NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 KARSHE CHAPTER 10 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Www.bankinhausanovels.com.ng
A JIYA MUN TSAYA
neman auren da ya taba rakitowa Karfi da yaji ya mayar da shi wani Baure, Ya jima yana kallonsa cikin nazari sannan ya tanka, Da mamaki gaskiya, to me ya janyo hakan?”
“Oho! Nima na sani! Zagi nake so in rusa amma na rasa wanda zan zaga, ni ko zuciyatada_ haka kawai muka rakito son abinda bai cancanta – ba? Allah ya tsine wa Salma wallahi, ni ban san abinda zan so a ita ba” Ga dariya ga kuma son yin nazari suka taru suka murkushe.Salmanu, sai ya hada su duk biyun yana ji dasu, :lCikin tsananin dariya.ya.ce da. Adamu, Jiya Salma ta sako kwalli? In ta saka saimu yi tsammanin Kifil ta sako maka” ‘“Allah ya isa ban yafe ba wallahi” . -Salamanu ya sake tuntsurewa da dariya yayin da Adamu ya sake sakin shassheKar kukan da ya tsayar da Salmanu dariyar da yake,
Wai baka yi bacci ba? Na san ka da sallar dare yau me ya hana ka? Ai da ka kai wa Allah Karar Salma yayi mana maganinta” ——Ya Kara da tuntsirewa da dariya
ZAMU TASHI
Asamu ya tsayar da hawayen yana duban salmanu
Kabar mayar da lamarinnan wasa wallahi da gaske nake zuciyarnan taci amanarmu sai abin ya fara bama salmanu mamaki yayi sukukwitare da neman tashar da zai kamo
Amma ya rasa har lokacin da yaga adamu ya miqe daga kan katifar tasa ya fara kaiwa da komowa a tsakiyar dakin salmanu ya daga kai ya bishi da kallo yana sauraronsa a tsanake lallai akwai wani abu dake shirin faru damu nida rayuwata abu mafi daure kai ta inda makomar husna zata bullo a rayuwata abu mafi muni shine kaddarar rayuwata ta zamo babu husna a cikinta dukda ina ceke da yakinin da wahala husna bata zamto mata gareni ba
Maiya kaika cin wannan alwashin dan allah salmanu ya tareshi cikin mamki da al,ajabi tare da zaton kamar ba cikin hayyacinsa yake ba adamu ya amsa cikin murmushin yake Www.bankinhausanovels.com.ng
“Akwai kyakkyawar alaka tsakanina da Ubangjina Salmanu, in dai na yi masa irin roKon da na yi akan Husna yana ba ni abinda na roKa,
shiyasa nake cike da fatan kutsen da Salma ta yi cikin zuciyata ba zai hana ni zama mijin Husna ba”
Har yanzu Salmanu cikin mamaki yake, sai ma ya rasa abinda zai ce. , Adamu ma ya kulle hira daga haka, ta hanyar ‘ ficewaya dauro alwala ya tayar da sallah. Yayin da Salmanu ya koma ya kishingida. ; Duk sammakon ficewar da suka doka sai da Salma ta riske su da farfesun dubiya ga Adamu. A bakin Kofa suka yi kacibis da Adamu bayan Salmanu ya fice waje, duk suka dubi juna da wani baKon kallo wanda ba su saba shi a tsakaninsu ba, a cikin wasu sakanni Kalilan, Salma ta riga shi tankawa, “Sai ina da sassafen nan?” Ya so ya tara gira ya kuma daure murya – amma sai yaji ya kasa. Ya jima bai tanka ba cikin
Www.bankinhausanovels.com.ng kallonta a sassauce sannan ya nisa cikin sanyin murya yace, — .
“Ke ma‘ me ya fito da ke da wannan – sassafen?” Ta fara KoKarin shiga dakin da yake son -rufewa kamar zata ture shi, da sauri ya bata _ hanya sannan ya bita cikin dakin yana sauraron ‘ amsar da take ba shi, “Dan abin sashe baki na kawo maka a matsayinka na maras lafiya” ~ uhm kawai ya iya tanka mata da ita. Ta zauna kan kujera shi ma ya nemi dandaryar kafet ya zauna suna fukantarjuna. ~~ “Yajikin?” . Ta tambaya tana dubansakaitsaye.. . Shi ya kawar da nasa idon ya amsa,_. , ~ “Athamdulillahi” Ta cigaba da kallonsa. tana son kore mamakin sauyawarsa don ita ta san dalilin sauyawar, “Kuma daga fitowarka jiyan nan daga asibiti Yaya Adamu sai ka kwashi jiki ka fice yanzu da sanyin safiya ba zaka bari ka warware ba? Www.bankinhausanovels.com.ng in kai baka damu da lafiyarka”ba fa akwai irinmu da muka damu da ita” .Yayi KoKarin fada mata mai daci ya ji harshensa ya kulle, mai dadi yake son furtawa zuciyarsa kuma tana Kyashi, don haka ya Kyale aka yi biyu babu. — Yau wai ya na gan ka duk asanyaye?” Ta tambayae shi cikin dariyar da biyu. Ya dago kai ya dube ta kawai, amma bai tanka ba. Haka ta yi ta ‘yan sambatunta yana bin tada ido harta sauke kular farfesunta ta samo filet ta zuba masa ta kai masa har gabansa, . “To dan taba wannan tunda sauri kake in ka dawo ka Karasa sauran” Ya dubi agogo sannan ya mike yana cewa, . “To bari na kira Salmanu ya taya ni” Ta yi KoKarin shan gabansa,
‘ “A ‘haba dai ka ci mana ba sai ka zuba masa wani ba tunda farfesun da yawa?” Fuskarsa ta dan nuna damuwa duk da yana yi .mata fada kar ta batawa Salma, ya kewaye ta ya nufi Kofa yana cewa, Www.bankinhausanovels.com.ng ai baza,ayi wasa tare da ci bambam bari. dai na kira shi” Ta bi shi suka bar dakin tare tana cewa ~ . “Shikenan, ni ma zan koma Allah ya Kara – lafiya” – : Ya amsa cikin fara’ar da Salma ba ta taba gani a wajensa ba A Kofar gida suka tarar da Salmanu zaune_.
kan dakali, suka gaisa da Salma ta wuce, shi_. kuma Adamu ya ja shi cikin gida suka fara kwasar garar farfesu. -Wai sai da suka ci suka side sannan Salmanu ya ce cikin zolaya,_ . . ‘ “Mu fa samari a irin wannan kwadayin namu_~ake neme mu, ka san mata da barbade-barbade”’ Da takaici ya kulle Adamu sai ya rasa da _abinda zai fanshe face kai wa Salmanu wani wawan mari, Allah ya taimake shi yakauce yana dariya. , – : ai“Kai wallahi KwanKwararren mugu ne, kasan’” da hakan sai da muka cinye zaka fada min?” . Salmanu ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng “Kai ma yakamata ka san hakan don kai kadai ka san abinda kake ji a Kirjinka game da Salma” – Sai kuma Adamu ya ga gaskiyarsa, amma daga daren jiya zuwa yau zuciyarsa ba ta da zabin tunani na kanta sai abinda aka zaba mata, ko ta fara sai ta tsinke, don haka yanzun ma tsinkewa tayi daga gasKata Salmanu da ta fara. Sai Salmanu ya canja Bari, “In muka fara sana’ar nan zaka ce na sanar da kai, zaka gane halayen mata da yawa” Adamu dai yayi shiru, daga shi har zuciyarsa ~ ba a nutse suke ba, ko ragon tunani ba za su iya ba bare su yi wanda za’a yaba.
**********
Sati daya a tsakani Adamu na shan wahala_ iyakar wahala, tun daga zuci har zuwa gangar jiki. Duk wani tsari da fata wanda yayi shekaru yana shiryawa a matar aurensa da iyalinsa cikin sati daya sun bi ruwa. Zuciyarsa ta zama fanko babu wani tanadi a cikinta sai jiran tsammanin abinda rayuwa zata zabar mata. , Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuciyasa ta bude makeken fili ta share a son Salma ko ciwon shigowarta rayuwarsa, Husna na can loko sakaye da tata matsananciyar Kaunar wadda ya fara jin yawa ne da ita kawai, amma ~ tabbas zuwa yanzu ba ta da tasiri, tare da yakinin rashin tasirin nata nakasu ne a kulliyar:tasa rayuwar.: . .
Abin ya zo masa, da sauki ne, kasancewar tsawon satin suna ta fama da kujiba-kujibar ‘harKallar da suka cacimowa kansu, shiyasa dare kawai yake mallaka yayi kukansa yayi roKonsa ga ubangiji kuma ya tinana abinda zai iya tunanawa a mafiyayyen son Salma da kuma dan asalin son Husna.
Sun gyara muhallin da zasu fara bokancinsu, – yanzu suna cikin atisaye ne na dabarun karbar kostomomi yadda bokayen gaske suke, da kuma koyar rufa idon da zasu dinga yi wa maziyarta, ga Adamu kenan wanda bai san kan garin ba. _~
Zuwa yanzu dai ya haddace rufa idon da ake da Kwai, Tiyo, kyandir da kuma karkashi. Sun samo wani abokinsu taKadari irinsu mai suna Tanimu, tafiyar ta koma ta mutum uku, Salmanu ne ‘Boka, Adamu zai dinga aiki biyu, Www.bankinhausanovels.com.ng muryar aljanu yayin da yake boye, in ya bayyana = kuma ya zama dan kore ga Boka, Tanimu kuma
shi ne mai nemo kostomomi, wataran kuma yayi shigar burtu a zuwan kostoma ya yi ta koda boka ‘a gaban bakin kostomomi, sun shirya in harka ta kankama zasu nemai Karin yara. Yadda suka dauko tafiyar sun’ hango mata samun tsabar kudade da nasarori, don haka . dukkansu hankalinsu kwance suke komai.
************
Ranar juma’a da yamma yana zune a dakalin
+ Kofar gidansu zuciyasa a mugun Kuntace, ya
, dinga ayyana, ina ma shi yaron goye ne, tabbas
yau da uwarsa ta shiga uku da tsinannen kukan da zai.balle. mata hancinsa, a yau sai ta ~
gwammace bata haife shi ba. Kuma da girman
Nasa ma ya so ya kwatanta har ya shiga daki ya
fara gwaji, amma da ya fahimci aikin baban giwa
yake babu wanda ya san yana yi kawai sai ya
share hawayensa ya fito waje yana rarraba idanu. — Kamar daga sama ya hango Husna ta‘nufo shi kai tsaye, ta ci kwalliyar da bai: taba ganinta Www.bankinhausanovels.com.ng cikin irinta ba, kai bai ma taba ganin wata ‘ya © mace mai daura zani a hannun hagu tayi ba. – – Kawai sai ya saki baki yana kallonta cikin . matsanancin bugun zuciya har ta Karaso gare shi, sannan ne ya lura tana dauke da wata leda Kunshe da kaya. _ _ Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar da ya so hadiye ta amma ta sanya masa Karfi, yakawar_ . da kai cikin jin gaba daya ma ya san ya gama – – bayar da maza. , Da sassanyar muryarta ta yi masa sallama. Ya amsa da tasa dakusasshiyar muryar ba tare . da ya dube ta ba, ya kuma rasa dalilin da ya sa ya kasa duban nata. “Ranka ya dade wannan gimbiyar taka kuwa ~ ” tana gari? Na ga ba ka nemi dinkin nata ba gashi . kuma tun jiya muka fara bikin” Ta fada cikin matsananciyar fara’ar da tayi awon gaba da dukkan fargabar da ke kaKale a . Zuciyarta . Cikin Kumaji ya juyo yana dubanta kai tsaye, – Kirjinsa na dakan uku-uku amma Karfin halinsa ya gama bayyana ilahirinsa, yayin da soyayyarta ta fito daga saKon da Kaddara ta bayar da ajiyarta Www.bankinhausanovels.com.ng tayi awon gaba da ta Salma wadda ta yi gida ta tare, . “Duk wata gimbiya ai bayanki zata bi ranki ya dade” , Ya fada cikin sanyin murya yana yi mata – kallon.da shi kansa ya san Karya ne a ce bai bayyana tsantsar Kaunar da yake mata ba.
Ta dora dan alinta a Kirji tana bude da baki cikin shauki da yi masa kallon mamaki, amma bakinta ya kasa furta kalma, . Ya kada kai mai nuna tabbatarwa, _ “Na rantse da Allah dama kayanki ne” . ” Ta ji tsaiwa na neman gagararta, sai ta doge, ta rausaya kai har yanzu ta rasa bakin Magana. —
To yaya hidimomi?” : Da kyar cikin sarkewar numfashi yanzu ta – daure ta tanka, – . -“Alhamdulillahi, komai na gudana yadda ake so” a “To masha Allah, dama yanzu da nake zaune tunanin yadda zan riske ki gidan bikin nake” . Ta sake dubansa galala. . Shirunta ya cigaba da bashi Karfin halin Magana, musamman yadda take dubansa cikin Www.bankinhausanovels.com.ng sanyin jiki yana da yakinin tabbas ita ma So yayi mata wawurar da yayi wa zuciyarsa da ilahirinsa, “Zuwa yanzu na gama juriyar hadiye soyayyata da zuciyata take miki, in ban samu na _ furta ba ina da tabbacin, zamu iya shari’ a da _ zuciyar™, Tamkar jiri zai tike ta garin kuma ya dauki haramar zagayawa. Da ita.
Cikin haka ta Kwato furucin, ‘Nikakeso?” Ya amsa, “Menene na shakka?” – Ta yi saurin girgiza kai. Ba shakka nake ba,.amma me yasa. saida naz0 Kofar gidanku zaka fada min? ka ragewa son da ka ce kana yi min daraja” . _ Ya girgiza kai cikin sanyin jiki, “Kar ki fadi haka, son da nake miki ina da yakinin ba a taba irinsa ba, amma sai jiya na san gidanku kuma a yau din nan nakeda niyyar Zuwa Farin ciki ya rufe Husna, sai ta kasa tankawa. Suna tsayen nan kowa sai ‘numfarfashi da murmushi.. , yake Www.bankinhausanovels.com.ng Kwatsam sai ga Salma tamkar an jefo ta, ita ma ckin kwalliya tane sanye da irin Kayan dake. jikin Husna. Adamu na ganinta. ya ji tamkar an ruguzo masa dutsen dala a Kirji, jikinsa yayi sanyi Kalau, zaciyarsa kuma ta dakata da zabi, “‘~ . Aka yi gaisuwar mutumci tare da ambatar sunan juna tsakanin Husna da Salma na shaidar an san juna, kai tsaye kuma Salma ta fara gabatar da Adamu a wajen Husoa a matsayin dan uwanta, sannan ta zarce da cewa, . * + “Kuma shi ne wanda zan aura in Allah ya so” . Duk da Husnha macace mai siyasa, amma siyasar tata ta kasa galaba a wannan muhallin, » sai da idanunta suka KanKance suna.shirin fara zubar da hawaye, ta bi Salma da kallo wadda fuskarta ta nuna alamar da gaske take. Da ta juya ta dubi Adamu shi nasa.arzikin ma sai ya ci uban na jiya, domin kada mata kai yayi cikin tabbatarwa ya kuma amsa mata da baki.’ “Haka ne, za mu yi aure cikin Kankanin lokaci” Www.bankinhausanovels.com.ng Husna ta dauke kai daga kallonsa lokacin da – wani malalacin hawaye ya sulmiyo mata ta yi ~ dabarar gogewa da mayafi.
Ko Adamu ya san tarkon sonsa ta fada ne shiyasa takanas ya shiryo mata wannan cin fuskar? , Sai ta daga kai ta cigaba da tsura musu ido su duka dan ta gane siyasar ce, cin fuska ce ko kuma iyakar gaskiyarsu kenan? . : Kamar sun manta da ita sai suka lula cikin hirarsu da ke bayyana son da suke wa juna kai tsaye.. .
MU HADU A LITTAFI NA BIYU