatan tashin da nayi maka banyi laifi ba?”

Zuba Mata ido yayi kamar me nazarin wani Abu sai yaga ta zame qasa cikin sanyin jiki tace “kayi hqr idan hakan ya bata maka rai bazan qar…..” Rufe Mata baki yayi tare da miqewa ya miqar da ita yayi hug nata tare da dora kansa saman nata yaja fasali yace “koma kin batamin na yafe Miki muje ki shiryani ki bani abinci” zaro ido tayi yayi dariya shima murmushi yayi yace “matsoraciya ba komai zanyi Miki ba”

Noqe kafada tayi tace “aa kaje ka shirya bari na qarasa hada break din bata jira cewarsa ba ta fice da sauri yayi ajiyar zuciya ya fice ya shiga nasa dakin ya jima kafin ya fito ya isheta a parlourn tana fesa room freshness zama yayi a dinning yace “abar aikin nan azo ayi Break” ajiye gongonin tayi tazo ta zauna ta hada masa ta miqa masa itama ta hada nata sunacin abincin Amma idonsa na kanta yana yabawa da baiwar da ilahi yayi Mata ta kowanne bangare tabbas itadin macece da yake fatan alfahari da ita,

Miqewa yayi yace “alhmdllh kitchen ya karbeki fatan nasara saina dawo” fatan alkhairi tayi masa ya fice ya shiga bangaren Ni’imah da alamu ma batama tashi ba parlourn duk abin Apple da lemo yayi qwafa ya nufi saman ya shiga tana kwance a gado tayi daidai abinda sai baccinta takeyi bathroom ya shiga ya ganshi a bushe ya dawo ya qure Mata A.C tare da kure gudun fanka yaja ya tsaya shi kansa sanyin ya damesa.

Murmushi yayi yanda yaga tana neman duvet din daya janye hakan yasata miqewa ganinsa a tsaye yasata jin wani dam yaja numfashi yace “baki sallah ne 8:40 baki tashi ba” harararsa tayi tace tunda Kai ka tashi dai ai shikenan Ina ruwanka da sallah ta” bai damu da abinda tace ba ya matsa jikin gadon yace “ki tashi kiyi sallah ki Kuma sabarwa kanki tashin asuba nagaji da fada Miki zan fara daukar mataki akanki shari’a tace yaroma idan yakai shekara bakwai yana qin yin sallah a dakeshi Kinga kuwa kema zaki iya shiga sahun”

Ta bude baki zatayi mgn ya dora Mata hannu a bakinta yace “bakinki ma wari yakeyi bakiyi brush ba kije ki gyara kanki idan kinason na saurareki inason mace me tsafta Rafi’ah kafin na tashi ma ta gama komai na gidanta yanzu dana fito in mutuwa zatayi da dawo ma saitayi tanada lkc kafin na dawo Amma ke bakida aiki sai bacci da hauka”

STORY CONTINUES BELOW

Yana mgnr yana tafiya yana idawa ya fice ta biyosa tanason yimasa diban albarka wai bakinta ne yake wari Kuma har yake hadata da  banzar matarsa, kafin ta sauko harya fice ya shiga mota takaici ya cikata ta juya zata koma zuciya ta tunzurata ta fito a fusace ta nufi bangaren Rafi’ah Rafi’ah na jikin window na dakinta ta hangota tayi saurin sakin labulen ta sauko qasan ta zauna daidai lkcn ta bude qofar ta bankade labulen tana huci dagowa Rafi’ah tayi ta zuba idanunta akanta tayi murmushi tace “Lah Ashe Ina ranki yanzu nake Shirin zuwa mu gaisa sai gaki kin tashi lfy” ashar ta qunduma Mata tace “ina ruwanki da lfy ta munafuka annamimiya maci amanar aminci zuwa nayi nayi Miki kashedi karki kuskura ki shiga harkatata na tsaneki Rafi’ah na tsaneki Kuma wlh zakiga abinda zai faru”

Murmushi Rafi’ah tayi ta miqe ta nufi freezer ta bude ta dauko ruwa bottle daya ta nufo Ni’imah ta bude ta tsiyaya Mata a cup tace “Calm down Matar mijina sha ruwan sanyi nasan zakiji sauqi a zuciyarki ni har gobe inasonki dama ace kinbi komai a sannu ni ba abokiyar rigimarki bace dacan a baya bamuyi ba yanzu da kusanci ya qara qarfi bai kamata muyi ba Koda yake naga kishi ya rufenki ido kin kasa yin karatun baya any way koma dai menene mijinki ne qaddara ta bani na aura babu yanda zanyi dashi babu yanda zaiyi dani duk da cewa shi ba zabina bane Amma ni zabinsa ce so da kinyi hqr qila da kinfi qima ke kinsani ni ba kalar matar da zan tsaya Ina Fadi in fada da kishiya bace balle Kuma ke ni practical zan nuna Miki kalar nawa salon” komawa tayi ta zauna tare da daukar wayarta daketa ring tace “Bestie kana lfy ya kewata?….”

Wani tuquqi ne ya tasowa Ni’imah tayi kan Rafi’ah da sauri ta miqe tace “sorry I call you later” Dora wayar tayi saman TV stand ta jirayi qarasowarta tana zuwa ta kawo Mata duka ta kauce tana dariya tace “ni haba yarinya ai bazakiyi dani ba” wayarta ta Zara ta haye sama tana cewa idan kin gama ki rufemin na gaji bacci nake buqata” binta tayi da zagi tana wani Harbin iska batako waiwayo ba ta shige dakinta ta fada gado ta kwanta tana murmushi tana Jinjina haukan Ni’imah wai akan namiji take haukannan namiji ma irin Ja’afar Wanda a zaman da ta danyi dashi na kwana biyu ta fahimci shi ba mutum ne da ake burgeshi ba abinda yaga dama shi yakeyi.

Duk irin bugu da zage zagen da Ni’imah takeyi Rafi’ah bata tankata ba kuma bata bude ba dakanta ta gaji ta tafi tana kwance taji ya sake kiranta ta daga yace “meye ya hadaki da Ni’imah kikaje har part dinta kika zageta?” Abin ne ya daure Mata Kai tace “ni Kuma nida tunda ka tafi Ina kwance ko qasa ban sauka ba saida naji kamar ana tabamin qofa nace maka zan kiraka anjima” numfashi yaja kawai sai ta Kama shassheqar kuka abinda ya tashi hankalinsa kenan yace “to meye Kuma daga tambaya sai kuka” jan zuciya tayi tace “ni bansan meye ta tarewa duk wani wanda ya shafeka ba da baya sona nima fah bason aurennan nakeyi ba qarfa qarfa akayimin….”

Katseta yayi da cewa “kinga naji Ni dama tunda ta fada ban yarda ba kawai na kiraki ne don na gasqata ai daga yanayinki ma ansan ke bame fitina bace” jan zuciya tayi tace “to nidai banaso kajawa matarka kunne kada ta qara qoqarin hadani dakai idan wani abu takeji akaina tazo ta sameni zan iya sammata lkc a cikin lkcnka inka yarda” dariya yayi yace “bama na buqatar kowa ya shiga lkcna ya tsaya iyakar nawa ni daya”

Kashe wayar sukayi tayi murmushi tace “salon wasan zai canza dama aunty Bushira ta fadamin saina sawa idona kwallin rashin mutunci zanyi miki illah idan kika matsa Ni’imah badon mijin ba saidon ki gane kowa yanada tasa baiwar” tayi bacci sosai sannan ta  tashi  ta shiga kitchen ta fara shirya dinner ta bata lkc matuqa wajen shirya musu abincin lkcn data gama biyar saura ta fada bathroom ta dauki wankan susuta megida ta harde a parlourn tana kallo tana chat bai shigo gdanba sai bayan magrib ya jima akanta kafin ta ankara shima Saida ya zare wayarta a hannunta ta dago suka hada ido da Ni’imah dake shigowa bakinnan kamar cokali kawai saita qara fadada murmushinta ta miqe ta rungumeshi tare da lalubo bakinsa ta hada da nata ya tallafo bayanta yana sakin wani nishi me qarfi mutuwar tsaye Ni’imah tayi saboda abin yazo Mata a bazata kallonta Rafi’ah tayi ta daganta gira tare da janyewa daga jikinsa ta shafa sajensa tace “yau na yini da kewarka sai nakejina kamar marainiya ka tafi ka manta damu…”

Rufe Mata baki yayi yace “ah haba kiyi istigfari wlh kina Raina munje anguwa da Mai martaba ne dana dawo Kuma sai na wucce sama mana Visa me kika tanadar min?” Rufe idonta tayi tana yar qaramar dariyar kirsa tace “a..bin…da…ka…fis….” A rarrabe tayi mgnr ya kwashe da dariya yace “wayyoh dadi matata kina shagwabani wai dama haka kike wow! Allah na gde mak….”

+

STORY CONTINUES BELOW

Muryar Ni’imah yaji ta rushe da kuka tana cewa “Allah ya isana wlh Allah ya isana kirana kayi don ka wulaqantani a gaban wannan yar iskar matar tak…” Tsawa ya daka Mata yace “keyyyy ki iya bakinki….” Rufe masa baki Rafi’ah tayi tace “Haba ranka ya dade saurin fushi ai ba naka bane ay rarrashi take buqata” sakinsa tayi ta nufeta ta kamota tace “kekuwa rabin jiki kiyi hqr mana ai bamusan dakeba idona rufewa yake idan Ina tare da mijina shine sanyin ruhina salamar rayuwata am sorry please iso muyi dinner yau abinda nasan kinaso fiye da komai shi nayi mana kowa favorite dinki zaici yau a gdannan”Fusge hannunta tayi ta hankade Rafi’ah tace “dake da favorite din na hadaku naci bura ubanku ni zakiyiwa bariki kina kallona kina wani qara rungumarmin miji kina tsotsar bakinsa har kina dagamin gira kice wani baki ganni ba kaikuma kwallon munafiki sullutu sallamamme da aka wanke wani guri aka bashi ya shanye har wani qara shigewa kake jikinta to ka hadiyeta mana qarewar so da kewa munafiki mara adal….”

Hannu ya daga zai kwada Mata mari Rafi’ah tayi saurin riqe Hannunsa tace “Don Allah ka rinqa tausasa zuciyarka mijina ai namijin gaske baa sansa da fushi a gidaba idan kana fushi meye sauqinmu ne muda zamu rayu a qarqashinka please yi Mata uzurin nan daka saba da wankama nakeso na tayaka kayi nasan ka gaji Amma naga tumbinka ya sauka ba haka na saba ganinsa ba muje na ciyar dakai yanda zaifimin dadin shafawa” ta qarasa tana shafa tunbinsa murmushi yayi ya dagata cak ya direta a kujerar dinning din takaici ne da baqin cikin abinda bata taba tunani ba yasa Ni’imah juyawa zata fice har takai bakin qofa yace “dokace ba umarni ba kin saba taka dokata Ina qyaleki wannan bazanyi uzuri ga kowa ba”

Sumsum ta dawo taja kujera ta zauna Rafi’ah tai murmushi ta hadawa kowa abincin ta turawa kowa gabansa ta diba a cokali zatakai bakinta ya riqe tasan me yake nufi ta matso da kujerarta ta rinqa bashi tuwon Cous-Cous ne da miyar kubewa da yaji bandar kifi sai fatan doya da yaji hanta babu kunya Ni’imah da ganda tasata yiwa kanta horon yunwa ta zage ciki ta nadi tuwon tasha hadin lemon da Rafi’ah tayi musu na kankana ta miqe ta Kama hanya zata tafi Ja’afar yace “ki jira na gama na rakaki tunda cikinki ya dauka a qa’ida ma fah ba ita zatake girki ba ke zakikeyi mana tunda ita sabon hannu ce da wanne zataji saboda haka daga gobe zaki fara aikinki zuwa sati” ta hadiya iyakar hadiya wai tayi musu girki suci tab aikuwa zaayi zaman yunwa a gdan to ita da wanda zataci ma batason girkawa itace zata girkawa qarata biyu abinci tab zaayi bala’i kuwa” a tsaye ta tsaya taqi zama shima Kuma yaqi tashi saijan Rafi’ah yakeyi da hira itace taga tsaiwar tayi yawa tace “am dare yayi zata gaji da tsaiwa ka tashi ka rakata” juyowa yayi ya dubeta ta kumbura fuska yayi murmushi yace “wlh na manta dake a tsaye sorry muje na rakaki” miqewa yayi itama Rafi’ah ta miqe ta rakasu har bakin qofa tace “asuba ta gari Best….”

Wata uwar harara da yayi Mata tasata juyawa da sauri ta fara harhade kayanta sake gyara parlourn tayi ta kunna turaren wuta a burner ta haura saman shima ta sake Masa sabon gyara tayi alwalar isha tara harta wucce tayi isha tayi shirinta na kwanciya gabanta na faduwa batason nacinsa cikin saa daya shigo din shima bai wani takura Mata ba sukayi baccinsu salamun salamun washegari litinin ta roqeshi alfarmar zataje tayi C.A a school da farko cewa yayi bata isa fara yawo ba Saida yaga  ta marairaice masa zatayi kuka sannan yace ta shirya yakaita suna fitowa Ni’imah ma tana fitowa da alamun fita zatayi iyakar son tuno abinda ya wucce dinsa yakasa tuna sanda ta tambayeshi fita Koda yake dama tunda aka fara mgnr aurensa da Rafi’ah bata tambayarsa zuwa unguwa saidai ya dawo ya tarar batanan.

Ya shirya Mata mugunta saboda haka ya nufeta da sauri yana zaro kudi a aljihunsa yace “Au na manta yau zanyi baqi daga Gombe ki bawa Yahaya kudi gasu ya siyo kifi nasan babushi a kitchen dinki wancan kin barsa ya lalace kiyi mana farfesu sannan kiyi mana tuwon alkama miyar kalkashi ki tabbatar kin gama kafin azahar zankai Rafi’ah makaranta  May be tare zamu dawo da baqin”

Bai jira cewarta ba ya juya yana murmushi ya shige motarsa yaja har suka fita takasa motsawa tashin hankalinta yanda zatayi wannan wahalallan girkin daya sata ita tunda take a gidansu bata taba ganin anyi tuwon alkama ba Amma wai yau ita zatayisa harma da tagomashin miyar kalkashi ga gyaran kifi da kullum ta gyara sai yace bata iyaba gdanta yana qarni, zubewa tayi a gurin ta dora hannu aka tanaso ta zunduma ihu Amma ta kasa daqyar ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta koma ciki ta rinqa zagaye parlourn tana tunanin ta inda zata fara kiran Hajiya Sahura ne ya shigo ta daga da sauri tace “ya munata jiranki boka yace dole sai kinzo aiki zaiyi yadda akeso ke Kuma kina bata Mana lkc” sai yanzu ta samu damar fashewa da kuka tace “Mom wannan dan gadon masifar ne ya hadani da aiki wai baqi zaiyi shine yace nayi masa tuwon alkama miyar kalkashi sannan nayi masa farfesun kifi harda cewa saina hada masa lemo don Allah ki turomin Marawiyyah nasan ta iya tunda girkinsu ne na yan qauye wlh idan banyi ba akwai matsala” Hajiya Fatsum ce ta karba tace

“Ke shashasha ce to ki fito mana idan aka gama abinda zaayi minti nawa ne zaki dawo kiyi masa inma kafi tuwon alkama ne Kuma ma idan ansamu yadda akeso ai bai Isa yace qala ba” dadine ya cikata tace “ok hakane ganinan” daukar Jakarta tayi da mayafinta ta fice tana dariya tana cewa “Ja’afar Wakil ka bonu ka lalace a gurina” mota ta dauka ta nufi qauyen tana zuwa ta tarar da uwar mijin nata da uwarta sunyi gurfane kamar masu neman gafara.

Dariya boka na gangare ya sheqe da ita yace “shegiya haihuwar asara ta sabawa umarnin miji ta fito toke an fada Miki wannan yarinyar a zaune take ai munafurtarki takeyi tana zagayewa tana bin manyan bokaye yo baki ganiba ko a yammatancinku tafiki farin jini ke Saida aka rinqa hadawa da layu da guraye sannan aka samu aka hadaki da wannan kaffafen mutumin da kurwarsa taqi juyuwa to ai baki sani bama tuni burinki yana gaf da rushewa ke wata biyar yana baki kinaqin karba ita kuwa tun ranar farko ta karbe yanzu haka da cikin yariman Azare me jiran gado a jikinta…..”

Zaro ido sukayi tare da dafe qirji dukkansu Hajiya Fatsum tace “ciki Kuma daga zuwanta haba boka sake dai dubawa ni dana bashida wannan azarbabin” tsawa boka ya daka Mata yace “ankare nutsu tsinanniya wacce ta fatalar da aljannarta na rantse da bukkata Rafi’ah amaryar danki Ja’afar tanada shigar ciki saidai a dauki mataki Amma cikikam akwaishi abinda yasa naqi yarda na rusa aurennan kenan na hango rabo me zafi yana yawo inma baayi aure ba to zaa lalace ayishi a titi yanzu mafita dayace idan bakwa buqatar cikinnan zanbaku wata laya kusan yanda zakuyi ku haqa saitin inda kukasan koba kullum ba wataran dole sai tabi gurin ku binne to indai kukayi haka duk sanda ta samu ciki ko ya Isa haihuwa indai ta taka gurinnan saiya bare hhhhhhhh tsinannu Kuma karba fa zakuyi ku?”

Tsoro ne ya shigi Ni’imah tace “kayy aa gaski…..” Bige bakinta Hajiya Sahura tayi tace “aa ubanki ai dole mu karba ke baki kishin kanki baki fatan ki zama uwar sarkin wataran” kallon Hajiya Fatsum Hajiya Sahura tayi duk hatsabibancin Fatsum tana shayin Sahura take tace “abamu boka nima banason shegiyar yarinyar nan ta hada iri da dana wlh irin Hajiya Amina ai irin masifane buzuwa ce fah tsafi sukeyi su bama asiri ba”………….

_Maganin sanyi! maganin sanyi!!_

_Mata sai _fa kun tashi tsaye wlh duk maganin matan da zaki sha idan har da sanyi ajikin to  bazai taba_ _miki aiki ba saboda sanyi  yanzu ya adabi kowa ba yara ba manya  ba_ _zawarawa ba yammata ba mazan ba matan kowa yiyake Dan haka Yar uwa  kizo ga magani_ _nazo miki dashi me kyau sadidan ba karya, Koda yake Ni bazance Miki komai ba saikin gwada  zaki bawa wasu labari._

_Yana maganin sanyi mai_ _sa kaikayin gaba da kuraje dadewar gaba daukewar niima karancin shaawa kaikayayin jiki ciwon jiki da ciwan Mara yawan Ciwan kai idan sanyi ya busa maza Yar uwa ki hanzarta kine mi_

_naki_

_Muna aikawa ko wani gari a kano kuma kowace unguwa Dan Allah idan kinsan baki shirya ba karki mun magana mubatawa juna lokaci._

_Serious buyers siyan daya ko sari ki shiga nan Domin qarin bayani_1

_____________________________

_____________________________

Numfashi yaja yace “shikenan Dad Babu komai Amma aja Mata kunne abubuwa da yawa Ina hqr dasune dominka kada takai hqr na qarshe” godiya Dad yayi masa suka aje wayar ya zubawa Rafi’ah ido tayi luf da ita ta lafe a katifar yanayinta ya kalla kawai ya fahimci da abinda yake damunta Amma dake miskili ne saiya shige bathroom ya fada wanka sanda ya fito tayi bacci,

Shima kwanciyar yayi yanajin yanda dumin jikinta yake hauhawa da hakadai shima bacci ya daukeshi washegari taso zuwa school ya fitittike ya rinqa ruwan bala’i waishi yayi aure Amma bazai samu lkcn matarsa ba da anyi mgn sai tace school, dole tanaji tana gani ta hqr aikuwa ranar tasan ta zauna a gda duk wata nutsuwarta Saida ya rabata da ita ko bakin qofar dakin yaqi zuwa wannan Abu ya dameta hakadai taketa daurewa har yammaci yayi wanka ya fice itakuma ta gyara bangaren ta sake kwanciya.

+

Yinin ranar sur bataji Motsin Ni’imah ba to dayake itama taji maza batako leqoba har dare yayi da daren ne ya shigo da murnarsa ya zauna a parlour yana shafa fuskarta ta bude idonta akansa yayi murmushi yace “ina fatan kin gama ready na tafiyarmu jibi zamu tashi” lumshe idonta tayi kawai batare da tace masa qala ba lamarin daya bashi mamaki yasan dai ba wani Abu ya fada Mata da zai dameta ba farin ciki ma ya kamata tayi.

Juyowar da zaiyi yaga hawaye yana zuba a idanun nata dagota yayi da matsanancin mamaki yace “mene Kuma ya faru daga mgn?” Hawayen ne ya qara qarfi tace “amma dai nazaci kasan cewa Ina karatu Kuma kanada lbrn burina akan karatuna meyesa ka dage saika tafi dani bayan bani kadaice matarka ba meyesa bazaka dauki Ni’imah ba tunda ita free take Ni ka qyaleni na qarasa karatuna kace 3 mouths kafin three months munyi exams mun gama don Allah ka qyaleni badon….”

Abinka dame zuciya a kusa sosai ranshi ya baci Amma Bai nuna Mata ba ya miqe ya haye sama tabisa da kallo jin shirun tayi yawa bai dawo ba itama ta miqe ta nufi saman ta bude dakinsa ta hangesa kwance kan gado matsawa tayi ta zauna kusa dashi ya zubawa selling ido Kama Hannunsa tayi ya janye ta bude baki a hankali tace “bansan bazaka fahimceni ba da ban fara fada makaba kayi hqr….”

Daganta hannu yayi yace “fita Rafi’ah” da sauri ta dago ya tashi zaune yace “ki ficemin a daki nace” miqewa tayi a tsorace ta fice daga dakin da sauri ya furzar da iska me zafi ya tashi ya kulle dakinsa  nata dakin ta shiga ta fada gado tayi kwanciyarta zuciyarta na tafasa ta tsani mutum mara fahimta a rayuwarta, da wannan tunanin ta tashi kawai ta dauka qur’ani ta fara karatu ta Jima tana karatunta sannan ta bari ta koma ta kwanta aikuwa bacci ya dauketa me dadi hankalinta kwance bata farka ba sai asuba tayi sallarta ta fito parlourn ta fara shirya breakfast tana kitchen din taji saukowarsa ta fito ya zubanta ido harta qaraso kusa dashi ta durqusa tace masa “barka da fitowa” wani gwauron numfashi ya sauke komai na me ilimi dabanne da oo ce sai suyi sati suna gaba da juna Dagota yayi ya hadata da jikinsa yace “na fahimcek….” Rufe masa bakinsa tayi tace “na hqr da karatun kayi duk yanda kakeso dani” wani dadine hade da tausayinta ya mamayeshi  ya qara matseta da jikinsa yace “are you sure?” Dagansa Kai tayi yayi murmushi me sauti ya sauke lips dinsa a goshinta yace “Allah yayi miki albarka zuciyata tafi aminta dana tafi dakene saboda inads tabbacin zamu qara samun kusanci da fahimtar juna bazan katse Miki karatunki ba jiya na gama Miki komai insha Allahu wannan daya dai bazai hanaki samun abinda kika Dade kina muradi ba sai kinzama doctor din da zaayi alfahari da ita a fadin Nigeria ki shirya yau zamu wucce Abuja gobe saimu tafi kinji amaryata?”

STORY CONTINUES BELOW

Yar qaramar dariya takeyi tana shafa qirjinsa ya sanya hannu ya balle bottle din rigarsa yajata suka zube a kujera ya sanya bakinsa ya Kama ZIP din rigarta na gaba ya zuge ta tsorata da inda taga ya nufa amma bata Isa nunawa ba yanzu sai rai yazo yana baci hakanan tanaso bataso suka bata lkc wajen romance din juna suna a haka sukaji ana buga qofar da qarfin gaske kallon idonta yayi itama shi take kallo ya janye yana mayar da numfashi yace.

“Uban waye zaizo yanamin bugun nan da sassafe?” Bude qofar yayi yana huci kawai sai ganin Hajiya Fatsum yayi tsaye tanata huci saurin saita kansa yayi yace “da safennan Hajiya sannu shig….” Daukeshi tayi da mari tace “da saikamin iso zan shiga munafuki Koda yake zama ka iya korata kace bacci zakasata sallamamme asararre” shigewa tayi daidai lkcn Rafi’ah ta gama zura hijjab dinta dan batamasan inda ya cilla Mata rigarta ba a dan darare tace.

“Hajiya sannu da zuw….” Tsawa ta daka Mata tace “dakata irin tsiya barden goyo karki kuskura wannan bakin naki na gadon maita ta ambaci sunana na lalace kamar yanda wannan dan asarar ya lalace waike makira wacce ta tsotsi kirsa a nonon uwa kinzo daga zuwa kwana hudu kin kanainaye komai wato har tafiyar da aka dade da shiryata da yarinyar nan yar albarka kin hana yanzu dake zaayi ko aikuwa indai nice na haiheka bakai ka haifi kanka ba to baka Isa ka tafi da yar iskar yarinyar nan ba saidai ka tafi da Ni’imah itace ma ta dace da tafiyar domin ita tayi kalar turawan wannan me baqin jiki da baqar zuciyar bata dace da zuwa canba ka bari idan zaka Niger ko Africa ta kudu ko Kenya saika tafi da ita nanne ya dace da ita, sannan Abu na gaba wannan cikin dake maqale a mararta ban yarda dashi ba ba naks bane dashi tazo dan bazance a waje kayi Mata ba domin kanada Mata inda kanada rabon a kusa da tuni kasashi a inda ya dace”

Tunda Hajiyan ta ambaci cikin suka kalli juna tana rufe baki sukace “ciki?” a tare kallonsu tayi da sauri domin tayi subutar baki saita waske da cewa “eh jiya Ni’imah take cemin tana kwance batada lafiya to inba ciki ba menene?” Ajiyar heart yayi ya taka ya qarasa gaban Rafi’ah dake durqushe ya dagota yace “ok babu mamaki ai abin rabone Hajiya am ki manta kawai dama ita Ni nayi Mata dole bason tafiyar takeyi ba saboda haka kowacce ta zauna kawai zanje na dawo lfy dama wata kwangila ce da zanyi da wani campony  so shine nakeson zuwa na gama komai kafin tsakiyar shekara Amma tunda abin ya zama haka zanyi qoqari na dawo nanda 2 mouths insha Allah”

Harara ta watsa masa tace “ba haka nace ba cewa nayi ka tafi da Ni’imah” qasa yayi da kansa yace “nifa wlh bazan tafi da itaba batada wani amfanin da zatayimin mace sai rakin masifa daka tabata tace ta gaji Hajiya babu ruwanki fah da harkar cikin gidana abinda ya shafi matana kowacce nasan amfaninta saboda haka babu me tsaramin yanda zan rayu da iyalina”

Fuuuu ya juya ya haye sama yana masifa muqus Hajiya Fatsum tayi saboda sanin halinsa ba mutunci ne dashi ba ko kadan juyawa tayi ta kalli Ni’imah dake tsaye riqe da qugu tama manta da Rafi’ah a gurin tace “wannan shegen yaron bayajin bari saidai Kai ka bari Kinga muje kawai waini wannan lemon kuwa kinbawa shegiyar nan Tasha?” Harara Ni’imah ta watsawa Rafi’ah ta waske da cewa jiya fa saboda wannan snatcher din yace na zauna a gidanmu ni wlh Hajiya na fara gajiya da wulaqancin danki idan bazaki iyaba ki qyaleni na tafi Mana saikace dole”

Ranqwashi ta zuba Mata tace “babu inda zaki kinanan Wai an dorawa kwado tanki wato so kike kibarwa baqar ashana gdan ta qoneshi ta qone me gidan ai kece mafitarsa idan ba hakaba kuwa to ganinsa ma saiya gagareni am ki barni da yar shegiyar nan da qafafunta zata tafi ai duk Wanda yaci tuwo Dani miya yasha ba Amina ba ko Niger ce gabadaya qarewar buzu shegiya me idon aljanu wlh a gidan dana dai baki Isa ki haihuwa saidai kita asarar qwayaye su lalace a banza”

Saukowarsa ne yasa su saurin juyawa suka fice tananan durqushe inda yabarta ba maganar Ni’imah ce ta batanta Raina ta Hajiya Fatsum ita a komai nata tana hqr Amma batason ana taba Mata martabar iyaye domin batada na biyunsu a duniya, sosai kuka takeyi harda shassheqa tana tambayar kanta ita wannan wanne irin aurene takeyi kowa baya qaunarta meyesa qaddararta tazo da wannan simatsin?”

Jitayi ya dagata cak ya nufi saman da ita bai direta ko inaba sai gado ya lullubeta da qirjinsa ta sakarwa kukanta jiniya tana cewa “don Allah ka qyaleni banaso Ja’afar wlh banason….” Rufe Mata baki yayi yana tsotsa yana sauke numfashi yana tura Hannunsa cikin sumarta tare da dora dayan a qirjinta ta rintse idonta ta tureshi ya fadi gefe kafin ya taso ta tashi a guje kamar walqiya ta shige bandaki shi dariya ma ta bashi yayi dariyarsa me isarsa ya miqe ya fice daga dakin sake shiryawa yayi ya hade abinda yasan zai buqata ya dawo ya ajiye Mata kudi masu yawa a saman bedside ya fice bangaren Ni’imah ya shiga tananan zaune sai chat takeyi daure da towel da alamun daga wanka ma ta fito murmushi yayi yace “kinji dadi ko kin hadani da mahaifiyata to meye ribarki don kinsa ta hanani tafiya da Rafi’ah?”

Tashi tayi zaune tace “ko banza munyi biyu babu ai Kuma sai aje a rungumi pillow abinda akewa bazaa samu ba saidai aci na kwararo” badan ya shirya tsiya ba da kwade bakinta zaiyi Amma dake yasan meye ya taka sai kawai yayi murmushi ya zaro kudi ya doranta a jikinta yace “kinyiwa kanki”

*_Cigaban na jiya_*

Ficewa yayi ya koma bangaren Rafi’ah dakinta ya shiga ya dauki qaramin akwatu ya zuba Mata kayanta bai bita kanta ba yaje yasa a mota ya dauki wayarsa ya kirata Saida tayi ring sai uku sannan ta dauka yace “ki fito Ina jiranki a parking space” yana fadin hakan ya kashe wayarsa yabarta tsaye sake da baki zuciya na raya Mata kartaje sanin da tayi cewa hakan zai bata ransa yasata daukar mayafinta ta zura takalmi riqe da wayarta ta fita bude Mata yayi ta shiga yatada ta kalleshi da sauri tace “hajiya fah tace kada ka tafi dani” Saida suka fice a get din ya waiwayo ya dubeta suna hada idanu sai hawaye sharr.

Tsuke fuska yayi yace “ikona ne hakan ba ikon Hajiya ba bata Isa ta yankamin yanayi da iyali na ba” daga haka Bai qara cemata komai ba itama taja bakinta ta tsuke sukayita sharara tafiya sune har Abuja a mota kafin sukai Abuja tayi bacci yakai sau hudu ita da kanta tana mamakin yawan baccin nata cikin sati guda da bikin nasu data zauna sai gyagyadi sai bacci.

+

Suna Isa gdan yayi parking ya sabi abarsa a kafadarsa ya shiga da ita ciki ya kwantar da ita a kujera ya zuba Mata ido lkcn da take bude idonta akansa murmushi ya sauke mata yace “baccinki yayi yawa saikace kasa Anya kuwa bansa babyn ba ta mafarkin na Hajiya” turo baki tayi tace “ni banida komai kawai gajiyar bikincan ne” ya bude baki zaiyi mgn tace “wayyoh kaina…” Saurin riqe Mata yayi yace “meye ya samu kan?” Harararsa tayi tace “ina ka kawoni?” Tambayar taso bashi dariya ya gimtse tare da daure fuska yace “au bakisan Ina satar mutane ba ai satoki nayi zanyi camping naki nayita baki aiki bazaki koma Azare ba saida kyautar babie”

Duka takai masa da pillow ya goce yana dariya ta miqe suka fara zagaya parlourn shammatarta yayi ya fada wani daki ya maqale jikin qofa tabisa ya kuwa rufe yace “masha Allah abani abinci na ko nayi aiki da qarfin da ilahi yabani na qwata” kukan shagwaba ta fara harda su dire diren qafa ya cafketa sama ya watsata gadon yabita ya turmushe sosai sukaba sama hayaqi suka jiyar da junansu dadi inda kowa yake baje fasaharsa wajen sarrafa dan’uwansa duk da bajin dadin abin takeyi ba har yanzu wuyar budurci bata barta ba Amma takan daure tunda ta fahimci mijin nata bamai takura bane indai kabashi yayi yanda yakeso to kaima zaka samu sauqi hakan yasa take sakar masa jiki tare da tayashi duk abinda ya dauko wannan Abu yayi mugun qara Mata martaba a idanunsa soyayyarta take qara narkewa a ruhinsa ta yanda take batattakar duk wani diso na son wani Abu bayan ita.

Wannan dare an more sosai washegari tashin asuba jirginsu yayi zuwa Mexico itadai bazata iya Dorar da tsayin tafiyar ba saboda wani irin yanayi da take a ciki ita ba me lfy ba ita ba mara lfy ba, sosai sun qoshi da tafiya tunda suka fara keta sararin samaniya take lefe a jikinsa shikuma sai shafa bayanta yakeyi inda suka bawa na kusa dasu aikinyi sukayita kallonsu suna shauqin jin dama sune, lkcn da suka sauka suka hau mota zuwa masauki sanyi kamar ya kasheta bata tabajin sanyin azaba irin na qasar ba ganin yanda take rawar sanyi yasasa kunna Mata room hitter.

Tare da bata wata Madara tasha ta haye gadon dake kusa da ita ta qudundune shima shiga yayi saboda ba qaramar gajiya yayi ba suka Kama bacci tsayin lkc sannan suka tashi tare sukayi wanka suka shirya ya bata wasu kayan sanyi da aka Basu a hotel din tasa shima yasa yabata coffee sukasha tare da cin abinci ya dauketa suka fice darene Amma kamar Rana tsirarun mutane sunata harkokinsu ta dade da lura da qasashen turawa da larabawa sunfi harkokinsu da dare,

Wani shagon siyayya suka shiga ya lodo Mata kayan sanyi suka fito ya sake biyawa wani gurin ya siya musu hot coffee sannan suka nufi masauki  suka fara sabuwar rayuwa dakanta ta fahimci Ashe sunso suyi ganganci subarshi ya taho shikadai itama da take mace yanayin azabar sanyin yana sata shiga yanayi bare shi namiji lafiyayye dole ya buqaci dumin mace a jikinsa aikuwa tanacin ubanta babu qarya danma yañada tausayi idan yaga ta shiga yanayi yakan qyaleta.

Satinsu biyar a qasar Mexico ta fara rashin lfy ta gaske da farko ya zaci weather dince ta dameta ya rinqa lodo mata kayan sanyi yana siyo Mata duk wani nau’in abinci da zaisa ta rage jin sanyi Amma daga bisani saiya fahimci ita sanyin ma takeso batada aiki sai kwanciya a qasa shan ice da sauran abubuwan sanyi ga rashin cin abinci sai tayi kwana uku bataci abinci ba saidai ice ki jus sosai ya shiga damuwa,

To yauma tun safe ya fice sha’anonin daya kawosa qasar ya matsu ya gama su tafi shi tunaninsa duk wannan yanayin ne yasata shiga ha’ula’iYana wajen harkokinsa yaji hankalinsa yayo wajenta ya dauki wayarsa ya kirata bugu kusan biyar bata dagaba abin ya tsumashi dole ya ajiye komai ya nufo hotel din da sauri ya haura saman ya bude dakin ya shiga bata parlourn hakan yasashi fara kiranta Amma Shiru bude qofar dakin yayi gabansa ya yanke ya fadi hangota da yayi kwance a qasa a sume bakinta sai fitar da kumfa yakeyi,

Da mugun gudu ya qarasa gareta ya ciccibota jikinsa yana Kiran sunanta a gigice yana jijjigata cikin tashin hankalin dabai taba shigaba, dagata yayi cak ya fito waje da gudu da ita ya nufi emergency care din cikin asibitin suna ganinsa suka tareta aka dorata a gadon tura marasa lfy suka shiga da ita wani daki suka dorata a gado tare da jorner Mata na’urori shikuma sai danna qirjinta yakeyi, jinyeshi likitocin sukayi duk da kasancewar bangarensa ne tashin hankalin da yake ciki bazai barshi ya bata taimakon da take buqata ba,

Duk wani taimako na gaggawa Saida suka gama batashi ta fara sauke numfashi sukayi ajiyar zuciya tare da likitocin dashi ya matso yana zana musu irin sign din da ciwon ya fara bayarwa kafin ta kwanta  hakan yasasu fara bincikarta cikin saa kuwa bincikensu ya nuna musu ai shigar ciki ke gareta na wata daya da awanni goma sha daya.

Wani ihu Ja’afar ya saki tare da yiwa Allah godiya ya rungumeta sai hawaye sharr ya sumbaceta yace “ni…Ni dama nasan aurena dake akai wani Abu me qarfi Allah baya hada lamarinsa a banza Allah na gde maka daka azurtani da samun qaruwa da mace mafi soyuwa a Raina Allah ka kareminsu ka tsareminsu daga sharrin duk wani abinqi” sake matseta yayi a jikinsa hawaye ya kwaranyo mata tun dirarsa ya tasheta taja ajiyar zuciya tare da qara gasqata girman Ubangiji tabbas Allah buwayi ne gagara misali burin Ni’imah kenan da anyi aurenta da Ja’afar ta samu ciki ta haifi Lil Prince Ashe ba haka Allah ya shirya ba ita da bata taba zataba bare ta kawo ita qaddara ta zaba a lissafin da likitan yayi ma ranar farko daya Santa mace ranar cikin ya shiga tabbas girman buwayar Allah abar jinjinawa ce.

Dagota yayi jikinsa cikin sanyin murya yace “har yanzu bakya sona Rafi’ah meyesa kika kasa koyawa zuciyarki son mijinki me sonki da qaunarki uban yayanki Ja’afar haba Rafi’ah me nayi Miki da kika kasa yafemin ne” rungumeshi tayi ta saki wani Kuma me ciwo tace “ni…nifa ba sonka ne banayi ba inajin tsoron Hajiya ta gane da gaske inada cikinka a jikina JM kasheni zatayi bata qaunata….” 

Rufe Mata baki yayi da nasa ya lumshe qananun idanunsa itama ta lumshe nata sun jima a haka kafin su saki bakin juna yaja numfashi yace “bandamu da kowa ya tayani sonki ba nidai inasonki Kuma nine zan rayu dake matata ki cire kowa a ranki don Allah ki manta da kowa kinji?” Dagansa Kai tayi yayi murmushi yace “bari nayiwa Hajiya Innah albishir nasan zata tayamu farin ciki” da sallama ya fara wayar suka gaisa yace “wlh tananan da sauqi muna asibiti ma batada lfy Lil Prince yana wahalar da ita” dariya yayi yace “aa Innata kawai dai na fadane ko Prince ko Princess duka Wanda Allah yabani Ina murna” sun jima suna waya tanayi masa fadan rage zafin zuciya me ciki batason yawan fada da fushi hakan yana dabi’antuwa ga yaron dake cikinta idan San samune ma zaifi su yawaita karatun qur’ani hakan zaiyi tasiri wajen halittar yaro zai dabi’antu da hakan sosai.

Godiya yayi Mata ya miqawa Rafi’ah wayar a kunyace suka gaisa tayi Mata fatan alkhairi suka aje wayar ya sake Kiran qaninsa Jamal ya fada masa amaryarsa tanada ciki steel ya sake Kiran Muhseen ya sanar dashi kafin dai wani lkc mgnr cikin ta cika wannan family Hajiya Fatsum itace qarshen Kira dake taji lbrn gurin Jamal saitaqi daga wayar sai text ya tura Mata tayi tsaki tace _“tsiyar zanwa fatan alkhairi?”_ tura Masa tayi ya duba sosai zuciyarsa na tafasa cije lips dinsa yayi yace “tsiya! tsiya!!” Numfashi ya sauke ya miqe ya fita bai jimaba ya dawo yana kallonta tayi qasa da kanta yayi ajiyar zuciya kallonta kawai yana kwashe masa damuwar da yake ciki zama yayi a gabanta yace “bansan me bebie na yakeso ba a fadamin na tafi ns Nemo” Lumshe idonta tayi tace “Abbansa yake feel…..”

Abin ya bashi dariya sosai yayi abarsa ta zuba masa ido yayi qiba sosai ya qara haske abinka da farin mutum ta sauke ajiyar zuciya tanajin wani yanayi game dashi, batayi aune ba taji ya dagota cak ya dauketa kamar babie ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta ya sauke Mata kiss me zafi yaja numfashi yace “bansan me zanyi ki gane irin farin cikin da nake cikiba Rafi’ah inason babien nan na cikinki tabbas shine asalin raba gardama ga duk me hankali yasan cewa zafin rabo shine ya rinqa azalzalar zuciyata Saida na mallakeki sonki da sha’awar kasancewa dake suka hanani duba kowace irin alaqa tabbas inajin cewa da wani qaddara ta gifta dana kasa samunki da zanyi Miki fyade Kuma zaki samu ciki to sai Allah ya dubi kyawun niyyata ya qadarta zamowarki matata mace mafi daraja aguna”

Lumshe idonta tayi yayi murmushi tare da direta a gadon yace “inasonki Rafi’ah kema kinasona?” Rufe idonta tayi da hannunta tana dariya shima dariya yayi ya miqe yace “har yanzu nakasa samun wannan kalmar kina Sona ya gagareki furtawa ko?”

+

Ficewa yayi ta miqe ta shiga bathroom tayo alwala ta dawo tana duba alqibla ya shigo da kaya a Hannunsa ajewa yayi yana kallonta ta tayar da sallar bayan ta idar ya matsa gabanta ya fito da kayan daya shigo dasu tarkacen ciye ciyene ya rinqa bata wanda zata iyaci ta karba Wanda bazata iyaba ta kawar dakai da haka saida ta qoshi sannan ya qyaleta.

Likitan ya Kira yabasu sallama suka fito tana kwance a jikinsa suka shiga dakinsu suna shiga ta fada gado duk jikinta batajin qarfinsa shikuma ya fada wanka lkcn daya fito har tayi bacci ya dubi agogo 10:30pm ajiyar zuciya yayi ya haye gadon ya janyota jikinsa ya matseta yana shafa bayanta zuwa mazaunanta ta sauke ajiyar zuciya tare da bude idonta Dora bakinsa yayi saman idon nata yace.

“ke kikace babie na ni yake buqata” turo baki tayi tace “aa nifa wasa nakeyi maka banajin feel naka…” Rufe mata baki yayi yace “ni inaji” daga haka Bai qara bata damar mgn ba ya kashe musu fitila sosai ya sanyata nishadi salonsa yana tsaya Mata arai bata iya bijire Masa dadine me ratsa kwanya yake bata itama tana tayashi Saida suka samu nutsuwa sosai sannan sukayi wanka suka kwanta.

Wayarsa da tun farko fara harkokinsu take ruri ya dauka ganin number Ni’imah yasashi tsaki kawai ya sata a silent ya koma ya kwanta ya sake rungume matarsa wayarta ce itama ta fara ruri gashi ya hanata tashi  bacci ne ya sakeyin dama dasu Basu suka tashiba sai asuba sukayi sallah suka sake kwanciya 11:00am suka tashi sukayi break ya fice ita Kuma ta danyi abinda zata iya ta sake kwanciya tare da janyo wayarta.

Missed calls tagani sunfi hamsin ta fara dubawa kusan duk na Ni’imah ne tayi murmushi tare da latsa layin Kira daya ta daga tace “sai yanzu kikaga damar daga wayar tawa?” Murmushi tayi tace “wlh kinsan dake ba zaman kaina nakeyi ba lkcn da kika Kira Ina tare da mijina shiyasa…” Wata dariya Ni’imah tayi tace “kaji fah masu miji mijine dake ko farka da akaga dama aka baki aronsa to bari kiji na fada Miki wani abu dole idan Mai fili yazo me trader ya dauke abarsa domin kuwa shi kansa yasan bazaiyi jayayya dame contenar ba to kamar hakane tsakanin ni dake nice me Ja’afar nice matarsa ta farko saboda haka shidin nawane ko kina da ja?”

Rafi’ah bataso kulata ba Amma idan ta barta haka tabbas zata siyawa kanta raini numfashi ta sauke tace “tabbas hakane kece matarsa ta farko bazaa taba canzawa tuwo suna ba saidai kinyi zuqu baki tsaya a iyakar matsayinki ba kinaso ki shiga nawa bawai Ina fada Miki bane dominsa aa Ina fada Miki ne domin ki kiyaye harshenki Ni’imah Ja’afar nawane zuciyarsa da ruhinsa dukka mallakinane domin ni aka haliccesa ki riqe wannan aranki akwai ranar da zaki maimaita dakank…..”

Katseta tayi da cewa “hhhhh taqamarki waike kinyi ciki ko lallai yarinya to bari kiji wlh sai naso zaki haifesa banza sakarya yar fashin miji kawai”….. Qit ta kashe wayar murmushi kawai Rafi’ah tayi tace “shashasha kawai” Kiran Anti Raziqa tabi tana dagawa tace “uwar hudu tun jiya nake kiranki baki dagawa saraki ne ya hanaki ko?” Murmushi tayi tace “aa a silent na sata sai yau dana danji qwari naketa bin Kira kema ya fada Miki kenan”Sun jima suna waya sukayi sallama ta sake Kiran ta Ammi itama dai murnar samun cikin tayi Mata kunya kamar ta nutse Ja’afar bashida kunya duk ya gama bazata a duniya yanzu kowa yasan meye sukayi har suka samu cikin, sosai Ammi tayi Mata nasiha akan ta qara kwantar da hankalinta su zauna lafiya da mijinta da abokiyar zamantasannan tace abbanta yana gaisheta shima jiya bayan Ja’afar ya kirashi ya fada masa ya kirata Bai sameta ba, a kunyace suka gama wayar bata qara tsinkewa da lamarin Ja’afar ba Saida wata wayar ta shigo ta daga tare da sallama jin muryar babban mutum ya amsa yasata shan jinin jikinta,

STORY CONTINUES BELOW

Gaisheshi tayi ya amsa da muryar Isa ya jima sannan ya sake jan numfashi yace “Sannu Rafi’atuh dama haka Allah yake ikonsa Allah ya rabaku lfy yabaki lfyr shayarwa da tarbiyya Allah ya tsareku da tsarewarsa jiya magaji yake fadamin na kirashi ban sameshi ba idan yazo kice nace munason takwara idan namiji ne idan macece Kuma to munason princess dinmu ta zama tayi halin uwarsu Innah saboda haka munason asa Mata Nana Hafsatu” itadai a kunyace take amsawa sosai Mai martaba yayi musu addu’a sukayi sallama Saida ya aje wayar sannan ta kashe tata cike da mamaki Ja’afar yawucce tunaninta.

Nan ta yini zaune waya ta ko Ina yimata akeyi hatta Hajiya Kaltume Saida ta kirata tayi Mata fatan alkhairi kowa a gidan murna yakeyi zasu fara samun jikan da namiji Lil Prince zaizo qasan zuciyar Kaltume baqin cikine fal duk qudurinta ya rushe idan har ta kuskura tayi saken da Ja’afar ya fara haihuwa shikenan mulki zai koma gurin Zuri’ar Fatsum sukuma sun tashi a tutar babu kenan, tashi tayi tana kaiwa da komowa tabbas dole tayi wani Abu akan Wannan lamari dole zataja Rafi’ah a jikinta ta hakane zata samu cikar burinta Ja’afar ya jima yana bata barkono ya jima yana cizon zuciyarta idan tabarshi yashata bisillah ta cutu batada hanyar ramawa saita hanyar raba tsakaninsa da Rafi’ah domin ta fahimci duk duniya babu abinda yake qauna kamarta Rafi’ah itace jarrabarsa ita kadaice zaa taba duniyarsa ta girgiza.

Murmushi tayi tace “Kulsum matanadar makirci Ja’afar lkcn daukar fansa yayi tabbas zaka gane ka tabani” mayafinta ta dauka ta fita ta shiga bangaren bayi ta Kira jakadiya tayi Mata ihsani tace Mata lallai yau tanason ganin Mai martaba, dariya jakadiya tayi tace “ai kin biya uwar dakina jeki jirani yanzu zan dawo da sakamako” murmushi Hajiya Kaltume tayi ta koma ta zauna tana karkada qafa awa daya bata cika ba saiga Jakadiya Indo tana rawa tana juyi tace.

“Anyi nasara uwar dakina ki shirya kije kawai” tafawa sukayi tace “ki jirani gobe zamu tattauna dole wannan aikin sai kin shigo ciki so nake na tarwatsawa Magaji farin cikinsa gabadaya na hanashi samun nutsuwa a duniya kamar yanda ya hanani amaryarsa tanada ciki nasan kin samu lbr don jiya yini akayi ana celebrating a gdannan zanyi duk me yuwuwa na zuge Mai martaba yasashi dawo da ita amaryar gidannan ta hakane zan samu damar janta jikina so nake nayi amfani da ita wajen ganin bayan mijinta”

Jinjina Kai Jakadiya Indo tayi tace “zaki iya uwar dakina Amma fah ance yarinyar batada sabo naji suna fada”

Murmushi Hajiya Kaltume tayi tace “babu ruwanki da rashin sabonta ki bari na gama aikina sai na baki naki kedai kiyi qoqari kiga kina nadomin abinda waccan makirar take ciki idan nasan abinda suke shiryawa shine nima zanyi amfani da hakan nayi nawa cikin sirri” Jinjina Kai Jakadiya tayi sukayi sallama ta tafi.

Itakuma ta fara shirin tafiya gurin me Mai martabaBayan ta gama komai ta hada masa zobo me dadi da sanyi ta nufi  turakarsa sai zuba qamshi takeyi ta qwanqwasa yayi Mata iso ta shiga yana zaune saman sallaya yana lazumi ta samu guri gefensa ta zauna ya dubeta ta sunkuyar dakai yayi murmushi ya ajiye carbin ya dubeta yace “Uwar gida saqonku ya ishemu dazu ta wajen su Jakadiya muna fatan dai lfy?”

Qasa tayi da kanta ta tsiyaya lemon a Kofi ta miqa Masa ya karba tayi farr da ido tace “lfy ranka ya dade kawai dai inason ganawa dakai ne saboda an kwana biyu baa zauna ba balle a shawarci juna” shanye zobon yayi yace “wannan gaskiya ne Kaltume to ai kudin ne kun fiye rigima shiyasa muka rabu daku” dariya tayi tace “to ranka ya dade ai baayi haka ba tunda Allah yabaku amanarmu ai sai kunyi hqr damu”

Murmushi yayi yace “hakane Allah ya qara Mana hqr” Hira sosai ta barke tsakaninsu inda cikin hirar ta lura duk Rabin maganarsa akan cikin da matar Magaji ta samu ne ba wani dadin hirar takeji ba Amma haka ta rinqa daurewa tana nuna masa dokinta akan cikin nandanan zuciyarsa tayi wasai saboda duk Wanda ya nuna yanason cikin jikin amaryar dannasa dadi yakeji, Nan ta samu dama tace “am dama Mai martaba nikam idan ka bani dama na kawo mana wata shawara Mana” dubanta yayi yace.

“To kaltume muna sauraronku” numfashi taja tace “duba da yanayin auren Yarannan Rafi’ah da Ja’afar da Kuma quruciya ni sai nake ganin tunda muna raye baikamata abarsu a gefe ita dashi suyi rainon cikin nan ba yakamata manya su shiga ciki domin zatafi samun kulawa ita da jikanmu dake cikinta” Jinjina Kai Mai martaba yayi yace “gaskiyane” sake qass tayi dakai tace “Me zai hana ya dawo da ita cikin gdannan idanma bazai bari taje wani bangaren cikin gidan ba tayi boffiɗonta acan ba to ta zauna a bangarensa na cikin gidannan kaga yafi kusa Kuma zatafi samun kulawa fiye da can da suke daga ita saishi dai kishiyar tata Kuma ba zaman lfy sukeyi ba kullum cikin fada suke saboda ita Ni’imah gani takeyi Rafi’ah taci amanarta to kaga ba wani kulawa zata samu ba kuma ma Koda zaman lfyr ai dukkansu yarane ba tabayi sukayi ba ita haihuwa irin wannan sammatsi gareta Allah shine me karewa saidai sa idon yanada amfani gaya”

STORY CONTINUES BELOW

Shiru Mai martaba yayi yana nazarin kalamanta can ya dago yace “kinyi tunani me kyau zamu duba sosai” da wannan suka shiga tattaunawa akan abinda ya shafi cikin gida tana qara tura Masa ra’ayin dawo da Rafi’ah cikin gdan.

Bangare Ni’imah kuwa tunda ta samu lbrn tabbatar cikin Rafi’ah ta tashi hankalinta ita da uwarta da surukarta babu dare babu Rana suna yason bin bokaye duk bokaye sun kasa sama musu mafita sai guda dayane yayi hobbasan yi musu alqawarin yiwa Ja’afar din kiranye ya dawo gida idan har ya dawo zai sauka a bangaren Ni’imah to duk abinda ta bashi zaici wannan karon ba asiri zasuyi ba tsafi ne Amma sai Ni’imah ta yarda an zuqi jininta zaa hada laqani dashi.

Wa’iyazubillah Allah kayi mana tsari da shirka,  aikuwa haka tabada hannunta bokan na dutsen shadan ya zuqi jininta ya hada da wani qarin magani yace taje tayi turaren gabanta dashi ta tabbatar ya kusanceta to daga haka ksda ta qara komai zataga zuwan da zowar Amma kafin turaren ta gauraya ruwan rubutun daya Bata da abinci ko lemo ta bawa Ja’afar din yaci.

                      *_MEXICO_*

Yau laraba ce a Maxico 21/3/ wanda yayi daidai da watannin uku a Mexico suna parlour a zube tana kwance saman jikinsa yana shafa cikinta da ya dan fara dago mararta yanajin dadi sosai Wai shima ya kusa zama Dad  murmushi yayi yanajin qauna da tausayinta yanda cikin nasa ke wahalar da ita yace “ina tausaya Miki Bestie babie na yana wahalar dake over” lumshe idonta tayi tace “ni baka wani tausayina bayan baka dagamin qafa”

Rufe Mata baki yayi ya dagata ya shiga da ita ciki yace “ok haka kikace” Nan fa suka rinqa kokawa daqyar yakaita kasa yaja musu bargo yana Mata dariya yace “sabida Kinga jiya na qyaleki shine kika samu bakin mgn” da turje turjen da komai ya rabata da komai sukayi komai ta miqe tana mita ta shiga bathroom tayi wanka shikuma bacci ya daukeshi bayan ta fito ta sanya kayanta itama ta kwanta ta fara bacci taji ya zabura ya miqe da sauri itama miqewa tayi taganshi riqe da kansa yana furta “a’uzubillahi minasshaidanur’rajim” jikinsa yana rawa duk gashin jikinsa sun miqe riqo hannunsa tayi tace “fatan lfy mijina” wani gwauron numfashi yaja ya zuba Mata idonsa da sukayi ja saboda bacci.

Baice komai ba ya miqe ya fada bathroom yayo wanka ya fito ya zura kayansa ya zauna kusa da ita yace “kinci abinci?” Dagansa Kai tayi ya Jinjina ya miqe yace “zan Dan fita ki kula da kanki kafin na dawo” itadai batace masa qala ba har ya fice ta sake kwanciya kanta ciwo yake ita dsma a laulayin ciwon Kai da amai sune sukafi komi damunta, baccinta tayi sosai sai yamma liqis ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wasu fitinánnun qananun kaya tayi kyau sosai duk da ramar da tayi ta dawo parlour ta hada madara da Zuma tanasha tana kallo.

Wayarta tayi ring ta daga suka gaisa Hajiya Innah ce take tambayarta jiki ta amsa Mata suka dan taba hira sukayi sallama, tananan zaune zaman jiran tsammani Bai shigo ba har saida tayi sallar Isha ta sake kwanciya waje 12:30am ya shigo ganin tana bacci yasashi bai tasheta ba tausayi sosai take bashi abinci kawai yaci ya kwanta shima ya janyota ta bude idonta yace “sorry uwar yayana na dade ko?”

Lbr ya fara bata yace “yau na gama komai daya kawoni qasarnan harma naje nayi mana duk abinda ya dace May be Nan da 1 week mu tashi zuwa gida am jiya Mai martaba ya kirani yake fadamin idan mun dawo Kai tsaye na kawoki nan gdan sarauta Zaki zauna a bangaren Hajiya Innah harsai kin haihu so nadai nemi alfarmar yabarki ki zauna a bangarena Amma bazan iya barikin ki zauna a bangaren matan gida ba”

Hakanan tunda ya fara bata lbrn taji gabanta na faduwa taso tayi masa garda sai taga rashin dacewar hakan kawai tayi shiru Amma ranta bai kwanta da komawarta gidan sarautar ba” kwanaki uku ya gamayi musu shirye shirye ta lura da gaske zumudin tafiyar yakeyi itadai batako kulashi tunda babu wani Abu daya fasayi Mata kulawar da yake bata Bai fasa ba sai kawai mayar da hankalinta akan kula da lfyrta.

Ranar da satin kuwa ya zagayo ranar tafiyarsu ta tashi da azababben zazzabi sosai da ciwon Kai ganin yanda yaketa rawar jiki yasa ta boye Masa ciwon nata ta shirya suka fito drivern hotel sinne yakaisu airport suka dago sai Abuja shigar talatainin dare sukayi saboda haka a hotel suka kwana da safe bayan sun karya suka fito shatar mota suka dauka har Bauchi.

Daya a Azare tayi musu shine ya dauki kayansu ya shiga dasu cikin bangarenta da yake ya fadawa Hajiya Innah dawowar tasu tasa an gyara musu bangarensu na gidan sarautar to Nan dinma an dan gyarashi saboda tasan qila shigowar dare zasuyi da addu’a ta sauko a motar saboda tsanantar faduwar gabanta tafi fitowa taji wani jiri ya debeta daidai qofar shiga parlournta ta saki qara ji kake yif ta zube a qasa sumammiya jiyo ihunta yasashi sakin jakar daya shiga da ita a guje yayi waje a kwance ya isheta cikin wani mawuyacin hali jini sai kwarara yakeyi ta qasanta,

STORY CONTINUES BELOW

Isa yayi da gudu ya dagota yana jijjigata yana Kiran sunanta daidai lkcn Ni’imah ta leqo daga sama ta hangesu gabanta ne ya fadi ta sauko da sauri ta iso ganin yanda ya gigice yasata zagayowa ganin jinin da yake zuba a qasan Rafi’ah yasata sakin ihun kirsa tace “meye hakan Ja’afar ka kaita asibiti Mana jini fah take zubarwa”

Sai lkcn ya iya miqewa ya sureta yasata a mota yana tuqin gabansa na faduwa ganin yanda jinin ke malala har lkcn suna shiga ya dauketa suka shiga ciki likitoci suka rufu akanta suna iyakar qoqarinsu sun jima basuga tashin hankali irin wannan ba jinin yaqi tsayawa da sun tsaidashi sai wani ya tsinke  gashi cikin yaqi fita sunyi sunyi su cireshi ma ko zasu samu jinin ya tsaya yaqi abun fah ya zama tashin hankali daga kawotan sunsa Mata jini leda uku, Basu suka samu jinin ya tsaya ba sai wajen shidda na yamma Allah ya taimakesu ya tsaya scaining sukayi Mata abin mamaki cikin yananan qalau dashi Ja’afar ya sauke ajiyar zuciya gabadaya yayi faca² da jini yayiwa Allah gdy da babu abinda ya samu cikinsa yasan wannan kariyar ubangiji ce kawai.

Hajiya Innah ya Kira ya fada mata halin da suke ciki itace tazo asibitin sannan ya samu ya tafi gda yana zuwa ya tarar da Hajiya Fatsum da Ni’imah a parlour sai dariya sukeyi yana shigowa kowacce ta shiga hankalinta Hajiya Fatsum ce tayi saurin cewa “ya me jikin yanzu nazo nake jiran Ni’imah tazo mine mu gano jikin” dadi yaji a ransa yadanyi ajiyar zuciya yace “alhmdllh Allah ya taqaita cikin Bai fita ba Anna tasha wahala Saida akasa Mata jini leda biyar iya yau….”

Miqewa tayi daga zaman da take tace “bai fitaba fah kace ya akayi ya tsaya naji ance faduwa tayi ruf da ciki Kuma ance jinine ya balle Mata” Jinjina kai yayi yace “eh haka Allah yaso” saurin saita nutsuwarta tayi tayi murmushin yaqe tace “to ai gara haka” hayewa yayi sama ya tarar dashi yanda ya tafi ya barshi takaici ya cikashi ya sauko ya fice ya nufi bangaren Rafi’ah anan yayi wanka ya canza kaya ya fito ya sake komawa yanzu ita kadaice ta rafsa uban tagumi ya jima akanta sannan taji shigowarsa tayi firgigit ta dawo hayyacinta tare da miqewa tace “ya me jikin?”

Zama yayi yace “da sauqi inajin yunwa” murna ce ta kamata ta miqe ta shiga kitchen ta hado masa abincin da suka cakuda da magunguna ta kawo masa ya sauko qasa ya bude qamshin abincin baiyi masa ba Amma yunwa yakeji ta gaske haka ya rinqa tsakura yanaci kamar dole daqyar ya iya cokali shidda ya ajiye ya tsiyayi lemon juice  yasha badon ya qoshi ba saidon bazai iyacin na arziqi ba qarni yaji abincin yanayi da alamun naman da akasa Bai samu gyara ba.

Dan kishingida yayi yana latsa wayarsa nan danan bacci ya daukeshi hakan yabata damar miqewa ta kunna garwashi tayi turaren da aka bata sannan ta sake zuba wani da akace tayi masa akansa idan ya shaqa nagana ta qare haka kuwa akayi cikin saa ta gama komai ta feshe parlourn d room freshner ta koma ya harde, ya jima yana baccin asara har akayi Isha sannan ya farka da salati yaji kansa ya Sara masa kamar irin sarawar da yayi masa ranar da yaji yanason dawowa 9ja.

Bude idonsa yayi ya zubawa Ni’imah data hade cikin wani less me tsadar gaske ba wata kwalliya tayi ba Amma sai ya rinqa ganin tana wani glowing miqewa yayi yanaci gaba da kallonta yana sauke ajiyar zuciya sama ya haura sabanin dazu yanzun ta gyarashi yayi murmushi yana Shirin shiga bathroom ta bude qofar da sauri saboda tuna cewa bokan shandan yace idan ta kuskura yayi sallah bayan yaci abincin kafin ya kwanta da ita to komai zai lalace ya juye kanta,

Zubanta ido yayi babu kunya ta matsa jikinsa tana matso hawayen kissa tace “ka dawo inason ganinka da jin duminka matarka ta Kama rashin lfy kun Kuma fita yanzun Kuma shine zaka shareni Ja’afar kana azabtar dani don kaga inasonka don Allah kada kasa zuciyata ta kamu da ciwon da zai iya zama ajalin me ita duk saboda so kake wulaqantani bakajin tausayina….”

Yanda take shigewa jikinsa da qamshin turaren tsafinta yasashi jin wani yanayin sha’awa me qarfi da baitaba jiba game da ita ya sanya hannu ya rungume shafaffun mazaunanta yana shafasu yana sauke ajiyar zuciya a hankali yau dake makirci ta shirya itace harda balle masa bottle din riga abinda akansa Saida afasa kwanciyar da ita a baya idan yace ta cire masa kaya gani takeyi ta fado yau sai gashi tanayi baisata.

Hakan ya tabbatar masa da ta fara nutsuwa ya jata suka zube a gadon sosai ko a wajen playing yasan zaren ba kalar yadin bane Rafi’ah dabance ko a rashin sani ta tabashi sai yaji saqon yakai masa har inda yakeso yaje Amma ita ta wani kwanta tayi masa seqeqe sai breast dinta kawai da take tattaro Masa dake irin manyan boobs dinnan gareta hakan yasa bata haihuba amma sun zube sabanin na Rafi’ah da kullum kamar qara tsaidasu akeyi.

Lkcn daya shigeta ne abubuwa suka rinqa canzawa shi ba dadi take wani samu na musamman ba saboda itan ko maganin Mata bata iya kadawa Tasha ba sai aukin turaren asiri Amma sai yaji yanajin wani shauqi hakadai sukayi suka gama tun kafin su gama ta fara tureshi sabanin Rafi’ah da take qara riqeshi tana dago jikinta sosai yanda zai samu nutsuwa,

Ranar tare sukayi wanka yanata rawar jiki akanta ta cika da mamakin aikin boka Koda yayi sallah cewa yayi ta shirya suje su dubo Rafi’ah batayi musu ba saboda tanason ganin qwal uwar daka fita sukayi anata yauqi da yatsina ita me miji aka shiga mota suka nufi asibitin yana riqe da hannunta suka tura qofar dakin suka shiga,

Lkcn Rafi’ah ta tashi Hajiya Innah ta hada Mata shayi tana Bata suka shigo ta dago kanta idanunta ya fada kansu babu kunyar Hajiya Innah Ni’imah qara shigesa takeyi wai ita me miji shikuma sai wani binta yake murmushi Rafi’ah tayi cikin sanyin muryarta tace “sannunku da zuwa Best Ashe tafiya kayi dazun dana farka nake tambayar Innah kana Ina….” Kafin ta rufe baki ya taso da bala’i “to zama kikeso nayi nayi gadinki saboda ga asararre mara aikinyi hakanma banyi Miki ba dana Nemo Innah ta zauna a gurinki ke wacce irin mara tunani ce daga dawowarmu kin fara cuta saboda kinibibi kada na samu lkcn iyali na ke nifa baayimin iskanci kinsan cin mutuncinki ba wahala zaimin ba ba ciki ba ko bayane dake shashasha kawai

_____________________________

Juyawa yayi fuuuu ya fice a fusace sai huci yakeyi inda suka kalli juna da Ni’imah Ni’imah tayi Mata murmushin mugunta tabi bayansa da sauri a jikin mota ta tarar dashi yanata huci ya bude Mata ta shiga shima ya shiga yaja suka fice daga asibitin sukabae Rafi’ah da sanyin jiki da faduwar gaba, sunan Allah ta rinqa ambato a hankali taji Hajiya Innah ta dafata tace.

“Ina mamakin zafin zuciyar Baban Innah shi komai nashi na fada ne ko meye abin bacin rai cikin kalaman ki sai naga kulawa ce da nuna damuwa da abokin rayuwa tasa kika damu da rashin nasa a kusa Koda yake wani abun sai anayiwa rayuwa uzuri kiyi hqr iya wuya kedin dai kece”

Sosai ta rinqa rarrashinta murmushi tayi tace “karki damu Hajiya nasan halinsa yanzu haka wani abun ne ya bata masa rai nasan fushinsa baya jimawa zuwa anjima zai sauko” ajiyar zuciya Hajiya Innah tayi sukaci gaba da tattaunawa saida tasan yanda tayi taga Rafi’ah batabar damuwar abin a ranta ba ranar a asibitin suka kwana saboda jinin da akasa Mata da magrib bai qare ba sai cikin dare.

+

Washegari har Tara baizoba aka sallamesu Hajiya Innah ta dauki waya ta kirasa ya daga suka gaisa ya tambayeta me jiki tace “da sauqi dama sàllamarmu akayi shine mukace ko zakazo ka daukemu” Shiru yayi na dan lkc sannan ya dago yace “aa Hajiya kawai bari na turo driver yazo ya daukeku ku wucce can fada kawai ni na danje unguwa ne idan na dawo zanzo” bataja mgnr ba ta kashe wayar ta miqe ta fara hada kayan lkcn da drivern yazo ta gama hadawa suka fita suka tafi suna Isa yana shigowa gidan ya tsaya jikin motarsa suka fito duk munafukai suna jira suka abinda zai faru qarasowa yayi ya rusuna suka gaisa da Hajiya Innah ya dago ya zuba idonsa akanta tayi wani haske ta qara ramewa yaja numfashi ya dubeta yace “ya jikin naki?”

Sunkuyar da Kai tayi tace “da sauqi” fasali ya sake ja yace ”nasa an qara gyara can bangaren muje na rakaki” kallon Hajiya Innah tayi idonta ya ciko da ruwa tayi saurin girgiza Mata Kai dole tasa ta hadiye kukan, taimako daya da Allah yayi mata tsakaninsu da Hajiya Innah babu nisa hakan tasa suka taka da qafa ya bude qofar shiga part din ya shiga itama ta shiga da Bismillah tana qarewa bangaren kallo tun daga waje zakasan ya kashe mazan kudi wajen gyarashi.

Yana tafe tana biye dashi a baya har suka shiga ya bude qofar parlourn ya shiga itama ta shiga ya mayar da qofar ya rufe ya juyo ya zubanta ido itanma shi take kallo fuskarsa a daure take sosai hakan ya tabbatar mata da babu wargi, rabashi tayi zata wucce ya riqo hannunta ta tsaya cik matsowa yayi ya riqo qugunta yana jan numfashi ya matsota sosai yace “meye yake damunki ne?” Dagowa tayi da mamaki so take tayi mgn Saidai yanda ya kafeta da ido yasa ta kasa furta komai sakinta yayi ya sanya hannu a aljihunsa ya zaro kudi masu kauri ya miqa mata yace “ki riqe saboda tsaro ki kula da kanki”

Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo yaja Mata qofar ya rufe itakuma ta taka taje ta murda Mata key ta nufi step din shiga dakin ba bene bane Amma an daga dakunan sun danyi sama sabanin babban parlourn da take a qasa nan din ma akwai parlour Amma baida girma sosai kujera daya ce doguwa sai wani qaton kilishi 24 pillow sai TV da dispenser sai manyan flowers da aka qara qawata parlourn dashi gefe Kuma akwai qaramin dinning table me kujera biyu.

Tsarin wannan parlour yayiwa Rafi’ah tayi ajiyar zuciya ta bude daki daki daya ta shiga shima an gyarashi sosai gadone na alfarma aka saka komai yaji taja fasali ta zube kudin daya Bata ta fara rage kayanta ta fada wanka ta jima tana wankan tanajin dadin ruwan kafin ta fito ta shafa mai ta bude wardrobe din kayanta ne jere reras ta dauko wasu masu sauqin nauyi tasa ta kwanta tana hutawa ta Jima a kwance tana tunanin abubuwa da yawa sannan taji ana taba qofar ta miqe a gajiye ta fito parlourn tana tambayar waye.

STORY CONTINUES BELOW

Amsa Mata akayi da cewa “nice Rafi’ah Ashe kun dawo to sannu kinji” jin an ambaci sunanta yasata budewa batasanta a zahiri ba domin bata taba ganinta ba ko lkcn da aka kaita bangaren fuskarta a rufe take, Hajiya Kaltume ce ta kawar da shirun da shiga parlourn tace “tubarkallah Masha Allah guri yayi kyau to ai haka yafi Amma da duk ya debeku ya tareku guri guda don shirme musamman ma ke da kike buqatar kulawa yanzu sannu kinji”

Sunkuyar dakai tayi ta durqushe da niyyar gaisheta tayi saurin Dagota da cewa “subhanallah kula kada kiyi barna haba yarnan keda ba lfy ta isheki ba ai bakya tsugunna ba zauna abinki ni uwarki ce banason ki takurawa kanki da jikana” tana mgnr tana zaunar da ita a kujera tace “to ya jikin jiya munji mugun labari Koda yake Allah ya taqaita wahala

A kunyace ta amsa Hajiya Kursum ta rinqa janta da Hira harda guzurin agwalumarta ta kawo Mata ta miqa Mata tace “kinsan abinki da me wannan Abu da son tsami tsami shiyasa na bayar aka siyo miki” kamar tayiwa Rafi’ah kyautar aljanna haka taji sukayita yar hirarsu tanata nuna kulawarta tare da bata shawarwari kamar gaske, shigowar Hajiya Innah ne yasata miqewa suka kalli juna Hajiya Kaltume ta harari Hajiya Innah tace “to Rafi’ah ki kula da kanki kinsan gdan namu gidan yawa bakasan cikin wani biyune ba saiya lashe maka kurwa” itadai bata tanka ba Hajiya Innah ta zauna tace “Allah ya kyauta” Shiru ce ta dan ratsa kafin Hajiya Innah ta bude kular da tazo da ita tace “dambu nayi Miki da fatan yakuwa ko Zaki iyaci naga duk kin fige wannan jika yana wahalarmin dake”

Kunyace ta kamata tayi murmushi tace “bantaba ganin yar da take kunyar uwata ba saike tashi kici abinci” xuba Mata tayi ta zage taci dambun sosai don ta dade tanason sa tunda ta samu ciki dashi da tuwo bata taba daina kwadayinsu ba sosai taci sauran ta ajiye tace taci da dare a kalamai baa bayyane ba Hajiya Innah take nunawa Rafi’ah tayi hankali da mutanen gdan fada gidan makirci ne kowa da abinda yake zuciyarsa, sosai ta shiga taitayinta ta qara Mata da cewa idan kadaici ya dameta tana gama abinda take ta taho bangarenta, Jinjina Kai tayi ta qara da cewa mutane da yawa sunayi maka dariya Amma basa qaunarka munafikinka yafi maqiyinka illa domin maqiyi baya zama kusa dakai balle ya samu damar cutar dakai Koda kuwa zai cuta maka saidai yabi ta gurin munafikinka da hausawa kance gadon bacciñka so kibi a sannu dariya ba so bace wata dariyar tafi sukar wuqa ciwo”

Maganganun sun shigeta ta nutsu kuwa tana nazarinsu lkcn da sukayi sallama tace “ki kulle bangarenki kiyi kwanciyarki ki huta surukarki batanan tace Damagaran balle kice zakije gaisheta” tana fita ta kulle part din ta shiga kitchen ta ajiye kayan abincin ta dawo ta dan gyara gurin data zauna

Sake Shirin kwanciya tayi tabi lfyr gado ta kwanta tana dan chat dinta bacci taji ya fara sumamarta yasata miqewa ta dauro alwala ta dawo ta sake kwanciya tare da qarawa a.c qarfi bacci ya dauketa cike da kewar mijinta ko a waya bai nemeta ba ita Kuma yanayinsa yasa ta dan tsorata ta kasa kiransa da wannan tunanin tayi bacci wajen biyun dare ta farka ta sauka a gadon ta nufi bathroom ta dauro alwala wannan sabonta ne tun batasan kanta ba Amminta ta sabar Mata da tashin tsakiyar dare ko bata sallah saita tashi tayi alwala tayi tulawar qur’ani tare da istigfari hadi da addu’o’in da suka sauwaqa harma jikinta ya saba da zaran lkcn yayi saita tashi.

Ta Jima tana jero nafilfilinta sannan ta shiga jerawa Allah kirari tare da neman albarkar aurenta da zuri’a ta gari tare da roqa musu dawwamar zaman lfy da fahimtar juna ta dade sosai tanawa mijin nasu addu’ar samun budi da kariyar Ubangiji a duk inda yake.

Bata koma ta kwanta ba Saida aka Kira asuba nanma tayi ta Jima tana azkar hakanan sai ta rinqajin gabanta yana faduwa ta roqi Allah ya sassauta Mata duk wani Abu da yake tunkarota yabata wuyan dauka tare da addu’ar kada Allah ya bata ikon juyawa mijinta baya a kowanne hali, saida Rana ta fito sannan ta kwanta takuwa Jima tana bacci ba ita ta tashi ba sai 12:00pm wanka tayi ta shirya cikin wata baqar doguwar riga ta zura hijjab dinta qato sannan ta dauki wayarta har yanzu gabanta faduwa yakeyi tayi Bismillah ta Kira lambar JM Kira daya ya daga muryarsa wasai yace.

“Maman Twins kin tashi lfy?” Murmushi tayi ta sanyaya muryarta tace “har naji sanyin dadi ya ratsa zuciyata dana tabbatar da cewa Daddyn twins ya tashi lfy” dariya yayi ya dubi Ni’imah da ta wani hade rai yace “tun jiya zuciyata tana gurinku keda BBY na yar’uwarki ta riqeni ta hanani zuwa naganku” abinka da kishi da bashi da kadan sai taji zuciyarta ta sosu dake tana da wayo sai tayi murmushinta da tasan yana kashe Masa jiki tace.

STORY CONTINUES BELOW

“Allah Sarki mijina nasan muna qasan ruhinka kada ka damu kabata lkc sosai ai ta cancanta am dama nace idan babu damuwa inason shiga cikin gida mu gaisa jiya duk sun shigo harda Hajiya Babba” gabansa ne ya fadi yace “hajiya babba kuma? Me tace Miki?” Ajiyar zuciya tayi tace “babu komai kawai dai ta kawomin agwaluma ne Best Kai dan gatane kowa tattalin unborn dinka yakeyi”

Ajiyar  numfashi yayi yace “ok kije Amma ki kula da kanki nifa don Mai martaba ya dage ne hankalina bai kwanta da zamanki a gidannan ba Rafi’atuh zuciyata taqi nutsuwa” fasali taja ita kanta bataji tata zuciyar ta yarda ba Amma saboda burinta kullum qarfafa masa gwiwa sai tace “karka damu insha Allahu zamu kasance cikin tsaro da kariyar Ubangiji” wani gwauron numfashi yaja yace “banajinki Amma ki jirani ganinan zanzo saina rakaki ko Ina”

Yana fadin haka ya miqe ya fice yabar Ni’imah da sakakken baki cike da mamaki  mota ya shiga zuciyarsa na ayyana Masa abubuwa da yawa game da Rafi’ah yana murmushi gabadaya jinsa yake kamar Wanda ya rasa wani bangare na jikinsa iyakar kwana biyu da yayi ba tare da ita ba musamman daren jiya daya kasa rintsawa tunda yake baitabajin irin yanayin daya kasance jiyan ba wani bangare na zuciyarsa yayi masa nauyi yanajin wani Abu daya kasa tantancewa idan ya rufe idonsa Rafi’ansa yake hangowa cikin wani yanayi na tashin hankali hakanan zai zabura ya miqe ya sake kwanciya sai ya ganta dauke da wani kyakkyawan farin yaro me kama dashi cikin  wata rijiya me zurfi ga wani duhu yana mamaye rijiyar tun yana jiyo ihunsu da salatinta tana Kiran sunansa har yakar da yadaina ganinsu da jinsu gashi an Tara mutane anyi anyi à daukosu ankasa shikuma sai hanqoron binsu yakeyi Hajiya Fatsum da Ni’imah sun daddaure shi wani abin haushi ya kasa qwacewa sai hanqoro yake da ihu Amma ya kasa samun mafita

Can nesa ya hango Hajiya Kaltume ta nufo rijiyar gadan² da wani ice yanaci da wuta ta cilla a ciki inda kafin ya dira qasa ita Kuma Hajiya Innah tayi tsalle ta fada rijiyar ta cafo itacen tayo sama dashi ta jefi sarqar da aka daureshi da ita take sarqar ta tsinke ya kwace da gudu ya nufi rijiyar….. A daidai nan ya farka yayo alwala ya tada sallah domin mafarkin ya tsoratashi firgigit yayi saboda horn din da yaji anata doka Masa dubawa yayi yaga ashe tsayawa yayi a tsakiyar titi numfashi ya sauke yaja motar ya qara gaba.

Shiga fadar sarkin qofar bangaren nasa ya bude Masa ya shiga yayi parking ya bude motar ya fito taka qafar da zaiyi yaji kansa ya sara gabansa ya yanke ya fadi take yaji zuciyarsa tana tafasa “ Innanillahi wa innah ilaihirraji’un” ya rinqa karantawa har ya murda qofar ya shiga ko Ina na gdan qamshi yakeyi yanason Rafi’ah komai da yakeso a cikin watanni hudun ta gama karanceshi tsaf baiji fitowarta ba saiji yayi ta rungumeshi ta baya tana yar qaramar dariyarta me sanyashi nutsuwa tace “Ur are welcome My life….” Ajiyar zuciya yayi yana shaqar qamshinta ya juyota yayi kissing kumatunta yace “inasonki fatan kina lfy” qasa tayi da kanta tace “ina lfy kamar Kai” kalmar ta bashi dariya yace “haba yarinya da wannan dumar da ta fara girma a tumbinki zakiyi lfy kamar tawa?”

Dagansa Kai tayi tana shafa mararsa yanajin wani irin yanayi ta dago ta dubeshi ya wani lumshe ido tace “zuciyar Rafi’ah da alama kanajin yunwa me kakeson ci na sama maka banson zaman gwarzon maza da yunw….” Bata qarasa ba ya hade bakinsu guri daya suka zube a kujera tasan yau ta ballowa kanta ruwa da alamun dama kadan yake jira daqyar ta qwaci kanta shima Saida ya samu nutsuwa tayi luf a jikinsa son mijinta takeji a hankali yana mamaye duk wani gurbi na qiyayyarsa na baya Ashe takusa ta cuci kanta da ta yarda son farin cikin wata ya hanata karbar nata farin cikin.

Dagota yayi yace “me kike tunani?” Murmushi tayi tace “son mijina nake fasaltawa a zuciyata nakasa gane yanayin girmansa da matsayinsa na yarda na mutu dakai mijina kaifa?”  Farin cikine ya cika masa ruhi ya rungumeta yace “na dade da yarda da hakan Rafi’ah tun kafin kisoni nasoki Kuma zan mutu da soyayyarki” luf tayi a jikinsa sun jima a haka Bai zaci zata sake magana ba yaji tace “kayimin uzuri a duk lkcn da na bata maka mijina bazan taba furta ko aikata abinda zai taba farin cikinka a halin Ina sani ba” sanyi jikinsa yayi ya sunsuna sumarta yace “Insha Allah” miqewa tayi tana takansa rawa yayi murmushi komanta dabanne ya dagata cak suka shiga ciki wanka yayi ita ta qara gyara jikinta ya fito ya canza kaya suka fita bangaren Hajiya kaltume suka shiga tana parlon tana ganinsu ta miqe tana washe baki tace “tun dazu naso zuwa naga lfyrki Dije tace baki tashi ba to sannu kinji yarnan Magaji meyesa baka kirani nazo mun gaisa ba me ciki batason yawo balle ita da ba lfy ce ta isheta ba” dadi yaji sosai a ransa ya zauna yace “hakane Hajiya shima motsa jikin yana da amfani” zama tayi suka gaisa ta miqe tace “bari na kawo miki wani Abu nasan jikalle na zai soshi”

Kitchen ta shiga bata jima ba ta fito dauke da wata kula ta bude wata lafiyayyiyar gurasa ce ta alkama da aka mulketa da Zuma sai kunun tsamiya sai zuba qamshi yakeyi” kwantar da kanta tayi a jikinsa ya dago kanta yaga yanda take hadiyar yawu sukayi dariya shida Hajiya Kaltume yace “ta koma kamar mayya komai tagani tanaso tunda mukaje Mexico take sani barnar kudi a Rana sai tace tanason abu kusan kala talatin”

Zaro ido tayi sukayi dari dukansu Hajiya Kaltume ta kirawo Jakadiya Indo tace “ki dauki wannan kayan ki kai bangaren magaji” gdy Rafi’ah tayi Hajiya Kaltume tayi murmushi tace “Ah haba babu komai ai dole mu kula dake haqqi ne akanmu am don Allah Ja’afar duk abinda ya faru baya a manta dashi ya wucce har abada Rafi’ah duk abinda kikeso ki aiko a karba Miki bani da wani amfani sai hidimarku”

Jinjina Kai Ja’afar yayi yanajin dadi a ransa idan aka nuna anason Rafi’ah da cikin jikinta ji yàke kamar yayiwa mutum kyautar duniya, miqewa yayi ya kamo hannunta yace “bari mu qarasa ciki mun gode da kulawa” fita sukayi tanata zubawa Rafi’ah sannu” suna fita ta kwashe da dariya tace “zakuci ubanku waikai ne Mata ita Kuma me ciki har wani godiya kakemin kamar ka mantani nice dai Ummu kursumu yar mage baki dadin goyo sai baqin naci har wani proud akeyi Wai batada sabo tunda ta samu kwadayayyen ciki ai dole ta saba dani zan shekara yi Mata hidima domin Rana daya tak yahudu tuba babu hhhhhhhh” ta qara kwashewa da dariya.

Bangaren Hajiya Innah suka shiga anan ya tafi yabarta saboda Hajiya Fatsum batanan anan ta kusan yini ita da Karimah qanwarsa yar wajen Hajiya Innah sunata hirarsu dake dama basufi sa’anni ba sai yammaci ta tafi bangarenta ta shiga hadimai sai hidimarsu sukeyi tayi wanka ta baje a qaramin parlour Dija ta kawo Mata kunun da gurasar tayi Bismillah taci tayi hani’an sauran tasa a freegde tayi alwala tayi sallar magrib ta kunna kallo anan yazo ya isheta shima yabiyeta sunata hirarsu abin da yakebashi tsoro da mamaki idan baya tare da ita sai kewa da tunaninta ya damesa Amma idan yazo sai ysji duk ya gundura duk wani motsi da zatayi maimakon birgeshi da yakeyi da yanzu haushi yake bashi,

Sai darema da sukaje kwanciya yini yayi yana feeling nata Amma yanzu sai yaji duk haushinta yakeji gashi shi baiga wani laifi da tayi masa ba balle yayi fada yaji dadi duk wani Abu da tasan zai sanyashi farin ciki shi takeyi, itakam batajin komai a ranta kawai dai yanayinss ne yake bata mamaki sai ya kwanta ya tashi ya sake kwanciya ya tashi Saida yayi haka sau uku tanajinsa batace komai ba taji ya miqe itama saita tashi ta rungume pillow a qirjinta yakai ya kawoya tsaya a gabanta yace “na rass meye yake damuna wani haushinki nakeji Rafi’ah Kuma wlh bakiyi min komai ba” Allah sarki sai kawai tayi murmushi ta miqe ta dauki qur’ani ta dawo ta rusuna ta miqa Masa yasa hannu ya karba tace “a duk lkcn da najini a irin wannan yanayin nakan bar duniya da abinda yake cikinta ta na koma ga Allah ta hanyar ambaton sunayensa tsarkaka da Kuma karanta zancensa me dadi da sawa zuciya haske mijina kaima kayi haka nasan zakaji sauqin abinda kakeji….”

Ajiye qur’ani yayi ya matso gabanta yana huci kamar wacce ta zagi uwarsa ya dago kanta kawai saiji tayi  dauketa da Mari ya hankadata a gado ya hau bala’i yana cewa “wato saboda kin rainani harni zaki fadawa yanda zanyi idan Ina cikin yanayi ai ba duniya ce tayimin zafi ba kece kikayimin Kuma wama yace Miki banayin karatun qur’ani ko yau da asuba saida nayi nifa banson kirsa waike ta Allah to fadamin wanda yake bautar ubanki…” Fuuuu ya fice daga dakin yana cewa haba nima da jarabata in Banda qaddara ma mezanyi dake nifa baa hakicceni domin wahala ba ke kika rasa ba yar iskar da zata doramin hawan ruwa sakarya kawai” miqewa tayi da sauri ta leqa ta window jin tashin motarsa agogo ta duba 1:49am kawai saita dora hannu a ka ta rushe da kuka ita ba cin mutuncin ne ya bata Mata raiba aa fitarsa a wannan lkcn gashi gda basu kadai ba kowa da abinda zai fassara ta jima tana kuka ganin bazai kaita ba ta tashi tayi alwala ita ta rungumi qur’anin da aka mareta dominshi tana karatun tana hawaye tunda take baa taba wulaqantata irin wannan wulaqancin ba harda zagin ubanta wai JM da bakinsa yake ce Mata yar iska, sake rushewa tayi da kuka tare da daukar wayarta ta fara kiransa Kira daya tayi masa ya daga shassheqar kukanta yasashi saurin cewa “kinga don Allah kiyi Shiru wlh bazan iya kwana a gidannan ba zuciyata tafasa takeyi kaina kamar zai tarwatse Rafi’ah bansan meye yake damuna ba na kasa jurewa idan na cika takurawa cutuwa zanyi”……..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *