NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 9 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Ya zauna bakin gado gefensa sunayiwa juna kallon kuda da alama kowa bakinsa cike yake da zance amma sai salmanu ya rigashi www.bankinhausanovels.com.ng furtawa cikin murya_ kasa-Kasa kasancewar dakin ba Adamu kadai ba ne mara lafiya. Ba Babu alamar ciwo a tare da shi yanzu amma ~ fuskarsa ta nuna jigata da farkowa dagaciwo. Malam ka daga min Kafa, na ce Mashin ne ya bige ka, banza kawai daga naushi daya sai ka macewa mutane?” : Adamu ya jima bai tanka ba. Salmanu ba ya shakkar in Adamu.zai kasa goya masa baya, ba yau yake da shi ba ba jiya ba. Hasashensa kuwa ya ci, domin sai gashi cikin murmushi Aadamu ya ce, Ka ci sa’a ban mutun ba Salmanu, inna -mutu ni da Husna ba zamu taba yafe maka ba, don ba ka bar mu a duniya mun auri juna ba” Salmanu ya kai masa bugu cikin murna da 1hu, “Au har ita ba zata yafe min ba? Ita da bata ma san kana yi ba?” Adamu ya kawar da kai, eh mana, ruhinta ba zai yafe ba domin akwai ranar da zai san a duniya yayi rashin wanda ba zai taba samun wanda ya so shi haka ba”

ZAMU TASHI 

” Shigowar Alh. bata hana Salmanu ya amsa masa cikin murya Kasa-Kasa ba, “Da ka mutun ai zan kai mata wannan canjin a matsayin diyya, su suka kashe ka su suka hana ka auren abinda kake so” Suna dariya tare da tafawa Alh. Ya Karaso cikin fara’ar nuna farin ciki da murnar yadda ya sami jikin Adamu, . : “Ah lallai jiki yayi kyau, Alhamdulillahi” Cikin ladabi Adamu ya rusuna kai ya gaishe da yayansa. Salmanu ne ya amsa, . “Wallahi kuwa jiki yayi kyau Alh, kawai su zo su sallame mu a kai wa Hajiya danta” Suka yi dariya su duka. ‘ Alhj ya duba agogo yace, ‘ “Sa’adatu bata gida ne tun safe, amma mun yi waya da ita tace min ta dawo gida har sun yi _abinci suna hanyar zuwa ita da Salma” Adamu yayi walankeluwa da bayanin yayan “nasa don ya ji suna Salma a ciki, har ga Allah ya tsani Salma, tsana mai

yawan da ya sha tambayar kansa dalilinta alhalin ta kasance ‘yar’uwarsa. Don haka yadda ya bata rai ba Alh. da ya san Www.bankinhausanovels.com.ng akwai tsama a tsakanin Salma da shi ba, hatta Salmanu da-yake daukar tsanar da Adamu ke wa Salma a matsayin shaKiyyanci sai da ya lura da hakan, Suna ta ‘yan hirarraki a tsakaninsu, Da Adamu aka taru aka dinga zagin mai mashin da ya buge shi har Allah ya kawo su Sa’adatu. . Aka gaisa a mutunce tare da yi wa juna jaje da Allah kiyaye gaba. . Kasancewar akwai Alhaji a wajen Adamu ya dake bai nuna tsama ba, Salma ma ta rakuye a can gefe rungumie da hannu tana satar kallon Adamu wanda ta lura yana ta faman buga mata shan kamshi ko kadan bai yarda: ma sun hada idoba, alhali a yanzu babu abinda take nema irin su hada idon ko hodar Boka zata kallo mata shi, tana son ta ga yadda‘za’a Kare saboda haka zuciyarta ta kasance cikin matsanancin bugu. “Zo ki zuba masa abinci Salma, mun gode  Allah Adamu an auna arziki”
Anti Sa’a ta farko da ita daga fargabarta, a hanzarce ta yunKura ta nufi ledar kayan abincin
tajanyo. yadda maganin zai yi aiki akan Adamu kadai duk da ba shi kadai zai ci abinci ba, Anti Sa’a ta fada mata a tukunyar gidan yawa ma ana zuba maganin Boka kuma ba wanda zai kama sai _ wanda aka nufa.
Adamu bai yi niyyar Kin karbar abincin ya ci ba, sai-da Salmanu ya zolaye shi ta hanyar yi
Www.bankinhausanovels.com.ng Tana zuba abincin cikin kasala da fargabar  masa inkiyar ga amaryarshi fa na hidimar zuba masa abinci. : : Da Salma ta mika masa filet din abincin. sai ya kawar da kai yana cin magani, “KenaKoshi” — Suka dubi juna ita da Anti Sa’ a fuskokinsu na aika sakon karaya. ~- “A’a me kaci? Kai da tun safe kake sume?” Inji Alhj

