NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 2 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Kasance da www.bankinhausanovels.com.ng
JIYA MUN TSAYA
“Ki bar Sani ya cigaba da amfana da furta Kalmar yana sona yana cika wani abu daga burinsa, ni kuma ya cigaba da tattaro cinikin markadensa yana ba ni tukwicin so, in aka hana masa wannan an tauye hakkinsa da yawa tunda ba zai iya tara kudin aurena ba, bai kamata a hana shi furta abinda yake ji game da ni a kirjinsa ba” , Cikin dariya Amina ta ce, “Ba ki da mutunci Husna” Ita ma tana dariyar ta amsa,
“Ba rashin mutunci ba ne, sauqin kai ne da iya zama da mutane. Sai dai hakan ba ya hana ni kokarin cimma burina, ba zan auri mara ‘ sana’a ba kuma ba zan auri mai Karamar sana’a ba
ZAMU TASHI
ban taba tunanin yin auren soyayya ba ni auren kudi kawai zan yi’’
Adamu ya dinga yarfe gumi a saye ba tare da lurar kowa ba. Macen da yake so sunanta Husna, yau ga shi zaune kusa da ita da tazarar da bata kai takun da za’a tsaya Kirga ba, sannan tayi magana, maganar da za’a iya gane alkiblarta da inda ta dosa har Karshen rayuwa. In babu irin son da yake mata lallai akwai aibu cikin maganganunta, sai dai shi mai rufaffen ido asO ya mayar da aibun nata yabo, sai ya mayar da dukkan aibun kansa da kan yayansa wanda shi ne bai so Husna ta gan shi a layin mazan da zata iya aure ba. ~
Rauni a zuciyarsa yanzu shin yaya zai yi da son da yake mata? Da ya laluba zuciyarsa ya tabbatar son ba irin wanda ake iya yafewa bane, saboda haka ina za shi ya samo kudin da zata aure shi don su? :
A kwanakin da suka gabata burinsa daya ne, shi ne Husna amma a yau ya Kara na biyu, shi ne kudin da zai farantawa Husna.
Bat san hakikanin abinda yake wanzuwa a kantin ba tsawon wani lokaci har sai da Husna
Www.bankinhausanovels.com.ng
‘ta farkar da shi da zazzakar muryarta cikin yanayin barkwanci,
“Ranka ya dade za mu wuce, da fatan zaka yafe wa telan da ya tauye maka mudun, in kuma ba zai yafu ba ka je ka kawo rigar na daura maka maballin a madadinsa”.
Ya dage iyakar dagiya ya wurga damuwarsa can bangon zuciyarsa, ya dago da murmushin yake,
Yace An yafe masa”
Yayi saurin kawar da kai saboda zaton dakewarsa ba ta cika mizanin da zata boye damuwarsa da rikitarsa ba. Yaji wani Kwarin gwiwa da kyau lokacin da cikin dariya Husna ta amsa masa, da
“To madalla da karimi mai kyautar yafiya” Bai shirya ba ya sami kansa da sake ce mata, .
“Da alama kin bambanta da_ telolin
* zamaninki, ni da kin iya dinkin maza wallahi
Sai ki zama Telata’
“Ayya ban iya ba, amma idan ka tashikawo_ –
dinkin amaryar taka ina maraba”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta amsa masa lokacin da suke ficewa daga kantin, matakin da ya tabbatar masa dabi’ar Husna ce kawai tayi aiki akansa ba don ya zama wani abu a zuciyarta ya sanya shi samun matsayin shimfidar fuskarta ba.
Nan ya shiga caje kansa ciki da bai, don ganin me ya rasa a kyaun halitta?
Baki ne sosai mai matsakaicin tsawo amma __ kakkaura,mai dogon hanci da manyan idanuwa wadanda suka dace da tsarin fuskarsa, yana da tsararren Saje da baki wanda yake sa masa kwarjini, musamman saboda sumar kai da yake Tarawa wadda tun Hajiyarsa na fada harta gajitadaina. —
A tsarin halittarsa ya tabbatar babu abin kushen da Husna zata Ki, matsalarsa kudi ce, – kuma dole zai nemo su in dai zasu bashi — abinda yake so, wato Husna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Adamu durkushe gaban Malam-na-Allah a dakinsa mai Karancin haske ko dada hasken rana balle wannan lokacin na duhun magariba dakyar yake iya gane abinda dakin ya kunsa tarin littafai ne zube ako ina nan da can a dakin sai kuma taron alluna rubutun sha suma birjik jingine jikin bangwayen dakin akwar raki rataye da kayayyakin malamin sai kuma kala kalar carbi manya da kananansu suma a rataye a jikin rakin daga can kusurwa akwai wata karamar kantar katako mai dauke da kwalaban turarukan wuridi suma kala kala bayan gajeruwar gaisuwa adamu ya gabatar da buqatarsa malam nima zuwa nayi a bani wuridinnan da aka bama sulaiman yanzu na gane mutum bashi taba kwanciyar hankali inba kudi ya mallaka ba
Malam yayi gajeran murmushi ba tare daya tanka ba ya bude wani kundi dake kusa dashi ya jaro takarda mai kunshi da rubutun ajimi da kuma bayani da fassarar boko a bayan tajardar Www.bankinhausanovels.com.ng
Gashi, kamar dai wancan ne da nabaka ka dawo min da shi” Adamu ya karba ya shiga dubawa, sai can ya dago ya dubi Malam, “Eh na gane irin wancan ne?” Malam yace, – “Ai dama ba ka kawo min turaren ba, koka salwantar nabaka wani?”’ Adamu ya girgiza kai, – : “Yana nan Malam” ° : Malam ya dubi agogo,–: ~~” “Shikenan sai kaje, abinda baka gane ba ka dawo gobe, yanzu dab ake da fara kiran salar“ magariba. Adamu ya fara godiya yana ” kokawar sa hannu a aljihu,, cikin ransa yana fatan Allah ya lsa kamar wancan lokacin Malam yace ya bar shi, don Allah ya sani duk bogi ne sa hannu a aljihun, naira hamsin ce a aljihun nasa. “A’a ka bar shi kawai, zamu hadu wani lokacin? In ji Malam, addu’ar Adamu ta ci kenan. Ya Kara wata godiyar sannan suka tashi -gaba daya Adamu nayi masa sallama. Www.bankinhausanovels.com.ng
*************
“Na kira ka ne in ji yadda aka yi ka san _gaibu”
Ko gaisawa da Yayansa ba suyiba, ya tare shi da wannan maganar cikin daure fuska, alhalin takanas ya aika aka yi kiransa._ –
Ya zaci ma wani abin kirk ne ashe wulakancin da aka saba za’a yi masa.
Kansa na sunkuye yana zaune kan kujera yayin da Yayan nasa ke tsaye Kerere a kansa. Sai dai duk bacin rai da rashin kunyarsa ya hadiye kayansa a ciki. Jiki a sanyaye ya daga kai ya dube shi,
“Alh, Ban gane na san gaibu ba fa, a ina na
fadi hakan?” Yayansa ya amsa masa ba tare da ya juyo ya dube shi ba, Shekaranjiya ka fada wa Hajiya”™ “Na ce mata gobe za a tashi kiyama?” ’ Ya amsa cikin cin mur da dakewa. Www.bankinhausanovels.com.ng Dama tun shekaranjiya bayan ya ji kudurin Husna na kin auren mara sana’a ko kuma mai karamar sana’a ya ji ya tsani kowa a duniyarsa, musamman ma Yayan nasa wanda ya fi kowa gina masa Katanga da sana’ar, kuma tun shekaranjiyan yake atisayen yiwa kowa bore, bai yarda a shigo rayuwarsa a tauye masa Husna a cikinta ba. “Karatu ne na bar shi kuma babu shegen da ya isa ya kuma sawa na yi Kalmomin da yaké ta maimaitawa kenan tun daga jiya zuwa yau,.da ma yanzu da yake gaban Yayansa cikin zuciyarsa.
‘Yayan na sa ya sha mamakin wannan baKar maganar da Adamu ya yarfa masa, amma dai ya hadiye yadda ta bata masa rai, yana kallonsa kai tsaye ya ce, ‘ “To ko hakan ma ka fada mata ne? gaskiya na ganka da wannan zabgegen carbi mai ‘ya’ya dubu kana neman gafarar ubangiji…
Takaici ya kama Adamu na ganin an canja – masa ma’anar wuridi..
“Ni ba Istigfari nake ba” , Ya tare Yayan a kuntace.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Oh Hailala kake kenan, musamman tunda gobe za’a tashi kiyama, shi ne kake sabunta shahada?” !
Adamu ya sake yin fuska yana murza ‘ya’yan carbin hannunsa daya bayan daya tare
da yin mus-mus da baki………: “Kalas! Da alama ta wannan hanyar kake iya hango abinda zai faru gobe”. In ji Yayan cikin nuna halin ko in kula.
– Har yanzu Adamu yaki ya tanka illa fuskarsa da take iyakarta na cin magani
bakinsa kuma ya dukufa da motsi. _
Yayan ya basar inda ya jira shi yayi adadin da yake bukata yana yi masa kallon tura aniya, sai da don kansa ya gaji da kallon da kuma murza carbi sannan ya ajiye, sai dai bai ce — komai ba.
_Yayansa ya fara safa da marwa a tsakiyar – _ falon cikin yanayin mazantaka,
“Hajiya ta sanar da ni cewa wai ka hango baka da abinci a karatun boko, haka ne?”
.. Adamu ya jima kafin ya tsinka. Har yanzu yanayinsa na nuna akule yake, – “Duba nayi kenan?” Www.bankinhausanovels.com.ng “Ah! To wa sani? Abinda nake tambaya tun dazu kenan rashin muhimmancina ya hana ka . bani amsa”’. – , Adamu ya dan fara mutsu-mutsu yana KunKuni,
“Ai ka ji matsalar, shiyasa ma babu amfani na batawa kaina lokacin yin karatu, domin idan zan zama Mongo park ba zaku taba yarda an halicci kwanyata da iya Kirkirar abin kirki ba”. Yayan ya Kara janye annurin fuskarsa yana. duban adamu, “Uhum! Cigaba ina jinka”
Adamu ya sake muskutawa rai a Bace yana. gyarawa. carbinsa zama, ba tare da ya dubi Yayansa ba ya ce, –
“Alh. Yadda kuke Kaddarawa ni ban iya wani abin arziKi a duniya ba, haka na kalli
kwanyata da rayuwata na gane sam babu abincina a karatun boko, don haka a daina yimin Kagen cewa na san gaibu’, “Kage? Uban wa yake maka Kage Adamu?” ‘ Adamu ya motsa ya sake motsawa cikin dauke kai, amma bai tanka ba. Www.bankinhausanovels.com.ng. Ya jima yana yi masa kallo mai fassara iri-iri, bai gamsu ba sai gashi a gaban Adamu cikin zafin nama, ya sunkuya ya dago habarsa -ya shinshina tsawon wasu sakanni sannan ya ture shi ya mike yana ja da baya cikin kallonsa, — “Babu alamun shaye-shaye a numfashinka Adamu, amma me yake cin kanka yau?” Adamu ya sake cin magani ya cigaba da jan carbinsa, sai jikin Alh. Yayi sanyi ya jima ~ tsaye yana nazarinsa cikin kasa’ hankula, bai ~ kai ga warwara ba ya zauna kujerar kusa da – Adamun ya dafa hannunsa yayi masa Magana da tattausar murya, ; , “Ka kasa gane nufina Adamu, Kudurorina akan ka sami kyakkyawan ilmi mai zurfi duk ba ni zasu amfana ba kai zasu amfana, babbar sakadanre bata isa komai ba da har zaka mallaketa kaja ka Bame, ina laifin ko ‘yar diflomar ka yarda ka samu tunda ka fara?” Yayi jiran cewar Adamu, amma har yanzu babu alamar zai tanka, sai dai ya rage cin magani da yake. Www.bankinhausanovels.com.ng Alh. Bai yi fishi ba ya cigaba da magana ‘ cikin taushin murya da sassaukan harshen fahimta.
| “Hajiya Uwa da mahaifinmu Mal. Musa mu biyu kadai suka mallaka wato ni Kabiru da kai Adamu wanda na bawa tazarar sama da shekaru goma., Lokacin kurucityata kafin kai’ kai bai waye da neman ilmin boko sosai ba don haka ban sami hasafinsa ba, lokacin taka ‘Kuruciyar kuma kuncin rayuwar . talauci . ya hana su maida hankali.akan karatunka” – Adamu ya: muskuta alamar nuna gajiyawa da gundura da wannan dadaddan tarihi da kullum Yayansa ya tashi yi masa nasiha sai ya hado masa da shi, sai kace mai gwada masa shiga kabari a fito. . Alh. Ya fahimci gundurarta Adamu amma sai ya share shi ya cigaba da maganarsa,
“Tun kana mitsitsinka na fara buga-buga ta neman kudi, yau wannan sana’ar gobe waccan . har ajalin mahaifinmu ya riske shi. Duk da ina da sauran Kuruciya bai hana nauyinku kai da’ Hajia’.ya dawo kaina wanda hakan ya sani Kara Www.bankinhausanovels.com.ng zage Kwanjin neman na kai, ‘Allah kuma ya dafa min har ya tsayar min da sana’ar nan ta safarar Goro daga kudu zuwa arewa, har kawo – yau da rufin asirin Allah ya lullube mu ta silarta har ni da Haj. mun shiga sahun wadanda za’a kira Alhazai” Ya dan nisa kamar alamun rashin alamun abin fadar ne-ya Kare har Adamu yana murna da tsaki cikin ransa, amma sai murnar ta koma _ ciki lokacin da Alh. Ya sake nisawa, Ba gorin kushe nake maka ba Adamu, amma tabbas na ci kashinka yadda idan ka bijire min ko kayi-min butulci Allah zai bi kadin hakina, na soka shigen son da Uba yake wa dansa, shiyasa burikana akan ganin cigaban rayuwarka suka yi Kamari. Burina ka zama likita,, amma da naga hankalinka baya kan katatun sai na sauke farashi, aKalla ko malamin makaranta ka zama. Haka kawai ni dai naji akwai buKatar ka tanadi ilmin ko da kuwa kafi sha’awar zama dan kasuwa, shiyasa ma na bayar da shawarar ka karanta kasuwanci kamar – yadda ka yarda ka fara bayan ka share shekaru |da dama kana zaman kasha wando. Www.bankinhausanovels.com.ng Na ci burin ka tsaya da kafarka yadda ko
bayan raina zaka iya cigaba da daukar nauyin kanka da mahaifiyarmu sannan ga nawa iyalin wadanda basu da kowa sai kai……”
Adamu ya muskuta cikin mita da kunkuni, inda yake cewa, “Kana tunanin abi maka kadin hakkinka a kaina, amma ka kasa tuna za’a bi nawa hakKin a kanka saboda. takurawar .da kayi. min da cukwikwiye ni sai nayi wata rayuwa wadda bani da sha’awarta saboda kawai na dauki nauyin rayuwar iyalinka inka rasu….” “Me kake cewa?” Alhaji ya tambaya cikin fuskar mamaki. “Cewa nayi Allah ne kadai ya san gawar fari” Adamu ya amsa cikin nuna gundura. . Alhaji Yayi kasake yana kallon Adamu, ya shafa abin dorawa ya rasa, sai kawai ya. rangwada kai yayi shiru. Hakan da Adamu ya gani ya sanya jikinsa . Yin sanyi, ya dan yi kame-kamensa sannan ya fara magana, Www.bankinhausanovels.com.ng “Wallahi duk na fahimce ka Alhaji Amma kai ma abind aka kasa ganewa shi ne, shi . karatu ba a sanya masa Karfi dole sai kwanya — da ra’ayi suna da sha’awa, Ni kwata-kwata idan ina da ra’ayin karatun boko Allah ya tsine min, shiyasa ma shekarun nan biyu na dinga samun kari oba, kuma wannan shekarar ma idan an matsa min Kila abin yafi haka..” “Allah ya kyauta” .° Alh. Ya fada cikin alamun gajiya da takaici. Suka jima cikin shiru kafin alh. Ya nisa, “Shikenan maganar karatu a barta in Allah . yaso amma fada min, menene Kudurinka, ~ menene burinka, menene ‘abinda kwanya da ra’ayinka suke sha’awa ba wanda ake musu~ sha’awa ba?” ai Da sauri adamu ya amsa, “Ni .sana’a nake so, Allah ya sani. ina so nayi aure” Zuciya tazo wa Alh. Wuya, amma ya dinga shanye kayarsa har ya hadiye fiye da rabinta. “Na san kana son aure tun tuni, amma a tsammanina zan iya tare ka har lokacin da idan Www.bankinhausanovels.com.ng kayi ba zai zame mana matsala ba, ban sani ba ashe Karya naci na kwana da yunwa” Adamu yayi shiru.
– Can.jimawa Alh. Ya sake nisawa, “An ce min Salma na sonka, in haka ne gara ayi ‘yar gida musamman da yake baka da _ KwakKwarar sana’a sannan ka san komai akanta, “yar yar mahaifiyarmu ce da ta rasu tun tana karama riKonta ya dawo hannuna don haka ta san ciki da bai a samu da rashinka kafin sana’arka tayi Kwari’. . Ba don wata fuskar tafi gaban mari ba babu abinda zai hana Adamu tura ashar. Sai kumburi yake kamar ya fashe ya tari numfashin yayan nasa, . “Wa yayi min sharrin cewa ina son Salma?” .“Cewa aka yi Salma na sonka, ba cewa aka yi kana son Salma ba” . . Alh. Ya amsa cikin tausasawa. – Adamu ya Kara bata rai, **Wa ya fada? Ni bata taba fada min ba” Alh. Ya sake daurewa Www.bankinhausanovels.com.ng “Sa’ adatu ta sanar da ni Babu kunya Adamu ya sake tare numfashin Alh. a sike, “Gaskiya ni bana sonta, wata yarinya nake so na aura” Alh. Ya gama kai wa bango, tsawon lokaci yana jinjinawa, “Ba ka sonta?” Adamu baitanka ba, iyaka ya cafko carbinsa ya fara ja. . } ~ Alh. Ya sake kada kai, “To da kyau! Nan ma an wuce, na yarda kaje ka auro yarinyar da kake so kuma kake son aure. Sai mu fado maganar sana’a, wacce kwanya da ra’ayinka suke sha’awa?” Hantar cikin Adamu ta kada daya fahimci turin Jeka-ka-mutu Alh. Ya shirya yi masa, ko kuma debi inga hankalinka, Ta ina zai sami sana’a babu hannun yayan nasa a ciki, in sana’ ar ba ta aikin Karfi bace ina zai nemo jari? Yana tuno tauhidi sai ya sami harshensa na bawa Alh. Amsa, “Muna nema wajen Allah?”
To babu laifi Allah ya zaba mafi alkhairi. idan an samo sana’ar a sanar damu mu taya murna tashi kaje
***********
Hmm ko me zai faru ku dai ku kasance damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng