NA SHIGA ALJANNAH BOOK 2 CHAPTER 10 KARSHE THEND BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Kamar kullum duk wani abu da ya danganci Salma zuciyarsa ba ta _bashi muhawara bare ya tantance ya zaba, kai tsaye daga can saman zuciyar tasa wani ke bashi zabi. ya aiwatar bisa dole. ° ‘ Yau ma ya so ya ji bijrewa da nuna wa Salma iyakarta, amma ya ji wancan Karfin na son matsa masa murnar zama angon da yake tafiya ga amaryarsa, hakan kuwa ya je mata har da siyayyar kaji da kayan jiKa maKoshi. Ya’ dinga nuna mata doki da zumudi tamkar dama ita kadai ce sauran burinsa a duniya ya kuma samu. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ban san kana sona haka ba Adamu”
Da kalmomin da ta dinga zolayarsa da su kenan, shi kuma yana amsawa tsakaninsa da_ ‘Allah,
“Yanzu kin sani Salma, ina son ki fiye da -son kowa a duniya”
In ya fadi haka Salma na jin wani munafikin hawaye na kurdo mata ta samu ta goge abinta, abinda take so kenan wato Adamu, ta kuma samu, in ba shi kadai ne burinta a duniya ba tana jin dai ya fi rabi.
ZAMU TASHI
Cikin sati biyu dukkansu rayuwarsu ta canja, Salma ta mamaye zuciyar Adamu tsab, duk wata mace a waje kallon Bahuwa yake mata, bata da kyau ko bata da kwalliya ko ma gaba daya sunan mata kawai take amsawa. Salmansa ce kadai mace, ita ce kuma Kawai idan an so ba a fadiba. Duk abinda Salma ke so shi yake’ so, wanda kuwa ta nuna bata so nan take yake jin tsanarsa, saboda haka ya zama tamkar da gaske sabon Adamu aka sake fil Ba wancan mai tsanar salma ba kuma ba wancan mai son — Husna a Kirji ba. Salmanu kansa ya fahimci haka, amma dai ya shanye ba ya tanka masa maganar Salma, ko shi ya kawo masa ma sai ya tankwabe shi da cewa, “Yanzu Salma iyalinka ce, bai kamata mu dinga hirarta ba” Da wannan hujjar suka dauke hirar Salma a tsakaninsu, iyakaci in sun hadu su yi abinda. ya hada su su watse. Sai dai manta Husna da Adamu yayi ba Karamin daga wa Salmanu hankali yake ba, .
musamman in ya tuna labarin da Adamu ya ba ‘ shi na yadda suka yi rabuwar Karshe da Husnan, da alwashin daya ci mata na aurenta nan da wata biyu tun a ranar. .
Wannan ya sa ya cigaba da sake-saKen ta yanda zai bullowa wannan bahagon lamarin, har ya fara jin cewa a wanna gabar zai yanke Www.bankinhausanovels.com.ng
_ danyen.hukuncin da zai nuna wa Salma
. iyawarsa. .
*****
Sana’ar bokanci ta cigaba da kawo . manyan kudi, don haka Adamu bai yi gigin
. barinta ya zauna a shago ba, kawai sai ya nemi yaro ya dora shi jira, shi kuma ya cigaba da gashi. .
Abinda ma ya takaice shi shi ne, Salmanu ba ya sakar masa kudi yayi yadda yake so ko .’ dan farantawa Salma rai.
Zasu raba kudin rumi-rumi su uku bayan sun ware na sallamar yaran. da ke yi musu hidima da kuma na siyayyar kayan aiki, amma
. kawai sai Salmanu ya daka wa na Adamu
wawaso, ya sunna masa abinda bai taka kara ya ‘ karya ba, ya ce wai zubin adashi suke, kuma wai kantinsa ya isa ciyar da Salma dai ba wata ba. Adamu ba ya son wannan dabi’ar, amma – ‘ dayake ba ya zargin Salmanu da cutar kudi sai yake shanyewa, yana da tabbacin ko ba dade ko ba jima sai ya fito masa da kudinsa. ~
+++++++++++
Sati daya, biyu, uku, hudu, Husna bata ga Adamu ba, tun tana basarwa musamman daidai lokacin da ta ji labarin ya tare da amaryarsa a_ – unguwar Dorayi, ta ci kuka ta ci ciwon ranta ta matse ta koma ta cigaba da zaman jiran ya . waiwaye ta tunda wata biyu ya dibar wa kansa na aurenta, har aka kusa wata daya da rabi ta fara debe tsammani, juriyarta kuma ta sare. Ta cigaba da damuwa ta cigaba da kuka kuma ta -cigaba da ramewa tare da lissafin ta inda zata _ bullowa wannan mugun ciwo daya sarKe ta.
– Rannan dai da ta ji zuciyarta na neman bugawa kawai sai ta wanki Kafa ta tafi gidan fawarta Amina domin neman mafita.
Ta sami Amina da maKociyarta Jamila suna hira cikin farin ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Amina na ganin Husna ta hau salati da sallallami,
“Wallahi yanzu nake zancenki Husna, ai kawai ki zo mu fasa mu ma mu shallo Adamu”
Husna ta zauna kan kujera jagwaf tana bin su da kallon rashin fahimta,
Amina ta shiga yi mata bayani tana nuna Jamila, .
“Kin tuna ranar da jamila ke tatsuniyar son
” mai gidanta ya sai mata mota yana cewa wai
bata da hankali?” so
Husna na dariyar yaKe ta ce,
“Na tuna, yanzu zai siya ne don ta yi hankalin?”
Suka kwashe da dariya su duka ukun.
Jamila ta mika wa Amina hannu suka tafa sannan ta dubi Husna tana kada mata mukullin mota, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Tun yaushe na yi hankali, Surajo ya ji . Wuya jiyan nan sai ga sabuwar mota ya samfa min” Husna ta zamo daga kujera tana zaro ido cikin mamaki, . “Da gaske? To duka kika fara ne ya gane in bai sai motar ba ba zaki warke ki bar dukan ba?” Suka sake tuntsirewa da dariya. Jamila ta ce, “Wanda: ya fi shi Karfi na sa yayi masa. mahangurba”™Har yanzu Husna na cikin dokin jin labari, ~ ta ce,“Don Allah ku fada min ku bar wana-ni” . Amina ta hau yi mata bayani. “Wallahi wani sabon boka aka samu mai aiki kamar yanka wuka, saboda tsabar son mota na Jamila sai da ta dangane da wajensa, ba a yi sati biyu ba kuwa kin ga har ta yi motar” _ Husna ta shiga gyada kai cikin mamaki da sha’awa,
“Kai! Ku dama akwai malaman Allah da gaske a duniyar nan?” ‘ Jamila ta kada kai, –
– “Wallahi ni ma abinda na yi ta cewa kenan Husna, kawai kasada na yi na je, amma sai ka yi ta zuwa wajen wasu asirin sai ki ga kamar an shuka dusa”Www.bankinhausanovels.com.ng
. “Wallahi tallahi” .
In ji Amina, Sannan ta dubi Husna ta zarce da cewa, “Wai gobe zata je yiwa bokan godiya, shi ne na ce me zai hana mu bi ta muma mu kai tamu bukatar? Ke ki kai Adamu, ni kuma zan kai Kamalu a kama min‘shi a hannu, wannan shegen kallon bal din nasa na dare a hana shi, don ni in akwai abinda na tsana a duniya ba zai wuce kallon bal din ba”
. . Husna ta ji wani dum! Kamar abin bai kai zafin haka ba, duk da ta gan son Adamu ba sanyi ne da shi a zuciyarta ba.
“Kar ki ji wani dar Husna, duniya sai da Kundumbala, ki daure ki Basar ki nemi cikar ~ burinki, Salman banza da zata hana ki samin_. . abinda kike so?”
Amina ta Karfafa mata gwiwa da wannan zantukan — . . Sai kawai ta miqa wuya. _ “A wane Kauyen bokan yake?” Ta tambaya. Jamilace ta amsamata “Nan nan Zawaciki yake, hanyar’ . Panshekara” A sanyaye Husna ta ce,To Allah ya kai mu, zan je. Karfe nawa . _zamu tafi?” Amina ta dubi Jamila. A “A motarki fa za mu; saboda haka ki zaba mana lokaci” , Kai tsaye Jamila ta amsa, “Mujeda la’asar’ -Allah ya kai mu” . Husna ta amsa asanyaye. Www.bankinhausanovels.com.ng
**********
Da la’asariyyar ranar yau su Adamu na sanya ran zuwan wani gagarumin dan siyasa_ – mai son tsayaawa a takarar dan majalisar taraiya.
kula da kyau fa! Yau muna buKatar ” takatsantsan don kar mu yi abinda kwabarmu zata yi ruwa, kudi muke so.. kun gane?” In ji Oga Salmanu lokacin da suka sami ’ wayar cewa yammar yau ko ta gobe Honorabul zai ZO. _ “Wane .sirrin damfarar zamu gwada masa?” a Adamu ya tambaya. Salmanu ya dan yi shiru alemar tunani. * Karaf Tanimu ya ce, “A yi masa na alkalamin nan, na ga yana dan rudar da kwanya”’ – Salmanu ya bigi kafadar Tanimu, “Yauwa! Ka kawo shawara mai kyau,a_ nemo, alKaluma a fente” – “Adamu ya tashi da sauri ya shige cikin zuwa taskar ajiyarsu. ya bar Salmanu da Tanimu, -Tanimun na yi wa Boka Salmanu bayanin tarihin Honorabul, — nasarorinsa, — faduwarsa da kuma. abokan adawarsa. ‘ _. Adamu ya jima sannan ya fito, “Akwai alaluma, amma babu Kusoshi”.
Salmanu da Tanimu suka dafe kai saboda. . jimami, kasancewar ba a samun Kusar kusa da – su har sai sun hau Mashin sun je Sabon titi. . –
Adamu bai shiga cikin jamamin ba, kawai sai ya sa kai ya fice yana cewa, :
‘ “Barina samo ta yanzun nan nadawo” : Salmanu na kiransa bai saurare shi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan dalilin ya bana Adamu da Husna * haduwa a wajen da dukkansu ba zasu so ganin ~ juna ba.
Tanimu ya shige ciki domin zama kujerar ‘Adamu ko da zata kama ayi muryar aljanu.
Salmanu kuma ya zauna a kujerarsa ta babban Boka. . ~~ –
Kasancewar sun saka dokar ba a shiga mutum biyu, Jamila ce ta fara shiga, ta yi godiyarta ta kuma bayar da dubu goma na goro
– ta fito.
Husna ce ta biyu. Ta shiga da alamun
tsoro da rashin sabo, Kafarta sai rawa take jiri – Www.bankinhausanovels.com.ng
– kuma na kwasarta, dole ta zube a Kasa ba tare da ta Karasa kan buzun da aka tanadawa masu ziyara ba. Yadda take jin dukan zuciya Salmanu ya ji fiye da haka na ganin Husna a gabansa a matsayinsa na boka ita kuma a matsayinta na mai buKata a wajensa. To wacce irin buKata? ‘ Abinda ya fi damunsa da sa shi faduwar gaba – kenan sai kuma fargabar kar Adamu ya dawo ya tarar da ita. Da sauri ya fara shirya ta inda zai Burma – ta. Ko Salmanu bai ci wani Make up ba da – -wahala Husna ta gane shi a yadda ta yi Kasa da kai tana jin kamar Kasa ta dare ta shige. Ba sai _ wani ya bude baki ya fada mata ba, ita da kanta – tana jin ta yi abin kunya, wato zuwa gurin boka a kan saurayi.- Fahimtar hakan da Salmanu yayi ya bashi tasa nutsuwar ta shirya yadda zai shammatota. “Kin zo akan maganar saurayinki Adamune?” Da sauri ta dago kai ta dube shi saboda – mamaki, amma kamar an cije ta, da sauri ta yi – kasa da kai cike da jin nadamar kallonsa, to — mutumin da ba ka kalle.shi ba ma shi ya kallo – abinda ke faruwa a duniyarka, ina ga ka kalle shi? Ta dai cigaba da gyada masa kai alamar Eh” : : , Ya dan shaki iska sannan a kasaice ya ce: mata, , ‘ “Ba ya ce ki jira shi nan da wata biyu ba? Ai yana can yana miki tanadi Hajiya” ‘ Husna ta ji wani yakini da Karfin gwiwa ya dake ta, cikin rawar baki ta amsa,
“Ai wata biyun aure yake nufi, dauke + Kafarsa gare ni na nuna rashin damuwarsa da ni . Malam, ni kuma ji nake ba zan iya rayuwar da. – babu shi ba, don Allah ka taimake ni…” Ta wuce da goge Kwalla. ‘ Ta yi shiru, Salmanu yayi shiru saboda rashin abin fada. . So Ita ta sake Magana cikin hawaye, Ina zargin ma ni asiri ya yi min, ban san ana son mutum irin haka ba, Malam da tunina – cire shi daga sabga ta wallahi” Tausayinta ya Kara damun Salmanu, ya .. yarda Adamu ya cuci Husna,.shi ya dinga zazzafar addu’a kan soyayyarta da samunta, gashi Allah ya amsa masa shi kuma ya juya — mata baya ya bar ta da wahala. – Www.bankinhausanovels.com.ng
~ Dole dai ya kakaro abinda zai Karfafa mata gwiwa lokacin da ya janyo kasko ya fara yafa turare. “Ki kwantar da hankalinki ba zai wuce watanni biyun da ya dibar miki ba, zai zo ya baki mamaki, ni na yi miki alKawarin sai kin juya Adamu a tafin hannunki, sai kuma ya ninka miki son da kike masa, amma-ba wani asiri da yayi miki. Husna ta sake jin wata nutsuwa a zuciyarta, ta fara godiya ba KakKautawa. Tamkar Www.bankinhausanovels.com.ng Salmanu ya saki fitsari a wajen lokacin daya ji tsayuwar mashin din Tanimu da Adamu ya fita da shi a harabar gidan gonar, . ya tabbatar kuma hanyar da zai biyo ko inda zai labe dole wadda’ zai iya ganin Husnace. Da sauri ya mike daga zaune ya shige _ cikin dakin yana cewa, : . “Ina zuwa, bari na kawo miki wani turare – da zaki zuba a cikin lallen Kunshi” . – Bai jira amsarta ba ya shige. ° . Ya yayimo Tanimu da ke lafe a duhu da tiyo a baki yana jiran alamar da zai saki muryar ~ aljanu, ;
“Maza je ka ka tare min Adamu kar ya shigo gidan nan, bitabaya?” = – – Tanimu ya tsaya yana, radar neman ba’asi – amma sai Salmanu ya tunkuda shi sai da ya kusa kifawa, dole yana tashi bai nemi wani . ba’asin ba ya fice ta Kofar bayan,; amma tuni Adamu ya kafe mashin cikin zafin nama ya _ tunkari masaukin bakin da suke jiran shiga . . Wajen boka Salmanu. Amina da Jamila na. zaune suna dako, kuma yana wuce su Husna zai tarar gaban Boka Salmanu. A nan zan dakata sai mun hadu a littafi na uku. MAIMUNA IDRIS SANI BELI
Www.bankinhausanovels.com.ng