Adamu ya tattara hankalinsa ga Alh. “maimakon kallon Salma wadda ta nace da mika masa farantin abinci duk da ya ce ba zai ci ba. Ba na jin ci ne Alh. maltina da madarar da na sha sun gamsar da ni, bakina babu dadi” Karaf Anti Sa’a ta shiga maganar,Www.bankinhausanovels.com.ng
Ai ba daka ta bakin naka zaka yi ba Adamu, ko loma biyar ne yakamata ka karbi hatsi ka watsa a cikinka, ga ruwan zafi ma idan shayi zaka sha” ’ Adamu yayi fuska, Tun da kin matsu kawai sai ki yi min dura” ~ “Wacce ni? Wannan sai dai Salma, ita zata yi maka durar” . Salmanu ya tuntsireda dariyar da ta Kara hasala Adamu. Idon. Alh ne ya sanya bai kashe Salma da harara ba sai kawai ya shaye ya kawar da kai. 
Salmanu ya mika hannu ya karbe abincin hannun Salma yana cewa, © . Kin ga ni ka Maltinar ban sha ba, manta da shi ki baninaci”. Dole Salma ta sakar masa abincin ta ja baya a – muzance zuciyarta cike da kade-kade, tsakaninta da Allah ko hanyar son abokin Adamu ba ta dauka ba, idan ya ci abincin shi kadat sihirin sonta ya kama shi fa? ; Anti Sa’a ta lura da wannan tashin hankalin na fuskar Salma don haka ta dinga rarrashinta da ido tana nuna mata kwantar da hankali, Www.bankinhausanovels.com.ng
Dai-dai wannan lokacin aka yi kiran Alh. a waya ya sa kai ya bar dakin domin ya amsa, da sauri Anti Sa’a ta yi wa Salma inkiyar ta saki fuskarta ta matsa kusa da Adamu. Ba karamin Karfin hali Salma ta yi ba na bin umamin Anti Sa’a, musamman da ta dubi Salmanu ta ga ya aika da rabin abincin kuma har yanzu yana kan ci. Anti Sa’a ta fara yaudaro Adamu da cewa,
Ni fa na zaci kun shirya da ‘yar tawa har na ji ka sai mata anko, amma yanzu takanas mun zo duba ka kana ta faman wani shassharewa, wai ko kalion fuskarta ba zaka yi ba bare ka ci abincin _ da ta kawo maka?” . Adamu yayi fuska ya tsurawa Anti Sa’an ido maimakon Salma da suke son ya kalla,
“Menene sabo a fuskar tata da ake son na. kalla? Ga abokina‘nan ya fanshe ni ya kalla, ba -shikenan ba” Duk su biyun suka ji kamar ya rusa musu guduma a Kahon zuci, na Salma dai-yafi bayyana saboda dama a tsorace take da cewa ta zubawa Adamu tsafaffen maganin bokan da ba ya Karya, abokinsa ya ci abincin. Www.bankinhausanovels.com.ng Sun Kara rikicewa lokacin da Salamanu ya debo murmushi yace,
Ga, shi yau Salma ta yi kyauwun da bata taba > yi ba, kuma ta yi girkin da ban taba cin mai dadi irinse: ba” “to ai sai ka yi mata abinda suke son ni na yi mata” Adamu ya Kara yin fuska ya fada. Sawu a likkafa Salma ta sa kai ta fice daga dakin, inda Salmanu da ma Adamun suka bi ‘ Keyarta da kallo. | . “Babu dadi cin fuska” . Anti Sa’a ta fada cikin takaici, ta Kara dacewa, : ‘ . “Duk tsiya mai sonka ya fi mai Kinka” “Me ya kawo wannan maganar?”  In ji Adamu rai abace, AntiSa’a tace, . “Abinda ka yi ne ban ji dadi ba, Salma fa ba neman kai muke da ita ba, kuma ba wani laifi bane dan ta nuna sonka a matsayinka na dan gida  wanda ba wani abu ya mallaka ba bare ace ba son Allah da annabi take maka ba, ka je ka tuna wannan’. ” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaki kawai Adamu yayi ya kawar da kai. Hakan ya sanya Salmanu yin shiru alhalin da yayi niyyar saka baki. “Ina ankon nata”’ Tatambaya. . Da sauri Salmanu ya kalli Adamu yana dokin jin Karyar da zai zabga. . Kai tsaye Adamun ya amsa, “Wa yake ta wani anko? An sace shi a nan inda hadarin ya faru. Ai maganinta kenan ma da na ce ta zo ta karba ta ce-min sai ni zan kawo |n mata, Allah Kara”
Murmushi kawai anti Sa’ a tayi ta basar da zancen suka kamo wani, har lokacin ziyara ya kusa Karewa sannan ta yi masa sallama ta tafi. A waje ta ci karo da Salma zaune a baranda cikin damuwa. Ta ce mata, “Yi maza ki Kara goga hodar ki je ki yi masa sallama kar ki damu’’. Cikin sanyin jiki Salma ta goga ta shiga
dakin, tana riKe d Karfen gadon Adamu tace, “To yaya Adamu zamu wuce, Allah Kara lafiya” Www.bankinhausanovels.com.ng Ya dago ya dube ta fuskarsa babu yabo babu  fallasa ya dago ya dube ta, ita kuma ta sakar ~ masa wani murmushi, sai ya ji wani dum! Tun daga idonsa har cikin ransa, amma dai bai bayar  da maza saboda canjin da yaji ba, cikin nutsuwa _ ya amsa mata, To sauka lafiya, na gode”
Ta dan yi dum! Da zaton bai kalle ta da kyau ba, musamman da yake ya kawar da kai. Amma babu yadda ta iya haka ta juya tana ficewa. Salmanu ya bi ta da kira, Ki zo ki tafi da wannan abincin da yaki ci kin ga yau za’a sallame mu” Salma.ko ta juyo bare ta nuna alamun ta ji abinda yake cewa. . _

***********

_ Adamu ya saba tsayuwar dare, amma yau bai. _ yi niyyar tsayawar ba dan har yanzu jikinsa ba Kwari, sai dai kuma baccin ya gagari idonsa da ma. zuciyarsa gaba daya, a kuntace take iyakar  Kuntacewa, haka kawai ransa ya dinga – mugun baci cikin daren nan ba tare da dalili ba, Www.bankinhausanovels.com.ng  ya kuma rasa wa yake jin haushi ko kuma abinda. – ke bata masa rai. Haka kuma Salma da Husna suka dinga tsere cikin zuciyarsa suna nuna masa kansu.
Ya san cewa shi ma‘abocin tunani ne, amma na Husna zalla! Salma ba ta taba samun ko a bonus ya zauna musamman ya tunana ta ba, tunaninsa a lokutansa na rana na yadda zai mallaki Husna ne da mafarkin yadda zasu shifida rayuwarsu, tunaninsa da’ lokutansa na dare na mika dukkan imani ne ga ubangiji da roKonsa ya mallaka masa ita yana mai cike da fatan Ubangiji ba zai juyar da rokonsa ba.saboda haka yake yi cikin dadin rai na jiran lokaci. Amma yau komi ya canja, shi da zuciyarsa neman sa Karfi suke su bar Allah, ba don su sami Husna ba sai dan su sami Salma ba tare kuma da  sun dena son Husna ba, abin da bayar da mamaki! . Fiye da rabin dare haka yayi ta juyi kan katifarsa rayukansa babu. dadi suna kuma ta damfara masa kala-kalar mamaki Bai tashi yayi sallar ba bare ya fadawa Allah, bai ma yi  Sha”awar hakan ba saboda kasala da rashin dadin
Www.bankinhausanovels.com.ng zuciya, kai da ma rashin tabbas din in ya tashi me zai cewa Allah? Shi da ya shafe watanni yana neman Husna a wajensa yau kuma sai ya durkusa neman abinda baya so wato Salma? Ita . wadda yake so ya kai ta ina, kuma Salman ma yaya zai yi da ita? : Duniyar ta taru tayi masa zafi har Karshen dare, musamman da ya Ankara duk yadda yaso ya nesanta ransa da Kawancen Salma hakan yaku° samuwa, Kara samun muhalli: take mai shegen zurfi a cikin zuciyarsa. Sai ga shi zaune da kuka shabe-shabe da hawaye har da sauti, yana yi yana ambaton, “Na shiga uku!”  Ya ci kukansa ya Koshi,, amma Salmanu da ke kishingide kan Kafet yana sharar bacci bai san yana yiba. Kasancewar ba’a sallamo su kan kari ba ne ya -sanya shi kwana a nan, abinda ya cewa su Hajiya kenan, amma gaskiyar ita ce, sammakon aikinsu _Suke son dokawa, a cewar Salmanu, ko babu . kudi yakamata su fara aikin da ba kudin yake. -bukata ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Musamman ‘Adamu ya tashi zaune. yana “zungurinsa cikin kuka. – A firgice Salmanu ya farka ya tashi zaune, Adamu jikin ne?”  Adamu ya sake carkewa da kuka, ; “Zuciyata ‘yar ta’adda ce Salmanu, ta kwaso ta’addanci ta kawo wa raina, sun hana ni bacci da Alama ma har Karshen rayuwata suke bukatar kar na runtsa” to
Salmanu duk da bai gama fahimtar Adamu ba  fuskarsa ta nuna iyakar damuwa, ya ce, .
Waime yafaru?”.Wai Salma muke so”. _ Ya amsa cikin shassheKa.  Salmanu ya sake tare gira nuna alamun rashin _ fahimta, Kaidawa?” “Ni da banzar zuciyata mana”. . . – Kamar Salmanu zai tuntsire da dariya, amma ‘har ga Allah ya ji tausayin Adamu musamman_ yadda ya ga yana kuka da hawayensa, a sanin da _ yayi masa jarumi ne daidai misali, kadayake shi  halittar so na saurin sanya shi kuka, haka wancan
Www.bankinhausanovels.com.ng neman auren da ya taba rakitowa Karfi da yaji ya mayar da shi wani Baure, Ya jima yana kallonsa cikin nazari sannan ya tanka, Da mamaki gaskiya, to me ya janyo hakan?”
“Oho! Nima na sani! Zagi nake so in rusa amma na rasa wanda zan zaga, ni ko zuciyatada_ haka kawai muka rakito son abinda bai cancanta – ba? Allah ya tsine wa Salma wallahi, ni ban san abinda zan so a ita ba”  Ga dariya ga kuma son yin nazari suka taru suka murkushe.Salmanu, sai ya hada su duk biyun yana ji dasu, :lCikin tsananin dariya.ya.ce da. Adamu, Jiya Salma ta sako kwalli? In ta saka saimu yi tsammanin Kifil ta sako maka” ‘“Allah ya isa ban yafe ba wallahi” . -Salamanu ya sake tuntsurewa da dariya yayin da Adamu ya sake sakin shassheKar kukan da ya tsayar da Salmanu dariyar da yake,
Wai baka yi bacci ba? Na san ka da sallar dare yau me ya hana ka? Ai da ka kai wa Allah Karar Salma yayi mana maganinta” ——Ya Kara da tuntsirewa da dariya. _

Hmmmmm LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *